Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ahmad Shettima, tabbas ina Jin Labarin guy d'in Amma ban tab'a tunanin kyawunsa ya Kai haka ba"

*WANE NE HASHIM AHMAD SHETTIMA?*
Hashim Ahmad Shettima d'ane ga Alhaji Ahmad Shettima, Ahmad Shettima shahararren d'an kasuwa ne Wanda yayi suna idan baizo a na farko ba, zai zo a na biyu, hakan yasa Bai fiye Zama ba yawanci a kasar waje yake business d'in sa, matar sa d'aya Hajiya Amina da 'ya 'ya biyu Hashim da Fadeelah,a sanadiyar neman na halal d'insa jirgin su ya fad'i ya Kone kurmus, iyalan sa sun Shiga tashin hankali sosai Amma babu yanda suka iya kullu nafsin za'ikatul maut.


Bayan rasuwar Alhaji Ahmad, Suraj Wanda ya kasance PA d'in Alhaji Ahmad ya Auri Fadeelah suna zaune cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali Babu abinda ta rasa har ta Haifa masa Yara biyu Adnan da islam, Hashim Kuma bayan rasuwar mahaifin nasu ya Koma kasar waje karatu ya karanci business, bayan ya gama ya dawo gida ya Fara kula da harkokin Mahaifin nasa.
Wannan shine cikekken tarihin Hashim.


"Hashim 'din Soyayya yake da Asiyah? Kai it can't be" tashi tayi tana kaiwa tana kawo wa " Dole na San abin da zanyi akai, sabida na kamu da son sa bugu da Kari Yana da kud'i Dole na rarrashi Mummy ta nema min mafita."

A Haka bacci ya d'auke, Hashim na tuki mamaki yake a zuciyar sa yace "Wannan wani irin gidane haka, tabbas yarinyar da na gani Yar uwartace don suna mugun Kama, Amma daga shigar ta kasan Yar hutu ce , Amma Asiyah kayan jikin ta duk a kod'e? Hatta uniform d'in da na Fara ganinta dashi a yage suke, Kai Dole na fad'ad'a bin cike akan ta, I need to help her."

Zaro wayar sa yayi a aljihun rigar sa ya yi dialing number faisal, Faisal daga d'ayan 'bangaren ya amsa da "Yane mutumina?"
"Kalau fa kana ina?"
"Ina gidan su zee"
" Mtswws Kai kullum sai ka jene, baka gajiya? "
" Gajiya haba malam ai gaya maka idan kaga na daina zuwa to nayi wuff da ita ne"
" Hmm to Allah ya kyauta yanzu ya za'a yi? Ina son ganin ka, ko na zone?"
" A'a malam idan na gama zan Zo har gida na same ka Kar ka rage min hanzari"
"mtsww zakaji dashi ai, sai kazo"
Sai ya katse wayar, ya Koma gida Yana zaman jiran zuwan sa.


Maman Yesmin tunda ta Koma gida ihu da nishin Boko da Baraka ne ya tsaya Mata a rai duk hankalin ta ya tashi wani irin feelings take ji, da zaran ta tuna sai ta taune baki Nan take marar ta ya Fara ciwo, sai saki take ta jaa a fili tace "Kai wallahi auran soja ma matsala ne yanzu ina bukatar mijina ba hali"

Wayarta ta d'auko ta bud'e Facebook account da sunan Maman Yesmin, Nan da Nan akayi ta turo Mata friend request, Kun San maza da zaran sun ga sabon account anyi ta rushing ana turawa request, tun da Fara accepting request a kwance take a gun har akayi sallar Maghriba da Isha bata tashi a gun ba, dake Yesmin ta tafi hutu, ita kad'ai ce a gidan.

Ana cikin hakan tayi arba da wani request Mai suna *Zahra Yar less* , da sauri ta bud'e profile d'in ta duba Tace "Wow garin mu d'aya" profile picture ta bud'e ganin hoton wasu Mata tsirara suna alfasha ta sake taune bakin ta, ganin nayi ta cire zanin jikin ta, ware kafafun ta tayi a kishingid'e ta Fara satisfying kanta, Ni ko da na hakan nayi sauri na fita na jaa Mata kofar nayi gaba abina.


*HASHIM*
"To gani duk kabi ka Dame Ni da Kira Wai ya akayine kam?"

"Faisal please Ina so Kan taimake ni ne"
"Ina sauraron ka taimako wani iri Kenan?"
" Maganar yarinyar Nan Asiyah"
Kallon sa Faisal yayi yace "Asiyah Kuma wace ce ita d'in?"
"Asiyah ta Mana,Wacce muka ganta ranar a GRA? "
" Oh kace min yarinyar da ka kusa kashe mu a kanta"
" Koma dai mene ne, tunda ka gane ta buri na ta cika, ina son yarinyar Nan so na aure? "

Gyara Zama Faisal yayi yace "Aure ka tabbata auren ta kake son yi kuwa?"
"Eh na tabbata so nake na aure ta, na gama Rayuwata da ita sabida ina sonta sosai"
"To yanzu me mafita kaga bamu San gidan su ba ko?"
"na sani"
"lallai dagaske kake har ka Nemo gidan su?"
" Tsaya Nan ai Wanda yake son d'an tsuntsu shi ke binsa da jifa"
" Ba shakka hakane yanzu idan ka shirye sai muje"
"alright Amma ba yanzu ba ina so na fahimci wani Abu a tattare da ita tukunna"
" Me Kennan Hashim? "
" Zan Sanar da Kai when the time comes"
" Kan ka akeji in tayi tsami zumuji"
Murmushi kawaii Hashim yayi, sukayi ta Hira har sai da akayi sallar Maghrib Faisal ya Koma gida.

*BAYAN KWANA BIYU*
Hashim ya Shiga damuwa tashin hankali na rashin ganin ta, ko Wacce Rana sai ya fita ya yi parking a layin su Asiyah Amma baya ganin ta sai ya dawo gida Rai a 'bace ya daina kula kowa sai dai ya shige d'akin sa ya kulle kofa.

Da Sallama ta Shiga katafaren parlor bin parlon take da kallo ganin yanda ya had'u har sai da ta Raina gidan su ta shagala sosai wajen kallon makeken hoton Hashim dake manne a bangon d'akin, motsin da taji a bayan tane ya dawo da ita daga tunanin da ta Lula, Murmushi tayi kana Tace "Sannu da zuwa yarinya"
"Yauwa Sannu ina wuni hajiya"
" Lafiya kalau zauna Mana"
Tana muna Mata sofa dake gefen ta, Zama tayi kana Wacce ta Kira da hajiya Tace "Gashi Kuma kamar ban gane ki ba"
Tana maganar tana sake Mata kallo ko zata gane ta.

Gyara Zama tayi Tace "Baki sanni ba,asali ma yau ne Kika Fara gani na a Rayuwar ki"
" Oh to to madallah, ya zan taimaka Miki?"
"Hajiya suna na Safiya, Hashim nazo nema"
Kallon ta ta sake yi dakyau, kana Tace " Hashim kike nema?"
Ta amsa da "eh" da fatan dai Lafiya ko?"
" Eh lafiya lau"
" Aiko hashim baya Nan ya fita"
Dafe Kai tayi kamar wata Mai Jin ciwon kai, kana Tace " Kash to Shikenan" ta mike ta d'aura da fad'in " Ni zan tafi sai anjima"
" To mu Jima dayawa"
Tasa Kai ta fice, tab'e baki hajiya tayi Tace " Oh yaran zamani ba kunya har gida,har gida kizo neman na Miji? To Allah kashirya Mana" ta shige ta.

Fitar safiya ke da wuya ta hango motar Hashim, Murmushi tayi had'e da Dariya karasawa tayi inda yayi parking, tabbas yayi mamakin ganin ta cikin sauri ya fito yace "Lafiya me Kika Zo yi anan?"
"Nazo wurin Kane so nake muyi wata magana
"Okay, Zo Muje mu zauna a chan"
Yana nuna Mata garden dake d'an nesa dasu, ba b'ata lokaci suka Isa gun suka zauna, babu wanda ya furta komai Hashim ganin shirun yayi yawa ya gyara murya yace "Ya dai since zamuyi magana Kuma kinyi shiru?"
Murmushi tayi kana Tace "Hashim na San baka sanni ba, baka ma San suna na ba"
Yace "hakane"
"Suna na Safiyya kanwace a gun Asiyah"
"Umm ina sauraron ki"
" Hashim tun raanar da na Fara Jin sunan ka naji kana burge Ni,bani da buri illa na ganin ka, sai Kuma gashi Allah ya kawo Kan gidan mu a saukake,tun ranar da na Fara ganin ka hankalina ya kasa kwanciya naji na kamu da son ka, I love you hashim"
Murmushi yayi yace " Dan Allah da gaske kike ko wasa?"
Murmushi tayi kana Tace "dagaske nake am in love with you."

"hakan ba matsala bane don kin Soni, Amma Ni Asiyah nake so,am in love with her, zamu iya Zama abokai in ba matsala"
Shiru tayi sannan tace "To Shikenan naji" ta mike da niyar tafiya, hashim Shima mikewa yayi yace "tafiya Zaki yi? Ki tsaya ko ruwan sanyine a kawo Miki"
"A a nagode" ta juya tayi tafiyar ta, tana ji Yana Kiran sunan ta tayi burus dashi, tab'e Baki yayi ya d'aga kafad'ar sa ya d'aura da fad'in "chan Miki" ya shige cikin gida.
💦💦💦💦💦💦💦💦
MU HAD'U A PAGE NA GABA

PLEASE SHARE AND COMMENT
*MILHAAT CE YAR TERAWA*

💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
*MATAR UBA*
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```NOT EDITED
CHAPTER 14```
"A a nagode" ta juya tayi tafiyar ta, tana ji Yana Kiran sunan ta tayi burus dashi, tab'e Baki yayi ya d'aga kafad'ar sa ya d'aura da fad'in "chan Miki" ya shige cikin gida.
💦💦💦💦💦💦💦💦
.......... Rai 'bace ta bar gidan, bata nufi ko Ina ba sai gida, tana Shiga compound na gidan ta hangi Asiyah da shamsiyya a zaune suna Hira, ta gaban su ta wuce bata kula su ba kitchen ta nufa ta d'ebo ruwa cikin bucket tayi waje dashi, ba tayi wata wata ba ta watsa musu ruwan, a razane duk su biyun suka Tashi.

Kama Baki tayi Tace "Oh my God ban San da akwai mutane anan ba" ta had'a da tsaki ta juya da niyar komawa d'aki shamsiyya Tace "Me dakata mu sa'annun ki ne? By waye ba ki iya bada hakuri Baki?"
Tsaki ta jaa ta juya ta tafi, ganin shamsiyya ta yo kanta tasa ihu ta Ruga a d'ari.

Huci sosai shamsiyya take, Asiyah sai hakuri take ta bata , shamsiyya Tace "Asiyah Dan Allah ki barni na koya Mata hankali, baki ga abinda tayi Mana bane?"

" Na gani, na gani Mana kiyi hakuri Kar ki kulata , neman maganace kawai"
"ai kuwa da ta Kashi na jaki, taci Albarkacinki if not da sai ja karya ta"
" Nagode nagode Muje na raka ki"

WASHE GARI
A hanyar ta ta dawo wa daga talla ta tarar Yana jiran ta, bayan sun gaisa ta nemi ya rage Mata hanya Taki, ya lura motar ne Bata son Shiga, hakan yasa ya kulle motar ya dauka Mata roban suna tafiya suna Hira anan ne ya mata tambayoyi game da Rayuwar ta sannan mene ne matsayin Safiyya a gunta, Bata 'boye Masa ba ta Sanar Masa da ita d'in kanwartace Amma ba Uwa d'aya ba, isar su ke da wuya ta hango motar Baraka sai da Taki kamar ta arce da gudu, Amma sai ta rike kanta Kar tayi abin kunya, Baraka parking tayi kana ta fito tana mishi kallon sama da kasa , cikin girmamawa ya gaida ta, hannu ta d'aga Masa had'e da daga Masa tsawa "Dakata who are you?"
Murmushi yayi yace "Sunana Hashim Ni Abokin tane"
" Aboki wannan wani sabon iskanci ne haka da zakace min Kai a Abokin tane, don rashin kunya shine harda rike Mata roba"
Ta Maida kallonta ga Asiyah Tace "ke don uwarki ki wuce cikin gida"

Kuka ta Shiga yi tana fad'in "Dan Allah mummy kiyi hakuri"
"Okay baza ki wuce ba kenan?"
Jiki a Sanyaye ta shige Ciki, Baraka ta fizgi roban da ke hannun sa , Tace "Kayi saurin barin Nan ko nasa a Canza maka kamanni"

Barin wurin yayi ba tare da ya ji me zatace ba, duk hankalin sa ya Tashi, ya koma gida, mahaifiyar sa na ganin sa ta bi bayan shi ganin yanda d'an nata ya sauya lokaci guda bayan ba a Haka ya bar gida ba, "son me ke damin ka ne?"
Kallon ta yayi da idanun sa da suka canza kala daga Fari suka koma jaa, murmushin takaici yayi ya hura iska Mai zafi kana yace "Ba komai kawai dai kaina ne ke ciwo"
"Kan ka na ciwo baza kasha magani ba sai kace wani yaro"

"Ai yaron ne Amma fa gunki"
Murmushi tayi Tace " Allah ya shirya min Kai son, dama akwai maganar da nake so muyi da Kai"
" To mummy ina sauraron ki"
" Son kasan kawata Nana? Mahaifiyar Yesmin"
" Eh na Santa"
Murmushi tayi Tace Good so nake kaje gun Yesmin ki fahimci juna mun zauna munyi shawara da mahaifiyar ta ya ta muka duba muka gani mu Kara dankon zumuncin mu, kaga idan kunyi aure ba abinda zai raba mu"

" Mummy kiyi hakuri akwai Wacce nake so"
Shiru tayi Sam Bata ji dadin maganar na sa ba, dai daita kanta tayi Kan Tace " Wace ce ita? Kar dai Yarinyar da tazo neman ka ranar?"

Murmushin gefen baki yayi yace " A a wannan Safiya ce Yar uwar Asiya uban su ne d'aya"
Tab'e Baki tayi Tace " Toh Shikenan Allah ya tabbatar da alhairi" ya amsa da ameen.

*BAYAN SALLAH ISHA*
hankalin Asiya ya kasa kwanciya, ta rasa dalilin da yasa duk sanda ta ganshi sai taji hankalin ta ya kwanta, Bata tab'a Jin haushi Baraka ba irin na yau Sam Hashim Bai chan chanci haka ba, a zabure ta Tashi ta sa hijab a jikinta ta fice daga gidan tayi sa'a Mai gadi Yana ban d'aki duk da tasan ba zai Hana ta fita ba,Kai tsaye gidan su Hashim ta nufa ta dad'e a tsaye a bakin gate kwasam sai ga motar da ,tun daga nesa yake hango mutum dake akwai street light a gun sosai, sai da ya karaso gate d'in ya gane ta,Yana ganinta ya kashe motar ya fito da saurin gaske had'e da gudu, ya karasa inda take Yana fad'in "Asiyah kece?"
Murmushi tayi ta amsa da "Eh nice"
"Kina lafiya? Me Kika Zo yi anan?"
"Nazone na baka hakuri akan abinda aka maka"
Murmushi yayi yace " No need ai Asiyah,Zo mu Shiga cikin mota,ba musu tabi bayan sa da kansa ya bud'e Mata marfin motar bayan ta shige ya Maida ya rufe ya zaga Shima ya zauna.

