Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya rungume Diyya da hannu d'aya kana ya kwantar da Asiyah a cinyar sa, daga bisani Shima baccin ya d'auke sa.

Diyya ce ta Fara farkawa, Murmushi kawaii tayi ta sake komawa baccin ta, basu farka ba har sai da jirgin su ya sauka Nija, a hankali Suma fara Bud'e idanun su. Idanun shi ya sauke Akan Diyya dake ta kallon sa gira ya d'aga mata Yana Mata kallon lafiya, Murmushi tayi Masa ya sa hannu ya shafa fuskar ta, Asiyah kuwa Mika ta shiga yi "Wayyo bayana"
Dariya sukayi yace "Allah ya bani hakuri Ni da kuka danne Ni"
Asiya Tace "hakkin Kane kula da mu,ko ba haka bane aunty?"
" Hakane Kanwata"
"Au had'e min Kai zakuyi lallai sai nayi da gaske"
Dariya kawaii sukayi,suna fita suka Tarar da Faysal na jiran su,Gidan su Diyya suka wuce yace "Zan zo Hira anjima" sukayi wucewar su.

Umma tayi matukar farin cikin ganin su musamman da yanzu Asiyah tana gani "Haba Badiyya tunda Kuka tafi ba Kira shiru haka gashi Ni ko na kira ba samun ki nake ba"
"Yi hakuri Ummu wallahi tunda mukaje muke ta fama da zuwa asibiti ban zauna ba shiyasa"
"Tunda an Samu abunda aka je nema ai Shikenan"
"Yanzu Asiyah ya ake ciki da maganar Baraka take da suna ko?"
"Eh umma Baraka,ban San yanda ake ciki ba,Amma insha Allah gobe zanje Ni gidan maman Yesmin naji yanda ake ciki"

"Har sai mun jira gobe? Ai ki tashi mu tafi kawaii yanzu,baza ki gane yanda na damu da aka Mata ba"
"Aunty daga dawowar mu sai mu fita ga gajiya ko hutawa ba muyi ba,ki Bari sai gobe kawai"
"Gaskiya Asiyah take fad'a ku bari sai gobe kuje d'in" umma ke wannan maganar.

"To" kawai Diyya tace don taso su je a yau d'in nan.

Mummy tayi mutukar farin ciki duk da Bata San dalilin sa na tafiyar ba, kwata kwata kwanaki biyar yayi baya gidan Amma ji take kamar ya fi wata,bayan ya huta ne ta zaunar da ita duk abubuwan dake tafiya, Kama daga kan Maganar Shirin auren da yayi na karya da Safiyya, har izuwa 'batan da Asiyah tayi da samun lafiyarta da Kuma Shirin da suke na kama Baraka, har izuwa alkawarin auren da yayi wa Asiyah da Diyya

"Oh Hashim duk wannan abubuwan dake faruwa Amma baka sanar Dani ba sai yanzu? Dama da Badiyya kuka yi tafiyar?"
"Eh da ita mukayi,sabida itace take kula da ita, Am sorry Mom naga Sam Baki kaunar yarinyar ne shiysa"

"A'a Hashim ba Haka bane kawaii dai naga yanda duk baka damu da kanka bane sai ita shiysa Kuma kasan bani da wani buri da ya wuce ka koma Kan aikin Mahaifin ka"

" Insha Allah Mom satin Nan zan Fara zuwa aiki"
" Aiko da na ji dad'i, yarinyar Nan Badiyya Yar Albarka ce duk irin Soyayyar da take maka kishi bai hanata kula da Asiyah ba"
"Hmmm mom Diyyata Kenan"

" Dan Allah rufe min baki wai Diyyata kamanta irin rashin mutuncin da kq shuka Mata ne, yarinyar Nan taxo gidan Nan don Kai yafi a irga"
"To Mom ai komai ya wuce yanzu ko,mun dai daita"
"Masha Allah,nafi kowa farin ciki,na tabbata da Mahaifin ka na raye ba karamin dad'in had'in Nan zaiyi ba,duk da ka bajire Masa a baya"
"Oh nikam na shiga uku"
"Tara ka shiga ba uku" dariya kawaii yake mikewa yayi yace "Ni zan fita"
"Ina Kuma zaka je,da Daren nan?"

"Hira zanje"
"Lallai Son Amma baka duba time ba ko?"
Agogon hannun sa ya duba "Inna lillahi wa Inna ilaihirraji'un"
"ya da salati Haka?"
"Mom karfe Sha biyu saura fa, gaskiya banji dad'i ba"
"Oh da Kai tunda ka cika Mara kunya gidan su Diyya zaka je da way zakayi Hira a cikin su?"
"Duk su biyun"

Mom yarfa hannu ta shigayi tana salati "A ina aka tab'a yin Haka Hira da Yan Mata biyu?"
"Ni Zan Fara mom"
Hab'ar ta ta rike Baki a Bud'e take kallon sa, dariya kawaii yayi yace "Ni zan kwanta sai da safe" ya haura d'akin sa Yana dariya.

"Oh Ni yasu,wani abu sai wannan zamani ko a littafin ban tab'a ji anyi haka ba,Amma da sauki tunda da amincewar su" tana Kai Nan itama ta haura d'akin ta.

Asiyah da Diyya sunyi ta zuba Ido don ganin Hashim Amma Shiru kaje ji, Diyya ta Kira layin sa yafi sau biyar bai d'aga ba, a Lokacin Yana parlor da mummy ya bar wayar a d'akin sa.

Yana ganin missed call d'in yabi baya ya Kira har sau uku ba a d'aga ba sai ya Kuma Kira har ya kusa yankewa a ka 'daga cikin muryar bacci Tace "Hello!!!"
Ajiyar zuciya yayi yace "You can't imagine how much I missed this voice"
Murmushi kawai tayi ya d'aura da fad'in "Am so sorry Diyya for not giving you the chance to explain yourself to me"

"Is okay kasan komai mukaddarine daga Allah, idan da a Lokacin Nan mukayi aure na tabbata baza ka had'u da Asiyah ba, Asiyah kaddarar kace ko ince kaddarar muce,gaba ki d'aya"
"Hakane, ke d'in ta dabance Queen, Nagode sosai da kike kula da kanwarki"

"Ban bukatar godiyar ka nayi ne don Allah sannan Asiyah yarinya ce Mai hankali manya,tun farkon Haduwar mu da ita naji ta shiga Raina,da Kuma nasan itace farin cikin ka sai na kud'iri a niyar kyautata Mata Sabida Ina son abunda kake so King"
"Kin San yanda nayi missing sunar Nan da ga bakin ki kuwa?"
"hmm a a sai ka fad'a"
" Ke dai Bari don bazai kwatantu ba"
" To Shikenan rankashidad'e na bari"
" kanwar taki tayi bacci ne?"

"Eh tayi bacci"
" Okay kema ya kamata ki Samu ki kwanta ko?"
"Har ka gaji da Jin murya ta?" Cikin muryar Shagwab'a take maganar, wani yaaarrr yaji a jikin sa Nan da Nan yaji wani irin shauqi ya kamashi.

"am sorry queen, nasan kin gaji sosai Kuma gobe nake so mu Fara processing yanda za a kama Baraka"
" Kamar kasan abinda ke cikin zuciya ta,gobe insha Allah Zamuje gidan Abban Yesmin"

"Allah ya kaimu to ku d'auke Ni driver Mana nazo Ni na Kai ki"
"Hahaha to Shikenan, an gama"
"idan Kun shirya goben sai Ku kirani"
"Toh Insha Allah"
"ki shafa min Kan karamar Queen"
Hannu tasa akan Asiyah tace "Na shafa maka"

" Toh saura na My Queen" tasa hannu a kanta ta shafa Tace "Done"
"Thanks Love,good night,ki kula min da Kanki kinji?"
"insha Allah, please do same"
"I'll bye"
A tare suka katse wayar.

Murmushi kawai take tana Jin wani irin dad'i, Asiyah ma Murmushi take yi don tun Fara wayar su har suka gama tana Jin su,Amma tayi kamar bata ji ba. (oh ni Milhaat ina ganin ikon Allah ,ni kam bazan iya irin wannan Soyayyar ba).

WASHE GARI
........... "Safiya Ni sa'ar kice ina magana kina Maida min magana?"
"Mummy me na Miki Kuma ,Wai ke meyasa kike son takurawa rayuwatane ke Baki da aikin yi sai masifa haba"

Tashi tayi ta wanka mata maruka biyu masu zafi Tace "Idan Kika sake ina magana kinayii sai na datse miki harshe Kuma na kashe ki"
"Mtswww akwai wani abunda Kika kware Akan sane Banda kisa to sai me idan kin kashe ni?"
Ganin tayi kanta tasa gudu tana biye da ita har Saida ta shige d'akin ta ta kulle kofar ta ciki.

A tsawace Tace "Safiya..... Safiya open this door"
"Baza a Bud'e d'in ba"
"safiya ni kike cewa Haka? Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,wai me ke Shirin faruwane,asirin Nan na kokarin karyewa dani kike zancen yarinya idan kin San wata baki San wata ba"
Ta shige d'akin ta.

Wani Kullin magani ta dauka a cikin Waldrope d'in ta, fridge ta Bud'e ta d'auko yoghurt ta juye Rabin maganin a ciki,ta girgiza da kyau ta Maida ta ajiye, Jakarta ta d'auko ta shige mota tayi ficewar ta.

Safiyya na Jin karar motar ta gane ta fita ne tsaki ta jaaa, ta fito fridge ta nufa ta d'auki wannan yoghurt din da Baraka tasa Abu a ciki, tana Bud'ewa ta kafa Kai ta shanye tass ko bismillah batayi ba,wani irin bacci ne taji ya kamata,har ta Fara haurawa Kan stairs taji baza ta iya ba ta dawo kan sofa ta kwanta.
💦💦💦💦💦💦💦💦
Please comment and Share
Milhat ce
Yar Terawa




An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment