Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aikinta akan yadda za ta ɓullowa case ɗin nan. Murmushi tayi ba ta san lokacin da ya suɓuce mata ba na jin hukuncin da zuciyarta ta yanke mata.
  Ƙarfe huɗu da rabi tabar office, kamar jiya napep ta tara ta koma gida. Bayan ta sauƙa ta ba shi kuɗinsa ta wuce cikin gida, da sallama ta tura ƙofar gida ta shiga, nan idanuwanta suka sauƙa samar Abba da yake zaune a bakin balcony nashi, hannunsa ɗauke da jarida.
  Ɗauke kanta ta yi ta nuna tamkar ba ta ganshi ba ta nufi falon Umma.
Abba da kallo ya bita har ta shige, sai kuma ya mayar kansa kan abin da yake. Duk yadda yaso kawar da cewa bata ganshi bane ya kasa, zuciyarsa ta kasa gaskata hakan cewa Mariya ta ganshi ta ƙi gaishesa.
...

  Mariya tana shiga falon babu kowa alama duk suna islamiyya, kai tsaye ɗakinsu ta wuce, ta samu Haneefa ta dawo suna zaune da Ummi Aisha. Sai hira suke wanda duk Ummi Aisha ce mai hiran. Sannu kawai ta musu suka amsa mata, ta cire hijab ɗinta ta ajiye jakarta ta wuce bathroom.
  Wanka tayi ta ɗaura alwala ta fito ɗaure da towel, ta nufi wardrobe ɗinta ta buɗe ta ɗauki riga simple ta saka, ta saka hijab ta gabatar da sallar la'asar. Tana idarwa ta miƙe ta fita don yunwa take ji, dining ta nufa ta buɗe abinci ta zuba ta ɗauka plate ɗin ta koma ɗaki. A bakin gado ta zauna ta ɗaura plate din a cinyarta kafin ta fara ci.
Tayi loma kusan uku ta kalli Ummi Aisha ta ce."Ina Umma?"

Ummi Aisha da take daf da ita kwance ta ce.
"Ta fita gidan Aunti Laila dubawa Salim da Baba ƙarami kaya, wanda aka kawo basu mata ba."

Kai Mariya a ta jinjina ba tace komai ba, ta ci gaba da cin abincinta. Haneefa da take jinsu tabar abin da take ta kalli Mariya.
"Ya aikin? Akwai wahala?"

Murmushi Mariya ta yi, ta furzar numfashi a hankali sannan ta ce.
"Babu laifi."

  Sanin iyakacin amsar yasa Haneefa ƙin cigaba da zancen, tasan yanzu ko ta matsa mata da tambaya amsar zai koma eh ko a'a.
  Mariya sauran ragowar abincinta ta ƙarasa cinyewa ta miƙe, ta fitar plate ta dawo ɗakin lokacin an fara kiran sallar magriba. Sanin alwalarta yana nam kawai ta gabatar da sallah, bayan ta idar ta ɗauki wayarta jin yana ƙara.
  Zakiyya ce ƴar Aunti Babie, ɗauka ta yi ta kafa a kunne tana mata sallama.
Daga can ta amsa tana tambayarta aiki. Mariya ita ma dai ce mata ta yi Allahamdulillahi kawai babu wani dogon zance. Sanin halinta yasa Zakiyyah yi mata sallama ta kashe wayarta.
  Haka suka zauna har dare lokacin cin abinci, basu fita ba duk da suna jin hayaniyar su Ikhlas da Maryam, sai Baba ƙarami da Abba da Khadeeja, ga kukan Salim ɗan shekaru huɗu, Hassan da Hussain da Faruq suna makaranta a hostel.
Haneefa da Ummi Aisha sai ƙarfe takwas suka fita cin abinci. Mariya kam tace ta ƙoshi yanzu taci.
  Ganin su biyu Umma da take bawa Salim abinci ta tambayesu.
"Ina Mariya?"
Ummi Aisha ta sanar mata cewa.
"Ai yanzu taci abinci."

