Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tape din gidan suka samesa yana amai kamar ze amaye yan cikinsa.

Kuma aman yellow ne,da sauri Hafsat ta isa gunsa.

Cikin tausayawa tace sir sannu,d'agowa yyi yakalleta yamayar da kansa.

Buta ta dauka ta Tara jikin tape din tacika,ahankali ta tsugunna kusa dashi,

Tana xubamishi ruwan yana wanke fuskarsa da bakinsa.

Mlm rabe da doctor suka shiga parlour sunajiransa.

Kallon sa tayi taga ya dan rame fuskarnan tayi fiyau har dan yellow take.

Ahankali yace hafsattttttttt!!

Har cikin kanta taji sunan ,ahankali tace sir sannu!

Kallon ta Yy yaga tana hawaye, murya asark'e yace ,meyene nakuka ai nasami sauki ko.

Waye yasanar dke ne? share hawayenta tayi tace mlm rabe ne.

Kallon ta yyi yace to muje ,amma banaso kisake kuka nafa sami sauk'i kinji.

To tace tabi bayansa dan shiga parlour, kallon sa tayi taga shirt ce da 3quarter ajikinsa.

Jikinnan nasa amurde yake ga gashi kwance baki k'irin ajikinsa.

Bayan sun zauna doctor ,yazo yafara treating d'insa.

Yarubuta masa mgni ,sannan yyi masa allura ga hannu,dg karshe yace yarage tunani.

Nan sir Aliyu yaba mlm rabe takardar magani dan yasiyo, sukayi sallama da doctor.

Dazasu fita mlm rabe yace ke Hafsat ki zauna kkula dashi , yakalli sir Aliyu yace ashe batason baka lpia ba,

Saida ta tambayeni kana ina nafada mata.

Murmushi sir Aliyu yyi yace ainasami sauki mlm, nan suka fita.

Hafsat bataso mlm rabe yace wai taje nemansa,tasan sir da disgi kadama yyi mata wata fahimta.

Shikuma Sir Aliyu ,samun kansa yyi da jin dad'in yadda Hafsat tadamu dashi ,gashi har kuka tayi masa na tausayinsa.

Hafsat tashi tayi , sir Aliyu yakalleta yace ina zaki, azuciyarsa ca yake Allah yasa kada ta tafi.

Tsintar muryarta yyi tana cewa, zan dan shiga kitchen ne sai in gyara gidan.


Yaji dad'in hakan har cikin ransa amma afili sai yace .

Nifa bana cin jagwalgwalenki, kinma iya girkine?

Bata ce komaiba tafita,azuciyarta tace oh mutumin nan ba,a iya masa, beda lafiyar amma jin kansa na nan.


Tsakar gidan ta share ta goge, tana bakin tape zata d'ibi ruwa, mlm rabe yashigo ,ledar magani yabata yace kibasa kice sai yaci abinci ,yasha.


To tace ta kar6a , shikuma yafita, parlour takai maganin tasami sir Aliyu baya parlour n.

Ajewa tayi ta fita tashiga kitchen, taga akwai komai na bukata.

Dubawa tayi taga electric da risho, nan ta kunna risho ,ta aza tukunya kafin ta tafasa tagyara wake.

Nan taxuba waken tayi dan jajjage a greater, tatsane waken bayan yazabku

Tasoya kayan miyan ta zuba kayan k'amshi da maggi.

Nan dai cikin 1 hour ta yi masa faten wake da dankalin turawa ,yaji kifi da alaiyahu.

Tuni gidan yadau kamshi,nan ta wanke kayan data bata.

Tun cikin bed room sir Aliyu kejin kamshin girkin nan,

Har parlour yafito amma kamshin karuwa ,yake .

Atake tsohuwar yunwarsa ta taso yaji yakagara yaci abincin ko zazzabi nsa yasauka.


Befi minti gomaba da zamaba, ,tashigo da kula da plate da serving spoon.

Zaunawa tayi gabansa tace sir mlm yakawo magungunan ,amma yace saikaci abinci.

Sannan kashasu, yatsina fuska yyi yace ok sai anjima innaje restaurant naci.


Turo baki tyi tace gara abinci na mararsa lfy kaci pls nyi serving dinka?

Ah ah,Yace ahankali tace meyasa sir,

Kallon ta Yy yawani langabe kai kamar wani yaro,yanunata.

Yace bakece kika dena cemun yayaba, aikinga bazanci abincin wadda bata daukeni yayantaba.

Dariya yabata sosai amma sai tadaure tace, bakaine kacemun yar kalan dangiba.

Murmushi yyi Yace tskanarki fa nake,
Kallon sa tayi tace to yaya zakaci abincin ko?

Kaga saikasha magani, haka doctor Yace,kafeta yyi da firgitattun idanunsa yana Kallo, yajin dadin yadda take lallabasa.

Kallon ta yasakeyi Yace,akwai sharad'i ,inkinyarda to zanci.

Azuciyarta tace ,towai dole saikaci abincin ne xakace saida sharad'i.

Amma a fili saitace meye sharadin Yace kinyarda muci atare.

Da Sauri tace ah ah banajin yunwa ai.

Had'e rai yyi Yace ok zaki iya tafiya, tunda bazakbi umarnina.

Murmushi tayi tace ,tsokanarka nake,fa nan tabude kular.

Tsaki yyi Yace tunda ga abokin wasanki ko,aidama ina hagwanki,amma zankamaki,zakison Wanda kikayima gwalo rannan.

Kamshin girkinne yadaki hancinsa yalumshe ido.

Bayan ta xuba musu a plate daya, tasa 2 spoon, tace bisimilla yaya.

Nan suka zauna kan carpet, suna kwasar girki.

Sir Aliyu har wani lumshe ido yake dan girkin very nice.

Can yasaci kallon ta yaga itama ba laifi cin abincin ta take.

Kuri yyi mata ,ganin ba hijab ajikinta da dankwali.

Gashin gaban goshinta yatashi iskar fanka na kad'asa gwanin sha,awa.

Ga doguwar rigar check pink dinta tabi jikinta,

Ganin zata kallesa yasa yadena kallonta.

Nan suka cigaba da cin abincin su har suka gama,nan takwashe kayan,

Ta fito ta kai kitchen, a window din kitchen din taga inwarta ta glass ba hijab da dankwali akanta.

Aratsane tayi sallati ,ta duba gefen datake tsaye taga dan kwalinta da hijab dinta.

Tunawa tayi d'azu tacire dazata aza girki da sauri tasaka, ta dauki swan water roba1

Dan kai masa yasha mgani, tana xuwa yaganta da hijab,aransa yace, k'ila dazata aza girki tacire.

Nan ta basa magani yasha ,bata kallesaba dan ta ji kunya daya ganta ba hijab da Dan kwali.


Tace yaya kaje ka kwanta kayi bacci.

Kallon ta Yy yace ni Kallo ma zanyi, sannan kina kallon wani gu kinamun magana.

Bazaki kalleniba , cikin shagwabar da batason tayiba ta mik'e tsaye tace,

Pls nidai kaje kayi bacci, zakafi samun saukin jikinka.

Juyawa yyi yanufi hanyar bed room ,sakamakon wani yanayi da yatsintsi kansa jin yadda take shagwaba.

Gab da zai shiga yace ,innayi baccin ina zakije?

Tace yaya zan koma hostel ,har hudu fa tayi.

Kallon ta Yy yace dama ba jinyata kikazoyiba ko,

Saiki tafi kawai hakan yyi kyau.

Bejira amsartaba yashige bed room.....

Share pls

[12/11, 9:16 PM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ21&22

Tsaye Hafsat tayi ,tayi shiru ,axuciyarta tace oh yaya fushi yyi kenan, Toni nafasa tafiyar.

Dan haka toilet na tsakar gd ta shiga tayi alwalla tazo, parlour tayi sallar la,asar.

Bayan ta idar, ta fito ta nufi kitchen danyima Sir Aliyu girkin dazaici da dare.

6angaran sir Aliyu kuwa ,yanashiga bed room toilet yashige yyi wanka da alwarla.

Bayan yyi sallah yacire jallabiya dg shi sai 3 quarter yakwanta.

Tunani yake meyasa yadamu dan Hafsat ta tafi?

Wani 6angaren na zuciyarsa haushin kansa yakeji ,akan
Yadda yadamu da ita,

Tsaki yaja,danshi atunanunsa ,ta tafi hostel , yana nan kwance har bacci yyi gaba dashi.

Hafsat bewar allah tanacan kitchen tana hak'ilon girka masa sakwara da miyar agushi.

Sai sauri take batason magrib tayi mata agidan sir Aliyu.

Ba,ita ta idarba sai 6 saura, tasaka komai ature takai parlour.

Sannan tashiga bed room din,kwance tasamesa ba Riga, ga uban gashi kwance a faffad'an kirjinsa.

Ta d'an tsorata dan bata saba ganin babba ahakaba, amma arantace oh ji mutum ko ina jikinsa gashi.

Da sauri tadawo bakin k'ofar shiga dakin ,ta bada baya ta shiga knocking ahankali.

Da addu ar tashi da ga bacci ,yafarka abakinsa, jin knock yasa yakalli k'ofa.

Amamakin sa yaganta tsaye ta bada baya.

Tsaki yaja yace ke lfy ,zakiyimun wani tsaye, meyasa kika dawo dakka tafi?

Batare da ta juyoba tace katashi magrib takusa, ga abincin da zakaci nan da dare ni xan tafi.

Haushin kansa yaji, da ya6a mata magnar da yayi,ashe da bata tafiba.

Ahankali yace muje na rakaki sarkin jin tsoro, kamar yason abinda ke ranta.

Dama sotake tace yarakata sbd tanajin tsoro,amma tanagudun fad'a masa ya disgata.

Jallabiyarsa yasaka ,yasameta a parlour ,nan yafito tabi bayansa ,

Wani gun amfara, kiran magrib,ahanya yace ke bakauya kincika tsoro wlh.

Sarai tasan Jan maganane sai ta sharesa, har gab da hostel yarakota, anan sukaga Pripet din da aka kora nashigowa da kyansu.


Kallon ta Yy yace ke ni nakoma, ahankali tace, Allah yak'ara sauk'i,saida safe.

Kallon ta Yy yace ameen ngd kinji, bejira amsartaba yyi gaba.

Ita kuwa daki ta wuce, tasami Fatima zata yi sallah Fatima, tace sis ina kkje tun dazu naketa nemanki.

Zama tayi tasanar da ita,ai sir Aliyu ba lfy, nan ta jajanta mata, Hafsat taje tyi alwalla tazo tayi sallah.

Washe gari byn sun gama shiryawa ,suka nufo area class, Aiko hadu da sir Aliyu xe bud'e office insa.

Nan Fatima ta ce lah sis ga sir can ze bud'e office yamaji sauki ,muje mu gaidasa da jiki.

Nan suka nufi office ,nasa bayan sun gaidashi sukamasa yajiki,suka fito,yaso yatsayadda Hafsat ,

Amma ganin ba ita1 bace yakyaleta.

********** bayan kwana2 sir Aliyu yawarware yasami sauki sosai,
Ya Tara Pripet, yasanar dasu kullum,sai sun share staffroom

Sun wanke toilet na malamai, sun share bakin get,

Kamar su mutu dan bakin ciki, bbu damar su Musa masa dole suyi,wani sabon tsanar Hafsat suka sake ji.

Yau Yakama talata, kullum sir Aliyu ,a step quarters yaje kwana ,amma yau saiyaji yanason kwana,

A office nasa sbd akwai bed room, aciki ,dan haka bayan isha,I yaje yakwanta can..

Da misalin karfe1:30 am,katti3 suka shigo skul din, kasancewar ba wadatattun masu gadi.

Gaba daya sun hargitsa skul in, sai ihu kato ake, ,students sun hade gu 1 bbu zancen wni Senior retie.

Atsakiyar makarantar inda suke ihun nan kattin suka zagaye su suka nuna masu wuk'ak'e, da sanduna akan sun atsu.

Dayan cikinsu ya kunna touch light, yana haska students koxaiga wadda ta yi masa,yabiya bukatarsa da ita.

Nan yafito da wata ss1 da ss 3 yasake haskawa cikin rashin sa,a yahasko Hafsat, atake yakwadaita da ita dan tanada kira me daukar hankali.


Fisgota yyi yanuna mata wuka, yafito da ita,tsabar kad'uwa saida Hafsat tasaki fitsari.

Atake students duka suka saki uban ihu ,kasancewar dare ko ina saida ya amsa.

Sir Aliyu kuwa cikin baccinsa ,yaga Hafsat tana kuka tana kiran sunansa yazo yatai maketa.

Atake yafarka ,yyi sharkaf da zufa ,dedenan Kuma yaji ihun students.

Da sauri. Yasaka jallabiyarsa ,afili yace skul din nan ba lfy wannan ihu haka, mlm rabe yakira, yasanar dashi su hadu a hostel dan bbu lfy.

Nan yace gashinan ,shima yaji kamar ihun students, kasancewar shima mlm rabe yana cikin step quarters na makarantar.

Da sauri. Sir Aliyu yafito yana haska wayarsa, jin ihun yyi yawa yasa yahada da gudu,

Yana shiga hostel din yabi inda yakejin ihun students, yana shan kwana, yahangosu sun cure gu1

Sannan ga wasu maza biyu da wukake ahannusu suna nuna masu.

Agefe Kuma ga wani yana cire kaya ga yaro 3 gefensa.

Innalillahi wa inna ilaihir raju, kawai yake maimaitawa atake yagane meke shirin faruwa.

Ai da sauri , yaciri wani rashe na bishiya dake bayansa batare da yaji tsoroba ,yasa wayarsa a aljihun wandonsa.

Da sauri yayi gunsu ,Dede nan dayan katon yyi gun daya daga cikin 3 dke gefensa.

Amamakin sir Aliyu ,sai yaji muryar Hafsat tana cewa wayyo Allah na yaya aliyu kazo katai makeni.

Kada suketamun haddi, yaya Aliyuuuuuuuuuuu!!!

Ai azabure had'e da fad'uwar gaba sir Aliyu ya ida isa kamar wani mayunwacin zaki,abunka da karfeffen mutum.

Hannu 1 yasa yadamk'osa ,sannan yasa ,reshen dayaciro yabugo sauran kattin dasuka nufosa .

Dan ceton dan uwansu,atake suka fadi kasa ,

Wani wawan punch yakaima na hannunsa a fuska ,yasake masa,

Atake bakinsa yafashe da hancinsa yafadi awahalce,

Sannan sir Aliyu yacigaba da suburbud'ar biyun dake kwance,

Akuma lokacin Hafsat ta fahimci sir Aliyu ne ,yakawo masu wannan agajin.

Da sauri ta buya abayansa tasa hannuwanta ta xagaye cikinsa,

Tana abayansa ,yacigaba da suburbudarsu, kamar actor nadukan yan gidan both lolx....

Duk students sunyi mmkin jarumtar si aliyu, shikuwa mlm rabe tsaye yyi yana ganin ikon Allah.

Dan bayan yafara dukansu yazo

Cikin 15 minit Sir Aliyu yabazar da kattinnan 3 nan mlm rabe yazo da igya ya dauresu.

Gaba daya Hafsat ta rud'e kuka kawai take, ta lik' e jikin sir Aliyu. Wai sai ya kaita gidansu ,kamarma bata hayyacinta.

Sai dukansa take akirji akan yakaita ita de gidansu.

Kok'arin rabata yake da jikinsa , amma sake manne mai take.

Mlm rabe ne yace mlm gsky bata hayyacinta ,tunda taki sakeka ,kaje da ita gdanka ta kwana ,

May bee ansan yadda za,ayi dasafe ,amma ko ka barta hankalinta bazai kwantaba,

Tunda dai k'anwarkace inaganin ba matsala.

Nan mlm rabe yacema students ko wacce ,ta tafi d'akinsu.

Fatima kukan tausayin.kawarta kawai take, haka ta tafi daki jiki ba k'wari.

Akan dole sir Aliyu ,yaja Hafsat ,kamar cingam suka tafi a step quarters.

Ko acanma babu yadda beyiba da ita akan ta kwana bed room, shi yatafi parlour.

Amma Hafsat tasa rigima ,ita gunsa zata kwanta,lura yyi da kamar bata hayyacinta yasa yakyaleta.

Ken bed din yakwanta tare da janyota Jikinsa ,

Yajamusu bargo,tareda shafar kanta ,itakuwa sai ajiyar zuciya take.

Wani kwance akan faffad'an kirjinsa,tasa hannunta daya ta zagaye cikinsa dashi.

Batafi minti 10 ba yaji tayi bacci, ahankali yazo kwantar da,ita gefensa, da nufin Yakima parlour.

Ai sai ta sake mannemai,aiba yadda ya iya haka suka kwanta.

Yanajinsa atakure dan betaba kwanciya da maceba a haka aayuwarsa sai yau.

Gaba daya tudin nashanunta sun tokaremasa kirji ga wani bak'on yanayi dayakeji atare dashi.

Addua kawai yake gari yawaye, lfy ko Hafsat tadawo tunanin ta,

Akan dole ya yard a su kwana gu daya dukda ya yarda da kansa, amma yasan shaid'an ze iya rays maka abu marar kyau.

Da wannan tunane tunanen bacci Yy gaba da shi,

Da misalin karfe5:30 am Hafsat ta farka da adduar tashi dg bacci.

Atake abinda yafaru yadawo mata, amma tyi zaton mafarki take.

Maido nefa akayi dakin yadauki haske ,kallon dakin tayi da sauri tajuya junta jikin mutum.

Kawai taga sir Aliyu kwance yana bacci, abinda yafaru jiya ta tuna.

Da sauri tabar jikinsa cikin jin kunya da ganin rashin dacewar hakan.

Ahankali yabude idonsa ,yaga Hafsat bata ,d'akin .

Da sauri yafito parlour, azaune yaganta tayi tagumi, ahankali,

Yace kintashi bata kallesaba tace eh ,yace jekiyi sallah lokaci yyi.


Tsakar gd ta fito ta yi alwalla a toilet, tazo parlour tayi sallah.

Bayan ta idar ,sir Aliyu yafito dg bedroom.

Yaxauna kan kujra , yakalleta, da sauri tace yaya ina kwana?

Lpiaqlau matsoraciya,turo baki tayi tace aide tsoro halak ne .

Tsaye ya mike yanufeta yana cewa kin rainani ko,

Da sauri ta zura aguje atsakar gd yarufa mata baya,su ka hau zagaye gdan.

Har hatsat tagaji da gudu ta koma parlour ta fada kan kujera tana maida numfashi.

Biyota yyi ,said hakuri take basa,yak'i sauraranta.

Zama yyi yajanyota kan cinyarsa ,ya matse mata hanci da baki.

Sai mutsu mutsu take yak'i saketa.

Can tasa hannunta a hamurtarsa tafaramai chakul kuli.

Da sauri yacikata yana dariya,had'e da aza kansa gefen wuyanta.

Har sajen fuskarsa na gugar gefen wuyanta, wani yanayi hafsat ,taji,

Da sauri ta kalli agogon bango tace yaya bara naje na shirya har 7 tayi kada na makara.

Nan ta tashi dg jikinsa ,tasaka hijab ta fito, bata kallesaba ,tayi ficewarta xuwa hostel....


Ina godiya ga masoya nida D'ALIBATAπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

Dan Allah masu bina ta PC akan natura masu dg farko pls kutambaya agrps dina zaku samu.

Share pls
[12/11, 10:07 PM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ23&24

Tana isa hostel tasami ,Duka malamai da dalibai, da police, antaru ga kattin nan zahiri suna a daure.

Nan principal tasa mlm rabe yakira mata sir Aliyu, ba bata lokaci yyi masa waya.

Ba,afi minti10 ba yazo, yasha kananun kaya sai zabga kamshi yake.

Gaba daya Kallo yakoma kansa , musammun ss3 kowace ji take inama yace ya k'yasa.

Nan malamai da principal suka jinjinamasa akan namijin k'okarin da yyi.

Sannan akatasa kattin gaba zuwa police station, dan ayi musu hukunci.

Sannan kowa ya watse ,Hafsat taje ta shirya suka nufo class itada Fatima.

*******
Yau Yakama Saturday, aranar Kuma ake visiting, kowa murna yake amma banda Hafsat dan tasan bazata ga yan gidansuba.

Sir Aliyu kuwa yana gidansu week end, zaune yake kan dinning area ga Kula's agabansa na abinci.

Yyi shiru yana ta tunani,mommynsa ce wato hjy Aisha ta fito ta na masa magna amma bejiba yana tunani.

Bubbuga table din tayi ,da sauri yakalleta yace my mommy.

Kallon sa tayi tace babana lfy me damunka kwana2 naganka kana yawan tunani?

Murmushi yyi yace no mommy ba komai, yanxunma zan wuce a skul nayi mantuwa,

Da sai dare zantafi, amma bari naje asamun abincin a basket.

Kallon sa tayi tace to, amma badan ta yarda bashida damuwaba.

Nan akasaka masa abincin a basket, yadauka, yasa agidan baya, yashige gaba yaja mota sai skul.

Hafsat na zaune a block din admin block, tana kuka harda hawaye.

Tunani take azuciyarta, tunda ta zo skul din bbu wani nata da yataba zuwa,wasu k'ayensu har ca suke basu taba ganin yan gidansu ba.

Saidai Fatima ,tace musu da safe ake xomata shiyasa.

Komai da ba Fatima suke amfani,ita tsoronta daya kada Fatima yau da gobe tagaza da ita.

Dukda bata tunanin Fatima zatayi mata hakan.

Amma tason dan Adam ,ze iya canjawa.

Sir Aliyu yyi horn aka bud'e masa get , yashigo yyi parking, yafito ra basket a hannunsa

Yanufi office dinsa ,ya bud'e ,yashi ga, ya zauna, tsintar kansa yyi da son yaga Hafsat.

Tashi yy dan yasan yau ake visiting, yanufi gundake da students ko xai ganta acikinsu.

Kamar ance yakalli gefensa, yahango Hafsat zaune tayi tagumi,tana kuka.

Yah salam! Yace afili da sauri yanufi gunta, ganin bata gansaba.

Yasa yarungume hannuwansa akirji yana Kallonta, k'amshin turaren sa taji da sauri ta d'ago kanta.

Idanunta tsab cikin na sir Aliyu, murya a sarke yace,hafsat ttttt!

Meke faruwa ,me Akamiki kike kuka haka?? Shiru tayi ,can Kuma tace ba komai.

Kallon ta Yy danbe yarda ba yasan da dalilin dayasa take kuka,

anacikin haka ,Fatima taxo. Nemanta ,tasame su tare da sir Aliyu, nan yakalli Fatima yace meyasa take kuka.

Fatima tace dan ba,azo mata visiting ba ,kumafa ba,a mata fashin xuwa duk month ,tayi masa karya.

Nan Fatima ta ce, dama naga ban gankiba nazo nan muna hostel kisamemu a can,

Bata jira amsartaba tayi tafiyarta cike da tausayin kawar tata.

Sir Aliyu yyi gyaran murya yace, dan ba zo miki visiting ba shine kke wanna n kukan.

Ai xasu zo,kobasuzo yauba zasuzo gobe da safe,kiyi shiru kinji kidena kukan haka nan.

Goge hawayen take wasu na sake zubowa,kallonta yyi fuska atamke yace .

Bazaki dena kukanba ko,wato ni ban isa kiji maganatabako, kinfi son kibatamun rai dankinga nadamu dake ko?

Da sauri ta girgiza kanta hade da hadiye kukan ,tace ,kayi hakuri na bari bazan sakeba.

Har cikin ransa yaji dadin maganar ta ,nan yace share hawayen.

Bamusu ta goge,yace muje ko,kallon sa tayi,yace yes muje, ba musu tabi bayansa har office.

Bayan sun zauna yace ta yi serving in su ,nan tayi serving a plate daya tatura masa gabansa .

Kallon ta Yy yace to bissimilla,nan suka faraci har suka gama batare da Hafsat ta yadda sun had'a ido da sir Aliyu ba.


Har ransa yaji Dadi daskaci abinci atare ,dan besan daliliba, yanajin farin ciki duk sadda suke atare ko suke cin abinci.

Bata kallesaba tace yaya natafi ,sai anjima, ji yake kamar yace ta zauna suyi fira.

Amma girman kai yahanasa ,ya furta,dan kada tama yimasa wata fahimta. Kawai sai yace

Ok sai anjima ,nan tafita, tayi hostel dan dama anxoma Fatima tun dazu.

Washe gari Monday , suna class after break ,aka turo wata ss1 ana kiran Hafsat Aminu a bakin get.

cikin mamaki Hafsat tabi bayan yarinyar,suna zuwa get me gadi yace gashi inji babanki,

Yana sauri yace abaki, baki bud'e ta kalli uban kwalayen da akace inji babanta da kaya Niki nik'i,

Kallon baba me gadi tayi tace gsky bani bace k'ila dai watace.

Harararta yyi yace kece mana, dama kwanaki yakawo sak'o abaki kikace wai bake bace ,amma kika karbe.

Dan haka in bakiso ,zaki iya tafiya ,jiki ba lakka ,ta kira wata mate dinsu zata wuce ,

Ta tayata suka kwashe kayan suka kai hostel , tana mamakin kayan.

Koda ta fada ma Fatima,ita wai ji take kamar ba,ita ake nufi ba.

Fatima ,ta nuna mata cewa,itace tason ko babanta yasami budi,Kuma ai bakomai ke tabbata ga dan adamba.

Da haka Fatima ta shawo kan Hafsat ,harta saki ranta.

Koda sir Aliyu yashigo class dinsu yalura Hafsat nackin farin ciki.

Dan haka yyi ta mata tambayoyi ,tana bashi amsa ,da haka har akayi ring in ,dazai fita yace su dage da karatu dan sauran 1 week exam....

Share pls

[12/12, 6:42 PM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ26&27

Washe gari, su Hafsat na class anata karatun exam,kasancewar ba teachers,sbd ankusa exams,sai noise aketayi wasu na karatu.

Can wani copper, yashigo yace duka class ,din suyi kneeling.

Nan yafita,yadawo da bulala,,yafara dasu Hafsat yan first sit,gaba d'aya ta tsorata,

Yanagamawa da Fatima ,yafara da Hafsat,hakadai ta daure, akayi mata har yafasa mata hannu.

Bayan yyiwa kowa ya fita , duk jikinta ba Dadi ga masassara ta sakko mata.

Nan Fatima ta kai ta dispensire,Dan akula da lfiyarta ,sannan tadawo,

Ahanyarta tadawo wa taga sir Aliyu bakin staffroom, da Hannu yyi mata alama taxo nan taje.

Dan yaga sadda takamo Hafsat ta rakata dispenser.

Bayan ta gaida shi, yadan matsa gefe ,yace dama Fatima zan miki wata tambaya 2 ne inafatan zaki bani amsar.

Nan tace in sha allah sir.

Kallonta yyi yace meke damun hafsat.?, nan ta sanar da shi dalilin ciwon.

Azuciyarsa yace k'ila jikinta beson wahala shiyasa duk sadda aka daketa sai tayi ciwo.

gyaran murya yyi yace nayaba da hankali,Kuma na lura hafsab batada,

K'awa,yar uwa,aminiya, sama dake,inaso kisanar dani wacece hafsat,? Kuma banason kisanar da ita munyi maganarta dke.

Shiru Fatima ta yi,da har zata boye masa,sai Kuma ta tuna da yadda yake taimaka ma Hafsat din.

Dan haka ba ,bata lokaci ta sanar da shi komai game da Hafsat. Harda sakin da mahaifin Hafsat yyiwa mamanta.

Kuma a yanzun Hafsat batason ina mamanta takeba saidai ta boye masa labarin deeni gidoga.


Ajiyar zuciya yyi cikin rudani ,da tausayin hafsat,din lallai hafsat tana cikin jarabawa,dole tayi kuka.

Ace mahaifinka anrabaka dashi,tana skul, betaba zuwa ba ko siyamata wani abu.

Kallon Fatima yyi, yace kada ki sanar da ita nasan komai game da ita kinji.

Na gode zaki iya, tafiya,nan ta barsa zai shiga office, ita Kuma ta nufo class da tambayoyi fal aranta..


A office kuwa sir Aliyu, zama yyi cike da tausayin hafsat,dan rashin uwa ga mace babban hadari ne ga rayuwarta.

Nan yakira mlm rabe a waya yace yatafo masa da doctor.

Ba,afi 15 minit ba sukazo da doctor din, nan sir Aliyu yace ma mlm rabe suje dispenser yaduba hafsat.

Nan yace to ,nan sukaje yarubuta mata mgani, mlm rabe yakaima sir Aliyu, yabashi kudi yasiyo.


Bayan antashi dg class, suka koma daki Kuma ta ji sauki ba laifi.

Pripet ne keta ringing dan lokacin dinning na rana yyi.

Dayake lebour ce on duty ,sai wani hauka take tana kora, har daki ,

Dakinsu hafsat ta shiga,batayi wata ,wataba, kasancewar tayi mugun tsanar hafsat.


Tacigaba da dukan hafsat da bulala wai tafita kitchen, ban tace bata lfy,sake dukanta tayi nan hafsat ta fito ta na hawaye.

Gaba daya sai taji skul in tafita aranta, taji gara taje gd inna Laure da abbanta suyita hantararta.


Fitowa tayi tabi layin mate insu, bata Dade da zuwa ba saiga sir Aliyu.

Jikinsa yabasa cewa ,hafsat na gun ,da sauri yabi layin mate insu yaganta.

Suna had'a ido ,tayi saurin sunkuyya da kanta,Dan ita , batasan yasan bata lfy ba.

Komawa yyi yazauna yana ganin yadda ake raba abincin,sai Wannan iyayi Pripet din keyi ko zai kulasu.

Amma basu sami hakanba,layi yazo kan hafsat,aka zuba masu har zasu wuce hafsat ta juyo ta saci kallon sa.

Carab suka had'a ido, alamayyi mata da ido tazo, nan ta tafi.

Gaidashi tayi be amsaba yakafeta da idanunsa, masu kwarjini.

Kallonta yyi yace yajinki, ahankali tace yaya ni lfiyata klau, ok xaki iya tafiya, yafada cikin basarwa had'e da nuna ko ajikinsa.

Itama data lura da yau sir Aliyu yan shan k'amshinsa sun motsa,sai tayi tafiyarta, dan itama yanzun bata son xuwa office insa ko yawan kebewa dashi.

Hakan najawo mata tsana ga waddanda suke son yarika kulasu,Kuma bataso suyi masu wata fahimta,dukda duka skul din daukar kanwarsa akemata.

Shikuwa sir Aliyu yaji haushin tafiyar datayi,azuciyarsa Yace zan dawomaki kamar da, dankinga nadamu dake.

Tunawa yyi be tambayi Fatima ,wanne gari suke itada hafsat.

Har zai kirata ,saiyafa komai yatuna oho.

***********

Yau laraba Kuma yau ake fara exam,gashi English ce farko,duk ss2 jininsu kan akaifa yake.

Dan sunsan sir Aliyu ko test ,shike tsarewa ayi ,Balle exam dinsa,Kuma da alama zaiyi muggan equations.

Anadawowa dg assembly, sir Aliyu yashigo class insu hafsat Yace duka sukoma assembly hole,anan ss2 duka zasuyi exam na English.

Ba bata lokaci ,duka ss2 aka halla ra ,yaraba masu equation paper,yaja kujera ya zauna.

Fuskarsa bbu alamar wasa,Yace duk wadda Yakama tana mgna zai kar6i paperta kobata gamaba.

Nan Yace su fara,shida hafsat suna satar kallon juna.

Aranta duk sai bataji dadiba ganin kwana2 duk sir Aliyu yanuna bedamu da itaba.

Ba bata lokaci suka cigaba da rubuta exam dunsu,abin mamaki hafsat ce farkon some meeting.

Ga yyi question da yawa,inbaki karatuba zakaci gidanku.

Koda ta gama ,kan dest din dayake zaune ta aza ,ta fita batare datace komaiba.

Hakafa su hafsat sukayi ta exam har suka gama, Kuma gobe Hutu,result finsu sai sundawo.

Sai parking kayansu suke duk students ana murna gobe kowa zaije gida amma banda hafsat.

Duk fargaba take ,gashi tasami kanta da kin jin dadin yadda sir Aliyu ya shareta,gashi

1 Comments On NIDA DALIBATA
avatar
isaitah-mujittapha

10 months ago

Reply

Masha Allah yayi dadi

Please Login or Register in order to submit comment