Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abu ga masoya saigashi yashawo kanta,hartahakura tamasa rakkiya hade da cewa sa'ada ta gaidamata mommy.

Sannan yaja motar suka bar anguwar.

Washe gari da misalin karfe 9:am sir Aliyu zaune kan carpet gaban daddy yazo gaidashi.bayan sun gaisa daddy yace kaga lokacin bikin nan yadan matso tunda saura3weeks yau xanje Dubai da mommy nku muhad'a lefe daganan muje Egypt mutaho da marar lafiyar nan a maodota gidan nan akwai wani doctor da zaixo yasake bincika rta. Shine nikeso ko inmuntafi ko bayan mundawo kaje gidansu yarinyar nan kuga juna kakuma gaida mahaifinta.

Wani fad'uwar gaba sir Aliyu yaji da Bacin rai jin maganar auran nan na nandai.

Jin yyi shiru daddy yace ina sauraronka ,inmuntafi zakaje ko kuwa sai bayan mundawo dg Dubai?.......

Share pls
[1/7, 11:22 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

Wannan page din nakune amintattun mata writer's association, tareda muhad'a kanmu writers, association.kuyi yadda kuke so dashi.. Kunfi kowa son nida dalibata nagode sosae da kaunarku agareni ,ana mugun tare.πŸ‘πŸ»πŸ˜πŸ˜

πŸ…Ώ91&92

cikin k'osawa da maganar yace daddy inkun dawo zanje tunda yau zaka tafi nikuma bansan gidanba.
"kuma suma ba su sanniba", murmushi daddy yy yace zasu sanka very soon Allah yakaimu sai insaka cikin body guards dina wani yyima ka jagora tunda sunsan gidan".
Atak'aice yace to had'e da barin part din,yanufi nasa part din.
Axuciyarsa kuw a cewa yake ko naje bazan sakan mata fuska ba dan kada yarinya ta kamun raini ,k'ila ma hafsat ta fita komai. Dukda nasan bazai zabamun marar tarbiyaba.

"" tsaki yaja hade da shigewa bath room dan yanason yaje ya kai Hafsat gun stea ming."cikin yan mintina yafito da kananun kaya sai k'amshi yake yanufi gun mota yashiga yabar gidan.
Ahanya kuwa sir Aliyu sai tunani yake ga wani kishin Hafsat dke tasomas a,yakudurta aransa duk ranar da yataradda wannan gajan da akace zata aura sai yamasa rashin mutunci k'ila ma yasuburbideshi saidai komai zai faru yafaru wlh.
"da wannan tunanin ya iso anguwar", fitowa yyi dan besan shiga cikin gidan sbd Laure kada wata rana taja masu sharri shida Hafsat dinsa."";;

" befi minti biyarba yaga Hafsat ta fito."

Kasancewar tun dazu ta ke jiranshi tunda jiya yace zaizo yau suje gun steaming din.

Tun kan ta ida isowa suke aikowa da juna sak'on mur mushi.harta ida isowa ,"ta kallesa hade da cewa Yayana ni kadai"!
dariya ta basa s hima yace Hafsat dina ni kad'ai.lumshe idanunta ta yi tace ina wuni?
"Ahankali yace lfy ." ina fatan bbu wata matsala ko damuwa ko?sunkuyadda da kanta tayi tace inada su Duka!cikin damuwa yace dan Allah kidena damuwa kibarwa Allah kinji?
Cikin shagwaba ta ce Aina hakura ya nxun Kaine damuwar banason inrabu dakai koda da minti dayane.tafad'a had'e da fashe masa da kuka .
Gaba daya ta d'aga masa hankali.
"Ahankali yaja hannunta yabud'e mota yasakata shima yaxagaya yashiga yatada motar",cikin rarrashi yace indai nine ba damuwa zandunga xuwa gidanki muna gaisawa kinji?yafad'ane dan tayi shiru amma bazai taba aikata hakan ba.

"da sauri tace dgaske kake yaya"?

" d'aga kansayy alamar eh."

Batare da yakalletaba yace muje yanzun agyaramiki gashinko tawan?

Murmushi tayi tace to Yayana ,dama inason ince kakaini sai gashi ka xoma da maganar ,murmushi yyi yace jikinane yabani kinason muje na kaiki.

"Ahankali tace duk lokacin damuke tare inajin kaina cikin farinciki ,pls yaya kada kak'i cikamun alkawarinka na xuwa gidana kullum had'e ransa yyi dan saiyaji koma tanason auren tunda har ta ke cewa wani gidanta. Fuska ad'aure yace yaron da akace zaki aura yafara xuwa kuna xance dashi ne?yafad'a had'e da kafeta da ido yanason jin amsarta cikin damuwa tace ah ah betaba xuwaba.
Wata ajiyar zuciya yasaki wadda besan ta fito filiba ." da sauri ta kallesa amma sai ya waske ."
Bayan sun iso da kansa yarakata yakoma mota ya jira har aka gama.sannan yabiya kud'in da besan adadinsuba yabiya mata,itakuwa matar ta karb'e tana godiya.

dg gun steaming suka wuce yyi mata shopping ,sannan suka dawo gida ,sai murna suke da farinciki, dan in suna tareda juna suna manta cewa wai sunada damuwa aduniya.

Nan sukayi sallama sir Aliyu yawuce gida cike da kewar hafsinshi.

****** ***** ******
bayan kwana ukku har daddy yadawo da mommy kuma sun dawo tareda mairo wato mahaifiyar Hafsat.

""" sun had'o kayan lefe nagani na fad'a anjeresu part din daddy washe gari zasukai gidansu amarya Hafsat."
Shikuwa uban gayyaar baya gidan lokacin da suka dawo ,yanzun haka shi ake jira yazo yaga kayan sannan daddy yasa guard dinsa yakaisa gidan mlm aminu.
Domin yagaidashi yaga kuma amarya Hafsat,dan har daddy yakirasa yashai da masa yau dansa zaixo yagaidashi.

"Mairo kuwa part daban akaware mata itada masu kula da ita."

Sir Aliyu bedawo gidanba sai bayan azahar,yasami su mommy a waiting parlour, bayan yyi mata sannu da zuwa ne .
"ta kallesa tace kaje kayan lefen na nan part din daddynku kagani sannan ka shirya da la'asar zakuje gun surikar tawa ,taf'ada cikin xolaya dan tasan ta k'ular dashi.
Yatsina fuska yyi yace haba mommy ni basai naganiba.sa'ada dke gefe tace eh wlh yaya kadama kagani tunda ba Anty Hafsat bace za'akaiwa lefen!da sauri mommy ta mata dakk'uwa ,sa'ada tayi shiru. Mommy ta kallesa fuska ad'aure tace wannan umarnin mahaifinkune banason musu maza kaje kagani kadawo ka shirya .yauwa inkadawo kuje Duka harda kabeer part din marar lfyar nan kuganta.

" to kawai sir Aliyu yace yanufi part din daddy. "

Fuska bbu yabo bbu fallasa yaga kayan ,sannan yafito dan shiryawa amma yanajin mugun fad'uwar gaba.

Bayan ya shirya cikin fararan suit fuskannan atamke bbu walwala ko fa'ara yafito yasami guard din zai kaisa a parking space. nan yashiga gidan baya shikuma guard din yaja motar.

"" tunda suka fara nufar anguwar kawo gabansa yacigaba da fad'uwa."

Bangaren su Hafsat kuwa adole baba yasa ta share soro ta shimfid'a tabarma babba ,sannan taje ta shirya rai bbu dad'i dan ta d'auniya niya saita masa rashin kunya kowane mugunne dakeson sanadin rabata da farin cikinta.
Haka ta shirya cikin arebiant gown dark blue, kuma sir Aliyu ne yasiya mata ita.
Shikuma baba hard a siyo swan water da exotic da za'a tari bak'o dashi.


Shikuwa sir Aliyu ganin sunshigo anguwarsu Hafsat yasa yakalli mutumin da sauri yace wai banganeba ina zamufara xuwane tukum?

Cikin girmamawa yace ranka yadade' ai nanne anguwarsu amaryar taka ga kwanar gidansu can,yafad'a yana nuna kwanar gdn su Hafsat.

Cikin kin yarda da maganar da yace wai ina wasa dakaine kafadamun yadda zan fahimta.

Cikin ladabi yace wlh nan anguwa r take,alokacin yyi parking agaban gdn, kuma Dede nan mlm aminu yafito da ga gidan.

Nuna masa mlm aminu yyi yace kaga mahaifinta can ma tsaye .....

Share pls[1/7, 11:22 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story&written by mmn fareesa

Ina mika godiya ta ga dukkan masoya nida dalibata comments hade da sharhi na jiya yafi na kullum kuyi hkuri wad'anda banmusu reply ba a PC ,amma nagani inajin dadin hakan nagode inamugun jidaku. Anatare🀝🀝

Dedicate to all my fans

πŸ…Ώ93&94

Tsantsar mamaki yahana sir Aliyu magana ,saimurxa idanunsa yake yaga ba bacci yakeba .ha nnunsa yasa abaki ya gartsa,atake yagane ba mafarki bane d gaske ne.amma tambayar kansa yake yahakan ta faru?karar bud'e motar da guard din yyi yafita shiyadawo dashi dg tunaninsa."ahankali shima ya fito",,suka nufi gun baba,baba kuwa mamaki yake ganin sir Aliyu tareda guard din senator ,tambayar kansa yake to ina aliyu yasansu? Kafe aliyu yyi da ido atake yahango kamannin senator a fuskarsa.dan tundayake da sir Aliyu sai yanzun yyi masa kallon tsab."isowarsu tadawo dashi tunaninsa."guard dinne yafara gaida baba ,sannan yace dama y'allab'ai yaturoni nayiwa ogah jagora yazo ya gaidaku !kallon sir Aliyu yyi yace ogah inajiranka amota inkun gama."bejira amsarsaba yyi gaba cikin tsananin farin ciki had'e da murna sir Aliyu yaduk'a yakwashi gaisuwa gun baba.baba cikin al'ajabi had'e da mamaki ya amsa tare da cewa aliyu mushiga ciki muyi magana dan har yanzun ina cikin duhu maganar bata nan bace ." muje ciki",bbu musu sir Aliyu yabisa a soro. bayan sun zauna baba yyi gyaran murya had'e da cewa dan Allah aliyu yimun bayani yadda zan fahimta.sir aliyu da bakinsa yak'i rufuwa dan murna ."ahankali yace baba da farko wanene kabawa auren Hafsat."bbu boye boye baba yasanar dashi yadda sukayi da senator. "Murmushi sir Aliyu yyi yace to baba nine dai aliyu dansa kuma ni yanemawa auren Hafsat". Ajiyar zuciya baba yyi had'e da cewa alhmdllh ala kulli halin.

"" agaskiya Aliyu naji Dadi kuma Nayi farinciki daka kasance Kaine zaka auri Hafsat."domin kafin mahaifinka yaxo anguwarnan har yaga Hafsat yaso nema maka aurenta wlh kai nikeda niyar cemawa inba matsala xanbaka ita dan nayaba da hankalinka da tarbiyyarka d'ari bisa d'ari to sai haka ta faru ,ashekuma Kaine mijin ,ubangiji yasa alkhairi da albarka da aurenku.

"Cikin jin kunya sir Aliyu yace ameen."

Mik'ewa baba yyi yace bara na turomaka ita dan bazan sanar da itaba ,idonta yanuna mata, nan yyi cikin gidan.

Hafsat dke d'aki ranta adagule jira take baba yakirata taje taga Wanda akace zata aura tayimishi rashin mutunci.

Kawai saiga baba yashigo bakinsa kamar gonar auduga dan murna "kallon Hafsat yyi yace kije yana soro yanajiranki", bejira amsartaba yawuce yanufi d'akinsa dama Laure bata gidan tana yawonta.

Cikin jin haushi Hafsat ta nufi soro,tun kafin ta ida isa taji kamshin turaren sir Aliyu da sauri tasaka kai asoron.turus tayi ganin sir Aliyu tsaye yakafeta da mayun idanunsa yana kallo dan soyake yafahimci Hafsat zatayi farinciki da zai kasance mijinta dan inbata nuna hakan ba shima bazai nuna yanason aurenba.

Cikin sark'ewar murya ta ke kallonsa hade da nunasa tana cewa y..yay..yaya,baka ga waniba asoron han yaxo guna dan baba yace mun yana asoro?

Kallonta yyi yace bangansaba nidai kuma nine dai bak'on da baba yace d'in!so kinyarda?

Zaro idanu tayi tace yaya Kaine da..da..maa Kaine bata k'arasaba tayi cikin gida da gudu sai dakin baba tana haki take tambayarsa da gaske sir Aliyu shine bak'onta ?

Bbu wani boye boye baba yasanar da ita komai,had'e da cewa nima Nayi mamakin hakan saidai ikon Allah yafi da hakan Dan matsayinsa na d'an masu Hali had'e da mulki banyi tunanin zai iya hudda da talakawa kamarmuba.cikin tsantsar farinciki had'e da mancewa baba nagun Hafsat ta d'aga hannunta sama tana.hawayen farinci race alhmdllh allah nagode maka da kacikamun burina,yah allah kacikamun dayan burina naga mahaifiyata ameen.babama yyi saurin cewa ameen, Aida sauri Hafsat ta rufe fuskarta dan taji kunya da baba yajita da Dan gudunta ta fito ta nufi soro gun sir Aliyu, saidai tana xuwa tasami zai shiga motar tanason tsaidashi tanajin kunya,shima juyowa yyi cikin farinciki ya kalli gidan kawai yaga Hafsat suna had'a ido tayi saurin saka tafikan hannunta ta rufe fuskarta.murmushi yyi afili yace zanciremiki wannan kunyar nan yashige motar guard din yaja sukabar anguwar.

" itakuwa Hafsat ciki ta koma murna fal aranta ",tanashiga ciki tayi alwarla tafara jera nafila dan nuna godiyarta ga allah dayabata Wanda tacire rai dasamunshi,hade dayiwa mamanta adduar allah yabaiyanata.

Bangaren sir Aliyu kuwa suna isowa gida ko parking guard din be gamaba yafito cikin d'oki yashige cikin gidan.

Mommy! Mommy!! Mommy!!!

Kawai yake k'walama kira tareda da zama kan kujera ,mommy dke kitchen suna aiki tareda masu aiki taji sir Aliyu na k'wala mata kira da sauri ta fito dg kitchen din tana cewa babana lfy?

"Murmushi yyi cikin farin ciki yace wlh mommy itace!"

"cikin mamaki mommy ta ce menene itace"?

Cikin murna da zak'uwa yasanar da mommy cewa Hafsat ce wadda zai aura Ashe,be boye mata komaiba.

Cikin fara'a mommy ta ce to alhmdllh naji Dadi sosai dama wlh jikina yabani kanada rabon aurenta da jiya saida Nayi mafarkinku ,kuna tare kaida ita harda y'an yaranku.

Murmushi sir Aliyu yyi had'e da hugging dinta yace nagode sosae mummy nah kicigaba damun addua,dungure masa kai tayi tace to sai adena mun ihu da cewa sai kayi ajalin Wanda zai aure maka mata.

Yar dariya sir Aliyu yyi yace pls mommy abar tada zancen.

Dariya tayi tace bazan bariba mujema part din mejikinnan kadubata nima nasake ganinta.

Bbu musu yabi bayan mommy suka nufi part din.

Saidai besan daliliba yaji gabansa na faduwa har suka isa part din.

Suna shiga suka sami tana bacci ,mommy takalli me aikin dke gefenmarar lfyar tace mundawo inta farka.

Kallon sir Aliyu take dataga yyi kuri da ido yana kallon mairo dukda bacci take.

" ahankali tace muje ."

Sir Aliyu dabesan tanayiba dan matar Sak irin fuskar Hafsat dinsa gareta ,mamaki yake Wannan wace irin kamace.

Mommy ce tayi saurin tab'asa race wannan tunaninfa?muje ko.

"Kafin yace wani abu har mero ta bude idanuwanta ta tashi da sauri tana kalle d'akin tana cewa inna lillahi wa inna ilaihir raju un.

Kallonsu mommy take tana k'ara kalle dakin tanacewa ina nike nan bayin Allah Ku suwanene??

Share pls
[1/7, 11:22 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ95&96

Cikin matuk'ar mamaki had'e da al'ajabi mommy ta ce Alhmdllh Allah mungode maka daka bawa wannan baiwataka lfy."cikin rud'ani mairo tace dan Allah",kuyimin bayani inna fahimceku kamar Nayi rashin lafiya ne nasamu tab'in hankali?"ahankali mommy ta dawo gefenta ",ta zauna had'e da dafa kafadarta tace kada kidamu yanxun xakiji dalilin shigowarki hannunmu.

" shikuwa sir Aliyu mutuwar tsaye yyi agun dan har ransa yabasa wani abu. "

""" bbu b'ata lokaci mommy ta shiga ba mairo labarin kad'eta da daddy yyi da kai ta waje da shekarun datayi har Allah yasa tasami sauk'i.
"Salati kawai mairo keyi ", had'e da cewa nashiga ukku yanxun ko a wana Hali Hafsat ta ke?" dan Allah kubarni naje naga halin da y'ata take.
"Jin kalaminta yasa sir Aliyu hawaye", na tausayin su, dan yama gama yarda wannan ce mahaifiyar Hafsat.
" itakuwa mommy ta yi mamakin ganin hawayen sa dan rabonta da ganin hawayen sa tun yana primary skul ta yi tabbata abin yagirmama.
Cikin damuwa had'e da tausayin su sir Aliyu yamatsa kusada su hade da duk'awa "ahankali yace mama !" Hafasat tana cikin koshin lfy.

Da mamaki sosai mommy ta ce wace Hafsat kke nufi?

"Murya asark'e yace Hafsat dina ."

Da sauri mairo takalli sir Aliyu tana kuka tace bawan Allah kana nufin kasanta?

"d'aga kansa yyi alamar eh." Had'e da cewa dan Allah kisanar da mu kewacece?

Bbu wani boye boye tasanar dasu ko ita wacece da sharrin da Laure tayi mata har ta rabu da Mlm aminu.

Bbu abinsu mommy keyi sai hamdala gun ubangiji dayaba mairo lfy,kuma atake mommy ta gane mairoce mahaifiyar Hafsat, nan kuma ta sanar da mairo matsayin Hafsat agunsu.

Cikin jin Dadi had'e da godiya mairo tace hjy nagode nagode da abinda kukamun nida y'ata lallai shigowarku rayuwarmu alkhairi ne ,Allah ubangiji yabiyaku da aljanna madaukakiya.
"Cikin jin Dadi mommy ta ce ameen." Hade da kiran daddy awaya tasanar dashi komai yace gashinan xuwa.

Shikuma sir Aliyu cikin jin kunya yabar part din hade da fasilta irin farin cikin da Hafsat zatayi intaga mamanta.

Cikin yan mintina gida kowa yasan ta warke kuma Ashe itace maman Hafsat wadda sir Aliyu zai aura.

Bbu bata lokaci daddy yaxo ,suka d'unguma mota 2 suka nufi gidan mlm aminu dan har da kabeer da sadeek duk sunanan.

Tun a hanya senator yakira mlm aminu yasanar dashi gasunan tafe da wata magana.

"Hakan yasa mlm aminu shimfid'a tabarma asoro yanajiran zuwansu."

Bayan sun fito Duka suka kutsakai cikin gidan,itakuwa mairo farinciki ne fal aranta zataga Hafsat dinta danba don sbd mlm aminu tazoba.

"Adede kuma lokacin Hafsat ta fito itada Fatima zata yimata rakkiya." Kawai tagansu da yawa sun shigo a cikin soron,ai da sauri Hafsat ta fad'a jikin mommy ta na murnan ganin ta danbata lura da mamanta suke ba.

Shikuwa sir Aliyu wani Dadi yaji ganin yadda Hafsat ke son family nsa,ta dauki mommy nsa kamar mominta.

"Itakuwa mairo tsurawa Hafsat ido tayi tana mamakin girmanta ." sai taga kamar d'axun suka rabu.

Shikuwa mlm aminu mutuwar zaune yyi da idanunsa sukayi tozali da matarsa abin k'aunarsa.

Cikin farinciki mommy ta d'aga Hafsat daga jikinta tana mata murmushi hade da nuna mata mairo dke bayan ta tace y'ata kinsan wannan?

Wani irin xabura Hafsat ta yi tana murza idonta ,atake tagane mamantace cikin kuka suka rungume juna.

Nan senator yyi gyaran murya had'e da cewa kowa yazauna za'ayi magana.

Itakuwa Fatima kamar andasata agun domin tuni ta fahimci komai,kuma tana taya kawarta murna.

Bayan annutsu senator yyi addua had'e da godiya ga Allah yayi duk wani bayani da Mlm aminu da Hafsat zasu fahimta.

Cikin kuka hade da godiya ga Allah dkuma godiya ga familin senator mlm aminu yace dan bani da abinda zanbiyaku dashi sai addua nagode sosae Allah yabar zumunci.

"Duka sukace ammen."

Mlm aminu yakalli senator yace'yallab'ai dan Allah ina Neman alfaemar kasaka mairo tadawo dakinta wlh duk abinda yafaru bayin kaina bane sharrin shaidan ne.

Da sauri mairo tace aikuma nagama zama dakai garinmu ma xankoma.

Murmushi daddy yy yace inde na isa daku kuduka to na yanke hukuncin maida aurenku gobe insha Allah, jibi saita tare .

Cikin jin Dadi mlm aminu yyi ta xuba godiya gun senator.

Itakuwa mairo ta yarda dan ayanxun ta dauki senator da iyalansa tamkar jininta kuma sun isa da ita.nan itama ta amince had'e da kara musu godiya, hakan yasa mommy da daddy jin Dadi.

Fatima kuwa dake atakure sakamakon kabeer da yatsareta da idanunsa ,yasa ta kalli Hafsat da sa'ada tace kuxo muje.bbu musu suka mike' sir Aliyu ne yyi magana Wanda tun d'azun idonsa nagun Hafsat .itakuma taki yarda su had'a ido dashi.

"Ahankali yace wai ina zaku mufa tafiya zamuyi?"

Cikin marairai cewa sa'ada tace gidansu Fatima nan yace kada kujima to,to saada tace suka fita.

Daddy yakalli mlm aminu yace zamu koma da mairo gunmu sai jibin zamu kawo maka matarka.

Cikin Dadi mlm aminu yace to had'e da k'ara musu godiya.

Sannan yakalli mairo yanemi yafiyarta ,anan kuma ta yafemasa.

"Laure dke cikin gida sai surutu ake da mahana asoro tun d'azun ank'i bari hakan yasa ta lek'o dan ganin lfy."

Ai turus tayi ganin mairo azahiri,kuma a kyakkyawan yanayi, cikin rawar murya had'e da inda inda ta nuna mairo tace, mai..mai ..ro kece kece?

Murmushi mairo tayi tace Aiko dai nice kinga ikon Allah ko?

Gaba daya bakin cikene kwance a fuskar Laure bbu alamar nadama atare da ita.

Mutanan dke soron ta kalla ,saurin dauke idanunta ta yi daga kallonsu,sakamakon mugun kallon tsanar da sir Aliyu ya Aiko mata dashi.

Wata tsawa mlm aminu yayi mata had'e da cewa zaki iya tafiya kinxo sai wani kallon mutane kke,doguwar tsuka Laure taja had'e da barin soron.

"Mommy afili tace Allah yashiryeki,lallai kinyi nisa."

Dan sai mommy ta ga jin mairo yafi ganintama.

Nan daddy yamik'e yakalli mlm aminu yace to mu zamu wuce.

Cikin farin ciki mlm aminu yace to y'allab'ai mungode Allah yak'ara girma.

Sir Aliyu ne yakalli kabeer yace jeka nan gidansu Ahmed Nasir kakiramin su sa'ada,ba musu kabeer ya tafi.dan dama abinda yakeso kenan dan tunda yaga Fatima yaji ta tafi da imaninsa kuma yaga matar aure dan da angama bikin sir Aliyu shima sai ayi nasa.da wannan tunanin yafito yanufi gidansu Fatima.

"Saidai a compound din gidan yagansu Fatima zata rakosu."

Murmushi yyi yakalli Hafsat yace antinmu kuje keda sa'ada mijinki na kiranku,nikuma kubani guri mu gaisa da matata ya fad'a hade da nuna Fatima.

Fatima da dama tun da tagansa taji guy din yyi mata, cikin jin kunya ta gudu cikin gida.

Murmushi kabeer yyi yace mun had'u a next tima.

Murmushi su Hafsat sukayi ,sa'ada tace ah lallai su yaya an kamu to ai kawatace sai kai kamun k'afa aguna na shigar da kai gunta.inkuma kaci zalin dina wlh nazugata kurabu.

Murmushi yyi had'e da marairai cewa yace haba y'ar autarmu ai yanxun nadena cin zalinki,muje gobe sai muxo tare gunta xance kinga sai ki shigar da ni sosai.

Sa'ada tace to shikenan Yayana muje.


Nan suka fito ,kabeer nata tsokanar Hafsat.

Awaje suka sami su mommy zasu tafi gida.

Nan Hafsat ta saka rigima ita abarmata mamanta ,dan tanajin kunyar xuwa gidansu sir Aliyu kasancewar shi xata aura da tuni ta bi mamanta acan sun kara gaisawa.

Rarrashinta mommy ta yi tace jibifa mamanku zata dawo kinji inkuma mutafi dke to sai kusake gaisawa.

"Cikin jin kunya tace ah ah."

Sir Aliyu kuwa da ita yake kallo yaso ta bisu amma sai tace wani ah ah.

Nan dai suka shige mota, Hafsat ta saci kallon sir Aliyu taga ya had'a rai yana wani shan kamshi ,juyawa tayi tabi baba cikin gida murna fal aranta da farin cikin.

sukuma su senator suka bakabar anguwa r cikin jin Dadi.

A cikin gida kuwa Laure hankalinta yatashi dan tasan kashinta yabushe ,musammun da ta tuna kalaman baba nacewa duk sadda yaga matarsa saisun rabu.

Hakan yasa ta dauki niyar yau in rana tayi sanyi zataje gun boka dan baza bari hakan yafaru ba dan saitara ba mairo da Mlm aminu kota halin k'ak'a.

"Tana cikin wannan mugun tunanin nata baba da Hafsat suka shigo suna murna,."

Tsaki taja hade da cewa wlh kaji kunya ace mace taje tagama yawon duniyarta ,tayo hayar kaya da mutane shine za'azo a yaudareka ko?

Wata harara mlm aminu ya Aiko mata da ita yace eh naji komai tajeyi bama yawon duniya ba ahaka nake sonta,sannan wad'anda kikace ta dauko haya to iyayan Aliyu ne Wanda zai auri Hafsat inbaki saniba ki sani sai bak'in ciki yakasheki.sannan yace kuma jibi matata zata tare dan gobe za amaida aurenmu,dan haka ayau za'a fara gyara a gidan nan sbd amaryata.


"bejira amsarta yanufi dakinsa."

Ai Laure jitayi kamar yawatsa mata muta ,sbd maganganun sun shigeta.

Hakan yasa ta dauki niyar tatwatsasu kota halin k'ak'a.


Bangaren su sir Aliyu kuwa.....

Share pls
[1/7, 11:23 PM] El-hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ101&102

Koda ya isa gidan,yyi parking yafito,dan yashiga ciki...turus yyi ganin yan matan acampound din gidan kowace da boy friend dinta suna xance.

"Yasha mamakin ganin kamal da Zakiyya."

Tunani yake aransa Ina suka had'u harta sansa suka fara soyayya?

Gefensu yabi dan wucewa ciki ,nan shima kamal yalura da shi ,cikin ladabi yaje yaba shi hannu suka gaisa,yawuce .cikin mamaki kamal yake kamal tambayar Zakiyya ina tasan sir Aliyu? nan ta sanar dashi ai yayantane,jikin sa yyi sanyi dan yacire rai da samun Zakiyya amatsayin matar da zai aura.
"nanta sake sanar dashi cewa aishine angon", dan ta sanar dashi inda yazo yasameta sunxo gun wa'azi na biki.kasancewar besan ko bikinwa akeba yadai zo yasameta,kuma besan Hafsat ce amaryarba.

Koda sir Aliyu yashiga ciki awaiting parlour yahadu da umman su Fatima bayan sun gaisa ta tashi tashiga ciki ta turo masa Hafsat.
" cikin shagwaba "ta yi sallama ,murmushi yyi ya amsa ta zauna a gefensa had'e da cewa yaya ina icecream dina yake?
cikin xolaya yace ban siyoba!mik'ewa tayi dan tafiya da sauri yace indai kika tafi munbata dake. Turo baki tayi tace to kabani abuna.
Miko mata ledar dke gefensa yyi yace hmm haba yarinya ALLAH kirage shan kayan sanyin nan kinga ke amaryace.
" yafad'a Yana dariya",cikin rashin fahimtar kalamansa tace to dan ina amarya saina bar shan abu maisanyi ,aiyanxun nafarama.batare da yakalleta yace hmmm kicigaba inkinxo hannu kinyi bayani,kuma ma in aka kawomunke bazan bari kina yawan shan abu mai sanyiba.
Shiru itadai Hafsat ta yi tana tunanin kalamansa harta shanye kayanta.
nan ta kallesa cikin tsokana tace sir katashi katafi gida.
da mamaki yakalleta ya maimaita kalmar SIR dan ya mance wai antaba kiransa da ita.mik'e wa yyi yabita ganin tana masa dariya hade da gwalo,Yana cewa ALLAH idan narike ki zaki gayamusu,wato nikike kora ko?
"Eh din"

Ta fada hade da xurawa aguje,tabarsa murmushi yyi yafita da ga parlourn.

Koda yafito yaga suna nan time yaduba yaga 9:40pm da sauri ya isa shiyarsu Mubarak yakalli sa'ada fuska daure dan kada tayi masa musu yace ke wuce muje gd dare yyi.

"sa'ada ta kallesa taga fuskarsa adaure tasan yau yaya Aliyu ba m".

Cikin tsoro tace pls yaya anan zan kwana ai!hararan da ya aikamata dashi yasa bbu musu ta bisa tana d'agawa Mubarak hannu.

Amamakinta saitaga yatsaya gun Fatima da kabeer yana korarsa shikuwa sai bada hkuri yake Yana cewa anan gidan zai kwana.sir Aliyu bece masa komai ba yayi gun motarsa dan yanzun rashin kunya irinta kabeer har yasaba da ita.

Nan sa'ada ta shiga ,yaja motar Yana kallon Mubarak da Zakiyya zasushiga mota sutafi gd.

****** ****** *****
Washe gari da misalin karfe 5:00pm,Hafsat ce da sir Aliyu cikin mota gidan baya. tana sanye da gown ta materiyar marun colour taci kwalliyar zamani tayi mugun kyau,kamar kasaceta kagudu tafito a amaryarta

1 Comments On NIDA DALIBATA
avatar
isaitah-mujittapha

1 year ago

Reply

Masha Allah yayi dadi

Please Login or Register in order to submit comment