Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko?"
Cikin Rawar murya ya " eh eh nine"
" Okay Amma ya akayi Naga ruwan barkono a idon nata? "
Zaro Ido yayi yace ruwan barkono?"
"Yes ruwan barkono"
💦💦💦💦💦💦💦💦
Mu had'u a page na gaba
PLEASE SHARE AND COMMENTS

MILHAAT CE✍🏻


```CHAPTER 16
NOT EDITED```
💦💦💦💦💦💦💦💦
Likatan ce ta fito ta nufi Inda baba Mai gadi yake Tace "Kaine ka kawo yarinyar Nan ko?"
Cikin Rawar murya ya " eh eh nine"
" Okay Amma ya akayi Naga ruwan barkono a idon nata? "
Zaro Ido yayi yace ruwan barkono?"
"Yes ruwan barkono"
💦💦💦💦💦💦💦💦
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Amma ya akayi Asiya tasa ruwan barkono a idonta?" Yana wannan maganarne a zuciyar sa, maganar da likata tayine ya dawo dashi daga tunanin da ya Lula cikin Rawar murya yace "Na'am likita me kikace?"

A karo na biyu ta Kuma maimaita maganar da tayi " Ana bukayar million biyar Wanda za a wanke Mata Ido cikin gaggawa daso samune ka ayi aikin a yau don idan ta Kwana a haka idanunta zasu it's lalacewa gaba ki d'aya ma'ana baza ta sake gani ba"
Baba Mai gadi Banda kalmar Innalillahi wa ilaihirraji'un babu abinda yake furtawa a nitse ta ce Masa "Baba lafiya kuwa"

Cikin rawa murya yace "Lafiya lafiya kalau"
"Okay to ayi maza a Nemo kud'in Nan"
"To likita" tana kai Nan ta yi tafiyar ta.

Baba maigadi kansa ne ya kulle ya rasa abinda zaiyi ya tabbata Baraka baza ta had'a kud'in ba sannan Yana da tabbacin itace ta watsa Mata ruwa, d'akin da Asiya take ya Shiga, Banda shesshekar kuka babu abinda yake ji a d'akin cikin muryar tausayawa yace "Sannu Asiyah, Amma ya akayi Kika sa ruwan barkono a idon ki? "
" Baba Mummy Ce ta sa ruwan zafi sannan suka sa barkono aciki ta bud'e idanuna ta watsa min" ta karasa maganar cikin kuka.

" Asssha me Baraka take nema a duniyar nan, Ni ban tab'a ganin Mara imani irin ta ba, me laifin yarinyar Nan don tazo a matsayin Yar mijin ki? Yanzu gashi tana kokarin lalata Miki Ido Asiyah, million biyar ake bukata Don wanke Miki Ido, Asiya Ina zan samo makudan kud'in nan?" Ya karasa maganar Yana kuka Mai cin Rai, murmushin takaici tayi Tace "Baba ka daina kuka, me zai Hana kaje gun dangin mahaifiyata, Ina ga su kad'ai ne zasu taimaka min?"

'dago kansa yayi a hankali ya kalle ta kana yace "dama kina da wasu dangi a garin nan? Amma Kika zauna a gun maras imanin Nan tana gallaza Miki azaba? "

" Baba Suma sun gujeni sanadiyar Abubuwan da mummy ta ke musu tun suna hakuri har suka daina zuwa inda nake"
Huci yayi kana yace "Allah shi kyauta ya Shiga tsakanin mugu da na gari"
Ta amsa da " Ameen ba"
" A wace unguwa suke? sai naje na same su, don Tace min Kar mu d'auki lokaci cikin gaggawa ake bukatar ayi aikin"

"Bayan rasuwar mahaifiyata Aunty Rukayyace kad'ai da kakata suke zuwa inda muke, bayan mutuwar mahaifiyar mu da shekara d'aya kakar mu ta rasu, Aunty Rukayyace kad'ai ta rage min sai Kuma Uncle Suleiman Amma shi ba a kasar Nan yake ba"
Tayi Masa kwatancen unguwar da Aunty Rukayya take sannan ta Masa kwatancen gida, tashi yayi ya fita.


