Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sake Cewa komai Knocking d'in kofar da akayi ne yasa Badiyya tayi saurin share hawayen dake fuskar ta Tace "Come in"
Baba Mai gadi ne a gaba,Abban Yesmin na biye dashi"
Mamakine ya rufe Badiyya cikin Rawar murya Tace "Baba....baba Kaine? Asiyah ga baba"
Asiyah cikin sauri ta cire hannunta a cikin na Hashim ta Fara lalube tana ambatan sunan sa.

Cikin sauri ya karasa inda take yace "Na'am Asiyah gani Nan" Yana maganar ya riko hannunta fashe wa tayi da kuka Tace " Baba Ina ka shiga? Ka barni ni kad'ai?"
Kad'a Kai yayi yace "gani na dawo ban barki ba"
"To Amma mun dad'e muna neman ka da Aunty Badiyya Amma bamu ganka ba"
" Bani da lafiya ne Asiya Amma yanzu Alhamdulillah naji sauki sosai"
Tace " To Allah yasa kaffarane duk suka amsa da "ameen"

"Baba kaje gun Aunty Rukayya kuwa?"
Huci yayi yace "Eh naje"
"Alhamdulillah ka same ta kuwa"
"A'a ban same ta ba"
Asiyah Nan da Nan fara'ar dake fuskar ta ya gushe Murmushi Baba yayi ya d'aura da fad'in "Amma da naje ta bawa Mai gadin ta sako a Baki,a fad'in sa Tace tasan Zaki Zo neman ta"
Murmushi tayi Tace " wani sako ta bani?"
Iska Mai zafi ya hura kana yace " Kiyi hakuri Asiya,motace ta buge Ni a wannar ranar Kuma wasikar na hannu na a wannan lokacin tun daga lokacin ban San inda nake ba sai shekaran jiya na farfad'o"
Murmushin gefen baki tayi Tace "Bakomai baba tunda kana da lafiya ai shi yafi muhimmanci a yanzu"

Abban Yesmin a Karo na farko ya yi magana yace "wasikar da kake magana akai d'azun Nan na d'auko shi a mota da niyar zan baka,Amma bara na Kira Matata ta kawo muga ko shi d'in ne" Yana maganar ya zaro waya ya kirata, tana picking yace 'dan kawo min envope "d'in Nan Mana a office d'in Dr Badiyya"
Ba 'bata lokaci ta Karo dake bai da wani nisa, da Sallama ta shiga ta Mika masa,ganin Asiyah ta Kama Baki ta ambaci sunanta "Asiyah kece?"
Ta amsa da "eh Amma pley Wace Ce?"
Murmushin gefen baki tayi Tace "Haba Asiya har kin manta Ni?"
Dr Badiyya ce Tace "Ai ta makance Bata gani?"
"Eh na sani,baba Mai gadi ya fad'a min, na d'auka zata d'auki muryatane"
Murmushi Asiya tayi Tace " Aunty Nana? Ko ba Maman Yesmin bace?"
Ita ma Murmushi tayi Tace "Eh nice nice"
" Hmm ai bazan tab'a manta dake ba Aunty Nana bazan tab'a manta ki da mummy ba"

Nana harkasa ta durkusa Tace "nasan bakya gani na,yanzu haka a gwiwowina na ke,Asiyah na cutar dake, na biyewa son zuciya ta,Amma wallahi yanzu na tuba ba Nanar da Kika sani bace yanzu haka na manta ranar da na sa Baraka a cikin idona Dan Allah na roke ki,ki yafe min,Kuma a shirye nake na taimaka Miki wajen ganin kin d'au fansar abinda Baraka ta Miki"

" Na yafe miki Aunty Nana har cikin zuciya ta dama chan ban kullace ki da komai ba"
" To nagode Asiya" tashi tayi ta mikawa baba Mai gadi wasikan yana gani yace "Tabbas shine wasikar ne,don ga sunan ta a jikin" Yana nunawa Abban Yesmin shi duk dad'ewar wasikar a gun sa bai San akwai sunna akai ba, mikawa Asiya wasikar yayi yace "Asiyah ga wasikar Nan"
Murmushi tayi tace "Baba da wani idon zan karanta? Kawaii ka karanta min naji"

"To bande ke da abinki Asiyah ai Ni ban iya karatu ba, sunan kin ma da nace Wanda ya bani wasikar ne yace min ga Nan sunan ki a rubuce" duk sukayi dariya sai ya ce " To ai gaskiya ne,yanzu Ke gashi ki karanta Mana" Yana Miki wa Dr Badiyya, hannu buya tasa ta karb'a cikin girmamawa.

Karanta sakon ta Fara yi kamar haka.
"Assalamu alaiki Asiya,da fatan kina lafiya, Kiyi hakuri Asiya da irin halin da Kika tsinci Kanki, ko kad'an bana Jin dad'in abinda ke faruwa daku,tun bayan mutuwar Anisa da Mahaifin ku Baraka take yin abinda ta ga dama har gidana tazo ta ci mutunci na da na Miji abin bai min dad'i ba Sam,har tayi ikrarin zata kashe ni idan na kuskura na Tako inda kuke shine dalilin da yasa na daina zuwa in da kike.

Baraka Bata da imani Bata tsoron Allah, Asiyah ina ji Ina gani ta sawa Yar uwata Maryam (Mahaifiyar Asiyah) guba a cikin abincin ta Amma na kasa fad'awa kowa a wannan lokacin ma ta yi min barazanar zata kashe ku sannan Nima ta kashe ni idan na kuskura na fad'a wa kowa maganar Nan, wannan shine dalilin da yasa ban fad'awa kowa ba.

A duk lokacin da sakon Nan ya iso gare ki,ga Nan number ta ki kirani Dan Allah ina Nan Ina zaman jiran kirin ki,sannan akwai Flash drive da na ajiye Miki acikin envelope d'in Video ne na lokacin da Baraka tasawa mahaifiyar ki guba sannan akwai recording na lokacin da take min bazarana"
Taki a kullum Rukayya

Asiyah fashewa tayi da kuka a yayin da, Badiyya tasa hannu ta Ciro flash drive d'in, Hashim ne yace "Alhamdulillah Allah ya kawo karshen azzuluamar Nan, yanzun Nan zan shigar da kararta kotu ba sai anjima ba" ya zaro wayar sa da niyar yin Kira.

Abban Yesmin yace " Dakata Dakata bawan Allah, wannan ba abin gaggawa bane Baraka shu'uma ce Dole mu bita a hankali,ba abun mamaki bane ta kashe mu duka ko Kuma ta haukatar da mu" Maida kallon sa yayi ga Badiyya yavei " Bani flash d'in Nan" ba musu ta mika Masa ya d'aura da fad'in "wannan zan Kai was aboki na babban lawyer ne Barrister Nabeel Yunusa nasan Kun San shi tunda shi ba 'boyayye bane a garin gombe"

Hashim yace "Ni a gani na tunda an samu wannan opportunity d'in Kar muyi Wasa dashi gara a kamata kawaii a Mata hukuncin da ya dace"
Baba yace "Hashim Ina ga maganar officer na Kan hanya kasan Shima jami'i ne mubar maganar Nan a hannun sa"

Abban Yesmin yace "Hakane malam Hashim yanzu mu Maida hankali wurin ganin yarinyar Nan ta samu lafiya"
" Hakane yallab'ai goben Nan zan kaita England da kaina,yanzun ma abinda zai Hana baza mu tafi yau ba sabida Bata da passport Amma yanzun Nan zan had'a komai" Yana Kai Nan ya sa Kai ya fice.

Badiyya kanta ne ya d'aure ganin yanda Hashim ya rikice "Yana son d'aukar fansar abinda akayi mata,duk yanda akayi soyyayaar yarinyar Nan ta Kai kololuwa a zuciyar sa,bazan tab'a Bari yarinyar Nan ta kwace min masoyi ba"

SHIN MENE NE A TSAKANIN HASHIM DA BADIYYA?

Harvard University United State of America, Yana d'aya d'aga cikin manyan University a United States, anam courses da dama both art and science.

