Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bari mu zo. Yanzu kuma muna ƙauyen Fembeguwa a zaune, saboda tsoron zama cikin birni gudun kada a sa a kamo mu."

Na kalli wacce ke kusa da ni, "A tafi da su wajen Sarkin gida ki ce baƙina ne a basu ɗakuna biyu, kowacce da mijinta. Ke kuma ki sa a basu komai da komai,ki tabbatar sun ci abinci.”

Na juya ga su Mansura, "Ku je a baku masauki zan neme ku in kun huta."

"Mun gode. Amma za mu koma mu ɗauko yaranmu."

"Kun haihu ne?*

"Eh, yaranmu bibbiyu."

"To shi kenan, amma da mazan nan naku su je su ɗauko su."

"To Gimbiya, haka za'ayi." In ji mazan.

Daga nan suka miƙe,. Har sun kai ƙofa na kira Sa'a.

"Ki ce wani ya kai su su ƙwaso har kayansu."

"Tanko direba ko Brown?"

"Duk wanda aka samu."

Suka juya suka tafi suna ta godiya.

**** *** ****

Yau garin Jos ya ruɗe saboda hidimomin bakukuwa ga taron sunana da nake yi, wanda gaba ɗaya taron gidan mu ake yin sa. Duk girman gida irin namu, wanda zai kai kilo mita uku, amma cike yake da mutane. Get uku ne a ƙofar shiga, kenan wacce ke kallon kudu a kowanne zagayen get gidaje goma ne na fadawa.

Get ɗin farko yaran gida ke zaune a cikinsa, kenan masu yi mana hidimomi da yi wa dawaki, fulawoyi. Kai aikin gidan gaba ɗaya. Get na biyu kuwa ƴaƴan dogarawa, wasu daga cikinsu, wanda shi ma gida goma ne. Get na uku ne ke da gida ashirin na dogarawa.

Idan an shiga daga ɓangaren gabas,ƙaton falo ne ƙwaya ɗaya, sai ɗaki ɗaya ƙaton gaske,an yi shi ne domin saukar Mai Martaba Sarki na ɗaya, sai ɓangaren yamma kuma barandun sama ne aka yi guda huɗu. Kenan kowanne ɓangare da aƙwai baranda sai ƙaton fili daga tsakiya,an tanade shi ne saboda wani gagarumin taro kamar na yau. Filin dai kamar filin wasan ƙwallon ƙafa (Football).

Ɓangaren Arewa ƙaton masallaci ne a cikin shi,aƙwai Islamiyyar yara da ta manya, wanda mata su yi da safe, da yamma maza su yi da daddare. A nesa da masallaci aka yi gidaje biyar. Limamin masallacin ke da ɗaya, ragowar huɗun malaman Islamiyya kowanne da matarsa da ƴaƴansa.

Idan aka iso ƙofar shiga gidan daga yamma kaɗan,ƙaton asibiti ne mai ƙunshe da ɗakuna taƙwas na jama'a kenan, sai ɓangaren manya aka yi wa likitoci hudu kacal. Dukkan gidajen ɗakuna biyu ne da falo a cikin shi, sai kuwa ɗakin samari a bayan gida, wanda yake tare da banɗakinsa.

Manyan falo taƙwas ne a gidan, uku na shi, uku nawa, dukkansu na karbar baƙi ne, amma ƙofa biyu ce ta shiga gidan da ƙofar shiga falona, sannan da ta shiga nashi falon.

Ɗaya cikin ɗaya ne, sai in da muke son zama. Ganin baƙin idan aka fita daga falukan namu da aƙwai wani fili a tsakiyar falukan, wanda ya ƙunshi ƙofofi biyu. Ɗaya ta shiga falon sa, koma in ce sashen shi, ɗaya kuwa ta shiga nawa sashen, amma idan ka shiga falo ne kowa a farko shine falukan mu mu da yaranmu. Kenan personal falon mu,amma kuma daga cikin falon kowa zaka iya shiga na ɗaya, kenan haɗe muke waje ɗaya, sai dai kowa da ɓangarensa.

Ɓangarena ɗakuna baƙwai ne, amma ɗaya ne nawa, sai na yara ɗaya, na ƙwamfuta ɗaya. Haka nan yake ba kowa a ciki,an yi shi ne kawai saboda baƙin a na kusa. Biyu kuwa na masu kula da ni da gidana da ƴaƴana, wanda su nasu kamar an yi su ne daga gefe ɗaya tare da banɗakinsu har da ƴar barandar su ta shan iska.

Nasa ɓangaren ɗakuna biyu ne kacal, ɗaya nasa, ɗaya na ƙwamfuta (Computer). Tsayawa lissafa abin da ke cikin gidan ma asarar baki ne, saboda ya dame gidanmu na farko sau ba iyaka. Idan kuwa an fita daga cikin ƙofar shigowar kuwa,nan kicin yake da sito, kenan ƙofar shigowa falona na cikin gida, amma na taryar baƙi, saboda ni biyu kenan cikin gida, ɗaya kuwa na cikin gida na karɓar baƙi, ɗaya ƴan gida ko mabuƙata.

In an zagaya bayan gida, barga ce, kenan ɗakuna ɗai ɗaya da banɗaki a jere guda taƙwas na ma'aikata ne masu yin abinci mata, da kicin ɗin su ƙaton gaske na yin abincin ƴan barga da duk wani baƙon da zai yi sallama, da wajen ajiye ajiyensu na kayan abinci.

Gefensu daga ɗan nesa kaɗan gidaje ne uku a kulle,su ma ɗaki biyu da falo ne, bayan gida duka kuwa ƙaton lambu ne cike da kayan marmari, waɗanda ba rani ba damina, duk kullum da ƴaƴan a jikinsu, amma tsakiyar lambun ruwa ne ke gudu ta ko'ina ka waiga za ka ga duwatsu, ballantana ma cikin lambun.

Yau ne aka ɗaurawa Ahmad aure shi da Idris ƙannan Yarima kenan, waɗanda suka auro ƴaƴan daga wajen garin nan. Ahmad ɗiyar Daraktan (Director) ce a Katsina, wanda suka haɗu da yarinyar a ƙasar Spain,inda ya yi karatunsa, wanda ita ma karatun ya kai ta. Duk da ita ba ta gama ba, saura shekara biyu, wannan yasa ma in an gama bikin can za su koma da zama har sai ta kammala, shi kuma zai yi wani karatun tattalin arzikin ƙasa a matsayin digirinsa na biyu.

Shi kuwa Idris ɗiyar Sarkin Dutse ce ta jihar Jigawa. Yara ƙyawawa, Fulanin asali ƴaƴan Sarkin adalci na ƙasa. Ana cikin hidimar biki ne na ga Mabaruka, muka gaisa. A nan ta ke bani labarin ta yi aure har ta haifi ɗan ta namiji yana gida ta baro shi. Nan ta yi mini barka da arziƙi.

**** *** ****

"Kai na gaji!”

Na ce daidai lokacin da na ƙwanta cinyar Yarima, wanda ke lallaɓa Nasir ya yi bacci. Ya waiga ya ja kunnena wai faɗan zan tashi Nasir. Na yi ƙara, haka kuwa ya sa ya tashi, da guduna na ruga saboda na san Honey zai iya cizona a kumatuna ko ma na sha mintsini.

Ya cije leɓe, "Zan rama ne."

Na yi masa gwalo. Ya ɗauko Abdul Nasir ya biyoni a guje. Abin ka da ƙaton ɗaki, sai na dinga zagaye a ciki. Kafin ya kamo ni jakadiya ta yi sallama. Na tsaya tare da kallon agogo. Ƙarfe sha ɗaya na dare,me jakadiya ta zo yi yanzu ɗakin mijina?.

Kafin in gama tunani Yarima har ya bata izinin shigowa. Tana shigowa ta yi saurin zama ƙasa.