Murmushi yayi yace "Asiyah na tambaye ki Mana please"
"Ina sauraron ka"
"Matar Nan ta 'dazu wace ce?"
"Matar Uba na Ce"
" Kai Amma bata da kirki, but kiyi hakuri fa na aibata mummyn ki"
Murmushi tayi Tace " bakomai"
Gyara Zama yayi yace "Asiyah akwai abinda na dad'e ina son fad'a miki Amma ban San ya Zaki d'auki zancen nawa ba"
" Mene Ne ina sauraron ka"
"Asiyah ina kaunar ki Soyayyar da ban tab'a yiwa wata a duniya ba"
Murmushi kawai tayi, yace " kin yi shiru?"
Rufe fuskarta tayi da hannayen ta, Tace "Nima ina kaunar ka Yaya Hashim"
Wani huci yayi na samu nasara Kan ya matso da kanshi kusa da nata, yace "Dan Allah dagaske kike?"
Kai kawaii ta d'aga Masa alamun "Eh"
"Alhamdulillah insha Allah baza kiyi Dana sanin Soyayya Dani ba"
Gani yayi har ta bud'e kofar ta fita da sauri ya Sha gabanta " ina Kuma Zaki?"
"Zan koma gida kar mummy ta nemi Ni"
"Hakane Muje na yi dropping d'inki"
" A a Kar ka damu yanzun Nan zan Isa"
" Bazanyi wannan gangancin ba kin manta ranar abinda yaso ya same ki da dare Allah ne kawai ya tsare? Kawai ki Zo nayi dropping d'inki"
Ba musu ta Shiga a dai dai bakin layi su ajiye ta, tana Isa ta shige d'akin ta.

Maman Yesmin charting take sosai da maza kala kala aciki har sukayi sharing contact da mutum uku suna WhatsApp suna Facebook, tafi wata d'aya haka, abban Yesmin ya lura da tana dare a online Kuma bada shi take chat ba, abin Bai dame shi ba ya d'auko Normal abune ganin abin sai gaba gaba yakeyi hakan yasa ya kudiri aniyar gano me takeyi.

Tana gaiyatar samarin ta gida idan Yesmin ta tafi makaranta ko islamiya, ko Kuma sai tayi bacci su shigo, hankalin ta akwance bata da wata damuwa da ta rage.

"Abokina na rasa dalilin da yasa Mata ta take chat har saita raba dare Kuma ba Dani take chat ba,abin Yana damina"
Murmushi yayi Kan yace "Ko dai zargin matar ka kake"
"Eh to kusan hakan dai, sabida abin yayi yawa gaskiya"
" Maybe tana chat da qawayen ta ne"
" Kawaye har ukun dare? Kai bazaiyu ba"
"yanzu abinda za'a yi na iya tracking zamu ga dukkanin abinda take yi zan duba maka,Amma fa kamin alkawarin duk abinda muka gani baza ka sake ta ba, sabida bana so na Zama sanadiyar mutuwar auren ka"
" Na amince"
" To Shikenan insha Allah Zan duba maka"
"To na gode Abokina."

Cikin dare ya yi tracking yaga irin chat d'in da Nana takeyi, hankalin sa yayi mugun Tashi, sabida bai tab'a ganin shaid'aniyar mace irin ta ba, yanzu ya rasa abinda zaicewa Abokin nasa shin ya fad'a Masa ne ko Kuma don babu Wanda zai ga irin wannan kazantar ya cigaba da Zama da ita, don ko shine yaga hakan bazai Bari ba.

