Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jikinsa had'e da sa hannunta ta zagaye bayan sa tana kukan shagwaba ,shikuwa duk yawani rud'e yarikiceyana tambayarta lfy?

Sukuwa ,k'awayen sa'ada suyi tsit Suna kallonsu kamar tb.

can Hafsat ta cikin kukan shagwaba ta ce bakai bane baka d'agani samaba kuma bakayi kissing dina ba.

Shikuwa sir da sauri yad'agata ,aiko takalesa tasaki murmushi shima yyi batare da bata lokaciba yacafke bakinta da azatonsa su sa'ada basa hangensu,tunda k'ofar arufe kuma gun dasuke corridor ne ba a yawan wucewa.

Itakuwa Hafsat tallabe kansa tana shafa wa, Suna maida numfashi, Saida sir yashanje duka janbakin dke bakinta tukum yacika ,itakuwa tayi wani kwance luf a k'irjin sa.


Kawayen sa'ada sun........

Share pls[1/12, 11:08 PM] El~hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story &written by mmn fareesa

πŸ…Ώ119

"" k'awayen sa'ada sunsha mamakin su sir da Hafsat ,ganin irin soyayyarsu,aisaikaji tsit .itakuwa sa'ada hakan ba bakonta bne agun su.
"dan ganin haka yasa ta tunada Mubarak dan irin yadda yarik'a nuna mata lokacin event din bikin tasan bbu d'aga k'afa intazo hannunsa."
Hafsat kuwa tana manne ajikin mijinta, can yad'ago kanta yace baby nah muje ko?to tace had'e da aza kanta gefen kafad'arsa,suka fito . gun motarsa ya wuce da ita ,bayan sun shiga har yafara driving yakalleta yyi murmushi yace ina zaki fara shiga gidan mama ko gidansu Fatima inmunje?"cikin shagwaba ta ce ",gidan mama nafara ganin ta ,rabona da ita tun sadda aka kani gidanka saidai muyi waya da ita.
Yar dariya yyi yace ai yanxun mama tafi ji dani akanki.turu baki tayi tace ai zantambayeta ,kuma nima aikasan yanxun mommy ta fi ji dani akan kowa dke gidan.
Murmushi yyi yace eh naji din,nidai mama tawace ni d'aya bansan kala." cikin shagwaba ta fad'a kan kafad'arsa had'e da jamasa sajen fuska ,y'ar kara yasaki had'e da cewa sulti Niko ?ALLAH zamu had'e da ke zankamaki yarinya dan kinga ina driving ko ?gwalo tayi masa tna dariyar mugunta.
"Adedenan yyi parking k'ofar gidan su Hafsat", hancinta yaja yace sulti ki gaidamun mama zan shigo anjima yanxun zanje na kula da bakin daddy dke hotel dasuka zo gun daurin aure.murmushi tayi tace to yaya nidai zan wuce gunsu Fatima ,abinda kenan munyi waya,nan tayi masa kiss akumatu ta fito dg motar ." shikuwa tabarsa da mamakinta dan yalura kalar soyayyar da Hafsat ke nuna masa ta yau tadabance nan yabar gun . itakuwa sakin baki da hanci tayi ganin yadda aka canxa wa gidan su fasali harda get ga fenti ,cikin mamaki ta tura get tashiga,a compound din gidan tasami shamsu da hanifa y'ayan Laure suna wasa.
"har kasa suka gaida ita suna cewa oyoyo Anty", cikin mamakin canxawar tarbiyyar yaran ta amsa musu cikin sakin fuska ,suka bita cikin gidan.
Mamace a tsakar gidan tana yanka latuce zasuci abinci." cikin ihun murnar ganin mamanta ta fad'a jikinta",itama tayi murnar ganin ta, bayan sungaisa ,Hafsat tace mata sir nagaida itah.
Yar dariya mama tayi tace ina ruwan Aliyu sarkin hidima kai ALLAH yyiwa yaronnan albarka gsky Hafsat kindace da miji nagari,abinda kawai zakiyi kibiyasa shine kimasa biyyaya.kingafa yadda yagyara gidan nan yamaidamu yan gayu ,harfa d'akinki yyi miki daban da komai aciki wai inkinxo kirik'a shiga abinki.kullum saiyaxo gidan nan yagaishemu da yimana hidima dan ma babanki yana hanawa,yanxun haka yasa ka su shamsu makarantar boko mai tsada,nima jiya yazomun da sabuwar freezer wai ko ruwa nadinga siyarwa ,kai ALLAH yakara bud'imai albarka Dan ALLAH kik'arayimasa godiya.
"Ajiyar zuciya Hafsat ta yi, tanajin wani tsananin son mijinta da k'aunarsa lallai ta yadda shigowar sir arayuwarta alkhairi ne.kallon mama tayi cikin farin ciki tace ni wlh duk begayamun ba mama,yar dariya tayi tace ai dan ALLAH yyi shiya sa.kije ga d'akin innarku Laure ki gaidota da jiki,kinga ga kwana can dakinbi sai d'akinki saiki bude kishiga.
Turo baki tayi dan ita wlh tama manta da wata Laure aduniya,dukda tasan ance tayi accident kuma bata gidan akayi bikinta.
"Kallon mama tayi tace bakije gun bikinba?"dan xaro ido mama tayi tace naje mana ,yanxun haka bandad'e da dawowaba munje mungama aiki sai anjima zankoma,kitashi kije mana gun Lauren.
Tashi tayi tana kumbure kumbure,girgixa kanta mama tayi tace hmmm babankuma naga baya tausayama dan shi soyayima su rabu dandai nahanasa nakuma sanarwa da mommynku tayiwa daddynku magana ,yahanasa da wlh bazaki sameta gidanba.kije inta nemi yafiyarki kiyafema mata dan ta yi nadama sosai ai ita rayuwa haka take nayarda ,duk Wanda baiyi cutaba to wlh yana tare da ALLAH, dan haka kigode masa.

" ji Hafsat ta yi jikinta yyi sanyi ."

dakin Laure ta nufa tayi sallama, zaune tasameta kan keken guragu ga k'afa d'aya nan me lfy ga kuma wadda aka yanke har dungun yakusa warkewa.

Salati kawai take a cikin zuciyarta.

Zama tayi suka gaisa ,nan Laure ta fara hawaye tana Neman yafiyar Hafsat,nan tace ta yafemata ,tabar d'akin cike da tausayinta.

"" inda akace shine dakinta ta wuce ta bude had'e da shigewa."

Mutuwar tsaye tayi ganin irin dukiyar da aka kashe a d'akin,komai na d'akin pink &white ne,murmushi tayi afili tace ai sana'ar mijinane had'a daki dole yamun Wanda yafi na kowa kan bed ta fad'a tayi kwance tana tunanin mijinta.

Can taduba agogo taga1:00pm nan tashige toilet tayi alwarsa tayi sallah ta gyara fuskar sannan ta rufe daikin ta nufo dakin mama.

Ainanma sakin baki tayi tana kallon dakin had'e da yabawa,nan mama ta kamata abinci taci zata fita baba yashigo.

"Rungumesa tayi tana murna,shima cikin jin dadin ganin yadda tayi kyau had'e da yin b'ulbul da ita,yake tambayar yasuke?"

Cikin farinciki tace lfy suke.nan baba ya zauna kusa da mama yana mata murmushi itakuwa ganin Hafsat yasa taki kallonsa tun bayan datayimasa sannu da zuwa.

Koda Hafsat ta lura da hakan saita fita tana cewa mama tatafi gunsu Fatima.


Bayan ta isa gadan gun umman su taje tayi mata ALLAH yasa alkhairi ,sannan tanufi gun yanmatan.

"Fatima na ganin ta tace ki koma sai yanxun kikagadamar xuwa ko?"

Cikin langabe kai tace sorry Mrs kabeer wlh ina gun mama kinsan tunda nabar gidan saiyau naje.

"Fatima tace eh hakane fa."

Nan k'awayensu na skul din su sai kallon Hafsat suke yadda sukaga tazama babbar yarinya da yawansu sunyi mamaki da akace sir Aliyu ta aura,Ashe soyayya suke ,amma yake nuna kanwarsace.

Nan dai akayita fira amarya da kawayenta,inda suketa jajjayarta ganin ankusa kaita.itakuwa duk atsorace take dan kabeer daga ganin sabazai saurara mataba,sukawa k'awayensu sai tsokanarta suke,suna nan akazo akatafi da Fatima akayomata fad'a tukum sannan mama ta fito da ita dan mik'ata gidan kabeer."nan su Hafsat yan kai amarya akayita fitowa anashiga mota,Hafsat motar amarya tashige dan sir tuni yaturo mata massege kada tasake ta shiga motar wani gardi yakalle masa ita,ta shiga motar da driver zaija akai amarya acikinta ,yaso yakaita to yana tare dasu Daddy.


