Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka bar Mariya wacce sai da ta tabbatar Abba ba ya falon ta fita ta zauna, duk da ba hira zata yi ba gwara ta zauna don ɗebe kewa tana sauraron su, na murmushin tayi wanda bai mata ba ta ƙi yi.
  Ƙarfe goma da rabi kowa ya nemi makwancinsa domin cikin yaran wasu har sunyi bacci a falon.

  Da safiyar ranar lahadi bacci suka sha kamar babu gobe, musamman Mariya ita ce ƙarshen farkawa wajen ƙarfe sha biyu saura mintuna ashirin, tayi mamakin baccin da tayi, amma idan ta tuna bata kwanta da wuri ba kuma bata samun bacci kwanakin ba yasa bai dameta ba.
Tana farkawa wanka kawai tayi ta fito tasa kaya ta fita, wasu suna falo wasu kuma alama suna ɗaki. Kusa da Umma ta ƙarasa tana gaishe da ita, ta amsa mata tana cewa.
"Kinsha bacci."

  Murmushi kawai Mariya tayi ta miƙe ta wuce dining, abinci ta duba taga babu sai guntu. Kitchen ta wuce ta dafa tea ta fara sha don yunwa, kafin ta ɗaura noodles. Tana tsaye ya dahu ta kwashe ta fito falon, zama tayi a dining ta fara ci.
Ta kusa cinyewa Abba yayi sallama ya shigo falon, cak ta tsaya da cin abincin bugun zuciya ya ziyarceta.
Abba da ya hangota bayan amsa gaisuwar yaransa da ya hanya ya ƙarasa dining ɗin, kujera yaja ya zauna yana faɗin.
"Me kike ci haka yanzu? Breakfast sai ƙarfe sha biyu Mariya, ba kya tsoron ulcer?"

Da ƙyar Mariya ta girgiza kanta, murya ƙasa ƙasa ta ce.
"Ina kwana. Ya hanya?" Sai yanzu tasan ma yayi tafiya, shi yasa jiya bai kwana a gida ba har dare suka kwanta bai shigo ba.
Ruwan da ta ajiye a bottle ya ɗauka ya buɗe bottles ɗin, bai fara sha ba sai da yace. "Hanya lafiya lau."
  Sannan yasha ruwan rabi ya ajiye sauran ya tura mata gabanta.
  Mariya miƙewa tayi ɗauke da plate ɗin gabanta, ta wuce kitchen ta ajiye. Wani ruwan ta ɗauka tasha ta jefa goran a dustbing, sannan ta fito ta ƙarasa dining inda Umma ta maye gurbin inda take, guntun ruwan bottles da Abba ya ajiye ta ɗauka ta wuce ɗakinsu dashi.
Abba da kallo ya bita fuskarsa ɗauke da murmushi. Umma da take kallon su tayi murmushi ta ce.
"Jan ajin ƴarka har na gida bai bari ba."

Maganar Umma yasa ya maido da hankalinsa kanta, ya faɗaɗa murmushinsa sannan ya ce.
"Hakan ya yi, gwara tayi ta gara kan yan maza manya da yara."

  Dariya ƙasa ƙasa Umma tayi don yadda kaf yaran yafi damuwa da Mariya da lamuranta, har wasu suna nuna kishin yafi sonta, sai dai yayi murmushi domin ai duk yaransa ne bai ga abin bambamci ba, Mariya kuma so yake tana sakewa dashi tamkar sauran.
...

  Haka suka gama wunin ranar babu inda suka je. Mariya ba ta ƙara fitowa ba sai da taji wani yunwar, da ƙyar ta fito bisa matsawar Haneefa suka fito suka ci abinci sannan ta koma ɗaki.
  Da dare kam ƙin fita tayi, da taga Haneefa zata matsa mata kawai ta ɗauko file din case din Isah Hamza ta fara dubawa. Dole yasa Haneefa barinta ta fice, tana gani ta fita ta mayar ta rufe ta ajiye.
Miƙewa tayi ta gabatar da sallar isha'i, tayi shirin bacci ta haye gado ta kwanta abinta, so take bacci ya ɗauketa don samun isashshen bacci domin farkawa da wuri ta tafi aiki akan lokaci karta makara.

#vote
#comment

GOBE DA NISA
Page 6
Na Pharty BB

Da sallama ya shigo babban falon gidansu cikin shirin fita aiki kamar kullum, da mahaifiyarsa da ƙannensa mata da suke zaune ya fara cin karo, suna ganinsa suka gimtse dariyar da suke, musamman Nabeela da ita ce kan gaba na dalilin dariyar nasu da yake cike da farin ciki.
Ciki ya ƙarasa sai lokacin suka lura da wacce take bin bayansa, ita ma cikin shirin fita nata aikin take. Take fara'ar fuskarsu ta ɗauke banda na Ammi.
Kujera Waliy ya samu ya zauna, wacce suka shigo tare ta zauna a hannun kujeran da yake. Kamar kullum shi ya fara gaishe da Ammi sannan ita, duk da abin yana sosa ran Ammi haka ta amsa don karta nunawa Waliy ɓacin ranta akan Rumana. Sannan su Nabeela suka gaida su.
Rumana ce ta fara miƙewa, ta kalli Waliy tana gyara siririn gyalen kanta tace. "B zan yi latti fa, mu tafi."

Miƙewa ya yi, ya kalli Ammi da ta ɗauke idonta ya ce. "Ammi zamu wuce."

"Allah ya kiyaye ya yi jagora." Ta faɗa musu tana dawo da dubanta kansu.
Murmushi Waliy yayi da ya ƙara fitar da kamilalliyar fuskarsa mai tsorata mutum, ya juya ya fice yabi bayan Rumana da tuni ta fice.
A harabar gidan ya sameta jingine a jikin motarta, wajenta ya ƙarasa ya tsaya a gabanta. Fuskarsa a haɗe kamar ba yanzu ya gama murmushi ba. Wani kallo ya aika mata sannan ya buɗe baki ya ce.
"Wai yaushe za kiyi hankali Ruman? Zamu ɓata ina faɗa miki idan ba za ki ɗauki mahaifiyata da daraja ba."

"Me nayi B? Naga dai gaisuwa ce na gaisheta." Ta faɗa da Hausarta da ba ya fita tana kallonsa. Don ita gaskiyarta ba ta ga wani abin da tayi ba, amma shi kullum faɗarsa bata ba wa mahaifiyarsa daraja. Kuma duk safiya tana shiga ta gaisheta sai kuma washegarin da safe, ita ma yanayin aikinta baya barinta wuni a gidan sai yamma take dawowa, ta dawo kuma fta gaji.
Tsakin Waliy da barinsa wajenta yasa ta kallonsa taga ya wuce wajen motarsa. Kwafa tayi ta buɗe nata ta shiga, tana zaune zai zo ya bata haƙuri don tasan baya iya dogon fushi da ita saboda ƙaunarta da yake tun tushe.
Haka Waliy ya fice a gidan cikin jin haushin Rumana, abin nata ya fara ba shi haushi, duk da yana mata uzurin yanayin tashinta kenan babu kwaba da kuma al'adun inda ta taso.
Yasan ba don son da take mishi tun bata san kanta ba da babu abin da zai sakata baro ƴan uwanta, iyayenta ta biyo shi don aurensa da burin zama dashi.

Shi da ita ɗin yaran Yaya da ƙani ne Abubakar da Talba, wanda iyayensu su kaɗai suka haifesu. Tare suka taso su biyu, Abubakar ya riga Talba aure hakan yasa Waliy ya zamto shine babba a gidan kuma ɗa namiji kaɗai.
Haka rayuwa ta tafi har Mami ta haifi nata yaran Mimi, Ihsan da Rahma sai Rumana auta, sannan lokacin Ammi ta sake haihuwar mata ita ma Sadiya da Shukrah, Radiyya, Farah da Nabeela auta, yaran kusan sa'annu suke.
Mimi da Sadiya kansu ɗaya, Ihsan da Shukrah, Rahma da Radiyya, Farah da Rumana, sai Nabeela ita ɗaya.
A gabansa aka haifi Rumana duk da lokacin shekarunsa bakwai. Tun ranar da ya kyalla ido ya ganta ta gansa ƙaunar junansu ya shiga ransu, gida ɗaya suka taso hakan yasa suka shaku. Shekararta goma ta gama primary shi kuma secondary a lokacin mahaifin Rumana ya samu aiki a ƙasar Canada.
Nan fa aka so rabasu don Talba yace zai tafi da yaransa gaba ɗaya huɗu mata har da Rumana da ita ce ƙaramar su. Tashin hankali da Rumana da Waliy suka shiga yasa mahaifinsa Abubakar cewa a tafi da Waliy ya yi karatunsa a can, kowa yayi na'am da haka.
Haka suka tafi inda ƙarfin shaƙuwa da soyayya ta ci gaba da wanzuwa tsakanin Ruman da Waliy, har takai ya kammala karatunsa na lauyanci ya dawo ƙasarsa bautar ƙasa, anan ya tarar jinyar mahaifinsa, ga ƙannensa mata bayan Sadiya da Shukrah guda uku sun taso, Radiyya, Farah da Nabeela.
Hakan yasa ko da ya kammala bai koma ba. Jinyar ajali yasa Allah ya karɓi abunsa inda ahlin sun ji mutuwarsa, dole Talba ya zo suka yi sati biyu suka koma harda yara.
Rumana da kuka ta koma don tana son zama tare da masoyinta, shi yayi ta lallashinta don makaranta da take ya kusa karewa, sai dai ya kula ta sake shagwaɓewa da sangarta ko don har yanzu ita ce auta, kuma yanayin al'adar can ba wa yaro damar yin yadda ya so.
Bayan komawar su kullum suna cikin waya da juna, a haka ya samu aiki ya fara a court, acan kuma Rumana ta kusa kammala karatun likitanci da take. Haka Waliy ya ɗauki dawainiyar kannensa da mahaifiyarsa duk da Baba Talba yana aiko musu da kuɗaɗe da wasu abubuwan buƙata.
A haka aka aurer manya biyu Sadiya da Shukrah har da yayun Rumana da Mimi, Ihsan, saura Radiyya, Farah da Nabeela da ita ce auta, sai Rahma sa'ar Farah.
Shekara ɗaya da aurensu Sadiya suka haihu, a lokacin Rumana ta kammala karatunta ta zama likita, duk yadda iyayenta suka so tayi aiki a Canada ƙi tayi, ta birkice musu ita Nigeria zata dawo wajen Waliy don yadda ta gansa a bikinsu Sadiya tsawon shekara ta kasa mance siffarsa da kyawunsa, wanda ya ƙara mata sonsa.
Ganin haka Baba Talba yayi wa Waliy maganar aurensu, tuni ya amince don burinsu kenan. Haka aka sha biki aka kawota gidansu a part nasa wanda ita da mahaifiyarta basu so ba, amma son da take mishi ya danne.
Haka suka fara rayuwa tare da juna cikin so da ƙaunar juna, duk da Waliy yana haƙuri da wasu halayyarta na sangarci da rashin girmama na gaba da ita, don sai abin da taga dama take yi. Ya sha mata magana sai tace ita fa bata ga laifin abin da tayi ba ba.
A cikin haka ya nema mata aiki ta fara fita inda lalaci yaci gaba, don aikin gida da girki mai aiki ce take komai, babu abin da take yi sai tayi wanka ta fita aiki, ta dawo ta ci tasha, hatta wajen shimfiɗa watarana sai Waliy ya nuna mata ɓacin ransa take yarda, wai tsoron ta lalacewa take, ƙasan ranta kuma tsoron samun ciki take duk da a matsayinta na likita ta yiwa kanta garkuwar hana ɗaukar ba yanzu ba.
Ammi tana lura da duk irin zaman da suke, sai dai bata taɓa nunawa Waliy ko a fuska ba, haka ta kwaɓi yaran yiwa Rumana rashin kunya don bata ba ta girma, balle shi da babu zancen raini tsakaninsa dasu. Sai dai Ammi da yaran su haɗu su yi ta tattaunawa.
Har yau da Nabeela tana basu labarin diramar Waliy da Mariya na jiya suna dariya, sai ga Waliy da Rumana sun shigo suka katse musu.
***
A haka Waliy ya ƙarasa office da takaicin Rumana, yana shiga bai nemi kowa ba yau yaci gaba da aikinsa.
Da ƙyar ya kawar da abin da Rumana ta mishi kafin ya samu sukuni, duk da hakan yasa a ransa dole zai mata magana kuma yaci gaba da kwaɓarta don hakan ba al'adar hausa ba ce rashin girmama na gaba musamman iyaye.
...

Ɓangaren Mariya ma da nata ɓacin ran ta wuni, amma haka ta danne tayi ayyukanta musamman da Barrister Waliy ya ce yana buƙatar ɗaya wani sati, hakan yasa ta dukufa da aiki babu abin da yake ɗagata sai sallah.
Ba ta bar wajen aikin ba sai la'asar lis wajen huɗu da rabi, ji take kamar kar ta je gida ta je gidan Aunti Babie, amma babu yadda ta iya dole sai ta sanar an bata izini kafin ta tafi.
Haka ta ƙarasa gida, bayan ta biya mai napep ta shiga ciki tare da sallama. Kaɗan zuciyarta ta koma cikinta ganin motarsa a fake cikin motocin gidan, jikinta rawa ya fara da ƙyar taja ƙafafunta ta nufi falon gidan bakinta ɗauke da addu'ar da duk yazo bakinta, don ba ta shirya haɗuwar su yanzu ba.
Da sallama ƙasa ƙasa ta shiga falon, tsit tamkar anyi ruwa an ɗauke ko babu rayayyu a ciki masu numfashi don yadda ya ɗauki shuru.
Idanuwanta ta ɗago taga Baba Ƙarami da Khadeeja da Ummi Aisha suna falon, amma babu wannan hira da surutun nasu.
'Tabbas yana nan.' Zuciyarta ta faɗa mata wanda tasa ta wurga idonta saman ƙofar ɗakinsa amma wayam, ta juya zuwa dining da sauri.
Cak numfashinta ya nemi tsayawa, taji ƙafafunta sun ka sa ɗaukarta, ta durƙushe daga bakin ƙofar tana sunkuyar da kanta ƙasa zuciyarta tana cigaba da bugawa
Cikin rawar muryar tsoro ta ce.
"Yaya ina wuni? Sannu da dawowa."

Tamkar Allah bai ajiye ruwan halittar a wajen ba, haka bai ɗago ba balle ya amsa mata, sai ma ci gaba da cin abincinsa ya yi hankali kwance.
Ita fa duk miskilancinta ba ta da masifa, amma shi ya haɗa dukka biyu, ga mugunta da baƙin zuciya.
Mariya tun tana sa ran zai amsa mata harta haƙura ta miƙe da ƙyar don ta gaji da durƙushen, ga fitsari take ji.
Ganin bai ko kalleta ba, bai amsa mata ba kamar kullum yasa cikin sanɗa ta nufi ɗakinsu, takunta biyar taji tsawar da kaɗan ta saki fitsari a jikinta.

"Kina ƙara taku sai na karyaki a gidan nan." Ya faɗa cikin tsawar da ya tsorata Mariya, hatta su Ummi Aisha da tsoransa ya sake shigarsu, tamkar wanda aka ƙarawa masa masifa a ƙasar da yaje ya dawo.
Tun safe da ya bayyana a gidan kowa ya shiga hankalinsa fiye da daa. Ba ya wasa ba ya ɗaukar raini.
Mariya durƙushewa ƙasa tayi a inda take, hawaye ya taru a idanuwanta sai dai ta hanasu zuba, sai matse cinya take.
Tana tsoron faɗa da duk wani tashin hankali musamman na Yaya Haydar wanda yake yiwa kowa a gidan, musamman ita da take ganin ya tsaneta ne sosai.
Yaya Haydar bai ɗago ba balle kallon inda Mariya take, haka ya gama cin abincinsa ya miƙe ya nufi ƙofar falo, har ya kama handle zai fita yaran suna murna har Mariya sai kuma suka ga ya fasa ya dawo baya.
Bai tsaya ko'ina ba sai saman kan Mariya, kallon daƙiƙa ya mata kafin ya taɓe baki ya juya yabar wajen, wai mitsitsiyar yarinyar nan har ta kai ta karanci lauya bayan shegen tsoro da miskilanci da yake cikinta, a hakan za ta fito gaban kotu a fafata da ita, asarar kuɗi dai. Haka ya fita a falon gaba ɗaya.
Kusan kowanne su sai da ya sauƙe numfashi, musamman Mariya da ta ɗauka bugunta zai yi kamar yadda ya saba lokacin da ya tsaya a kanta.
Cikin sauri ta miƙe ta faɗa ɗakin su, kayan hannunta ta ajiye a saman gado ta wuce bathroom da sauri, fitsari tayi ta ɗaura alwala ta fito jin ana ƙiraye ƙirayen sallar magriba.
Sallah ta gabatar, bayan ta idar ta sake komawa bathroom ta watsa ruwa, ta fito ta canza kayanta ta haye gado ta kwanta, tunanin abin da ya faru ya dawo mata.
Tuna haka gaba ɗaya taji jikinta yayi sanyi, har take jin anya yadda Yaya Haydar yake zai iya barinta cikar burinta. Ya tsaneta zai iya warzaga mata dukkan plans nata musamman a matsayinsa na babban lauya da ya fita sanin kan aikinsa, ya karantu sosai.
Siraran hawaye ne suka zubo mata a saman kyakkyawar fuskarta, tasa hannu ta share tare da miƙa dukkanin lamuranta ga Allah. Tasan shi ne ya bata tsawon rai da damar zama Barrister don cikar burinta, tasan Allah zai bata mafita.
Haka ta zauna a ɗaki duk yunwar da take ji, duk da tana jin hayaniyar yara da ya ba ta tabbacin Yaya Haydar baya falon amma tsoronfita take.
Ana yin sallar isha'i ta miƙe ta gabatar ta haye gado ta kwanta. Tun tana ji motsi da hayaniyarsu har bacci ya ɗauketa.

A can falo suma yaran suna gama yin abin da zasu yi suka shige ɗakunan su gudun yayan nasu ya dawo ya same su ya lallasa su. Umma da Abba kam dariya suke musu don yadda suke tsoransa ko su basa tsoro.

Da safiyar gaba ɗaya ahlin da ƙyar suka yarda suka haɗu a dining don breakfast da Abba yasa Umma ta shirya yau, ciki har da Mariya da take jin kanta a mutuƙar takure. Ita da zasu barta da ko breakfast ɗin ba zata yi ba za ta tafi, amma Abba ya tsiri yi kamar da haka ake yi.
Ɓangaren sauran yaranma haka ne, kamar su yi ihu da wannan abun.
Basu ƙara tsorata ba sai da sallamar Yaya Haydar ya ratsa dodon kunnuwansu, cikin muryarsa mai firgitasu da fitarsu a hayyaci.
Mariya tuni ta nemi guntun nutsuwarta ta rasa, zuciyarta ta fara bugawa da sauri.
Har rige rigen amsa mishi sallamar suke da gaisar dashi, ciki har da Mariy. Amma kai kawai ya ɗaga musu yaja kujeran kusa da Abba ya zauna wanda gefe ɗaya Mariya ce a zaune. Suma ne kawai ba ta yi ba lokacin, jikinta ya hau rawa.
Muryar Abba ta ji ya daki dodon kunnenta da ya ƙara firgitata ya ce.
"Mariya zuba mana abinci."

Kallon shi tayi da sauri, ta ga shi ma ita yake kallo da murmushi ɗauke saman fuskarsa, babu shiri ta kawar idanuwanta don yadda ya haddasa mata ci gaba da bugun zuciya.

Yanzu aka soma wasan.

#comment
#vote
[06/06, 7:28 pm] Pharty BB: GOBE DA NISA
Page 5
Na Pharty BB

Mariya ɗauke manyan idanuwanta ta yi a cikin na Barrister Waliy da ya kallota. Zuwanta court yau Litinin ta samu labarin za ayi zaman shari'a, hakan yasa ta nufi inda ake yi.
  Turus ta tsaya a bakin ƙofa ganin Barrister Waliy cikin kayan barristers, saman coat ɗin jikinsa ruwan toka. Kayan sun mishi kyau sosai, yana zauna shi ɗaya gabansa computer da alamu har da shi za a fafata a shari'ar da za a gudanar.
  Ƙoƙarin neman wajen zama ta fara a gefe. Ta ji an dafata, ta ɗago da sauri ta ga wata budurwa ce da kayan gida.
   Fuskar budurwar ɗauke da murmushi ta ce. "Brother yana miki magana."

  Mariya hannun budurwar tabi da kallo inda take nuna mata, karaf suka haɗa ido da Barrister Waliy, ta yi azamar ɗauke idonta ta kalla budurwar, idan idanuwanta basu yi ƙarya ba kamanni ta ga suna yi da shi.
  Kasa magana tayi ta juya ta nufi wajensa jiki a sanyaye da bata san na menene ne ba, budurwa ta bita da kallo tana murmushi cikin ranta tana faɗin. 'Allah yasa halin ba ɗaya ba, don na hango ita ma miskilar kanta ce."
Wani murmushin tayi mai kama da na mugunta tana cije lips ɗinta, idan da hakan zai kasance tasan ahlinsu zasu fi kowa murna, ko don cikar burinsu da suka daɗe suna neman yi.
...

  Mariya tsayawa tayi gefe da shi kaɗan bayan isarta wajensa, murya ƙasa tace. "Ina kwana sir."
Kujeran gefen sa ya nuna mata bai ɗago ba daga abin da yake yi.
"Zauna." Ya ba ta umarni.
  Babu musu ta zauna inda hakan ƙara musu kusanci ya yi, kujerun don daf da juna da suke, hakan yasa taji ta takura sosai, ga ƙamshin turarensa ya danne nata sosai.
  Barrister Waliy ma hakan ya ji, sai dai ya fuske ko ba komai akwai idon jama'a musamman na ƙanwarsa Nabeela da idan dai zai yi zaman shari'a sai ta halarta, don ita ma burinta kenan ta zama Barrister.
Kuma dole Mariya ta kasance tana kusa dashi don ita ce ta ƙarasa binciken shari'ar, hakan yasa da yaga shigowarta da kallon da ta mishi ta wuce don neman gurin zama ya ƙira Nabeela ta turota.
Barin abin da yake yi ya yi ya ce.
"Miƙo min file ɗin can."

Mariya wacce tasan da ita yake ta gyara ta ɗauka ta ajiye mishi a gabansa, ya buɗe ya sake bi ya tura gabanta.
"Ki sake dubawa domin yanzu za ayi zaman shari'ar."

  Babu musu Mariya ta buɗe ta fara dubawa, yadda ta ba shi har yanzu yana haka, hakan yasa taji daɗi ya ratsata ganin bai canza komai ba.
Shigowar alkali yasa kowa ya nutsu aka miƙe aka ce. "Court."
Bayan alkali ya zauna sannan suka zauna, alkali ya nemi sanin me ake tafe dashi yau na shari'a. Regista ya miƙe ya gabatar, alkali ya nemi mai ƙara da mai laifi, tsoho ɗan shekatu saba'in ya fito ya shiga cikin doc, sannan yarinyar da take ƙarar tsoho ta fito da cikinta da har ya fito sosai.
Lauyan mai kare mai laifi ya miƙe ya gabatar da kansa tare da mataimakinsa, haka Barrister Waliy ma ya gabatar da kansa a matsayinsa na lauyan mai ƙara, bayan ya zauna Mariya ta miƙe cikin faɗuwar gaba ta gabatar da kanta a matsayinta na mai taimakawa Barrister Waliy sannan ta zauna. Gaba ɗaya a tsorace take wai yau ita ce gaban court, abin da ta jima da mafarkin gani.
  Barrister Waliy ne ya fara miƙewa ya fara gabatar da shari'ar da duk abin da ya shafe shi, sannan ya fara watsa musu tambayoyin da Mariya ta rubuta dukkan su tsoho da yarinyar.
Bawan Allah duk ya rikice da tambayoyin Barrister Waliy, hakan yasa yayi ta sakin zance har magana ta tabbata cewa aikinsa kenan a unguwa, neman ƙananan yara musamman zawarawa, bayan haka ga shaidu da Barrister Waliy ya gabatar na ƴan unguwa da suka jima da zargin hakan.
Lauyan mai kare tsoho sai ya tashi zai yi magana sai alkali ya hana don magana ta riga ta tabbata, tsoho ya karɓi laifinsa da cikinsa. Hakan yasa take alkali yanke mishi hukucin riƙeta da ciyar da ita na tsawon har ta haihu, kuma ya ci gaba da ciyar da abin da ta haifa, idan yayi wayo ya karɓi abinsa.
  Sannan ita ma da laifinta da ta biye mishi ga abin kunyar da ta samu, sannan ba shi da hukuncin fyaɗe don da yardarta ya nemeta har ta samu cikin.
Haka aka watse tsoho kunya kamar ya nutse ƙasa ganin yau dai Allah ya toni asirinsa, iyayen yarinya da yarinya sun ji taƙaici da kunya saboda akwai laifin ƴarsu, amma ko ba komai sun ji daɗin hukuncin da aka yanke mishi, kuma sun tona asirinsa ko ire-irensa tsofin banza zasu hankaltu.
Bayan gama shari'ar aka watse kaf a gurin amma Barrister Waliy ba shi da niyar tashi, hakan yasa Mariya ƙoƙarin tashi amma ya dakatar da ita ta hanyar mata tambaya.
"Na gama dake?"

Ba tayi magana ba ta koma ta zauna, a ranta tana mamakin wannan halinsa na nuna isa da gadara.
Kamar daga sama ta ji ya nemi sanin sunanta, sai da taja lokaci har ya ɗago ya kalleta don yasan ta ji amma ta basar sannan ta ce.
"Mariyatul Kibdiyya Harun."

  Bai ce komai ba ya ci gaba da abin da yake. Sallamar Nabeela ya katse shurun su, tabi su da kallo zuciyarta tana hasko mata wani abu daban, cikin murmushi ta ce.
"Yaya zan koma gida."

"Da ni na kawoki?"
Ya faɗa yana ɗagowa ya watsa mata wani kallo, sannan ya miƙe yana faɗin. "Biyo ni da kayana office."

  Daga haka ya fice, Nabeela da Mariya suka bi shi da kallo. Nabeela ta ɗauke idanuwanta ta kalla Mariya ta ce.
"Sai haƙuri, haka yayan nawa yake. Kinyi ƙoƙari sosai da kika samu gurbi wajen shi."

Murmushi kawai Mariya tayi da ya fito da dimples ɗinta, ta miƙe ta ɗauki handbag ɗinta ta fara ƙoƙarin barin wajen. Nabeela da sauri ta tareta ta ce. "Kayan nashi fa?"

Sai lokacin Mariya ta buɗe baki ta mata magana bayan ta dakata da tafiyar."Ina ke yake nufi."

Da sauri Nabeela ta girgiza kanta, ta taɓe baki tace. "Ni? Ba kowa yake bari ya shiga mishi office ba, duk son zuwana iyakata court. Ɗauki ki kai kafin kiyi wani laifi."

  Mariya wani abu taji ya maƙale mata a maƙoshi ta haɗiye yawu da ƙyar, ta koma ta kwashe komai ta juya ta fita.
Nabeela ta bita da murmushi a ranta tana faɗin. 'Dole sisters su samu rahoto, har Ammi ma."
...

Mariya tana fita office ɗinsa ta nufa, duk kallon da ɗaiɗaiku da suke haɗuwa a hanya suke mata hakan bai sa ta damu ba, hasalima bata san suna yi ba, a haka ta ƙarasa office ɗinsa.
Ƙwanƙwasa ƙofa ta yi ya bata izinin shiga, ta shiga da sallama ta ƙarasa bakin table ɗinsa ta ajiye mishi, ta fara ƙoƙarin barin wajen.
  Ganin haka Barrister Waliy dakatar da ita ta hanyar faɗin. "Ke kinfi ƙarfin saka suit ne?"

Cak Mariya ta dakata jin maganarsa cikin dodon kunnenta cikin muryarsa mai sauƙar mata da tsoro.
Juyawa tayi a hankali kanta a ƙasa, murya a ɗan tsorace ta ce.
"Sorry sir, zan takura..."

Katseta yayi cikin muryar nan nasa ta hanyar faɗin. "Kin gama duba waɗannan case ɗin?"

Girgiza kai Mariya tayi, cikin rawar murya ta ce. "Saura kaɗan."

"Kafin next week ina buƙatar ɗaya. You can go." Ya faɗa yana miƙewa, ya buɗe wani ƙofa alamar bathroom ne ya shige ya barta tsaye.
Da ƙyar Mariya taja ƙafafuwanta tabar office ɗin, da tunanin ta ya za ta saka suit haka ta ƙarasa office ɗinsu, sai

Please Login or Register in order to submit comment