Yana Isa unguwar ya Shiga neman gida ya d'auki tsawon awanni biyu bai gane gidan ba duk da ya sha tambayar mutane daban daban daga bisani ya samu gidan, kwankwasa gate d'in yayi aka bud'e Masa bayan sun gaisa sai ta shaida Masa Rukayya yake nema ma'ana matar gidan, mutumin da ya bud'e gate d'in yace "Ayya ai sunfi watanni biyar Basu kasar Mai gidan ya samu chanjin wurin aiki sun koma chan da Zama"

Durkusawa baba Mai gadi yayi ya d'aura hannu a Kai yace "Allah Sarki Asiyah ke Kuma Taki kaddarar Kenan ya Allah gamu gare ka, Kai ka San yanda zakayi da wannan baiwa taka"

Da sauri Mai gadin ya fito Yana Kare wa baba Mai gadi kallo yace "Kamar sunan Asiya naji ka ambata ko?"
"Eh hakane" Yana maganar yana kokarin share hawayen dake idon sa, Murmushi yayi yace " Ai kuwa an bani sako na bata, Hajiya Tace tasan Dole watan watarana zata nema ta shiyasa ta bani wata takarda ina ka kamar wasika ce, bari na d'auko maka?"
Sai ya shige Bai d'au lokaci ba ya fito hannun sa rike yake da wata farar takarda ya mikawa baba Mai gadi had'e da fad'in "Dan Allah ka bata don Hajiya ta tabbatar min da cewar Yana da muhimmanci"
" Kar ka damu insha Allah yanzun Nan zan Kai Mata" sukayi ban Kwana ya Kama hanyar shi ta komawa asibiti Bai ji d'adin Jin Rukayya Bata gari ba Amma ya ji hankalin sa ya kwanta na ganin bata manta da Asiyah ba.


Tafiya yake yazo zai tsalle titi Bai lura ba wata mota ta sako Kai da gudu, ta kad'e shi Nan take yafi sumamme.
Nan da Nan mutane sukayi chaaa akansa, mutumin da ya buge shi ya fito a firgice jikin sa sanye yake da uniform na soldier da alama soldier ne, ya nemi taimakon mutanen dake gun a ka Sa Shi a mota Kai tsaye asibiti suka nufa, emergency room aka Kai shi sabida ya buge kansa ya zub da jini sosai.

Safa da marwa yake har likita ya fito yace "Kaine ka kawo mutumin da yake zub da jini?"
Ya amsa da "Eh nine"
Yace " Okay ya fita a danger mun samu mun tsayar da jinin yanzu Haka Yana bacci, Amma zamu rike shi anan sabida ya d'an bugu akan sa"
Iska Mai zafi ya hura yace " Kana nufin zai samu sauki ki babu abinda ya same shi?"
"Eh insha Allah"
"Ga wannan a aljihun sa aka samu, kamar wasika ce kuma da sunan wata akai"
Karb'a yayi ya duba ya ga an sa sunan " ASIYAH" da manyan harufa,
"Okay na gode sosai"

Wayar sa ce ta Fara ringing ya amsa da
"Hello abokina ya?"
"Kalau ka isa gidan ne?"
"A'a a hanya ta ta tafiya na buge wani yanzu Haka ina asibiti"
"Subhannallahi kaga shiyasa nace maka ka kwnatar da hankali Kar ka Bari sabida Nana ka cutar da kanka"

" Ya zanyi ne Ameenu? Ya zanyi? Yanzu fisabillilhi Nana abinda zata min Kennan, yanzu ko don yarmu Yesmin baza ta daina abinda take ba? Taya za a yi ina ji ina gani matata ta Zama public toilet kace min na kwantar da hankali na?"

" I know,I know it's not easy,but ya kamata kabi komai a Sannu ka fahimce Ni? Yanzu ina mara lafiyan yake hope dai da sauki?"
" Eh da sauki, bari na Shiga na duba shi"

" Okay Shikenan duk yanda ake Ciki let me know please"
"Alright ba matsala" a tare suka katse wayar.

Bayan ya Shiga ya duba shi ya fito ya nufi hanyar gida, a hankali yake driving don gaba ki d'aya ji yake kamar baida lafiya,Yana Isa layin gidan say ya hangi motar Maman Yesmin ta fito da alama fita zatayi, packing yayi don ganin inda zata je ganin ta yi gaba,yasa ya Fara bin bayanta ga mamakin sa har fita sukayi a cikin gari Bata tsaya ba Saida taje wani jeji kana ta fito ta shiga,tana tafiya tana waige waige,Shima parking yayi Dan nesa sa ita, ya dad'e a gun Yana jiran fitowar ta Amma shiru kake ji, bin bayanta yayi ga mamakin sa wata Yar karamar bukka ya gani,tun daga nesa yake jiyo muryarta tana wasu irin surutai Wanda yake fatan ba abinda yake tunani bane jiki a Sanyaye ya Shiga cikin bukkar, a tsawace yace "Nana" ba ita ba kad'ai ba harda boka ya tsorata don sunyi nisa cikin shashancin su Basu sanda mutum a gun ba,a razane boka ya tashi Yana kokarin duba inda wandon sa yake, ita Kuma ta neman inda kayan ta suke, cikin muryar kuka yake magana "Nana Ni? Ni zakiyi wa haka yau ke na Kaka red handed da wuni turmi da tarb'arya kin cuceni Nana, Allah ya Isa tsakani na dake" Banda kuka babu abinda da take yi, ganin bokan na kokarin guduwa ya cukumo shi ya fara na d'a Masa na jaki ran Soja ya b'aci sanda ya had'a Masa jini da majina ya kyale a tsawace yace "Ke kuka wuce mu tafi" jiki na rawa ta fice daga bukkar da gudu ta Shiga motar ta ta nufi gida Shima ya bi bayanta.
💦💦💦💦💦💦💦💦
Mu had'u a page na gaba

PLEASE COMMENT AND SHARE
MILHAAT CE
YAR TERAWA

💦💦💦💦💦💦💦💦
*MATAR UBA*
💦💦💦💦💦💦💦💦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
https://my.w.tt/74zuBLzuihb?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* 📚🖊️
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
```NOT EDITED```
```CHAPTER 17```

cikin muryar kuka yake magana "Nana Ni? Ni zakiyi wa haka yau ke na Kaka red handed da wuni turmi da tarb'arya kin cuceni Nana, Allah ya Isa tsakani na dake" Banda kuka babu abinda da take yi, ganin bokan na kokarin guduwa ya cukumo shi ya fara na d'a Masa na jaki ran Soja ya b'aci sanda ya had'a Masa jini da majina ya kyale a tsawace yace "Ke kuka wuce mu tafi" jiki na rawa ta fice daga bukkar da gudu ta Shiga motar ta ta nufi gida Shima ya bi bayanta.
💦💦💦💦💦💦💦💦
.......... Nana na isa gida Kai tsaye bed room d'inta ta nufa, a kusuwar d'akin ta rakub'e ta zauna sai aikin kuka take.

Baban Yesmin na shigow parlor bai ganta ba hakan yasa ya haura sama don ya tabbata tana parlor, Yana shiga d'akin yana ganin ta sai yaji tausayin ta ya Kama shi, tabbas so makahone Zama yayi a bakin gado ya had'a Kai da gwiwa ya rasa me yake masa dad'i, babu Wanda yace was d'an uwansa komai sun dad'e a Haka kana yayi ajiyar zuciya yace "Nana kin cuce Ni, kin zalunce Ni kin ci amanta, me na Miki da na chanchanci it wannan cin mutuncin, ke wace irin jarrababbiyace ina sane da duk Abubuwan da kike yi, jiya kin Kwana da wani da safen Nan ya tafi hakan Bai ishe ki ba Kika koma gun boka kazami, Kai ya Salam, Allahumma ajirni fii musibati, wannan masifa da me tayi Kama?" Ya karasa maganar Yana share hawayen da ke zubo masa.

