Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai Abdul ya koma gida . Hakan yasata kullum taba cikin kyewa .


Batasan da mgnan Aureb ta da Abdul ba sai ana saura kwana uku daurin Auren su ,sannan Oumma 6ingel ta cire kunya ta fadi mata . Tayi murna batayi murna ba ,don batason rabuwa da Oumman nata .


Tun daga wannan lokaci lela bata kara ganin Abdul ba har ranan daurin Aure . Tun ana saura kwanaki ukunne ake mata adon fulani hadi da kimtsata da gyaran lalle ...gashin nta kam yasha gyara anxuba man shanu.

Aranan Daurin Aure ne lela tasan ita wacece da salin ta ,kuma anan takejin suma dangin Abdul din sun san komai .

Mahaifiyar Abdul ce tace batason komaj na dangin Amarya itace uwar amarya ,ita su zasuyi mata komai na daki . Don sosai tayi murna da wannan Auren duk da yan tsegumi da masu son Abdul din yayan Aminan ta ,suna dariyar ya auri bagidajiyar bafullatana. Ciki kam harda Nabila wacce ta dauki aniyar ganin bayan Lela a gidan Abdul.


Sadeeq,Areef sune angwaye don sunfi angon dauki ,tunda shine yafara aure a cikin su .


Shigar fulani akayi mata na bakakken sak'i wanda da yammaci motoci suka taho don daukar Amarya . Kai munga duniya abun da ba'a ta6a ba ,don harda Mahaifiyar Abdul wato Hajiya Sa'a aka zo daukar amarya .

Sosai Lela tayi kuka na rabuwan ta da Oumma 6ingel wanda koda Suka isa garin Adamawa gidan Mom sa'adah aka wuce da ita.


Anan ne tasa aka fara yi mata gyara na musamman masu gyaran jiki dana Amarya .wanda lokaci daya laila ta koma kaman wata wayayyiya wacce bata san ma ya rayuwar Rugar take ba.


Abunka ga fillo da iya daukar wanka da ado idan an masu iyawane fa da sauki kam.


Riga da skirt aaka bata tasa na lace mai launin pink da cyan colour .

Makeup kadan akayi mata irin ta amare hadi da bata takalmi mmai tudu kadan da mayafi aka yafa mata.

Yan uwa da kawayen Mom sa'ada da aka zuba ido aga amarya akoma ayi gulma da dariya ,ganin Laila yasa su duka tsuke baki wasu suna kus_kus din cewa dama ashe ba yar kauyen rugar bace .


Kila dangun ta ne acan ,haka dai sukayi ta gulman su duk suka darara. Wanda tun kan a fita da laila nabila ta rike hannun ta gam tana manne mata tare suka nufi moton da zaa kaita gidan Ta.


Mom sa'adah ce gyefen ta ta sanya ta moton ,hadi da rufowa...ita dai idon lela a rufe yake har motocin suka fara barin gidan Hajiya Sa'a.

Ji tayi an riko yatsun hannun ta hadi da matsasu a hankali kamshi mai dadi ya mamaye cikin motom .


A hankali ta bude idon ta hadi da kallon mazaunin drivern Areef tagani yana driving cikin shigar sa ta manyan kaya kaman shinr angon ,sai gyefe guda Sadeeq adayan barayin .


Juyawa tayi ga gyrfen ta mazaunin bayan ta anan ne taga Gogan nata yana sakin mata kayataccen murmushi wanda yake narkar mata da zuciya .


Wanj irin kunyar sa ce ta kamata ,wanda yasata saurin sada kai kasa .


Murmushi yayi don sanin halin kunya irin na Laila yana mai kai Fuskan shi samn gyrfen wuyan ta hadi da shakan kamshin jikin ta da tasha gyara gurin Mom sa'ah .


Wani irin kissing yake binta dashi a hankali da babu mai jiyowa yana bin ta da lips din shi yana wani irin sauka daga kasan wuyan ta da sanyayyar kiss.


Kokarin matsawa take don mamaki ne ya kamata lokaci guda tom wannan meye kuma?? Meye abdul keyi matane?? Tambyar da take mawa kanta kenan hadi da jah baya . Tana dan tureshi a hankali kar su Areef su gani.


Muryar Areef suka tsinkaya yana cewa" kai oga sir kabari ku isa gidab ku mana ,wannan abu da mai yayi kama . Kabar yar mutane ta sauke gajiya mana!!

Dariya Sadeeq yayi kamin ya amshe da cewa" anya xaka rinka barin Laila tana hutawa kuwa ,vaxaka dameta da jaraba ba?...



*SIYAASA TA! na kudi ne banyarda ki karantamun baki biya ba ,idan kk karanta baki biya keda Allah"*


Maman teddy🧸
0808120293248_49
Murmushi su duka sukayi kana yace" ku kam dai da saka ido kuke ...tom ai dole masa ko wannan rawar kafan da kakeyi ka jawo hankalin mu ...Sadeeq ne mai mgnan don yafi Areef iya tsokana . Kaji rabu dashi Muma dai zamuyi auren nan muji mai sukeji ne da tun a moto kamin akai Amarya yake ta wannan rawar kafa.

Dariya duka suka saka banda Lela da tayi shiru tana tunanin Abubuwa barkatai game da rayuwa . Nisawa lela tayi tana sakin murmushin da batasan zata iya yin shiba a wannan lokaci .

Allah sarki Abdul mijina abokin rayuwa ta ban kyauta mawa kaina ba ,na cuce kaina dana rasa Abdul a rayuwa ta . Mgnan take lokaci guda hawaye ya tsanan ta da tsiyaya a kwarmin idon ta. Tuno da yanda Nabila ta ribace ta ta sanyata a hanyar madigo da mutumcin ta na Aure yasata fara doka mawa nabila allah ya isa . Tana cigaba da shar6an kukan ta harda kyekyatawa.

Abdul yasan komai na vaira6a wulakantani a rayuwa ba .ya maisheni tamkar Wacce tayi rayuwar wata kaasa bama nageria ba ,bare kuma har a kalleni ace wai na taso ne a cikin karkara ,tabbas indaba don nina fada ba ,kowa wani yaje ya fadamasa cewan ga Asali na babu mai yarda .

Ganin yanda Abdul ya gogar dani harda masu kula dani wurun shirya komai na yasa na zama cikakkiyar Matar Alhaji masuji da tashe matasa masu rumbin dukiya . Irin Arxikin abdulrahman yasa na jefa kaina cikin wannan mawuyacin dabia ,na koma mara kirki sam . Kai wayyo ni Laila nayi nadama ,alokacin da bashi da amfani gareni. A wannan dare kam laila kwanan zaune tayi tana kuka .wanda har duhu dubu take gani saboda tsaban kuka idon ta ya kumbura jijiyoyin idon ta sun rirrike mata .

Bangaren Ko Areef rasa abunyi yasa shi ba tare da 6oye mawa mahaifin shi ba yasanar masa komai game da mgnan da sukayi da honorable .

Murmushi Daddy yayi yana kallon Yaron nasa kamin yace"Ai wannan shine dalilin da yasa na aura maka Ahyaan ,tun farkon ganin ta dan uwanka da yayi ya fahimci cewar ita jinin kuce .

Momy ce da take sauko ta fara tsinkayar mgnan tasu kaman daga sama.


Saurin karakowa tayi cike da mmki take bin Daddy da shikan shi Areef da kallo wanda a iya yanxu idon shi ke tsiyayar da kwallah . Ba amamaki da ikon Allah ,duk da lamarin shi da Ahyaan ikon Allah ne .

Ya aureta daga gidan marayu ashe itadin itace farin cikin sa da ya dade yana nema safiya da mraici ,farin cikin Ammien shi da ta kaasance a jinya da lalura tsawon shekaru.


