Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nake"
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Asiyah Ashe haka Kika kware gun karya ki dubi tsabar idona kice min gidan su shamsiyya Kika kwana?" Tana maganar tana yarfa hannu.

" Wallahi daga chan nake Ni ba Yar iska bace"
Tab'e baki tayi Tace " Chan Miki matsalar kice ba tawa ba,tashi ki bani wuri ko yanzun Nan na Tara Miki na jaki"

Cikin sauri ta haura sama,tana Shiga d'akin ta ta sauke ajiyar zuciya, a bakin kofa ta zauna ta had'a Kai da gwiwa kuka take sosai Wanda hakan yasa idanun ta sukayi jajir jiyoyin kanta suka you rad'a rad'a, sai da tayi kuka Mai isarta ta Fad'a toilet tati wanka sannan ta d'auro alwala, bayan ta idar da sallar walha, ta d'auko kayan ta masu datti da niyar wankewa, backyard na gidan ta nufa ta Fara wankin kayan ta, zuciyar ta faal bakin Ciki duk duniyar taji ta daina Mata Dadi a fili Tace "Dama ace ni matattiyace, Ina ma ace nice ba mutu ba ku ba" ta karasa maganar tana kuka tasa hannu ta sharce majinan hancin ta.

Ba ta ankare ba sai gani tayi an waso mata Kaya masu uban yawa a razane ta mike ga mamakin ta Safiyya ce tsaye a gaban ta tana wurga Mata harara tsaki taja sannan Tace "Malama ki bar wanke kayan Nan da kike ki wanke min nawa yanzun Nan"

Murmushin takaici tayi sannan Tace " Safiyya nice zan Miki wanki" tana maganar tana nuna kanta, "eh ke Zaki wanke ko ban Kai na saki bane?"

"Lallai Safiyya wuyanki yayi kauri,ko ba komai ina gaba dake Amma kike min magana kamar wata sa'ar ki?"
" An Miki din Kuma dolen uwarki ki wanke"
" Uwata?"

Cikin sauri Asiyah ta shige cikin fidan tana Kiran sunan Mummy, cikin sauri ta fito "lafiya me ta Faru kike min irin wannan kiran haka?"
" Mummy Zo ki gani"

Cikin Rashin fahimta ta bi bayan Asiyah, Asiyah Tace "Mummy jinga abinda tayi Wai nice zan Mata wanki bayan nace Mata nice gaba da ita ta nemi ta zage Ni"

Yarfa hannu ta Shiga yi sannan Tace " Amma Asiyah kinyi mugun Raina Ni, yanzu ke don uwarki Kiran da Kika min Kenan, to me a Ciki don tace ki Mata wanki?"

" Mummy wanki fa wa Safiyya kanwatace Amma Kuma na Mata a gani na hakan Bai dace ba"
A tsawace Tace " Would you shut up your dirty mouth, ki wanke su sannan ki tabbatar sunfita idan Naga Basu fita ba sai kin sake wanke su, bayan haka Kuma ki goge Mata su, wuwuyar banza idan Kika sake min haka wallahi zan Miki illa"

Ta Maida kallon ta ga Safiyya ta ce " Ke Kuma ki wuce d'aki weather da zafi kije ki Sha sanyin AC"
Murmushi tayi Tace "Toh mummy" tare suka shige suka barta a gun zubewa tayi a kasa duk damuwar duniya ta hadu ta Mata yawa, kukan ma yanzu kasa yin shi tayi, a ranar wunu tayi tana wanki bayan sun bushe ta goge su, sai daff da la'asar ta gama , d'akin ta tashiga tayi wanka
Sannan tayi alwala, bayan ta fito ta saka jallabiyar da take sallah dashi ta shimfida prayer mat 'yar karamar tsaki ta jaa sannan Tace "An sa mutum zaiyi tarikussalat" tana idar da sallah Bata tsaya shafa Mai ba ta zurma uniform d'in islamiyar ta, d'akin Baraka ta nufa tayi Sallama Amma taji Shiru, a fili Tace maybe suna garden, cikin nitsuwa take tafiya harta Isa garden d'in sannan ne ta lura motar Baraka Bata Nan hakan ya tabbatar Mata da Bata gidan, "Safiyya idan Mummy ta dawo kice Mata naje islamiya"

Shiru Bata tanka Mata ba,ta sake Mata magana a Karo na biyu, Bata tanka ba, tab'e Baki tayi ta nufi gate, Cikin gadara da izza safiyya ta kwala Mata Kira "Asiyah!!!"
A nitse Asiyah ta waigo, hannu ta d'aga Maya alamun kizo, har ta juya zata tafi sai Kuma ta dawo da baya, "Gani lafiya?"

Sai da ta d'auki tsawon mintuna biyu tana tsaye Kan Safiyya Tace "Jinga wanchan" tana nuna Mata ledan pure water guda biyu sai tray na silver, da ido tabi hannun ta sannan ta Maida kallon ta gareta Tace "Eh ba gani ya akayi"

"Mummy Tace na Fad'a Miki ki d'auka kije ki sayar sannan idan baki sayar ba Kar ki dawo gidan Nan"
" Islamiyar da?"
" Oho chan Miki, idan Zaki Koma kije ki cire uniform d'in da zai fi Miki kizo ki d'auka Kiyi yanda Tace"
Shiru tayi na 'dan wasu lukata sanan ta hura iska Mai zafi sannan ta shige cikin gida, Safiyya kuwa tabi bayanta da kallo sannan ta kwashe da dariya, "Yarinya Baki ga komai ba, Wanda mummy take Miki nafila ne Akan Wanda Ni zan Miki, Mummy da Bata San da maganar pure wata ba"

Bata dad'e ba ta fito jikinta sanye yake da Pakistan dress green an mishi kwalliya da flowers jaa, da gyallen kayan tayi rolling sannnan ta d'auka ta fita, Mai gadi tausayin ta yaji sosai ganin yanda kamar Abubuwan da suke Mata bai dameta ba, ya Mata fatan Allah ya tsare ta amsa da ameen.

Tasha ta nufa don ta tabbata zaiyi saurin karewa hakan kuwa akayi Bata d'auki awa d'aya ba ta sayar dashi Tass, ta nufi hanyar gida sai da ta shigo estate dinsu ta nemi inuwar wata bishiya ta zauna tana huta gajiyan da tayi don ta tabbata in ta Koma ba barin ta za'a yi ta huta ba.

********
Motar Hashim na gani yana tukin Yana dube dube ko Allah zaisa ya ga wucewar ta don ya tabbata zuwa yanzu an tashi daga islamiya, parking a gefen titi kansa ya d'aura a Kan steering motan, da zaran ya rufe idon say ita ce take Masa gizo kullum cikin tunanin ta yake baida aiki sai tunaninta yayin da wutar so da kaunar ta yake Kara kururuwa a birnin zuciyar sa, hannu yasa a aljihunsa ya Ciro d'ankwalin ta da Bari ya sa a fuskan sa ya d'auki tsawon lokaci a haka, ganin basa ta Zo ba ya jaa taking ya kalli gefen motar sa, har ya tada motar sai Kuma yayi saurin kallon gidin bishiyar dake gefen motar sa, zaro idon sa yayi don ganin ita dince ko gizo ta ke masa, Murmushi yayi had'e da dariya Wanda baisan sanda yayi ba, da sauri ya bud'e kofar motar ya fito, ya dad'e a tsaye a kantaΒ  ganin kamar kuka take yasa yayi sauri ya sunkuya yace "Kuka?"
A razane ta d'ago Kai ta kalle shi, ganinsa yasa ta d'an jaa da baya,cikin tashin hankali yace "Meyasa kike kuka? Me aka Miki?"
Tashi tayi da niyar barin gun yayi saurin fad'in "Dan Allah ki saurare Ni, yau shine Karo na uku ina neman magana dake Amma kin hanani Dan Allah kinda shine zai Zama taimako na karshe da zan nema a gunki ki saurare Ni"

Shiru tayi a zuciyar ta Tace " Asiyah ki saurare Shi kiji da me yazo Miki, ko h
Ba komai ya ceci rayurwar ki a gun Yan iskan Nan, da Allah ne kad'ai yasan abinda zasu Miki"

Kai a kasa tana Wasa da hannun ta Tace "Ina sauraron ka"
Murmushin samun nasara yayi yace "Daga farko dai Ni suna na Hashim,ko zan iya sanin sunan ki?"
Chan Ciki ta amsa " Suna Na Asiyah"
Murmushi yayi yace " Nice name Asiyah, Ina so mu kulla abota da ke ,idan Kuma Zaki bani dama na zame Miki jigo a Rayuwar ki?"

'dago kanta tayi Tace " Jigo kuma? Kamarya?"
Murmushi yayi yace " kina da murya Mai Dadi,Ina nufin na zame Miki Dan Uwa Amma fa idan baza ki damu ba?"
Murmushi tayi Tace " Na amince , nagode ranar ka Shiga tsakanina da mugayen nan"

Shafe kansa yayi, sai ya juya Mata baya Yana Jin wani Dadi a ransa ko ba komai yasan baza ta manta dashi ba, sai ya juya da niyar Mata magana, ga mamakin sa bata gun, a gigice ya Fara duba ta Bai ganta ba , ya duba yaga ta manta tray d'inta , ya d'auka da sauri ya Shiga mota ya kunna Mata key, ya Fara yawon duba ta, Cikin Sa'a ya hango bayan ta tana Shiga cikin gida, Murmushi yayi yace "So Nan ne gidan su" sai ya juya ya bar gun.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
PLEASE SHARE AND COMMENTS

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
*MATAR UBA*
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.

```NOT EDITED
CHAPTER 12
PREVIOUSLY```
Shafe kansa yayi, sai ya juya Mata baya Yana Jin wani Dadi a ransa ko ba komai yasan baza ta manta dashi ba, sai ya juya da niyar Mata magana, ga mamakin sa bata gun, a gigice ya Fara duba ta Bai ganta ba , ya duba yaga ta manta tray d'inta , ya d'auka da sauri ya Shiga mota ya kunna Mata key, ya Fara yawon duba ta, Cikin Sa'a ya hango bayan ta tana Shiga cikin gida, Murmushi yayi yace "So Nan ne gidan su" sai ya juya ya bar gun.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
.......... Driving yake Yana Murmushi, shafa gashin kansa yayi sannan yace "Ya Allah ka mallakamin yarinyar Nan" sai Kuma yayi shiru na 'dan wasu lokuta Kan yace "Amma me yake damin ta kullum cikin kuka take, damn it" ya fad'a a tsawace had'i da boga Kan stirring motar sa, cikin wannan tunanin ya Koma gida.


Tana Shiga gida ta sauke ajiyar zuciya Hadi da Zama a Kan Yar karamar kujerar Mai gadi, zamanta yayi dai dai da fitowar sa daga ban d'aki hannun sa rike da buta Yana d'aure mazargin wandon sa, cikin sauri ta kau da kanta had'e da mikewa, cikin sanyin murya ya ambaci sunan ta a hankali ta Juyo ta amsa da "na'am" "lafiya kike kuwa?"

"Eh lafiya Lau baba"
"kin tabbata?"
" Eh"
" Toh Shikenan Shiga gida abinki" Kai kawai ta d'aga Masa ta shige cikin gida, Kai tsaye d'akin Safiyya ta nufa, ganin bata d'akin ta ajiye kud'in da ta sayar da pure water a Kan gado tayi ficewar ta.


Bayan ta Koma d'akinta ta tayi wanka, wata irin muguwar yunwa take ji, jiki na Karfi ta sauko ta Shiga kitchen dukkanin jikin ta ciwo yake Mata, indomie ta girka ba b'ata lokaci ya nuna da ke Alan gas cooker ne, bayan ta gama ta zauna a kitchen din ta cinye Tass ta had'a tea d'inta Mai kauri ta Sha bayan ta gama ne ta wanke kwanon da kofin da ta Sha tea din ta gyara kitchen 'din tsaf kamar ba'a yi komai a cikinta ba, d'akin ta ta Koma tayi sallar Maghriba kana ta Fara tilawar haddar ta, bata tashi a gun ba har sai da aka kira sallar Isha bayan ta idar ta jero azkar 'din da ta Saba kana ta tashi ta sawa kofar d'akin ta key ta Koma ta kwanta, bacci Tasha sosai don har sai da ta kusa makara sallar asuba,mamaki ne ya kamata ganin babu Wanda ya neme ta ba Safiyya bare Baraka.

Tashi tayi da addu'ar tashi daga bacci kana ta Shiga ban d'aki ta d'aura alwala tayi Sallah kana ta Fara gyran gidan, karfe Bakwai ta gama komai ta had'a musu breakfast ta jera akan dinning already dama taci nata sai da taji ta koshi Kan ta fita daga kitchen 'din, ta haura don Shirin makaranta.

Baraka na saukowa daga d'akin ta ta Fara dube dube da kalle kalle ko zata ga wani Abu Wanda ba dai dai ba, girgiza Kai tayi a bayyane Tace "Allah ya taimake ki."

Bayan ta gama Shirin ne ta fito har kasa ta durkusa ta gaida ta,chan Ciki ta amsa, Bata tsaya 'bata lokaci ba tayi ficewarta, bayan ta fita Bata yi nisa sosai ba ta hango motar su shamsiyya da sauri ta karasa inda suke tana waigawa a ganin ta Baraka na kallon ta, tana Shiga ya sawa motar key Bai tsaya ko Ina ba sai school.


Safiyya na gani tana saukowa tana tauna chin gam, hannun ta rike da wayar ta yayin da d'ayar Kuma na rike da jakar ta, dinning ta nufa ko kallon inda Baraka take batayi ba, a tsawace Tace "Ke don ubanki baki ganni bane?"

A 'dan tsorace Tace "Haba mummy kin tsorata Ni wallahii"
A Karo na biyu ta Kuma cewa "Baki ganni bane nace?"

"Na ganki Mana mummy"
"Okay kin ganni Amma baza ki iya ce min ina kwana ba?"
"Kar ki Zama Haka Mana please gaisuwa Kam ai ba Dole bane ba,kawai kin Zo kin tsorata mutum?"

" Lallai wuyan ki ya Kai na yanka ,iyee Ni kike fad'a wa haka?"
Tashi tayi Tace. " Ni wallahii kin isheni ke Baki da aiki sai surutu da shegen masifa Kya Kya Kya kamar agwagwa Bari na tafi na bar Miki gidan Kiyi ta surutanki ke kad'ai"

Tana Kai Nan ta fita, driver ya jaa motar suka bar gidan, Baraka Kam kasa Motsi tayi, dafe kirjin ta tayi Tace "Yau me zan gani Safiyya yace take Gaya min magana Haka? Ni Kya kya, aiko Banga ta Zama ba , alamu sun nuna maganin Nan ya daina aiki Dole na sake komawa gun Malamin Nan, cikin sauri ta haura sama, ba 'bata lokaci ta sauko hannun ta d'auke da jaka, ta saka wata shegiyar eye glass kamar na baba ari🀭 , Bata zarce ko Ina ba sai gidan kawar ta, ta kwashe Mata yanda sukayi da Safiyya, "tirkashi Aiko Baki ga tazama safiyyar ce ta ce Miki haka? Gaba gaba Kam ai dukan ki zatayi Naga alama"

" Ke dai bari kawata yanzu ai tashi zakiyi Muje gun malam gobe da nisa"
" Toh muje barina d'auko wayata ko?"
" Okay ta Shikenan zan jira ki a mota"
" Alright"


Bayan ta d'auko wayar tata ta iske Baraka na jiran ta a mota,tana Shiga ta sa wa motar key suka bar gidan sai gun malam.



Wata iriyar dariya yayi yace "Ai na fad'a Miki maganin bazai dad'e a jikinta ba sabida Soyayyar da 'yar ki take yiwa yarinyar Nan sone na Yan uwan taka, baza ki iya Shiga tsakanin suba"


Kallon juna sukayi kana maman Yesmin Tace "Amma boka ya kamata ace akwaiwata mafita ai ko?"
Ya amsa da " Eh to baza a rasa ba"

Gyara Zama Baraka tayi tana Murmushi had'e da fad'in "yauwa"
Dariya yayi kana yace "daka ta kiji Ko mene ne tukunna"
"Boka ko mene ne zanyi in dai bukata ta zata biya"

" Aljani 'dan maliki Yana bukatar jikin ki, idan kin shirya ki Shiga daga Ciki" Yana nuna Mata d'akin dake bayan sa, dafe kirji tayi ta zaro Ido had'e da girgiza Kai Tace "aljani Kuma boka? Ni duk iyayi na bana zina"
A tsawace yace " Tashi ku tafi"
Cikin sauri ta maman Yesmin Tace " Tuba muke boka, Kar ka Kore mu idan ka Kore mu wa zai biya Mana bukatun mu?"
" Naga kun Zo min da rainin hankaline"
Maman Yesmin Tace " Kinga Baraka ki tashi kiyi Abinda yace shine kad'ai zai iya Miki abinda kike so, kinyi laifin da ya fi zina tunda kika yi Shirka,kinyi kisan Kai to me ya rage kawaii ki tashi"

" Haba ya zakice min haka abin Kuma cin fuska ne?"
" A a gaskiya dai nake fad'a Miki"
Jiki a Sanyaye ta ajiye jakarta ta shige d'akin Shi Kuma ya rufa Mata baya, ganin ta tsaya kallon sa yayi Murmushin gefen baki yace "Cire kayan zakiyi" ba musu ta hau cire kayan jikinta, Yana tsaye Yana kallon ta sai lashe Baki yake kamar sabon maye,ganin hakan yayi saurin raba kansa da kayan dake jikin sa ya fad'a kanta, tun tana jure irin Dakar da yake har ta Fara ture shi, shi kuma anan ne ya sake samun Karfi kuka take tana tureshi Amma ko a jikin sa , har ya Kai ga kawarta na iya jiyo kukan ta, tsaki ta jaa a fili Tace "Ji yanda take kuka sai kace yariya, idan nice na samu kakkarfan na Miji kamar wannan ai na more" sai ta Cigaba da chta d'inta

Ya d'auki kusan awa d'aya yana abu d'aya Baraka tayi laushi don ko Motsi bata iyayi,taahi yayi yasa wandon sa kana ya fito sai washe Baki yake jikinsa duk zufa, sai da ya Sami gu ya zauna yace "Je ki fito da ita don Naga alama baza ta iya tashi ba"

'yar karmar dariya tayi kana Tace " To" ta mike ganin ta akwance duk ta ware kafafunta yasa ta kwashe da dariya " Dallah malama me haka Bai ishe ki bane na Kira wo Miki shi"

Murya chan Ciki, Tace " 'dagani please" tab'e Baki tayi kana ta Mika Mata kayanta ta saka kana suka fito, Yana ganin su ya tirmike fuska kamar ba shi ba,bayan sun zauna ya Mika Mata wasu ledodi guda biyu, yace "Na farin ledan a ruwan wanka Zaki sa Mata, na bakin ledan Kuma a abinci"
Kai kawai ta d'aga Masa, a daddafe da taimakon maman Yesmin suka bar gun, key ta Mika Mata Tace "Kiyi driving din bazan iya ba"

Dariya tayi sosai Kan ta karb'i key din, driving take da zaran sun had'a Ido sai ta kwashe da dariya, gyara Zama tayi Tace "Ke malama ya ishe ki haka kin ji ko"

"Dan Allah ki kyaleni nayi dariya, wallahi kin bada Mata, irin ihu Haka na tabbata bakiyi hakan a first night d'inki ba"
" Hmm ke dai bari wallahi mutumin Nan Bai da imani Kinga abin nashi kuwa wallahi sai da na tsorota"

Dariya ta Kuma yi tana bubbuga stairing motar, " An dai ji kunya wallahi kin bada Mata Ni wallahii banga abin tsoro anan ba"
" Baza ki gani ba ai,tunda ba ke ji yanda naji ba"
" Ni wallahii banga d'a na mijin da zai sani kuka ba, ba a haife shi ba"

" Ke kam ai dama jarrababbiyace shiysa kullum khamal yake karewa kamar kud'in guziri"
" Sai Kuma Kiyi ai, Hajiya matar Boko gidana zamu Koma ko gida Zan kai ki?"
" Kaini gidana Dole naje na gasa jikina"
" Toh ranki shi dad'e"

Tunda daga nan babu Wanda ya sake furta komai har suka Isa gidan Mai gadi ya wangale musu gate suka Shiga, Tace "Ni bazan Shiga Ciki ba, ki sauka kawai anjima ki Aiko a karb'a Miki motar"
" Okay nagode"
Ta fice daga motar ita Kuma ta tada motar ta tafi, Baraka kuwa tana Shiga ban d'aki ta fad'a ruwa Mai zafin gaske ta Hana ta sa dittol a Ciki ta Shiga da nayar Zama a Ciki wani Kara ta sake Kan ta sake Kara ruwan sanyi a Kai, ta zauna zafi take ji sosai Amma tasan in ba hakan tayi ba baza ta daina Jin rad'ad'in da take ji ba.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
Mu had'u a page na gaba

PLEASE SHARE AND COMMENT

*MILHAAT CE YAR TERAWA*

πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
*MATAR UBA*
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
_(A True Life Story_ )
*Short story*
```Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)```
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

🌎 *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* πŸ“šπŸ–ŠοΈ
_('Kungiya d'aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

NOT EDITED
CHAPTER 13
Ta fice daga motar ita Kuma ta tada motar ta tafi, Baraka kuwa tana Shiga ban d'aki ta fad'a ruwa Mai zafin gaske ta Hana ta sa dittol a Ciki ta Shiga da nayar Zama a Ciki wani Kara ta sake Kan ta sake Kara ruwan sanyi a Kai, ta zauna zafi take ji sosai Amma tasan in ba hakan tayi ba baza ta daina Jin rad'ad'in da take ji ba.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
.......... "Asiyah in tambaye ki Mana?"
"Ina sauraron ki"
" Ranar da Kika kwana a gidan mu bata tambaye ki a ina Kika Kauna ba? "
Murmushin tayi kana Tace "ke ma kin San jazaman ne wannan, har Saida ta kusa dukana ma"

"Ya salam, Dan Allah Asiyah ki dawo gidan mu, ki rabu da mutanen Nan, so suke su kashe ki misali ranar da ta Koro ki yanzu da sun cutar dake Kuma fa, daba don taimakon Allah da taimakon mutumin Nan ba da yanzu Labari ya Sha ban ban"

" Laa kin tuna min ma mun sake had'u wa dashi"
Gyara Zama shamsiyya tayi Tace " Haba Dan Allah da gaske kike?"
"Eh wallahi da gaske nake mun gaisa na mishi godiya, har ya fad'a min sunan sa"

"Mene ne sunan nashi?"

" Hashim"
" Wow hashimu"
" Shamsiyya nifa Hashim nace Miki"
" Toh Hajiya ai ainahin sunan Kenan"
" Toh iyani naji, Kinga na daukoy uniform na islamiya yau ba sai na koma gida ba"
" Yauwa yafi ai, sai biya ta gidan mu Kan Muje islmiyar ko? "
" Tih Shikenan ba matsala."

Nan suka cigaba da hirar su har Mai driver din shamsiyya yazo,Kai tsaye gidan su shamsiyya suka nufa, bayan sunci abinci sunyi sallar la'asar ya Kai su Islamiyya.

Baraka tunda ta samu tayi wanka taji saukin azabar da take ji, tana fita ta kwanta Bata d'au lokaci Mai tsawo ba baccin wahala yayi awon gaba da ita.

Yesmin tunda ta dawo daga school ta Shiga d'akin taga mummyn ta na bacci ta jaa Tsaki had'i da fad'in "Mata Bata da aikin yi sai bacci" tana Kai Nan ta Maida kofar ta rufe, kitchen ta nufa ta girki Abinda zata sa cikin ta, bayan ta gama ne ta ta Shiga ta watsa ruwa kana ta yi Sallah ta fito garden ta zauna a Kan kujera tana chat tana sipping five alive, horn da taji a gate ne yasa ta Maida kallon ta a gun, Mai gadi da sauri ya leka ta karamar gate don ganin wane ne.


A nitse yake tafiya cikin nitsuwa ya gaida shi "Ina wuni baba"
Ya amsa da "lafiya Lau 'dan Nan"
"Baba Dan Allah tambaya nake"
"Toh Allah yasa na sani"
"Asiyah nake nema"

Baba Mai gadi mamaki ne ya Kama shi, a zuciyar sa yace "Asiyah ake nema a Karo na farko ban tab'a ganin an Zo neman ta ba Allah yasa dai lafiya"
A fili Kuma yace "Lafiya kake neman ta?"
" Dama...... "
Muryar shamsiyya ne ya katse shi tana fad'in "Mai gadi Wai wane ne haka?"
Tana maganar ta karasa ta fito waje, tsuman tsaye tayi don ganin kyawun sa, Hashim ganin kallon yayi yawa ce "Sannun ki" ta amsa da "yauwa San sannu, how may I help you?"
"Dan Allah Asiyah nake nema"
Wani Abu Taji ya tokare ta a kirji da kyar ta samu ta sai saita kanta Tace "Asiyah da fatan dai Lafiya?"
"Eh lafiya Lau,jiya ne ta manta tray d'inta a bakin hanya shine na kawo Mata."


Wani irin kallo ta Masa ta ce "Dama Kuna had'uwa ne?"
"Eh to, ban San yanda zance Miki ba dai, kawatace"
" Kawa?"
" Eh please don't think otherwise, na lura Bata gida ko?"
" Eh Bata Nan"
" Islamiya taje ne?"
" Ni dai ban sani ba"
" Ba Yar uwar ki bace"
" Yar Uwa Tace"
" Kuma kice Baki San inda taje ba" tab'e baki yayi had'e a d'aga kafad'a Wanda hakan ya zame Masa jiki, sai ya d'aura da fad'in "Any ways ganan tray d'in da ta manta" Yana Mika Mata ya juya da niyar tafiya, da sauri Tace "To in ta dawo wa za'a ce Mata?"
Murmushi yayi Wanda ya nuna kyawun fuskar sa ya nuna dimple d'insa, d'an juyawa yayi yace "kice Mata Hashim Ahmad Shettima."

Zaro Ido tayi tace "Hashim Ahmad Shettima?"
Bai tanka manta ba ya shige motar sa ya bar gun, ganin tsayuwar da take bazai amfane ta da komai ba, ta shige Ciki, Zama tayi a garden d'in Taji zaman ba dad'i ta jaa tsaki ta shige d'akin ta.

Kwanciya tayi akan gado tayi ruff da Ciki, a bayyane Tace "Hashim

Please Login or Register in order to submit comment