Cikin kuka tace "Dan Allah kayi hakuri ka yafe min nasan ban chanchanci yafiyar ka ba amma Dan Allah ko don Yesmin...."

A tsawace yace "Yesmin? Da kin San da ita ne kike iskancin ki har cikin gida? Ke Baki ji tsoron Kar wataran ta ganki ba me zaki ce mata in ta ganki kina aikata wannan mumu Nan aikin?"
Kasa cewa komai tayi sai aikin kuka take ta dad'e tana kuka yayin da shi Kuma Yana jin zafin kukan nata sabida Yana son matar sa sosai, chan Ciki Tace "Abban Yesmin kayi hakuri wallahii bazan sake ba Amma Ina so late sani Nima ba yin kaina bane, Abban Yesmin kayi guje Ni ka fifita aikin ka a kaina yau kimanin wata shida Kenan ban sa ka a Idona ba, bayan kasan cewa ba ci da Sha da tufatarwa bane kad'ai hakkina Akan ka, Kuma ka hanani zuwa inda kake, kasanni Ni Wace irin mace ce Amma ko kad'an baka tausayi na... " Kuka ne ya kwace Mata ta kasa karasa maganar.


Maganar Abokin sa Ameenu ya tuna tabbas shine silar halin da ta Shiga ko da ace tana da laifi to nashi yafi yawa, cikin murya Mai sanyi ya ambaci sunan ta "Nana Khadija" a hankali ta d'ago kanta sukayi Ido had'u Murmushin takaici yayi yace "Kinyi gaskiya laifi nane Amma ki koma ga Allah ki ruki gafarar sa sabida Zina babban zunubi ne, da auren ki kike zina" shiru ya d'an kananya d'aura da fad'in " Bazan rabu da Ke ba sabida ina kaunar ki Nana, auren Soyayya mukayi sannan idan Yan gidan mu sukaji abinda kikayi har ya Kai ga mun rabu zasu min dariya, ke Kanki kin San irin wahalar da nasha Kan mukayi auren Nan, sabida Haka na yanke shawara zamu koma Kaduna da Zama ki Sanar da Yesmin ki Fara Shiri" tashi yayi har ya bud'e kofa sai ya juyo yace "ki shirya muje asibiti sanadiyar tashin hankalin da na Shiga d'azu na buge wani yanzu haka Yana asibiti Rai a hannun Allah."
Yana Kai Nan ya fita.


Nana tayi matukar da na sani har sai da taji ta tausayawa kanta har da shi mijin nata, ajiyar zuciya tayi ta d'aga hannun ta sama Tace "Ya Allah nagode maka da aka azurtani da miji irin Isah, ya Allah ka gafartamin" tana Kai Nan ta mike ta Shiga ban d'aki ta watsa ruwa ta tarar dashi a mota Yana jiran ta, Basu zarce ko ina ba sai asibiti, bayan sun Isa Kai tsaye d'akin da baba Mai gadi yake suka nufa har yanzu dai bai farka ba, hankali a tashe ya Shiga office d'in Dr, Dr ya tabbatar Masa da zai tashi ya kwantar da hankalin sa, zuwa yayi ya biya kud'in magani sannan suka soma d'akin da yake, shiru yayi baice komai Nana ce Tace "Abban Yesmin tunda Yana bacci me zai Hana mu koma gida sai mu turo Mairo tazo ta Rika kula dashi, Ina ga kamar barin shi, shi kad'ai abun baiyi tsari ba"

" Eh hakan za'ayi"
" Amma ya Naga Banga ciwon da yaji ba?"
" Eh dake ya juya Mana baya ne, ki koma ta gaban sa Zaki ga ciwon da yaji"

" A'a ba sai na duba ba, Allah ya bashi lafiya" ya amsa da "ameen, mu tafi ko? in ya so anjima mairon sai ta dawo"

Tace "to" a tare suka fita,suna Isa ta had'a was Mairo duk wani abunda zasu bukata a asibitin sannan Tace idan suna bukatar wani Abu ta kirata ta sanar da ita.

Yesmin na dawo wa ta ga Abban ta tayi matukar murna Amma Jin Labarin zasu bar garin jikin ta yayi sanyi Bata son hakan Amma babu yanda zatayi sabida Abban ta mutum ne Mai magana d'aya fatan ta hakan ya zame musu Alhairi.


Likita ganin har yanzu baba Mai gadi Bai dawo ba hakan yasa hankalin ta ya tashi tun sanda taji Labarin da Asiyah take bashi taji tausayin Yarinyar ya kamata hakan yasa ba ta tsaya b'ata lokaci ba ta tashi ta Fara duba patient d'inta d'aya bayan d'aya kwasam ta shiga d'akin da baba Mai gadi ya ke cike da mamaki take kallon sa Maida kallonta tayi ga Nurse d'in Dake bayan ta tace "Wannan fa me ya same shi?"

" 'dazune wani ya kawo shi ina ga kamar buge shi yayi"
" Subhannallah yaushe akayi haka?"
" Dr ai tun safe yake Nan Dr Hassan ne ya karb'e shi"
Maida kallon ta tayi ga Mairo Tace "ke Yar uwarsa ce?"
Ta amsa "Da eh"
Kad'a Kai tayi alamun ta gamsu Tace "To Allah ya bashi lafiya"
Duk suka amsa da ameen.

Fita sukayi daga d'akin a hanyar su ta Shiga d'akin da Asiya take tace "Ya Rabbis samawati Wai me ke Shirin faruwa ne da yarinyar nan Anya tasan ma bayi da lafiya?" A zuci take maganar Bata tare da tasan ya fito ba, Nurse Tace "Na'am Dr dani kikeyi ne?"

Cikin Rawar murya Tace "A aa ba dake nake ba, ungo wannan kije ki sayo min indomie da kwai" magana take had'e da Mika Mata kud'i, ba musu Ra karb'a ta juya zata tafi tace "idan kin dawo ki kawo min d'akin Nan" tana nuna d'akin da Asiyah ke Ciki ta amsa da " Toh Dr."

Da Sallama ta Shiga Asiya ta amsa, Likita Tace "Sannu ya jikin?"
Ta amsa "Da sauki Dr"
Gyaran murya tayi tana kokarin b'oye damuwarta " 'dazu kina bacci kakan ki yazo ya ce min bai samu kud'in ha Amma ya fita zai dawo anjima, sai dai gashi Naga har dare yayi lokacin tashi na tayi"

A dai dai Nan Nurse d'in ta shigo da food flask na abinci da d'an yatsa ta nuna mata inda zata ajiye, tana ajiye shi ta fita.

Asiya Tace "Allah sarki Baba Mai gadi sai faman wahala yake a dalili na"
"Gaskiya yana da kirki d'azu nazo wucewa naji Labarin da kike bashi gaskiya matar uba batayi ba, bata da imani ko kad'an, Amma Dan Allah ya sunan ki?"
"Asiyah"
" Masha Allah Asiyah, tun safe Baki ci komai ba tashi ki zauna, da fatan zaki ci Indomie?"
Murmushi tayi ta amsa da "Eh" dama Asiyah yunwa take ji kamar zata mutu rabon ta da abinci tun jiya da safe Nan ma shayi da two slice of bread ta ci, A Baki Dr ke Bata abincin sanda ta cinye shi Tass ta Bata ruwa Tasha Tace "Nagode sosai Dr, Allah ya daka da Alhairi"

Murmushi tayi Tace "Asiya kenan zan so ki kirani da Badiyya"
Ita ma Asiyah Murmushi tayi duk da bata ganin ta Tace "Toh Aunty Badiyya nagode"
Shafa kanta tayi tace "Bakomai Asiyah."

Shiru sukayi babu Wanda ya sake cewa komai, ko wanne zancen zuci yake Asiyah tunanin ta duk ya koma Kan baba Mai gadi a yayine da Dr Badiyya tunaninta ya koma Kan Asiyah,"shin Anya zan iya barin yarinyar Nan anan ita kad'ai? Kai ina idan nayi hakan hankali na bazai kwanta ba kawai zan Kwana anan muga yanda Allah zaiyi zuwa gobe"


Asiyah ce ta dawo da ita daga tunanin da ta Lula Tace "Aunty kince Zaki koma gida ko kamar dare Yana yi?"

"Eh Asiyah so nake na jira Nan da karfe Tara muga ko zai dawo"
" Yanzu karfe nawa ne Aunty?"
" Karfe takwas ne na dare"
Kai kawaii ta d'aga Mata,ita Kuma Dr Badiyya kallon agogon hannunta tayi lokacin karfe Tara har da rabi ne.


Hashim tun bayan rubuwar su day Asiyah yake Jin hankalin sa a tashe,ji ya jikin sa Asiyah na cikin damuwa Amma Taya zaiyi ya tabbatar da hakan,bazai iya zuwa gidan su ba sabida duk sanda yaje sai ya Zama dalilin kukan shi Kuma baya son kukanta ko da Wasa ne sannan bata da waya bare ya kirata.

Tashi yayi ya d'auki motar sa ya fice daga gidan a hanyar islamiyar su yayi parking Yana jiran fitowar ta daga gida ganin har karfe biyar tayi a fili yace "Maybe ta Riga ta wuce, Asiyah zan jira har ku tashi don hakan shine kad'ai kwanciyar hankali na."
Zama yayi agun kamar yace har karfe shida duk d'aliban sun wuce Amma bai ganta ba jiki a Sanyaye ya koma gida a ransa Babu irin tunanin da baiyi ba daga bisani yace "Kila aiki aka sata ko Kuma an Hana ta tunda sun Saba a haka ya kwanta bacci barawo ya sace shi.

Baraka da Safiya hankalin su a kwance yake babu abinda ya Sha musu kai kid'a suka saka kure Volume d'in sukayi sai shashewan su suke sun manta da maganar wata Asiya da Mai gadi,a fad'in ta gobe zata nemi wani tunda ya kuskura ta tsallake aikin sa ya bar Mata gate ba kowa.

*ASIBITI*
"Aunty Badiyya ki tafi kawaii abunki ba sai kin jira shi na Naga har yanzu Bai dawo ba"

Rike hannun ta tayi tace " Kar ki dmau Asiyah har Kwana sai muyi dake anan ban damu ba fatana Allah yasa ya samu kud'in Nan"
" Toh Shikenan Aunty Nagode."
A ranta Tace " Kiyi hakuri asiyah i have to lie, Dole na miki karya, don idan na fad'a Miki halin da yake ciki hankalin ki Kara tashi zaiyi."

Abban Yesmin karfe biyun dare ya fad'a ban d'aki yayi alwala sannan ya tada Nana "Nana bacci bai kamace mu ba ya kamata mu koma ga Allah don mu nemi gafarar sa"
Ba musu ta tashi ta d'auro alwala, tunda suka Fara jero nafilfili Basu tsaya ba har sai da aka Fara Kiraye-kirayen sallar asuba sai da sukayi sallar asuba suka koma bacci.

Yesmin ganin mahaifiyar ta bata fito ba hakan yasa ta Shiga kicin ta had'a wa kanta breakfast ta wuce makaranta.
💦💦💦💦💦💦💦💦
Mu had'u a page na gaba

MILHAT CE
YAR TERAWA
CHAPTER 18
NOT EDITED
💦💦💦💦💦💦💦💦
Yesmin ganin mahaifiyar ta bata fito ba hakan yasa ta Shiga kicin ta had'a wa kanta breakfast ta wuce makaranta.
💦💦💦💦💦💦💦💦

WASHE GARI
............ Hashim na farkawa bayan ya idar da sallar asuba ya kud'iri aniyar yau sai ya Asiyar sa, shiryawa yayi tsaf a gaggauce ya nufi hanyar gidan su Asiyah, tun karfe shida da minti arba'in yake kofar gidan su Yana zaune a cikin motar sa bai da wani buri sai na ganin ta, har bacci ya Fara d'aukan sa kasantuwar jiya ya kasa bacci, Jin karar mota yasa yayi saurin d'ago kansa dake Kan stairing motar, Murmushi yayi yace "Alhamdulillah makaranta za'a Kai su" bin bayar motar yake har suka Isa makarantar Amma ga mamakin sa Safiya kad'ai ya gani, jikin sa duk yayi sanyi, anan NE ya tuna Asiyah ta tab'a fad'a Masa bad kaita da mota murmushin takaici yayi har ya juya sai Kuma ya dawo cikin sauri ya Isa inda Safiya take sai kaud'i da Rawar Kai take, Sunnan ta ya Kira cikin sanyin murya da sauri ta juya don ta tabbatar was kanta abinda kunnen ta yake jiye Mata, a fad'in ta a tarihin rayuwar ta Bata tab'a gani ko Jin Mai murya irin tasa ba.

Murmushi tayi had'i da dafa kirji race "Na am" Shima murmushin yayi yace "Dan Allah in baza ki damu ba Inna so nayi magana dake."

A dai dai na bell na assembly ya Fara kara, Murmushi tayi Tace "Ba matsalar mu d'an koma daga gefe."

Bayan sun gaisa yayi shiru Yana kallon kafarsa ya rasa ta ina zai Fara tambayan ta inda Asiyah take a yayin da ita Kuma sai murmushi take "Finally Allah ya karb'i addu'a ta, idan ya furta kalmar so a gare Ni na bar makaranta Kenan don Wallahi, bazan Bari ya kufce min ba, I love you so much my prince" zancen zuci take, maganar da yayi ne yasa tayi saurin kallon sa Nan da Nan ta had'a Rai kamar bata tab'a dariya ba, Rai a d'an b'ace Tace "me naji kace?"

Gyara tsayuwar sa yayi yace "Cewa nayi, Inna Asiyah take in ta cikiyar ta yau kwanaki uku Kenan ban sa ta a Idona ba."

Wani abune taji ya rike Mata wuya, kirkiran Murmushi tayi Tace " Ban sani ba" tayi saurin juyawa don Kar yaga hawayen dake idon ta, cikin sauri ya rike Jakarta Yana fad'in "Dan Allah Safiya ki fad'a min inda take, zan biya ki ko nawa ne, Dan Allah ki taimake Ni" hannu a had'e alamun roko, girgiza kai tayi Tace " Me zakayi da wata Asiya Hashim kasan fa Ina sonka Kuma ina kaunar ka, harfa gidan ku naje na cire kunyata Amma kai baka gani, dame ta fini ne Dan Allah Hashim ka manta da maganar Asiyah" ta Kara maganar cikin kuka.

Tausayin ta ne ya kamashi don yasan illan rashin abinda kake, yace "ba Wai bana sonki bane ki fahimce ni hankali na ya karkatane a Kan ta, Amma yanzu maganganun ki sun San na fahimci wani Abu, zan Baki number ta sai muyi magana amma da Sharid'i d'aya" Yana nuna Mata Yar yatsan sa, sa hannu tayi ta share hawayen ta Tace "Mene ne sharad'in?"

"Sharad'in shine Zaki fad'a min inda Asiyah take, and I promise za mu zauna mu fahimci juna dake, Akwai Ajiyata a gun ta shiyasa Kika ga ba damu sannan abin sirri ne bawai ita d'in nake son gani ba, kin fahimce Ni?"

Kallon ka Raina min wayo ta Masa a zuciyar ta Tace "Ji d'an raining gabkaliy Ni zai rainawa hankali wai baya sonta, Amma idan Kuma dagaske yake fa? Kai Bai kamata na Bari wannan Daman ya wuce Ni ba, this is my only chance" iska ta hura tace " zan fad'a maka inda take, Amma ja sani idan na Kira ka baka d'aga ba bazan sake taimaka maka ba, sannan Ina so na San Wace irin ajiya ce"

Murmushin cin nasara yayi kana yace " Kar ki damu you have my words, Ina zuwa" komawa yayi mota ya d'auko katin sa ya

Please Login or Register in order to submit comment