Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kokensu suna nadamar irin abubuwan da suka aikata arayuwarsu, tabbas duniya mai ganin iyakar kowa ce shiyasa akeson mutum ya taka asannu ya dinga aikata alkhairi kada kabi kowa da sharri duk wanda ya biki da sharri kibarsa da ubangiji baya kwana baya angaje, shi zai miki sakayya tun anan duniya saboda haka kubi duniya asannu 'yan uwana mata.
Washe gari da safe misalin k'arfe sha d'aya na safe dubban mutane suka shaida d'aurin auren Ridwan Shafi'u da amaryarsa Safina Jamilu akan sadaki dubu d'ari lak'adan, d'aurin auren ya samu halattar mutane da dama cikin kuwa harda abokan Alhaji Shafi'u da k'usoshin gwamnati wad'anda akeji dasu awannan k'asar tamu, dayake Alhaji Shafi'u babban mutum ne daya shahara aharakar kasuwanci da shiga da fice k'asashen k'etare, shiyasa ya zamo sananne shahararre acikin wannan k'asar tamu yanada tarin dukiya da kadarori wadanda bazai iya lissafa adadinsu ba..........
[12/6, 3:20 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 15*


Bayan an d'aura aure lafiya ango Ridwan ya dinga gaisawa da abokansa da 'yan uwan arzik'i, sannan mutane suka watse kowa ya kama gabansa.
Da dare aka mik'a amarya Safina d'akin mijinta Ridwan Shafi'u saidai muce ubangiji ya basu zaman lafiya da zuri'a d'ayyiba.

*WA NENE ALHAJI SHAFI'U MATAWALLE*
Alhaji Shafi'u matawalle asalinsa d'an jahar Kaduna ne iyayensa Alhaji Mahadi da mahaifiyarsa Lubabatu ,mahaifinsa shahararren mai arzik'i ne tun zamanin da domin sune gwamnati ke amsar kud'i garesu, Shafi'u tun yana k'aramin yaro iyayensa suka rasu awata rana da annobar gobara ta kama gidansu suka k'one su biyu banda Shafi'u da ubangiji ya tseratar dashi.
Ganin gobara ta zamo ajalin iyayensa rik'onsa ya koma hannun maigari da dukiyar daya gada awurin mahaifinsa, haka maigari ya cigaba da d'aukar d'awainiyarsa cikin rufin asiri da k'auna har yakai munzalin ya mallaki hankalin kansa, sannan ya damk'a masa dukiyarsa ahannunsa ya aura masa wata budurwa Khaleesat, Khaleesat k'yak'k'yawar budurwa ce ta bugawa amujalla tana kirki da halin dattako,tun lokacin da ta auri Shafi'u bata tab'a k'etare umurninsa ba akowane lokaci cikin yi masa biyayya take batason ganin abinda zai sakashi cikin b'acin rai ko damuwa, shima yana tsananin son Khaleesat tareda k'yautata mata fiyeda misali zamansu zama ne na fahimtar juna da tsantsar soyayyar gaskiya.
Cikin haka ne ubangiji yaba Khaleesat ciki zo kuga farin ciki da tsananin murna afuskokin wad'annan bayin Allah, tattali da tsantsar kulawa Shafi'u yake bata saboda yana matuk'ar son yara k'anana, itama gwargwado tana kulawa da cikinta duk abinda takeso bata b'oye masa shi kuma jiki yana rawa yake nemo mata shi domin ganin ya faranta mata.