Wai me kuke cewa ne nifa ban gane ba ,wata Ahyaan dinne Diyar zainab ?. Ahyaaan dai matar ka danake jirar ka akanta?? Ahyaan diyar gidan marayu ?! Innalillahi wainna ilaihir rajiun shine kalmar da momy tayi ta nanatawa kenan tana komawa hadi da zama a daya daga cikin kujerun falon jaraf ....


Tuno da Wulakancin da tayi mawa diyar mutane da cin mutuncin da tayi ta mawa Justice Zainab Ammie ,nan Momy tafara zubar da kwallah mai nannade da zallar madarar nadama da danasani da ban hakuri .....





Gn
Mmn teddy🧸50_51
Maganan Alh tambuwal ne wato Daddyn Zulaihat yasa su duka maida hankali a kansa ,yanxu meye mafita ?? Shin yarinyar zata yarda zata gasgata cewar Da gaske ne Zainab mahaifiyar tace kuwa??!.

Daddy zamu fahimtar da ita tare da bata labarin tama wanda batasan dashi ba a rayuwarta . Cewar Nauwaf da yake mikewa hadi da cigaba da cewa" Yah Areef ba kuka ne yakaamata kayi ba Godiya ga Allah da har ya kawo maka warakar Ammie cikin gidan ka. Alhmdllh Kalmar da Momy ke da su Daddy ke nanatawa kenan kamin su duka su mike hadi da dunguma xuwa Government Hause .

Ahyaan ita kam dai tsawon lokaci ta dauka tana bin Zulfah da kallon mamaki kwakwalwarta ne ya tsaya cak a yayin da takejin maganganun dake fita daga bakin ta .

Kar ki firgita Ahyaan da jin kalami na ,ni jinin kice Ammie kuma Mahaifiyar mu ce ,Abban mu shine ya jefa rayuwata da naki cikin garari . Ceton Rayuwarki daga mugun hannun sa yasani Daukar ki a matsayi na ta wacce ba rayyaya ba ,ni Rauwan ce ba mutum ba . Mahaifin mu shine ya kasheni Ayayin da Ammien mu ke zubar kwallahn bakin ciki da rasa mafita da kuma babu yanda xata iya da Alh Dasa'a wato Hanorable.


Innalillahi don Allah Zulfah kidaina fadimun irin wannan maganganun wlh kwakwalwata baxata dauka ba ,ki daina fadamun cewa ke ba mutum ce kamana ba .

Tun ina yarinya ke ce nake gani naji sanyi babu mai ra6ata sai ke ,ke kika nuna mun soyayya tamkar son da iyaye kemawa dan su ko yar su . Don Allah Xulfah kar ki barni... Mgnan ne ya dauke mata sakamakon wani irin kuka da ya taho mata .


Kiyi hakuri Ahyaan nima ina son ki ,amma dole na tafi ,kuma tafiyar da baxan dawo ba .

Naji dadi da yakasance na cika ma Areef burin shi na ganin kin zama mallakin shi ,ya nuna maki soyayya tun kan ki taho duniya shiya sa na kaiki inda xaki rayu kuyi rayuwa na har abada. Kuma na tafi ki fada mawa Ammie tayi hakuri ki rikemun ita da Amana .


Kuma ki fada mata ta yafe mawa Honorable nima na yafe masa ,duk da nasan abune mai wiya Ta iya yafe masan ,amma ko bakomai idan ta yafe masa shi din mahaifin mune kuma baxai ta6a chanjawa ya tashi a uba gare mu .

Ki kula da Ammie Ahyaaan ni xan tafi baxan kara dawo maku ba ,xan koma na kwanta a makwancina na har abada .


Wani irin kuka Ahyaan ta saki tana kokarin ciciyo zulfa tana kankame ta . Amma kawai sai ta fara ganin tana komawa kaman jido tana bacewa a hankali tun tana ganin ta dishi_dishi ta dawo bata ganin komai nata. Wayyo na shiga 3 ni Ahyaaannnn!!! Wani kuka ta rushe da shi mai cike da tsantsan ban tausayi ... Wanda babu sunan da take kira sai na Zulfa .


Saurin mikewa tayi da gudu tayo waje tana nufan Side din Ammien Areef .

Jah da baya tayi tana tsayawa Turus kallon _kallo suka tsaya sunayi tsakanin su ,duk da hakan idon ta babu abun da yakeyi sai tsiyayar da hawaye .

Ganin yanda jiri ke dibarta tana barazanar faduwa yasa Momy sauri kamata a matukar rude da halin da suka ganta ciki ta hau tambyar ta Ahyaan meke faruwa ne?? Me ya sameki ?!.

Wani irin numfashi tajah wanda yake barazanar barin gangan jikin ta .

Momy shikenan wayyo wayooo niiiii kawai sai takara rushewa da wani irin kuka tana gaza magana sai hawayen da kwaranya yana dada ambaliya a saman fuskanta .

Ahyaan Ahyaan fadamun meye sameki me yafaru dake?? . Areef ne a wannan karon yayi mgnan yana Riko Ahyaan hadi da tallabota jikin shi .

Yah Areef Zulah na ...Zulafah na yau ta tafi ta barni ,tace mun baxata dawo gareni ba shikenan na shiga uku na rasa Zulfah na ,wlh baxan yafe ma duk wanda ya rabani zulfah ba ,don Allah Momy kisa ta ta dawo!!!.

Rungumeta Areef yayi yayin da su Daddy suka shiga halin rudu wacce zulafn take nufi ??

Momy ne abunka ga ita akwai garda_gar cikin mmki tace" Ahyaan wacce zulfan?? Zulfa dai nasan diyar Ammie ce kuma ta dade da mutuwa .....


Wani irin kuka Ahyaan ta balle masu dashi don har a lokacin bata yarda cewan da gske zulfah Ta mutu ne kaman yanda ta fada mata ba .


Wani irin numfashi taja wanda nan take Numfashin ta ya tsaya cak .....kirjin ta na daina har bawa .


Innalillahi wainna ilaihir rajiun...shine kalmar dasu daddy ke nana tawa kenan Momy kam tuni hawaye ya cigaba da kwaranya mata kaman ma yanxu ne taji labarin .

Subhanallh Nauwaf Areef meke faruwa ne anan??!. Cewar Ammie da take takowa tana tahowa tabbas ita dai abun da ta tsinkaya shine kirar sunan Zulfa shine kalmar da ya dawo da ita hayyacin ta . Da batasan tayi fama da wata lalllura ba baya .


Cak Duk suka tsaya suna mmkin Jin muryar Ammie cike da kamalan ta kaman da baya .


Me yake faruwa ne kukayi mun shiru ina zulfan take??! Tayi maganan dai dai tana karakowa zuwa inda suke a tsaye .

Ammie³ cewan Areef da nauwaf a tare ,wanda cike da farin cikin ganin ta a halin dawowan hayaccin ta suka rungumeta suna mai sa wani irin kuka har da jinjiga ... Mmki ne ya rufe Ammie ,hannun ta takai tana shafa sumar Nauwaf da Areef kamin ta kallli Daddyn tambuwal tana cewa" Ai zulfa ta mutu ko baxata dawo ba ....wanda ya mutu kunsan baya ta6a dawowa . Don haka Areef Nauwaf sai kace kananun yara !! Kuyi hakurrrrrr bin Momy tayi da kallo ganin ita tana tsiyayar da kwallahn Tana kuma rungume da Ahyaaan wacce bata santa ba .


Momyn Nauwaf meke faruwa ne wai ?! Wannan wacece ?!! Tayi mgnan tana sauke idon ta kan na Ahyaaan...


Cikin muryar kuka Momy ta amshe da cewar Ai ita din diyar ki ce . Mene kaman ya?!! Ammie tayi mgnan ta na ware idon ta bisa na Momy hadi da ware_ware tana kallon su daddy da shi kansa hankie yasa yana matse kwallahn idon shi .


Ita kam Rahinart da t tsaya kem tsawon lokaci takasa motsaawa tun daga jin mgnan Ammie da yanda ta dawo hayyacin ta da kuma wai jin Ahyaan din yar Ammie ce yasata kamewa .

Cikin sauri Areef ya dauki Ahyaan cak yana nufar Wata doguwar kujera 3 str yana kwantar da ita ,momy ce da Rahinart da ta saka hannu badon taso ba ,tana mai daure wani abu da son sanin gskyar lamarin ta fara kkrin ganin sun samu daidaituwar numfashin ta .

Numfashin Ahyaan taja tana gigif hadi da mikewa daga zaune tana kokarin tashi tsaye . Ammie ne tayi saurin rikota tana cigaba da kuka hadi da cewa' Ahayaaan kefah musulmace da gske ne Rahinart ta mutu kuma dukkan musulmi ya kayakama yayi imani da kowacce irin kaddara mai kyau ko marar kyau duk daga Allah ne ...ki yarda Zulfah ta mutu kuma duk wanda ya mutu baya dawowa ..


Jin maganganun Momy yasaka Ahyaan jikin ta saki kawai sai ta koma ta zauna jaraf jiki bb kwari ,idon ta na cigaba da fidda zazzafar hawaye .


Alh tambuwal ne da daddy suka fara mgn hadi da kokarin kwantar da hankalin Su Momy musamman Ahyaaan.

Zama su duka sukayi ,nan take Alh Tambuwal yafara bada lbrn komai tundaga Haihuwar Ahyaan da yanda ita wannan zulfa ta sace Ahyaan tayi amfani da kanta kasacewar itadin Rauhan ce ta kuma kaita gidan Marayu na tsawon shekaru .

Wanda hakan ne ya haddasa ciwonAmmie da bata warkeba sai a yau . Nisawa yayi yana cigaba da sanar da mgnan Alh Dasa'a kan Abashi diyar shi kaman yanda yace da kuma sain san da sukayi da Areef . Nan take falon akayi tajin tajin ,masu kuka nayi masu jimami nayi . Ita kam Rahinart bata ko daya daga ciki .


Kwalla Ammie ta goge wanda cike da kamalliyar muryar ta ta amshe da Ahyaan kiyi hakuri nasan bakiji dadin uwa kaman sauran yaya ba . Baxan ce komai da honorable ba kasancewar shi matsayin mahaifin ki .


Amma wlh Honorable yaje shi da Allah ,alokacib da nake cikin Gida na ,ina kwance a mahalli mai kyau da nagarta ,ya ta tana can inda xata kwana take nema ,walau ta kwana a kasa ko kuma ta a filin tsakar dajin gidan marayu ...


A lokacin da nayi karin kumallo da abinci mai gina jiki ita adaidai wannan lokacin waina ne ake basu gutsure gutsure suci suna rububi shikenan fah tsawon lokaci....hawaye ne ya tsaban ta da saukowa a bisa idon Ammie .


Goge wa tayi tana mai cewa wannan shind kaddarar ki Ahyaan ,ki dauki komai a jarabawan ki Allah ne ya kaddarta maki Honorable ya kasance mahaifi gareki amma maganan gsky bakiyi dace ba .



Nayi hmdallh nayi gdy ma Allah da Da na wanda nafi so Areef ya Auri diya ta ,koba raina nasan baxata wulakanta ba .areef kana karamci .


Kirar sunan Areef da tayi ne yasa shi kallon Ammie idon shi ya yi jazir ,don tsabon rudu ga kukan da yayi wanda rabon da yy irin shi tun lokacin da Ammie ta samu da wannan lalluran.

*Ki tausaya karki fitar mana dashi in kin siya ,Inkinsan siya zakiyi don kiyi sharing don Allah karki siya mun hutashsheki,Haƙƙin mallakar marubutanne su kaɗai,Ki tausaya masu plz ,Inkinga wani pages na yawo to na sata ne ki runtse idonki karki karanta ki biyo ki siya ,mun gode*


•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*SIYASA TAH!* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA'AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba'a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000


•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi'u. GTbank_


Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ ```Sai munjiku Masoyan Amana....Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍```♡♡



*MAMAN TEDDY*52_53
Ammie na bana so ki na wannan furucin ,ammie baki da lafiya don Allah kiyi shiru ki yafemawa Daddyn Ahyaan ...aa wlh ko Ammie ta yafe mai ni baxan yafe masa ba ,baxan yafe masa ba har sai ranan da ya tuba ya daina abun da yakeyi sannan .

Ahyaan ce ta katse Areef da wannan mgnan ,wanda jin furucin ta ya daga hankalin su Daddy matuka .


Shiru duka akayi na wucen gadi ,wanda A hankali Mgnan gidan Tv Tazara new tv yafara mamaye ilahirin falon ....a yaune 27 ga wata Jirgin Da ya dauka daga nigeria zuwa Kasar india tayi hatsari ,wanda mutane da dama sun rasa rayuwar su ciki kam akwai wnnan shahararriyar yar kasuwar Wato Hjy Atika dasa'a . Anyi nasarar daukar gawarta xuwa gidan mijin ta wato Alh Honorable Dasa'a ,wanda a yanxu mun samu lbrn gidan nasa ya kama da wuta ta koina ,amma gwamnati takai mawa gidan nasa taimakon gagagwa. Wanda anan zamu rufe rahoton mu ,a jurace mu xuwa gobe da misalin wannan lokaci don muji lbrn kasar mu wato nigeria ,wanda suka mutu Allah kaji kansu da rahama .


Salati falon Aka dauka banda Ahyaan Areef da Nauwaf da Rahinart . Kowa na tunanin yanda rayuwa xai cigaba masa .


************************

Zaune Meemah take ranta duk a kullum a dagule yake, yanxun ne tagama nadama da nasani tuli a rayuwrta .


Ina Mummyn nawa take?? Tajiyo muryar yarinyan yana wade falon cike da masifan yara .

Wacece kuma !??? Cewar Meemah a bayyane ,Nanah ce naje part din mom dina ban ganta ba ,sai wai yanxu na ganki a nan ,kece momyn nawa?!! Tayi mgna cike sa tsigalewa tana bin meemah da kallon sama da kasa ka dauka wata iri babbace mai shekaru .


A sanyaye meemah tace aa ,don ta fahimci yarinyar lela ce.


Jiyo muryar Major sukayi bayan su yana fadin " nana second momma din kice ,ki mata oyoyo....


Dad??? Tayi mgnan cike da mmmki tana kallon shi yarinya karama tasan kishi ,kukan rigima tasa tana bubbuga kafanta kasa hadi da fadin ni banason ta daddy mom lela na nakeso ,ka kaini wurin ta ,ni ita nakeso ....



Sauri riko Narna yayi yana rungumeta hadi da mata mgna a hankali yana shafa bayan ta alamun rarrashi ya isa haka bby na ,gobe xan kaiki wurin mom Laila taje gida ne ta gaida Oumma .


Muje Bedroom dina Aunty momyn ki na fada maki wani abu . Jin haka yasa Narna amince wa suka nufi bedroom din Meema da ta tsaya sororo tana bin ssu da kallo .


Kaman mintuna biyu kuma sai gashi ya fito ,kallon ta yayi wanda a wannan karon tayi mmki kadan ganin va wanna .kiyayyar da yake mata ,cewa yayi ki shirya mawa Bbby Nana Dinner ,a nan part dinki xata kwana.

Kin sanni nayi ma Lela alkawarin baxan ta6a kwana da wata mace batare da ta amincemun da hakan ba .

Yana gama fada mata haka ya juya yana nufar bedroom.din nata .


Da ido Meema ta bishi har ya shige ,lallai wnnan mutumin dan rainin hankali ne ,amma bakomai lokaci ne!" abun da tace kenan tana nufar Kitchen don yin abun da ya umarceta.


Itakam Zubaida Gidan Aikatau din ta ne xaman shi ya isheta tijarar tayi yawa ,ga shi wannan sojan da ya dawo kwarto ne ga shaye_shaye ga yin zina da yayan jama'a wannan yasata tattarawa cikin dare tana kokarin guduwa daga gidan Hjy Dada don ta nuna mata ta amince da Wannan sojan dama ita hjy dada iyayen karuwai ne.


Cikin dare take tafiya babu tanayi sauri sauri wai donta nufi tasha tasamu moton dare da zata tashi.


Tsallake titin tazoyi ,wanda bata ankara ba taji moto tayi gaba da ita .


Ba ta kuma kara sanin inda take ba ,sai dai farfadowa da tayi taganta a garin adamawa , a wani asibiti .


Bude idon ta tayi tana ware_ware nan taga Mama Hajja da Baba Audu ,wanda daka kalli fuskan sa fal nadama ne cikin ta


Sannu zaubaida kalmar da yace mata kenan ,wanda a sanyaye cike da mmki ta amshe da yowa baba ...Mama ce ta maida kwallan da ya taru mata don sai bayan tafiyar Zubaida ne Abdul da kanshi ya fada masu gskyar komai hadi da basu hakuri .


Basu fada masa sun kori zubaida ba ,sai sai har cikin ransu sunyi nadama kuma sun yafe masa.


Mama ya akayi na ganni anan?? Kodai duk abun da yake faruwa dani daman mafarki ne ?!!


Aa zubaida ba mafarki ne ba da gske ne .mm tayi mgnan tana zama gyefen zubaida . Baba Audu ne yafara fadi mat duk abun da yafaru ashe makocin su ne ya bugeta a garin kano ,sanin tada yy ne da kuma neman ta da akeyi yasa shi kawai nufo da ita garin adamawa .


Kuka zubaida take sosai kamin tace" Baba Mama nasan nadade ina naimo maku.mgna amma don Allah ku garface ni ku yafemun ...!l


Habawa zubaida babu wanda vaya kuskure a rayuwa ,na yafe maku har abada wlh. Cewan Baba Audu .haka ma Mama ta tace ta yafe masu ai yarinta ce ke dawainiya dasu a da baya.


Shikam ALH dasa'a komai nasa na dukiyar sa ce tayi karkaf ta kone a wannan gobara ,dodon tsafin sa haka tayo titi saboda zafin wuta tuni da yake karshe yazo ta haukace tana bin titi ....moton agaji da ruwar kashe gobara ne suka taketa batare da sun sani ba . Nan ta yi flat sai gawar wannan halitta .


Honorable kam a duk arxikin sa da yake takama dashi akashi 50 babu talatin wannan yasa shi shiga halin kidima da rudu .


Sam ankasa samun nasarar dakatar da wutan nan sai da komai ya kone har ginin sannan ta zube.


Tabbas honorable a wannan lokacinne yasan allah dayane,yana a wannan halin ne kuma kasar America ta taho da tuhuma akan shi cewar tana bun shibashi kuma suka sanya ranar da zasu hadu a kotun kasar America don amsan kayan su . Lamarin honorable kam sai dai muce inalillhi wainna ilaihir rajiun .....

*Ki tausaya karki fitar mana dashi in kin siya ,Inkinsan siya zakiyi don kiyi sharing don Allah karki siya mun hutashsheki,Haƙƙin mallakar marubutanne su kaɗai,Ki tausaya masu plz ,Inkinga wani pages na yawo to na sata ne ki runtse idonki karki karanta ki biyo ki siya ,mun gode*


•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*SIYASA TAH!* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA'AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba'a barku a baya ba,ganaku kaɗan

Please Login or Register in order to submit comment