"Allah ya ja da rai an iso da ita, tana ɗakinta.”

Ya yi shiru ta kai minti uku, sannan na ji ya yi magana.

"Ki ce ina yi masu sannu da zuwa. Bayan minti ashirin ki kawo ta nan ta gaishe da Yayarta,su san juna."

Na yi tsaye, amma ban fahimci komai ba, har jakadiya ta gama kirarinta ta tafi.

Inda na ke tsaye ya iso yana dariya, ya kama ni, "Na kama ta! Na kama ta!! Nasir mai za mu yi mata?"

Yasa hannu ya mintsini kunci na ɗaya.

"Tsaya don Allah Yarima,wai wacece aka kawo? Ban fahimci maganar ku ba?”

"Za ki gan ta yanzu.”

"Wace ce?"


######
[3/2, 15:46] Ummi Tandama😇: *ƘASAITA BOOK 3*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 13


"Amaryar ki. Ko kin manta ne?"

Na ɗauki hannunsa mai shafa kumatuna na ajiye gefe. Na karɓi ɗana daga hannun shi, na tafi na zauna bakin gado. Tun da na ƙurawa ƙasa ido ban kuma ɗagowa ba. Magana ba irin wacce Yarima bai yi mini ba, ballantana in kalleshi. Babu abin da Yarima bai yi mini ba, amma ko motsi ban yi ba. Har cakulkuli ya yi mini,amma motsi na kasa yi, alhali abin da ke sani ƙarar wasa da ihun neman ceto,idan Yarima na yi mini shi.

Ganin na zama mutum-mutumi yasa ya ƙyale ni ya koma saman kujera ya ƙwanta yana ta ƴan surutai.

"Ni ki ka ƙyale? Mijinki ne fa, shi kenan na gode."

Ya samu ɗan tsayin lokaci, sannan na ji sallamar mata. Inda na ke zaune na ji gabana ya faɗi.

"Ku shigo jakadiya."

Jakadiya na gaba ragowar na biye da ita har gaban wanda ya basu iznin shigowa ɗakin.

"Barka da dare?"

Haka na ji an ce cikin siririyar murya.

"Barka da zuwa amarya."

Jin an zauna kusa da ni yasa hankalina ya dawo dai-dai.

"Yasmin." Na ji an ambaci sunana. Ban iya amsawa ba. Bai jira na amsa ba ya ci gaba.

"Wannan ita ce ƙanwar ki Asabe, daga yau kin zama babba a gidan nan, saboda haka ki riƙe girman ki."

Ya juya ga Asabe ya ce, "Asabe."

"Na'am, Sarkin Sarakuna."

A take na ji wasu abubuwa guda uku sun tsaya a ƙirjina.

"Wannan ita ce Yayarki,kin gan ta, aure ne tsakanina da ita, ina son ta matuƙa, ita ce sirrin zuciyata, ita ce ƘASAITAR jikina, saboda haka kiyi biyayya a gare ta,idan kuwa na samu akasin haka, zan saɓa miki matuƙa."

"Yasmin ga Asabe.”

Na ƙi motsawa.

"Asabe ga Yayarki Gimbiya Yasmin.”

"Allah ya ja da ran Gimbiya Yayata.”

Na ji an dafa mini ƴan yatsun ƙafa ta.

Wannan ya ba ni damar matse jaririna a jikina, har yasa ihu.

"Yasmin,kawo shi. Ke sakar shi kin matse shi da yawa. Jakadiya ku tafi gani nan zuwa."

Ina jin fitar su jakadiya, sai na ji abubuwan nan uku sun danne mini ƙirji,da ƙyar lumfashina ke fita.

Ina jin shi yasha kokawar ƙwaƙule Abdul-Nasir da ke ƙwalla kuka, amma na hana. Ina ji ya hayo gado sosai, ya bi bayana. A daidai kunnena na ji yana magana, tare da zuge zub ɗin rigar baccina.

