Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aliyu murmushin mugunta kawai yake ,yana satar kallon Hafsat,ita kuwa ta d'auka wani abu ne yadatse mata k'afa ganin sir Aliyu yana murmushi kuma ita yake kallo yasa tagane shine.fakar idonsu mommy ta yi ta galla masa harara,kara take k'afar yyi,da ido take basa hakuri,sai can dayaga dama ya janye kafarsa,itakuwa ta murgud'a masa baki had'e da harararsa, ta had'e k'afafunta yadda bazai sake take mata suna .nan Hafsat ta ce ta koshi sir Aliyu yace aidama mommy haka take batason cin abincin sosai, murmushi mommy ta yi tace kiladai bakunta take mana. nan sa'ada ta ce ita ta koshi ,taja Hafsat sukabar gun.

"Shima sir Aliyu yatashi yatafi masjid."

___________________ Zakiyya ce zaune kan bed adakinta tanajin wak'ar music awayarta.

Mubarak yashigo yazauna kan bed side,yakalleta yace sis yasu nan yarinyar da kikaga yaya ALiyu da ita a shopping males?

"da mamaki Zakiyya ta kallesa tace lfy yaya?'

Murmushi yyi yace ki amsamun tambaya ta.

Zakiyya tace sunanta Hafsat!

Mubarak yace to naganta da yaya aliyu yau agidansu yaje da ita!, kutumar uba zakiyya ta fad'a cikin karaji,murmushi Mubarak yyi yace minene abun tada jijiyar wuya ,ni yarinyar tamun wlh danko bansame taba inason inhuta da ita dan kalar skin d'inta yamun,saidai inatsoron yaya Aliyu wlh dan naga kamar sonta yake.

Wata muguwar dariya irinta basawa Zakiyya tayi tace naji Dadi data maka dan nadau ki alk'awrin kota halin kak'a saina auri yya Aliyu.

" kabarmin komai zanbincike akanta ."

Mubarak yace to shikenan dan ni inzan aureta inaso inkuma bazan auretaba inason in lashi zumarta.

Wani mugun murmushi Zakiyya tayi tace kada kadamu ko satota sai muyi ko mu nunawa iyayanta kudi su aura maka ita.

"Dan ina tunanin yar talakawa ce."

Nan Mubarak yace to shikenan yafita.

Da misalin 8:00pm sir Aliyu yashigo parlourn gidansu yasami sa'ada zaune a parlour ,yace ina mommy da Hafsat?

Sa'ada ta ce mommy na d'aki sallah take ,itakuma Hafsat ta na d'akina tana game.

Da sauri sir Aliyu yanufi dakin,yana shiga yasami Hafsat ta na game tana dariya ,kawai tagansa kamar daga sama.

Kusa da ita ya zauna ya kalleta yace wana kama?

Shiru tayi tana zare ido,can tace to bakaine kayita takemun k'afaba.

Murmushi yyi yace hmm saina gyaramiki wannan bakin da kike turowa.

"Ahankali tace yauwa yaya kiramun baban mu gaisa saika bani inyi game da wayarka.

Kallonta yyi yace bazan kiraba.

Aisaita hau kukan shagwaba harda dire dire ita sai yakira mata babanta.

Sir Aliyu kuwa lumshe idanunsa yyi ,azuciyarsa yanace wa yah salam sakamakon wani abu dayakeji ganin yadda Hafsat ke Wannan shagwaba r dan yalura akwai kuruciya da ita.

Share pls
NIDA DA'LIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿67&68

"""" Ahankali Hafsat ta ce bara naje nafad'awa mommy kak'i kiramun baban a."bud'e idonsa yyi yace hmm aibazaki iyaba ,abinda kunya r momin kike,marairaicewa tayi tana lallab'a sa sannan yakira baba n,Hafsat tayi mama kin yadda sir Aliyu ya saba da babanta ganin yadda suke fira dashi.
Sir Aliyu ya mik'a mata wayar yafita nan Hafsat suka sha fira da baba yyita mata nasiha tayi hakuri da rayuwa kuma ta rik'e mutuncinta.sannan sukayi sallama,tafit o dg dakin dan kaiwa sir Aliyu wayarsa."";;

A parlour tasamesu harda mommy, nan taje ta mik'ama sir Aliyu wayarsa sai kallonta yake da idanunsa dasuka canja kala.

Mommy ce tace suje ayi deener,Hafsat tace ta koshi,wani kallo sir Aliyu yabita dashi yace mekika ci da har kika k'oshi?

Sunkuyadda kanta tayi tace nasha fura gun sa'ada ai.

Girgiza kansa yyi yace banyarda fura zata k'osar dakeba oya muje kici abinci.

Murmushi mommy ta yi tana kallonsu cikin birgewada sha'awarsu ,tace kai babana kacika takura dole sai taci aboncinne?kallon Hafsat ta yi tace y'a ta zakici ko kin koshi?Hafsat ta saci kallon sir Aliyu taga yyimata alamar intace ta koshi in yakamata zata gayamusu ai da sauri tace eh mommy zanci!murmushi mommy ta yi danta lura da abinda sir Aliyu yanuna wa Hafsat. Dining area suka nufa,bayan sun zauna mommy ta yi serving in kowa,harsuka gama sannan ,sukayi sallama kowa yawuce makwancinsa.

Washe gari da misalin karfe 6:30am ,Hafsat ce ta fito da ga d'akin sa'ada,kasancewar bayan sun idar da sallah sa'ada ta koma bacci.itakuma ta kasa komawa Dan tasaba agidnsu da anyi sallar asuba Laure zatayi ta sakata aiki,zai zirga xirga take bata waiting parlour bata part din sa'ada,gash I tanason ganin sir Aliyu, kuma batasan inda yakeba,mommy dake part dinta taji motsin yyi yawa ta fito ta sami Hafsat zaune kan carpet ta yi shiru.

"Ahankali mommy ta ce y'ata yaya dai?"

Da sauri Hafsat ta gaida,ita ta amsa fuska cike da walwala,kan kujera mommy ta zauna ta ce zonan kinji,ba musu Hafsat ta je ,hannunta mommy ta kama ta zaunar da ita kusa da ita.tace kifad'amun mekkso?inde kin d'aukeni mamanki kinji?

"Ahankali Hafsat ta ce ina yaya yake banganshiba?"

Murmushi mommy ta yi tace, yana part dinsa ,k'ila bacci yake,amma ai lokacin motsa jikinsa yyi ,yanzun kingansa yazo,inkuma xakije ga kwana can inkikabi har part dinsa sai kije.

Da sauri Hafsat tace ah ah mommy basai najeba.

Murmushi mommy ta yi, dan tasan da k'yar taje,dan talura yarinyar akwai tarbiyya da kamun kai.

"Can kuma Hafsat ta mik'e tace mommy na tafi gun sa'ada!mommy tace to y'ata,nan ta nufi dakin,kafin ta ida isa taji kamshin turaren sa da sauri ta juya sukayi4eyes dashi yana sanye da kayan motsa jiki wani killer smile yasakar mata ,itama tayimasa.

" murya k'asa k'asa yace my Hafsat kintashi lfy ?"

Turo baki tayi tace lfy had'e da duk'awa ta gaida shi murmushi yyi ya amsa tare da cewa sarkin rigima to menene kike wani tura baki gayamun kinji?

"Ahankali tace bakaibane bangankaba sai yanzun."

Kallon ta yyi yace to sorry ina part dina ai yanzun gani ,mujema kirakani gun exersic . mak'e kafada tayi alamar ah ah bazata jeba.murmushi yyi yace shikenan zamu bata kuwa.....muryar mommy yaji tana cewa Auta sai yanzun kika tashi har Hafsat ta rigaki tashi,wata irin kunya sir Aliyu yaji,itakuwa Hafsat bata juyaba da gudu ta shige dakin sa'ada, shima ko kallon mommy be iyaba sum sum ya wuce.

Ita kuwa mommy murmushi tayi ,axuciyarta tace allah yasa kunada rabon mallakar juna ,dan daga gani Hafsat saita canja maka ak'ida,gashi dama bakason raini ita kuma tana girmamaka ,ko dazata gaidashi saida ta duk'a fg ita harshi sun manta da ina gun ,amma zan cigaba da adduah allah yazaba abinda yafi alkhairi.

Bayan su Hafsat da sa'ada sunyi wanka ,sukayi break fast Wanda sir Aliyu be zoba dan yanajin nauyin mommy sai dai sadik , shikuwa kabeer yana skul. Nan sa'ada taja Fatima suka wuce islamiyarsu.

"Sir Aliyu da ke bed room dinsa yaga fitarsu ta window."

Basu jima da fitaba yaji k'arar anbude get ,da sauri yaduba yaga ko sadiq zai fita da mota dan anhanasa fita da mota yyi karanta aceawar sir Aliyu. Kawai saiyaga motar Mubarak yyi parking ,hakanan sir Aliyu yaji wani mugun fad'uwar gaba, yajikuma be yadda da zuwan Mubarak ba dan yasan dagashi har Zakiyya basa zuwa gidansu saida dalili,be auneba yaga sun fito mota tare da Zakiyya, nan yasake mamaki,amma sai yasake bude labulan windon dan yagansu sosai ,amamakinsa sai yaga sun nufo setin windon dayake da sauri yasaki labulen windon,har zai juya yakoma kan bed sai yaji muryarsu suna magana k'asa k'asa.

"da sauri yatsaya yafara sauraransu."

Ji yyi Mubarak yace kin gane sis inkinje ki nuna kinzo musu yini ne ,Nina kawoki zanzo na d'aukeki .
Kinsan sa'ada fa surutu sai kibigi ciki nta kiji inane anguwarsu da kuma iyayanta,kinga in talakawane ta kwana gidan sauki,sai muje muyi musu b'arin kudi ,kin gane? Wata yar dariya Zakiyya tayi tace babu damuwa Allah yasa zan iya dan mugun haushi suke bani daga Hafsat din har sa'adar.

"Ahankali Mubarak yace kinga inmun sami information akanta shikenan, sai mubita gidansu dg nan inta yarda zata aureni ba matsala."

Inkuma tak'i kawai sai insaka asatomun ita nabiya buk'atata da ita.

Dariyar mugunta Zakiyya tayi tace kaga ko yaya aliyu ya aureta bazata yi daraja gunsaba tunda abud'e zai sameta,ballema bazan bari ya auretaba.

"""" mutuwar tsaye sir Aliyu yyi agun ,sai wata irin zufa ke keto masa,innalillahi wa inna ilaihir raju un kawai yake maimai tawa,had'e da jin wani fad'uwar gaba da b'acin rai,Atake idanunsa sukayi jajir suka k'ank'ance,da sauri yaja glass din windown.

Arazane Zakiyya da Mubarak suka juyo sukayi 4eyes da sir Aliyu.

Ai take yan hanjin cikin Mubarak suka kulle dan tsabar firgita yatsorata da yadda yaga idanun sir Aliyu.

Ita ma Zakiyya ta tsorata sosai musammun data lura da sir Aliyu yaji duk firarsu da sukayi.

Basu auneba sukaga sir Aliyu baya bakin window din,arazane Mubarak yace muje mukoma mota wlh zagayowa zaiyi ,kinsan kuwa mukayi arba dashi kashina ya bushe asukwane suka nufi gun da suka yi parking.

Adede nan kuma Hafsat da sa,ada suka turo get suka shigo ciki.

Sir Aliyu kuwa da sauri yafito dg part dinsa, zai nufi k'ofar fita parlour n, da sauri mommy ta tsaidashi ganin yanayinsa dan tasan ba lfy.

Da sauri tace ina zakaje ne haka ranka bace?

Cikin damuwa yace pls mommy kibarni naje kada su gudu .

Mommy ta ce su wanene? Da sauri yace Mubarak da Zakiyya,kara su cutarmun da Hafsat mommy ki barni naje dan Allah yafad'a kamar zai yi kuka.

Cikin mamaki mommy ta basa hanya ya futa afusace kamar zai tashi sama.

Ya fita ya hango har get man yabud'e masu get zasu fita, da gudu yakoma ciki ya dauko key din motarsa ya fito mommy na tambayarsa ina zaije be kulataba ya fito asukwane.

Parking spaces yawuce,nan yahango su Hafsat zasu shiga ciki,da sauri yashige motar yabata wuta.

Dan yyi alk'awarin ko gaban abbansune karshe kenan sai yakoya musu ahankali.

Da mugun gudu ya isa gidansu Zakiyya,a parking spaces yaga motar Mubarak da alama suna ciki shida Zakiyya.

Azuciye yafito dg motarsa yyi cikin gidan afusace....

Share plsNIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿69&70

Ko sallama bbu ya afka cikin parlourn fuska ba annuri.yas amesu zaune a parlourn Mubarak yana shan lemo,ai yana ganin sir Aliyu yasaki cup d'in lemo n had'e da mik'ewa tsaye yana tari sbd k'warewar da yyi.
Shikuwa sir Aliyu gu n mubarak yyi gadan gadan,mommy na ganin haka afusace tace kai lfy zakashigo min gd bako sallama? Ko gun datake sir Aliyu be kallaba ,fisgo Mubarak kawai yyi yafara basa kyawawan maruka masu rai da lfy Atake Mubarak yasaki ihu had'e da cewa mommy ki ceceni dan Allah. Ita kuwa mominsu tsinewa sir Aliyu kawai take yi had'e da aibatasa.shikuwa ko ajikinsa,dukan Mubarak kawai yake yana cewa dakaji dukan dnayi maka a farko dabakayi yink'urin abinda kayi yanxunba ,bedena suburbudarsaba sai da yakumbura masa fuska tukum .sannan yanunasa da yatsa yace wlh wlh wlh duk abinda yasami Hafsat Kaine da Zakiyya dan wlh zan aje yan uwantaka gefe Nayi muku hukunci da abinda kuka aikata,ai inkacika tantiri basai kasaka asato maka ita ba kabiya bukatarka da itaba ah ah har gidansu zakaje da kanka gaban kowa saika d'aukota ammafa in zaka iya.

Ita kuwa Zakiyya part dinta ta gudu ta rufe.

Koda sir Aliyu yajuya yaga bbu ita yasan guduwa tayi.

Cikin masifa mommy ta ce wlh saina dau mataki akanka dan kafi k'arfinsa saika rik'a zalintarsa ,kuma akan wata banzar mace ma .

"Ahankali sir Aliyu yakalleta yace mommy ina ganin girmanki kidena zagina haka,yaradai k'annena ne kuma na isa dasu insunyi laifi na hukuntasu. "

Wani tsaki taja tace wlh z....muryar abbansu Zakiyya taji yana cewa kincuceni Hajara kin b'atamun tarbiyyar yara gaba d'aya kuma Nayi duk abinda Aliyu yafad'a kinaji yace zaisa asato masa yarinya ya aikata masha'a da ita amma bazakiga laifinsaba,saikirik'a zagin Aliyu.cikin b'acin rai Abba yakalli sir Aliyu da kansa ke duke yace inaso kaje d'akin Zakiyya kazanemun ita,umarni na baka yafad'a had'e da mik'a masa wasu keys yace kabud'e dakin inta rufe.

"Da sauri sir Aliyu ya karba dan dama haka yake so dukda bayason dukan mace amma yaci ace Zakiyya jikinta yagayama ta."

Ita kuwa mommy ba bakin magana dan ta lura Abba ransa b'ace yake.

"Bayan sir Aliyu yanufi dakin Zakiyya," Abba yakalli mommy yace hukuncinki zai biyo baya ai naga sadda aliyun yashigo gidan nikuma dawowata kenan nabiyo sa natsaya bayan labile naji koma.

Wata harara yaaikaea Mubarak dake kwance da k'asa da kumburarrar fuska yace Allah yashiryeka yafad'a had'e da barin parlourn.

""" sir Aliyu kuwa bude d'akin Zakiyya yyi yasameta kwance da earpiece akunnabta,saidai tagansa kamar dg sama beyi wata wataba ya zare belt d'in dake k'ugunsa yashiga jibgarta tana ihu hade da basa hkuri be k'yaletaba saida ta daku,sannan ya kalleta had'e da nunata da yatsa yace inaso kisani duk abinda yafaru da Hafsat kune kuma bazan taba k'yalekuba,sannan kince saikin aureniko?to bari kiji da in aureki gwara na tabbata bbu aure har k'arshen rayuwata.yafad'a tareda da Jan doguwar tsuka yabar parlon.""";;


Yaje yadauki motarsa yabar gidan.

Ko a hanya tunani yake azuciyarsa yace meyasa masa keson keta mata haddi ne?

Ko wanne gaja yanason b'ata mata rayuwa,wata zuciyar race sbd tana da kyawu had'e da k'ira me daukar hankali.

Wani mugun tsaki yaja ,koda ya isa gd straight part dinsa yanufa be kulasu sa'ada dake zaune parlour itada Hafsat suna firaba.

Mommy ce ta tashi tabisa d'akinsa dan ta lura yana cikin damuwa har yanzun.

Ta samesa kwance rigingine yyi tagumi yak'urawa seeling ido yana tunani.

Da sauri ta karasa gunsa ta hau tambayar lfy me yafaru dazu kuma me su Zakiyya suka masa??

Cikin damuwa ya zaiyane mata abinda yafaru,salati kawai mommy keyi tace lallai yarinyar da aka bamu amana suke shirin aikata hakan akanta,amma ai alhmdllh tunda Allah yatoni azirinsu.

"Amma bbna kayi hkuri kaje kayi break fast ."

"Ahankali yace na k'arya awaje na koshi ,yafad'a had'e da rufe idanunsa."

Fitowa mommy ta yi, ta isa kusada Hafsat ,ahankali ta dafata tace y'ata kije gun yayanku yana cikin damuwa ki lallab'asa ,sannan kixo kikai masa kayan break dinsa dan beyi break ba dan naga kunshak'u dashi kinji ko?

"To Hafsat ta ce ta tashi tanufi dakinsa."


Tana shiga tasamesa kwance idonsa arufe ,sallama tayi ta zauna nesa dashi,murya k'asa k'asa tace yaya shine na shigo d'akinka ka shareni?

Bud'e idanunsa yyi yana kallonta,ta sunkuyadda da kanta k'asa.

Cikin shagwaba ta ce yaya natafi tunda kak'imun magana ka shareni,ahankali yace ni ban sharekiba.

Murmushi tayi tace hmm hakane ,amma kasan kamun alkawarin dena saurin fushi amma naga kamar fushi kke yanzun badai nice Nayi laifinba ko?ta fad'a had'e da langabe kai tana kama kunnanta.

Besan sadda yyi dariyaba,yace my Hafsat bake bace kuma yanzun naji na huce nabar fushin murmushi tayi tace eh hakane amma meyasa bakazo mukayi break tareba ?

"Shiru yyi tanatunanin me zai ce mata?"

Can yace banajin yunwa,ai turo baki tayi race amma ni jiya ka tursasani saida naci abinci to yanzun zan kawomaka break kayi dan bakayi break ba nikuma banason yunwa takamamun kai ko?

Ai sai yyi kamar wani dolo dan besan sadda yace to kawomun my Hafsat innaci zakiyi farinciki?

Da sauri tace eh hade da fits.ba jimawa tadawo da plate chips ne aciki da cup din tea mai kauri ta aje masa gabansa.

Tace yauwa Yayana kacigaba da ci kaji ba musu yafara cin abincin sa tana masa fira har ya cinye komai Ta's,cikin jindadi tace yauwa ko kaifa.


Murmushi yyi yace gobe bayan sallar axahar zanmaidake gd dan lokacin baba yadawo ,dan munyi waya dashi dazun.

Murna sosai Hafsat ta hau yi,had'e rai sir Aliyu yyi yace wato ke murna ma kike ko bazakiyi missing dinaba kinfiso mu rabu?

Shagwabewa tayi tace Allah Yayana bahaka bane ,ai naga saura 6days mukoma skul kuma zan ganka a can shiya sa.

Shiru yyi bece komai ba.

Fita tayi takai dan kai plate din da cup din waje,koda mommy ta ganta taji Dadi sosai aranta dama tasan sir Aliyu bazaima Hafsat musuba kuma tasan yanzun yahuce daga Fushun da yake,sai murmushi mommy keyi tanasa ma hafsat albarka.

Bayan ta kai kayan kitchen tadawo dakin tasamesa yana latsa waya gefensa ta zauna cikin shagwaba ta ce yayaaaaa!

Kallonta yyi da sauri yace my Hafsat yar rigimata kimun firanki kinji?

Tashi tayi tace barama nagyaramaka dakinka amma saika fita.


Murmushi yyi yafita ,cikin yan mintoci ta gyare dakin parlour da bed room.

Sannan ta koma toilet ta wanke shi Ta's,harzata fita taga fararen vest dinsa da jallabiyoyi guda biyu ajik'e a bucket, bbu bata lokaci ta duba taga bbu boxes aciki ,saita wankesu Ta's ta shanyasu a toilet din ta had'a masa ruwan wanka ta fito da ga toilet din .

Tana fitowa ,yanashigowa kallonsa tayi tace yaya kaje kayi wanka kaji?

Murmushi yyi yace to my Hafsat yaude anaji dani sosai.

Murmushi tayi ta fito,shikuma ya shige toilet.

Wani farin ciki yaji aransa,yaji Hafsat ta sake samun.matsayi me girma agunsa.

Yaji Dadi sosai da yadda yaga ta wanke masa kayansa sai murmushi yake har yagama wankan ya fito.

Bayan ya shirya ya fito cikin farin ciki dan yanason xuwa campaninsa,yaga ba kowa a parlour ,motsinsu yaji a kitchen can yanufa.

Yasami du Hafsat itada sa'ada suna aikii.

Murmushi yasakarma Hafsat ya ce sannunku da aiki, murmushin itama Hafsat ta yi masa tace yaya sai ina?

Ahankali yace zan je office muje kirakini mota kimun addua.

Sa'ada tace haba yaya saita wani rak.... Hararar da ya aiko mata yasa tayi shiru.

Hafsat kuwa ba kunya ta bisa har parking spaces yayi masa adduar da yabukata ta dawo cikin gidan.

Washe gari....NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿71&72

Washe gari.
Bayan sallah azahar sir Aliyu ne tsaye a waiting parlourn gidansu yana kallon Hafsat sun rungume juna da sa'ada suna ban kwana,Hafsat kamar tayi kuka sbd sabon datayi agidan dakuma batasan rabuwa da sa'ada.
Mommy ce tazo taja hannun Hafsat tasaka mata wata babbar Leda ahannunta ,hafsat zatayi magana mommy ta rufe mata baki,takalli sir Aliyu dake tsaye yana aikin kallonsu. Tace babana kuje dan Allah ka lallab'ata kaji?

"Yatsina fuska yyi yace haba mommy lallabata d'in me zanyi,ya kalli Hafsat yace oya muje."

"Turo baki tayi tabi bayansa."

Ya shige mota yabarta ,yak'i bud'e mata ,itakuma tak'i shiga sbd yasaba shike bud'e mata duk in zata shiga motarsa.

Shikuwa yana sane yyi hakan Dan yaji haushin yadda ta nuna damuwa kan zata rabu da sa'ada amma shi bata damu dan zasu rabuba.jin shirun yyi yawa yasa yafito ya kalleta fuska daure yace wai bazaki shi ga bane kome kkejira?
Kauda kanta tayi gefe tace cikin shagwaba tonika bud'e mun nashi ga. Kallonta yyi yace keko kin rainani kwa nannan ko? batace komaiba can yabud'e mata sannan ta shiga yaja motar ,saida yabiya yasiya mata su ice cream da ga sassun kaji dasu biscuits da chacoolat,sannan suka wuce anguwarsu.

Bayan yyi parking da sauri ta kai hannunta dan bude k'ofar ta jita yasa lock,shiru tayi dan dama tunda suka shiga motar batayi masa magana dan zama da shi yasa takoyi miskilanci.

Kallonta yyi murya k'asa k'asa yace wato dan zakiga baba ki koma gunsa shine kikemun haka ko?

Share pls[1/7, 11:20 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

🅿73&74

Bayan kwana biyu.
Gaba daya shire shiren komawa suke skul,baba yayiwa Hafsat siyayyar komai,itama tagama shirinta gobe sai skul.

Yanzun haka Hafsat ce zaune a d'akin ta suna fira da babanta,amma hankalinta baya gun firan sotake ta karb'i wayarsa takira sir Aliyu su gaisa rabon ta dashi tun ranar da ya maidota gida.

"Can wata dubara ta fad'oma ta."

Da sauri tace baba bani wayarka zanyi wani lissafi!bbu musu yabata tareda cewa Nina fita dan ukku tayi ankusa la'asar,inna dawo na karba.
"Ahankali tace to baba adawo lfy nan yafita .Hafsat cikin zumud'i ta shiga cikin contacts, cikin sa'a taga bbu number sir Aliyu. Shiru tayi,can kuma tashiga receive call ta duba rana da lokaci Atake tagane number dukda ba suna.";;

Atake tasaka kira,harta tsinke ba'a d'agaba,turo baki tayi cikin jin haushi kamar agabansa take,kawai taji wayar na ringing tana dubawa taga shine yakira,saida takusa tsinkewa ta d'aga batare da tayi magana ba.cikin girmama wa sir Aliyu yyi sallama had'e da cewa baba barka da rana,murmushi Hafsat ta yi me sauti atake yagane itace,cikin zumudi yace my Hafsat kece? Wani murmushin tasakeyi tace nice yayanah,kaga nadamu dakai ko amma kai baka damu dani ba gashi Nina fara kiranka.

" cikin marairai cewa had'e da rarrashi yace ayya my Hafsat bahaka bane, wlh inason muyi waya amma inajin nauyin cewa baba yabaki ne shiyasa,amma yanzun kin hakura?"

"Kamar yana ganinta ta d'aga kai had'e da cewa eh."

Murmushi yyi yace to nagode ai nasan kinada hakuri da sauri yafiya,amma kina yawan tunanina?

Yar dariya tayi tace ah ah.

Had'e rai yyi yace to shikenan tunda ma bakya tunani,nima zan dena tunaninki.

Cikin shagwaba ta ce, yaya dan Allah kada kadena tunani na nafison koda yaushe ina cikin ranka.

Lumshe idanunsa yyi yajin dadin sweet voice dinta hade da kalamanta.

"Ahankali yace um um kema ai bakya tuna ni ."

Dasauri tace ah ah wlh ina tunaka namaka dubarane dan inji kana tunani,shiyasa,ammafa ko yanxunfa tunanunka nikeyi ,nayiwa baba dubara na karbe wayarsa nakiraka.

Murmushi yyi yace Allah tawan.

Lumshe ido tayi tace eh mana,yanzun kana ina ?yace ina part dina, tace inasu mommy da sa'ada ?

Murmushi yyi yace sunyi kewarki sosai,dariya tayi tace nima haka.

Murya k'asa k'asa yace gobe sai skul ko?turo baki tayi tace eh yaya ni banso in koma gobe nafiso sai next week murmushi yyi yace gobe insha Allah zaki koma skul.mur gud'a baki tayi tace to sai anjima, dasauri yace kingaji da magana danine? Ahankali tace ah ah kawai dai banso baba yasameni ina waya Bacin ban fada masa ba.ajiyar zuciya yyi yace hmm wata ta koma mak'aryaciya ko?

Cikin shagwaba ta ce allah niba mak'aryaciya bace ni munbata dakai.

Dariya yyi yace dama rannan kinmun gwalo ko? To zamu hadu askul gobe saina saka mlm rabe yabani dorina na zabeki.cik in kukan shagwaba ta hau basa hkuri,shikuwa jin tana hakan yyi saurin k'ashe wayar sbd wani yanayi da bak'on al'amari da ya tsinci kansa aciki.ita kuwa Hafsat ta dauka da gaske yake tunda har yakashe kiran duk saita ji tsoron komawa skul gobe duk da wata zuciyar nacewa wasa yake miki.

Washe gari da misalin karfe 4:00harsu Hafsat sungama shirinsu ,baba yyi mata nasiha akan takulada kanta tayi kuma karatu tunda Wannan ce shekararsu ta karshe dazasuyi askul.har yan hawaye saida ta yi,Laure na kallabta tana tab'e baki had'e da hararanta,sarai Hafsat ta lura da ita tadai nuna kamar bata gani ba, kallon su hanifa da shamsu kannanta tayi tace suxo sutayata d'aukar kaya,kallonsu Laure kawai tayi suka gane meta ke nufi. Atake sukak'i zuwa ,baba da agabansa akayi ya kallesu yace kuje kutayata dauka ko ranku yab'aci,ganin ba wasa afuskarsa yasa sum sum suka bita, suna tayata.awaje taga Fatima da driver,nan akasaka komai aboot suka dauki hanyar skul dinsu.


****************
6angaren sir Aliyu kuwa, mommy ta yi masa miyar kaji da danbun naman rago had'e da provision tace yakaiwa Hafsat a skul.

Sir Aliyu yyi Dadi sosai yyi farin ciki da yadda mahaifiyarsa ke nuna k'auna da tausayawa ga Hafsat.

Haka yaci wankan sa,cikin kananun kaya, sai k'amshi yake,abin sai Wanda yagani yaja motarsa sai skul.

Koda ya isa, office dinsa ya bude yashiga ya zauna aciki,yabar windows abud'e dan yana hangen get dg office dinsa.

"Yafison da Hafsat ta dawo yaganta."

Befi15minit ba yahango Hafsat cikin pink checks na doguwar Riga idanunta sunyi d'an ja alamar tayi kuka kenan.

"Azuciyarsa yace yah salam me tayiwa kuka ne?"

Hangowa yyi sun gama shigowa da kayansu Fatima ta saka ana dauka ana kaimusu daki,su kuma sun biyo bayan su.

"""""Hafsat ta saci kallon office din sir Aliyu taganshi abude, kallon Fatima ta yi tace sis xomuje gun sir naga office insa abud'e yake!da sauri Fatima ta ce ah ah sis kedai kije bari ni naje najere mana kayanmu a laka.Hafsat tace ba damuwa,nan tanufi office din Sir Aliyu. Shikuwa yana hangota yafito dan bayason yawan ke b'ewa da ita dan gudun ajimasu wani zato.

Tana ganinsa ta tsaya,shikuwa kafeta yyi da mayun idanunsa yana kallonta, murya k'asa k'asa yace waya samun ke kuka gayamun kinji tawan?

Sunku yadda kanta k'asa tayi tace ba kowa kawaidai banson in rabu da babana.

Murmushi sir Aliyu yyi yace kada kidamu zan rik'a kira miki shi kuna gaisawa.

Murmushi tayi had'e da kallon sa tace yauwa yaya nagode sosae, harnaji Dadi wlh.

Murmushi yyi yace nima har naji Dadi da kika kasance cikin jin Dadi.

" ahankali yace ga kayanki can a office da mommy ta bani nakawomiki."

d'an zaro ido tayi tace oh wai yaya mommy bata gajiya da yimun hidima ai d'awainiyar tayi yawa dan Allah.

"Ahankali yace kada kidamu mommy haka take."

Nan yaje yad'auko mata kayan tayita masa godiya sukayi sallama, ta nufi hostel shikuma ya nufi step quarters.


________________
WAIWAYE.....
Mahaifiyar Hafsat tunda mlm aminu yasaketa yakwace y'arsa tarasa ina zata gashi batada ko sisi Balle ta tafi gombe garinsu,kuma rabontada garin tun sadda mlm amunu yadauko ta dg

1 Comments On NIDA DALIBATA
avatar
isaitah-mujittapha

10 months ago

Reply

Masha Allah yayi dadi

Please Login or Register in order to submit comment