Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

dukkan abubuwan da suke faruwa a ƙwaƙwalwarta zuwa waje ɗaya.
 Haka suka fito janye da akwatinan su, har lokacin suna falo a zaune Umma sai maimaita zance take, Abba yana faɗi ta kwantar da hankalinta su da suke da Yaya Haydar, balle ma ƙarya ne kowa ya sani.
 Mariya da Haneefa babu wacce ta kalle su, suka ja akwatinan su suka fita a falon. A haka suka fita a gidan da suka taso, gidan iyayensu da suka basu dukkan gata da kulawa tsawon shekaru.
Suna janye da akwatunan su babu wacce tayi magana haka suka isa bakin titi, Mariya ce ta tara musu napep suka shiga. Bayan yaja ta sanar masa inda zai kaisu.
Haneefa dai bata ce komai ba har lokacin, ta jefa zuciyarta cikin tunani abubuwada dam.
 Har ƙofa ya ajiye su, suka sauƙa Mariya ta cire kuɗinsa ta ba shi yaja napep ɗinsa.
Haneefa tana kallon Mariya ta ce. "A tunanina gidan Aunti Yahanasu zamu je."

 Girgiza kai Mariya ta yi taja akwatinan hannunta zuwa ƙofar gida, ta ƙwanƙwasa get.
Haneefa ma ta jawo na wajenta ta ƙaraso lokacin an buɗewa Mariya kofa ta shiga, ita ma kawai ta bi bayanta.
Basu tsaya a ko'ina ba sai cikin falo suka shiga da sallama, babu kowa falon sai Zakiyyah. Cikin murna ta miƙe ta taresu sai dai turus ta tsaya ganin yanayin su ga manyan akwatuna tare dasu.
Mariya kanta ta ɗauke ganin kallon tuhuma da tambaya da take binta dashi, ta ƙarasa cikin falo ta zauna saman kujera.
Zakiyyah ganin haka ta bar wajen Haneefa da sauri ta nufi kitchen wajen Aunti Babie don ƙiranta.
Haneefa ita ma ƙarasawa tayi ta zauna tana sauƙe mugun numfashi.
 Cikin sauri Aunti Babie ta fito a kitchen ɗinta, bayanta Zakiyyah da ta sanar mata zuwan su Mariya da yadda ta gansu. Kujeran kusa da Haneefa ta zauna ta kallesu ɗaya bayan ɗaya ba ta ce komai ba.
 Mariya a hankali ta gaishe da ita, haka Haneefa ma. Da ƙyar ta amsa tana sauƙe numfashi sannan ta kalli Zakiyyah ta ce.
"Ki kai su ɗakinki su kimtsa jikinsu."

 Mariya ta ji daɗin rashin tambayoyi da Aunti Babie ba ta mata ba, don gaba ɗaya ta gaji da magana.
Haka ta miƙe ta nufi ɗakin Zakiyyah, Haneefa da Zakiyyah suma suka miƙe suka bi bayanta.
 Bayan shigarta akwatin hannunta ta ajiye ta faɗa bathroom don tana buƙatar wanka, shi ta yi tana juya abin da ba ta yi zaton faruwarsa a yau ba ya faru ba.
Bayan ta gama ta fito Haneefa ta shiga, Zakiyyah tana jera musu kayansu a gefen nata cikin wardrobe ɗinta duk da babu girma.
 Mariya riga da wando ta ɗauka ta saka wanda bai kamata ba kuma rigar har guiwarta. Bayan ta gama ta shafa turare kawai lokacin Haneefa ta fito, ita ma riga dogo ta saka simple.
Zakiyyah kallon su tayi ganin sun gama, ita ma ta kammala jerawa lokacin ta ce. "Muje ku ci abinci."

"Magriba ta kusa fa."
Haneefa ta faɗa daga zaunen da take, duk yunwar da take ji babu shi.

"Haka ne" Zakiyyah ta faɗa tana miƙewa ta fita.
 Shuru suka zauna har Zakiyyah ta dawo da ruwa a gora ta zuba musu a cup ta basu, babu musu suka karɓa suka sha, ta ɗauki cup ɗin ta fitar.
 Sai da suka gabatar da sallar magriba har Zakiyyah wacce ta dawo ɗakin, bayan sun idar suka miƙe suka fita. A dining suka ga Aunti Babie da mijinta Dady tare da kannen Zakiyya mata biyu da namiji ɗaya.
Ƙarasawa suka yi suka gaishe da shi, ya amsa cikin farin cikin sanin matsayin su wajen matarsa, haka sauran yaranma suka gaishe dasu suka amsa sannan suka zauna.
Zakiyyah ba ta zauna ba ta zubawa kowacce abinci ta ajiye a gabansu sannan ta zauna. A hankali suka fara ci, sai dai duk ƙoƙarinsu su ci mai yawa sun kasa, kowacce da damuwa a cikin ranta.
 Aunti Babie duk tana lura dasu, sai dai ba ta musu magana ba saboda idon yara da mijinta.
 Ɗaya bayan ɗaya kowa ya gama suka miƙe suka bar dining, haka Mariya da Haneefa ma.
 Mariya ɗaki ta wuce ta yi kwanciyarta don ta gaji sosai, Zakiyyah da Haneefa suka zauna a falo tare da sauran yara, Aunti Babie da mijinta suka wuce falonsa.
 Har dare ya shiga suka kwanta babu wanda ya tambayi dalilin zuwan su Mariya, hakan ya yiwa Mariya daɗi ban da Haneefa wacce taso Mariya ta yi wani maganar, amma tasan ta matsa mata da tambaya dole ya zama amsar eh ko a'a.
...

 Ƙarfe goma da mintuna biyar a gidan Barrister Waliy. Zaune suke shi da Rumana a falon su, gaba ɗaya shi kam hankalinsa yana kan Mariya akan ya ta samu mutanen gidan su? Me suka mata? Musamman Barrister Aliyu Haydar wanda sam basa shiri kowanne yana ji da miskilancinsa da kasaita, yasan dole zai matsa mata da tambayoyi da furzarwa, inda yake fatan Mariya ta ji maganganunsa kar ta faɗi komai, kuma tayi amfani da iliminta kar ta ba shi damar satar amsa ko ɗaya.
 Motsin Rumana ya dawo da shi hankalinsa ya kalleta, murmushin ƙarfin hali ya mata ya shafa fuskarta. "Ya aka yi My R?"

Ɓata fuska ta yi tana faɗin. "Mene ne damuwarka My B? Na kula fa tun da ka dawo ba ka da walwala."

Rankwafowa yayi ya sumbaci leɓbenta, ƙasa ƙasa ya ce.
"Ke ce matsalata. Ruman tsawon lokaci fa ba ayi ba, ke babu ruwanki idan bani na nemeki ba. Kuma fa naga kina jin daɗi sosai idan ana yi."

Dariya ta yi ta rufe fuskarta jin abin da ya faɗa a ƙarshe, duk ƙi da take yi ba wai don ba ta jin daɗin tarayya da shi bane, ita tsoro take ta samu ciki ta ragwabe ya yi baya da ita ya hango wata, duk da tasan yayantan ita ɗaya ce a zuciyarsa tun yarinta har yanzu.
Tana cikin tunani ta ji anyi sama da ita, ido ta buɗe da sauri taga Waliy ne. Ɗakinsa ya nufa da ita ya ajiye kan gado ya bita yana kissing ɗin bakinta, mutsu mutsu ta fara ya hanata ya fara aikata mata sakwanninsa, a hankali ya rabata da kayan jikinta cikin salo ya hau sarrafata.
Duk dabarar Rumana haka Waliy ya hanata dukkan motsi, yabi da ita ya sama musu nutsuwa sosai yw gushar da abin da yake ji. Rumgumeta yayi suna sauƙe numfashi, sun jima a haka har baccin gajiya ya kwashi Rumana don ta gurzu wajensa, dama idan ya kamata sai ya biya dukkan bashin da yake binta.
Shi kam miƙewa ya yi ya shiga bathroom ya tsarkake jikinsa ya fito, ɗagata ya yi a gadon ya ɗaurata a sofa, ya canza musu zanin gadon sannan ya mayar wani, ya ɗauketa ya mayar kan gado shi ma ya kwana a gefenta.
 Maimakon bacci ya ɗauke sa nan tunani ya ce salamu alaikum. Shi har mamakin kansa yake akan yadda ya damu da lamarin Mariya, dole ya jingina hakan da ta yarda da shi ne har ta nemi ya taimaka mata ya, ga tausayinta
....

  Washegari

 Ƙarfe takwas Mariya da Haneefa suka bar gida har lokacin babu wanda ya tambaye su dalilin zuwan su, kuma su ma basu faɗa ba har Haneefa don ita ma jiran ƙarin haske take daga Mariya.
  Tare da Zakiyyah suka fita wacce ita ma saura mata watanni ta kammala service ɗinta. Kowacce wajen aikinta ta wuce.
 Mariya tana sauƙa a napep ta wuce ciki cikin sauri ganin ta makara sosai, zuciyarta ce ta buga ganin motar Yaya Haydar a parke, kuma ba ta tantama kamar a kunne.
 Ɗauke kanta ta yi ta ci gaba da tafiya ta dosa inda zai sadata da office ɗinsu. Ba ta lura ba kaɗan su yi gwara taja baya tana faɗin."Sorry."

 "Kina kula, ko duk damuwa ce?"
Barrister Waliy ya faɗa yana binta da kallo.

Jin muryarsa yasa Mariya ɗago kanta da sauri, suka haɗa ido ta ɗauke nata da sauri.
Girgiza kai ta yi ta ce. "A'a, ina kwana."

Numfashi ya furzar sannan ya amsa.
"Lafiya lau. Biyo ni."
Ya faɗa yana juyawa ya fara tafiya, babu musu Mariya ta bishi da sauri don jin mene ne.
...

 Yaya Haydar yana zaune a motarsa yana hangosu, zuciyarsa kamar ta faso kirjinsa tsabar zafi, wani haushin yarinyar da Barrister Waliy ya rufe shi.
Tabbas akwai abin da suke shiryawa kullum suna tare, ya lura kamar sun kulla alaka a tsakanin su.
Murmushin gefen baki ya yi da yasa dimples ɗinsa na gefen lotsawa, shi kuwa zai basu mamaki haka ya ɗaukarwa kansa alƙawari.
...

Whatspp paid group #300
First bank
Fatima Bello Bukar
Evidence of payment 07037487278

#vote
#comment 
GOBE DA NISA
Page 12
Na Pharty BB
Last Free Page

WhatsApp paid group
#300 2028167156
First bank Fatima Bello Bukar 
Evidence of payment
http://wa.me//+2347037487278


Shuru da Barrister Waliy ya yi ya fara takurawa Mariya, ga ƙamshin turarensa duk ya cikata tamkar babu nata a gurin, gare shi ma hakan ne ba ta sani ba amma ya basar.
 Yana sunkuye yana ta rubuce-rubuce a file sabo, wanda bayan shigarsu office ɗinsa ya ɗauko ya fara yi.
 Tsawon mintuna goma ya gama ya ɗago, ya kalla Mariya da take zaune a ɗaya daga cikin kujerun office ɗin, kanta a ƙasa tana wasa da zoben yatsarta.
 Sunanta ya ƙira a hankali sannan ya ci gaba da faɗin. "Akan case naki ne, yau da safe na samu ƙira daga court ta bamu ranar zama sati biyu mai zuwa. Don haka zamu fara haɗa dukkan shaidu, so ina buƙatar waɗanda kike dasu domin tattara bayanai da ɓullowa shari'ar."

 Kai Mariya ta jinjina cike da farin ciki, cikin sanyin muryarta ta ce.
"To Allah ya kaimu. Sai dai babban shaidata yana gidanmu kuma mun bar gidan jiya sun koremu, tashin hankali da muke ciki yasa na manta dashi."

 "What? Kuna ina? Ke da wa?" Barrister Waliy ya jera mata tambayoyi cikin sauri, cike da mamakin ta ya iyaye zasu kori yaransu a gida, don kawai an kama su da wani laifin daban bai kamata su aikata musu hakan ba.

 Mariya cikin raunin murya na neman yin kuka ta ce. "Ni da ƴar uwata my twins sister, muna gidan Auntinmu ƙanwar mahaifiyarmu."

 Dafe kai Barrister Waliy ya yi, mamaki yake wannan wani irin iyaye ne suka samu. Ya jima a haka ya ɗago ya kalla Mariya wacce ta gama share hawayenta.
 Cikin kwantar murya ya fara ce mata. "Kin ga ki daina zubar da hawayenki, Allah zai kawo muku mafita balle ma in sha Allah ina tare daku. Maganar shaida kuma dole ki ɗauko, amma ta ya? Kina ganin ba zasu koraki ba idan kika koma?"

 Shuru Mariya tayi don ba ta da masaniya, duk gidan babu wanda ta yarda dashi shi yasa tsawon shekaru ta ɓoye inda babu mai gani ko da Haneefa ce.
 "Magana nake miki?" Barrister Waliy ya faɗa ganin ta faɗa tunani.

Kallon shi tayi sau ɗaya ta sunkuyar kanta ganin shi ma ita yake kallo, a hankali ta ce. "Gaskiya sai dai da sassafe kamar ƙarfe shida, lokacin duk suna baccin safe."

 "Gobe kina da free?" Ya tambayeta yana miƙa mata wayarsa ya ci gaba da faɗin. "Saka min contact naki."

 Babu musu ta karɓi hadaddiyar wayarsa ta saka mishi lambarta, tasan babu abin da zai yi da shi sai don taimaka mata. 
 Bayan ta saka ta miƙa masa, ya karɓa yana saving ya ce. "Shike nan ki koma bakin aikinki, sai mun yi magana."

 "Na gode sosai."
Mariya ta faɗa tana tashi, daga haka ta juya ta fita. 
 Tana fita office ɗinsu ta wuce ta shiga ta zauna bayan ta musu sallama. Ƙoƙarin kunna computer na gabanta ta fara ta ji ƴar gefenta ta ce. "Barrister Aliyu Haydar yana nemanki."

 A mutuƙar razane Mariya ta kalleta, ita kuwa ta ɗauke kanta cike da jin haushin Mariya da ya fara kamata, ba ita kaɗai ba hatta ƴan gurin ganin baristoci biyun masu ji da miskilancin da kwazo tana neman shige musu, musamman na yau da Barrister Aliyu Haydar ya ƙira a turo mishi Mariya, mutumin da baya ɗaukar raini ga shegen girman kai, wani lokaci har gwara Barrister Waliy akansa.
 Mariya wacce tana cikin tunanin me ƙiran Yaya Haydar yake nufi a gareta sam ba ta san suna yi ba, tasan ƙiran Yaya Haydar gareta mugunta ce ko neman tarwatsa mata shirinta, ko ya tsoratata ta janye niyarta. 
 Tuna haka yasa ta ji idan dai haka ne ba zata je ba, tana da Barrister Waliy zai tsaya mata ya taimaka mata ba zata sake haɗa ko hanya da Yaya Haydar ba, har ya samu damar mata wani muguntar.
 Haka ta zauna ta fara aikinta duk da ta ka sa cire tunanin kar Yaya Haydar kar ya zo ya sameta, amma har azahar ta yi suka fita zuwa masallaci shuru. 
 A nan ta ga babu motarsa ma alama ya fita, hakan yasa taji nutsuwa. Bayan sun yi sallah suka nufi cafeteria suka ci abinci, sannan suka koma office. 
 Har ƙarfe huɗu ta yi suka tashi ba ta sake ganin alamar Yaya Haydar ba, haka ta fita ta wuce gida. 
Bayan isarta ta samu Zakiyyah ta dawo ban da Haneefa. Ta gaishe da Aunti Babie ta wuce ɗaki, wanka ta yi ta gabatar sallar la'asar ta fito.
 Dining ta nufa ta zuba abinci taci cikin nutsuwa, bayan ta kammala anan ta zauna ganin yara a falo da Zakiyyah suna kallon wani film mai daɗi da ya ɗauki hankalin su, ita ma kallon ta fara. 
 Ƙiran sallar magriba ne ya miƙar dasu ba a gama ba, suka gabatar suka dawo suka ci gaba. Har ƙarfe bakwai da rabi sannan aka kammala, sai lokacin kowa ya nemi abincin dare banda Mariya da ta ɗauki fresh milk tasha mai sanyi, daga nan ta wuce ɗaki ta kwanta.
 Tana kwance tana sakawa da warwarewa har aka ƙira isha'i ta miƙe tayi ta sake komawa ta kwanta, a haka bacci ya ɗauketa ba ta san lokacin da Zakiyyah ta shigo ba.
 Ƙarfe biyun dare da minti goma Mariya ta farka a mutuƙar gigice, tare da faɗin. "Bana so don Allah ka bari."

 Zakiyyah maganganun Mariya da firgitar da take ya farkar da ita, ta riƙota tana faɗin. "Mafarki ne Mariya."

 Sai lokacin ta ji nutsuwa ta rumgume Zakiyyah tsam tana sauƙe numfashi kamar wacce tayi gudu, ita kanta Zakiyyah ta tsorata da yanayi Mariya, ta san ba ƙaramin mafarki ba ne yake farkar da mutum a bacci har yana surutu haka ba. 
 Mariya a jikin Zakiyyah wani bacci ya ɗauketa, jin haka Zakiyyah ta gyara mata kwanciya ita ma ta kwanta, da ƙyar wani baccin ya ɗauketa. 
 Ƙarfe biyar na asuba suka farka shi ma ƙarar wayar Mariya ne ya farkar dasu. Da ƙyar ta jawo ta ɗauka ta gani, ba ta san numbern ba ga ƙiran asuba, har zai yanke ta tuna da maganar da suka yi da Barrister Waliy, hakan yasa ta ɗauka da sauri tana kafawa a kunne.
 Tana ji daga ɓangaren sa ya yi mata sallama yana faɗin. "Kin yi sallah ma? Ko you're off."

"Um um. Yanzu zan yi." Ta faɗa bayan ta amsa sallamarsa, cike da jin nauyin faɗa mishi ba ta yi sallah ba duk da har yanzu akwai masallatai da suke.
 Maganarsa taji yana faɗin. "Na ba ki 10mins ki kammala. Kafin nan turo min address na gidan da kike."

"To sir." Faɗin Mariya tana cire wayarta ta kashe, da sauri ta shiga bathroom ta ɗaura alwala ta fito. Zakiyyah kuma ta koma bacci don ba ta sallah. 
 Mariya kafin ta fara gabatar da sallah sai da ta ɗauki wayarta ta tura mishi address ɗinta kamar yadda ya buƙata, sannan ta fara sallah.
 Tana idarwa ta miƙe ta ɗauki wayarta ta fice a ɗaki, tararwa tayi falo babu kowa, cikin sanɗa ta buɗe ƙofar ta fice fit. Haka get ma ta samu a buɗe don daga dawowa sallah mai gadi bai rufe ba dama ba ya rufewa, hakan ya ba ta damar fita.
 Tafe take garin har yanzu da ɗan duhu, sauri take zabgawa tare da addu'ar Allah yasa ta samu napep masu fitowar asuba.
 Haskata aka yi ta gaban hanya, tasa hannu ta kare fuskarta tana matsawa gefe. Motar a hankali ta taho har ta tsaya gaban Mariya, kallon mai motar tayi mamaki ya bayyana a fuskarta ganin Barrister Waliy, wanda hasken alfijir ya ba ta damar kallo. Sam ba ta yi tunanin zai zo bane yasa ta tura mishi address ɗinta. 
 Barrister Waliy ɗauke kansa ya yi daga kallon da Mariya take mishi yau na kurilla, manyan idanuwanta da basa kallonsa sosai yaji sun hanashi kallonta da kyau.
"Zagayo ki shigo rana tana yi." Ya faɗa a hankali. 

 Sai lokacin Mariya ta ankara, ta ɗauke idanuwanta tana sauƙe numfashi. A hankali ta zagaya ta buɗe ta shiga, shi ko ya yi riverse suka bar unguwar. 
 Tafe suke shuru har lokacin ba a fara fitowa ba, sai matafiya nesa da ɗaiɗaikun napep, a haka har suka isa gidansu Mariya, yayi fakin a gefe kaɗan. 
 Kallonta ya yi wacce ta zubawa ƙofar gidansu ido, yasan akwai zafi da ciwo iyayenka su koreka a gida, amma ya ta iya? Nata ƙaddarar kenan.
 Numfawa ya yi a hankali sannan ya ce."Ki yi sauri ki shiga ki fito."

 Mariya ba ta iya magana ba a hankali ta buɗe motarsa ta fita, ta nufi gidan zuciyarta cike da addu'o'i. Tana isa get ɗin a hankali ta tura ƙofar ya buɗe, tasan mai gadi yana bari a buɗe. Hakan ya ba ta damar shiga ta shige cikin gidan, babu motar Abba sai na Yaya Haydar. 
 Cikin sanɗa ta nufi falon gidan, a bakin ƙofa ta tsaya ta kama handle ɗin ƙofa ta tura a hankali tana saka kanta. Falon shuru babu kowa alamar duk suna ɗaki, ajiyar zuciya ta sauƙe ta ƙarasa shiga ciki, ba ta tsaya dube-dube ba ta nufi ɗakinsu da sauri.
 Ummi Aisha ta samu tana ta bacci, a hankali ta taka har zuwa inda bedside drower yake, ta jawo ta buɗe tare da tura hannunta ciki sosai ta ƙasa don ba irin mai cirewa ba ne. Nan taci karo da folder da take ajiyewa shekara da shekaru, ta jawo ta ɗauka tana mayar drawer.
 Miƙewa tayi a hankali ta fice a ɗakin zuwa falo, har lokacin babu kowa sai dai wutar falon a kunne, motsi ta ji a kitchen. Jin haka ya haddasa mata tsoro, cikin sauri ta fice har da ɗan ƙarawa da gudu, haka ta fice a gidan tare da ƙarasawa wajen motar Waliy ta shiga. Motar a kunne hakan yasa yaja suna barin wajen cikin sauri. 
 Yaya Haydar jin motsi a falo da ƙarar buɗe ƙofa yasa ya fito a kitchen, sai dai wayam babu kowa. Har zai koma ya ka sa zuciyarsa ta ka sa aminta cewa wani bai shigo ba, haka ya juya ya fita har zuwa get ya buɗe, amma sam babu alamar kowa, hasalima layin shuru. Haka ya koma cikin gidan, bai shiga kitchen ba ya fasa ya wuce ɗakinsa.
...

 Sun yi nisa Barrister Waliy ya kalla Mariya wacce take damƙe da foldern, ya mayar kansa kan titi sannan ya ce.
"Fatan babu wanda ya ganki?"

 Kai ta ɗaga masa tana faɗin."Babu."

 Tafiya suka ci gaba da yi babu wanda ya ƙara magana, har ƙofar gidan su Mariya ya faka.
 Mariya foldern ta miƙa masa, ya karɓa ya ajiye a gefe sannan ta ce. "Sai anjima."

 Kai ya ɗaga mata ta fice a motar tana shigewa gida. Sai da yaga shigarta yaja motarsa yabar harabar gidan.
 Gidansa ya koma ya samu Rumana ta farka tana shirin aiki, shi ma wanka ya yi yai shirin ganin takwas saura. Suka yi breakfast sannan suka nufi wajen Ammi. 
 Cikin girmamawa Waliy ya gaishe da ita ta amsa, haka Rumana ma ta gaishe da ita kamar yadda take yi kullum.
 Ammi ta amsa mata kamar babu komai. Daga nan suka mata sallama suka fito, bayan sun yiwa juna sallama kowanne ya shiga motarsa suka fita suka nufi wajen aikin su.
...

 Mariya lokacin da ta shiga gida Zakiyyah ta farka tana bathroom, jiranta ta yi ta fito sannan ita ma ta shiga. Fitowa tayi ta hau shiri cikin coat ɗinta, tayi kyau kamar kullum sai ƙamshi take.
 Bayan ta kammala ta fita falo, ta samu Aunti Babie ta farka tana shirya yara makaranta. Gaishe da ita ta yi sannan ta wuce kitchen, tea ta haɗa tasha a tsaitsaye ta fita, ta yiwa Aunti Babie sallama ta fita.
 Napep ta tara ya kaita office, kai tsaye office ɗinsu ta wuce bayan ta sauƙa. Bayan ta musu sallama ta zauna a desk nata, ta ɗauki ɗayan case din da ya rage mata ta fara dubawa. 
 Ranar haka ta wuni babu wanda ta haɗu dashi daga Barrister Waliy har Yaya Haydar. Ƙarfe huɗu da rabi ta bar office ta wuce gida.

Kwanakin da suka wuce kafin sati biyu ranar zaman shari'a 
...

To fa ana wata ga wata?
Tambayoyi nasan da yawa a cikin ranku dangane da kowa a cikin littafin da komai da yake faruwa. 
Ku biyo ni don samun amsoshinku har da wanda ban lissafa ba. Akwai ƙaddara, sadaukarwa, kauna da zazzafan soyayya(hot love) da ba ku taɓa karantawa a littafaina ba, sai kun karanta kawai. Kun san littafaina but wannan daban ne.

 Mai buƙatar Books 2 completed akwai a ArewaBook a farashi mai sauƙi.

#vote
#comments
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels

DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment