Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakana na aurenki duk lokacin da iyayenki suka shirya ashirye nake, amma ke har yanzu naga kamar babu aure cikin tsarin rayuwarki".
"mi kake nufi da babu aure cikin tsarin rayuwata Mubasshir ko kuwa nufinka banida ra'ayin aure kwata kwata azuciyata ?".
Girgiza kansa yayi alamar a'a ba haka yake nufi ba cikin tattausan lafazi yace"ba haka ne nufina ba Raihana kada kiyimin gurguwar fahimta, ganin nayi ak'alla mun shekara biyu muna soyayya dake amma ko sau d'aya baki tab'a yimin maganar aure ba amma bana nufinki da sharri ko kad'an azuciyata".
Harara ta wurga masa tareda murgud'a baki tana masa kallon matsiyaci wanda bayada komai, sannan ta dubesa ido cikin ido tace"kalleni da k'yau daga sama har k'asa".

"na kalleki Raihana".

"da k'yau nayi maka kamada matar matsiyaci irinka wanda bayada ko sisi sai tarin littafan addini da jalabiyu, kai makahon ina ne da kakeson ka had'a matsayina da naka wannan ai rashin nazari ne da tunani!".

Mubasshir ya tari numfashinta yace"ya isa dakata da maganarki yanzu dai ban fahimci inda maganarki ta dosa ba mi kikeson kice mini?".
Cikin rashin kunya tace"nufina bakada masu gidan rana saboda haka ko amafarki kada kayi tunanin ni Raihana zan iya aurenka".
Cikin jin zafi da rad'ad'in maganarta yace"haka kika ce?".

Ta rik'e k'ugunta tana karkad'a jikinta tace"nace ko bakaji bane in maimaita abinda na fad'a?".
"a'a naji basai kin maimaita ba amma agaskiya kin bani matuk'ar mamaki Raihana, ban tab'a zato ko tsammanin *KWAD'AYI DA BURI* kika sawa gaba ba sai yanzu ashe dama son kud'i da rud'in duniya kika sawa gaba? Kiji tsoron Allah ki cire kwad'ayi da buri azuciyarki domin zasu iya kaiki mahalaka, tabbas idan kika shiga motar kwad'ayi a tashar nadama da walak'anci zaki sauka!".
"ka gama wa'azin isasshe!? ".
"ban gama ba".
"to cigaba har ka gama".
Mubasshir ya k'ara da cewa"ita rayuwar duniya da kike gani ba wurin jin dad'in mumini bace sannan rayuwar duniyar nan batada tabbas saboda mai kud'in yanzu wata rana shine talakan gobe talakan yau wata rana shine mai kud'in gobe, saboda haka ki taka ahankali ita duniya da kike ganinta juyi-juyi ce yau gareka gobe ga d'an uwanka kada ki bari *SON ZUCIYA* da rud'in shaid'an ya kaiki ga nadamar da batada amfani".

Raihana taja tsoki mtssss tace"in tambayeka wai?".

"ina jinki".
"ana aure dole ne? ".
Mubasshir ya girgiza kansa cikin d'acin rai da bak'in cikin irin kalaman da take gaya masa marasa dad'i azuciya yace"a'a ba'ayi".

"yauwa kaba kanka k'yak'k'yawar amsa to tunda ba'a aure dole bari kaji daga rana mai kamar ta yau kada in k'ara ganin k'azaman k'afafunka sun tako bakin k'ofar gidanmu! ".

Murmushi mai tattare da bak'in ciki yayi azuciya amma afuskarsa bai nuna mata komai ba yace"kiyi hak'uri nina kawo kaina k'ofar gidanku da har kikayimin walak'anci amma da yardar Allah bazaki koma ganin na tako k'afata ba da sunan nazo wurinki ba, saboda haka ki gafarceni Raihana ubangiji yaba kowa mai k'aunarsa da gaskiya".Yana k'arasa maganarsa yaja k'afafunsa ya nufi hanyar gidansu yabarta atsaye tana hararar bayansa.
Saida taga b'acewarsa ta saukar da numfashi tace"aikin banza na yarda k'walan mangwaro na huta da k'uda idan banda samarin zamani basuda tunani da la'akari kamar ni wannan matalaucin zaice yana sona saboda rufewar idanu da toshewar basira".Tana rufe bakinta ta juya ta koma cikin gidansu.

_Ni Mugirat dake tsaye kusa gareta nace jita dan Allah wata kama gareta, amma gudun tijararta yasa naja bakina nayi shiru domin kada taji abinda na fad'a._ 😁
____________________

*BAYAN KWANA BIYU*

Ridwan yazo fira wurin Raihana suka shige cikin motarsa sunata fira suna cin naman kazar daya siyo yazo dashi domin sufi jin dad'in fira, suna cin naman suna jifan junansu da kallon k'auna da shauk'in soyayyar gaskiya.
Alokacin ne Ridwan ya cire hannunsa cikin naman ya dubeta yace"Raihana soyayya wata aba ce mai wahalar da zuk'atan masoya muddin mutum ya afka cikin kogin soyayya, to sai yasha fama da hak'uri da danne zuciyarsa domin akowane lokaci yana cin karo da abubuwan da zasu b'ata masa rai, hmmmmm amma ke kam kullum cikin sakani farin ciki kikeyi gwargwadon iyawarki bak'ya son ganin na shiga cikin damuwa da b'acin rai ".
Raihana ta rausayar da kanta cikin dafin k'auna tace"soyayyarka da nakeyi maka bazata bari in sab'awa umurninka ba habibi tabbas da ana bud'e zuciya dana bud'e maka tawa zuciyar, saboda ka gani ko zaka iya iyakance adadin k'aunar da nake maka arayuwata alal hak'ik'a ina alfahari da kasancewarka masoyina abin tink'ahona".
"Akullum dare da rana da tunaninki nake dashi nake tashi azuciyata ban tab'a fad'awa tarkon son da yayimin mummunan kamu ba irin naki, anyah zan iya rayuwa idan babu ke *ADUNIYAR SO*?Gaskiya bazan tab'a rayuwa idan babu ke my Raihana ".
"ni kaina ina mamakin yadda idanuwana suka makance akan soyayyarka kunnuwana suka rufe basa sauraron maganar kowa sai naka, duk numfashin dazan fitar daga cikin hancina to k'aunarka ninkuwa yakeyi arayuwata".
"ai shiyasa akullum nake k'ara godiya ga Allah daya bani mai share hawayena tabbas na fahimci cewa *SOYAYYAR GASKIYA* kikeyimin wadda babu algussu acikinta ".

"bakada damuwa habibi muddin muna tareda juna zan cigaba da baka tsantsar farin ciki da tsagwaron soyayyar gaskiya saboda ni akan abunda nakeso babu abinda bazanyi maka domin kaji dad'i azuciyarka".

"har kinsa naji sanyi araina *ABAR SONA*".
Haka dai suka cigaba musanyar kalaman soyayya wa junansu mai sanyaya zuciyar masoya.
Suna cikin motar ne na tsinkayo tahowar Baba Iliyasu zuwa wurinsu ya fito daga kasuwa, tun daga nesa ya hango Raihana zaune cikin motar saurayi b'acin rai da tsantsar takaici ne kwance cikin k'wayar idanunsa akan bak'in ciki har duhu duhu yake gani cikin idanunsa, dak'yar ya k'araso bakin k'ofar gidansa ya shige cikin gidan fuuuuuu kamar zai tashi sama akan sauri.

Yana isa tsakiyar filin gidan ya hango Inna Zulai zaune tana wak'e-wak'enta cikin farin ciki da kwanciyar hankali daga sama taga mutum tsaye akanta fuskar nan amurtuk'e yace"yanzu saboda Allah yadda kike d'aurewa yarinyar nan gindi tana aikata abinda taga dama kin k'yauta Zulai? ".

Inna Zulai ta mayarda kallonta gefe cikin halin ko inkula tace"mi tayi ne da zakace ina d'aure mata gindi nifa banason ganin laifi da abinda zai sakani cikin damuwa? ".
"bakima san abinda Raihana takeyi ba agidan nan".
"ban sani ba idan na sani zan tambayeka? ".
Baba Iliyasu yayi doguwar ajiyar zuciya tace"to yanzu naga Raihana zaune cikin motar saurayi tana fira ace duk waje bai ishesu fira ba sai sun shiga cikin mota, wannan bai kamata ba sannan na gaji da ganin dandazon samari a k'ofar gidana akullum idan tazo ki gaya mata nace ta fitar da mijin aure, na gaji da yadda ake zagina agari ana cewa 'yata tafi k'arfina kema kinada laifi acikin wannan lamari saboda ke kike goya mata baya akan komai".

Inna Zulai ta hasala matuk'a da kalamansa kallonsa tayi cikin tsantsar takaici tace"to domin tana fira da saurayinta cikin mota shine mi? Iliyasu banason irin abubuwan da kakeyimin bana jin dad'insu sannan ko anzageka ba gareka farau ba bale ak'are akanka".

"haka kikace idan tayi fira cikin mota ba wani abu bane ko? ".

Inna Zulai ta gyara zamanta tace"eh mana chanjin zamani ne ai 'yan matan yanzu haka sukeyi saboda haka ka shafawa kanka lafiya,ni banason neman fitina da jidali mutum ace kullum bazai fad'i alkhairi ba sai sharri ".
Baba Iliyasu ya jijjiga kansa cikin rashin kuzari da d'acin rai saukar da numfashi yayi yace"naji bana fad'in alkhairi sai sharri Zulai ki guji rud'in duniya da son zuciya wallahi wata rana zasu iya kaiki cikin halaka da nadama su baro! ".

"kada ka kuskura kayimin baki tunda ni ba d'iyarka bace bakinka ya sari d'anyen kashi".

Baba Iliyasu yace"Allah ya shiryeki Zulai".Yana kai k'arshen maganarsa ya shige cikin d'akinsa domin ya watsa ruwa ajikinsa yaji sanyi.

Inna Zulai ta cigaba da zage-zagenta tana ji nini da guna-guni saboda kalaman Baba Iliyasu sun b'ata mata rai tareda saka bak'in ciki da takaici azuciyarta.

___________________
Mubasshir daya fice daga wurin Raihana bai zarce ko'ina ba sai gidansu yana isa tsakiyar gidan ya hango Umma tana karatun qur'ani mai girma saida ya bari ta kammala karatun sannan ya gaidata, ta amsa fuska asake cikin k'aunar d'anta tace"Mubasshir ina ka fito ne?".

"gidansu Raihana naje Umma".

Umma ta rufe qur'ani mai girma ta kallesa cikin nazari tace"to ta amince zata aureka ne ko kuwa soyayyar kawai kuke tayi da juna?".
Mubasshir ya duk'ar da kansa k'asa cikin rashin walwala da takaici azuciyarsa yace mata"hmmmm Umma Raihana bata sona mai kud'i takeson aura bani ba da naje wurinta karkiso kiga yadda ta cimin mutunci tareda gayamin magana son ranta, wannan yarinya babu aure cikin tsarin rayuwarta *KWAD'AYI DA BURI* kawai ta sawa gaba rayuwarta tana cikin matuk'ar hatsari! ".

"lallai yarinyar nan tayi nisa dama shiyasa banso ka fara neman aure ba tun yanzu ba nafison ka daure saika kammala karatunka, amma ka nunamin kanason Raihana shiyasa na k'yaleka ka fara nemanta tun farko".

"ai yanzu na shafe babinta arayuwata na cireta cikin zuciyata saboda ni ba zuciyar kare gareni da zan cigaba da sonta ba".

"babu komai gara daka rabuda ita ubangiji yaba kowa abokin rayuwa nagari, amma kam ko mahaifiyarta ba mutunci ne da ita saboda barewa bata tuma d'anta yazo yayi rarrafe duk mugun halinta ta kwaso ".
"sudai suka sani Umma babu abinda ya shafeni kwad'ayi dai mabud'in wahala ".
"haka ne shiga cikin d'aki abincinka yana nan cikin kula"."To".Ya fad'a tareda mik'ewa tsaye ya shige cikin d'akinsa domin ya watsa ruwa ajikinsa yaji sanyi,cire tufafinsa yayi ya fad'a cikin toilet bai jima ba ya fito yana share sauran ruwan dake jikinsa sannan ya shafa manshafi ya d'auko jalabiyarsa brown ya sanya, abincinsa ya jawo ya fara ci atsanake yana tunanin irin maganganun da Raihana ta gaya masa masu rad'ad'i da k'una azuciya........
[12/5, 9:30 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 5*


Cikin matuk'ar mamakin maganarsa Inna Zulai ta nuna kanta tace"akan tsinanniyar yarinyar nan zaka kirani da mahaukaciya!?"."Zan iya kiranki da abinda yafi wannan kalmar muni ma saboda na fahimci bakida hankali"."Karka k'ara zagina Iliyasu sai dai idan uwarka ce mai Tankwa mahaukaciya mara hankali! ".Baba Iliyasu ya kad'u jin yadda take zagin mahaifiyarsa yace"ni kike zagin mahaifiyata?".
Inna Zulai ta rik'e kwankwasonta tana karkad'a jikinta cikin son fitina da tsantsar tashin hankali tace"an zagi mahaifiyarka nida ka zageni uwarka fina tayi!?".
Baba Iliyasu ya girgiza kansa cikin jimami tace"hak'ik'a koda naje neman aurenki idanuna arufe suke shiyasa nayi zab'en tumun dare! ".
"k'warai kuwa kayi zab'en tumun dare baka sani ba sai yanzu bayan ruwa ya kawo maka awuya lusari wawan banza!".
"zaki gane kurenki da sannu zaki fahimci ainahin kalata".
"kanada wata kalace bayan wanda na sani da zaka zo kana mini cika bakin yofi".
"a'a banida".Yana rufe bakinsa yaja hannun Rayyanatu suka nufi wurin shagon mai shayi domin su karya, suna isa suka zauna teburin mai shayi Baba Iliyasu ya siya biredi mai shayi ya had'a musu shayi suka fara breakfast.

*********************
Inna Zulai zaune itada Raihana suna cin k'osai da biredi suna zancensu alokacin ne Raihana ta zumb'ura baki tace"Inna yanzu kina nufin Rayyanatu ta dawo gidan nan gaskiya banji dad'i ba".
Inna Zulai tayi tagumi cikin b'acin rai da hasala matuk'a tace"Babanki ne ya dawo da ita gidan nan bani ba saboda haka ki daina damuna da maganar takaici kinji na gaya miki! ".
Raihana ta langwab'e kanta tace"kiyi hak'uri Inna domin ta dawo gidan nan ba abin damuwa bane, ai yanzu mun samu baiwa maiyi mana share-share da wanke wanke ko ya kika gani?".
Inna Zulai tayi shiru na d'an wani lokaci can ta musk'uta tace"maganarki gaskiya ne ashe dai kinada tunani".
"afff da ki tsaya kullum kullum kina neman almajirin dazai yi miki ayyukan gida ai gara ki dinga sakata muna rage takaici da haushinta".
Inna Zulai tayi murmushin mugunta tana kallon Raihana tace"shawarar da kika bani da ita zanyi amfani saboda haka ki zuba idanu kiyi kallo, daga yau zan fara sakata aiki bazan duk'a inyi mata tuwo ta bud'e wargajejen bakinta ta cinye ba".

"ai shine na gani Inna".
"kedai ki zuba idanu kiyi kal.......".Sallamar Raihana ce ta katse mata magana ta shigo cikin tsakiyar gidan gabanta yana dukan uku uku!.

Inna Zulai tana ganinta ta mik'e tsaye azabure ta nufi wurinta gadan gadan babu alamun rahama afuskarta, yayinda Rayyanatu ta dinga ja da baya akan ta tsorata da lamarin Zulai tana isa wurinta ta fisgota da k'arfi tareda rik'e mata kunne d'aya wanda asanadiyar haka saida ta saki kuwwa tana hawaye akan zafi da rad'ad'in da gefen kunnenta keyi bakinta yana rawa tace"dan Allah Inna kiyi hak'uri".

Katsa mata tsawa tayi cikin hargowa tace"yimin shiru 'yar iskar yarinya daga zuwanki yau kin haddasa mana fitina atsakanina da mijina daga ganinki annoba ce wallahi! ".

Raihana tayi charap tace "bar munafuka argugunmar yarinya! ".

Inna Zulai ta jawota da k'arfi ta iso da ita wurin kwanonin da suka b'ata da miya tace"tunda na fahimci Iliyasu yana neman ya fifitaki akanmu to daga yau babu ke babu hutu duk ayyukan gidan nan kece zakiyi su, ga wanke wanke nan ki fara idan basu wanku ba sainayi gudunwa gudunwa da naman jikinki acikin gidan nan babu mai k'watarki ahannuna! ".
Tana k'arasa maganarta tayiwa mata mugun dundu abaya Rayyanatu ta sake fashewa da rikitaccen kuka mai cin rai da ban tausayi, dole ta isa wurin wanke-wanken ta farayi tana zubar da kwallar zallar takaici da bak'in cikin rayuwa.

Inna Zulai sai harararta takeyi kamar idanunta zasu fad'o a k'asa akan tsantsar tsana da *RASHIN SO*,daga baya ta juyo da kallonta wurin Raihana tace"'yar Inna mu shige d'aki kafin ta kammala wanke wanken in bata dahuwar shinkafa da miya".

Raihana ta shagwab'e fuskarta tace"to Inna bakida sauk'i cikin lamarinki".

"irin wannan shegiyar yarinya ba'a yi mata sauk'i sai da zafi zafi".Inna Zulai tana kai k'arshen maganarta taja hannun Raihana suka shige cikin d'aki sukabar Rayyanatu tana wanke wanke tana sharar majina yab'e yab'e afuskarta.

Haka ta cigaba dayi harta gama wanke wanken ta wanke hannunwanta duk dayake kwanonin sun fita zad sha'awa,tashi tsaye tayi ta nufi d'akin Inna Zulai tana isa bakin k'ofar tace"Inna na gama".

"shigo ki amshi shinkafa ki dafa mana".

Rayyana ta shigo cikin d'akin ta amshi shinkafar ta fito ta kunna wuta amurhu, dayake tun mahaifiyarta tana raye tana koya mata dahuwa shiyasa bata sha wahalar girka shinkafa ba harta dahu, tana dahuwa ta kwashe takai d'akin Inna Zulai ta sake bata kayan miya domin tayi miyar, jajjagen kayan miya tayi ta aza tukunyar miya ta sanya sinadarin magugguka na miya, haka ta saka komai cikin miyar harta dahu sannan ta juye cikin k'aramar kula ta dauk'a ta nufi d'akin Inna Zulai.

Tana isa tsakiyar d'akin ta gurfana tace"Inna ga miyar na kammala".

Inna Zulai ta amshi kular miyar tareda bud'e murfin kular tace"bari in d'and'ana idan tayi dad'i saboda tun wurin miya ake barin dad'in girki baya".Tana rufe bakinta ta sanya yatsarta ta lakaci miyar kad'an tareda lasawa, runtse idanunta tayi tana b'ata fuska dak'yar ta had'iye miyar a mak'oshinta mak'wat tana bintsire baki tace"miyartaki gishiri yayi yawa dan kutumar ubanki ya akayi gishiri ya zarce!? ".

Jikin Rayyanatu ya mutu cikin fargaba tace"kiyi hak'uri Inna ko lokacin da Innata tana raye dahuwar shinkafa take yawan sani ita keyin miya da kanta".

"zancen banza! Wato kina nufin uwarki bata koya miki miya ba dahuwar shinkafa kawai ta koya miki? To bazai tab'a yiyuwa ba ya zamo dole ki iya duka ayyukan cikin gida kafin wani shege ya aureki".

"Allah ya huci zuciyarki Inna".

"dallah gafara can! Raihana d'aukomin kwano in saka mata rabonta".

Raihana ta tashi tsaye ta d'auko kwano Inna Zulai ta amsa ta sanya shinkafa 'yar tsito wadda ko isarta bata yi, tana gama zuba mata ta mik'a mata awalak'ance tana harararta tace"amshi iyakar rabonki kenan tunda ba gidan ubanki bane koda ya mutu bakida gadonsa! ".

Kalamanta sun soki k'ahon zuciyarta tareda sanya b'acin rai da tsantsar bak'in ciki aranta, duk'awa tayi ta dauk'i abincin ta fice daga cikin d'akin hawaye masu zafi sai sintiri sukeyi afuskarta wani irin tururin d'aci da zogi zuciyarta keyi, d'akinta ta shiga ta zauna ta fara cin abincin cikin damuwa nan da nan ta cinye abincin tass ta kawo uban ruwa masu yawa tasha domin cikinta ya d'anyi nauyi nauyi saboda ko rabin k'oshi batayi ba,haka dai ta kwanta saman katifa zuciyarta cunkushe da tsantsar tashin hankali da takaicin rayuwa, nan da nan ta fara lumshe idanunta barci mai nauyi yayi awon gaba da ita batare data ankara ba..
____________________

Haka dai rayuwar Rayyanatu ta cigaba da gudana cikin gidan Baba Iliyasu atsangwame da k'iyayya, had'i da walak'anci duk wasu ayyukan cikin gidan ita keyi tun bata k'ware da iyawa sosai ba har tazo hannunta ya k'ware wurin sarrafa abinci da sauran ayyukan gidan, Raihana 'yar gata ko kauda kara batayi batasan ko yadda ake aza tukunya asanya ruwa ya tafasa ba saboda uwarta ta d'aure mata gindi tana aikata abubuwan data gadama babu mai kwab'arta sai Baba Iliyasu koshi idan agaban Inna Zulai ne hana masa magana takeyi, tace masa kada ya takurawa d'iyarta Raihana shi kuma ko tayi magana bashi zai hana ya ciwa Raihana mutunci ba tareda ja mata kunne akan tabi ahankali duniyar nan ta ishi kowa riga da wando wanda baixo bama jiransa takeyi.

Ire-iren wad'annan abubuwan da Baba Iliyasu yake gayawa Raihana yasa taji ta tsani mahaifinta saboda wai acewarta baya sonta ne, shiyasa yakeyi mata wasu abubuwa marasa dad'i tun yana mata nasiha da wa'azi har yazo ya daina yawan zama cikin gidan yana ganin abubuwan takaici da abinda bai dace ba, ita dai Rayyanatu baiwar Allah iyakarta ta zuba idanu tana kallon ikon Allah yadda uwa ke bada gudunmuwa wurin tab'arb'arewar rayuwar 'yarta da tarbiyarta.

Bayan shekara hud'u alokacin ne Raihana keda shekara goma takwas aduniya yayinda Rayyanatu keda sha shidda, tsantsar k'yawonsu da dirinsu ya bayyana k'arara afili lokacin ne Raihana ta had'u da saurayinta na farko Mubasshir suka fara soyayya da nunawa junansu zallar k'auna, dashi ta fara soyayya tasan miye soyayya domin komai yana yi mata gwargwadon k'arfinsa saboda shi d'alibi ne karatu yakeyi a higher institution, cikin haka ne soyayya da shak'uwa mai k'arfi ta shiga atsakaninsu ta yadda kowanensu bazai iya rayuwa idan babu d'ayansa ba.

Shima Baba Iliyasu ya amince da Mubasshir azuciyarsa saboda yaron akwai natsuwa da hankali yasan abinda ya kamata, sannan ya fito gidan mutanen k'warai masu halayyar kirki haka ne yasa mahaifin Raihana ya yarda dashi d'ari bisa d'ari, amma ita Inna Zulai mace ce mai kwad'ayi da buri har cikin zuciyarta batason d'iyarta ta auri talaka tafison ta samu mai kud'i inda zataje ta huta taci abinda ranta keso harta kawo mata itama ta dangwali arzik'i, haka rayuwarsu ke gudana kowa da abinda yake k'ullawa cikin zuciyarsa domin ganin buri ya cika...


Farkon had'uwarta da Ridwan ya samo asali ne ranar da Raihana taci had'ad'd'iyar kwalliyarta da atamfarta green colour ta kawo mayafi green ta yafa ajikinta, Inna Zulai ta bata kud'i ta siyo musu kifi d'anye akasuwa wanda za'ayi miya dashi Raihana ta amshi kud'in ta fice daga cikin gidan, bayan taje kasuwa ta siyo kifin akan hanyar dawowa tayi gamdakatar da Ridwan wanda tozali d'aya yayi da k'yak'k'yawar fuskarta farat d'aya ya kamu da matsananciyar soyayyarta, akan hanya ya tareta yayi mata lift ita kuma babu ko kunya ta shiga cikin motarsa ya kawota har bakin k'ofar gidansu ya ajeta kafin ya wuce saida sukayi exchanging numbers sannan ya bata kud'i dubu ishirin yayi ficewarsa daga bakin k'ofar gidansu.
Da murna Raihana ta shiga cikin tsakiyar gidan tana tsallen farin ciki da tsananin nishad'i tana isa wurin mahaifiyarta ta rungumeta cikin jin dad'i, Inna Zulai ta saki baki tana matuk'ar mamakin ganin d'iyarta cikin farin ciki kauda komai tayi ta fara tambayarta abinda ya sanyata cikin farin ciki...........
[12/5, 9:30 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 4*


Cin abincin yakeyi yana sak'e sak'e azuciyarsa har ya kammala ya mik'e tsaye ya d'auko handouts d'insa yana nazari da karatu,phone d'insa dake gabansa tayi ruri alamar tana neman agaji receiving call yayi yace"hello Muk'addas ya akayi? ".
Ab'angaren Muk'addas ya ajiyar zuciya yace"lafiya k'alau friend dama inason in sanardakai lecturer Haris zaiyi mana tests anjima".
"OK friend which time?".
"k'arfe hud'u da rabi 4:30pm bayan la'asar".
"nagode daka sanardani saboda yau kwata kwata banyi niyar shiga school ba".
"ai shiyasa na gaya maka da wuri saboda malamai yanzu k'iris suke jira suba mutum carry over".
"tabbas maganarka gaskiya ne friend ubangiji yasa mu tsallake sharrinsu".
"Amin sai anjima".
"OK".Muk'addas ya katse wayar yayinda Mubasshir ya jawo handout d'in lecturer Haris yana dubawa.
___________________

Inna Zulai tana zaune itada Raihana suna zancensu k'usu k'usu tareda sassauta muryarsu domin basu son Rayyanatu taji abinda suke zantawa.
Inna Zulai tace"Raihana ki daina barin mahaifinki yana ganin kina shiga cikin motar saurayi kuna fira, saboda kinga daya shigo ni yakeyiwa fad'a da surutun banza da basuda ma'ana ko dad'i".
Raihana ta zumb'ura baki tareda b'ata fuska takaici ne shimfid'e afuskarta tace"haba Inna ki daina biyewa surutun Baba shi fa baisan inda duniya ta sawa gaba ba, ai yanzu zamani ya chanza kai ya waye babu mai yin harakar k'auyanci saina wayewa".
"maganarki gaskiya ne maxan yanzu idan kina harakar k'auyanci babu mai sonki saboda yanzu kai ya riga ya shigo zamanin wayayyi".
"Inna Ridwan yana sona shiyasa nake mutuwar sonsa banason rabuwa dashi arayuwata".
Inna Zulai ta dafa kafad'arta tace"ki kwantar da hankalinki babu abinda zai rabaku sai mutuwa".
"har naji dad'i araina Inna ina wai Rayyanatu taje ne naji banji motsinta ba?".
Inna Zulai ta gyad'a kanta tace"tun safe da tayimin wanke wanken kwanoni tana cikin d'aki bari in kirata tazo ta dafa mana abinci muci yunwa nakeji".
Raihana ta yamutsa fuskarta tace"nima yunwa nakeji".
"to bari inje d'akinta".
"Uhmm Inna".Inji Raihana cikin sagarci da shagwab'a.
Inna Zulai ta tashi tsaye ta nufi d'akin da Rayyanatu take barci tana isa tsakiyar d'akin ta hangota kwance saman k'aramar katifa tana barci,jijjiga kai Inna Zulai tayi cikin zafin rai ta tunkari wurinta tana isa ta dunk'ule hannunta tayi mata mugun bugu abaya, asanadiyar haka saida Rayyanatu ta zabura da k'arfi afirgice jikinta sai mazari da k'yarrrma yakeyi saboda ta tsorata sosai, ganin Inna tsaye agabanta yasa hankalinta ya tashi fargaba da tsantsar tsoro ne ya bayyana k'arara afuskarta cikin shakku tace"Inna lafiya mi nayi miki?".

Inna Zulai tayi mata dak'uwa tace"ungo kinci gidanku ni zaki tambaya kice mi kikayimin dan kina d'iyar shegiya! Waye ya baki iznin barci bayan kinsan bakiyi girki ba?".

"yi hak'uri Inna nima bansan lokacin da barci ya saceni ba wlh".

"rufemin baki! Banason k'aryar banza tashi kije ki girka mana abincin rana muci ko yanzu jikinki ya gaya miki".

Rayyanatu ta tashi tsaye hawayen takaici sai shatata sukeyi afuskarta wani irin tururin d'aci da zogi zuciyarta keyi, noce kanta tayi a k'asa tace"mi zan dafa Inna? ".

"dafadukan shinkafa da taliya zaki girka mana sannan ki share munafukan hawayenki afuska, saboda ba dukanki nayi ba bale ki azamini kukan munafurci bak'ar makira wadda tayi gadon mugun hali!".

Rayyanatu tasa tafin hannunta ta share hawayenta tsab ta fice daga cikin d'akin da sauri, domin kada Inna Zulai ta jibgeta abanza da yofi saboda tasan k'iris take jira ta rufeta da shegen duka.
Inna Zulai ganin Rayyanatu ta fice daga cikin d'akin yasa itama ta fito a d'akin ta nufi d'akinta.
*********************
Rayyanatu ta cigaba da kai da kawo cikin kitchen tana kichaniyar girka dafadukan shinkafa da taliya, jajjagen kayan miya tayi ta zuba cikin tukunya bayan ta gama tafasa mangyad'a, sinadarin magugguka da komai ta sanya cikin dahuwar k'amshin girkinta sai tashi yakeyi,zaune tayi har abincin ya dahu ta kwashe cikin kula ta rufe sannan ta zubawa tukunyar da tayi dahuwa ruwan sanyi domin kada ta bushe.
D'aukar kular abincin tayi ta nufi d'akin Inna Zulai tana isa bakin k'ofar tayi sallama, babu wadda ta amsa mata daga cikinsu akan sun tsaneta atsawace

Please Login or Register in order to submit comment