Masha ALLAH gidan amarya yyi ,nan akayita watsewa dukda Hafsat taso xuwa gidan sa'ada da Zakiyya,amma ba Wanda zai kaita driver yatafi.

gidan duk an watse dg amarya sai kanwar umman su da wata budurwa sai Hafsat kawai suka rage agidan.

Nan Hafsat taji anyi horn da sauri ta fita dan dubawa ko driver ne yakawo wasu.

"Tana xuwa taga shine yakawo kabeer ango,nan tanufesu,adede Sadda ta isa ,kabeer ya fito cikin manyan kaya fuskar nan awashe kamar anmasa bushara da gidan aljanna.yana ganin Hafsat yace gsky antynmu kuma kawar my one dina,kin kyauta dan dama yanxun zanshiga nafito da duk wadda ta zauna mun agd dan yakamata abamu guri hakan.....yar dariya Hafsat tayi dan tasan kabeer yadda yake rawar kan nan yau Fatima zataji jiki,saitaji wani tausayinta.

" mota ta bude had'e da cewa hmmm sannu mai gida to akwaidai Anty kanwar umman su aciki zasuyimata yan gyare gyare sannan su fito inkuma korarsu zakayi ga wuri nan,ta kaiwanan ta shiga had'e da cewa driver gidan sa'ada zai kaita.

Bayan sun isa gidan sa'ada tsaitsaye taje ta rarrashi sa'ada akan tayi hkuri abubuwan sun had'e ne shiya sa amma xataxo mata yini,nan tabarta tana ta shankuka.

Kaitsaye gidan Zakiyya suka wuce can ma tsaitsaye taje ta fito tace driver yamayar da ita gidansu.

Koda ta shiga gida gun mama taje taci tuwo ,tukum ta koma d'akinta tayi wanka da sallah ta kwanta akan bed din ta.babu jimawa kiran sir yashigo awayarta,tana d'agawa tafara sakar masa kukan shagwaba rta,shikuwa cikin rarrashi yace sorry kinji sulti nah wlh ina busy ne duk agajiye nike ,yanxun kina ina nazo mutafi gida?

"Cikin shagwaba ta ce ina gidan mama kuma adakina ."

To yace hade da datse kiran.

Befi minti 15ba yashigo cikin gidan ,besamu kowaba,kawai ya wuce dakin Hafsat .

Ya murd'a k'ofar kwance yasameta ,da gudu ta fad'a jikinsa yarungumeta had'e da juyawa da ita suna dariya.

Hancinta yaja yace oya muje kinxomana gida ko?

Murmushi tayi tace eh din had'e da rikemasa hannu suka fito ,dakinmama sukaje ,bayan sun gaisa sir yace mamanah asamin tuwo !da sauri mama tajawo tiren dke gefenta tana murmushi had'e da cewa oh Aliyu bakagajiya da cin tuwo.

Murmushi yyi yace ai mama tuwanki nadabanne, itakuwa hafsat tasha mamakin yadda sir yayi irin wannan shakuwar da mama.

Bayan mama tayi serving dinsa ,ta tura masa gaban hade da cema Hafsat ta kamasa ruwa ,turo baki Hafsat tayi tace ni mama naga ma baki wani ji dani yanxun.

Yar dariya mama tayi tace eh naga alama kina kishi da aliyu ko?to eh nafi jidashi akanki,tana fad'a tabarmusu dakin.

Shikuwa sir sai dariyar mugunta yakewa Hafsat.

Kwafa tayi tafita yakawo masa ruwan had'e da zama gefensa tana mintsininsa.shareta yyi yagama cin tuwansa yafita gun tape a tsakar gidan yawanke hannu yyiwa su mama da Laure Saida safe dke zaune a tsakar gida.

Nan mama takoma dakin gun Hafsat ,tace bara nabaki wani magunguna ,nan ta shiga bed room ta fito da wata jarka wadda tsumine aciki ,tace ungo maganin basir ne kullum kisha sau3arana koda inkinje gun mijinki kinajin zafi zaki dena ,ta mika mata wasu magaunguna k'ulle aleda tace kirik'a sha da madara insun k'are kimun magana ,kuma kada kibari mijinki yaganikisaka ajikka.

Cikin murya ta karb'a jin harda maganin dena jin zafinnan Wanda dama tanason yiwa mama maganar tana jin kunya.

Nan sukayi sallama tafita gunsir.


****** ****** ******
Hakafa rayuwa tayita tafiya gun sir da Hafsat kullum suna cikin faranta ran juna,dan yanxun Hafsat tuni ta aje kunya tana farantawa mijinta hade da yima biyyaya,kuma yanxun tadena jin wannan zafin kullum suna manne da juna in yafita suna yin waya akai akai.

Bangaren su amarema bbu laifi love kawai suke sha abinsu,musammun su Fatima da kabeer dinta dan kabeer bbu sauki abinda kullum Abu daya tun Fatima bata sababa har ta saba hakan.

Yau Yakama week end ,sir ne zaune Hafsat na tsakiyar jinyoyinsa yana mata tsifa dan komai sir yakemata ko yatayata suyi tare.

daga ita sai wani dan wando iya gwiwa da y'ar Riga iya cibi sai shagwarta take zubawa son ranta.

Can ta kama tari ,daganan sai kakarin amai da sauri ta tashi tashige toilet ta dinga kwata amai,shikuwa sir arikice yabiyota yana tambayarta lfy meke damunta kotace wani abu?

"Ahankali tace ah ah."

Taimaka mata yyi yace ta wanke bakinta sannan yacanja mata kaya yace ,baby muje hospital.

Dire dire tahauyi ita ah ah kada ayimata allura.

Lallabata yyi yace bazai bari ayi mata ba,sannan ta bisa suka wuce hospital.

Wata private hospital sukaje ,nan Sir yabukaci son doctor mace ta dubamasa suntinshi,nan akahad'asa da wata docter ta fara bincikar Hafsat tayi mata yan tambayoyi shikuwa sir yana zaune tana kan cinyarsa ake dubata.

Nan akabata wata yar roba akace tayi fitsari,nanta tashi,har sir zai bits docter tace ah ah yajirata ta fito.

"Bbu jimawa ta fitota mik'amata robar."

Nan aka auna fitsarin atake akagano tana ciki ajikinta ,koda ta fad'a musu wani ihun murnar sir yyi yarungume Hafsat itama cikin murna tace yaya munkusa zama parent muna ko?

Eh yace had'e da cewa ALHMDLLH.

Itakuwa docter sai kallonsu take dan sun bata sha'awa ,nan sir yajata bayan anmata secarning angano cikin wata2ne.

Hannunsa cikin nata suka fito fuskarsu cike da farin ciki,zasu shiga motar ,sukaji wata nacewa bewar ALLAH kece Hafsat?

da sauri sir da hafsat suka juyo.

K'ura ma wadda ta tsaidasu idanu Hafsat tayi atake tagane labor ce wadda suka mata mugun suka suka kuma had'a baki da kamal ,suka kaita step quarters .

"Yatsina fuska sir yyi yace malama fy?"

Duk'awa tayi had'e da bayyana kanta tana rokar Hafsat yafita ,nan tace ta yafe had'e da kallon sir tace my dear mujenan suka shige suka barta gun.

Itakuwa tagane sir Aliyu, kuma ganinsu hakan yatabbatar mata su masoyane kuma ma auratta.

Tun amota sir sai nan nan da Hafsat yake yana tambayarta metakeso na masu ciki yasiya mata?

Cikin shagwaba ta ce muje nidai gun mommy nah ka kaini gunta nike so .

Murmushi yyi yace to my Princess.
Wayarsa yafito yafara sanar da mommy dasu mama bbu ko kunya sannan yakira su Mubarak da kamal,sannan kabeer.

Lokacin dayakira kabeer suna tare da Fatima akicin yana tayata aiki aiko dayaji sir yace Hafsat Nada ciki,aisai yakalli Fatima yace oya muje ALLAH bazai yuyuba muje nima nabada himma ko babyn yaya yasami k'anwa kinga sai ayi yar gida ,abada zumunci ,yafad'a had'e da kashe mata ido.

Itadai murmushi tayi tabisa ,suka wuce k'uryar daki abinsu.

Sukuwa sir gidan mommy suka nufa ,bayan sun isa ,Hafsat na hannunsa suka wuce ciki......


Share pls
[1/15, 11:39 AM] El~hajj: NIDA D'ALIBATA
🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

πŸ…Ώ121

πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š

Itama Hafsat ba taso xuwa gd ba tafison gun mijinta dandai kawai bata nuna hakanba.
"Koda suka isa gidansu d'akinta aka wuce da ita ", nan jama'a suka cigaba da zuwa yan barka.
Yayinda umman su Fatima ta ja Hafsat domin yin wanka.
Shikuwa sir cikin bacin rai yakoma gd dan baison koda da minti d'aya ne yarabu da sultin shi ,dandai kawai bayason yacika yin musu da mommy ne shiya sa yahakura.
" Hafsat sarkin tsoron ruwan zafi hakadai umma ta gasheta da kyau har aka gama ta fito dg bayin ta nufo dakin", su Zakiyya ,sa'ada ,Fatima duk sun cika d'akin ko waccensu da tulelen cikinta.
Murmushi sukayi dsuka ga Hafsat nan suka fara tsokanarta suna dariya, zama tayi tasaka kaya ta shirya ,yayinda babyn ke gunsu sunata santin yaron .suna dariya dacigaba da tsokanarta . itama dariyar tayi tace hmmm kune abin dariya kuma abin tsokana zakuji yadda haihuwa take tunda har na haihu ai wankan jego bazai bani wuyaba,inkuma kuna dariyar nadawo gd to ko waccenku ita gida zata dawo."nuna Fatima ta yi tace balleke inkindawo mutuminki yazama abin tausayi dan daga gani bayada hakuri",Fatima tace hmmm kedai bari dan my one indai gun harkane ba sauki shiya sa da wuya muyi fad'a ,inma munyi ma shirya wlh kodon sbd in dare yyi z....shiru tayi ganin su ,Mubarak da yaya Ahmed shida Anty salma matarsa da sir yana rik'e da d'ansu,kabeer da kamal abayansu.sunzo duba jariri.
"Fatima ta tashi tana gaidasu had'e da karbar ameer d'an yy Ahmed dke hannun sir", Aida sauri kabeer yace my one yi ahankali kinsanfa da akwai ajiyata jikinki,dariya yy Ahmed yyi yace oh nida sabon shiga!babyn sa'ada tabasu suna kallo suna yabashi Masha ALLAH, suna mamakin rashin kunya irinta kabeer itadai Zakiyya gun mijinta ta matsa tanamasa shagwaba ita ice cream takeso ,shikuma yana lallabata tayi hkuri sbd babynsu kada ta haifeshi da mura ,sir ne yalura da su,murmushi yyi yace oh yarannan ALLAH yashiryaku.
" kallon Hafsat yyi yaga tana dariya",kusada ita yadawo yace sulti mekikewa dariya?"kallonsa tayi tace hmmm my dear su sa'ada mana ,yaya Mubarak yawani jata waje baza'ayi maganar agabanmuba.,fuska kalar tausayi yyi yace ,aini angama dani tunda anmaidominke gd ,tura baki tayi tace yaya harfa wanka sukamin da ruwan zafi kamar zai k'onani,dan zaro ido yyi yace Saida nacewa mommy sumiki ahankali yafad'a had'e da kai bakinsa saitin kunnanta yace zonxo da dare ,amma bazan bari kowa yaganniba,ingaisa da ababena......yaya Ahmed yace oh friend agabana ALLAH zansanar dasu umma ai tana cikin gidan,tsaki sir yyi had'e da mik'e wa yace kadad'e baka fad'adinba.
"Itadai Anty salma sai yar dariya take ,nan yy Ahmed yabata babyn yakalli Hafsat yace kanwata friend yakoyamiki rashin kunyarsa ko?" Sa'ada data shigo taji maganar da sauri tace yaya itamafa wlh takoya masa, hararanta Hafsat ta yi, suka saka dariya,nan suka fice sukabar matansu nan dansu yini anan.

Hakafa suka zauna suna firar su da labarin maxajansu ,har sukaci abinci sukayi sallah, suna like da baby da mamansa,basubar gidanba sai dare.

"da misalin 8:30 pm sir yakira Hafsat yace bakowa dakinki?"

"Tace eh"

In shigowa zakayi ba damuwa dan babyn na part din mama da yan barkan dare shine nafito naga duk manyane,cikin jindad'i yace ok ganinan xuwa ,yana fad'a yakashe kiran yashige cikin gidan .

d'akinta yanufa ,Aida gudu Hafsat ta yi hugging dinsa ,kafin tace wani abu yacafki bakinta yana kissing.

Babu musu ko gaddama Hafsat ta biye masa suna mugun romancing juna kamar zasu cinye juna ganin zai wuce iyaka yasa ta tsaidashi,cikin dubara tace naji ana kirana k'ila babynka ne ke kuka bara naje nan ta fita tabar sir zaune yawani lumshe ido.

Tana fita ta had'e da mama zata kawo babyn yana kuka,hamdala tayi dan da mama tasamesu a cikin wannan yanayin ai kashinta yabushe .mama tace ina zaki naga kinfito?"cikin in'ina tace dama yaya ne yaxo yanxun yace na karbosa yagansa mik'amatashi tayi had'e da cewa to wlh kibidai ahankali banda zama gab da juna inma naji shiru zaku ganni ,cikin jin kunya Hafsat ta ce to mama kinsanma hakan bazai faruba. girgiza kai maman tayi ta wuce ,Hafsat ta koma dakinta.
Tana shiga ta azamasa babyn acinya ,had'e da yin ajiyar zuciya ta zaiyyana masa fitarta kenan ta had'e da mama.
dan zaro ido yyi yace oh sulti dataganmu da wlh naji kunya,barama nagansa na wuce ainarage zafi.
Nan yayita kallon babyn yanajin sonsa da k'aunarsa kissing insa yyi yace sulti nah dani da babyn nan wakikafi so?
"Murmushi tayi tace Wanda nafara samu shinake do", ahankali yace nima haka sultina ALLAH yabarmu tare kingama mun komai arayuwata nidake mutu karaba.lallai danabi zugar wata zuciyar dke cemun kada kaso dalibarka,yau gashi NIDA D'ALIBATA har munyi aure mun haihu ikon ALLAH kenan.
Cikin jin dadin kalamansa ta sumbacesa agoshi had'e da karbar yaron tana cewa yaya kaje kada mama tashigo,hancinta yaja had'e da shafa kanta yyi wa yaron da ita kiss yace kikulamun daku sai munyi waya,cikin shagwaba taje yanxun inkafita inazakaje?
" ahankali yace zance",wata harara ta galla masa had'e da cewa kai mijin mace d'aya ne tunda kai subutar baki ka fad'a a first night dinmu.
Murmushi yyi yace to maida wuk'ar ,in inatare dke duk sauran mata kallon maza nikemusu ,insha ALLAH kece anan duniya kuma a aljannah matata kedaya.murmushi tayi mai sauti had'e da dagamasa hannu har yafita.

Adaren ranar sunsha kalaman love awaya ,sun raba dare suna firar su ta masoya har bacci yasace Hafsat,jintayi shiru yagane tayi bacci yakashe wayar ya kwanta cike da farinciki.

********************

Hakafa aka cigaba da zaman jego ,kwanci tashi har yau Yakama suna.

Inda yaro yaci Suleiman ,sunan daddy suna kiransa da khalifa.

Mejego da kawayenta ko ince yan uwanta su Fatima sunsha kyau har sun gaji inda gidan cike yake da jama'a ga mai DJ a compound din gidansu yasaki kid'a.

"Anci ansha me jego tasami kyaututtuka gun ja'ama."

Uban gayyar kuwa har walima yashirya shida friends dinsa.

Hakafa taro yatashi lfy inda akabar me jego tacigaba da wankanta agidansu,tana samun kulawa itada babyn sosai agun mama .

Kullum sai sir yazo sau 2yagansu , safe da dare yakamusu wannan yakamusu wancan,sannan susha romance dinsu.

Koda mama ta lura da yadda sir kedokinsu aisai tashiga tsima yartata da gyarata ,kai harsu dulka akamata .

Aranar datayi40ta koma ,hmmm kada kuso kuga irin rawar kan da sir yyi ai ranar abun ba magana ,har kukan dad'i sir yyi.

__________________
Haka rayuwa tacigaba da kasancewa inda khalifa yyi bulbul dashi dan fari yyi wayo ga yaron da farin jini kamar ubansa.

Ayanxun watansa ukku kuma sir yamaida Hafsat skul yanaso tazama koda nursing ne.

Inda sa'ada,tahaifi yarta mace kafin suna Fatima ta haifi d'anta nmj ,bayan sunyi 40zakiyya tahaihu itama mace.

Haka zamansu yakasance cikin farinci da yadda da juna .

Inda sir yaje har gombe yyi binciken dangin maman Hafsat ,yadawo yahadasu da mama kuma yataimaka musu.

Bayan shekara5

gidan alhj Suleiman rabo na l'eka tun a compound din gidan naga yara sunkai 14suna wasansu ,amma daya na gefe kamar babushi agun.

Wata yar baby gils ce tazo gabansa tana cewa yaya khalifa kaga arfat tana Jana ,yatsina fuska yyi yace to ai ance kudena kunki,bacemun dagani .da gudu tayi cikin babban parlon gidan .

Hafsat ce zaune kan kushin ta aza k'afa daya kan daya tana kallon tb.araina nace masha ALLAH su Hafsat anxama manyan mata tayi k'ara haske da y'ar k'iba jikinnan yyi fresh .yarinyar na xuwa ta fada ajikinta tace many kinga arfat na Jana,nagayawa yaya khalifa yakoreni.

Tsaki Hafsat ta ja tace rabu da shi Yaro sai shegen miskilanci ntsiya har yace ma daddy n Ku be iyaba tun yana yaro inaga ya girma,kiyi hkuri zanzane arfat kinji.....

Sir ne yashigo dakin cikin nutsuwa ,yakara girma yazama babban mutum matashi mai ji da naira had'e da ilimi uwa uba kyau ga shi Dan gata agun matarsa.yara biyune ahannunsa ,wsu sun biyoshi abaya ,zama yyi kusada Hafsat yana murmushi had'e da cewa sulti nah ,gida zamuje yanxun.

Cikin shagwaba ta ce ,um um bamu dadeba fa,kuma mommy ta na ciki tayi bak'i,aibana tafi ba bbu sallama.

Hancinta yaja yace har yanxun bazaki girmaba ko?kinada yara4amma kina shagwaba.radamasa tayi tace aini yar yarinyace agunka.

Murmushi yyi yace eh hakane,aiyanxunma xuwa nayi muje ki sallameni yafad'a had'e da kashe mata ido d'aya.

Yaran dasuka shigo su Tara ,wato 3na kabeer 3na sa'ada,3na Zakiyya, yace my children yanxun kuma ,za azo daukarku.

Khalifane yaja kannensa ,arfat dkeda sunan mommy, minal da kuma yusuk suka wuce gun motar sir suka shiga ,sauran yaron nata wasansu a compound din gidan.

Sir ya mikar da Hafsat yana cewa sulti muje in mommy ta ji shiru tasan muntafi ,murmushi tayi tace to mijina...

TAMAT BI HAMDULIILAHI

Anan nakawo karshen Wannan labari, kuskuren danayi acikinsa yah ALLAH kayafemun.

Ina mik'a godiyata sosai ga....

Nida d'alibata fans grp,1,2&3.

Muhad'a kammu writer's association

Amintattun mata writers association

Tap ten Hausa novels

Sadnaf novels

Mubeenah fans

ramin mugunta fans

Novels &kitchen grp

Yasmin Hausa novels

da duk sauran grps din da ake posting wannan novel na gode sosai.

Afuwan!Afuwan!!Afuwan!!!

Yaro ko babba duk Wanda na batama rai akan wannan novel ina rokan yafiyarku.

Nagode!, nagode! Nagode!

ga dukkan wad'anda suka fara bina tun farkon fara wannan novel harxuwa wannan lokaci, sai mun had'e a sabon novel d'ina mai xuwa insha ALLAH.

Akarshe nasadarkar da wannan littafin gareki,yar uwa k'awa ,aminiya,AMEERA marubuciyar K'ASATA, kinfi kowa son NIDA D'ALIBATA kiyi yadda kkso dashi, mallakinkine halak malak na gode...

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including

1 Comments On NIDA DALIBATA
avatar
isaitah-mujittapha

10 months ago

Reply

Masha Allah yayi dadi

Please Login or Register in order to submit comment