Zaune take ta a Kan stairs, jikinta sanye take da atamfa kalar curfew brown an Masa design da da milk color anyi Masa d'inkin girma, crystal stones aka zuba a gaban rigar daga sama har kasa,kanta kuwa d'aurin Aisha buhari tayi Ana iya ganin bakin gashin ta a waje, Rolling tayi da karamar gyalle milk haka ma takalmin da ke kafarfa, hannun ta rike yake da littafi da alama karatu take ganin yanda ta Maida dukkanin hankalin ta akai.

Da sallama ya Kara sa inda take ya zauna a gefen ta,a hankali ta d'ago kanta ta kalle shi Murmushi tayi Wanda ya bayyana dimple d'in dake fuskar ta,rufe littafin tayi tana kallon sa ba tare da ta ce masa komai ba yace "Angel dama anan kike tun d'azu nake ta neman ki?"
"Eh wallahi Ina d'an duba practical d'in da makayine d'azu"
" Shine akace ki manta da mijin ki? Wace irin matace haka da ba ta damu da mijin ta ba?"

Had'a hannun tayi with guda alamun bada hakuri Tace " Tuba nake rankashidad'e"
'daga kafad'a yayi Yana kwaikwayon muryar ta "A'a nikam ban hakura" dariya ta shiga yi sosai tana fad'in " Na fad'a maka ka daina kwakwayona sai ka Zama kamar mace dama kamannin ka na Mata ne"
"laa Ni d'in kike cewa na Miji?"
Ya Kai hannu zai rankwashe ta,ta watsar da littafan dake hannun ta, ta gudu tashi yayi ya bi bayan ta sai guje guje suke acikin makaranta,Yan cikin makarantar inda Sabo sun Saba ganin wannan masoyan Wato Hashim da Badiyya soyyayar su ta Kai so sun Zama abin kwatance hakan yasa wasu ke Kiran su da Romeo and Juliet.

Karatun su suke sosai, soyyayar su Bata Hana su karatu ba duk da already an musu baiko, Hashim na karanta Business yayin da ita Kuma take karantar ophthalmology (Likitan Ido). Shekarun su biyar Kenan suna soyayya basu samun sab'a ni idan kuwa kaga sunyi fad'a to kishin Hashim ne sila akwai wani Course mate d'in badiyya Mai suna Amma Khan, ba indiye ne Yana matukar kaunar Badiyya,Amma ganin yanda take son Hashim yasa ya hakura da ita idan kaga ya Mata magana to magana ce da ta shafi karatu, uwa uba Yana bala'in tsoron Hashim bazai tab'a manta dukan da Hashim ya Masa ba har sai da ya kwana a sume a school clinic.

Yau suke celebration na gama makaranta, ko wani department da inda suke nasu bayan sun gama a ka had'a general party dukkanin graduating students na ko wani department, Badiyya tun jiya take rokon Hashim Akan suje Amma yaki.

"Hash please Muje Mana Kaga jiya akayi departmental celebration Amma baka je ba,yau general me Dan e Muje Kar kace baza Kaje ba"

Rai a d'an b'ace yace "I have told you bazanje bazanje ba Ana Dole ne idan kina son zuwa kije Mana ban Hana ki ba,Amma Ni bazan je ba"
Rai a 'bace ta fice daga cafeteria d'in.
Hashim ko a jikin sa,komawa yayi d'akinsa ya kwanta abinsa.

Badiyya kuwa zuwa tayi ta shirya yau kananann Kaya tasa,bakar pencils skirt da farar T-shirt an ruba Opthalmologist a gabar rigar bayan ta Kuma Badiyya Hash aka sa, rawa ake Ana ci ana Sha, Badiyya na matukar son rawa hakan yasa ba a bar ta a baya ba tana tsakiyar dance floor,Ammar na ganin ta ya taso da niyar yi Mata magana Bata ankare ba ta buge shi a ido,cikin sauri ta juya don ganin wanda ta buge "Ammar oh Am so sorry please"ganin Yana murza idon Tace "hold on let me see" ganin idon yayi jaa ta Fara hure Masa idon, a dai dai Nan Hashim ya shigo daga nesa ya hango bayan ta, ransa ne yayi mugun 'baci gadan gadan ya nufo su fince ke ta yayi ya hau dukan Ammar dakyar aka shiga tsakanin su, wurin ne yayi shiru a fusace Badiyya Tace "hashim what do you think you're doing? What's the meaning of this"

"What's wrong with me? What's wrong me? You're here kissing this thing and you're here asking me what am I doing? tell me what you're doing with him?"
Cikin rashin fahimta Tace " What? Are you kidding me?"
💦💦💦💦💦💦💦💦
PLEASE VOTE AND COMMENTS

CHAPTER 23
NOT EDITED

"What's wrong with me? What's wrong me? You're here kissing this thing and you're here asking me what am I doing? tell me what you're doing with him?"
Cikin rashin fahimta Tace " What? Are you kidding me?"
💦💦💦💦💦💦💦💦
......."Am I kidding you" magana yake ransa a mugun 'bace idanunsa sun canza daga Farare zuwa jaa, ran Badiyya yayi matukar 'baci Rai a d'an 'bace Tace "Hashim Anya kana cikin hankalin ka kuwa?"

"Ke zan tambaya Badiyya, but is okay.... Is okay" Yana maganar Yana dariya had'e da kuka Yana d'aga kafad'a Yana Kai Nan yayi ficewar sa,duk gun kallon sa a ka tsaya yi, abokin Ammar ne ya d'auki mic yace "Please we are sorry,DJ ka samana kid'a" Nan suka cigaba da shashewar su, Badiyya Kan Ammar ta nufa ganin ya fasa baki sannan  gefen idon  sa  ya  kumbura  hakan ne yasa suka je clinic aka wanke Masa ciwin, banda sorry babu abinda take cewa masa ji take kamar taje ta Rama Masa a fad'in ta baida hujjan dukkan sa.

Hashim kai tsaye d'akin sa ya wuce zama yayi akan one sitter daje d'akin sa, d'an kwanciya yayi Yana kallon saman d'akin hawayene masu zafi suke sauko masa,da zarar ya rufe idanunsa Badiyya yake gani da Ammar, tsaki yayi yace "kin cuce Ni Badiyya,ki rasa Wanda Zaki kula sai Ammar har kiss?" A bayyane yake maganar.

"Hashim Kennan, kana matsala wallahi kishin ka yayi yawa yanzu Dan Allah me amfanin abinda kayi?"
'dago idanunsa yayi don kallon Wanda yake magana d'an tsaki yayi ya ce "Look Farees baka ga abinda na gani ba ne Dole kace haka"
"Hakane ni banga abinda ka gani ba...." Zama yayi a bakin gado Jana ya d'aura da fad'in "Babu yanda za a yi idanuna su gane min abinda ka gani,sabida kaga Ni da hankali na"
Gyara Zama yayi yace "Okay idan na fahimce ka Farees kana nufin mahaukacine Ni bani da hankali ki"

'yar karamar dariya yayi yace " Kai kace hakan Ni bance maka mahaukaci ba,Amma me ma difference d'in ka da mahaukacin? Ka tsaya kana ta ihu akan rashin gaskiya,kace min kana da hankali?"

"Farees na roke ka Dan Allah ka kyale Ni naji da abinda yake damina"
Rai a 'bace ya mike yace "anki a kyale ka Kai Kennan ba hali a fad'a maka gaskiya? Na Sha fad'a maka ba haka ake soyayya ba,Amma baka ji,nifa da idona Naga sanda da buge shi da hannun ta Bata sani ba, shiyasa take hura Masa ido"

A tsawace yace "Kar ka Raina min hankali Mana inga tana kissing d'insa kace min ba Haka ba"
"You see your life kaga shine illan tab'a jikin ta da kake yi,kana kissing d'inta ba Dole kayi zargin ta ba, me bakayi da ita, shaidar da zan maka d'ayane shine nasan bazaka yi Zina da ita ba but nasan babu abinda baka sani ba a jikin ta ba,Kuna ganin hakan waye wane" tsaki Mai tsawo ya jaaa ya fice, sai Kuma ya leko yace "Faisal ya Kiran yace Yana Kiran ka baya shiga idan ka gama haukan naka sai ka Kira shi" ya ja kofar ya rufe Masa yayi tafiyar sa.

Farees cousin brother d'in Faisal ne, hakan yasa Hashim Faisal da Farees suka zama abokai.

Tsaki Hashim yayi ya koma ya zauna Hashim kasa bacci yayi tunda ya zauna Bai tashi ba sai tsaka wa yake da warwara Yana kallon kofar d'akin a ganin sa Badiyya zata Zo ta Bashi hakuri kamar yadda ta Saba,Amma Bata Zo ba,Bai tashi a gun ba sai da lokacin sallah tayi bayan ya idar da sallah yace "Baza ta Zo ta bani hakuri ba Kenan Hmm,ko da yake ma hakurin me zata bani tunda tana son hakan?"

Badiyya ma hakan take ba tayi bacci ba sai kallon wayar ta take ko zai kirata ya Bata hakuri Amma shiru kake a fili Tace "Wato bazai Kiran ba Kenan bayan yasan yayi laifi a tunanin sa zan je na Bashi hakuri ko? To wannan karon Kan karyan ka Tasha Karya" ta cigaba da harkar gaban ta.

Projects d'insu suke kokarin had'awa hakan yasa makarantar busy, Yau kwanaki uku Kenan Badiyya Bata Zo inda yake ba Haka ma Hashim bai nema ta.

Department d'in su Badiyya ya shiga, Badiyya na ganin sa tayi Murmushi a zuciyar ta Tace "Nasan zaka dawo" ga mamakin ta sai taga ya wuce ta Baki a bud'e ta bishi da kallo, Hashim Sarai ya ganta Amma yayi kamar bai ganta ba, inda ya hango Farees ya nufa dake  course d'in badiyya da Farees d'aya.
Farees na ganin sa ya 'bata Rai, hannu Hashim ya Mika Masa had'e da fad'in "Assalamu Alaikum"
Farees Mika Masa hannu yayi ya amsa chan ciki ba don ya so ba.

Zama Hashim yayi yace "Ina ka shiga ne haka two days ba a ganin ka?"
Farees yace " Ni d'in kuwa?..... Ina Nan ba a dai neman ba" sai ganin Hashim yayi Farees ya Fara tattara takardun sa, cikin rashin fahimta Hashim yace "A'a Ina kuma zaka?"
"Bacci nake ji zanje na kwanta"
"Bacci Kuma to Muje man" ya tashi da niyar bin sa Farees yayi saurin fad'in "No thanks bakaji bacci nace ma zanyi ba?" Yana Kai Nan Bai tsaya Jin me Hashim zai ce ba ya bar gun. Hashim jikin sa sanyi yayi murmushin takaici yayi yace "To Allah ya kyauta."

Badiyya na kallon su duk da bata Jin su ta gane akwai matsala, hakan yasa tayi ficewar ta, Hashim Zama yayi Yana kallo a wayar sa duk ji yake baya Jin Dadi,ba Masoyiyar sa Babu abokin sa,tsaki yayi sa wayar a jaka,ya fice.

AFTER THREE DAYS
Badiyya ganin Hashim yaki kulata hakan yasa ta shiga tashin hankali, sukan samu misunderstanding Amma Basu wice kwanaki biyu sun shirya idan yayi yawa 3 days, hakan yasa ta shiga Kiran sa,Yana gani har cikin ransa yaji dad'i har ya sa hannu da niyar d'aga wayar sai ya tuno abinda ya gani sai yayi saurin d'auke hannun sa, Yana ji ya na gani ta jera Masa missed calls biyar.

Badiyya cikin murya kuka Tace "Ammar he refused to pick my calls"
"No Don't say that maybe he is sleeping or something else please think always think postive"

" You won't understand Ammar I know Hashim very well he is not sleeping,and whenever he saw me he keeps on ignoring me repeatedly"

"Don't think about it too much Badiyya, nasan Hashim Yana sonki kawaii dai yayi fushi Ne kuma kema ai kin san halin sa,tunda shi d'in ba bakon ki bane"
Murmushin takaici Badiyya tayi Tace " Balqees Kenan ko da yake kin fad'i gaskiya Amma sanin Kanki ne bai tab'a fushi har haka ba,abin ma mamaki yake bani"

(Balqees kawar Badiyya yace, Ruwa biyuce Mahaifin ta ba indiye ne mahaifiyar ta Kuma bafulana ce,fulanin Gombe (bajoga) duk da zaman su yafi yawan India hakan bai hanata iya hausa da fulani sosai ba).

"Hakane Kam Bai tab'a hakan ba,Amma kema ai da laifin ki tunda kin San halinsa Kuma kina sonsa bai kamata ki bari har Ku Kai three days baku shirya ba"
Gyaran murya Ammar yayi yace ", Alright you people won't stop speaking hausa right"
A tare sukace "sorry "
Yace " it's alright but please Badiyya, if he didn't call you go and meet him"
Ta amsa da " Okay"
Yace "No no, Promise me you'll meet him"

"I promise I'll meet him"

Nan suka cigaba da hirar su.

Karfe 10 saura na dare zaman jiran Kiran sa take Amma shiru,hakan yasa ta d'auki gyallen ta ta yafa, minti goma ya d'auke ta Isa kofar gidan wani dogon ajiyar zuciya tayi kana,ta kwankwasa kofar had'e da kusa kanta cikin d'akin, Hashim karar bud'e kofar yaji hakan yasa ya bud'e sleepy eyes d'insa ya d'aura idon sa a kanta,kau da Kai yayi kana yace "what brings you here?"
Murmushin takaici tayi Tace " Magana nake so muyi"
" Dawa? "
" Dakai Mana"
A hankali yace "idan ina bukatar hakan ko? "

"At least Hashim ka tashi Mana muyi Magana dan Allah, tun fa da na shigo kake kallon bango, ko kallo na bakayi ba"
"Bana bukatar ganin ki Diyya"
" Hashim me yasa kake da taurin Kaine Dan Allah? Yanzu kana nufin ka rabu dani Kenan?"
" Eh" kawai yace a takaice,
Zagayowa tayi ta zauna a bakin gadon tana kallon sa, hawayen da ta gani a idon sa ne yasa ta Fara kuka, Tace "Hashim Dan Allah Kar ka Mana haka, ya kamata kayi bincike Kan ka yanke hukunci a kaina"

Tashi yayi tsaye sa hannun said yayi a aljihun three quarter wandon sa ya juya Mata baya, Kana yace "wani bincike ya rage nayi? Bayan Ni Nan ganaune ba jiyau ba" Yana maganar Yana d'an bubbuga faffad'ar kirjinsa

Cikin shesshekar kuka Tace "Wallahi tallahi ba abinda kake tunani bane kawai....." Juyo wa yayi a tsawace "kawai me? Nace kawaii me Diyya? Baki da abinda Zaki fad'a min, dama na dad'e ina zargin ki dashi Kuma kin tabbatar min da zargina"

Fashe wa tayi da kuka Mai sauti Tace " am sorry please Hashim kana tsorata ni ban tab'a gannin ka acikin irin wannan halin ba,kayi hakuri ka yarda dani Dan Allah"

" In yadda dake Kika ce? Hmm" ya share hawayen dake fuskar sa kana ta d'aura da fad'in "Ta ina kike so Na yarda dake,idan da dagaske kike ai da tun a ranar zaki nemi muyi sulhu Amma Baki Zo ba,sai d'azu Zaki kirani,sai da muka d'auki two weeks"
" Nasan Kana fushi ne shiyasa na bari ka huce"

A tsawace yace " To hell with you Diyya,I hate you"
Tashi tayi Tace "Karya kake Hashim you love me  Hashim and you'll forever do"

Murmushin gefen baki yayi ya d'aura hannayen sa a kunkunmin sa yace "Okay haka kikace?"
"Eh Haka nace,Kuma haka yake"
"Alright,get out of my room"
Yana Maganar Yana nuna Mata kofa

Cike da mamaki ta nuna kirjin ta Tace "Ni? I should get out?"
"Yes get out"
"Hashim Ni kake cewa na fita a d'akin ka?"
"Eh ke waye ce ke da ba zan ce ki fita ba? Kawai malama ki fice min daga d'aki"
Huci tayi Tace "Okay naji zan fita,Amma Hashim tell me one thing ya kake so muyi da su Daddy da mummy? Kasan cewa dawowar mu kawai ake tunda an Mana baiko"
"Wannan Kuma ke ta shafa ki fad'a wa iyayen ki cewar Ni Hashim Ahmad Shettima na janye Maganar auren dake tsakani na da ke"

