Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yaya Haydar kallonta ya yi ganin ta tsaya yaga kanta a ƙasa, murya a cunkushe ya ce. "Mene ne kuma?"

Cike da tsoron me zai ce ta girgiza kanta, ruwan hawaye ya taru a idanuwanta ta kalle shi, da ƙyar ta yi ƙoƙarin kallon cikin idanuwansa ta ce."Ni ba zan iya kwana ni ɗaya ba."

  "Ina Ummi Aisha da Haneefa." Ya faɗa yana juyawa ya dubi Umma da Abba, sai lokacin ya lura babu su duk hayaniyar.
Maganar Mariya yasa ya dubeta lokacin da ta ce. "Ba ta nan, Haneefa tana asibiti."

  Bai ce komai ba yaja hannunta suka nufi ɗakinsa da yake daga can ƙarshe. Ai Mariya ji ta yi da ba ta sanar da shi ba, jikinta rawa ya ci gaba da yi yadda yafi na farko. Ita tun da take ma za ta ce bai fi sau biyu ta shiga ɗakinsa ba, shi ma sai ba ya nan gudun ya ce ta mishi laifi ya daketa.
  Tana ji tana gani babu damar mishi musu, haka ya buɗe ɗakinsa suka shiga. Ɗakinsa mai kyau da shi komai fari da blue, tsaf da shi kamar ɗakin mace sai ƙamshi da sanyin AC. Fagen tsafta Yaya Haydar ba baya ba ne domin yana da mugun tsafta da kyankyami.
  Suna shiga ya sakar mata hannu ya nufi wardrobe ɗinsa, hakan yasa ta tsaya ta ka sa ƙarasawa ciki.
  Yaya Haydar duvet ya ɗauka sabo ya dawo wajenta, miƙa mata ya yi babu musu ta karɓa da sauri. Gurinta ya bari yana fadin.
"Ki kwanta a saman sofa."

  Daga haka ya haye saman gado ya kwanta ya rabu da ita. Mariya ta kusan mintuna uku a tsaye, ta ka sa ko motsawa, mamakinsa take yadda yake nuna mata kulawa, abin da hakan bai taɓafaruwa tsakanin su ba.

"Za ki zo ki kwanta ko sai na ɗaukoki." Ta ji mugun tsawarsa da ya dawo da ita hankalinta, ta dube shi da sauri ta ga ya tashi zaune.
Kanta ta sunkuyar ƙasa ta ja ƙafafuwanta ta nufi sofar da yake facing ɗinsa ta zauna.

"Tashi ki fita min a ɗaki." Ya faɗa cikin tsawar da ya tsorata Mariya.
  Da sauri ta kalle shi ta ga ya watsa mata wani kallo da manyan idanuwansa masu tsoratata, cikin azama ta ɗauke nata ta gyara kwanciyarta ta rufe jikinta har saman kanta, zuciyarta sai bugawa take da sauri na tsoron kasancewa da Yaya Haydar da kuma abin da ya faru.
  Tasan Allah ne kaɗai ya ceceta daga afkuwar komai, da ba ta san ya za tayi ba, kuma ba ta san wa za ta tuhuma ba. Ba ta hayyacinta balle ta bambamce wanene, har ta gano ina ya shiga lokacin da ya gudu dalilin ihunta.
  Tana wannan tunanin har bacci ya ɗauketa ba ta sani ba, sai dai cike da tsoro take yi don cikin baccin ma sai mafarki take.
  Yaya Haydar bayan ya kwanta shi ma da ƙyar bacci ya ɗauke sa tuna abin da ya faru, yasan Allah ne kawai ya rufa asiri yau.
  Ƙiran sallar asuba ya farkar dasu, shi ya fara miƙewa ya shiga bathroom ya ɗaura alwala ya fito. Wajen Mariya ya nufa ya tsaya a kanta, gaba ɗaya jikinta a rufe ta kudundune sai fuskarta da ta buɗe.
  Innocent face nata fiyau, gashin kanta da yake a wargaje ya bazu a saman pillow wani a gefen fuskarta, ta ɗan turo ƙaramin bakinta alama  ba ta jin daɗin baccin ko sanyi ya dameta duba da yadda ta dukunkune.
  Ruwan hannunsa ya watsawa fuskarta da yasa Mariya firgita tana neman yin ihu. Ganin Yaya Haydar yasa ta nutsuwa tana yin ƙasa da kanta ganin ya watsa mata wannan kallonsa.
  Gurinta ya bari bai ce mata komai ba ya fita a ɗakin. Numfashi ta sauƙe tana mamakin halinsa, duk abin da yaga dama yi yake babu ruwansa, idan mugunta ne yasan duk ta inda zai yiwa mutum.
  Miƙewa ta yi ta ɗauki duvet ɗin da ta rufu da shi ta linke, ta ajiye a saman sofa ta bar gurin tana fita a ɗakinsa, sam ba za ta iya shiga mishi bathroom ba, salon ya zo ya samu na jibgarta ya ce ta mishi wani abun.
  Ɗakin su ta buɗe ta shigar da ƙyar don tsoro, hakanma ganin asuba ne kuma kowa ya farka, bayan ta shiga key ta sawa ƙofa, tabi ɗakin da kallo yana nan yadda yake, sai lokacin mamakin yadda aka fitarta a ciki take. Tasan dai tana tunani da jiran ko Ummi Aisha za ta shigo har bacci ya ɗauketa, ba ta sake sanin komai ba sai lalubarta da taji ana yi tamkar a mafarkinta farka.
  Kawar da tunanin tayi da sauri ta wuce bathroom, kulle ƙofa ta yi kafin ta yi fitsari ta yi tsarki ta ɗaura alwala ta buɗe ta fito. Rigar jikinta ta cire ta saka wani, ta ɗauki hijab ta saka ta nufi inda sallayarsu yake shimfiɗe ta fara gabatar da sallar.
  Ko da ta idar ka sa komawa bacci ta yi, ta zauna tana azahar, ƙarshe ta miƙe ta ɗauki Alkur'ani ta fara karantawa. A haka har gari ya yi haske rana ta fito, ƙwanƙwasa ƙofa da aka yi yasa ta miƙe tana rufe Alkur'anin ta miƙe ta isa bakin ƙofa ta buɗe.
  Umma ce tsaye, Mariya ta gaishe da ita cikin nutsuwa. Umma ta bita da kallo cike da tausayinta.
  "Kin farka lafiya?" Ta faɗa tana amsa gaisuwarta.
  Mariya kanta ta ɗaga alamar lafiya. Umma ta kamo hannunta suka shiga ɗakin, a bakin gado suka zauna tana binta da kallo ciki da waje kusan mintuna.
  Murmushi Mariya ta yi ta ce. "Babu komai fa Umma."

"Kin tabbatar?" Umma ta tambaya tana miƙewa.
Mariya kai ta ɗaga tana faɗin. "Eh, shiryawa ma zan yi na tafi aiki."

  Jin haka yasa Umma yarda lafiyarta ƙalau, fita ta yi ta samu Abba da ya turota duba lafiyar Mariya ta sanar mishi.
Numfashi ya sauƙe sannan ya miƙe ya ce."Shike nan zan wuce, bana son yin rana ne, zan dawo da yammacin yau ƙarfe huɗu zuwa biyar. "

Umma ta miƙe ta mishi rakiya har filin gida wajen motarsa, sannan ta dawo falo ta ci gaba da ayyukanta.
...

  Da safe sanin Abba yabar gida yasa yaran babu wanda ya zauna dining don yin breakfast. Musamman da dodonsu yana zaune shi ɗaya a wajen, ai hakan yasa wasu ko gigin yin breakfast ba su yi ba suka bar gidan, ciki har da Mariya.
  Ya zauna bai jima ba Mariya ta fito cikin sanɗa ta fice fit a falon kafin ya ankara da ita.

  Maryam ma hakan sai dai ita ya hangota, dole yasa ta dakata ta gaishe da shi. Hannu kawai ya ɗaga mata ta miƙe ta fita.
  A tunaninsa Mariya tana ciki ta fito ya hanata tafiya aiki, haka ya yi ta zama don jiranta har ƙarfe tara, leɓbensa ya cije zuciyarsa ta fara hasala.
  Miƙewa ya yi cikin ɗaga murya ya kwalawa Ummi Aisha ƙira. Shuru ba ta amsa ba, sai Khadeeja ta fito jiki yana rawa ta durƙushe ƙasa.

   "Ina yarinyar nan?"
  Ya faɗa cikin ɓacin rai.
Khadeeja cikin mutuƙar tsorata ta ce. "In dai Maryam ce ta fita."

Cikin daka tsawa ya tareta ya ce.
"Dalla ba ita ba Kibdiyya."

Sanin shi ɗaya yake ƙiranta haka yasa ta gane da Mariya yake, cikin sauri ta ce.
"Ta fita tun ƙarfe bakwai saura."

"What!?" Ya faɗa a mutuƙar mamaki cikin tsawa, bai ƙara faɗin komai ba ya juya yabar falon.
  Khadeeja numfashi ta sauƙe sai kuma cikin sauri ta miƙe ta shige ɗakinsu duk ƙira da Umma take mata a nata ɗakin.
  Wayarta ta nemo ta ƙira lambar Mariya, ringing biyu ta ɗauka. Ba ta jira me zata faɗa ba ta sanar mata Yaya Haydar yana nemanta me ta mishi.
  Daga ɓangaren Mariya tsoro ne ya kamata, cikin raunin murya ta ce. "Babu komai."

"To wallahi ki san nayi, don ya fita cikin ɓacin rai."
Khadeeja ta faɗa cike da tausayin Mariya, sam ta rasa me yasa Yayan nasu yafi takurawa Mariya a kansu, baza tace su ba ya musu mugunta ba ko dukansu amma na Mariya yafi nasu don ko yaya tayi abu laifi ne.
Bayan haka yau kam ko me ta mishi ya rabu da ita duba da abin da ya faru da ita jiya, wanda har yanzu babu wanda ya maimaita maganar, ƙarshe ma kowa ya kama harkar gaban shi kamar babu abin da ya faru.
  Zare wayarta tayi ta ajiye jin Mariya ta kashe, ta miƙe cikin sanyin jiki don amsa ƙiran Umma.
...

  Mariya tana gama waya da Khadeeja ta miƙe, ta ɗauki file ɗin case na Isah Hamza da ta gama dubawa yanzu ta fita.
  Cikin sauri ta nufi offices ɗin Barrister Waliy, ƙwanƙwasa ƙofa take tayi babu kakkautawa don tana tsoron Yaya Haydar zo ya tarar da ita, ba ta san me kuma ta mishi ba.
  Daga ciki ya bada izinin shiga, cikin sauri ta buɗe ta shiga. Da kallo Barrister Waliy ya bita ganin kamar a birkice take, ganin ta tsaya ta ƙi ƙarasawa ya nuna mata kujera.
"Zo ki zauna."

  Babu musu Mariya ta matsa ta zauna tana sauƙe ajiyar zuciya, sai da ta nutsu ta ajiye file ɗin hannunta ta ce.
"Ga wannan na kammala, saura ɗayan."

  Barrister Waliy ɗauka yayi ya ajiye a gefe, ya kalleta kanta a ƙasa, ganin ba ta motsa ba kuma ba ta da niyar tashi ya ce. "Shikenan, zan duba."

  Mariya ka sa tashi ta yi, kanta a ƙasa tana murza yatsun hannunta, zuciyarta tana ta kai-kawo akan hukuncin da ta yanke mata, tana faɗa mata ta sanar da shi kudurinta ko zai taimaka mata, amma wata zuciya tana hanata.
Barrister Waliy da ya gama ƙare mata kallo ya gama karantar yanayinta ya yi gyaran murya, sannan ya ce.
"Kina da matsala ne?"

  Mariya kai ta ɗaga a hankali ba ta kalle shi ba har lokacin kanta a ƙasa, cikin sanyin murya ta ce.

"Ina da babbar matsala a rayuwata tsawon shekaru, kowanne dare takan yi tsayi a idanuwana har nake ganin GOBE TA MIN NISA, da fargaba nake kwana a kowanne daren rayuwata. GOBE TA MIN NISA balle burina ya cika. Ta ina zan fara? Ta ya zan cika burina da mafarkina? Sai da taimako, amma ban san wa zan tunkara ba. Don haka ina neman taimako domin samun wanda zai tsaya min ya taya ni bani ƙarfin guiwa."

  "Mene ne matsalarki." Ya tambayeta zuciyarsa tana son fassara kalamanta daki-daki. Abin mamaki hawaye ya gani zar sun zubo saman kyakkyawar fuskarta, ba tasa hannu ta share ba ya ji ta fara faɗin.
"Ban kai matsayin da zan tsayawa kaina ba, bani da kowa da zai taimaka mini daga cikin ahlina."

  Shuru office ɗin ya ɗauka sai ajiyar zuciya da Mariya take sauƙewa yake tashi, zuciyarta tayi rauni kuka take son yi sosai ko za ta samu salama. Tsawon shekaru ta samu ta fitar da abin da yake ranta, wanda take ɓoyewa yana damunta kullum.
  Barrister Waliy ya ka sa faɗin komai, yayi shuru tsawon sakanni biyar yana tattara bayanan Mariya cikin ƙwaƙwalwarsa guri ɗaya.
Numfashi ya furzar ya kalleta yadda take share hawaye mugun tausayinta ya rufe shi, ashe gaskiyarsa da yace akwai wani abun a rayuwarta. Yana ci gaba da kallonta murya a hankali ya ce.
"Zan tsaya miki zan taimaka miki, zan yi dukkan ƙoƙarina naga kin samu nasara. Mene ne matsalarki? Wace shari'a kike son shigarwa."

  Wani sanyi Mariya taji ya ratsa kahon zuciyarta, wasu hawaye masu zafi suka taru a idanuwanta. A hankali cikin rawar murya ta sanar mishi mafarkinta, burinta da kudurinta don samun cika alƙawarin da ta ɗaukarwa kanta tun ba ta kai haka ba, a ƙarshe ta fashe da kuka.
Barrister Waliy jikinsa har tsuma yake jin abin da Mariya ta faɗa, ga kukanta yana ƙara baƙanta ransa, zuciyarsa tana bugawa da ƙarfi  gaske, gani yake tamkar yanzu komai yake faruwa a gabansa.
  Cikin ɓacin rai a mugun fusace ya miƙe, ya zagaya ta wajen Mariya ya tsaya saman kanta yana dubanta yadda take kuka sosai. Cikin muryarsa mai tsorata mai sauraro ya ce. "Tashi muje."

  Daga haka ya juya ya nufi ƙofa, Mariya miƙewa tayi da ƙyar don yadda yanayin jikinta ya canza, ji take da ba ta faɗa masa ba, da ba ta fallasa ba ta ci gaba da ɓoyewa a ranta kamar yadda take yi.
Sai yanzu take tunanin me zai je ya dawo ya zo mata amma bakin alƙalami ya bushe.
Haka tabi bayansa bayan ta share hawayenta, sai dai kallo ɗaya za ka mata ka gane ba a nutse take ba, gaba ɗaya tamkar ba ita ba.
Barrister Waliy yana gaba tana binsa a baya har office ɗin register inda ake rubuta ƙara, a kujera ya zauna ya kalli Mariya ya mata nuni da ta zauna bai ce komai ba. Babu musu ta ja ta zauna suna facing ɗin juna.
Ya juya ya kalla register da duk ya tsure ganin Barrister Waliy da kansa.
"Cika takardar tuhuma."  Ya faɗawa register ya juya ya kalli Mariya da ta tsura idanuwanta a takardar da register yake rubutu, ya ci gaba da faɗin."Ki sanar mishi."

  Mariya da sauri ta kalli Barrister Waliy, ya haɗa rai yana mata wani kallo don ya hango tsoro a tare da ita wanda yake karyar da ita, har ta ka sa aikata komai tun farko.
Sunkuyar kanta ƙasa tayi ganin irin kallon da yake mata, cikin rawar murya cike da fargaba ta faɗa mishi, tana gama faɗa wasu hawaye masu zafi da suka taru a idanuwanta suka zubo, zuciyarta ta cunkushe wani yawu mai tauri ya maƙale mata a maƙoshi.
  Barrister Waliy duk yana lura da ita sai dai bai hanata kukan ba, yasan dole ta yi, irin wannan babbar masifar na bibiyar rayuwarka.
  Register dai yana ta rubutu, bayan ya gama ya sanarwa Barrister Waliy. Bai karɓa ba ya miƙe sannan ya dube shi, muryarsa har yanzu a cunkushe ya ce.
"Yanzu-yanzu ka aika. And da ni za ayi wasan."

  Register kai ya jinjina, duk da yasan barrister Waliy da ba wa aikinsa mahimmanci da kwazo akai ya lura na yau dabanne. Hakan yasa ya miƙe ya fita don bada saƙo.
  Barrister Waliy kallon Mariya yayi, cikin taushin murya kamar ba shi ba ya ce. "Tashi muje."

  Miƙewa tayi babu musu suka fita, office ɗinsa ta ga sun nufa, ta dakata da tafiya ta tsaya, ganin zai yi nisa bai lura da ita ba tabi bayansa a hankali.
  Ya rigata shiga, ita ma ta shiga sai dai bata zauna ba ta tsaya. Shi kam wajen fridge ya yi ya buɗe, ya ɗauki goran ruwa ya buɗe ya hau sha ko zuciyarsa za tayi sanyi, kusan shanyewa ya yi sannan ya dakata, ya ajiye ya ɗauki wani ya nufi wajen Mariya.
  A gabanta ya tsaya daf har sai da ta ɗago ta kalle shi, idanuwansa da suka ɗan canza kala cikin nata, da sauri ta mayar ƙasa. Shi ma ya janye nashi yana miƙa mata goran ruwan.
"Karɓi kisha."

  Hannu tasa hannu ta karɓa a hankali, cikin muryarta da ya fara dashewa ta ce. "Zan koma office."



Bai amsa mata ba yabar wajenta, ya zagaya ya zauna a kujeran sa yana jawo files ɗin da ta kawo mishi, ya buɗe sannan ya ce.
"Shiga ki wanke fuskarki sannan."



  Ɗago kanta tayi taga hankalinsa ba ya kanta, jiki a sanyaye ta nufi bathroom ɗinsa, kafin ta shiga ta ajiye goran ruwan a saman wani desk ƙarami sannan ta wuce.
Fuskarta ta wanke ta yagi tissue ta goge, tayi fiyau da ɗan ja abinka da farar fata musamnan saman hancinta, sai cikin idanuwanta da suka ƙanƙance don kuka har fatar ya kumburo kaɗan.
  Bayan ta gama ta fita, ta ɗauki ruwan ta buɗe tasha ta riƙe sauran tabar wajen, zagayawa tayi don fita ta ji ya ƙirata. Dawowa tayi ta tsaya kanta a ƙasa tana amsawa.
  Barrister Waliy yana ci gaba da duba abin da yake yi ya ce.
"Duk abin da za ki ji ki gani karki ki tanka. And maganar shaidun da za ki bani sai har mai laifi ya shigo hannu, kotu ta bamu lokacin zama. Zan karɓa sannan zan yi iya ƙoƙarina don sama mana nasara."

"Na gode, in sha Allah zan yi duk yadda ka faɗa." Mariya ta faɗa wani hawayen yana taruwa a idanuwanta.
  Kai ya jinjina mata sannan ya ce.
"Shikenan, ki je sai na nemeki."

  Mariya juyawa ta yi ta fita. Barrister Waliy rufe files ɗin ya yi ya jinjina kansa a kujera tare da lumshe idanuwansa.
Mugun tausayin Mariya ya rufe shi, yarinyar ƙarama da faɗawa wannan iftila'in, masifa tana bibiyar rayuwarta da karancin shekarunta. Duk daren Allah ba ta da kwanciyar hankali. Shi ya ga ƙoƙarinta ma da take ɓoyewa.

'Me mutane me suke nema a rayuwar su?' Ya tambayi kansa ya rasa me ba shi amsa, sosai yaga ƙoƙarinta na iya kawar da komai take rayuwa, duk da mai kula ire-irensa idan ya zauna da ita zai karanci yanayinta.
...

   Mariya tana fita office ɗinsu ta wuce, table nata ta wuce ta zauna tana sauƙe tagwayen ajiyar zuciya.
  Kamar an jefosa ta ga ya tsaya a saman kanta, cikin mugun tsoro ta miƙe ta mishi kallo ɗaya, ta ɗauke kanta ganin wannan mayun idanuwansa masu cike da bala'i waɗannan bata iya juran kallo suna kallonta.
Jikinta mugun rawa ya fara, cikin tsarkewar harshe ta ce."Yaah...Haydar me nayi."

  Zai yi magana wayarsa ta ɗauki ƙara, leɓbensa ya cije ya zaro wayar da niyar kashewa ya fasa ganin ƙiran mai muhimmanci ne.
Ɗauka ya yi ya kafa a kunne bai ce komai ba, da hanzari kuma ya ce.
"What? Ina zuwa."

  Daga faɗin haka ya juya ya fita bai kalla Mariya ba. Ita kam komawa ta yi ta zauna tana addu'ar Allah ne ya kuɓutar da ita daga muguntar sa, sai dai zuciyarta ta ka sa daidaituwa akan ƙiran da ya samu.
  Sai lokacin tsoron me za ta tarar a gida ya faɗo mata, tasan da wuya su yarda har su bata haɗin kai, abun zai zo musu a ba zata kamar yadda ita ma ta faɗa a gabar da bai dace ba, domin ba yanzu ta so ba sai nan da lokacin da ta ɗauka, amma komai ya canza.
  Haka ta wuni a wajen aikin ba ta tabuka komai ba, gaba ɗaya jikinta ya mutu, ga kukan da tasha ya saka mata ciwon kai. Ana yin sallar la'asar ta tattara ta bar office zuwa gida, tare da fargabar me zata tarar.
...

  Haka ɓangaren Barrister Waliy ma da tunanin halin da Mariya take ya wuni, da ƙyar ya daure ya yi wasu aikin don samun sauƙi nan da litinin, ƙarfe huɗu yabar office ya tafi gida.
Ba Rumana ba hatta Ammi ta lura yaron nata baya cikin walwala, sai dai babu wanda ya tambaye sa suka bar abun akan aiki ne.

   Finally Mariya ta faɗawa Barrister Waliy burinta, saura muma mu ji a gaba.
  Ko Abba da Umma zasu yarda su ba ta haɗin kai ta cika burinta idan suka ji?
Yaya Haydar fa? Wanda ya takura mata?
...

Free pages ya kusa ƙarewa Book 2 akan #300 First Bank, Fatima Bello Bukar. Evidence of payment 07037487278

#vote
#comment
GOBE DA NISA
Page 11
Na Pharty BB

  Cikin sanyin muryarta mai cike da tsananin tsoro ta yi sallama tana shiga falon, shuru falon tsit duk da akwai mutane a ciki, daga Abba, Umma, Yaya Haydar, Ummi Aisha babu sauran yaran. Can idanuwanta ya hango mata Haneefa a zaune ta haɗa kai da gwuiwa da alama kuka take.
 Jikinta ne ya fara rawa, tsoro ya sake shigarta, ƙafafuwanta har rawa suke da ƙyar taja su ta nufi ɗakinsu don ta rasa ina za ta yi. Taku biyu ta yi taji mugun tsawar da ya nemi tarwatsa ƙwaƙwalwarta.
 Cak ta tsaya tana juyawa lokaci ɗaya ta durƙushe ƙasa don ba ta da ƙarfin tsayuwa.
 Haneefa wacce ta ɗago jin tsawar Abba ta rarrafa ta nufi wajen Mariya, jikinta ta faɗa tana fashewa da kuka. Kukan Haneefa ya karya zuciyar Mariya taji nata idanuwanta sun cika da kwalla, ranar da take guje musu kenan.
 Falon shuru sai tashin kukan Haneefa, Mariya kam sai sharan hawayenta take waɗannan suka samu zuba.
  Umma daga inda take ta taso ta ƙaraso wajensu, lafiyayyan mari ta sakarwa fuskar Mariya wacce ta ɗago kanta don ganin Umma tsaye a kansu. Babu shiri ta runtse idanuwanta jin zafin marin har tsakar kanta.
  Kafin kiftawa da bismilla Umma ta rufe Mariya da duka, ta ko'ina dukanta take iya ƙarfinta tamkar an aikota. Mariya tun tana ƙoƙarin kare kanta har ta kasa ta barwa Allah tana ci gaba da kukanta.
 Haneefa ma kuka take iya ƙarfinta tana rokar Umma ta rabu da Mariya. Tsakanin Ummi Aisha da Yaya Haydar babu wanda ya yi ƙoƙarin tashi ya taimaka musu, haka Abba da yake ji bai ko motsa ba.
 Sai da Umma ta yiwa Mariya lis sannan ta rabu da ita, lokacin da ƙyar take iya kukan.
 Umma tasa kafa ta haureta sannan ta ce. "Don ke shegiya ce uban naki za ki yi wa sharri? Ubanki ne fa Mariya?"

  Abba daga inda yake zaune ya tashi, ya ƙarasa gabansu ya durƙusa saman ƙafafunsa. Ido cikin ido suka kalli juna da Mariya wacce ta ɗago kanta da ƙyar ta kalle shi, ya sakar mata wani shegen murmushi da kullum ya mata yana tsinka zuciyarta kafin ya ɓata rai lokaci ɗaya.
Ita kaɗai ta lura da hakan, cikin sauri ta yi ƙasa da kanta wani hawaye yana zubo mata a kumatunta. Maganganunsa ne suka sakata ɗago kanta da sauri ta kalle shi inda yake faɗin.
"Salon aikin kuma a kai na zai fara? Sharri za ki min Mariya? Ni za ki yi wa ƙaryar lalata miki rayuwa? Don kin ga jiya ban ɗauki mataki akan abin da ya faru ba. Me yasa ba za ki same ni mu yi maganar ba? Balle ma ina da niyar yi don ɓullowa abin akan yau idan na dawo, sai kuma na iske wannan takardar tuhumar mai cike da sharri. Amma tun da hakan ki ka nema mu haɗu a court."

 Umma cikin ɓacin rai ta bar gurin tana faɗin. "Ai ko duniya za su taru babu wanda zai yarda da hakan. Wannan abin kunyar har ina? Uba da lalata ƴarsa."

  Abba daga faɗin haka ya yayyaga papers na hannunsa ya watsa a fuskar Mariya. Ya miƙe ya mata wani kallo ita da Haneefa ya ɗauke kansa ya ce.
"Na ba ku minti goma ku tattara komai naku ku bar min gida."

 Haneefa da Mariya an rasa mai magana a cikinsu, Haneefa kukanta ne ya karu yayinda Mariya take juya kalaman Abba a ranta.
Umma da take zaune kusa da Yaya Haydar wanda idanuwansa sun kasa sun yi ja, ya ma rasa ya zai fassara abun yasa bai tanka ba, ta kalle su cikin daka tsawa ta ce.
"Don uwarku ba magana ake muku ba, dangin mayu."

 Mariya idanuwanta ta runtse jin zagin da ta musu, ta miƙe ta miƙar da Haneefa tare da jan hannunta suka nufi ɗakin su. Zaunar da Haneefa ta yi saman gado, ita kuma ta miƙe ta ɗauki manyan akwati uku ta buɗe tare da fara ɗaukar kayansu tana zubawa a ciki, duk da ciwon da jikinta yake mata da kanta haka ta daure.
 Babu abin da ta bari nasu a ɗakin, ta rufe akwatinan ta miƙar, ta koma wajen Haneefa da ta daina kukan sai ajiyar zuciya take sauƙewa.
 Durƙushewa tayi a gabanta, ta kamo hannunta suna kallon juna. Mariya cikin sanyin murya cike da rauni ta ce. "Tashi muje."

 "Ina? Ina muke da shi bayan nan gidan iyayenmu." Haneefa ta faɗa cikin dashashshiyar muryarta tana neman yin wani kukan.

Miƙewa Mariya tayi ta ce. "Duk inda Allah ya nufa."
 Haneefa miƙewa tayi ta ɗauki hijab nata ta saka saman kayanta na nursing. Don dawowarta kenan ta shiga ɗaki taji hayaniya ta fito, anan ta samu Abba yana lallashin Umma wacce take ta faɗa akan abin da aka aiko mishi, ganinta yasa suka rufeta da faɗa ko tana da masaniya akan abin da Mariya tayi.
 Tuni ta fara kuka tana musu rantse rantse amma sun ƙi yarda musamman Umma, a cikin haka Abba ya ƙira Yaya Haydar ya dawo, hakan yasa sauran yaran suka watse, sai Haneefa da Ummi Aisha da ta kasa faɗin komai tana tattara

Please Login or Register in order to submit comment