*NEXT DAY*
Abban Yesmin ne ya shigo d'akin Abokin nasa, "Abokina ya akayi kasan jiya kasa bacci nayi shin ka duba min ne ko Kuma,wallahi da abin na kwan a raina."
Kallon sa kawai yayi kana ya kau da Kai yace
"Na duba"
"Uhmnn ina sauraron ka"
"Yaushe rabon ka da zuwa gida?"
"Eh to na Kai watanni shida ban je ba"

Murmushin takaici yayi yace " Ko kad'an ban ga laifin Nana ba Kaine ka cutar da matar ka lalata Mata Rayuwa"
" Kamarya Kenan ban fahimce ka ba?"
Gyara Zama yayi Kan yace " Ka saurareni da kunnen basira"
Yace "Kai nake sauraro"
💦💦💦💦💦💦💦💦
Kakakara Kaka,yau akeyinta, fansa yakuje ganin zata kasance shin Kuna ganin idan ya rufa Mata asiri yayi dai dai,ko Kuma ya fad'a Masa don Kar ya cutar da Abokin Sa?

Ina jiran amsoshi da comments d'inku

*MILHAAT CE YAR TERAWA*

PLEASE COMMENT AND SHARE



💦💦💦💦💦💦💦💦
*MATAR UBA*
💦💦💦💦💦💦💦💦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```NOT EDITED```
```CHAPTER``` ```15```
Murmushin takaici yayi yace " Ko kad'an ban ga laifin Nana ba Kaine ka cutar da matar ka lalata Mata Rayuwa"
" Kamarya Kenan ban fahimce ka ba?"
Gyara Zama yayi Kan yace " Ka saurareni da kunnen basira"
Yace "Kai nake sauraro."
💦💦💦💦💦💦💦💦
.........."da farko dai zan sa so ka sawa zuciyar Kan ruwan sanyi, sannan ka tuna da alkawarin mu da Kai"
"ina sauraron ka"
"matar ka tana cin amanar ka kamar yanda kake zargi,nayi screenshot d'in chats d'in gashi ka gani da idon ka"
Ya Mika Masa wayan, Abban Yesmin ya karb'i wayan hannun sa na rawa, kirjinsa na dukan uku uku, ya fara karanta chat d'in tun Kan yayi nisa idon sa ya cika fal da hawayen bakin Ciki, kasa karanta sauran chat d'in yayi ya Mika Masa wayarsa.

Murmushin gefen baki Abokin nasa yayi yace "Kaji ba dad'i ko? To Kar ka ji haushin kowa sai Kan ka sabida kaine ummul aba'isin abubuwan da take yi"
Rai a 'bace yace "kamarya zaka ce laifina ne? Bayan kaga Abubuwan da take yi"

"Kaine mana, yanzun Nan kace min ka Kai 6 months baka je gida ba, how do you expect her to do Kai ka na Nan kana bin matan banza hankalin ka a kwance ita Kuma ka kyaleta a chan ko oho, kaga Ni I know nayi nisa da matata, Amma hakan baya hanani zuwa ko Kuma ita tazo, sabida ba iya abinci bane hakkin ta akanka kamar yanda kake da hakki a kanta haka itama take da hakki a Kan ka"

Shiru yayi kana yace "Amma kasan idan na Miji yayi iskanci ado ne a gunsa ko?"
"Lallai ma bawan Allan Nan a wani aya ko hadisi akace haka?"

Shiru yayi kawai Yana kallon sa, alamun bayi da amsa, kad'a Kai yayi yace " You see baka da hujja iskanci wani riba ka samu a Ciki? Banda tarin zunubai? Kamar yanda kake Zina da Yar wasu Kai ka za'ayi wa naka, haka da matar ka sabida itama 'yace so ni Banga laifinta ba dama ai ramuwar gayya tafi ta gayya"

"Hakika nayi babban kuskure da na Maida Zina abin yi, Ni gani nake abinda nake yi waye wa ce, Amma yanzu ka tada Ni daga baccin da nake, yanzu tell me, me zanyi don Wallahi kaina ya kulle"

"Abu Mai sauki kawai ka dawo da ita Nan ko Kuma ka nemi posting a Maida ka gida, but a shawarace ka dawo da ita Nan zaifi"