  Hakan yasa ta ci gaba da bawa Salim nashi, sauran wasu suna kallo wasu su wuce ɗakin baccinsu.
Bangaren Mariya miƙewa ta yi ta gabatar da sallar isha'i, ta canza kaya zuwa na bacci ta haye gado, addu'a tayi ta rufe idanuwanta don so take bacci ya ɗauketa.
  A hankali kuma abin da ya faru tsakaninta da Barrister Waliy ya faɗo mata. Kamar yana kallonta ta taɓe baki, tana mamakin wasu da idan suka ga sunfi mutum su dinga nuna isa. Kawar da tunaninsa ta yi gefe, ta faɗa na yadda za ta ɓullowa case din, nanma kawarwa tayi ta shiga na wanda tayi lokacin tana masallaci.
  Motsin taji yasa ta buɗe ido taga Haneefa ce ta shigo, mayar idanuwanta tayi ta rufe, a haka bacci ya ɗauketa ba tasan lokacin da dukkansu suka kwanta ba.

  Ƙarfe ɗayan dare da minti goma.
A mugun firgice Mariya ta farka dalilin mafarkin da ta yi gamo dashi a baccinta, ta dafe kirjinta jin yadda yake bugu da ƙarfi gaske tamkar yau ta fara. Ganin ba gaske bane kamar kullum yasa ta karanto addu'a na neman cigaba da tsarin mafarkinta a gaske da mafarki.
  Bayan ta gama ta kwanta tana matsawa jikin Haneefa sosai tamkar za ta shige mata. Ƙarshe ma ta ɗaga hannun Haneefa ta ɗaura a jikinta yadda ko me zai faru za taji itama. Daga haka wani baccin mai daɗi ya kwasheta.

#vote
#comment

GOBE DA NISA
Page 3
Na Pharty BB

Motsi da Mariya ta yi ne ya farkar da Haneefa, ta ji Mariya ta rumgumeta, ba ta iya hanata ba ta sake ƙarfin riƙeta a jikinta da kyau, domin mafarkin da Mariya take yi ta fara sabawa dashi, sai dai har yau ta ka sa tambayarta dalili, ta bar abin a mummunar mafarki ne da kowa yana yi. Haka suka koma bacci.
  Da asubanin bayan sun gabatar da sallah basu koma ba, Mariya ta hau gyara kayanta, Haneefa ta tattare ɗakin tas, suka barwa Ummi Aisha shara tunda tana gida ita.
  Wanka suka yi suka shirya zuwa aiki suka fita, a falo suka samu Umma da sauran yara da suka shirya zuwa makaranta. Gaishe da ita suka yi yaranma suka gaishe dasu, daga nan suka yi breakfast suka mata sallama suka fita a gidan.
  A hanya suka rabu kowacce ta hau napep ta wuce wajen aikinta.
Mariya kasancewar yau tayi sauri sai bata damu ba, a cikin nutsuwa ta ƙarasa cikin office ɗinsu. Wayam ta gani alamar babu kowa amma kuma a buɗe. Agogon ɗaure a tsintsiyar hannunta ta duba taga takwas da kwata saura mintuna kafin tayi latti. Abin ne ya ɗaure mata kai da tunanin ko basu zo bane ganin lokaci yaja.
  Rasa mai bata amsa yasa ta taɓe bakinta ta fara ƙoƙarin zama, kamar daga sama taji maganarsa. "Me ya hanaki zuwa meeting?"

  A hanzarce ta juya taga Barrister Waliy tsaye a bayanta, suna haɗa ido ta ɗauke nata shi ma ya janye nashi yana barin wajen, dama wucewa yazo yi don zuwa meeting ya ga office ɗin a buɗe ya leƙa ko akwai wani a ciki.
  Mariya cikin sauri tabi bayansa don ba sanin ina za ayi tayi ba, kuma sam bata da labarin meeting ɗin sai dai idan yau da safe suka haɗa.
  Babban compress room taga ya shiga, ita ma tabi bayansa ta shiga bakinta ɗauke da sallama ƙasa ƙasa. Jama'a ta tarar a wajen har da wanda bata sansu ba a ma'aikatar, manyan baristoci da suka jima a aikinsu, alkalai har da su register, ga sabbi irinta. A cikinsu ta samu guri ta zauna cikin sauri.
  Tamkar ita ake jira ta zauna gurin ya ɗauki shuru. Barrister Hamza ne ya miƙe ya fara jawabi da musu sannu da zuwa, tare da karfafa musu guiwa akan aikinsu su jajirce sannan kar suji tsoro ko shakkar kowa. Haka ɗaya bayan ɗaya manyan suka gabatar abin da zasu yi.
Barrister Waliy shi ne a ƙarshe.   Cikin muryar nan nashi mai saka tsoronshi a zukatan jama'a ya fara nasa jawabin.
 Mariya duk yadda taso jurewa karta kalle shi kasawa tayi, a hankali ta ɗago kanta tana kai idanuwanta gare shi.
  Tamkar walkiya haka ya hango fararen idanuwanta suna kallon sa, kallonta ya yi suka haɗa ido. Mariya da sauri ta ɗauke idonta ta sunkuyar ƙasa jin yadda zuciyarta ta buga.
Barrister Waliy ma janye nashi ya yi yaci gaba da bayaninsa.
Awanni uku aka ɗauka ana abu ɗaya wanda duk su Mariya ake ƙarawa sani a fannin aikinsu a matsayinsu na sabbi. A wajen aka raba musu abin ci da abin sha aka ajiyewa kowa a gabansa, ɗaya bayan ɗaya kowa ya fara ɗauka yana sha.
  Mariya kasawa tayi ganin uban jama'ar nan ta ɗauki abu tasha, ji take ai zata kware.
Haka aka gama taron wajen ƙarfe sha biyu saura sannan aka sallame su, kowa ya miƙe ɗauke da abin da bai ci ya fita. Mariya kasa ɗauka tayi, tana miƙewa ta juya ta fice.
Duk abin da tayi idanuwan Barrister Waliy akanta, daga jiya zuwa yau ya karanceta tsaf, babu abin da yake hangowa tare da ita sai miskilanci zalla.
Miƙewa ya yi daga inda yake ya nufi inda ta zauna, hannu yasa ya ɗauki abubuwan da babu abin da ta taɓa ya fice a compress room ɗin. Office ɗinsa ya wuce kai tsaye, bayan ya shiga ya ajiye snack ɗin hannunsa saman tables sannan ya zauna. Landline na office ɗinsa ya jawo ya yi ƙira.
...

  Ƙara ne ya cika office ɗinsu na landline, dukkansu sun tsorata don ba a taɓa ƙiransu ba. Kafin ya yanke ɗaya namiji ya miƙe ya ɗauka da sauri yana kafawa a kunne, sallama ya yi a hankali kamar mai tsoro.
  Daga can ɓangaren Barrister Waliy jin muryar namiji ya amsa sallamar ya ba shi umarni.
"Ka turo min waccan mai white hijab, Barrister Waliy ne."

"Ok sir."
Ya faɗa yana zare wayar jin ya kashe. Wajen zamansa saurayin ya koma, ya dubi matan ciki yaga banda Mariya babu mai baby hijab fari, sauran gyale ne sun yi rolling, hakan yasa ya gane ita yake nufi.
"Barrister Waliy yana ƙiranki mai hijab."

Mariya da sauri ta ɗago kanta jin abin da ya faɗa sanin itace kaɗai mai hijab. Taga ya nuna mata landline yace.
"Yanzu ya ƙira kina ji."

Ɗauke kanta tayi don ba za ta musu ba don taji ta gani, miƙewa tayi ta fita bata ɗauki ko handbag ɗinta ba balle files din da ya bata. Tasan akan case din da ya bata kaɗai zai tambaya, ita kuma zata sanar dashi bata gama ba.
  A haka ta ƙarasa office ɗinsa, da bismilla ta ƙwanƙwasa ƙofar tana dakatawa. Taji ya bata umarnin shiga, a hankali ta murɗa handle ɗin ƙofa ta shiga da sallama.
A can ƙasan makoshi ya amsa mata, ba dan ta kasa kunne ba kuma babu surutu ba zata ji ba. Ƙyam ta tsaya kanta a ƙasa ita ma cikin murya ƙasa ta ce.
"Gani Sir."

Bai ɗago ba daga rubutun da yake, ya ce."Kwashe waɗannan kayanki."

Sai lokacin Mariya ta ɗago kanta takai idonta kan kayan da yake faɗa, nan ta yi tozali da abin da aka raba musu ne na ci da ta bari. Kasa motsawa ta yi balle ta ɗauka.
Jin shuru yasa Barrister Waliy barin abin da yake yi ya ɗago ya kalleta, suka haɗa ido ta yi saurin ɗauke nata. Kallon daƙiƙa ya mata ya ɗauke kansa, duk yadda ake cewa yana da miskilanci yarinyar nan ta dama sa, yana mata magana kuma yasan taji amma ta ƙi ko motsi.
'Ko dai tana da matsalar kunne.' Ya tambayi kansa a zuci, a zahiri kuma cikin ɗaga murya ya ce.
"Kar ki bari na tashi."

Jin tsawar da ya yi yasa Mariya ɗagowa a tsorace, ta kalli kayan sai lokacin ta buɗe baki cikin sanyin murya ta ce.
"Me zan yi dashi to?"

"Ki zubar."
Ya faɗa yana buga tsaki iya ƙarfin, haushin kansa ne ma ya kamasa da ya ƙirata ta ɗauka, da ya sani ya bari a wajen ko ya kyautar.
Matsawa Mariya tayi tasa hannu ta ɗauka, ta juya tana barin wajen ta fita a office ɗin. Tsaki ya buga yana cigaba da yin aikinsa.
...

  Mariya tana fita office ɗinsu ta koma, bayan ta ajiye kayan hannunta ta zauna ta zubawa kayan ido. Mamaki take ashe yana kallonta ta kasa cin komai.
'To kuma me zai damu kansa sai taci.' Wani sashe na zuciyarta ya tambayeta.
'Gudun yin asara?' Ta bawa kanta amsa, da sauri ta girgiza kanta ganin tamkar yafi ƙarfin hakan, ba shi kaɗai ba dukkan manyan gurin sunfi ƙarfin asarar abin dubu biyu.
Ƙiran sallar azahar da aka kwada ne ya shiga dodon kunnenta, a hankali tabi har aka idar, bayan an gama tayi addu'a, ta ɗauke kayan ta buɗe drawer ta ajiye ta miƙe ta fita.
  Masallaci ta nufa tayi sallah ta dawo, bata shiga cafeteria ba ta koma office. Bayan ta zauna ta buɗe drawer ta ɗauki snack ɗin ta fara ci.
  Kasancewar babu yawa yasa ta cinye tas, sai drinks ɗin da ta rage kaɗan, sai lokacin taji daɗinsa cewarta yau ta huta da zuwa siyan abinci. Bayan ta ƙoshi ta fara aikinta, sai dai duk yadda taso rubuta tambayoyi ta kasa dole tana buƙatar zuwa wajen mai ƙara.
  Barin abin da take yi tayi ta kalli agogon hannunta, uku saura ta gani. Tana da lokaci kaɗan, daga nan ma za ta wuce gida ba sai ta dawo ba, tuna haka yasa ta miƙe ta ɗauki files din tare da handbag ɗinta ta fita. Da kallo ƴan gurin suka bita dashi suna mamakin halinta na rashin son magana, wasu hakan ya burgesu yayinda wasu haushi taba su.
  Mariya bata ma san suna yi ba domin tuni ta samu ficewa a court ta tari napep, bayan ta faɗa mishi stations da zai kaita ya yarda ta shiga yaja. Har ƙofar ya kaita ta sauƙa ta biyashi sannan ta wuce ciki.
  Da sallama ta shiga wajen, suka tareta cikin girmamawa. ID card ɗinta ta nuna musu ta gabatar da kanta, tare da neman Isah Hamza wanda aka kama sati ɗaya da ya wuce bisa zargin sata, lauyansa ne ya turota za ta masa tambayoyi.
  Babu ɓata lokaci suka yarda, DPO yasa aka fito dashi aka basu guri. Bayan sun gaisa Mariya ta nemi ya faɗa mata gaskiya, tsaf ya sanar mata. Cikin hikima Mariya ta cigaba da mishi tambayoyi yana bata amsa tana rubutawa, a haka ta tsinci abin da za ta samu. Ganin lokacin yaja ta miƙe tana faɗin.
"Na gode Malam Isah. Zan iya dawowa kowanne lokaci don wasu tambayoyin."

"Ni ne da godiya, ki ƙara yiwa oga godiya bisa dawainiyar da yake dani."
Faɗin Isah don ko ahlinsa sun banzartar dashi, abokansa ne suka yi shiga da fice suka samu damƙawa Barrister Waliy case ɗin domin ya tsaya mishi bisa zargin da unguwa ake mishi yana musu sata. Duk da yana matsayin abin zargi hakan bai hana Barrister Waliy kin kula dashi ba.
Murmushi kawai Mariya tayi ta yiwa ƴan waje godiya ta fita. Napep ta tara ta shiga ya nufi gida da ita, bayan sun isa ta sauƙa ta biyashi ta shige gida.
  Yau babu motar Abba alama baya nan, numfashi ta sauƙe taji wani nutsuwa ya sauƙa mata. Cikin falo ta wuce ta samu ahlin gaba ɗaya suna zaune a falon.
  Sallama ta musu, ta durƙusa ta gaishe da Umma. Cikin fara'a tana kallonta ta ce.
"Sannu Mariya. Ya aiki?"

"Allahamdulillahi." Mariya ta faɗa tana miƙewa ta wuce ɗakinsu. Babu kowa, hakan yasa ta cire kayan jikinta ta faɗa bathroom.
Kamar kullum ruwa ta watsa ta ɗaura alwala ta fito ta saka doguwar riga ta gabatar da sallah, bayan ta idar ta fita falo. Dining ta nufa ta zuba abinci ta zauna ta hau ci anan saɓanin wani lokaci da take ci a ɗaki. 
Tana jin hayaniyar su da surutunsa amma ko a bata tanka ba, sun san ba baki zata saka ba hakan yasa babu wanda yasata a hiran su.
Bayan ta gama cin abincinta ta miƙe ta kai plate ɗin kitchen, ta ɗauki ruwa a fridge ta fita ta wuce ɗakinsu. A bakin gado ta zauna, ta buɗe ruwan hannunta tasha kusan dukka ta ajiye sauran a bedside drawer.
  Miƙewa tayi ta ɗauko files din data zo dashi ta haye tsakiyar gado, buɗewa tayi ta fara bin daki-daki na jawabin Isah Hamza tare da tambayoyin da ta rubuta. 
Tambayoyi kaɗan ta rubuta cikin abinda ta fahimta ta rubuta, ta ɗauki files ɗin ta ajiye a guri mai kyau.
  Kan gado ta kwanta bayan ta ɗauki wayarta ta fara dannawa, a haka har dare ya shiga babu abin da yake ɗagata sai sallah. Yau bayan sallar isha'i bata kwanta ba ta miƙe ta fita falo, duk da ba magana zata yi ba gwara ta zauna cikinsu tana saurara.
  Sosai suke hira a tsakaninsu, musamman Ummi Aisha da Maryam da muryarsu yafi na kowa fita, ga Abba da Baba ƙarami ma suna nasu hiran, Haneefa ce take saka baki a rigimar Ummi Aisha da Maryam, Khadeeja ma ba mai yawan surutu bace hakan yasa jifa jifa take saka musu baki. Salim na tare da Umma.
  Cak falon ya ɗauki shuru bisa sallamar da aka doka, gaba ɗaya suka zubawa ƙofar ido ganin mai shigowa musamman Mariya da taji muryar mai sallamar har tsakar kanta, wanda ya haddasa mata bugun zuciya.

#vote
#comment
GOBE DA NISA
Page 4
Na Pharty BB

   A facing ɗinta ya zauna, yana jifanta da murmushin nan nasa mai tsinka zuciyarta ya amsa gaisuwarta, tare da tambayarta ya aiki.
  Mariya kanta kawai ta girgiza alamar lafiya ta ka sa yin magana. Gaba ɗaya a takure take da zaman, hakan yasa ta miƙe tana cewa.
"Sai da safenku."

  Umma ta amsa ta bita da kallo, ta juyo ta kalli Abba da ya bita Mariya da kallo ta ce.
"Wannan shegen miskilancin yarinyar nan naka ya ishe ni, ace mutum magana yana ba shi wahala."

  Abba da yabi Mariya da kallo harta shige ɗaki ya juyo ya kalli Umma jin abin da ta faɗa, fuskarsa da murmushi ya ce. "Abin gado ne."

  Umma baki ta taɓe ta miƙewa.
"Sai dai a wajenka." Tana faɗa tabar wajensa ta nufi fridge ta ɗauko mishi ruwa, sauran yaranma ɗaya bayan ɗaya suka miƙe suka shige ɗaki. Shigowarsa dama yasa gaba ɗaya suka nutsu, sallamarsa ne ta katse musu surutun su.
  Ummi Aisha da ta shiga ɗakinsu ta zauna kusa da Mariya da take kwance saman gado idanuwanta rufe, kallonta tayi tana faɗin.
"Kinji kin ƙara taɓa Umma. Wai don Allah bakinki ba ya tsami?"

  Mariya idanuwanta ta buɗe tana kallon Ummi Aisha, tamkar ba za ta tanka ba, tayi murmushi da ya bayyana dimples ɗinta sannan tace.
"Ina yi mana, kawai dai bana saka kaina hiran da bai shafe ni ba, sai kuma wanda bai game ni ba nake ƙin tankawa."

"A wajen aikinma haka kike musu?"
Ummi Aisha ta tambayeta ganin yau ta buɗe baki ta mata magana mai tsayi.
  Girgiza kai Mariya tayi ta rufe idanuwanta, tasan idan ta biyewa Ummi Aisha sai su kwana surutu.
Fitowar Haneefa a bathroom yasa Ummi Aisha miƙewa ta shige bathroom don yin wanka. Haneefa bayan ta saka kayan baccinta ta zauna kusa da Mariya, buɗe ido Mariya ta yi ta kalleta ba tace komai ba.
Haneefa ta mata murmushi ta ce.
"Me ya faru naga kamar kina da damuwa."

Girgiza kai Mariya tayi sannan tace.
"Babu komai, gajiya ce."

  Jin abin da ta faɗa yasa Haneefa hawa gadon sosai, ta kwanta gefen Mariya bata kara cewa komai ba.
Ita ma Mariya kwanciyarta ta gyara tana matsawa tsakiyar gado ta barwa Ummi Aisha ƙarshe don dama koyaushe ita ce a tsakiya sai idan Haneefa bata nan.
Dalilin yawan mafarkan da take masu firgitata ta farka yasa Haneefa take sakata tsakiyarsu, don da zaran ta farka itama sai taji wani lokaci, watarana kuma bata jinta har ta yi ta koma, shi yasa idan take da night duty kullum tunaninta yar uwartan ta kwana.
Haka Ummi Aisha ta fito ta gama shirin baccinta ta kashe wuta ta haye saman gado ta kwanta. Addu'a suka yi kafin dukkansu su kwanta.
  Cikin ikon Allah yau har gari ya waye Mariya ba tayi mafarki ba balle ta farka, hakan ya musu daɗi dukkansu duk da dama takan jera kwanaki uku zuwa huɗu ba tayi ba.
  Bayan sun gabatar da sallah kamar kullum suka tattare ɗakin suka shirya suka fito, Umma suka gaishe suka yi breakfast kafin su fita. Ɓangaren Abba suka nufa suka gaishe dashi wanda da farko Mariya kamar kar taje, amma ganin Haneefa yasa ta binta.
Bayan ya musu fatan alheri kafin su fito suka bar gida kowacce ta kama gabanta zuwa wajen aikinta.
Mariya yau ma akan case na Isah Hamza ta wuni, har aka tashi ta musu sallama ta dawo gida.

  Haka kwanakin suka tafi a rayuwar ahlin kamar baya.
Mariya ta dage da zuwa aiki da take jajircewa akai don cikar nata burin, basu kara haɗuwa da Barrister Waliy ba.
Bai nemeta ba akan aikin da ya bata, hakan yasa ta kwantar da hankalinta take bin komai daki-daki wanda har ta kusa kammala na zargin Isah Hamza da ake yana sata a unguwar su, saura ɗayan.
A haka har aka shiga weekend, mai maimakon su huta amma Ummi Aisha ta kwakulo musu tafiya gidan ƙanwar Abba yini. Mariya haushinta taji sosai don ita kam burinta ta huta a weekend ɗin nan, kuma idan ta zauna ita ɗaya za a bari domin har su khadeeja da suke yara zasu je.
  Dole yasa ta shirya cikin riga da skirt na lace blue da ash, ta yi amfani da ash mayafinta, sai ƙaramin handbags ɗinta kalar takalminta. Tayi kyau sosai domin Mariya akwai kyau da tsarin halitta mai burgewa, wanda da dama shi yake fisgar jama'a.
Haka Haneefa irin lace nata ta saka sai banbancin color, na Haneefa brown da mint green maimakon color irin na Mariya, sai kamminsu ya sake fitowa.
Bayan sun gama shiryawa Abba ya bada mota driver ya kaisu har gidan Aunti Yahanasu, tayi murnan ganin yaran yayan nata sosai, suka haɗu da yaran gidan sai suka cika gidan sosai da hayaniya, kowa ya kama abokinsa suna kuskus abinsu.
Mariya, Haneefa da Ummi Aisha su ma gefe ɗaya suka haɗe da ƴan biyun Aunti Yahanasu suka kafa cafta. Hira suke sosai, da ƙyar Mariya tayi ƙoƙarin sakewa take saka baki gudun su kafa nata chapter na rashin son magana.
Hakan ko ya musu daɗi har Hassana sai da ta tanka ta ce.
"Yau za ayi ruwa da kankara."

"Ko kuma gwamna zai zo gidanku ba."
Ummi Aisha ta faɗa, fahimtar zacen sauran suka kwashe da dariya, ban da Mariya data murmusa tana cije lips ɗinta, tasan da ita suke.
Suna wannan yanayi aka yi sallama aka shigo, tuni Haneefa ta haɗa rai jin mai yin sallamar, shi ko ganinta yasa ya ƙara faɗaɗa fara'ar fuskarsa ya ƙarasa wajensu.
Zama yayi facing ɗinta yana jifanta da murmushi, ita ko ta haɗa rai tamkar ba ita ba.
Ummi Aisha ce ta fara gaishe dashi ya juya yana amsawa, haka Mariya ma ta gaishe dashi, ya amsa sannan ya juya kan Haneefa.
"Ke ba za ki gaishe dani ba."

"Ina wuni."
Ta faɗa ƙasa ƙasa tana sake haɗa rai. Sam baya burgeta saboda halayensa, duk yadda ya matsa mata da ƙoƙon barar soyayyarsa, kuma rabi da kwata Mariya ke ƙara karfafa mata guiwar ƙin sa, daɗinta ɗaya babu wanda ya sani a iyayen don tasan zasu iya amincewa tuni.
Maganarsa yasa ta kalle shi ta ɗauke kanta, gaba ɗaya gani tayi ya ƙara lalacewa ya rame. Girgiza kanta tayi ta miƙe tabar wajen gaba ɗaya don yafi mata alheri.
Nafiq ya bita da kallo sannan ya juyo kan Mariya itama ta haɗa ran da yafi na Haneefa, hakan yasa ta sake mishi kwarjini fiye da kullum.
Ka sa mata magana yayi ya miƙe yabar wajen, hakan ya basu damar cigaba da hiransu ban da Mariya da zuciyarta da ƙwaƙwalwarta suka faɗa wani tunanin daban.
Tashinsu tsaye yasa ta dawo hankalinta, ta kallesu ba ta iya tambayarsu ba. Ummi Aisha da tasan halinta ta ce.
"Da kika kasa tambayar to ɗaki zamu je."

  Babu musu ita ma ta miƙe suka shiga daƙi wajen Haneefa, kwance suka sameta suka ƙarasa suka zauna gefenta. Anan suka ci gaba da hiransu har azahar, suka yi sallah kafin su haɗu su fita zuwa kitchen suka haɗa hannu suka ɗaura abincin rana.
Wajen ƙarfe biyu da rabi suka gama suka fitarwa kowa nashi, suka ƙira yaran suka karɓa sauran nasu, sauran suka jera a dining bayan sun zuba nasu suka wuce ɗaki dashi.
Ranar sunyi wunin daɗi, sun yi hira, sun ci sun sha sun kawar da kewa, hatta Mariya sai daga baya taji daɗin zuwa.
Ƙarfe biyar da rabi driver yazo ɗaukar su cewa Abba ne yace ya zo. Babu musu suka shirya suka yiwa Aunty Yahanasu sallama, ta basu tsarabar turaruka suka tafi.
Suna komawa gida yaran suka zagaye Umma suna nuna mata tsarabar da bata labarin hirar su, su Mariya kam suna nuna mata ɗaki suka wuce kowacce ta canza kaya zuwa doguwar rigar shan iska na zaman gida.
Har dare basu fito ba sai bayan sallar isha'i, Ummi Aisha da Haneefa suka fita

Please Login or Register in order to submit comment