Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mika nata yace " Uhmn Ina sauraron ki Ina take?"

Tsotsa keya tayi irin na Mara gaskiya tace " Tana asibiti" a takaicw, Hashim Jin ta ambaci asibiti hakan ya tada Masa hankali,Β  yayi kokarin b'oye tashin hankali da ya Shiga Amma ya kasa, kad'a Kai kawaii Safiya tayi Tace "Sai anjima" ta shige makaranta, Hashim ya d'auki kusan mintuna biyu a tsaye jiki ba Karfi ya shige motar sa, ya kunna key ya bar gun sai da yayi nisa ya taka birki wani Kara naji kiiiikkii, ya daki stairing motar da karhi yace "God damn it, ban tambayeta a wani asibiti take ba, Taya za'ayi na nema ta? Kuma me ya same ta? Hashim me Yake damin ka ne?" Magana yake shi kad'ai Kuma da mugun Karfi da ba don glass din motar a d'age ba na tabbata da mutannen dake wucewa zasu ji abinda yake cewa.

"Dole na koma makarantar, ko da take nasan Safiya zata kirani daga Nan sai na ji a wani asibiti take" Ya tada motarsa Rai a b'ace yana mugun Jin haushin kansa.

*ASIBITI*
"Aunty Badiyya, Baba bai dawo haryanzu ba, na tsorata kamo dai Bai same ta bane yake Jin bazai iya Gaya min ba? Ko Kuma wani mumunan Abu ya same shi?" ta na maganar cikin muryar kuka.

Badiyya 'dan dafe kafad'ar Asiyah tayi Tace "Always think positive Asiyah, zai dawo karki damu insha Allah Yana cikin koshin lafiya."

"Ina fatan Haka aunty"
Murmushi tayi Tace "Kar ki damu" a zuciyar ta Tace "Ya salam, Asiyah kina cikin jarabawar rayuwa, gashi Ni wata na shida Kenan da Fara aiki Dana biya Mata kud'in aikin,and now Dole sai an fita da ita kasar waje, Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Asiyah Allah ya saka Miki" muryar Asiyah ne ya dawo da it's taga zurfin tunanin da ta Shiga Tace "Aunty ta na ji Kinyi shiru?"

Cikin Rawar murya da son 'boye kukan da take Tace "Akwai abinda nake dubawa a waya na ne."

Asiyah tashi tayi ta zauna tace "Aunty kamar kuka naji kike yi"
Kirkirarren dariya tayi Tace " Kuka Kuma me Kika gani?"
"Ji nayi muryar ki ta canza"
"Murace,murace take so ta kamani"
" Allah sarki sannu Allah ya sauwaka ya Baki lafiya" ta amsa da "ameen."

"Asiyah zan koma gida naje nayi wanka, zsn dawo anjima,zan Aiko Nurse ta kawo Miki abinci sai kici kinji?" Ta amsa da "Toh Aunty nagode" Badiyya shafa kanta tayi ta fice.

Bayan ta fita ta bawa Nurse kud'i a sayo Mata breakfast, sannan Tace idan ta kawo ta tabbatar tayi feeding d'in ta sabida Bata gani,sannan ta tabbatar taci ta koshi,zBredi da kwai sannan da thick tea aka kawo mata, Asiya taci bredin Nan Sosai dake dama tana son bredin,sai da ta koshi nurse d'in ta fita.

'bangaren baba Mai gadi Kuma haryanzu bai tashi ba, likita mamaki abin yake bashi bai tab'a ganin hakan ba,gashi dai Yana numfashi Kuma Yana Motsi Amma Bai farka ba, Kiran Nurse d'in da tayi Night duty ya Kira yace ta nuna Masa alluran da ta Masa Yana gani ya hauta da fad'a "Baki da hankali ne? Alluran bacci ne fa kika Masa har sau uku, wane ne ma ya d'auke ki aiki anan San Baki San aikin ki ba,yanzu bawan Allan Nan sai ya Kai 3 days Yana bacci Kan ya farka"Β  sallamar da yaji ne yasa ya waiga don ganin wane ne, Abban Yesmin yayi musabahaΒ  sukayi sannan ya tambaye shi ya Mai jiki, a Nan ne ya Masa bayanin abinda ya ke faruwa ransa yayi mugun 'baci shi da yake so ta koma Kaduna yau ko gobe Amma yanzu yarinyar Nan ta lalata Masa komai,kallon hanne yayi yace "Zo Muje gida anjima ki dawo." Yana Kai Nan ya fita.

Da sauri tabi bayan sa,Dr ya d'aura masifar daga inda ya tsaya.

*Hashim* tunda ya koma yake zaman jiran ganinΒ  Kiran ta Amma shiru kake ji,Yana kwance kwasam wurin karfe Tara na dare yaji Karan wayarsa take jikin chaji da saurin gaske ya tashi ganin *Badiyya* ya bayyana a screen d'in wayar sa yayi tsaki ya koma ya kwanta a haka bacci yayi awon gaba dashi.

Wayar hannun ta take kallo Tace "Dan Allah Hashim ka d'aga Kiran Nan I need you" Maida kallonta tayi ga Asiyah dake sharar baccin ta.

Safiya na kwance chat d'in ta take babu abinda ya Sha kanta a fili Tace "Ni zaka rainawa wayo nasan kana Nan kana jiran kirana Ni Kuma ba Kiran ka zanyi ba sai Nan da kwana biyu" da wannan tunanin tayi bacci.

*WASHE GARI*

Da sassafe ta shirya driver ya kaita makaranta don gudun Kar Hashim ya biyo ta, hakan kuwa akayi,tana barin gidan Hashim yazo yayi parking har karfe takwas tayi bai ganta ba hakan yasa ya koma gida.

*ASIBITI*

Dr Badiyya duk kwanan duniya sai to duba Baba Mai gadi don ganin ko ya tashi Jin irin alluran da akayi Masa Tace sai ta sa an kori nurse d'in da tayi hakan.

Badiyya Tace "Asiyah Zaki iya wanka da Kanki? Ko na Miki?"
Kunyar maganar taji Kai kawaii ta d'aga, Badiyya Tace "Zaki iya?"
Ta amsa da "Eh" Murmushi tayi tace baza ki iya ba,Sabi da Baki Saba ba,San Miki Ina so ki saki jikin ki Nima mace ce kamar ki,tunda lalura ce ba matsala Ni zan Rika Miki kinji?"
" Toh Aunty Amma aikin ki fa?"

Murmushi tayi Tace " Yau Ina break sai gobe" da taimakon Dr Badiyya Asiyah tayi wanka sannan ta d'auko Kaya daka cikin kayan da ta kawo Mata.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
PLEASE VOTE AND COMMENT


Murmushi tayi Tace " Yau Ina break sai gobe" da taimakon Dr Badiyya Asiyah tayi wanka sannan ta d'auko Kaya daka cikin kayan da ta kawo Mata.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
..............Yau kwanaki uku Kenan Hashim kullum yana zaryan zuwa gidan su Asiya,Amma baya samun ganin safiya,hankalin sa kullum a tashe take,har Saida mahaifiyar sa ta kasa gane kansa sashi tayi a gaba akan ya fad'a Mata abinda yake damin sa,ansa d'aya ya ke Bata "Ba komai" Dole ta hakura ba don taso ba.

Nana kullum cikin istigfari da nafilfili take, tana da na sanin abinda da aikata,sannan tayi Allah wadai da qawa irin Baraka sabida itace ummul aba'isin abubuwan da takeyi, sosai Abban Yesmin yaji dad'in ganin yanda ta canza a cikin kwana biyu.

ASIBITI

Dr Badiyya na gani tana tsaye ta hard'e hannun ta tana kallon Asiyah dake bacci tun d'azu,iska ta hura Mai zafi kana tace "Allah ka kawo Mana mafita."

Hannu tasa a aljihun lab coat dake jikinta ta zaro wayarta wayar Hashim ta Shiga kira, wayan na hannun sa yana ganin kiranta yayi taking ta kashe wayar a fili yace "idan always Kiran da nake jira to na Safiya ne,ban San dalilin da yasa ta ki kirana ba, yau kwanaki uku Kenan Amma shiru."

Tsaki ya jaa Mai tsawo ya shafo kansa Rai a d'an b'ace yace "Dole naje gidan su,Sam ban yarda da Safiya ba maybe ma sun cutar da ita ne."

Dr Badiyya Murmushin takaici tayi Tace "Allah sarki Hashim,wannan karon ba abunda kake tunani bane ba,idan bai d'aga call dina ba har gidan su zanje" tana kaina ta fice daga d'akin tana goge hawayen da suka zubo Mata.

Safiya ita kanta tana son Kiran Hashim,Amma taki kiran sane sabida ta jaa Masa Rai Had'i da son cika wata mummunar munufar ta Akan sa.
Hashim tunda ya kashe wayar sa sai da yayi sallar Isha ya kunna wayar,kunna wayar da yayi ke da wuya yaga Kira da private number, hannu na rawa yayi picking, ya Kara a kunnen da ba tare da yace komai ba, Murmushi tayi Mai d'an sauti hadey da fad'in "Malam Hashim ka wuni lafiya?"

Ya amsa da "Lafiya lau" Yana kokarin gano muryar Amma ya kasa ganewa Tace "Baka gane Ni bako?"
"Eh please Wace ce?"

Yar karamar dariya tayi Tace " Sunana Safiya" tashi yayi ya zauna a d'an razane yace "Safiya kece? Safiya meyasa Zaki min haka? Haka mukayi dake?"

Dariya tayi sosai kana Tace "Duk wa'an Nan tambayar Ni kad'ai ce zan amsa su? To eh nice,nayi hakan be sabida wayata ta samu matsala,sannan ba haka mukayi da Kai ba." Murmushi yayi yace " Okay Ina sauraron ki a wane asibiti take?"

" Haba Kai kuwa Babu gaisuwa babu komai sai maganar ta?"

" Am sorry,am sorry ya kike, ya gida?"

" Lafiya Lau ya Jin d'adin ka?" Tana maganar tana karya murya hatda wani fari da Ido yake kamar a gabansa take,ya amsa da "Alhamdulillah"

"Zan fad'a maka inda take Amma da sharad'i"
" Sharad'i Kuma Safiya? Wane irin sharad'i ne haka a wannan lokacin?"
" Sharad'i ne Mai sauki idan ka d'auke shi da zafi Kuma yana da wahala"

" Ina sauraron ki"
" So nake ka turo gidan mu ayi maganar aure"
Murmushi yayi yace " Safiya Kenan wa yake ta maganar aure bayan Amaryar bata da Lafiya, please be serious Mana"

Rai a b'ace Tace "Ni nace maka amarya bata Nan?"
"Eh man da bakin ki kikace min tana asibiti"
"eh munyi haka" Amma a zuciyar ta Kuma Tace "Aikin banza Ni ban ma San a wane asibiti take ba, ko tana da Rai ko ta mutu oho."

Maganar da yayi ne ya katse Mata tunanin da takeyi murya na rawa Tace "Me kace?"

"Cewa nayi a wane asibiti take?"
"Hashim Ina so ka saurare Ni da kyau kaji abinda zan fad'a maka,idan kana so kasan inda Asiyah take to ka tabbatar ka turo iyayen ka gidan mu ayi maganar aure na da kai,idan kayi haka zan fad'a maka inda take,idan ka amince ka Zo gidan mu gobe bayan sallar Isha" tana Kai nan ta katse wayar ba tare da ta ji abinda zai ce ba,Jin ta kashe ya bi wayar da ido yana jinjina hali irin na Safiya.

Shiru yayi har motsi ya kasa yi, chan sai yayi saurin dialing number Faisal, Faisal na picking yace "Toh manyan gari Hala mantuwa kayi ko Kuma kuskure kayi ka kirani?"
"Ba kuskure nayi ba sannan Kuma ba mantuwa bane ba?"

" Tooooh ya akayi lafiya ka kirani?"
" Ji yanda kake magana kamar da bana Kiran ka"
"Kana kirana Mana Amma idan Naga Kiran ka a wannan lokacin bazai wuce maganar yarinyar Nan bane Asiyah,when last ka Kiran?"

" Look Mr man, kana ina ne? Ina so muyi magana"
" Nasan za'a Zo Nan ai,kayi sa'a Ina gida babyna tayi tafiya da wallahi Ni da Kai sai dai gobe"
Bai bashi amsa ba ya katse wayar.

Yana Isa gidan su Faisal Kai tsaye side din sa ya nufa Bai tsaya b'ata lokaci ba ya kwashe komai ya Sanar dashi, "tirkashi,lallai Abokina kana ganin jarrabawa,to Amma Kai me ka yanke?" Faisal ke magana Yana kallon abokin nasa cike da tausaya.

Cikin murya Mai sanyi yace "I don't know Faisal,I don't know gani nake kamar sun cutar min da ita, wallahii wallahi idan suka Mata wani abu sai Naga Wanda ya tsaya musu a garin Nan" ya karasa maganar Rai a 'bace.

Faisal dafe kafad'ar Hashim yayi yace "calm down ina da shawara,me xai Hana ka amince da bukatan ta kaje gidan nasu gobe sannan muyi was hajiya magana kawaii aje gidan nasu,in yaso ko da anyi aure sai ka sake ta"

" Haba Faisal Kai da nazo neman mafita a gun ka Kuma kace na aure ta, gaskiya shawarar Nan ba tayi ba,ka canza wata"
" To Ni gaskiya shine kad'ai shawarab da zan iya baka ka je ka sake tunani a Kai"
Iska ya hura Mai zafi kana yace " Na amince zanje gidan nasu Duk yanda ake ciki San Sanar da Kai."

Sallama sukayi ya fice ya shige motar sa ya nufi gida.

ASIBITI
" Dr mutumin Nan yau kwanaki kisan hud'u Kenan Bai tashi ba,ko dai ya mutu ne kake b'oye min"

Yar karamar Murmushi yayi yace " Yana Raye kawaii dai ya Shiga comma ne."

Abban Yesmin dafe kansa yayi Yana ambatan sunan Allah "Comma Kuma Dr? Yanzu yaushe zai tashi?"
"Gaskiya I can't tell Amma zai iya tashi at anytime Haka Kuma akwai wa'anda suke Kai shekara Basu tashi ba"

Abban Yesmin Maida kallon sa yayi ga Nana yace " kinji Ina ga Dole na tafi na barku anan zan koma Zaria,sai ki rika kula dashi please"

Bata so hakan ba Amma babu yanda ta iya da to kawaii ta amsa.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
RASHIN VOTE DA BANA SAMU SHIYASA BANA TYPING DAN ALLAH KU RIKA MIN VOTE
VOTE AND COMMENTS

Abban Yesmin Maida kallon sa yayi ga Nana yace " kinji Ina ga Dole na tafi na barku anan zan koma Zaria,sai ki rika kula dashi please"
Bata so hakan ba Amma babu yanda ta iya da to kawaii ta amsa.
πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦πŸ’¦
............. Hashim kasa bacci yayi sai zancen zuciya yake "shin shawarar da Faisal ya bashi zaiyu kuwa, shi baya son Safiyya, asalima ya tsane ta" tashi yayo ya fad'a ban d'aki yayi alwala ya Fara jero nafilfili sai da aka Kira sallab asuba ya fice ya Shiga masallaci, bayan ya dawo daga massallaci bacci barawo ya sace shi.

Da sallam ta Shiga gidan, d'ago kanta tayi don ganin wace ce take sallam, ji tayi gaban ta ya fad'i dafe kirji tayi tana ambatan sunan Allah a zuciyar ta, mamakine ya kama Baraka karasawa tayi ta zauna Tace "Qawata ya dai lafiya kuwa Naga kina min irij wannan kallon?"

Cikin Rawar murya Tace "Lafiya Lau sannu da zuwa, ya gida?"

"Lafiya Lau"
"Daga ina kike da yamman Nan?"
" Bangane daga Ina nake ba? Yau na Fara zuwa gidan ki war Haka?"

Kirkirarren Murmushi tayi tace " no ba Haka bane Naga kamar you're all dressed up ne, shiyasa nayi tunanin unguwa Kika je"

Itama Baraka murmushin tayi Tace " A'a daga gida nake naji ki shiru kwana biyu bakya nema shine nazo na duba ko lafiya?"
Tsosa keya Nana ta Shiga yi cikin inda inda Tace "Laa... La. Lafiya lafiya Lau"
"To ya kin sake komawa gun bokan Nan kuwa, Naga alama tunda Kika ji dad'in sa Kika kasa hakuri?" Magana take kasa kasa had'e da kashe Mata Ido.

Tab'e Baki Nana tayi Tace "Banje ba"
"Meya Faru? Nana ya na ga Duk kin canza ne Kuma sai na ga kamar counter ne a hanun ki?"
" Eh hakane"
" Ke kuma me had'in ki da counter?"
" Ban fahimce ki ba Baraka, me had'i na da counter ina musulma kice min me had'i na da counter, to istigfari nake yi"
Baraka dariya ta Shiga yi irin na kin Raina min hankalin nan tana yi tana yarfa hannu "ke d'ince kike istigfari?"
"Eh kina mamaki ne?"
"Ahhh, kema kin sani mamaki Dole ne abinda ban tab'a gani kina yi ba"

Murmushin gefen baki tayi Tace "To ki daina mamaki"
Dariya Baraka ta Shiga yi sosai Saida tayi Mai isarta cikin dariya Tace "Ki tashi ki shirya please Zaki rakani wani wurine"

"Ni?" Tana nuna kanta ta d'aura da fad'in " Na raka ki Ina?"
" Unguwa"
" A'a ba inda zanje a dawo lafiya"
" Ai wallahi Baki Isa ba, kin san tun yaushe nake tsara fitan Nan, wani Alhaji ne fa yazo daga paris, Yana son anal sex Kuma da Mata biyu kema kinsan harkar babbace"

A d'an tsawace Tace " Am not interested"
Murmushin gefen baki Baraka tayi ta d'an dafe kafad'ar ta Tace "Qawata wallahi idan mukaye mutumin Nan Don ne aikin million 5 ne fa Kar ki b'ata min tsari"

Ture hannun Baraka tayi daga jikinta tana nuna ta da d'an yatsa Tace Kar ki kuskura ki sake tab'a jiki na kin gane ko? Sannan Kar ki kuskure ki sake tako min gida da irin wannan maganar in ba Haka ba wallahi zan had'a Miki jini da majina."

Mamakine ya kama Baraka murya jabrawa Tace " Amma Nana kin gane da wa kike magana kuwa? Baraka ce fa aminiyar ki Ni kike fad'awa irin wannan maganar"
A tsawace Tace "To hell with you Baraka ke d'in banza ke d'in wofi ke kanwar uwata ce da bazan fad'a Miki Haka ba? Na Gaya Miki Kar ki sake Tako min gida munafuka anna mimiyi"

Rai a b'ace Baraka Tace " Dani kike zancen Nana wallahi sai na tuna Miki a Siri zan Kira Abban Yesmin na fad'a mishi Duk abubuwan da kika Shukka hatta bin mazan da kikeyi"
Nana dariya ta Shiga yi kana Tace " idan kin fasa fad'a mishi kinji tsoro"

Baraka Dariya ta Shiga tayi Tace " Allah sarki har na hango ki akan titi kina bara don na tabbata idan iyayen ki sukaji abinda kikayi sai sun tsine Miki sunyi Allah wadai da halin ki"

"ko kad'an hankali bazai tashi ba in hakan ta Faru Dani idan na gyara tsakanina da ubangiji na ya wadatar dani"
" Wani ubangijin Kenan? Ubangijin da kike had'a sa da wani? Kar ki manta Allah baya yafe Wanda ya had'a shi da wanin sa"

" Ummmn, Allahu gafururahim, na tabbata zai yafe min in dai nayi tuban gaskiya, Kuma laifin da nayi Masa tsakanina dashine kawaii,ki sani idan na koma Kan titi ke Kuma Zaki koma gidan yari Ina da video da recording na kisan Kan da kikayiwa Mahaifiyar Asiyah,Anisah Kai harda Sadiq Ina da komai da komai,Kinga nice da riba sabida Allah baya yafe laifin wani was wani"

" Ina da kud'in da zan wanke kaina Kuma wallahi sai na Kira shi na fada masa,tun wuri Ina Baki shawara kizo mu had'a Kai mu d'aura daga inda muka tsaya" tana maganar tana kokarin rike hannun ta.

Wata gigitacciyar mari Nana tayiwa Baraka har Saida ta fad'i akan sofa dake gefen ta.

Baraka rike kuncin ta tayi da hannu biyu Tace "Kai kai kaaii Kika an mare Ni?"
"An mare ki"
'dago was tayi da sauri ta nufe ta da niyar Rama Marin da ta Mata,Abban Yasmin dake tsaye tun shigowar Baraka ya nufu inda suke da sauri, hankad'e Baraka yayi ya shafa Mata maruka guda biyu masu kyau sannan yace "This should be the last time da Zaki sake shigan min gida kina jina ko?"

Ba Baraka kadai ba hatta Nana ta tsorata don Bata San sanda ya shigo gidan ba, Murmushi baraka tayi ta mike Tace "Baka San me ya Faru bane Amma bara na baka Labari kad'an daga cikin abubuwan da wannan munafukar matar ka take yi ta kasance tana cin amanar ka da maza,itane gidan boka,itane lesbian"

" Uhmn sai Kuma me Ina sauraron ki" hard'e yayi Yana kallon ta,jikin ta jikin tane yayi sanyi har ta kasa magana a Karo na biyu Tace "Kinyi shiru Shikenan ko Akwai wani Abu?"

Murya chan ciki Tace "Shikenan."

Had'a hannun sa yayi guri guda yace "to nagode sosai thank you for informing me, yanzu ki fice min daga gida ko in kashe ki yanzun Nan,Kuma kin sani Sarai idan na kashe ki na kashe banza"

Jiki na rawa ta fice daga gida tana mamakin yanda bai d'auki maganar ba "ko dai asiri ta Masane?" Shafa kumatunta tayi Tace "To wallahi sai Kun San Kun mare Ni" ta jaa motar ta ta wuce hotel d'in da sukayi zasu had'u,Yana ganin ta ita kad'ai ya tambaya ina kawartata take ta Fara Masa kame kame ba 'bata lokaci ya Koreta daga d'akin, Hakan ya sake hassala ta tana driving sai huci take ta ce "Wallahi wallahi sai nayi ajalinki" cikin wannan tunanin ta koma gida.

Safiyya tunda tayi sallar Maghriba ta yi wanka ta ci kwalliya,abaya tasa pink an Masa kwalliya da stones ruwan Bula (Royal blue) tayi Rolling da d'an kwalin rigan ta sanya takalmi irin Mai igiyi Shima kalan ruwan Bula,tayi kyau matuka dama Safiyya Kyakkyawa ce kawaii dai halin uwa ta biyo,Duk da dama Safiyya, Anisah da Asiyah kamanin su d'ayane kamannin Mahaifin su Sadeeq, tana ji a jikin ta Dole Hashim zai Zo tunda dai Yana son Asiyah.

Baraka na zaune a parlor ga dai TV a kunne Amma hankalin ta ba a Kai take ba sai kunce wa take ta warwareww, Sallama Safiyya tayi ta zauna ganin hankalin mummyn nata baya gunta tab'e Baki ta Shiga boga game a wayan ta.

"Hashim kasan Allah da Kai na kwana a Rai na, Yarinyar Nan shaid'aniya ce gata karama yarinya Yar ss2 kam me ta sani a zamanin mu Amma ka duba kaga makircinta ko mace Yar shekara arba'in baza tayi ba"

Murmushin takaici yayi yace "Ni kaina abun na bani mamaki Faisal,Amma ya zanyi Ina son Asiyah Ina so na San a wani hali take ciki Dole nayi yadda take so"

" Kasan mene ne, hashim? Duk yanda za'a yi ka nuna Mata ita d'in kake so kayi ka nuna Mata baka son Asiyah,Dole game zamu buga kamar yadda take so"
" Kamar ya Kenan fa ban fahimce ba"
" Abin nufi zaka tura gidan su,ayi komai da komai, Kan ranar auren Kai ma ka nuna Mata in dai Bata fad'a maka inda Asiya take ba zaka fasa by then Bata da option Dole ta fad'a maka sabida kaga a wannan lokacin lokaci ya kure Mata sun gayyaci Yan uwa da abokanan arziqi babu yadda zatayi Dole ta fad'a maka idan ka tabbatar da hakan ka ganta sai ka fasa"

Murmushi Hashim yayi Wanda shi kansa ya manta ranar da yayi yace " hakan za'a yi Abokina nagode sosai"
" Kar ka damu yanzu ka tashi Muje masallaci Naga Ana Kiran sallah daga Nan sai mu wuce gidan nasu."

Hakan kuwa akayi suna idar da sallan Kai tsaye suka wuce gidan su Safiyya horn sukayi aka bud'e musu gate dake ta sanar da sabon Mai gadin da zuwan su, tana Jin horn ta tashi jiki na rawa da niyar zata fita.

A tsawace Baraka Tace "And where are you going to?"
Murmushi tayi Tace "Mummy bako nayi"
Cikin rashin fahimta Tace "bako? Daga Ina?"
Murmushi tayi Tace "Mummy kiyi hakuri idan na dawo zan fad'a Miki komai." Tana Kai Nan ta fita da sauri.

Baraka na kiranta Amma Bata juya ba bare ta ji me zata ce, kad'a Kai kawaii tayi ta cigaba da mugun Shirin ta.

Faisal yace "Kirata Mana"
"To ai bani da number ta"
"Kamarya baka da number ta dame kukayi waya?"
" Uhmn hiding number tayi"
Kama Baki Faisal yayi yace " Lallai yarinyar Nan ta wuce tunani na,Allah ya kyauta."
Ya amsa da "ameen, Bari na aiki Mai gadin ya Mata magana kawai" har ya sauke kafa d'aya sai ya hango ta ya waiga ya kalli Faisal yace "gata chan ma tana zuwa"

Da sallama ta Kara so inda suke, da Murmushi d'auke a fuskarta ganin su biyu ne sai taji wani iri,Tace " Sannun ku da zuwa"
A tare suka amsa da "yauwa sannu"
"bismillah ku Zo mu Shiga ciki"
Babu wanda yace Mata komai,kawaii fita sukayi suka bi bayanta, Faisal murya kasa kasa yace "Mutumina yarinyar Nan fa karshe ne gun kyau wallahi ta had'u"
Hararar da Hashim ya Masa ne yasa yayi saurin Kay da kansa.

Maganar da yayi ya sauka Akan kunnen Safiyya Aiko tana jin hakan ta canza tafiya sai yauki take,a parlor da ake saukan bakin ta ajiye su, Yar aikin gida tasa ta kawo musu drinks, Faisal ya sa hannu ya d'auki exotic ya Fara Sha,gyaran murya hashim yayi yace "Abokina kaga gimbiyar tawa ko?"
Murmushi Faisal yayi Yana kokarin had'iye exotic da ya cika bakinsa da shi don dama shi masoyin exotic ne, sai da ya had'iye yace "Na ganta Abokina tabarakallah Masha Allah,sannu Amaryar mu."

Safiyya wani irin dadi taji rufw fuska tayi da hannu biyu Tace "yauwa sannu abokin mu,da fatan kana lafiya?"
"Lafiya lau,ya gida yasu hajiya?"
" Suna lafiya Lau"
" Masha Allahu."

Hashim gyara zaman sa yayi yace " My princess gani nazo,ya ake ciki?"
Cikin muryar shagwab'a Tace " So nake cikin satin Nan kazo neman aure na"
Murmushi yayi yace "shine kawaii?"
Ta d'aga Kai alamun "eh"
Murmushi irin na Zaki Raina Kanki yayi yace "Consider ita My Sofiyat"
"Wow Amma naji dad'in sunan Nan"
" Dan Allah dagaske kike?"
" Eh dagaske nake har cikin Raina naji shi"
" To in ko Haka ne yanzu Kika Fara Jin dad'i don yanzu na Fara kirin ki da sunaye masu dad'i"
Murmushi tayi tace "Nagode sosai,Allah ya bar mu tare"
Ya amsa da Amin Amma a iya baki ya tsaya.

ASIBITI
"Asiyah inaso ki kwantar da hankalin ki ki saurare ni,Kuma ki fahimce Ni kinji?" Dr Badiyya ke maganar Nan cike da tausayin Asiya, Asiyah ta amsa da "Toh Aunty Ina sauraron ki"
"Baba Mai gadi Yana Asibitin Nan"
Tashi tayi ta zauna tana Murmushi Tace " Baba ya dawo Alhamdulillah, ina yake?"
Nan ta fad'a Mata tun ranar da aka kwantar dashi Bai tashi ba,bare ma aji ya samu aunty Rukayya ko Bai same ta ba.

Kuka ta Shiga tana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ya Allah me nayi me nayi da chanchanci irin wannan laifin, Allah na tuba ka yafe min"
Dr Badiyya rungumarta tayi Tace " Ki daina fad'in haka Zaki yi sabo Allah ya na gwada bayin sa ne Wanda take so,ki d'auki wannan a matsayin kaddarar rayuwar ki,insha Allah komai zai wuce Allah ya Baki ikon cin

Please Login or Register in order to submit comment