"My love, kada ki sa zuciyata ta fashe mana,ki yi tunanin alƙawarin da ki ka ɗauka a Kaduna, wannan alƙawari sai da na nanata shi a gaban Sarki, saboda hotunan da aka kai masa da kaset, na san ba ki san ko waɗanne ba ne. Waɗanda ki kasa aka yi a mota lokacin da ki ka tsare ni, lokacin da ki ka sa aka kai ni a hotel na yi ƙwana uku ban ga ƙyakƙyawar fuskar ki ba."

Ya saɓule rigar jikina yasa hannunsa ta bayana ya rungume ni.

"Yasmin ba zan iya son kowacce mace ba sai ke. Please ba ni Abdul ki tuna wahalar da muka sha kafin mu same shi.”

Lallashin yasa na miƙa masa Nasir,sai na ji yana ta lallashin shi, amma ya ƙi yin shiru. Ya zagayo ya ɗora shi a cinyata ya zaro mama ya saka masa a baki. Yaro ya dinga sha, wannan yasa na saka kuka.

"Me ye na kuka Yasmin?"

"Ɗanka ne fa." Na cuci kaina dana tuno abin da na sa aka yi maka a hotel.

Haya na ɗauki wata karuwa, aka ba shi baliyan maganin bacci, ya sha, shi ne ta cire masa riga, ita ma ta cire ta ƙwanta a ƙirjinsa, shi ne nasa aka ɗauke su hoto. Haka sai kuma muka haɗa kai da ita a kan ta san yanda aka yi aka haɗa wannan kaset ɗin. Haushi takaici suka tarar mini.

Ya tsugunno gabana, "Honey zan tafi" na yi shiru.

"Ba za ki yi mini addu'ar dawo lafiya ba?"

Wani ƙwarin gwiwa ya zo mini da na tuna abin da Aunty Salwa take gaya mini a kan idan namiji na son abu,ka nuna ka fi shi so, haushi ma ka ke bashi.

"Na ji kin yi shiru?"

"Yanzu zan yi magana ka riga ni. A dawo lafiya, a gaishe da amarya.”

"A'a, sai dai ki zo mu je ki raka ni.”

"Ba damuwa, jira ni Abdul Nasir, ya kammala sai na raka ka. Ka sa manyan kaya mana."

"A'a waɗannan ma sun isa,gudun kada ta sha wahala wajen tuɓe mini."

Na harare shi kaɗan, "Ni tashi mu tafi."

"Ba komai in na je zan gaya mata,in ce harara ta ma ki ka yi. Amma bayan kin gama kuka."

"Ni ba kai nayi wa kuka ba, kaina na yi wa kuka. Ka ga a daina wannan maganar, tashi mu je. Amma gaskiya sai an gyara ka."

Na miƙe na ajiye Nasir,na isa na ɗauko wata sabuwar doguwar rigar hutawa da alkyabba na iso gaban shi. Yana tsaye na cire kayan jikinshi na sa masa sababbi, ban da turare da na dinga fesa masa.

Ni ce har da farar hoda sai da na shafa masa, saboda ya ƙara fitowa. Kallon mamaki na ga yana yi mini. Na ɗauko takalma na durƙusa na ajiye masa. Ina ɗagowa zan juya ya riƙo hannuna, madadin ya yi magana, sai kawai na ga ya haɗa ni da jikinsa, haɗa kumatuna ya yi duk biyun ya ɗago su sama, sai kawai na ga ya haɗa bakina da nasa yana tsotsa kamar zai mayar da ni ciki. Har wani jikinshi ke rawa.

Na ɗago kansa, "Lafiya Yarima?" Bai iya amsa mini ba. Zame jikina daga gare shi na yi, na tafi cire rigar baccin jikina, ina faɗar.

"A yi rakiyar ango da rigar bacci?" Sai da na tabbatar ni yake kallo, sannan na saki rigar baccin ƙasa, daga ni sai ɗan wando, sai kuwa rigar mama, sannan na ɗauko kaya na fara sakawa.