Badiyya ganin Hashim dagaske yake tace "Kar kamin haka hashim,zaka sai  Mana dariya"
" Tunda ke baza ki fita ba Ni bara na fita bar Miki d'akin"
Wayar say ya d'auka ya nufi hanyar fita sai da yazo daf kofar yace "Idan kin gama ki rufe min kofar" yayi ficewar da, Badiyya bin bayan sa tayi da kallo ita gani take abin kamar Wasa Amma dagaske yake,zama tayi a bakin gado ta shiga kuka sai da tayi Mai isarta kana ta shiga toilet ta wanko fuskar ta, tana fitowa da fice daga d'akin ta rufe Masa kofar kamar yadda yace ta ajiye Masa makulli a inda yake ajiyewa.

Yana ganin fitowar ta yayi saurin d'aura waya a kunnen sa kamar Yana waya, kallon sa ta tsayi tafi minti biyar tana kallonsa,Hashim ganin zata iya Karya Mata zuciya hakan yasa yayi saurin barin gun, kad'a Kai tayi ta fice da ga compound d'in.

Yana ganin ta tafi ya koma d'akin,kwanciya yayi Yana jallony saman d'akin yana tunanin happy moments da sukayi spending da ita,tabbas Yana kaunar ta Amma bazai iya auranta ba.

Badiyya bata gaji da bibiyarsa ba,amma ganin wulakancin a yake Mata hakan yasa ta hakura,har suka kammala projects d'insu Bai bari sun hadu ba haka Kuma baya picking calls d'inta d'ga bisa ni yayi blocking d'in ta,ya goge duk wani abun da ya shade ta, number ne kad'ai ya bari Shima Kuma bai San dalilin da yasa ya kasa gogewa ba.

NIGERIA
A tsawace yace "Baka da hankali dama ban sani ba? Ni kake so ka kunyata a idon duniya Hashim?"
Kai a kasa yace "No  daddy ba haka  bane, babu yanda za'a yi na jawo maka abin kunya,Amma idan ka bari aka d'aura aure na da Badiyya shine abun kunya ba auren ta ba"

Zama Daddy yayi yace " Me yasa kace haka,akwai wani abinda ya kamata na sani wanda ban sani ba?"
"Eh Daddy"
" Uhmn ina sauraron ka" Maida hankalin sa yayi don ya fahimci inda Maganar tasa ta dosa, bai rage komai ba haka Bai Kara komai ba, Mummy dake zaune tun d'azu akan sofa Tace "Kai Hashim kaji tsoron Allah ka fad'a mana gaskiya dukkanin mu mu mun San Badiyya yarinya ce mai tarbiya"

" Hakane Mummy amma Badiyya da kuka sani a baya dabance da ta yanzu"
Ta amsa da " Allah ya kyauta"
Suka amsa da "Ameen"
Daddy yace "Tashi ka je zan duba na ga yanda za'a yi"
Yace "Toh Daddy na gode"
Ya tashi ya fice.

Daddy Maida kallon sa yayi ga Mummy yace "Amina,ya kike ganin zamu b'ullowa al'amarin yaran nan,wallahi kaina ya kulle"
" Nima haka Alhaji,to Amma ya zamuyi yaron Nan dai shi ga yarinyar Nan yace Yana so,Kuma yanzu yace ya fasa bai kamata mu sa shi yin abinda baya so ba"

"Okay idan ma fahimce ki,so kike na janye Maganar auren sa da Badiyya Kar ki manta fa, Mahaifin yarinyar Nan amini na ne fa,idan na Masa haka ai ban kyauta Masa ba"
" Hakane Alhaji,Amma ya kamata ka Sani yaran yanzu ka haife sune Amma baka haifi halinsu ba,tunda yace baya so a janye Maganar Kar Kuma a Zo Ana da na sani"
"Kai Amma banji Dadi ba ko kad'an yanzu ban San yanda zan tin Kari Alhaji Usman ba"

" Ka kwantar da hankali Alhaji,yanzu tunda dama jiran su Hashim ake a had'a auren su day Fadeelah ina ga kawai gara a Sanar dasu ayi bikin Nan Nan da wata d'aya"

"Toh Shikenan zan

Please Login or Register in order to submit comment