Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'arasa ginin gidanka ka turo magabatanka gidanmu asa mana rana".
Kallon bakida hankali yayi mata sannan ya sakar mata yaudararren murmushinsa wanda yake k'ara narkar da zuciyarta ta afka cikin kogin sonsa yace"ki k'ara bani lokaci baby har na fara had'a lefenki so nake idan na kammala had'awa sai ayi auren sharp sharp".
Raihana tayi jugum har cikin zuciyarta tana kwankwaton kada Ridwan ya yaudareta bayan ya rabata da abu mafi daraja arayuwarta wato budurcinta, amma gudun kada ya zargi tana shakku akan kalamansa yasa tayi ajiyar zuciya tace"ba damuwa ubangiji ya nuna mana lokacin lafiya yasa munada tsawon rai".
"Amin babyna koke fa ki yarda dani bazan tab'a cin amanarki ba".

Raihana ta jijjiga kanta alamar gamsuwa da maganarsa tace"na gamsu da bayaninka nasan bazaka cutar dani ba habibi".
Cikin zuciyarsa yace zan baki matuk'ar mamaki Raihana idan banda kina jaka mai k'wak'walwar kifi taya za'ayi bayan na sanki 'ya mace tun kafin in aureki sannan daga baya inzo in aureki,wannnan bazai tab'a yiyuwa ba har abada saboda niba lusarin namiji bane dazan auri fankon mace!.

_Komawa gefe nayi ina matuk'ar mamakin halayyar Ridwan bayan shine ya lalata mata rayuwa amma yanzu yake kiranta da fankon mace,lallai namiji da kuke gani mugu ne duk hanyar da zaibi ya yaudari mace ya cimma burinsa akanta sai yayi sannan daga k'arshe ya nuna baima tab'a ganinki arayuwarsa ba._

*********************

*BAYAN SHEKARA BIYU*
Alokacin ne Mubasshir ya kammala karatunsa ya dawo gida ya fara fafutukar neman aiki amma dayake mun shigo cikin wani irin lokacin da sai kanada galihu kake samun aiki, ganin babu inda baikai takardunsa ba amma bai samu aiki ba dole ya samu shago yana tsaro ana biyansa dubu goma duk wata, ta haka ne yake samu yana d'aukar lalurar mahaifiyarsa da d'awainiyarsa cikin rufin asiri.

Wata rana suna zaune shida Ummansa suna zancensu na tsakanin uwa da d'anta sai Umma ta kallesa cikin k'auna da tausayin d'anta tace"Mubasshir inason yin wata muhimmiyar magana dakai".

Mubasshir ya mayarda hankalinsa kacokam wurin mahaifiyarsa yace"ina saurarenki Ummana".

Umma ta saki doguwar ajiyar zuciya cikin kamala da sanin ya kamata tace"Mubasshir ya kamata ace kayi aure hakanan ka kai munzalin daya kamata ace ka ajiye iyali".

Mubasshir ya natsu yana sauraren maganar dake cikin bakin Ummansa saida ta dasa aya yace"nifa Umma bawai auren ne banaso ba ta yaya kike tunanin zanyi aure alhalin muna cikin matsanancin hali, abinda zamu ci wata rana gagararmu yakeyi to yaya kike gani idan na d'auko wani nauyi na aza saman wuyana?".

Umma ta gyad'a kanta cikin jimami da sauyin yanayi tace"ka daina fad'ar irin wannan kalaman Mubasshir shi arzik'i da kake gani na Allah ne, sannan mutum baya tab'a cire tsammanin zai samu arzik'i ko bazai samu ba? Kowane irin bawa da irin nashi k'addarar rayuwa ka kwantar da hankalinka d'ana kaje ka nemi budurwa kayi aure da yardar Allah *JINKIRIN ALKHARI* yana nan tafe".

Mubasshir yace cikin tattausan lafazi mai dad'i"naji bayaninki Umma insha Allahu zan nemo mata in aura hankalinki ya kwanta nima in samu natsuwa".

Umma tace"yayi k'yau matuk'a ubangiji yayi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya".

"Amin amin Ummana ina godiya ga ubangiji daya bani ke amatsayin mahaifiyata mai son farin cikina".

"nima ina alfahari da samun d'a nagari irinka Mubasshir ko cikin 'ya'ya daban kake".

Haka cigaba da firarsu sukeyi cikin matuk'ar natsuwa da tsantsar k'aunar juna, wasa da dariya sukeyi kamar basuda wata matsala arayuwa.
____________________

Lauratu matar Baba Iliyasu tuni ta haifi 'ya'yanta 'yan tagwaye mace da namiji sunansu Nazir da Nazira mahaifinsu yana tsananin k'auna da sonsu bayason abinda zai sakasu hawaye, yayinda Inna Zulai da Raihana babu abinda suka tsana aduniya irinsu Nazira da mahaifiyarsu domin ayanzu kwata kwata Zulaiha bata cikin zuciyarsa Lauratu ta riga ta siye zuciyarsa wurin k'yautatawa da iya lafuzza masu dad'i da sanyaya zuciyar mai sauraro, duk da ganin ta samu fada azuciyar Baba Iliyasu baisa ta walak'anta rayuwar Inna Zulai ba saidai idan haukarta ya tashi tayita fad'a kamar mahaukaciya kamun hauka Lauratu ko kallonta batayi bale ta biye mata suyi fad'a.

K'yaluwar da takeyi mata shine abinda yake k'onawa Inna Zulai rayuwa tareda sanya zafi da tsantsar bak'in ciki azuciyarta, Baba Iliyasu ma dayake ya fahimci Inna Zulai babu abinda take nema sai fitina da tsantsar tashin hankali shiyasa ya daina shiga sha'aninta aranar girkinta idan ta gadama ta kulasa idan ta gadama ta fita batunsa, babu abinda ya damesa domin yasan halinta tuntuni batada kulawa da darajashi tuntuni shiyasa ma ya k'udurta azuciyarsa wannan shekara bazata k'are ba batare daya aurar dasu Raihana ba, kowaccesu zai k'ok'arinsa yakeyi yaga ta samu mijin aure ya aurar dasu ya huta da ganin wulgawarsu cikin gidansa..

Cikin haka ne wata rana Lauratu ta kira Rayyanatu ta aiketa zuwa kasuwa da rana dayake yarinyar akwai natsuwa da kirki tamkar mahaifiya ta dauk'i Lauratu, saboda tunda ta auri Baba Iliyasu ta daina barinta tana zama da yunwa da yawan kad'aici idan miji baya d'akinta sai tasa Rayyana ta koma d'akinta tana tayata zama da fira, shiyasa buzut d'aya Lauratu ta siye zuciyar Rayyanatu da k'yautatawa da matuk'ar nuna mata tausayi da tarairaiyarta kamar k'wai.
Ganin yadda Lauratu ke nunawa Rayyanatu so da kulawa yasa hassada da tsantsar bak'in ciki ya wanzu azuciyarsu Inna Zulai, sukaji kamar su kashe kansu akan damuwa da takaicin rayuwa amma dayake Lauratu tasha gabansu babu yadda suka iya saida hak'uri da dangana dole saboda atsaye take da k'afafunta bata wasa da karatun qur'ani da yawan azzakar shiyasa duk irin mugun nufin dake cikin zuciyarka ubangiji ya kareta baka isa kaci galaba akanta ba.

Rayyanatu taje kasuwa ta dawo akan hanyar dawowarta tayi kicib'is da Mubasshir wanda yaketa sauri ya koma gidansu, ganin sun bugi juna yasa suka d'ago idanunsu atare suka fad'a cikin na juna cikin sanyin hali Rayyanatu tace"kayi hak'uri bawan Allah ban lura dakai ba shiyasa na bangajeka".

Murmushi Mubasshir yayi yace"ni yafi dacewa in baki hak'uri baiwar Allah saboda haka kiyimin afuwa".

Rayyanatu tayi murmushin dake bayyana tsantsar k'yawonta tace"ayyah ba komai wallahi tsautsayi ne ai".

"OK shikenan k'anwata nizan wuce inda zanje"."Ohh ba matsala".Tana rufe bakinta ta nufi hanyar gidansu yayinda Mubasshir yake binta abaya sannu ahankali saboda ganin da yayi mata farat d'aya yaji ta kwanta masa arai, sannan daga ganin yanayinta ya tabbatar da batada girman kai ganin gidan data shiga yasa ya gano gidansu tsohuwar budurwarsa ce Raihana, hakan baisa yaji d'igon son dayake mata ya ragu ba ganin gidan ne yasa ya juya ya nufi hanyar gidansu domin ya gayawa Ummansa ya samu mata.

Rayyanatu tana shiga cikin gidan direct d'akin Lauratu ta nufa ta bata sak'onta godiya sosai Lauratu tayi tana murmushi afuskarta tace"amma kinyi matuk'ar sauri sosai Rayyanatu ubangiji ya nunamin lokacin aurenki".

Rayyanatu ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta cikin kunya tace"amin Aunty aganinki nayi sauri kenan? "."Jaye hannunki babu kunya atsakaninmu kinji ai gaskiya nake fad'a kinyi sauri".Rayyanatu ta jaye hannunta farin ciki k'unshe afuskarta tace"naji Aunty".

Lauratu ta kalleta tace"ga abincinki nan kici idan kika kammala saiki wanke kayayyakinsu Nazir"."To".Kawai ta fad'a ta nufi wurin da aka ajiye mata abinci ta d'auko ta zauna tana ci sannu ahankali kamar batason taunawa,saida ta kammala cinye abincin sannan ta mik'e tsaye ta kwashi tufafinsu Nazira ta fara wankewa tana shanyawa akan igiyar shanya.........
[12/6, 3:20 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 11*



Rayyanatu tana wankewa tana shanyawa akan igiyar shanya harta kammala wankinta ta duk'a tana wanke hannayenta da ruwa masu tsabta,saiga Raihana ta gifto gabanta tana tafiya guda guda kamar zata karye kallon walak'anci tayiwa Rayyanatu tace"baiwar banza ahaka rayuwarki zata k'are abautar k'atanyar banza da yofi! ".Jin saukar magana a dodon kunnenta yasa ta d'ago fuskarta ahanzarce dayake bata lura da tsayuwar mutum kusa gareta ba tace"babu abinda ya shafeki ko na k'are rayuwata ahaka sannan ko nayi bauta awurin Aunty Lauratu ta cancanci fiyeda haka awurina, saboda tayimin abinda yayar mahaifiyata wadda suke uwarsu d'aya ubansu d'aya ta kasa yimin tareda tsamgwama da musgunawa rayuwata, yabon gwani ya zamo dole Raihana ina matuk'ar k'aunar Aunty Lauratu dayi mata tsantsar *SOYAYYAR GASKIYA* wadda babu yaudara cikinta"..
Raihana ta harzuk'a zuciyarta ta kawo awuya tace"keee shegiya karki nemi ki gayamin maganar banza yanzu nan in jibgeki in jibgi banza! "..
Rayyanatu ta tashi tsaye tace"ada ba ayanzu kinyi kad'an kice zaki dakeni ban rama ba tunda ni ba jakar uwarki bace! "..
Raihana ta nuna kanta cikin matuk'ar mamakin sauyin yanayin Rayyana tace"mahaifiyata kike zagi? Bayan uwarki kafin ta rasu saida tayi cikin shege kuma kowa ya sani! "..
Maganarta ta soki k'ahon zuciyar Rayyanatu cikin firgici da kad'uwa akan kalamanta wani irin tururin d'aci da bak'in ciki ne ya gauraye jininta da zuciyarta tace"mahaifiyar tawa ce tayi cikin shege Raihana shin bakisan cewa itama mahaifiya ce agareki ba?".

"na fad'a da babbar murya uwarki tayi cikin shege na kuma maimaita miki kiji da kunnenki in yaso zuciyarki ta tarwatse ki mutu banida hasara sai riba!".

Hawaye masu zafi suka wanke fuskar Rayyanatu cikin matuk'ar b'acin rai da k'unar zuciya tace"bazan mutu ba sai lokacina yayi Raihana duk sharri da k'azafin da kikayiwa mahaifiyata wadda bataji bata gani ba sai ubangiji yayi mata muguwar sakayya akanki da mahaifiyarki! ".Tana k'arasa maganarta Raihana ta d'aga hannu zata kasheta da mari Rayyanatu tayi sauri ta chapki hannunta cikin matuk'ar zafin nama, kallonta tayi cikin ido da ido tace"karki kuskura ki k'ara kuskuren cewa zaki mareni Raihana saboda haka ki kiyaye domin gaba".

Raihana tace cikin matuk'ar mamakin k'arfin hali irin na Rayyanatu "sakarmin hannu ko inci ubanki!".

"bazan saki ba".

Jin hayaniyarsu ta gauraye gidan yasa Aunty Lauratu da Inna Zulai suka fito kusan atare daga cikin d'akinsu,suka nufi wurinsu Raihana dake tsaye suna jifan juna da bak'ak'en maganganu suna isowa Aunty Lauratu ta shiga atsakaninsu taja hannun Rayyana ta mayarda ita gefe tace"kuyi hak'uri bai kamata ace 'yan uwan juna daku ba kuna sa'insa wannan ba girmanku bane".

Inna Zulai tayi charab tace"dakata tsohuwar munafuka ina ruwanki da shiga sha'anin daba naki ba, ai duk abinda Rayyanatu keyi kece kike zugata tareda d'aure mata gindi tana walak'anta mutane ada batasan tayiwa Raihana rainin wayo ba sai zuwanki gidan nan annobar gari! ".

Kalamanta sun k'ona zuciyar Aunty Lauratu tareda sanya b'acin rai da bak'in ciki azuciyarta, kallon Inna Zulai tayi tace"amma matar nan bakisan mutunci ba ni kikewa k'azafin cewa ni nake zuga Rayyanatu?"..

Inna Zulai ta zaburo mata cikin hargowa tace"eh mana kece duk abinda yake faruwa acikin gidan nan na munafurci duk sharrinki ne".Kamar zata dungurewa Lauratu goshi akan son fitina, ganin Inna Zulai tana batun takai ga jikinta yasa Anti Lauratu ta chapke mata hannu tace"na fahimci bakida hankali saina tsira miki hak'orin hankali".

"kece bakida hankali karuwar gari wadda saida ta biye gari da yawon karuwanci sannan wawan nan ya aureki".

"da karuwancin da komai ahaka mijinki ya gani ya aura har yafi sona akanki saboda bakida mutunci bakisan muhimmancin miji ba! ".

Inna Zulai ta buga kuwwa tana ifface ifface tace"wato haka Iliyasu yake gaya miki idan kuka shige cikin d'aki ko?".

"eh mana haka yake gaya mini baki sani ba".Tana rufe bakinta saiga sallamar Baba Iliyasu ya shigo cikin tsakiyar gidan hangosu yayi tsaye cirko cirko suna hayaniya, shiyasa yazo ya rabasu cikin matuk'ar b'acin rai da takaici azuciyarsa yace"wai mi yake faruwa ne kun mayarmin da gida kamar gidan dabbobi? Hayaniyarku da fad'anku kawai akeji agari! ".

Inna Zulai ta rik'e k'ugunta tana girgiza jikinta tace"duk abinda yake faruwa cikin gidan nan kaine kake zuga shegiyar matarka tayimin rainin wayo da rashin mutunci?".

Baba Iliyasu ya kalleta cikin rashin fahimta yace"mi kike nufi Zulaiha ban fahimci maganarki ba".

"matarka Lauratu ita ke turo Rayyanatu tana zagin Raihana tareda gaya mata bak'ak'en maganganu marasa dad'in saurare.... ".Ta kwashe k'arya da gaskiya ta gayawa Baba Iliyasu bayan ta gama bayaninta.

Baba Iliyasu ya juya b'angaren Anti Lauratu yace"naji bayaninta kema ki fad'i musabbabin fad'anku?".

"har sai ka tambayeta idan ba rashin adalci kakeson yi ba! ".

Baba Iliyasu ya daka mata rikitaccen tsawa yace"dakata!Kiyimin shiru in saurari bayaninta banason neman fitina da rigima".Yana kammala maganarsa Anti Lauratu tayi nata bayani sannan ya tambayisu Raihana d'aya bayan d'aya kowace daga cikinsu ta kawo bayaninta.

Bayan ya gama jin bayanin kowaccesu sannan ya saki doguwar ajiyar zuciya yace"dama kune musabbabin haddasa fitina acikin gidan nan! To ku saurara da k'yau kujini ke Rayyanatu wani yaro ya turo iyayensa wurina domin ya nemi iznin fara zuwa fira wurinki, kuma na aminta dashi na bashi dama ya nemi soyayyarki ke kuma Raihana na baki wata biyu rak ki fito da mijin aure idan ba haka ba zan aura miki duk wanda na gadama nadai gaya muku gaskiya kowacceku ta shiga taitayinta dani".Yana k'arasa maganarsa ya nufi hanyar cikin d'akin amaryarsa Lauratu yayinda itama Lauratu ta bishi abaya,Rayyanatu cikin sanyin jiki ta nufi d'akinta yayinda Inna Zulai taja hannun Raihana suka shige cikin d'aki.

Suna isa tsakiyar d'akin sukayi masauki saman gado kowacessu da abinda take sak'awa cikin zuciyarta, can Inna Zulai ta kalli Raihana cikin damuwa da matuk'ar sanyin jiki tace"Raihana tunda babanki ya furta cewa aure zaiyi muku ya kamata ki gayawa Ridwan ya turo da magabatansa asa muku ranar aure".

Raihana ta d'ago fuskarta cikin tsananin damuwa tace"zan gaya masa abinda ake ciki Inna karki damu".

"ya dace ki sanardashi kinji Babanki ya baki wata biyu ki fito da mijin aure idan suka cika zai iya aura miki miji talaka, kinsan shi baisan duk inda duniya ta sawa gaba ba babu mai son auren talaka ".

Raihana ta bintsire baki tace"bazan yarda ma da zab'insa ba ko Rayyanatu dayace ta samu mijin aure nasan baya wuce takala wanda bayada ko sisi".

"maganarki gaskiya ce Raihana ai Iliyasu bayada tunani komai saidai kiji yace da talaka da mai kud'i duk d'aya ne, alhalin ba d'aya bane tunda abinda mai kud'i ke iyayi talaka ko yaso yayi baya iyawa".

"aiko awurin furtasu ba d'aya bane Inna shidai haka rayuwarsa take baya dogon nazari kafin ya yanke hukunci".

**********************
Raihana tayi magana da Ridwan akan ya turo magabatansa ad'aura musu aure ya lallasheta da yaudararrun kalamansa yace mata zai turo, ayayinda Mubasshir har ya fara zuwa zance wurin Rayyanatu kuma sun fahimci juna farat d'aya taji ya kwanta mata arai zuciyarta ta amince dashi ,shima ya yaba da natsuwa da hankalinta ya tabbatar yayi dace da mace ta gari abar alfahari ga kowane d'a namiji , ganin soyayya mai k'arfi ta k'ullu atsakaninsu yasa Mubasshir ya turo magabatansa aka saka ranar aure nan da wata biyu, Raihana bata fahimci da ko waye Rayyanatu take soyayya ba sai daga baya har azuciyarta taji ciwo da zafin yadda Mubasshir yayi soyayya da ita sannan daga baya ya dawo son Rayyana wadda take matsayin k'anwarta, hakan yasa ta k'ara tsanar Rayyanatu tareda nuna mata tsantsar hassada da bak'in ciki afilin wuri, duk abinda takeyi Rayyanatu ta ganota amma dayake itace tayi *SAKE* har akayi mata sakiya shiyasa bata shiga cikin sha'aninta saboda tasan tankawa ma yabawa ne.

Haka dai al'amurran suka cigaba da tafiya da dad'i daba dad'i agidan Baba Iliyasu bak'in ciki da damuwa duk sun taru sun cunkushe azuciyar Raihana, saboda taga Baba Iliyasu duk ya sassayi kayan aurensu itada Rayyanatu komai iri d'aya ya siya musu bai nuna bambanci ba, hakan da yayi ya matuk'ar yiwa Inna Zulai da Raihana zafi da tsantsar bak'in ciki azuciyarsu saboda babu yadda suka iya ne shiyasa sukayi shiru da bakinsu, Anti Lauratu ta yiwa Rayyanatu sayayyar kayayyakin aure saikace itace ta haifeta domin ita da zuciya d'aya take zaune da ita kuma tana sonta tsakani da Allah.

*BAYAN WATA D'AYA*
Bikin Rayyanatu sai gabatowa yakeyi alokacin ne su Anti Lauratu suka kammala sayen duk abinda ya kamata ya dace, itadai Inna Zulai ko abinda bataso bata siyawa Rayyanatu ba saidai d'iyarta Raihana ,ana nan wata rana Raihana ta kamu da matsananciyar rashin lafiya wanda kallo d'aya zakayi mata ka gano tana d'auke da ciki idan har mace tanada lura, ganin d'iyarta Raihana batada lafiya yasa duk hankalin Inna Zulai yayi k'ololowar tashi ji takeyi gabanta yana yawan fad'uwa! Baba Iliyasu baisan abinda yake faruwa ba saida Inna Zulai ta gaya masa tace Raihana batada lafiya ya kamata ya bata kud'i ta kaita asibiti, addu'ar fatar samun waraka yayi mata sannan ya ciro kud'i daga cikin aljihunsa dubu goma yaba Inna Zulai amsawa tayi cikin rashin godiya baba Iliyasu yayi gaba ya fice daga cikin gidan ya nufi inda zaije.
Inna Zulai da kanta ta taimakawa Raihana ta shirya sannan suka tari keke napep ya kaisu bakin get d'in asibiti ya aje, Inna Zulai ta biyasa kud'insa ya k'ara gaba jan hannunta Raihana tayi suka nufi cikin asibitin suna isa suka yanki kantin ganin likita aka bud'awa Raihana file, zaunawa sukayi saman kujera suna jiran har akirasu layi yazo kansu bada jimawa ba likita ya kira sunan Raihana Iliyasu suka mik'e zumbur itada Innarta suka shiga cikin had'ad'd'en office d'in doctor, bayan sun zauna saman kujerar dake cikin office d'in doctor ya fara tambayarta mi da mi yake damunta? Raihana tayi masa bayanin duk yanayin da takeji ajikinta sannan daga k'arshe ya bata k'aramar kwalba tayi fitsari cikinta shiga tayi cikin toilet tayi fitsari cikin kwalbar ta basa, yayi rubuce rubucensa sannan yace musu su dawo wani sati ya basu result d'in abinda yake damun Raihana,su Inna Zulai sukayi godiya suka fice daga cikin office d'in doctor suka nufo hanyar zuwa gida..........
[12/6, 3:20 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 12*


Suna dawowa Inna Zulai ta tambayi Raihana mi takeson ci dayake ta fahimci kwata kwata bata iya cin abincin kirki, Raihana ta zumb'ura baki cikin shagwab'a tace"nama da yoghurt".Inna Zulai ta jawo mayafinta ta yafa ajikinta tace"bari in samu yaro amak'wabta ya siyo miki 'yar lelen Inna".
Raihana ta cize baki cikin matuk'ar zafin ciwo tace"to Inna".Inna Zulai ta fito daga cikin d'akinta kicib'is ta had'u da Anti Lauratu tana ganinta taja tsoki mtssss tace"komai dai bak'in cikin tanda sai munci waina ko ba'a cewa d'iyata ba ya jiki bashi zai hana ta samu lafiya ba".Anti Lauratu tace"ayyah yi hak'uri ban sani ba aini bana fatar tak'i samun lafiya saboda d'iyar mijinka ai d'iyarka ce".
"hmmmmm haka kike fad'a abaki baikai zuci ba".
Ganin Inna Zulai neman fitina takeyi dole yasa Anti Lauratu taja bakinta ta tsuke bata sake tanka mata ba, saboda tankawa ma yabawa ne shiyasa Inna Zulai ta isa bakin k'ofar gidan ta kira wani saurayi Sani domin ya siyo mata yoghurt da nama, saurayin ya amsa bai dad'e ba ya kawo mata sak'onta tayi godiya ta dawo cikin gidan direct d'akinta ta nufa da leda ahannunta tana isa ta taimakawa Raihana ta tashi zaune tareda mika mata ledar ta fara cin naman da sauri sauri tana shan yoghurt saida ta cinye naman tass da yoghurt d'in sannan taji ta k'oshi ta koma ta kwanta barci ya saceta batare data ankara ba.

Inna Zulai tayi jugum cikin matuk'ar damuwa sai kallon 'yarta takeyi tana tausaya mata, duk wani motsin da Raihana zatayi akan idanun mahaifiyarta ne saboda bata d'aga ko nan da can ba adalilin rashin lafiyar Raihana.
____________________

*BAYAN SATI D'AYA*

Su Inna Zulai suka shirya tunda safe suka nufi hanyar asibiti suna isa basu dad'e ba suka samu ganin doctor dayake sunyi sammako, suna shiga cikin office d'in doctor ya basu result d'in abinda yake damun Raihana kallon Inna Zulai yayi da murmushi k'unshe afuskarsa yace"congratulations Inna yarinyarki tana d'auke da cikin wata uku".
Dummmm gaban Inna Zulai ya buga da k'arfi hankalinta ya d'unguma zuciyarta sai fat fat fat takeyi, cikin yak'e Inna Zulai tace"ban fahimci inda maganarka ta dosa ba likita sake fad'a inji?".
Doctor yace fuskarsa asake"ina nufin d'iyarki tana d'auke da cikin wata uku ya kamata kuyi gaggawar sanarda mijinta wannan k'yak'k'yawan albishir".
Inna Zulai batasan lokacin data zabura da k'arfi ba yayinda Raihana duk ta rikice da kad'uwa cikinta sai k'ugin tsoro yakeyi jikinta yana k'yarrrma, ganin Inna Zulai ta gigice yasa doctor ya kalleta cikin matuk'ar mamaki yace"lafiya Inna miye ya firgitaki?".
Inna Zulai ta tattaro dauriya da natsuwa ta danne komai cikin zuciyarta tace"a'a babu abinda yake damuna farin ciki ne ya sanyani shiga cikin wani yanayi saboda aurenta yakai shekara biyar bata samu haihuwa ba"..
Doctor yace"ayyah komai lokaci ne wani *JINKIRIN ALKHARI* ne Inna saboda haka kusa aranku babu abinda yake dawwama aduniya farin ciki ko bak'in ciki".
Inna Zulai ta jijjiga kanta alamar gamsuwa da maganarsa tace"haka ne likita mungode sosai da wannan albashir ke tashi muje gida mu sanarwa mijinki abinda ake ciki".
Cikin mutuwar jiki Raihana ta tashi tsaye damuwa da takaicin rayuwa k'unshe afuskarta, jan hannunta Inna Zulai tayi suka fito daga cikin asibitin suka nufi wata hanyar daban inda mutane basu cika giftowa ba.

Suna isa wani lungu Inna Zulai taja tayi tsaye turus tana yiwa Raihana kallon tuhuma da bak'in ciki idanunta sun kad'u sunyi jawur akan b'acin rai yayinda Raihana ta duk'ar da kanta k'asa cikin alamun rashin gaskiya, uwar ta sanya hannunta ta d'ago fuskarta cikin kakkausar murya tace"d'ago fuskarki ki kalleni Raihana ki gayamin maganar gaskiya waye yayi miki ciki?".
Raihana tayi shiru jikinta duk yayi lak'was zuciyarta ta tsinke tayi shiru bata ce komai ba, ganin tayi shiru yasa Inna Zulai ta hasala matuk'a da k'yaluwarta tace"wallahi sai kin gayamin ko waye yayi miki ciki ko yanzu in kasheki in huta da takaicin duniya! Duk kud'in da kike samowa kina kawomini ashe cinki akeyi ban sani ba ashe kin iya gwale k'afafuwa ana zura miki maciji cikin k'ugunki,saboda haka ki gayamin waye yayi miki ciki!?".Ta fad'a atsawace.

Hawaye masu zafi suka cigaba da gangarowa afuskar Raihana jikinta yana mazari da k'yarrrma tace"babu wanda yayi mini ciki".

"zancen banza kenan! Babu wanda yayi miki ciki kece kikayiwa kanki ciki ko aruwa kika sha? Wannan k'aryar taki bata ko kawo kallo ba kece kika ci kanki ba namiji ya ci ki kenan ba, lallai da kisa inji kunya cikin mutane gara na kasheki in binne gawarki anan babu wanda zai sani munafuka! ".

Inna Zulai ta d'auko k'aton dutse ta rik'e ahannunta tace"zaki gayamin gaskiya ko bazaki gayamini saina fasa miki kai da dutse kin mutu in huta da takaici da bak'in cikin rayuwa!?".

Ganin Inna Zulai da gaske take zata iya fasa mata dutse akai nan da nan jikinta ya d'auki mazari da rawar tsoro tace"Inna Ridwan ne yayi mini ciki ba kowa ba!".

Inna Zulai ta yarda dutse ahannunta ta sake maimaita sunansa tace"Ridwan!?".Tace cikin matuk'ar kad'uwa da mamakin wautar Raihana.
Raihana ta girgiza kanta alamar eh mana tace"eh wallahi shine yayi mini ciki!".

Inna Zulai ta musk'uta cikin matuk'ar b'acin rai da tsantsar tashin hankali tace"lallai yau zai gamuda b'acin rai muje gidansu inga ubansa kinsan gidan iyayensa dan ubanki?".

"eh.. eh. ma...na... na sani... ".Tace cikin rawar murya".
"to muje gidansu 'yar iska mara wayo! ".Tana rufe bakinta taja hannun Raihana suka fito daga cikin lungun suka nufi titi suka tari keke napep tareda yi masa kwatancen unguwarsu iyayen Ridwan.

Sunyi tafiya mai nisa suka iso a k'ofar tangamemen gida mai fankacecen get mai keke napep ya saukesu suka biyasa kud'insa ya k'ara gaba, jan hannun Raihana Inna Zulai tayi suka iso wurin baba maigadi suka gaidashi ya amsa musu cikin sakin fuska, alokacin ne Inna Zulai tace masa"dan Allah tambaya muke".
"ina saurarenku".Cewar baba maigadi.
Inna Zulai tace"gidan Alhaji Shafi'u matawalle".
"nan ne miyasa kuke nemansa?".
Inna Zulai ta marairaice fuskarta kamar zatayi kuka tace"taimakonsa muke nema d'iyata ce takeda lalurar tab'in hankali shiyasa nakeson ganinsa domin ya taimaka mana da kud'in da za'ayi mata magani".
Baba maigadi yace"bari in shiga cikin gida in gaya masa kunason ganinsa ubangiji ya bata lafiya".
"Amin amin bawan Allah".Inji Inna Zulai.
Baba maigadi ya juya ya shiga cikin gidan bai wani jima ba sai gashi ya fito yace mata"Alhaji yace su shiga cikin gidan su iskosa".
Babu tunani da fargabar komai suka afka cikin gidan Inna Zulai tana gaba yayinda Raihana take biye abayanta har suka iso tsakiyar parlourn, suka iske Alhaji Shafi'u zaune saman cushion

Please Login or Register in order to submit comment