Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA🤴🤴


********************** ? **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************? **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels



Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ? **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ? **************************



*Written by Hafsat MN*





IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_





*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINQAI*





1-5






Kallon mahaifinshi yake cike da murmushi yana girgiza kanshi "yanzu Abdul jalal kafison hakan? Kamar wanda magana take yiwa wahala ya bude bakinshi


"Baffa kudin ne da yawa ga baki daya albarkar gonar nine nake amfani da ita kaga hakan be dace ba jalilah ma tana buqatar kudi tayi ilmi"


Abdul jalal jalilah macece kaje kayi registration da kudin kuma banason musu kaji na gaya maka? Murmushi kawai yayi ya tashi ya fice



Dakin mahaifiyarshi ya shiga ya zauna,, harara tayi mishi "jalal bazaka daina halin nan naka ba ko? Tashi ka fice ka bani wuri" sorry ummi nayi sallama bikiji bane" murmushi tayi mishi ya mayar mata


"Ummi gobe zan tafi zaria baffa yace naje nayi registration" cike da farin ciki take kallonshi "idan zaka tafi zan baka saqo ka siyowa jalilah kayan kwalliya" kallon mamaki yayi mata


Jalal ya zanyi da rikicin jalilah tace sajidah acen aka saya mata nata idan zaka tafi ka siyo mata dan Allah banason rikici,,,, kai kawai ya gyada mata




Da waqa ta shigo tana ganinshi ta fara dariya "ya jalal alqawarina" kallonta kawai yake ta matsa kusa dashi tana qoqarin zama kan jikinshi ya dakatar da ita yana mata wani kallo,,, turo baki tayi cike da shagwaba


Ya jalal toh me nayi kuma? Harara yayi mata


Kuka ta fara yimishi yayi saurin dakatar da ita "meyasa kika gayama ummi ta saya miki kayan make up? Zama tayi kan jikinshi "kwalliya nakeso na koya irin na aunty jiddah" murmushi kawai yayi "kije ki gayama ummi bakyason kayan make up din kawai" ido ta zaro "ya jalal Allah inaso" aa kije ki gaya mata kinga ummi batada kudi idan naje zan saya miki da kudina" toh inga kudin naka?


Hannu yasa cikin aljihu ya fito da naira dubu uku ya nuna mata

Dariya tayi "harda tulare ka siyomin dan Allah" toh naji je ki gaya mata kin fasa"


Da gudu ta shiga dakin ummi " ummi na dawo daga islamiyya" sai akace kada kiyi sallama? Sorry my mom, ni so nake kada ki sayamin kayan make up banaso" murmushi kawai tayi




Rakiya tayi mishi zai tafi yana riqe da hannunta "ya jalal bani ashirin dan Allah" kallonta yayi "me zakiyi da ashirin? Sadaka zanyi maka Allah ya tsareka" sosai ta bashi dariya

"Jalilah madarar kuka zaki saya" dariya tayi har saeda beauty point dinta ya fito sosai


Hamsin ya dauko ya bata cike da murna ta juya ya janyota "ke meye haka? Bana hanaki gudu ba? Toh ai banason ta qarene? Kiyi tafiya banason gudu kinji ko? Kai ta gyada ta juya ya tsayar da mashin ya hau ya nufi tasha


Yana sauka yayima ummi waya ya sanar da ita ya sauka,,, jalal kaci abinci sosai banason wannan zama da yunwa da kakeyi kuma a riqayin ibada akan lokaci" murmushi kawai yayi "jalilah fa? Tana wurin baffan jalal" murmushi yayi kawai ya katse wayan


Baffan ya kira cike da murmushi baffa ya daga wayan "abdul jalal ina fatan ka sauna lafia? Lafia qalau baffa jalilah fa? Wayan baffa ya bata ta karba


"Yaya jalal kyaun alwawari cikawa" ba ya hanya sai zancen kayan make up jalilah? Dariya tayi Yaya nasan ka sauka lafia ai" hmmm toh naji ki tabbatar kinje islamiya" ya jalal ai yanzu daga wurin baffa cen zan tafi"


Toh kiyi karatu sosai kinji? Ta amsa da toh sukayi sallama



Tsaye yake cikin school din duk ya gaji gashi yaso ya koma kafancen amma ba yanda xeyi sai ya kwana

Da dare ya shirya ya nufi wani store yana tunanin ta ina zai fara sayen kayan make up din



Cike da fargaba ya kwashi kayan make up dinda yake tunanin basuda tsada



Wurin da ake biya yaje akayi mishi bill ajiyan zuciya yayi yana murmushi ya ciro kudin ya biya


Kallonshi take kamar tanason tayi mishi magana amma sam ba alaman faraa a tare dashi har ya fice tana kallonshi tana mamakin wannan baqon al amari.......
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA🤴🤴




*Written by Hafsat MN*






IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_





6-10





Cike da murna taje ta taryeshi "ya jalal oyoyo" murmushi ya sakar mata suka qarasa ciki direct wurin baffa ya nufa ya gaidashi "abdul jalal sannu da hanya" yauwa baffa ya gajiya? Alhamdulillah


Murmushi ta sakar mishi ya maida mata "Ummi sannu da gida" jalal ya hanya? Lafia qalau


Ciki ya shiga yana riqe da hannun jalilah "ya jalal ka siyomin kayan make up din? Harara yayi mata


Ke bakisan idan mutum yayi tafia yana buqatar hutu bane? Toh ka huta sai ka bani,,, murmushi kawai yayi ta juya ta fice ya bita da kallo



Zaune yake dakin ummi tana kallonsu ahida jalilah sunacin abinci har ya kammala yabar jalilah dan duk da kasan cewarta qarama ta fishi cikin abinci


Tashi yayi ya nufi dakinshi ya dauko saqon jalilah ya bata cike da farin ciki ta tashi taje tayi wanka ta dawo ta zauna ta fara kwalliya


Kallonta ummi take ciki da mamaki yanda take tsara kwalliya har sai da ta kammala ta dago ta ware ma jalal idanuta saida tasashi dariya "ya jalal meye abin dariya banyi kyau bane? Allah kinyi kyau sosai jalilah dariya tayi ta tashi taje ta sanya kaya ta fito "ya jalal dauremin gashina" ya kama gashin ya daure mata ya daura dan kwalli duk ummi na kwallonta tana mamaki yanda jalilah ta iya kwalliya


"Jalah wai nawa ka kashe ka kayan kwalliyar nan? Kamar beji me tace ba "jalal bakaji ina magana bane? Toh ummi me zance? Ai nasan bakada abin cewa tunda ka kashe kudi masu yawa"


Tashi yayi yana murmushi ya fice zuwa dakinshi dan yana buqatar yayi bacci



*********************************


Zaune yake a gaban mai marata ba duk ranshi a bace yake cikin qasaita ya kira sunanshi "abdul jabbar arayuwa mutum baya sanya sabon Allah gaba kaji tsoron Allah a gaba kaji tsoron Allah shine kawai zan gaya maka mutuwa tana biye dakai aduk inda kake kuma baza ta gaya maka zuwanta ba sai dai ta risqeka dan haka kayiwa kanka tanadi mai kyau" yana kaiwa nan ya gyara kwanciyarshi cike da girmamawa yayi godiya ya tashi ya fice



Dakinshi ya nufa ya shiqa zuqar sigari "ya dai cool A J? Busar da hayaqin bakinshi yayi "AK bansan meke damun abba ba nifa gaskiya dolene nabar qasar nan dan bazan iya wannan takurawa ba can you imagine wai wannan imran din ne ya gayama abba wai shaye shaye nakeyi kuma wai zance aure fa mami takemin duka yaushe na gama secondary school wai zan lalace idan baayimin aure ba? Dariya AK yayi toh kai kaje ka nemi mata acikin matan da suke sonka mana


Haba AK I can't do that kai bari kaji nifa I wish to finish my life single


Dariya AK yayi harda riqe ciki dan yana mamakin hali iri na abokinshi shi sam mata basu dameshi ba kawai yasha gida da sauran kayan maye yayi wanka ya shiga gari ya kashe kudi kawai yayi bacci



Haka suka ci gaba da shan kayan mayensu har sukayi bacci





*********************************




Cike dajin kewar su yake tafiya cikin mota ba abinda ummi bata hada mishi ba haka baffa ya bashi kudi sam beyi tunanin baffa ya tara wannan kudin ba


*8:45pm* abdul jalal yana zaune cikin dakinsu ga baki dayansu sabbin zuwa ne ba wanda yake magana da wani,,,,, wayanshi ya dauko ya kira ummi cike da sanyi take mishi magana



"Ummi kin fara bacci ne? Murmushi tayi,,, jalal kewarka ce ke damuna,,, dan murmushi yayi "Ummina ga jalilah bazata debe miki kewa ba? Hmmm toh ina fatan ba wani damuwa ko? Ummi ba wani damuwa komi lafia qalau


Toh adai kiyaye dokokin Allah banason ayi wasa kaji ko? Dan murmushi yayi ba tare da yace da ita komi ba tasan ba magana yake ba shiyasa ta kawar da zancen zuwa zancen ya riqa cin abinci haka sukayi sallama


Washe gari ya shirya ya nufi wurin lectures cike da natsuwa yake sauraren lectures din bashi ya fito ba sai 2pm ya nufi masjid



Kallonshi yayi yana murmushi shima ya mayar mishi tare da tashi ya fita daga masjid din ya nufi hostel


Zaune yake bayan ya kammala cin abinci yana bida jotting dinda yayi ya shigo da sallama ya amsa mishi "na fito daga masjid ban sameka ba ashe ka dawo hostel" murmushi kawai jalal yayi mishi ba tare da yace dashi komi ba


"Gashi muna room daya saida bansan sunanka ba,,, duo jalal ji yake an takurashi

"Abdu jalal" ya bashi amsa a takaice "nice to meet you abdul jalal am mubarak muhmud" kai ya gyada mishi sorry abdul from which department? Ahankali ya dago yana kallonshi kafin ya bashi amsa

"Information technology" dariya mubarak yayi "nima fa information technology suka bani, wow am so happy gaskiya pls can we be a friends? Ya fada tare da tsareshi da ido, murmushi jalal yayi tare da gyada mishi kai cike dajin dadi mubarak ya zauna kusa dashi ya fito da wayanshi mai tsada ya kira mami dinshi "mami kinga na samu friend kuma yanada kirki" dariya jalal yaga mubarak yayi shi ga baki daya mamaki ya cikashi

Wayan mubarak ya bashi karbi Ku gaisa da mami ba musu ya karba

Sallama yayi mata cike da girmamawa ya gaidata ta amsa sosai taji ya burgeta "ya sunanka? Abdul jalal, masha Allah toh kayi karatu banda wasa "in shaa Allah" tace da ita ya bawa mubarak waya sukaci gaba da magana da ita




Kallonshi mubarak yayi "abdul anjima zamuje muyi karatu a tare ko? Kai kawai ya gyada mishi yaci gaba da karatunshi ga baki daya mubarak ya takurashi


*8:30pm* mubarak ne tsaye yana jiran abdul jalal su fita shi sam hakan be mishi dadi ba haka ya haqura ya shirya suka fice sai faman janshi da surutu mubarak yakeyi amma sam baya kulashi har suka qarasa lecture hall din suka nemi wuri suka zauna


Tunda suka fara karatu mubarak be qara yiwa jalal magana ba har suka gaji suka nufi hostel


Chin chin jalal ya fito dashi daga cikin kayanshi kafin yayi magana mubarak har ya fara ci,,, kallon shi mubarak yayi "amma fa chin chin din ya hadu wa yayi mana shi? "Ummi" ya bashi amsa kirata nayi mata godiya pls "tayi bacci" okay kawai tace yaci gaba dacin chin chin din kuma yaci sosai ya tashi ya fita ya dawo musu coke mai sanyi ya ba jalal "no thanks" harara yayi mishi ya kawar da kanshi "Allah sai kasha,,, ya karba yasha kadan yayi kwanciyarshi


**********************************


Kallonta kawai yake tana zuba mishi fada kamar zata cinyeshi "Allah kayima kanka fada kafin mai martaba ya yanke maka hukunci da zai baka mamaki kasan dai baya wasa gara kaje kayi registration ka koma school ya fiye maka


Mami amma kin janye zancen auren ko? Kai ta gyada mishi cike da farin ciki ya tashi ya fice direct sai school ya kammla komi nashi yayi shirin fara lectures


Zaune yake cikin mota na zuqar shigari yana shan waqa




Juwairiya kinga maras kirkin nan ya dawo zo mu sanja hanya, tsaki tayi "ina ruwanki dashi dan Allah muje kinga ni yunwa nakeji" sam AJ be kulasu ba har suka fice dan shi takaicin mata ma yakeyi shi sam bass gabanshi




"Abdul kayi sauri kada mu makara pls" saida ya kammala shirinshi ya dago yana kallonshi ya sakar mishi harara "Allah ka iya wulaqanci sai nayita faman magana kana wani shareni nima fa JININ SARAUTA ne" sosai yaba jalal dariya dan shi bayada alaqa da sarauta yanayi ne kawai


Haka suka qarasa lecture hall din har 1suna ciki koda suka fito kowane yunwa yake ji,,,, kallonshi mubarak yayi "muje eatery yunwa nakeji" wani kallo jalal ya watsa mishi ya juya ya nufi hostel mubarak ma yabi bayanshi cike da takaici suka qarasa sai faman fada mubarak yake jalal be kulashi ba ya dora ruwan zafi saida suka tafasa ya dauko garin kunu ya dama ya zuba a flask din da ummi ta bashi ya dauko farin dan wake ya hada mubarak sai kallonshi yake har ya gama ya tashi ya fita be wani jimawa ba ya dawo da crete na egg da coke da ruwa ya dafa egg din ya yankashi cikin dan waken ya zuba yaji da mai kafin yayi magana har mubarak ya fara ci shikam kunu yasha yaje masjid yayi sallah ya dawo yayi kwanciyarshi saida akayi laasar mubarak ya tadashi sukaje masjid sukayi sallah


Kallon mubarak yake ya bude jakanshi ya bedo chinchi yazo ya zuba kunu a cup ya fara sha har ya kammala jalal be kulashi ba

"Abdul me zaka girka mana anjima? Ko kallonshi beyi ba bale ya kulashi "cool jalal ko baza muci komi bane? Sai a lokacin ya kalleshi kamar me nazari dariya yayi "Allah ni kana bani mamaki kai haka kake rayuwa ba magana? Sunkuyar da kanshi yayi kawai yaci gaba matsa wayanshi "assalamu alaikum" a dayan bangaren kuma baffa ne ya amsa "baffa bacci nake koda ka kira" jalilah ce keson magana dakai murmushi kawai yayi baffa ya bata waya "ya jalal dan Allah ka qaromin foundation idan zaka dawo " meye hakan? Wanda ake shafawa kafin a shafa powder" jalilah banfa gane ki bari dai zan bincika, toh amma fa kuma irin wannan nakeso, toh bayada wani suna ne? Ailin liquid foundation murmushi yayi "toh naji hope kinje school yau? Eh naje, islamiya fa? Ya jalal kasan banawasa fa, murmushi yayi toh ki haifa ummi ta amsa ta bawa baffa wayan


"Abdul jalal karatu da sauki ko? Eh baffa ba wani wahala

Allah ya taimaka a riqe ibada sosai kaji? Kai ya gyada kamar yana ganinshi sukayi sallama ya ajiye waya...........
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴





*Written by Hafsat MN*




IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_





11-15





Kallon shi mubarak yayi "amma kai asalin bahaushe ne wallahi" kallon shi yayi da alamar tambaya, harara yayi mishi "ai ni dana kira mamina na baka kun gaisa at least ko qanwarka ka bani mu gaisa mana amma kaqi" murmushi kawai jalal yayi ya zuba dan wake a plate ya fara ci


***********************************


Tsaye yake bakin hall din da zeyi lecture yana zuqar shigari yana matsan wayanshi hankalinshi a kwance gashi yasha wanka ya hade iya haduwa


Prof dan asabe ne ya biyo yana sauri zeyi musu lecture cike da mamaki yake kallonshi ko ajikinshi sai da ya kammala shan sigari kafin ya nufi cikin hall din



Dakatar dashi prof yayi "abdul jabbar pls get out" cikin black spectacle dinshi yayi mishi kallon raini, ahankali ya taka yaje kusa dashi "atarihi ka tabajin an kori zaki daga dawa? Cike da takaici prof yake kallonshi sam besan hali irin abddul jabbar ba kodan yana ganin shi dan sarki ne? Murmushin takaici yayi ya juya yaci gaba da bawa yara lecture abdul jabbar kuma ya juya ya fice ya hau saman motanshi ya kunna sigari ya shiga aikinshi


A J how far? As usual "ya kafita? Dan tsaki yayi "nifa daman ba lectures din nakeso ba kasani amma wai wannan dan asaben ya zanyi dashi ne zan sa adan mishi bulala ne ko ayi mishi na yaren Igbo da yoruba? Aiko A K yace me zeyi inba dariya ba "A J man din nan fa ba yaro bane me zaisa kayi mishi bulala? Kawai naga ya fiye rashin ji ne" amm ya zancen imran? Kawai nasashi ya hada kayanshi ya koma hostel kuma na gaya mishi idan yayi exam ya wuce gidan ubanshi" sosai A K yayi dariya "cool A J kana shaaninka fa" saukowa yayi daga kan mota dan bayason surutun A K

In zaka? Cikin motan ya shiga ya dauko giya kawai ya fara sha "cool A J ba anan ya dace kasha giya ba fa kasan ni ba yanzu zan koma gida ba" harara yayi mishi yasha iya shanshi ya tada mota kawai cike tashin hankali AK yake kallonshi saida yaje ya samu wuri inda yake da itatuwa acikin school din ya kwabe sit ya shiga baccinshi




Juwairiya kinga mutumen naki fa,,, salma Allah zamu bata dake" dariya salma tayi,,, bari kiji Allah nafison baqin kumurci akan wannan guy din shi sam besan darajar mace ba



Bikiga yanda sukayi da fatima muktar ba kawai ya tureta ba tare da ya juyoba yayi mata sannun ba ya wuce abinshi ta sameshi kinsan itama ba sauki ne da ita ba taje tayi mishi masifa kawai ya kira wani wai zan biyaka ko nawa kakeso kayi mata bulala cike da mamaki ta tsaya tana kallonshi sam batayi tunanin rashin kirki irin na cool A J yakai hakan ba



Manta da zancenshi ni banida lokacinshi


Fira suke har suka qarasa hostel



Zaune suke shida mubakar suna karatu wayanshi tayi ringing ya daga kallonshi juwairiya tayi yana magana da ummi har ya kammala ya ajiye wayan ba tare da ya kalli mubarak ba dan bayason qorafi



Salma kinga wani ikon Allah? Salma kam baki ta bude tana kallon jalal yana karatu


Kallon mubarak yayi "ka gaji ne? Murmushi kawai yayi mishi "toh muje mana" ya tashi suka fice


Amma they are related ko? Anya? Haba wannan kamar tayi yawa har voice dinsu fa


Ke kyaleni da zancen nan banaso


Dariya Salma tayi sukaci gaba da karatu




Cikin parlour ya sami mai martaba zaune cike da girmamawa ya gaidashi ya amsa "abdul jabbar da gaske ne ka koma makaranta? Abba na koma" murmushin qasaita yayi


Allah ya taimaka "ameen abba" ya tashi ya fice............
[25/12, 13:21] Hassan Atk: 🤴🤴JININ SARAUTA 🤴🤴





*Written by hafsat MN*





IN DEDICATION TO
_AUNTY AMINA ALHASSAN_






16-20






Wanka yaje yayi ya shirya cikin qanana kayan ya zuwa rings dinshi na gold guda biyu yasa agogonshi na Rolex ya dauki mota ya nufi cikin school yana tafe yana shan waqa har ya qarasa ciki ya bude motan ya fito ya haye saman motan yabar motan bude waqa yana tashi ahankali



Cike da yanga ta biyo wani tsaki yaja "wai macece zata fito tana wari har take ganin ta hadu tana yanga


Iya bacin rai juwairiya tajishi amma ta danne zuciyanta ta shareshi kawai ta wuce abinta dan ita tasan bata wari dan Arabian sultan take amfani dashi



Har ta qarasa A G T (Agric theater) ranta a bace ta nemi wuri ta zauna ta zuba tagumi tana tunanin wulaqancin da zata yiwa cool A J


Dariya mubarak yake lokacin da suke qarasowa cikin AGT din jalal sai faman murmushi yake dan ba kadan shima mubarak din ya bashi dariya


Cool jalal zanso ganin ranar da zakayi tadi gaskiya,,, bata ranshi yayi ya nemi wuri ya zauna sam ba wani nisa ne suke da da juwairiya ba


Abdul jalal wai kai wannan shurun baya damunka? Kallonshi abdul jalal yayi amma sam bayajin zai iya magana kuma badan bayada abinda zai gaya mishi ba " kayi magana mana ka tsareni da ido haka gashi ni wannan idanun naka bawai so nake kana riqa dorasu akaina ba dan sai naji kamar nayi laifi an tsareni" kawar da kanshi yayi yana murmushi


Wayanshi ce tayi ringing yaga ummi ce ya daga

Cike da hanzari mubarak ya karbe wayan yayi mata sallama ta amsa ya gaidata


"Ummi sunanan mubarak nima yaronki" murmushi tayi saboda ya bata dariya "sannu mubarak ya karatu? Lafia ummi sai dai matsala na daya abdul sam bayason yimin magana eh aa ne kawai tsakanina dashi" mubarak haka yake ko a gida idan kaji yayi magana toh jalilah ce ta sanyashi magana" Ummi jalilah tana ina? Ai gata kusa dani, ummi bata mu gaisa"


Sallama tayi ya amsa "ya jalal baka manta da alwarina ba ko? Kuma ka siyomin abaya dan Allah inaso na riqa shigan larabawa kuma kada ka manta ka qaromin tulare na kusa qarasa wannan" dariya yayi "wannan ya mubarak ne ba ya jalal ba kuma zan saya miki saboda ni kika gayama" kai waye? Nima yayanki ne

Toh ya jalal kuma fa? Gashi,, ya bashi wayan ya karba


"Ya jalal wannan waye? "Bana hanaki yawan surutu ba? Yaya jalal ai nayi tunanin kaine kasan bana magana da wanda bansani ba


Toh anjima zan kira Ummi sai muyi magana ki gaida ummi kuma ki tabbatar kinje kinyi kitso "Yaya jalal ba wanda zai rakani" aa kiyi haquri kije kinji? Dariya tayi ta amsa mishi ya katse wayan




"Ya jalal jalilah zatakai shekara nawa? Kamar beji me mubarak din yake fada ba "jalal fa? Kallonshi yayi cike da nazari "bazan iya ganewa ba" kamar ya? Ba qanwarka bace? Murmushi yayi yaci gaba da karatunshi


"Kaji dashi cen" cewar mubarak tare da matsawa kusa da jalal din


Kallonshi juwairiya takeyi koda baa fada ba tasan ba wani hali ne dasu ba saboda yanayin kayan jikinshi da wayanshi kadai ya tabbatar mata da hakan



Haka suka qaraci karatunsu suka nufi hostel



_after a

Please Login or Register in order to submit comment