" Toh Shikenan nagode sosai Abokina, na godewa Allah da ya bani Kai a matsayin Abokina"

Murmushi kawaii yayi, ya cigaba da Danna wayarsa.

"Asiyah!! Asiyah!!! Safiya ce ke Kiran sunan ta tana bubbuga Mata kofa, a hankali ta bud'e kofar idon ta a kumbure da alama Tasha kuka ne Kan tayi bacci, tsaki taja tace "Malalaciya kawaii, tun dazu ake kiranki kina Jin mutane" wurga Mata Abu tayi Tace "Gashi inji mummy ki sayo Mata kosai" tana kai Nan ta tafi, Asiya jiki ba Karfi ta durkusa ta d'auki kud'in taga naira biyar ce, tab'e Baki tayi ta shige toilet ta wanko fuskar ta ta fice daga gidan, bayan ta sayo kosan a hanyar ta ta dawo wa suka had'u da Hashim Yana exercise, Yana hango ta ya Fara Murmushi bayan sun gaisa ta Sanar dashi zata wuce gida, baice komai ba ya Bata hanya ta wuce, kallonta ya tsaya yi har sai da ya ga ya daina ganinta kana ya cigaba da gudun sa, Asiyah na komawa gida ta tarar da Mummy da safiya a tsakar gida, durkusawa tayi har kasa Tace "Mummy ina kwana?"
"A gidan ubanki na kwana" a tsawace

Asiyah ko kad'an hankalin ta bai tashi ba don Inda sabo ta saba, "har zakice min ina kwana? Wato Asiya Rayuwar da Kika zab'awa Kanki Kennan ko, iskanci Zaki Fara yimin a gidana? Wallahi tir da halin Baki Isa tun daga yanzu kina fita kina kwana waje ba"
Asiya dafe kirjin ta tayi a tsorace ta mike ta tsaya Tace "Kwana a waje Kuma mummy wallahi Ni ban kwana a waje ba yanzun Nan na fita Kuma safiya ce tace kin aiken na sayo kosai gama ledan" tana nuna mata ledar dake hannun ta.

Murmushi gefen baki tayi Tace "Saifiya a Ina kika ganta?"
"Mummy yanzun Nan na fita don na Sha iska na hango su a wani lungu Yana rungume da ita sai kiss yake Mata"

" Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, haba safiya kiji tsoron Allah sharri Zaki min?"
Wata mahaukaciyar mari ta mata Tace "Don uwar ki safiya ce zata Miki? Safiya je ki d'auko min ruwan nan"

Wani shu'umin dariya tayi ta shige Ciki Bata d'au lokaci ba ta fito da wata karamar roba a hannun ta Baraka duka ta Fara kaiwa Asiyah ta ko ina, sai da ta Mata dukan tsiya Wanda ko Motsi ba ta iya yi da kyau, cikin sauri ta karb'i roban da ke hannun safiya ta watsa Mata a Ido, ihu Asiya take yi tana kuka a kawo Mata agaji, tana ihun "Idona Idona Mummy Idona Dan Allah ku taimake Ni" a daddafe ta rike kafar Baraka ba tausayi ta hankad'e ta dafa, ta riko hannun Safiya suka barta a gun, baba mao gadi da yanzu shigowar sa ya karasa inda take da gudu Yana Kiran sunan Asiya "Asiya me ya same ki?" A tsorace yake maganar don ganin yanda take ihu tana tsalle,tausayin ta ya Kama shi sosai
"Baba idona, Idona Dan Allah ka taimake Ni, Ka kaini asibiti"

Cikin Rawar murya yace " Toh toh tashi muje" Yana 'daga ta ya goya ta, duk da Yana Jin nauyin ta sosai hakan Bai hanashi gudu ba , shi a tunaninsa acid aka watsa Mata, a gajiye suka Isa wani private hospital dake kusa dasu, emergency aka karb'e ta, idon akayi kokarin wanke wa Amma aikin Yana bukatan kud'i sosai.

Likatan ce ta fito ta nufi Inda baba Mai gadi yake Tace "Kaine ka kawo yarinyar Nan

Please Login or Register in order to submit comment