Cigaba da rainon cikin Khaleesat sukayi har alokacin haihuwarta yayi ta haifi sankacecen d'anta namiji yaci suna Ridwan, anyi biki lafiya cikin aminci Khaleesat ta cigaba da rainon Ridwan tareda bashi tsantsar kulawa, shima Shafi'u ba baya ba wurin kulawa da d'ansa Ridwan saboda babu abinda yakeso aduniya daya wucesa.
Haka dai suka cigaba da gudanar da zamantakewar rayuwar aurensu cikin fahimta da kwanciyar hankali har Ridwan ya isa sawa makaranta mahaifinsa ya sakashi school na 'ya'yan masu kud'i, yana fara zuwa school dayake yanada k'ok'ari nan da nan yake haddace abu acikin k'wak'walwarsa,amma rashin ji da buge d'iyan mutane aschool babu sauk'i kusan kullum sai ankawo k'ararsa wurin iyayensa amma Shafiu bayason laifin d'ansa shiyasa yake shiga da fita yaga case d'in ya mutu, Khaleesat abinda Ridwan yakeyi yana b'ata mata rai domin batason rayuwar yaronta ya lalace.
Shiyasa wata rana da kanta tayiwa Shafiu magana akan ya daina biyewa Ridwan yana fad'a da mutane, nan da nan ya rufeta da fad'a ta inda yake shiga batanan yake fita ba yana ci mata mutunci, hawayen takaici sai shatata sukeyi afuskar Khaleesat zuciyarta cunkushe da tsantsar bak'in ciki aranta, Shafi'u ya kalleta cikin rashin walwala ya rubuta mata takardar saki ya bata.
Hak'ik'a Khaleesat taji zafin sakin walak'ancin da yayi mata nan ta kwashe kayayyakinta tabar masa gidansa, kunji dalilin rabuwar Shafi'u da uwar d'ansa Ridwan, tun daga lokacin daya rabuda Khaleesat bai sake tunanin k'ara aure ba duniyarsa ya dinga ci da tsinke, kawo matan banza yakeyi yana zina dasu cikin gidansa shiyasa Ridwan daya taso yaga irin mummunan abubuwan da mahaifinsa keyi shima ya fara sha'awar irin rayuwar mahaifinsa, da sannu sannu har yazo ya fara zina da 'ya'yan mutane yana basu kud'i .

Haka Ridwan ya cigaba da lalata rayuwar d'iyan mutane har yazo ya had'u da Raihana farat d'aya yaji tsananin sha'awarta ya shiga cikin zuciyarsa, nan da nan yabi duk hanyar da zaibi ya fara soyayya da ita kamar da gaske yana nuna mata tsantsar soyayyar gaskiya da k'auna wadda babu algussu acikinta.

_Dawowa cikin labarin_.

*BAYAN WATA BIYU*

Rayyanatu ce na hango sai kai da kawo takeyi cikin kitchen tana kichaniyar girka abincin rana, bayan ta kammala girkin ta juye abincin cikin kula madaidaiciya ta rufe tana k'ok'arin wanke hannunwanta taji arungumeta abaya ana shinshinnarta ,murmushi tayi domin taji k'amshin turaren mijinta Mubasshir waigowa tayi ta kallesa cikin so tace"sannu da zuwa k'albina".

Mubasshir ya lakaci hancinta yace"yauwa wifey ya ayyukan gida".

Rayyanatu ta shagwab'e fuskarta cikin sagarci tace"har na kammala mijina ina fatar komai yana tafiya cikin nasara".

"to Rayyana ina nan ina shiga da fice domin ganin na samu aikin dazan iya d'aukar d'awainiyarmu amma har yanzu shiru".

Rayyanatu ta langwab'e kanta cikin matuk'ar marairaicewa tace"ayyah k'albi karka damu komai yayi farko yanada k'arshe fatarmu shine ubangiji ya kawo mana *JINKIRIN ALKHARI* kuma da sannu ubangiji zai kawo mana mafitar alkhairi".

Mubasshir yaji dad'in kalamanta har cikin jini da jijiyoyin jikinsa farin ciki ne kwance afuskarsa yace"wannan maganartaki haka ne wifey ubangiji ya bamu inwar marece wadda tafi ta safe ".

"Amin amin k'albina".

"idan ki k'arasa aikin muje d'aki mana".

"to".Kawai ta fad'a.
Mubasshir ya mak'ala hannunsa cikin na Rayyanatu suka dauk'i kular abincin tareda shiga cikin d'aki, suna shiga Rayyanatu ta d'ibawa Umma abincinta ta dubi fuskar Mubasshir tace"k'albi bari inje in kaiwa Ummanmu nata abinci".

Mubasshir ya sakar mata murmushi yace"ba damuwa abar sona".

Rayyanatu ta fita daga cikin d'akin ta nufi na Umma wadda take kishingid'e saman pillow tana tasbihi, da sallama ta shiga ciki abakinta Umma ta amsa mata fuska asake cikin k'aunar Rayyanatu, isowa wurin Umma tayi ta gurfana agabanta cikin ladabi tace"Umma ga abincin ko akwai abinda kike bukata akawo miki?".

Umma ta dubeta cikin so da k'auna tace"a'a Rayyanatu d'iyar albarka babu abinda nake buk'ata ubangiji yayi miki albarka ya kuma saukeki lafiya ya baki rayayye ko rayayya masu albarka".

Akunya ce Rayyanatu tace"amin Umma".
Tana rufe bakinta ta fito daga cikin d'akin ta nufi d'akinta.

Zaune ta isko Mubasshir yana jiranta k'arasowa tayi wurinsa ta zauna saman jikinsa tana murmushin dake k'ayatar da fuskarta cikin k'auna ya shafi lafaffen k'aramin cikinta wanda bai wuce wata biyu da rabi ba, ita kuma sai wani lumshe idanunta takeyi tana k'ara narkewa ajikinsa can yace"bari muci abinci sai inga lafiyar babyna".

Rayyanatu tayi fari da fararen idanunta tace"to k'albina".Sannan ta jaye saman jikinsa tareda zuba musu abinci aplate d'aya fara cin abincin sukayi cikin natsuwa da kwanciyar hankali kallo d'aya zakayi musu ka gano su d'in masoyan juna ne.

Saida suka k'oshi sannan suka fad'a cikin bathroom sukayi wanka tare cikin k'auna, tare suka fito d'aure da towel ajikinsu sukayi masauki saman gado manshafi suka shafe jikinsu dashi Mubasshir yayi mata kwalliya mai sauk'i, ciro kayansu mara nauyi sukayi suka sanya ajikinsu tareda fesa turare mai k'amshin dad'i.

Soyayya mai tsabta suka cigaba da nunawa junansu zallar k'auna wadda tafi gaban kwatance ko misali, sun riga sunyi nisa cikin kogin so da k'auna sai shawagi sukeyi acikinsa.

_Hmmmmm soyayya tanada dad'i har dai idan mace tayi dace da masoyin gaskiya,mai nuna mata kulawa, tausayi, k'yautatawa, kawaici da tsantsar soyayyar gaskiya,Allah ubangiji ina rok'onka ka bamu mazaje na gari masu yi mana *SOYAYYAR GASKIYA* wadda babu yaudara acikinta._

Tun lokacin da Anti Lauratu tayiwa baba Iliyasu nasiha akan ya dinga kula dasu Inna Zulai yaji nasiharta ya dawo yana nuna musu tsantsar kulawa da tausayi musammam Raihana dake d'auke da tsohon ciki haihuwa yau ko gobe, ganin ya sake musu fuska yasa damuwarsu ta ragu suka saki junansu kamar wani abu bai tab'a faruwa ba arayuwarsu .
Bayan wani lokaci Raihana ta haifi sankacecen d'anta namiji yaci suna Mudassir yaron ya biyo mahaifinsa sak wurin kammani kamar yayi kaki ya tofar , duk wanda ko wadda ta kallesa saita k'udurta azuciyarta Ridwan ne mahaifinsa, haka dai akayi taron suna lafiya aka watse cikin k'oshin lafiya duk wata hidimar suna baba Iliyasu ne ya d'auki nauyinsa daga ragon suna har zuwa abinda aka kashe kud'i ne masu yawa, aranar mai jego da mahaifiyarta Inna Zulai k'unshewa cikin d'aki sukayi sunata kukan nadama da bak'in cikin rayuwa tabbas sunyi bak'in cikin tahowar wannan bak'ar rana mai k'unshe da d'acin rai da muguwar k'addara!.

Bayan haihuwar Raihana da wata d'aya Inna Zulai ta kamu da matsananciyar rashin lafiya wanda ya buge mata jiki zama guda, ganin rashin lafiyar yayi tsanani yasa duk hankalinsu baba Iliyasu da Anti Lauratu ya tashi nan da nan batare da b'ata lokaci ba aka fara bata maganin gargajiya tana sha, amma ina ciwon sai k'ara anzama yakeyi duk tabi ta fige ta rame ta koma bak'ik'irin kamar ba ita ba, ganin ana magani babu wani alamun nasara dole yasa baba Iliyasu da Anti Lauratu suka taimaka mata suka d'unguma zuwa asibitin dake kusa da unguwarsu, suna zuwa da ita rai ahannun Allah nan da nan akayi emergency room da ita batare da jimawa ba likitoti suka taru saman kanta suna bata taimakon gaggawa, sunyi sunyi iyakar bakin k'ok'arinsu domin ganin sun ceto ran Inna Zulai amma ina lokaci yayi nan ubangiji ya amshi ranta ta rasu!. Ganin ta rasu yasa suka shafe mata idanu wani daga cikinsu yaje ya sanarwa baba Iliyasu Allah yayiwa Inna Zulai rasuwa. Ina lillahi wa inna ilaihirraji'una! Itace kawai kalmar dasu baba Iliyasu ke furtawa saboda sun kad'u da tsantsar raxana akan mutuwar Inna Zulaiha, hak'uri likitan ya basu tareda yi musu jagora zuwa room d'in da gawar Inna Zulai take kwance suna shiga ciki suka iske mutum kwance a mimmik'e saman gado, nan da nan hawaye masu zafi suka dinga shatata afuskar Lauratu baba Iliyasu tsaye yayi jugum cikin matuk'ar tashin hankali da bak'in cikin rayuwa, dak'yar suka samu aka turo aka dauk'i gawar direct suka nufi hanyar zuwa gida saboda ayi mata wanka akaita gidanta na gaskiya.

_Allahu Akbar duniyar kenan fad'in ubangiji ne dukkan mai rai saiya d'and'ani zafin mutuwa, hmmmm idan ina tuna mutuwa da kwanciyar kabari hankalina tashi yakeyi wallahi fatanmu burinmu ubangiji yasa mu cika da imani muyi k'yak'k'yawan k'arshe._😭😭😭😭😭

~Shin ko ya rayuwarsu Rayyanatu zata kasance shin Raihana zata samu miji tayi aure kuwa, shin Ridwan zaiyi nadamar cin amanar da yayiwa Raihana? Saiku biyoni sannu ahankali domin jin yadda zata kasance atsakaninsu.~


```Ina sonku masoyana aduk inda kuke a fad'in duniyar nan.```` 😘
[12/6, 3:20 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*

*LAST PAGE*

*PAGE 16*



Suna isa da gawar Inna Zulai gida baba Iliyasu yayi mata wankan gawa yana hawayen zafin mutuwa da tsantsar rad'ad'in rabuwa da ita,rabuwa na har abada Raihana data fahimci mahaifiyarta ta rasu aranar tayi suma har yakai sau uku tana sha kukan bak'in ciki mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro, dak'yar Anti Lauratu ta samu ta lallasheta itama tana kukan sabo da zafin mutuwar Inna Zulai, haka dai akayi mata wanka aka kaita gidanta na gaskiya.
Bayan mutuwar Inna Zulai Rayyanatu tazo gaisuwa da kukanta dak'yar da sud'in goshi aka lallasheta ta daina kuka,sannan tayi shiru anan gidan ta yini tana yiwa Raihana maganganu masu dad'i da yi mata nasiha akan hak'uri da rungumar k'addara duk yadda tazo maka, da zata wuce da marece tayi musu alkhairi mai yawa mijinta yazo ya d'auketa suka tafi gida cikin jimami da tsantsar zullumin mutuwar Inna Zulaiha.
Tabbas duk abinda mutum yakeyi aduniya wata rana dole ya barta saboda rayuwa ce ko munaso ko bamaso dole mu awayi gari munbar duniya mai tattare da bak'in ciki da k'uncin rayuwa.

**********************
Acikin katafaren parlourn Ridwan wanda yayi zaune saman cushion yayinda Safina take agefensa, tagumi yayi fuskar nan tasa amuturk'e kamar wanda ya rasa komai arayuwarsa kallo d'aya zakayi masa ka gane akwai abinda yake damuwarsa, Safina ce ta kallesa cikin nazari da sanyin jiki tace"my one wai mi yake damunka akwanakin nan naga ka rage walwala kwata kwata?".
Ridwan yayi mata wani irin kallo mai d'auke da ma'anoni da yawa yace"hmmmm Safina kina bani matuk'ar mamaki taya za'ayi bazan shiga cikin damuwa ba ace tun lokacin da mukayi aure baki tab'a yin ko b'atan wata ba sannan kice bazan shiga cikin damuwa ba".
Safina ta bintsire baki ta b'ata fuska takaici ne shimfid'e afuskarta tace"haba Ridwan kai miyasa bakada wata magana sai ciki ciki to idan ubangiji bai bamu ba sata kakeson inje inyi? Nifa gaskiya ka daina ganin laifina duk abinda ubangiji ya k'addarowa bawa babu makawa saiya sameshi! Saboda haka ka cire komai cikin zuciyarka ka fawwalawa Allah lamarinka shi yasan irin tanadin da yayi maka".
Ridwan ya girgiza kansa cikin jimami da rashin gamsuwa da kalamanta yace"gaskiya Safina inason haihuwa bazan iya hak'ura ba in mutu abanza babu mai yimin addu'a".
Safina ta hararesa tace"idan bazaka hak'ura ka yanke hukuncin daya kamata mana! ".
"yauwa tunda kin bani dama aure zan k'ara Safina nan bada jimawa ba".
Dimmmmm taji gabanta ya fad'i amma saita tattaro dauriya tace"ubangiji yasa ayi lafiya".Tana rufe bakinta taja k'afafunta fuuuuuu tayi cikin d'akinta hawayen zafin kishi da rad'ad'in kishiya yana shatata afuskarta wani irin tururin d'aci da zogi ne ya tokare mata a k'irji.
Ridwan bai bi bayanta yayi zamansa yana sak'a da warwara cikin zuciyarsa da tunane-tunanensa.

Zuwa wani lokaci Ridwan ya auri wata yarinya Sukaina tazo ta tare amma shiru itama bata haihu ba, ganin bata haihuwa yasa ya k'ara auren wata budurwa Nafiya itama ana aure shiru shiru bata haihu, hakan yasa Ridwan ya dinga auri saki yana aure amma shiru babu wani chanji har yanzu Safina ce kawai bai saka ba suna tare har yanzu. Ganin bai samu haihuwa yasa ya tuna da Raihana yaje har k'ofar gidan mahaifinta yasa yaro ya kirata, dak'yar da lallashi Anti Lauratu tasa Raihana ta fito daga cikin gidan hannunta rik'e da d'anta Mudassir, suna isa wurinsa idanunsa ya sauka akan d'ansa fassss yaji zuciyarsa ta buga saboda tozalin da yayi da mai irin fuskarsa sak dak'yar ya bud'i baki yace mata cikin sanyin murya"Raihana".
Batare data amsa ba fuskarta tana kallon k'asa.
Ridwan yace"hakika nasan na cutar da rayuwarki da cin amanarki nasan nayi miki butulci arayuwa amma tun anan duniya na fara ganin sakamakon abinda na shuka! Saboda haka gani gabanki ki taimaka ki yafemin ki bani d'ana ya dawo wurina ina matuk'ar buk'atarsa ayanzu fiyeda tunaninki".Yana kai k'arshen maganarsa hawaye masu d'aci suka gangaro afuskarsa yayinda bak'in ciki da damuwa suke kwance cikin k'wayar idanunsa.

Raihana ta kallesa yayinda hawayen takaici da tsantsar bak'in ciki ne ke shatata afuskarta cikin zuciyarta sai k'una da zafi yakeyi mata, dak'yar ta bud'i baki tace"tunda har ka bud'i baki ka rok'eni gafara na yafe maka amma ka sani har abada bazan baka d'ana Mudassir ba! Saboda tun lokacin da nake d'auke da cikinsa ka tsamgwameni da hantarata alokacin da nake buk'atar taimakonka".Tana kai k'arshen maganarta taja hannun Mudassir suka shige cikin gida batare da sun tsaya ta saurari abinda zai fito daga cikin bakinsa ba.

Ridwan ya jima tsaye jugum babu abinda zuciyarsa keyi sai tafasa da k'una, numfashi ya sauke mai tattare da bak'in ciki da damuwa kallo d'aya zakayi masa ka gane yana cikin rad'ad'i da zafin rashin haihuwa, can dai ya shige cikin motarsa jikinsa amace na ganin bai samu nasarar da Raihana zata fahimceshi ba, tadda motarsa yayi ya nufi hanyar zuwa gida hawaye masu zafi sai sintiri sukeyi afuskarsa.

*BAYAN SHEKARU BIYAR*

Abubuwa da dama sun faru ciki kuwa harda komawar Mudassir gidan babansa Ridwan, domin tun lokacin da Ridwan yazo ya rok'i Raihana akan ta bashi dansa Mudassir ya dawo wurinsa amma tak'i ya, ganin ta fita batunsa yasa ya dinga zirga zirga zuwa wurinsu baba Iliyasu yana rok'onsu yana kuka wiwiwi kamar mace, hak'ik'a yabasu baba Iliyasu tausayi sosai shiyasa nan da nan suka dauk'i Mudassir suka bashi, nan ya fad'i k'asa yana godiya sannan ya wuce da yaronsa.

Raihana ganin ta rabuda d'anta yasa ta shiga cikin wani irin yanayi akan so da sabo Anti Lauratu ce ta lallasheta ta bata hak'uri, haka dai rayuwar gidansu ta cigaba dayi har ubangiji Allah yaba Raihana mijinta mai suna Alk'asim 'ya'yansa hud'u da matarsa Nadiya tayi aurenta ta huta.

Agidansu Mubasshir da Rayyanatu ubangiji ya d'aukakasu domin ya samu babban aiki a companyn man fetur, nan ubangiji yasa hannu cikin arzik'in Mubasshir kud'in suka bunk'asa ya zamo shahararren mai kud'i wanda yayi suna cikin jaha.
Rayyanatu tana zaune itada yaranta Maleek da baby Maleeka dake rungume ajikinta ga Mubasshir kusa gareta suna fira.
Mubasshir kallon soyayya yayiwa Rayyanatu yace"k'albi kinsan wani abu?".
Rayyanatu tayi murmushin dake k'ayatar da fuskarta k'yawonta ya k'ara fallasa tace"saika fad'a farin cikin rayuwata".
Mubasshir ya musk'uta yace"ban tab'a zaton zamu samu chanjin yanayi ba alokaci guda ba, sai gashi ubangiji ya d'aukakani zama guda ashe komai lokaci ne dashi".

Rayyanatu tayi murmushinta mai k'yau tace"mijina kenan komai da kake gani lokaci ne dashi tabbas aduniya babu abinda yakeda tabbas,farin ciki, bak'in ciki, arzik'i, talauci, kaga yanzu ubangiji ya kawo mana *JINKIRIN ALKHAIRI* lokaci guda shiyasa akeson mutum duk halin daya tsinci kansa yayi hak'uri saboda komai yanada lokaci.

Mubasshir ya girgiza kansa alamar gamsuwa yace"maganarki gaskiya ne my Rayyana hak'ik'a komai na duniya yanada farko yanada k'arshe dukkan tsanani yana tare da sauk'i, shiyasa akeson komai ya samu mutum ya mik'a lamarinsa wurin ubangiji Allah".

"haka ne farin cikin rayuwata".

Maleek ganin sun k'yalesa yasa ya zumb'ura baki cikin shagwab'a yace"mom yunwa nakeji fa".
Rayyanatu ta kallesa cikin k'auna da tsantsar soyayyar d'anta tace"Abdulmaleek yunwa kakeji kuma?".

"eh mana mom".Yace cikin sagarci.

Rayyanatu ta dubi fuskar Mubasshir mai k'unshe da annuri tace"daddyn Maleek muje dinning table muyi lunch d'ana yunwa nakeji".

"OK ba matsala muje d'in".Yana k'arasa maganarsa yaja hannun Maleek suka nufi dinning table yayinda Rayyanatu ke rungume da Maleeka ajikinta.
Suna isa dinning table suka ja kujeru suka zazzauna yayinda Rayyanatu ta mik'e tsaye ta fara serving d'insu, tana kammala serving d'in kowa ta koma ta zauna ta fara cin abincin tana sanyawa baby Maleeka cikin baki dayake yarinyar har ta fara cin abinci tuntuni, ci sukeyi bakajin motsin komai saina TV cikin natsuwa da kwanciyar hankali suke cin abincin Mubasshir sai kallon soyayya yake jifar Rayyanatu dashi, itama sai murmushi takeyi tana jin sanyi da tsantsar farin ciki cikin zuciyarta sai kwaranya yakeyi asassan jikinta, alal hak'ik'a tasan tayi dace da masoyin gaskiya mai nuna mata tsantsar soyayyar gaskiya da kulawa.
Text message yah Mubasshir ya turawa Rayyanatu cikin phone d'inta kamar haka:

_Matata kece farin cikina abar tunanina akowane lokaci ki sani har abada babu macen dazan so tamkarki azuciyata, hak'ik'a nayi nutso cikin kogin soyayyarki sai shawagi nakeyi babu macen dake iya fitar dani sai ke Rayyana._
_Ina sonki har abada._
Rayyanatu sai karanta text message d'in takeyi tanata murmushi tsananin farin ciki k'unshe afuskarta.

Alhaji Shafi'u matawalle kuwa wata rana ya fita daga cikin gidansa ya nufi hanyar zuwa lambunsa, yayi tafiya mai nisa ya fita daga cikin gari kwatsam motarsa ta tsaya cak,Alhaji Shafi'u ya fito daga cikin motar domin yaga abinda yasa motar ta tsaya ya fara dube dube kenan can mutane hud'u sukayi fitar burgu daga cikin hakukuwan dake cikin dajin, suna fitowa basu tsaya b'ata lokaci ba suka iso wurinsa suka kewayeshi juyar da zaiyi kenan yaga mutane sun sakashi tsakiyar, ganin haka ne yasa gaban Alhaji Shafi'u ya fad'i rassss hankalinsa yayi k'ololowar tashi ya duba gabas kudu arewa yamma baiga hanyar tserewa ba, kuwwa da kururuwa ya dingayi nan da nan suka nausheshi sukayi masa yankan rago!.
Suna kashe Alhaji Shafi'u suka shige cikin motarsa suka gudu suka bar gawarsa kwance awalak'ance.

_Ina lillahi wa ilaihirraji'una!Allah ubangiji yasa muyi k'yak'k'yawan k'arshe, dama k'arshen azzalumi baya tab'a k'yawo duk abinda mutum ya shuka tabbas saiya girbi abinsa._


*ALHAMDULILLAHI*.
_Godiya ta tabbata ga ubangiji mad'aukakin sarki daya bani ikon kammala wannan novel nawa mai suna *JINKIRIN ALKHAIRI* ,ina rok'on ubangiji ya yafe mini kurakurrena abinda na fad'a daidai ubangiji yayi mini sakamakon alkhairi, ina fatar makaranta littafaina zasu dauk'i darasin dake cikin wannan labari su watsar da abinda nayi cikin kuskure._

*Ku cigaba da kasancewa tareda ni Mugirat Musa domin samun daddad'an labarai daga gareni, ina muku fatar alkhairi arayuwarku masoyana sai kun jini asabon novel d'ina mai suna *SAKACI* .


_Mugirat Musa ce mai son farin cikinku zaku iya nemana ta wad'annan nombobi._

08163650557
08035370039

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment