Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Inna Zulai tace"dallah ki shigo cikin d'akin tunda ba bak'onki bane banason kininbibi da salon makirci!".
Cikin tsoro da tsinkewar zuciya Rayyanatu ta shigo cikin d'akin ta durk'usa agaban Inna ta ajiye kular,tana ajiyewa kular ta tashi tsaye zata fice daga cikin d'akin Inna tayi charap tace"dawo in zuba miki naki ko kuwa idan kika wuce uban wa zai kai miki naki abincin!?".
Rayyana ta juyo ta dawo Inna ta umurceta data d'auko plate taje ta d'auko ta kawo, abinci d'an kad'an Inna Zulai ta sanya mata duk ita ta girka wanda baifi tayi loma biyu cikinsa ba, haka ta dauk'i abincin ta fice daga cikin d'akin tana sharar kwallar zallar takaici tana kallon abincin da Inna ta sanya mata wanda ko k'aramin yaro zama d'aya yakeyi ya cinyesa.
Tana shiga cikin d'aki ta zauna ta cinye abincin sannan ta d'auko indomie biyu ta jik'a cikin ruwan sanyi, saboda idan ta jik'u taci ko yunwar da takeji zataji dama dama, kwance tayi tana tunanin abubuwan da suke faruwa arayuwarta, saida taga minti ishirin sunyi sannan ta bud'e murfin kwano tareda tsiyaye ruwan dake cikin indomien sannan ta zuba maggin indomie da dakakken yaji ta zuba ta yamutse ,tana gama yamutsewa ta fara cin indomien da sauri da sauri domin kada Inna Zulai ta gifto taga tana cin abinci ta k'wace su cinye itada Raihana, haka ta cigaba daci harta cinye tass ta kawo ruwa masu sanyi tasha tareda Alhamdallah ga ubangiji daya rufa mata asiri, kwantawa tayi saman katifa tana tunanin mahaifiyarta data rasu ashekarun baya hawaye masu zafi sai sintiri sukeyi afuskarta, saboda ta tuna da jigon rayuwarta mai son farin cikinta wato mahaifiya kenan.

*TUSHEN LABARI*
Rayyanatu 'yace ga Mustapha da Basira iyayenta sunyi auren soyayya ne tun suna matasa sunso juna cikin k'auna da tsantsar soyayyar gaskiya wadda babu algussu acikinta, Mustapha da Basira fulanin asali ne gaba da gaba dukansu 'yan kebbi ne kasuwanci ne ya maidasu zama cikin garin jega suka cigaba gudanar rayuwar aurensu cikin fahimta da kwanciyar hankali, zamansu zama ne na yarda da fahimtar juna saboda kowanensu yana iya bakin k'ok'arinsa wurin ganin sun farantawa junansu, cikin haka ne Basira ta samu ciki zo kuga farin ciki da tsananin murna afuskokin wad'annan bayin Allah musammam Mustapha da yakeda tsananin son yara k'anana yaci buri azuciyarsa idan ta haifi namiji ya sanya masa Rayyanu idan mace ce ya sanya mata Rayyanatu, tun bai furta sunan da yakeson ya sakawa abinda zata haifa ba har ya gaya mata da bakinsa ko bayan rayuwarsa, Basira tayi na'am da sunayen daya furta tareda fatar ubangiji ya sauketa lafiya.

Haka dai suka cigaba da rainon cikin Basira tareda nuna mata kulawa na musammam fiyeda misali, Mustapha yana k'ok'arinsa wurin ganin ya bata abinci iri iri masu gina garkuwar jini da k'arin jini, itama yayarta Zulai tana yawan zuwa duba lafiyar jikinta domin su biyu kawai ne ga iyayensu kuma sun rasu a had'arin motar da sukayi da zasuje kai ziyara akan hanyarsu ta zuwa sukayi mummunan had'ari nan take ubangiji ya amshin ransu.

Mustapha shi kad'ai yake ga iyayensa bayada yaya ko k'ane, haka cikin Basira ya cigaba da girma har ya kusa haihuwa ana nan wata rana Mustapha ya kamu da matsananciyar rashin lafiya wanda yakaishi ga kwanciya, ganin halin da yake ciki yasa hankalin Basira yayi k'ololowar tashi zuciyarta ta tsinke babu abinda takeyi idan ba kuka ba jikinta duk ya mutu, Mustapha da kanshi yake tattaro dauriya yana lallashinta domin bayason ta shiga cikin damuwa da bak'in ciki.

Cikin haka ne sannu sannu ciwo yazo yaci k'arfin Mustapha har ya zamo sanadiyar ajalinsa aranar Basira tasha kuka kamar ranta zai fita, domin mutuwar mijinta ya gigita da girgiza k'wak'walwarta akan haka ne ta fad'i ta some su Inna Zulai suka kwasheta sukayi asibiti da ita acan ta haifi santateliyar d'iyarta mace k'yak'k'yawa son kowa k'in wanda ya rasa saida aka binciki lafiyarta dana jaririya sannan likita ya sallamosu suka rankayo suka dawo gida.

'yan uwa da abokan arzik'i sukayi ta zuwa turururu suna ganin jaririya da yin gaisuwar rasuwa, abin ya zamo guda biyu ga haihu ga rasuwa haka dai Basira ta cigaba da kukan zuci tareda kula d'iyarta domin kada ta lalace, sati yana zagoyawa yarinya taci suna Rayyanatu mak'wabta da 'yan uwa duk sunzo anyi taro lafiya an watse cikin k'oshin lafiya wanda kallo d'aya zakayiwa mai jego ka gano bata cikin kwanciyar hankali da farin ciki adalilin mutuwar mijinta, babu yadda ta iya haka ta daure tana harakokinta tareda b'oye damuwarta.

Bayan shekara goma alokacin ne Allah ubangiji ya karb'i rayuwar Basira Rayyanatu tanada shekara goma aduniya, aranar tasha kukan maraici da zafin mutuwar mahaifiya amma babu yadda zatayi saboda duk abinda ya samu bawa rubutacce ne awurin ubangiji.

Mahaifiyar Rayyanatu tana rasuwa Baba Iliyasu yazo da kansa ya mayarda ita gidansa, koshi saida sukayi fad'a kaca-kaca shida Inna Zulai domin cewa tayi ba zata zauna da Rayyanatu ba saboda ba itace ta kashe mata mahaifiya ba .
Baba Iliyasu ya dubeta yace"lallai na tabbatar da bakida imani Zulai yanzu d'iyar k'anwarki uwa d'aya uba d'aya kike bak'in cikin ta dawo wurinki wannan wane irin rashin imani da rashin tsoron Allah ne?".

Inna Zulai tayi masa kallon banza tace"eh banida imani Iliyasu karka kuskura ka kawomin d'iyar kowa bazan iya wahalar banza tawa d'iyar ta isheni! ".Raihana dake zaune tasa wasar k'asa tana sauraren duk abinda suke fad'a yayinda Rayyanatu ke rakub'e gefen bango jikinta yana rawa domin ta fahimci duk akanta ne suke sa'insa.
"aikin gama ya gama Zulai saidai kiyi hak'uri na riga na d'auko Rayyanatu ta dawo gidan nan sannan ki kiyayeni banason shirme da haukar banza".
Inna Zulai ta dinga waige waige tace"ina take in kashe d'iyar banza taulalin wahala! ".Baba Iliyasu ya jawo hannun Rayyanatu daga inda take lab'e ya kawota gaban Zulai yace"gata ki kasheta idan ke kin cika babbar mahaukaciya ke kuma akasheki haka shari'a ta yanke hukunci "..........
[12/5, 9:30 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 6*


Raihana ta saukar da numfashi ta fara bata labarin yadda ta had'u da masoyinta Ridwan har takai k'arshen labarinta, sannan ta ciro kud'in daya bata ta nunawa mahaifiyarta ai kuwa Inna Zulai ta fashe da dariyar farin ciki harda taka rawar murna tayi akan d'iyarta Raihana ta samu kud'i abinso ga 'yan matan zamani, can ta tsagaita da yin rawar tayi gud'a tace"ayyirurihhhh nanaye Allah mun gode maka daka nunamin wannan ranar farin ciki 'yata ta samu miji mai arzik'i".
Raihana tasa hannu ta toshe mata baki tace"ki daina d'aga murya sosai kada mak'iya suji su dinga yayatani agari kinsan ba kowane mutum ke sonka azuciya ba".
"nayi shiru kedai d'iyar k'warai aiko ubanki yana iya kushewa dayi miki bak'in ciki kinsan babu abinda ya iya sai hassada!".
"na sani Inna shiyasa kikaga na tsaneshi arayuwata".
"hmmmmm to yanzu ya zakiyi da wannan matsiyacin yaro Mubasshir? Tunda kin samu mai kud'i ki sallamesa kowa ya kama gabansa saboda dama tun farko baku dace da juna ba kinfi kamada matar mai kud'i ba talaka ba! ".

Raihana ta yamutsa fuskarta tace"aiko bakice korar kare zanyi masa nidashi mun raba hanya ana batun mai kud'i wa yake maganar talaka Innata, aini idona idon ganin kud'i saboda haka ki kwantar da hankalinki ni nasan yadda zanyi dashi ".
Inna Zulai tace"hakan ya kamata kam ki rabudashi ki kama mai arzik'i kinga idan kika auresa mun huta da talauci".
"ai daga yanzu munyi bankwana da talauci mudashi sai gani sai hangen nesa! ".
"haka ne d'iyata shiyasa nake k'ara sonki saboda k'wak'walwarki tana ja sosai akwaiki da tunani ".
"na gaji tunani awurinki".
"haba dai? ".
"Allah kuwa da gaske nake fad'a".
Suna k'arasa maganarsu suka fashe da dariya tareda tab'awa da juna kamar k'awayen juna suna k'yak'yatawa akan farin ciki.

Rayyanatu tana cikin d'aki tana sauraren duk abinda suke tattaunawa, babu abinda take musu fata face ubangiji Allah ya shiryesu yasa su dawo kan hanya madaidaiciya.
____________________

Soyayya mai k'arfi ta k'ullu atsakanin Ridwan da Raihana wanda ya zamo sun riga muguwar shak'uwa da yarda juna, akowane lokaci suna manne da wayoyinsu domin suji muryar juna kalaman k'auna suke musanya dare da rana, sun riga sunyi nitso cikin kogin soyayya sai shawagi sukeyi atafkin k'auna, Baba Iliyasu baisan da Ridwan yana zuwa wurinta ba sai daga baya karkaso kaga yadda ya nuna b'acin ransa afili akan ta fita daga sabgar Ridwan amma itada uwar sunyi kunnen uwar shaggu dashi, sun nuna bai isa dasu ba baida wani daraja da kima acikin idanunsu, ganin sunyi biris da maganarsa yasa ya kawo na mujiya ya sanya musu wad'anda basa ci basa gani.

Itadai Rayyanatu sai k'ara azabtar da rayuwarta sukeyi tareda yi mata gorin cewa batada farin jini, idan abin yaci mata rai iyaka ta k'unshe cikin d'aki tana zubar da hawayen maraici da takaicin rayuwa, cikin haka ne Mubasshir yaga sauyin yanayi afuskar Raihana domin idan yazo takan b'ata fuska tareda nuna masa batada lafiya, haka zaice mata sannu yayi ficewarsa zuwa gida wata rana idan ya sake dawowa magana ciki ciki takeyi masa wanda shi ya kasa fahimtar inda ta dosa, idan ya nemi ta gaya masa ko mike damunta saita rufeshi da fad'a mara kan gado asanadiyar haka saiya sassauta murya yana bata hak'uri ,idan yaga ta sauko yayi mata sai anjima yayi tafiyarsa inda zaije.

Haka Raihana ta cigaba da walak'anta rayuwar Mubasshir tareda ci masa mutunci tana zaginsa wanda ahakan yake hak'uri yana danne abin cikin zuciyarsa ko Ummansa baya sanar mata irin k'alubalen da yake fuskanta awurin Raihana, har takai ta kawo da bakinta ta sanar masa bata iya auren talaka sai mai kud'i wanda asanadiyar haka Mubasshir ya rabu da ita tareda cireta daga cikin zuciyarsa domin ya fahimci babu abinda ta sawa gaba illa kwad'ayi da dogon buri.

_Dawowa cikin labari_ .
____________________

Rayyanatu tana kwance tana barci kamar amafarki taji saukar ruwan zafi ajikinta zumbur ta tashi zaune afirgice tana wuk'i-wuk'i da idanunta, d'ago fuskarta da tayi idanunta ya fad'a cikin na Inna Zulai wadda take tsaye k'yam idanunta cikeda masifa nan da nan jikin Rayyana ya d'auki k'yarrrma da mazari domin ba k'aramin tsoronta takeji ba.

Kallon tsana ta jefeta dashi tace"ke ubanwa yace kiyi barci dan ubanki? Aike agidan nan baiwa ce bakida lokacin yin barci saida tsakar dare!".

"kiyimin afuwa bansan lokacin da barci ya kwasheni ba".

"ki daina bani hak'uri banaso saboda hakan yana bak'antamin rai! Kinsan na tsaneki ban k'i ace an wayi gari kin mutu ba amma kikeson yimin maganar banza".

Rayyanatu ta noce kanta a k'asa tana kallon k'asar dake malale cikin d'akin kwalla sai zubo mata takeyi afuskarta tana sharewa, k'arin bak'in cikinta ace wai yayar mahaifiyarta uwa d'aya uba d'aya tana musgunawa rayuwarta akan batada imani da zuciyar tausayi wannan wace irin k'addara ce mai cikeda bak'in ciki da takaicin rayuwa?.

Haka dai ta kama sak'e sak'e azuciyarta tana tunanin mahaifiyarta da mafita amma ina ta kasa hango mafitar data kamata, ganin tayi shiru bata sake cewa uffan ba yasa Inna Zulai ta harzuk'a zuciyarta ta kawo awuya tace"keee!Bak'ya jin inata miki magana kin k'yaleni adole ke gaki nakkasassa! ".

Firgigit tayi ta dawo cikin hayyacinta tace"banji bane".

"tun d'azu ina miki magana kice baki jiya ba? ".

"da gaske banji abinda kike fad'a ba Inn........ ".Bata bari ta k'arasa maganarta ta rufeta da duka ko'ina ajikinta Rayyanatu kuka kawai takeyi tana neman agajin gaggawa, amma ina babu kowa cikin gidan sai Raihana ita kuma babu abinda ya shafeta saboda itama ta tsani Rayyana fiyeda tunanin mai karatu, kuwwa da kururuwa Rayyana ta cigaba dayi duk da haka baisa Inna Zulai taji tausayinta ba saida taga tayi mata lilis da duka dak'yar take motsi tana fitarda numfashin galabaita,sannan ta tsagaita da dukanta taja ta tsaya tana nishin gajiya tace"gobe idan ina miki magana kice baki jiya ba nice ajalinki acikin gidan nan! ".Tana kai k'arshen maganarta taja k'afafunta fuuuuuu kamar kububuwa tabar cikin d'akin.

Tana wucewa Rayyana ta cigaba da rusar kuka mai ban tausayi da tsuma zuciyar mai sauraro, hawaye masu zafi sai sintiri sukeyi afuskarta wani irin zogi zuciyarta keyi zaune tayi taci kukanta saida ta k'oshi, idanunta sukayi jajir da kumbura akan yawan kuka sannan ta tashi tsaye ta fito daga cikin d'akinta tareda nufar wurin famfo domin ta wanke fuskarta, tana kammala wankewa ta koma cikin d'akin ta kwanta hawaye sai shatata sukeyi afuskarta zad tausayi.
____________________

*BAYAN WATA BIYU*
Rayuwar Rayyanatu haka ta cigaba da tafiya agidan Baba Iliyasu cikin tsamgwama da musgunawar rayuwa domin kuwa har yanzu bata sauya zane ba Inna Zulai azabtar da ita kawai takeyi tareda mayarda ita wadda batada wani gata sai awurin ubangiji, ita kuma 'yar gaban gashi Raihana babu abinda ta iya sai tara samari a k'ofar gida tareda yin fira dasu saboda batada aji kowane shege yazo saiya sallamo mata, haka ta mayarda rayuwarta mara gata da 'yanci uwar sai zugata takeyi tareda k'ara nuna mata yadda zatayi idan saurayi yazo wurinta.

Ridwan na hango ya parker motarsa abakin k'ofar gidansu Raihana ya kira yaro yayi masa sallama da ita, yaron ya shiga cikin tsakiyar gidan bada jimawa ba ya fito yace tana zuwa naira dubu Ridwan ya zaro daga cikin aljihunsa yaba yaron, amsawa yayi yana godiya sannan ya fice daga bakin k'ofar gidan yana murna.

Ba'a dad'e ba saiga gimbiyarsa ta fito daga cikin gidansu tana tafiya guda guda cikin kuri kamar batason taka k'asa, tun daga nesa ya tsura mata idanu yana k'arewa surar jikinta kallo wani irin abu ne yaji ya game cikin jini da sassan jikinsa lumshe idanu yayi yana shak'ar k'amshin turarenta,wanda yake k'ara dulmiyar dashi ya afka kogin k'aunarta bud'e murfin motar tayi ta shigo ta zauna saman kujera sai jifan junansu sukeyi da kallon soyayya da shauk'in so .

Can suka kauda idanunsu daga barin kallon juna Ridwan ya sakar mata murmushi yace"hmmm kinyi k'yawo masoyiyata Raihana ji nake kamar in mayarda ke cikin cikina akan so".

Raihana tayi murmushin dake bayyana hak'ora tareda yin fari da idanunta tace"nagode habibina kaima k'yak'k'yawa ne shiyasa nake matuk'ar kishinka azuciyata domin banason ka had'a soyayyata da kowace d'iya mace".

"karki damu ke kad'aice azuciyar Ridwan babu wata mace aduniya dazan so fiye dake tuni na baki makullin zuciyata kika ajiye ahannunki, babu macen dake iya bud'e zuciyata ta shiga cikinta sai ke muradin zuciyata ".

Tabbas Raihana taji dad'in kalamansa har cikin jini da tsokarta murmushi k'unshe afuskarta wani irin sinadarin farin ciki sai yawo yakeyi cikin sassan jikinta, saukar da numfashi tayi tace"nima na riga na baka amanar zuciyata aduniya banda tamkarka ka sani har abada kaine *ABUNDA NAKE SO* da gani".

"naji dad'in yadda kika bani babban matsayi azuciyarki ni kuma nayi miki alk'awarin bazan tab'a cutar dake ba".

"ina godiya da soyayyarka gareni ".

"kinfi k'arfin komai awajena yanzu dai bari muje super market ki d'auki duk abinda kikeso".

"kayyyy heartbeat irin wannan d'awainiya haka nagode sosai".

"bana buk'atar godiyarki ki rik'e abarki ".Yana rufe bakinsa ya tadda motarsa tareda saitata saman kwalta ya fara tafiya, tafiya sukeyi suna firar soyayya har suka iso babban super market d'in da akeji dashi Ridwan ya parker motarsa agaban super market d'in sannan ya fito daga cikin motar, b'angaren Raihana ya nufa ya bud'e mata murfin k'ofar ta fito cikeda k'asaita da gadarar ita d'in wata ce rufe murfin yayi sannan suka jera atare suka shiga cikin super market kallo d'aya zakayi musu ka gano su d'in masoyan asali ne.
Suna shiga ciki dayake Ridwan sananne awurinsu nan da nan yaran suka dinga gaidashi cikin girmamawa yana amsawa cikin isa da tink'aho, direct wurin kwandon saka kayayyakin suka nufa Ridwan ya d'auko ya bata,Raihana ta amshi kwandon ta fara zagayar wuri tana jidar abinda takeso Ridwan gefe ya koma yana danne dannen wayarsa yana jiran ta kammala d'aukar abinda takeso da ra'ayi..........
[12/5, 9:30 PM] Mugiratmusa66: 🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
*JINKIRIN ALKHAIRI*
🛸🛸🛸🛸🛸🛸
🛸🛸🛸🛸🛸🛸

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*®✍🏻
[Onward together].


*WRITTEN BY MUGIRAT MUSA*


*PAGE 7*


Saida ta kwashi kayayyakin son ranta sannan ta k'arasa wurinsa tana zumb'ura baki cikin shagwab'a tace"na kammala siyayyar heartbeat".Kallon kayayyakin data siyo yayi yace"iyakar abinda kike buk'ata kenan baby? Wad'annan kayan sunyi kad'an bari in k'ara miki wasu".Raihana ta saki baki cikin mamakin maganarsa tace"yanzu wannan kayan ne sukayi kad'an ?"."Eh mana baki dauk'i wasu ba".Yana rufe bakinsa yaja hannunta suka nufi gefen turarurka da sabulu masu k'amshin gaske ya kwasa mata, sannan ya d'auko wani zaben zinari ya sanya mata ayatsa, sannan suka zarce wurin mai lissafa kud'in da mutum ya kashe calculating amount of money yayi Ridwan ya zaro kud'i a aljihunsa ya bashi nan da nan ya lissafa kud'in zai bashi chanjinsa yace ya barsu, kayayyakin suka amsa suka saka musu cikin leda babba tareda ba yaronsu ya biyosu Ridwan abaya har inda ya parker motarsa boot ya bud'e ya sanya ledar, sannan yayiwa yaron ihsani yayi godiya ya koma bakin ajikinsa.
Ridwan saida ya fara bud'e mata murfin k'ofar ta shiga ta zauna sannan ya rufe tareda zagayawa ya zauna mazaunin driver tadda motarsa yayi suka nufi wata hanyar daban, Raihana bata lura ba hanyar gidansu bace sai daga baya ta kallesa tace"heartbeat ina zamuje ne naga ba hanyar zuwa gidanmu bace ka biyo dani?".
Wani irin yaudararren kallo yayi mata tareda kallon cikin k'wayar idanunta yace"gidana zan kaiki kiga tsarin gidan ko yayi miki kafin muyi aure ko bak'ya son ki gani ne mu juya mu koma?".

Sai yanzu taji hankalinta ya d'an kwanta murmushin dake k'ayatar da fuskarta tayi tace"a'aaa inaso in gani mana kafin inzo in rayu cikinsa".
"ko kefa amma kina wani jin tsoro kina tunanin zan cutar dake ne?".
Raihana ta nisa tareda gyara zamanta tace"ko d'aya bana tunanin ko amafarki zaka cutar dani".Tana k'arasa maganarta taja bakinta ta tsuke d'ayansu bai sake magana ba saida suka k'araso bakin wargajejen k'aton get mai girma da fad'i, Ridwan ya danna horn da k'arfi getman ya shek'o da gudu ya wangale musu get d'in, ya danna hancin motarsa cikin gidan har parking lot ya isa ya parker motar ya fito, gefen Raihana ya dawo ya bud'e mata murfin k'ofar ta fito daga ciki tanata kalle-kallen tsari da k'awatuwar gidan saboda kallo d'aya zakayiwa gidan ka gano an kashi naira matuk'a, murmushi ya jefeta dashi yace"mu shiga ciki mana".
Tace"to heartbeat".

Nufar cikin parlourn gidan sukayi suna isa tsakiyar parlour suka zauna saman cushion d'in dake kewaye cikin parlourn, sannan ga k'atanyar plasma nan manne da bango akan girmanta kana hango mutane cikinta manya-manya, suna zaunawa Raihana tayi hamma alamar yunwa takeji tace"washhhhh na gaji sosai".
"ko inzo inyi miki tausa ne baby?".
"a'a na hutassheka".

Tashi tsaye yayi ya nufi hanyar cikin kitchen bai jima ba ya fito da tire ahannunsa cikeda drinks da kayan mak'ulashe, gabanta yazo ya dire tiren d'in sannan ya kalleta yace"sauko saman carpet kici abinci saboda nasan kina jin yunwa".
Firfito da idanunta tayi awaye cikin matuk'ar mamakin zancensa tace"waye ya gaya maka inajin yunwa?".Tareda saukowa k'asan carpet ta zauna ta lank'washe k'afafunta ta yadda zatafi jin dad'in cin abinci.

Ridwan yayi murmushi yace"zuciyarki ce ta isar da sak'o zuwa ga tawa zuciyar saboda kinsan sunada alak'a mai k'arfi atsakaninsu ".

Raihana ta jijjiga kanta alamar gamsuwa da maganarsa tace"haka ne gaskiya habibi".
"yanzu dai bari mu gama kintsa cikinmu saimu cigaba dayin firar".Inji Ridwan.

"To".Ta fad'a kawai.
Tana kallonsa ya zuba musu abinci aplate d'aya suka fara cin abincin atsanake cikin kwanciyar hankali.

Bayan sun gama kintsa cikinsu Raihana ta kwashi kayayyakin ta shiga cikin kitchen ta wankesu fass, tana kammala wankewa ta adanasu cikin kwando sannan ta wanke hannayenta ta fito daga cikin kitchen d'in ta isa wurin Ridwan dayake zaune yana dannar phone, yana ganinta yayi mata murmushi tareda d'aga mata gira yace"har kin gama?".
Raihana ta zauna saman carpet tace"eh mana heartbeat".
Nannauyar numfashi ya sauke ya kalleta cikin so yace"yanzu mu shiga cikin d'aki kiga yadda tsarin d'akin yake idan yayi miki".
Raihana tace"to ba damuwa muje in gani masoyina".
Ridwan shi ya fara mik'ewa sannan itama ta tashi tsaye ya wuce gaba tana biye abayansa har suka iso cikin tsakiyar d'akin wanda ya k'unshi kayan alatu sannan ga fankacecen gado nan atsakiyarsa da wardrobe d'insa da mirror, Ridwan ya zauna saman gadon yace"ya kikaga tsari da k'yawon d'akin yayi miki?".
Raihana ta kama kalle kalle akan tsaruwa da had'uwar d'akin murmushin jin dad'i kawai ta dinga saki tana gyad'a kanta, numfashi ta saukar ta dubesa tace"gaskiya heartbeat gaba d'aya gidan ya tafi da imanina yayimin k'yawo sosai wallahi ".
"naji dad'i nima danayi miki abinda ya saka zuciyarki cikin farin ciki xauna mana kinyi tsaye tun d'azu".

Raihana tazo ta zauna gefen gadon tsakaninsu babu wani tazara mai yawa, can Ridwan ya matso gab da gab da ita suna jin numfashin junansu yace"baby kihau gado da k'yau mu d'an kwanta zuwa anjima sai in kaiki gida".

"har sai anjima zaka kaini gida bayan kacemin ganin tsarin gidanka ka kawoni? Ai yanzu tunda naga gidan saika kaini gida to".

Ridwan ya fara cire tufafinsa ya koma dagashi sai guntun wando da singlet sannan yace"na gaji wlh ki bari zuwa anjima in kaiki gida".Yana rufe bakinsa yahau saman gado daga shi sai guntun wando.
Hakan ne yasa Raihana tayi saurin kauda idanunta daga barin kallonsa saboda ganinshi ahaka ya tayar mata da hankali, jikinta duk yayi lak'was hankalinta ya d'an tashi amma bata nuna masa ko afuskarta ba, tana zaune tayi nisa cikin tunani taji ya aza mata hannunsa abaya yana shafa saurin juyowa tayi ta kallesa cikin firgici da tsantsar tashin hankali tace"miye haka kake wani shafata kamar matarka ta sunna!? ".
Lumshe idanunsa yakeyi yana bud'esu cikin shauk'in buk'atuwa da son cimma burinsa akanta yace"ki kwantar da hankalinki baby ki bani had'in kai mu shayar da junanmu madarar soyayya".

Raihana ta fitar da idanunta awaje cikin mamakin maganarsa tace"ban gane mi kake nufi ba Ridwan?".

"Ina nufin ki amince dani inji dad'i dake ko na minti talatin ne ".

"kasan abinda kake fad'a kuwa anyah kana cikin hayyacinka?".

"ina cikin hayyacina nasan kuma abinda nake fad'a ".

Raihana ta girgiza kanta tace"nikam gaskiya bazan iya aikata zina ba kaga ma tafiyata gida yanzu".Tana k'arasa maganarta ta tashi tsaye zata fice daga cikin d'akin kenan Ridwan ya mike tsaye da sauri cikin zafin nama ya chapko hannunta tareda sanyawa d'akin key ya kulle ,jawota yayi da k'arfi ya mayar da ita saman gadon yace cikin zafin rai "babu ke babu fita daga cikin gidan nan har sai kin biyamin buk'atata Raihana, idan ba haka saidai kiyita rayuwa cikin wannan gida har abada!".

Raihana ta girgiza kanta cikin kad'uwa tace"karka ketamin haddi Ridwan soyayya bata ce haka ba!".

"keee!Kiyimin shiru banason jin maganar banza abakinki kin zata ni wawa dazan dinga kashe miki kud'i abanza halan bansan aikin da nakeyi ba, halan banida k'anne da mahaifan dazan dinga k'yautata musu in samu lada?Saike saboda haka ki bani had'in kai muyi abinmu asirrance batare da sanin kowa ba".

Raihana taji hankalinta ya k'ara tashi zuciyarta sai luguden tsoro da fargaba takeyi dimmmmm, hawaye masu zafi sai sintiri sukeyi afuskarta tace"ka taimakamin kabarni in tafi gidanmu Ridwan kada ka lalatamin rayuwa".

Tsaki yaja mtssss yace"ki bari muyi kawai awuce wurin kina b'atamin lokaci fa!".

Raihana ta dinga ja da baya baya Ridwan ya fisgota da k'arfi tana turjewa hannunsa yasa ya yaga mata riga tareda cire mata zane ta koma daga ita sai pant da bra, nan ta sadak'ar da tabbatarwa k'aryarta ta k'are babu mai k'watarta ahannun Ridwan sai Allah shimfid'eta yayi saman gadon da k'arfi sai kallon boob's d'inta yakeyi manya manya jajir dasu yana had'iyar miyau mak'wat a mak'oshinsa kamar tsohon maye.

Bayan ya kwantar da ita saman gadon yahau samanta yayi mata rumfa fisge bra d'inta ya yassuwa saiga bayyanar tantsa tantsar na fulaninta afili, ganinsu afili yasa Ridwan ya zauce da rud'ewa idanunsa sun chanza colour akan jaraba da sha'awa ,nan da nan ya fice cikin hayyacinsa ya fara kissing d'inta yana shafa ko'ina asassan jikinta, ita kuma sai numfashi take fitarwa sannu sannu tana lumshe idanunta yamutsata ya cigaba

Please Login or Register in order to submit comment