Jin an riƙe mini hannuwa, waɗanda ke ƙulle zanena ta baya, shi yasa na ɗan yi alamar na tsorata.

"Au! Da kai ne har ka bani tsoro?" Na juya zan cigaba, ya riƙe ni.

"Yasmin kin daina sona ne?"

"Me ka gani?"

"Ga ni nayi murna ki ke yi zan tafi in barki."

"Ba haka ba ne ba,dama ai yanzu dole ne so ya ragu, tun da mun zama mu biyu, balle ita fa ganinta ka yi ka ce kana son ta. Ni kuwa fa,ƙyauta ta aka yi....."

Ya zagayo gabana tare da nuna hankalinsa ya tashi, ya riƙe kafaɗuna ya zame hannayena da ganin yanda yake yi ya rasa yanda zai yi, ya ɗauko rigar da alkyabba ya miƙo mini.

"Sa ka zo mu tafi. Ya juya ya ɗauki Nasir,ni kuwa a hankali na saka kayana, ganin na cika nawa, ya zo ya kama hannuna, hannu ɗaya na tallabe da Nasir.

Kusan in ce ja na ya dinga yi ba ma tafiya ba da sauri. Bai zame ko ina ba sai ɗakin jakadiya, wanda yake sashen gidana.

"Jakadiya." Kiran da ya yi mata kenan. Ta fito da sauri tare da kifawa ƙasa da sauri.

"Ga ni Allah ya huci zuciya, daidai nake da a hukunta ni idan har an same ni da laifi."

"Mansura! Ina Mansura?"

"Tana ciki?"

"Kira ta.”

Ta miƙe da saurinta ta shiga wani ɗaki,a inda na ga ta shigo da amaryar da aka kai min ɗakina. A tsaye na yi wa kaina tagwayen tambayoyi. "Shin Mansura ya aura? Ina mijinta? Amanata suka ci ko me? Ai kuwa...."

"Jakadiya ya aka yi?"

"Allah ya ja da ran Gimbiya,dama haɗa baki muka yi da Mai Martaba Yarima, ya ce a rufawa Mansura kaya a kai masa ita domin a zolaye ki, saboda ya zamo jan kunne a gare ki na ƙin daina yiwa mijinki alƙawarin kin amincewa ya yi aure.”

"To kin ganta nan, nuna mini ta yi bata sona yanzu don na yi haka."

Na san halin Yarima a kaina, wannan yasa na yi ƴar dabarar dariya ni kuma irin ta mu ta manya.

"Jakadiya, nunawa ya yi ni yanzu an gama da ni. Ni kuwa na nuna masa ni kuma yanzu nake yayin kaina, shi ne ya ji haushi.”

Ya ɗago hannu zai ɗan kai mini duka, na goce. Aka sa dariya, shi ma sai na ga ya yi dariya.

"Jakadiya haɗe mini kai ku ka yi da Gimbiyar taki. Zan rama, sai na yi maku bazata.”

Muka yi dariya, sannan ya juya.

"Sai da safen ku, ga angon ki nan na kawo muku har da ribar ɗa."

"Wallahi." Ya faɗa. Ni kuwa na juya. Bai shigo ba sai da har na ƙwanta. Yana shigowa ya wuce gadon Nasir ya ƙwantar da shi, sannan ya zo ya zauna gefen gado.

"Yasmin."

"Ina jin ka.”

"Taso nan." Na mirgino na sauka na tsugunna gabansa.

"Matso." Na matsa.

"Ɗago." Na ɗago. Yanda yake tamkar an yi durƙushen raƙumi, kunnena ya kama har da, ƴar ƙara na yi masa.

"Daga yau kada in ƙara jin kin ce ai ba ni ne na gan ki na ce ina son ki ba. Kina jina?"

Na ɗaga kaina.

"Kada kuma ki ƙara cewa wai kin daina sona,in na ƙara jin haka, duk hukuncin da na yi miki ke ki ka ja. Yanzu ma don ina tausaya miki sati biyu da suka wuce kin sha wahala da yawa, da sai na kai ki ƙara wajen Daddy ya yi mana Shari'a."

"Na tuba,saboda Daddy na yanzu ya fi sonka da ni. Kada kasa ya zane ni da bulala."

"Honey,an ruɗe an ga amarya."

"Dole in ruɗe. Ka yi tunanin yanda ka ke nuna mini so,ƙauna a gaban kowa,yau in wayi gari in ga ana yiwa wata irin shi. Ka san yau da da gaske ne,ƙila in ƙarasa mutuwar da na kusan yi rana....."

"Kada ki tayar mini da hankali. Yanzu a bar wannan maganar." Ya ɗago ni ya zaunar da ni a cinyarsa.

"Ni yanzu tunanin da nake shi ne me zan yi wa Jakadiya da su Mansura?" Na yi ɗan shiru kaɗan.

"Honey akan me?"

"Na ɓangaren ƙyauta."

"Eh, gaskiya, amma ni na san Jakadiya ba za ta bar gidan nan ba, da zata iya barin shi da sai a bata ƙyautar gida cikin gari ta koma ita da ƴaƴanta da jikokinta."

"To tun da kin yi wannan tunanin,to ko mu samu gida mu saya mai ƙyau babba a baiwa ƴaƴanta su tashi daga gidan sarauta a basu jari. Ita kuma a ɗebi bayan gida a yi mata gidanta mai ƙyau a zuba mata komai."

"Haka za'ayi Mai Martaba na biyu. Su Mansura kuwa na san har ka gama tunanin yanda za ka yi dasu. Abin da ya rage ni,ni kuma ina son zuwa gidan Yaya Ahmad a can Spain in ɗan huta,ka ga har na gaido kakannina,in gano iyalinshi ma."

"Ki bar wa?"

"In bar ka, ka san Sarki ba yawo,wa zaka barwa mulkin?"

"Ki yi shiru ko in gama ki da Mama."

"Gaskiya ni....”

Sai kawai na ga ya ɗauki waya. Na yi saurin alamar ƙwacewa, ya haye gado. Na bi shi sai na ji yana cewa.

"Barka da dare Mama.... lafiya ƙalau.... ga ta nan dama ita ce take...”

"Barka da dare Mama."

"Lafiyar shi lau, ga shi can yana bacci."

"A'a dama cewa na yi bari in shigo mu gaisa."

"To, to, insha Allah sai anjima.”

"Mama,Mama.” na yi saurin rufe bakinsa.

"Na tuba na haƙura."

"Kin rufawa kanki asiri da yanzu kin sa na koma ƘASAITA ta in dinga ja miki rai.”

"Me ka ce?"

"Cewa na yi ƘASAITA,a waje ake yin ta ba a gida ba wajen iyali. A gida Honey ita ke da ƘASAITA. Ni kuwa sai in zama shalelenta."

Yanzu kuma sai dai in yi miki godiya game da shawarwari da haɗin kai da ki ka ba ni har na zamo na samu ɗaukaka ga jama'a da mahaifina, ga talakawa, yanzu komai ya wadace su ba sai na tsaya jiran gwamna ko shugaban ƙasa ba. Na gode da shawarwarin ki.”

"Tsaya ina da magana."

Ina jin ki."

"Amma na gama haihuwa haka nan?"

"Ki ɗan ƙara ɗaya."

"Ni dai a'a." Yana dariya wai ganin yanda na yi. Ya rungume ni.

"My love,my life,my body,my soul. Na gode Allah da ya ba ni ke."

Ya janyo ni muka ƙwanta tare da kashe fitilar ɗakinmu. Addu'ar ƙwanciyar bacci ita ta zamo murfin maganarmu, sai dai muka yi wa junanmu addu'a a zuciya, ta Allah ya taya mu riƙon junanmu.

ALHAMDULILLAH!
Na gode
Mai ƙaunarku a kullum:-
AUNTY MARYAM KABIR MASHI.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment