Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

taga yau kwana2 bata gansaba a skul din.

K'ila yakoma gidansu ko gidansa ,hakadai hafsat ta yini cikin damuwa.

Washe gari kowa murna yake ,anyi hutum,second term,4 weeks aka basu.

8:00 aka bud'e get students nata tafiya, wasu anxo daukarsu wasu nahawan motar haya.

Nan Fatima ,ta hango yaya Ahmad din gidansu da gudu tayi hugging nasa tana dariya.

Kallon sa tayi tace yaya ,ai nadauka bakai zakazo daukarmuba,murmushi yyi Yace to sarkin surutu,

Muje mana ina hafsat ma naga banganta ba,nan Fatima ta nuna masa gefenta ,

Tace gatanan, nan hafsat ta gaidashi ya amsa,yasamu su kayansu a boot ,

Suka shige mota, yajasu suka dau hanyar gd""""";;;;;;;


Sir Aliyu ne zaune a bed room dinsa dake gidansu,yana tunani ,yana ganin bedace yarika share hafsat ba.

Yau kwana3 kenan rabonsa da skul din ,yason yau ake Hutu, gashi yanason yaga hafsat kafin sutafi gd.

K'ila ma motar haya zata,hau wata zuciyar tace, ga Fatima ai tare zasu tafi,bazata bartaba.

Afili yace ,bari naje da kaina in nuna daukar ta ,naje dan kada ayi tunanin da Fatima ta dogara.

Musammun tunda ana mata daukar kanwata.

Da sauri yatashi ,yadauki car key yafita, awaiting parlour yahadu da mommy,

Da sauri ta ce babana lfy Wannan sauri haka,kamar zaka tashi sama.

Be juyoba Yace mommy zan dan karbi wani sako ne kiyimun addu ar ki ,

Murmushi tayi tace kullum inayi,saidai k'arawa.

Yana fita yaja mota atsiyace, dayake ba nisa sosai cikin 20 minit ya iso skul din.

Babu irin dubawar da beyiba amma ba hafsat ba alamarta.

Har yaci re jida kai yatambayi wasu mate dinsu hafsat cewa dazu sun ganta?

Nan sukace aisun fi 10 minit da tafiya itada Fatima.

Kallon duk mutanan gun yyi yagama ankusa watsewa, jiki ba lakka, yashiga mota,

Yanufi gd duk ransa ba Dadi,Kuma besan dalili ba,nikuwa nace dalili dan bakaga hafsatba......


Ashe haka masoyan NIDA D'ALIBATA suke da yawa,naga comments ba adadi agrps daban da ban,musammun, nida dalibata fans da nida dalibata fans grp 2 , kuyi hakurin jin. Bana yawan magana wlh sak' unna ssunmin yawa amma ina duaba comments dinku sosai, nagode love u so muchπŸ˜πŸ˜πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»

Share pls.
[12/12, 8:46 PM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ27&28

Su Hafsat ,suna isowa ,unguwarsu,ita yaya Ahmed yafara saukewa, skul bag inta da trolley inta kawai ta dauka.

Tana musu godiya ,Fatima nace mata zata shigo anjima.

Haka ta nufo gidansu gabanta na dukan Tara Tara, tayi sallama, bakowa atsakar gidan, ko ina yyi kaca,kaca.

Dakin da ake aje kayan tarkace ,Wanda da shine dakin mahaifiyarta,can ta nufa ta ajiye kayanta ta fito.

Dakin babanta ,ta nufa ganin ,takalmi ak'ofar dakin alamar yana nan.

Ta daga labulen dakin ta shiga ,kwance tasame sa kan dan tsohon gadonsa,da alama kamar bashida lfy.

Amsa sallamar ta yyi yana murmushi, hakan yaba Hafsat mamaki,sosai,taje ta duk'a gabansa tace baba ina kwana?

Fuska kalar tausayi ya amsa ,yace ,Hafsat naji Dadi da Allah yamaidoki lfy,Hafsat ki yafemun na zalinceku keda mahaifiyarki,

Da akabani amanarta,naci amana ,mamanki bansan inda ta tafi ba ,batada kowa garin nan.

Wasu abubuwan bana hayyaci nayi kiyafemun kinji ,alhakinku bazai barni inji Dadi arayuwata ba.

Cikin kuka Hafsat tace na yafe maka baba,Allah yabaiyana mana mama ,yasa tana cikin kyakkyawan yanayi aduk inda take.

Ameen yah Allah Yace cikin damuwa, sannan Yace bayan kin koma makaranta.

Tsautsayi yagibta min aka bankeni ,nasami karaya, akafa, tsakanina da Laure sai kyara da tsangwama ,

Ganin bana iya fita inne momusu wani abu, ko waddannan yaran shamsu da hanifa, ban isa insasu su taimaka suyimun wani abu ,

Sai Laure ta hana,tace ai ba abunda nike tsinana musu dashi, ita ke wahala dasu.

Kuma alokacin ne duk wani sihiri na jiki nah da Laure tamun yakare,sbd Wanda ya kadeni da mashin malamine.

Shiyabani taimako dana kariyar jiki, dukda abinda nayi ba a haiyacina nayiba.

Cikin tausayin babanta,Hafsat tace ba komai baba ,Allah yaba ka lfy.

Ameen yar albarka,ai nasami sauki,sai dan abinda ba arasaba tunda da sanda nike yawo......

Be rufe bakiba,inna Laure ta shigo kamar anjehota,bako sallama ta watsawa Hafsat wani mugun kallo

Tace to alhudda hudda sarkin karatu saiki fito ga aikin gd najiranki,ke me uba kinxo kun wani had'a kai ko,

To aibayada wani amfani yanakasa dukda nike ciyyadashi tunda beda zuciya.

Shiru Hafsat tayi zuciyarta na k' una , ta tashi, babanta Yace kiyi hakuri kinji duk tsanani yana tare da sauki.

Doguwar tsuka Laure taja,atsawace tace oya muje,ga wanki can kimun da wanke wanke,

In kin gama ki aza girkin rana,nan Hafsat ta fita dan yin aikin.

Tulin uban wankine,danata dana yayanta,harda na shamsu dan shekara 9,

Haka Hafsat ta zage taci uban wanki kamar jaka,

Bayan ta idar tayi wanke wanke, sannan ta aza girkin rana.

Dakin babanta ta koma ,ta gyareshi Ta's tahado kayansa masu datti ta wanke ta shanya.

Tacigaba da girkinta har ta gama ,tayi wanka,wata atamface tasaka red robber.

San taje gun inna Laure tace ,inna ina abincina?

Wani mugun Kallo tayi mata ta banko ashar ,tace eh ina abincinki ko ,

Tunda ubanki ya nemo ko,to akwai saura atukunya zaki iya tafiya ,ki kankaro.

Jiki asan yaye Hafsat ,taje ta kankaro abincin harda kanxo ,ta zauna ,ta fara ci.

Kamar dg sama saiga deeni gidoga yashigo gidan ,sai warin taba yake jiki na tsami.

Cikin muryar shi ta katti,yace ah my wife ,kindawo lfy.

Banxa dashi Hafsat ta yi, ta ida cinye abincinta ta tashi,saurin shan gabanta yyi ze tabata tayi saurin ja da. Baya taja tsaki.

Atake ta tuna da sir Aliyu, tasan da yananan bazai bari deeni har yayi yunkurin tabata ba.

Wani mugun kewarsa taji, sai taji kamar ta koma skul ta ganshi.

Muryan deeni ce tadawo da ita hayyacinta ,Yace miyasa kke guduna ,

Ai wlh inna Laure bazataci kudina abanxaba ,race Bakida miji sai ni,

Ko kiso ko kada kiso,deden nan babanta yashigo yana dogwara sanda,

Deeni naganinsa yabar gidan,nan tabi babanta dakinsa ,tayi masa sannu da wowa,

Yaga yadda dakinsa yyi kyau,ga wankin da ta yi masa, yaji Dadi sosai ,yaita sa mata albarka,

Yana mata sannu ,nan yabata fura da nono Yace ta dama musu,nan taje ta dauko kwano ta dama furar .

Bayan sun gama Shane,Hafsat tajita ta koshi tayi hamdala,

Suna nan zaune suna fira itada babanta, saiga inna Laure ta shigo,fuska ba yabo ba fallasa.

Takali Hafsat ta ce ke xomuje ga aya can gyad'a ki kaimun karshen layi ki siyar.

Wani mugun Kallo baba ,yawatsowa inna Laure ,cikin kakkausar murya ce,

Y'ata bazatayi tallaba ta girma haka ,aje a lalatamun ita,ki gode wadda ta yi miki abaya.


Cikin mamakin kalaman baba, Laure tace aiko saita dauki tallar nan dan bazan ciyar da ita a banzaba.


Tsaki baba yyi Yace meyahana kisawa ,shamsu ko hanifa tallar?

Aisu sunyi karanta, race ,afusace ,baba Yace ai itama Hafsat din tun kafin takaisu kke aza mata tallar.


Azuciyar Laure race dole in canja boka tunda mutumin nan nason fin k'arfina.

Afili Kuma sai ta harari Hafsat ta ce zakixo muje ko saina mangareki.

Muryar babace tadaki kunnan Laure ,yana cewa inhar kika samata talla wlh bakin aurenki.

Bakiji bud'e take kallon sa ,tace wai sbd yarka kke fadamun haka,

Yace ,eh Kuma ki barmun daki ayanxun.

Ai sai kaji tsit,su Laure ba bakin mgana, anji saki,dan tason kota rabu da Mlm aminu,

Da wuya ta shige ,ga batada hakoran gaba,sunxube ga goshi.

Haka ta fita tana ,mitarta, da zumar saita dau mataki.

**********

Bangaren sir Aliyu kuwa ,haka yakoma gd ,cikin son yaga Hafsat.

Ayanxun haka zaune yake, sai yanzun yafahimci yashaku da Hafsat sosai yyi missing dinta,

Lumshe idonsa yyi yana tuna in Hafsat tana cikin yanayin tsoro tafi kyau.

Murmushi yyi daya tuna lokacin da beda lfy duk ta rude harda kuka tayi.

,ga muryanta me sanyi hade da shagwabarta, muryan momi yaji tana cewa ,

Babana ko tasamu ne ,naga kana ta murmushi, kai daya.

Kallonta yyi Yace wani abun ban dariya natuna mommy shiyasa.

Hmmm banana kenan muje kayi lunch,tashi yyi yabai bayan ta.

Bayan 1 week

Hafsat ce zaune itada Fatima adakinta sunsaka kaya iri d'aya sunyi kyau musammun Hafsat.

Fatima ta kalli Hafsat ta ce oh sis wai baki jajan sir Aliyu, kin manta dashi.

Katsina fuska Hafsat ta yi tace to nikuwa tunawar me zanyi dashi,tunda agd muke ba a skul ba.

Murmushi Fatima ta yi tace amma sis. .labulen da aka daga yasata yin shiru.

Deeni ne yashigo ,ya kalli Hafsat Yace my wife xo ina son magana dake,ina fatan nikikayiwa ,

Wannan kwalliyar,doguwar tsuka Fatima taja dan tayi mugun tsanar deeni,

Da sauri deeni ya kalleta ,Yace ke dawa kke da kikeyin tsaki,

Agadarance Fatima tace da Wanda yatsargu da kansa nike.

Afusace Yace ke kishiga hankalinki wlh namiki shegen Duka ,inbatamiki wannan fuskar taki.

Mik'ewa tsaye Fatima ta yi race ,da allah mlm ka kama kanka dukana sai ruwan sama ,

Shima sai inna tsaya,katabani saikayi babban nadama arayuwarka,

Ai raggon nmj shike dukan mace,nan ta hau xaginsa da turanci da gayamai magana,

Itadai Hafsat batace komaiba ,tashige gaban Fatima ta na cewa ta kyalesa.

Shikuwa deeni kwa k'walwa bakomai sai iskanci bemajin me Fatima kecewaba yadai San turanci take.

Belt yake kokarin xarowa ahaukansa yadaketa baba yashigo Yace yafitar masa dg gida.

Fatima ta Kalli Hafsat ba yan baba yafita tace.

Wlh da sake haka kawai wani banxa yarik'a kiran ki da matarsa sai kace da gaske ke matar sace.

Cikin damuwa Hafsat ta ce to sis yazanyi shiyasa in ina skul hankalina kwance.

Nan Fatima ta ce ni natafi marece yyi,nan ta raka har k'ofar gdn su, takoma gd.


Da misalin 9:00 pm Hafsat ce kwance sai tunanin sir Aliyu take,takasa bacci,

Tana tuna bayason ganin wani ya zalinceta ko yaganta cikin kunci.

Ahaka bacci Yy gaba da ita,

Washe gari, bayan Hafsat tagama Duka aiyikanta tacema baba zata tafi islamiya .

Nan yyi mata addua ta fita,gidansu Fatima taje ta biya mata suka wuce tare...

Sir Aliyu ne kwance ,yana bacci amma Kuma yana murmushi.

Hafsa ce yagani ,wani suna tare sai was on guje guje suke suna dariya

Can yahango wani mutum baki k'irin bama a ganin fuskarsa,

Yatafi gunsu ,yasa hannu zai ja Hafsat ita Kuma tasaka ihu ta rike sir Aliyu.

Nan sir Aliyu ,yarika Jan Hafsat yanason rabata da mutumin amma taki saketa

Da kyar sir Aliyu ya kwaceta a hannunsa bayan yasha wuya.

Dede nan sir Aliyu yafarka yyi sharkaf da zufa....

Share pls.
[12/13, 9:19 AM] Aysha Galadima: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ29&30

Addu a yyi, yana tunanin anya Hafsat ta na lfy, kuwa,atake yatuna ,wancan mafarkin da yyi sadda katti suka shigo musu.


Kwata kwata yashi ga ko kwanto,haka yatashi ,yashige toilet yyi alwarla yafito yanufi masjid.

Yadade a can ,Kuma yasaka Hafsat a aduarshi Allah yasa ,tana lfy.

Sannan yanufo gd,yana tunanin labarin Hafsat da Fatima tabashi,sai yanzun yaga wautarsa dabe tambayi ,

Garinsu ko anguwarsuba,wata zuciyar tace to inkasanima,inkaje kacemusu me?

Matsayinka na medinta ,zakaje afilili Yace a malaminta.

Dede nan yashi ga parlour, tunkan ya ida shigowa yakejin kabeer ,k'aninsa me bi masa.

Yana waya da mace sai wannan lallabata ,yake yanacewa baby kada kidamu zanshigo anjima ,kimun kwalliya kinji.

Ilov.... Duguwar tsukar da sir Aliyu yaja ne ,yasa kabeer kin karasawa ,yyi saurin kashe wayar.

Yana Sosa kai, harara sir Aliyu ya aiko masa da ita ,tare da cewa tsoron Allah zakaji ba mutum ba.

Wai duk Dan alsbd mace kake wannan rawar kan ,hmm indai matane gaka gasu.

Mommy ce ta karaso,Dan duk tanajinsu,dariya tayi tace ah ah babana, kabarshi yyi soyayya,

Tunda kai bazaka yiba,sai kazama tuzuru munbada kai sadaka, ai kabeer ya isa fara kula mace,

Yanada 27 years ace bazai kula ,mace ba, dukda kaimai 35 kaki aure,dukda kai kaso,

Hade rai yy Yace to nidai mommy abar maganar, shikuma ,yaje yyita soyayya, anacikin haka,sa ada ta shigo dawowarta kenan dg islamiya,

Ta fada jikin sir Aliyu, tare da cewa ,yaya nagaji,wlh, dan tureta yyi Yace to sarkin son jiki,

Tunda kin gaji saiki sauketa akaina ke bakison kin girmaba,turo baki tayi tace yau wa yaya,

Wai ina wannan Hafsat din take?

Atake yaji gabansa yafadi, amma dayake jarumine ,be nuna hakanba, agundure ,Yace oho ,aidayake da ita zanrika yawo,bacin kinsan anyi Hutu.

Lah hakane yaya ,amma gobe tunda Tuesday muje ka kaini gidansu inaso tazama kawata.

Hararanta yyi Yace surutunki marar ma,ana ya isheni, dan tana dalibata ,dole sai nason gidansu.

Juyawa yy yanufi. Part dinsa, yabarsu, nan ,mommy ce ta kalli sa ada ta ce ,wacece Hafsat ? Kuma.

Sa ada ta ce, dalibarsace ,mommy kinganta kyakkyawa ta hadu karshe wlh,

Shiru mommy ta yi tana tunani ,anya ba akwai wani abu ba ,dama ta lura kwana2 nan Aliyu na yawan tunani ,kodai so yakamashine?


Hmmm kodai minene zan cigaba dayimasa addu a,""";;;;

***********

Hafsatce zaune a tsakar gidansu ,tagama ayyukanta ta gaji sosai ,ga girki a kicin data idar.

Inna Laure take jira tazo ta raba amma ba ta fito ba

Tana zaune anan baba yashigo,yanata fara a,fuskarsa shar da farin ciki, yanzun yaji sauki banda sanda yake yawo.

Yakalli Hafsat yace sannu yar albarka,kinji,murmushi tayi ta masa sannu da zuwa,tace babana,

Da alama yau kana cikin farin ciki, yau Yace kedai bari, yau nasamu jarin da zandogara da kaina kema na miki abinda kkso.

Murmushi tayi tace Allah yatai maka yasa alkhairi, cikin jin Dadi Yace allahumma ameen.

Inna Laure ta fito dan ta labe bakin window taji duk abinda suke cewa,

Tace Ashe ansamu abinyi shine kk'i fad'amun sai yarka kke fadamawa,to ai naji dg gobe ,zakaci gaba da kula da gidanka,

Kuma ka biyani kudin da naciyar maka da yara,ehe, ko kallon inda take baba be yiba,yashe daki yabarta nan.

Hafsat itama ta bisa,ai sai Laure ta hau aika mata da zagi da tsinuwa,


Sannan ta ce kinja ma kanki, bazakici abincinnan ba dukda ke kika girkasa.

Adaki baba da Hafsat sun ba banxa ajiyar ta sunshareta sai firarasu suke.

Can Hafsat ta ce baba bara naje gidansu Fatima,murmushi yyi Yace adawo lfy tasaka hijab ta fito.

Inna Laure dke cin abinci tayi dariyar mugunta hade da hataran Hafsat tace to yawan maular za ako,

Saidai kije can kyaci abincin amma bawai na gidan ubankiba,

Itadai Hafsat batace komaiba tafitarta,tanama inna Laure,adduar shiriya.

A parlour tasami Fatima,da ummanta suna Kallo,da gudu Fatima ta yi hugging in Hafsat suna dariya.

Hafsat tagaida umma,ta amsa cikin sakin fuska ,nan Fatima ta ja Hafsat ska tafi dakinta.

Suna shiga Fatima ta bude wardrobe, ta fito da yunifoam da checks, dinkakku tace sis ga kayanki dazu aka kawosu dg gun dinki.

Umma ce ta dinka mana, cikin jin Dadi Hafsat ta ce ,nagode Allah yasa ka da alkhairi, Baku gajiya da mun hidima,meye zanyi insaka muku sis keda iyayanki.

Murmushi Fatima ta yi tace, kibarmun godiya ,dan bbu ita tsakanunmu,nadaukeki,yar uwata ta jini.

Murmushi Hafsat ta yi tace, Allah yabar zumunci,nan Fatima ta kira me aikinsu ta kawo masu abinci sukaci tare da Hafsat.

Bayan sun gama, Fatima ta ce, sis hutufa yakusa karewa sbd ke ma zamu koma ,ka,ida ko kin huta,

Da jarabar Laure da deenin bantsarnan.

Hafsat tace eh nasani ai gara mukoma ka,ida zai fi gaskiya, Kuma kinga ,

Wahalar mu tazo karshe damun koma third term za a bamu shadows babu batun xuwa compound,

Hankali kwance kayita karatunka,eh wlh sis nan suka ta6a ,sai gab da magrib sannan Hafsat ,

Ta fito tayima umma godiya sosai sannan taje gd,

Bayan1 week

Yau yarage jibi su Hafsat zasu koma a skul,mlm aminu yyi mata provision nagani nafada yasa adakinsa yarufe sai ,

Sai ranar da zasu koma zai fiddo mata sbd yasan halin Laure zata iya sace kayan.

Hakan yyima Hafsat Dadi,dan yanxun jinta take kamar ko wace y'a.

Damuwarta ,daya shine sanin halinda mahaifiyarta take cikine.

Saidai ita da babanta basu sareba dayin addua ba dare ba rana akan allah yabaiyanata.""""


Alh Suleiman rabone ,wato senator zaune a dining area shida iyalansa suna cin abincin .

Dayake duk dare gaba daya sukeyin dinner.

Sa ada na kusada dadtnta tana shagwaba,

Daddy yy gyaran murya Yace wai aliyu yaushe zakayi aure ne wai?

Nagaji da ganinka a haka duk randa ka cikamun ciki,sadakarka zanbayar kaji nagaya maka.

Sosa kai yyi Yace daddy adan k'aramun lokaci,zan fitar.

Itakuwa sa ada sai dariya take jin wai za abada sir Aliyu sadaka in be fitarda mataba.

Sir Aliyu yadago yawatso mata kallon zamu hadu, murguda masa baki tayi,

Atake ya tuna Hafsat,dan itama akwai murgud'a baki.

Murmushi yyi da yatuna jibi ake komawa ,Hutu,, mik'ewa yyi yanufi part dinsa.

Yason yakusa ganin Hafsat dan yyi kewarta da yawa,wata zuciyar tace kasan koba jibin zasu komaba.

Sai sun kara 1 week ,atake murnarsa takoma ciki, amma yadau alkawarin xuwa jibin in basu dawoba to sai yadawo gd.


____________

Yau asabar Kuma gobe su Hafsat ke komawa, zaune take tana daka yaji a turmi.

Gasu kuli da mai a gefenta cikin roba ,tanata dai shirye shiryen ta.

Tana tuna k'ila gobe kamar yanzun suna skul ,k'ila ma taga sir Aliyu.

Batason sadda tayi murmushiba,said tsintar muryar deeni tayi yana cewa,

My wife da alama kinfara sona gashi kina murmushi da kka ganni.

Doguwar tsuka taja rai bace ,tace kai wawa ,jakancinka ya isheni haka nan.

Kada kasake kirana da matarka, dan bazan taba zama mallakinkaba .

Laure ce ta fito zani a hannu cikin masifa tace karya kke wlh Bakida mj sai deeni.

Ki rubuta ki aje na fada Miki wlh, dariyar bosawa deeni yakece da ita ,

Yace lallai yarinya wuyanki yyi kauri ,nikike gayama magana haka,hmm ai wlh koban aureki ,

Tabbas sai na lashi zumarki kota halin kak'a,dan kudina bazasu tafi abanxaba.

Laure tace kada kada kadu ,batada miji saikai,aitakusa gama Wannan k'addararrar makarantar.

Muryan baba sukaji Yace ,gsky kunyi kyan kai kedashi ,

Inaso kusani ,bazan aurawa y'ata dan iskaba sai mutumin kirki, Kuma bazan mata auren dole ba.

Maganar karshe kada kasake shigomun gd,yakalli Laure Yace ,

Ke Kuma kibi sannu da duniya, duk randa ta huta miki baya bazakiji da dadiba.

Ashe ke deeni ya kalli baba Yace ,wlh daukewar numfashi kawai zata hanani shigowa gidan nan,

Amma gani canma nashigo, murmushi baba yyi Yace allah yabaka sa,a.

Nan deeni yafita afusace yabar gidan,inna Laure tashige daki tana surutanta.

Baba yakalli Hafsat Yace kashe kayan kikai daki tunda kin gama .

Ki kyalesu kada kidamu ai nine mahaifinki ko to bazan badake ga deeniba.

Nan ta kwashe kayan ta bi baban daki, tashirya komai da komai nata tafiya kawai take jira.


Ina mika godiyata ga duk masoyana aduk inda suke ,inaganin comments da godiya da addua agareni ,nagode sosai ina mugun yinku irin sosai dinnan.😍😍🌹🌹

Love u allπŸ’‹πŸ’‹

Share pls[1/3, 2:23 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa


πŸ…Ώ31&32

Washe gari ,bayan duk Hafsat ta gama abinda take tashirya kayanta tsab a trolley.

Lokaci kawai take jira, yyi dan da karfe4:00pm,zasu koma skul din.

Bacci taje tayi bata farkaba sai, 3:00pm ba bata lokaci ta shirya cikin check pink dinta.

Tana fitowa dg daki Fatima nashigowa,tace sis kinde gama had'a kayanko?

Eh Hafsat tace,nan takama mata suka fito da kayan driver yasa a boot,suka shige mota, yajasu,suka dau hanyar skul.

6angaren sir Aliyu kuwa,beson daliliba yau yanajinsa cikin farinci,karfe 4 a skul dinsu Hafsat tayi masa.

Dede bakin get yazauna kusada baba me gadi,yatsare k'ofar get din da ido.

Ba a fi,30 minit ba da zamansa ,saiga su Hafsat da Fatima suna shigowa da kayansu.

Kwata kwata Hafsat bata lura da sir Aliyu ba ,shikuwa yakafeta da mayun idanunsa, yana Kallo.

Can tana kokarin komawa tadakko wasu kayan dan har Fatima ta koma,kamar ance ta juyo jin kamar kamshin turaren sa, da sauri tawaiga carab idanunta cikin na sir Aliyu.

Gaba daya yakasa dauke idonsa akanta,ita kuwa sunkudda kanta tayi.

Cikin husky voice insa Yace ke zonan ,shiru tayi batace komaiba, yasake cewa bazakizoba ko?

Turo baki tayi tace sunana Hafsat,murmushi ya kubce masa dama zolayarta yake,ganin ga baba me gadi yasa yarabu da ita.

Fatima ce ta dauko sauran kayan nan ta ga Sir Aliyu, tagaidashi,sannan yatashi dg bakinget yanufi office.

Hafsat data dauko sauran kayan,tasaci gundayake zaune da Kallo taga wayam bbu sir Aliyu.

Tsintar kanta tayi da kinjin n dadin tashin da yayi.

Jiki ba lakka suka koma hostel dan jera kayansu,Fatima na lura da ita kamar tana cikin damuwa.

Shikuwa sir Aliyu gd yakoma sai Monday zai dawo.

Washe gari, suna gaban class zaune Hafsat ta hango sir Aliyu zai bude office dinsa.

Da sauri ta tashi ta karasa,bakin office din,cikin sanyin murya tace yaya ina kwana.

Harararta yyi Yace kirik'e gaisuwarki ,kinji,ko?

Kallon sa tayi tace yaya miyasa?

Tsaki yaja yashige office dinsa yabarta tsaye.

Cikin jin haushin barinta da yyi ta koma class dinsu.

Bayan kwana2 ba laifi students andawo,skul din takara yawa.

Su Hafsat na tsaune a class ,saiga wani guy ba laifi yahadu yaci wankan kananun kaya, Kallo daya zakamasa kasan beda kunya waishi kamal.

Yashigo bayan sungaisa da class yyi introducing din kansa,akan ammasa transfer ne ,zai rik'a daukarsu chemistry.

Sai wani kallon yan matan class din yake yana wani murmushi, can yahango wata ,budurwa Yace wow baby yasunanki?

Wata had'add'ar murya mai zaki' hade da taushi yaji tace pls uncle ba tambayar suna zakayiba ka fara mana abinda yataramu anan.

Da sauri yajuyo yakalli Hafsat,a azuciyarsa kuwa cayake wai allah yaxuba halitta anan wannan kyau ,kamar aljana.

Cikin iyayi yaketa kallon Hafsat Yace ok ba damuwa.

Yatsina fuska tayi dan ita kwata be kwanta mataba,ita tama k'agara yagama yafita sir Aliyu yashigo.

Dan da yafita zai shigo,haka yaci gaba da explanation, Rabi yana kalle yammata.

Amma yadarsa wani nufi aransa game da Hafsat.

Har ringing anyi amma yaki fita,saima ya matsa gun sit dinsu Hafsat, yanabinta da shu ummin kallon.

Dede nan sir Aliyu yanufo class din dan prieod dinsa ce,kawai yahango sabon malamin da aka gabatardashi dazu agun sauran teachers.

Gaban sit dinsu Hafsat yana mata shu umin kallo, damashi sir Aliyu hakan yaji be masaba sadda aka nunama teachers.


Wani abu yaji yatokare masa kirji atake yaji mugun tsanar uncle kamal ta shigesa.

Shikuwa kamal sai kallonta yake Yace tabasa not book dinta ze duba wani abu,kafin Hafsat ta ce wani abu, Fatima ta ce ,uncle ga sir nan awaje kai yake jira kafita dan kashiga period dinsa.

Kallon Fatima yyi azuciyarsa Yace kema xamuje dake .

Nan yafita,yakalli sir Aliyu yabashi hannu sukayi musabiha yayi tafiyarsa shikuma yashiga class din.

Fuska a tamke bbu wasa dan yau miskilanci ya motsa ko tambayarda yake mata be mataba .

Haka yyi lesson ,kowa ya natsu sosai gudun kada yasa mlm rabe ya suburbud'esu,haryafittta ta be kalli inda Hafsat takeba.

Itakuwa fushi take dashi ,kan disgin da yyi mata washe garin dasukadawo skul.

Bayan antashi ,su Hafsat na bakin tape ,sir Aliyu yazo zai wanke hannunsa ,tana ganinsa da sauri tabar gun.

Shikuwa mamakinta yyi ,nan yatabe baki yawanke hannunsa ya wuce office.

Haka akayi kusan kwana4 in Hafsat taga sir Aliyu saitabar gun in Kuma class dinsu yashigo bata kallonsa kota yarda su had'a ido.

Tun abun be damunsa har yafara tambayar kansa ,wai me yarinyarnan take nufi ne wai?

Wata zuciyar tace kashareta kaima,wata tace tokodai kayi mata laifi ne .

Tashi yyi ya lek'a window ,atake yaji gabansa yafadi, ganin uncle kamal yana kokarin tsaida Hafsat ita Kuma zata class nasu .


Da sauri yazagayo yaga tatsaya suna nesa da juna,fuska adaure yakarasa gunsu,ko kallon kamal beyiba ,Yace ke xo nan.

Da sauri kamal Yace mlm yi hakuri zan aiketane,wani kallo sir Aliyu yawatsowa kamal,

Atake yasha jinin jikin sa sbd sir Aliyu akwai kwarjini,

Cikin isa da bada umarnin sir Aliyu Yace ,bana bukatar sa insa dakai dan kai basa ana bane,Kuma da ba,itace bace katsaidaba bazan kulakuba daga Kai har ita.

Harara ya aikama Hafsat Yace ,kifada masa matsayina agunki.

Hafsat takalli uncle kamal tace ,Yayana ne...

Doguwar tsuka sir Aliyu yaja Yace ,oya kiwuce kitafi class kafin na sa6amiki.

Nan tajuya tashiga class ,nan sir Aliyu yawatsawa kamal wani kallon kyama yawuce abinsa.

Shikuwa kamal yatsorata da sir Aliyu Kuma yadauka yayanta ne uwa daya uba daya, dan har wani kama yaga sunayi.


Sannan yaga kaf malamai bbu Wanda yyi haduwar sir Aliyu da ita wanka,da hawan babbar mota.


Azuciyarsa Yace anya gara kawai na rabu da yarinyarna danko mun gwada k'wanji dashi da alama ni zansha wuya dan dg gni karfaffane.

Da wannan tunanin yatafi staffroom.

Ana tashi braek sir Aliyu yanufi kitchen yaja kujera ya zauna ,yana kallon yadda ake raba abinci,

Can yahango Hafsat da hannu ytimata alama tazo,nan taxo ta duk'a gabansa,

Kallonta yyi Yace daga yau kada insane ganinkin tsaya da wannan yaron kina jina koya kira ki kice masa na hana ki, xuwa .

To tace ,amamakinsa yaga hawaye da sauri Yace mene kike kuka fadamun me aka miki kinji??

Turo baki tayi cikin shagwaba ta ce bakai bane ka disgani sai Karina shareni.

Murmushi yyi jin ba wani abu bane kedamunta,ba ahankali Yace to naji nadena shikenan ko?

Shiru tayi,Yace hhafsatttttttt!

Kallonsa tayi tace share hawayen kidena saurin kuka kinjiko?

Share hawayan tayi yace yauwa kokefa to yi mun murmushi kinji.

D'agowa tayi suka had'a ido ,atare suka sakarma juna murmushi.

Ahankali Yace ,sa ada na gaidake sosai.

Murmushi tayi tace lah yaya ina amsawa ,nima ina gaida

1 Comments On NIDA DALIBATA
avatar
isaitah-mujittapha

10 months ago

Reply

Masha Allah yayi dadi

Please Login or Register in order to submit comment