Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

talatin alhalin na san
cewa baka kaunata ka tsaneni kamar yadda ka tsani mutuwarka
saboda karagar mulki
ina son ka tura su izuwa can kauyen limras su karasa sauran rayuwarsu a can a matsayin talakawan gari
kawai koda ba zaka taimaka musu da komai ba
na san wacece matata shamilat macece mai zuciyar maza ko
babu aure zata iya rike kanta kuma tare da abinda ta haifa
Guyson Sunana
Koda sarki hisham yazo nan a zancensa sai hawaye ya sake zubo masa a lokacin da ya kurawa
yarima zamaru idanu
nan take yarima zamaru yaji ya kamu da tsananin kunyar sarki hisham gami da
matukar tausayinsa har shima hawaye ya sake zubo masa
kawai sai yarima zamaru ya mike tsaye ya juyawa sarki hisham baya yace nayi alkawar idan har matarka da abinda
ta haifa sun shigo cikin garinan a raye lallai
zan zamo mai rike su da amana kamar yadda ka
rikeni har izuwa sa adda mutuwa zata rabani dasu
koda
gama fadin hakan sai yarima zamaru ya fice daga cikin turakar yana kuka da fitowarsa yana kuka yayi arba da sarkin yaki amzadu
a tsaye shi kadai a kofar dakin nan fa sukayi wani irin kallo kallo na rashin yarda kawai sai
yarima zamaru ya yiwa amzadu dan guntun
murmushi yyi tafiyarsa shi kuma sai ya bude kofar turakar
da sauri a dimauce ya shiga ciki
da shigarsa yayi arba da sarki
a kwance kamar yadda ya fita ya barshi dazu
cikin hanzari sarkin yaki amzadu yaje ya sake zama daf da sarki ya dubeshi a
firgice yace
ya shugabana me ya faru tsakaninka da dan uwanka na ga shima ya
fita yana kuka
koda jin wannan tambaya sai sarki hisham yayi dan guntum murmushi cikin
matukar karfin hali sannan yace Alhini ne na rabuwa
da juna ya sakaga duk muna kuka
domin mutuwa zata shammace
mu a lokacin da bamu taba zato ba tafi na sallame ka
wasiyata ta karshe a gareka ita ce ka tuna da duk
irin abubuwan alherin da nayi maka a rayuwa
a duk sa adda wata masifa ta taso kada ka kasance mai
yin butulci a bayana
sa adda sarkin yaki amzad yaji wannan batu daga bakin sarki sai ya kamu
da tsananin
mamaki kuma ya kasa fahimtar abinda yake nufi har ya budi baki da nufin ya sake
tambayarsa sai ya kasa
nan dai ya juya ya fice daga cikin turakar cikin tsananin
damuwa da tashin hankali wanda bai taba tsintar
kansa ba
.
Daga wannan rana sarki hisham ya ci gaba da ciwo wanda
ba sauki kuma babu alamar za a sami saukin
har saida ta kai cewa ko motsi da baki baya iya yi
abinci ma da ruwa idan aka dura masa baya shiga cikinsa
a ranar kwana na bakwai ne ciwon ya tsananta
ainun
hankalin kowa ya dugunzuma a tsawon kwanaki bakwan da sarki hisham ke kwance
cikin jinya yarima zamaru bai sake zuwa ya duba shiba
amma sarkin yaki Amzad kuwa dare da rana yana tare dashi
a ranar kwana na bakwan da magariba rai yayi
halinsa nan fa labari ya bazu a ko ina cikin kasar mutane
suka kama koke koke sai a wannan lokacinne aka
ga yarima zamaru ya shigo cikin fadar a lokacin da aka fara shirye shiryen binne
sarki ana ganin yarima zamaru hankalin kowa ya tashi
domin an san cewa dolene yanzu komai ya
sauya a birnin duk irin adalcin da ake yiwa talakawa
an daina kuma za a matsa musu a kan biyan haraji mai yawa za a rinka zaluntarsu
babu sauran masu jin dadi da kwanciyar hankali
face sarakai da attajirai wadanda zasuyi biyayya ga sabon sarki Yarima zamaru
nine dai Al amin Ahmed misau
Guyson nake
Bayan an gama jana izar sarki hisham an binne shi a cikin dakin da aka binne
sarakuna arba in da uku na
kasar sai yarima zamaru ya tara gaba dayan yan
majalisar kasa a dakin taro ya tabbatarmusu da cewa
gobene za ayi bikin nadin sarautarsa sannan kuma ya umarci sarkin yaki da ya tabbatar da tsaro a ko ina
a cikin birni da kewaye kuma ya sanar da dakarun dake tsaron
kofofin gari cewa ba shiga kuma ba fita daga yanzu har izuwa gobe sa adda za a kammala bikin nadin
sarautar tasa
koda jin wannan umarni sai kowa ya cika da tsananin mamaki
amma sai gaba daya yan majalisar sukayi shiru suna masu sunkuyar da kansu kasa saboda
tsoron yarima zamaru aka rasa wanda zaice kala sai sarkin yaki amzadu
ne ya dubeshi yace yakai sarkin gobe kayi sani
cewa wannan hukunci da ka yanke baiyi dai dai ba domin tsarin mulki bai yarda da hakan ba saboda bai dace ba ka
hana mutane zuwa cikin gari nan ba koda ka hanasu
fita a wannan lokaci da ake ciki na babban rashin da akayi na dan uwanka
ka sani cewa mutane da yawa zasu zo ne domin
su ziyarci kabarin sarki su nemi tabarrakinsa kuma suyi masa addu a wasu kuma zasu kawo ziyara ne izuwa
kallon bikin nadin sarautarka,
sarakuna da yawa daga makwabtan kasashe ma zasu zo wannan gagarumin biki
kafin sarkin yaki amzad ya gama rufe bakinsa tuni yarima zamaru ya tari numfashinsa
yana mai daaka masa tsawa yace wanene kai harda zaka gaya mini abinda zanyi
ka sani cewa in banda kana da matukar muhimmanci
da amfani da yanzu take zan sauke ka daga kan mukaminka
na sallameku kowa ya kama gabansa nan take kowa
ya kama gabansa jikinsa a sanyaye ya fice daga cikin dakin taron
aka bar yarima zamaru a zaune shi kadai
Al amin Guyson, lokacin da sarkin yaki amzad ya isa
kofar gidansa sai ya hango kofar gidan wayam babu dakarun
da suke yi masa gadi kuma kofar gidan a bude take wanwar al amarin da yayi matukar razana shi kenan yayi wuf ya sauko
daga kan dokinsa yana mai zare takobinsa kawai sai ya ruga da
gudu izuwa cikin
gidan yana mai kiran sunan matarsa
da danta himar wanda ya kasance yaro dan shekara
hudu amma shiru baiji sun amsa ba kuma baiji duriyarsu ba
,,,
Al amin Guyson Kenan
Anan Zan dakata
amma Kafinnan
Nidinne dai
AL AMIN AHMED MISAU
guyson inkiya
Admin Na zauran Labarai
KISAN GILLA
Littafi Na Daya (1)
Part C.
.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
Yana isa falo yayi turus saboda tsananin kaduwa
da mamaki bisa abinda yayi arba dashi ba wani abu ya gani ba face
yarima zamaru zaune akan
kujera cikin shigar yaki ya harde kafafu daya kan daya yana kallonsa cikin murmushi abuna farko da ya daure masa kai shine
yaya akayi zamaru ya riga shi zuwa nan alhalin a can gidan sarauta
ya barshi kuma yaushe ma ya canja kayansa har yazo nan din kawai sai amzad ya baiwa kansa amsa
yace tabbas wannan al amari ne na tsafi cikin alamun
fushi sarkin yaki ya dubi yarima zamaru yace ina iyalina
tuni
jikina ya bani cewar wani abu makamancin wannan sai ya
faru kuma yanzune na tabbatar da cewar kana da hannu
a kan ciwon da sarki ya samu wanda ya zama sanadiyar
ajalinsa
lokacin da yarima zamaru yaji wannan batu sai ya bushe da mahaukaciyar dariya
lokaci guda kuma ya turbune fuska yace ina son mutum mai
kaifin kwakwalw
da hasashe irinka
tabbas duk abinda ka fada haka yake gaskiya ne nine na
kashe sarki domin na sami wannan karagar mulki
wacce ta gagareni tsawon shekaru
ban zo nan domin muyi doguwar magana nazo ne domin na sanar dakai
cewar iyalinka suna hannunmu kuma mun boye su a inda babu wanda ya isa
ya gansu ko ya dauko su face mu da kanmu ina son
yanzu take ka debi dakaru dubu dari shida a cikin shigar badda kamanni ku nufi
jeji na bayan gari ku tari gimbia shaliat tare da dakarun mahaifinta
wadanda sukayi mata rakiya izuwa nan birnin
ina son duk yadda za ayi ka kashe su gaba dayansu
ban son mutum daya ya tsira
da jaririn da ta haifa ku tabbatar da cewa kun kashe shi idan kuka yi wannan aiki
dai dai zan dawo maka da iyalinka gobe da safe idan kuma ka ki bin umarnina gawar iyalanka zamu kawo maka
idan kunne yaji gamgar jiki ya tsira
kuma shawara ta rage ga mai shiga rijiya
Koda gama fadin hakan sai yarima zamaru yayi
girgiza ya bace bata daga cikin dakin yana mai
kyalkyala dariya tamkar bai taba wanzuwa ba a ajan
Al amin Guyson nake
nan fa sarkin yaki amzad ya dimauce
kuma ya fusata ainun bai san sa adda ya kurma uban ihu ba kuma ya fashe da matsanancin kuka
saboda tsananin bakin ciki da takaici daga can sai ya juyada sauri a guje ya koma
kofar gida ya kama dokinsa ya hau ya zabureshi da gudun tsiya
A can daji kuwa Gimbia shamilat na zaune a cikin keken
doki
rungume da jaririnta dakaru sun kewayeta gaba da baya
dama da hagu ana tafiya saboda kwarjinin wadannan dakaru da irin kayan yakin da suke dauke dasu
babu abinda zai gansu bai yi shakkarsu
ba , da yake duhu yayi gaba dayan dakarun sun kunna fitilun itace don haka hanya sai tayi haske
sai sauri ake
tayi saboda an san cewa saura baifi tafiyar rabin sa a ba
a iso cikin birnin madinatul hashwar
a wannan lokacinne shamilat na cikin tsananin farin ciki
sai yawan kallon
jaririnta take yi tana murmushi saboda tunanin cewa a yau ne sarki hisham zai ga dan cikinsa da idonsa abinda ya shafe shekara da shekaru yana burin gani
bai gani ba
saboda zakuwar da tayi taga an isa cikin garin har umarni take bayarwa a kan a karawa dawakai kaimi
nan fa aka ci gaba da gudu kai kace hari za a kai
kaico rashin sani yafi dare duhu ashe
wadannan zuga ba su san cewa mahallaka suke kai kansu ba lokacin da tawagar
gimbiya shamilat suka iso
dai dai wani fili mai fadi wanda tsakaninsa da karshen dajin bai wuce zira i arba in ba
sai kawai sukaji ana yi musu ruwan kibiyoyi ta gabas da yamma kudu da arewa wayyo Ajali idan yayi kira sai an amsa
babu makawa
Nan fa dakarun da dawakai suka rinka ihu da haniniya suna zubewa kasa matattu kafin su ankara an kashe kaso daya a cikin kaso uku
ita kanta gimbiya shamilat taga matukar tashin hankali domin ta gefen idanunta da kunnuwanta kibiyoyi
suka rinka giftawa da kyar aka sami wasu zakwakuran mayaka suka rinka kade kibiyoyin
da ake harbo mata da takubbansu
A sannan ne kuma dakarun suka yi wata dabara
wadanda keda
garkuwoyi sai suka yi kawanya a tsakiya suka kare sama da kasansu
aka sanya gimbiya shamilat da sauran dakarun a tsakiyar da irar duk da haka sai aka ci gaba da harbo kibiyoyin
har zuwa tsawon lokaci
a wannan lokaci jaririn shamilat na ta faman kuka itama gimbiya tana kukan sai da aka saina harbo kibiyoyin
sannan shugaban dakarun ya dubi gimbiya shamilat yace
ranki ya dade yanzu me ye abinyi
ba muga wadanda suka kawo mna wannan hari ba
har yanzu domin sun boye ne a cikin duhuwar bishiyoyi
shin zamu ci gaba da tunkarar birnin madinatul hashwar ne
wanda tazararmu da shi a yanzu bata wuce zira i arba in ba ko zamuyi kokarin komawa da baya ne
domin mu tserar da rayuwarki data wannan yaron naki
sa adda shugaban dakarun yazo nan a zancensa sai hawaye ya zubowa gimbiya a lokacin da zuciyarta ta buga da karfi
kuma tsoro ya shigeta kawai sai ta dubi shugaban
dakarun ta ce sarki Hisham ya fadi ''
cikin kaduwa shugaban dakarun ya cubeta yace
ranki ya dade ya akayi kika sani?
Shamilat ta fara zubar da hawaye ta ce inda
mijina yana raye babu yadda za ayi a taremu a kan iyakarsa
domin a hallakamu
abu ne mai hadarin gaske muci gaba da tunkarar
cikin birninnan yanzu kawai muyi
Kokarin komawa da baya in munyi sa a mu tsira da ranmu
kafin gimbiya ta gama rufe bakinta sai kawai
sukaji sukuwar dawakai an durfafosu kafinsuyi wani
yunkuri dakarun masu yawan gaske ninkinsu uku sunyi musu kawanay
gimbiya shamilat ta fito daaga cikin keken dokinta a fusace
rike da jaririnta domin taga ko suwaye ne wadannan dakaru da suka kawo musu hari
kawai sai taga ashe dakarun sunyi shiga ne irin ta
bakaken kaya ba shigar kayan yakin dakarun birnin madinatul hashwar ba kuma duk
sun rufe fuskokinsu da bakin kyalle idanunsu kadai ake gani
a dai dai wannan lokaci ne shugabam dakarun gimbiya ya rugo gareta ya dubeta
cikin alamun tsananin tsoro da damuwa yace
haba ya shugabata yaya zaki fito fili haka gaban wadannan makiya
alhalin muna kare rayuwarki da ta jaririnki
shamilat tayi ajiyar zuciya tace ai zancen kare ni da
jaririna ya kare ka dubi wadannan dakaru ka gani ai sarkin yawa yafi sarkin karfi kuma ba zamu iya guje musu ba
duk mutuwa zamuyi ni kawai
yanzu ina son na san wanda ya turo a kasheni kafin na mutu
Al amin Guyson Sunana
don bana son na mutu cikin wasu wasi
koda gama fadin hakan sai gimbiya shamilta ta dubi wadannan dakaru masu bakaken tufafi
ta daka musu tsawa tace ku su waye kuma waye ya turoku ku kasheni
mtar sarkin birnin madinatul hashwas
dajin wannan tambaya sai bakaken dakarun suka dare
shugabansu ya ratso ta tsakiyarsu ya matso kusa da ita ya tsaya
duk da cewar fuskarsa a rufe take idanunsa kadai ake gani saida gimbiya shamilat ta shaida ko wanene shi nan take hawaye ya zubo daga cikin idanunta
ta dubeshi tace yakai Amzad yanzu dakai za a hada baki aci amanar mijina
Yanzu ashe dama zaka iya yiwa sarki butulci aashe zaka iya mancewa da duk
irin halaccin da yayi maka a rayuwa
sa adda shamilat tazo nan a zancenta sai sarkin
yaki Amzad ya kwaye fuskarsa sai ga hawaye na zuba masa a lokacin da suka kurawa juna idanu shi da ita
tsawon yan dakiku dayansu baice
uffan ba sannan Amzad yace ki gafarceni ni ya shugabata idan ban bi umarni ba nima zan rasa matata da dana
Koda jin haka sai shamilat ta fashe da kuka tace
haka ne rai baifi raiba amma kafin ku kashe mu
ina son ku fada mun iyakar gaskiyar menene ya faru ga mijina
dajin wannan tambaya sai hawaye ya sake zubowa sarkin yaki amzad ya ce mijinki ya mutu
koda jin haka sai jiri ya debi shamilat ta yanke jiki zata fadi kasa
cikin zafin nama amzad ya daka tsalle ya dira a gabanta ya tallafeta tare da jaririnta yana mai baiwa dakarunsa umarnin su hallaka dakarun gimbia
kaico Ajali ba a sa ma rana nan da nan dakarun amzad suka kama ragargazar dakarun shamilat
wuri ya hargitse banda ihun mazaje babu abinda mutum ke ji
duk da cewar sarkin yawa yafi sarkin karfi sai da aka jima ana gumurzu a karshe dai ragas aka yi aka karar da gaba dayan daakarun
kowanne bangare ya zamana cewa babu daya da ya rage a raye face
sarkin yaki Amzad a dai dai wannan lokaci ne gimbia ta farfado daga dogon suman da tayi idanunta suka bude tana mai gani
dishi dishi idanunta na washewa tayi arba
da sarkin yaki amzad a zaune daf da ita rungume da jaririnta
gaba dayan dakarun dake wajan na kwance a kasa sun zama gawa
shamilat ta mike tsaye zumbur ta rugo iduwa wajan amzad ta miko hannayanta
da nufin ta karbe jaririnta amma sai ya tokare da kotar takobinsa a kirjinta yace ya shugabata
kiyi sani cewa yarima zamaru ya umarceni da na kashe ku keda jaririnki in ba haka ba kuwa sai ya kashe matata da dana ba zan iya kashe ku ba
domin idan nayi haka naci amana
Koda yazo nan a zancensa sai ya durkusa bisa gwiyoyinsa agaban shamilat a lokacin da idanunsa suka
ciko da kwalla yace ina rokonki daki bar garin nan kuma karki koma birnin darul hashbush ki sanar da mahaifinki abinda ya faru
domin kina gaya masa zaice zai yaki sarki zamaru kuma kin
sani cewa mayakan mu sun ninka nasa sau goma a yawa da karfin makamai
cikin tsananin bakin ciki shamilat ta fashe da kuka
kamar ba zata daina ba daga can saita dago kai idanunta sunyi sharkaf da hawaye tace shi kenan ka bani dana nayi alkawarin
zan tafi izuwa wata nahiyar daban na reni dana a can har
abada ba zan dawo nan ba kuma ba zan taba gayawa dana matsayinsa ba
koda jin wannan batu sai hawaye ya zubowa sarkin yaki amzad ya dubeta yace
ba zan iya baki yarima ki tafi dashi ba
cikin razana shamilat tace yanzu kana nufin zaka rabani
da dana kenan wanda shi kadai ne abinda ya rage mini a duniya
amzad yace
kawar kuwa domin barinsa awajanki ba karamin hadari bane nayi miki
akkawari zan reni wannan yaro a cikin birnin madinatul
hashwar
kusa da karagar mulkinsa ba tare da ya san ko shi wanene ba
kuma komai dare dadewa in dai kina raye yana raye nima ina raye saina sadaku
zan tsare lafiyarsa da ransa kamar yadda na tsare na mahaifinsa wannan shine kadai
gatan da zamu iya yiwa kanmu da wannan jariri
naki idan har muna son mu tsira da rayukanmu
sa adda sarkin yaki amzad yazo nan a zancensa sai shamilat ta sake
fashewa da kuka daga can sai ta matso daf da amzad ta shafa kan jaririn ta sumbaci goshinsa sannan kuma ta ciro wata laya dake wuyanta ta
Daurata a wuyan jaririn ta dubi amzad tace
ina da laya irin wannan sak don haka ka gayawa dana
cewar duk ranar da yaga mai irin wannan laya ba wata ba
ce face mahaifiyarsa
koda gama fadin hakan sai ta karbi jaririnta ta rungumeshi
a kirjinta ta sake fashewa da kuka al amarin da ya karyar da zuciyar sarkin yaki kenan ya ji ya kamu da tausayinta fiye da ko yaushe
sai da ta jima a kankame da jaririn sannan sarkin
yaki ya karbeshi ta tafi izuwa inda keken dokinta yake tana waigen jaririn nata
tana zubar da hawaye
Wow nIma Al amin Guyson na tayata haka dai taje ta zauna a kan keken dokin
ta sakarwa dawakan linzami suka zabura da gudu suka nausa da ita cikin
daji suka nufi wani bangare daban wanda bai shafi nahiyar ba gaba daya
a sannan ne shima sarkin yaki Amzad ya tafi da jaririn izuwa inda dokinsa yake ya kama ya hau ya nufi
hanyar da zata kai shi cikin madinatul hashwar
a lokacin da yake bacewa a cikin duhun daren
tun kafin sarkin yaki ya iso kofar shiga gari ya boye jaririn a bayansa tamkar baya dauke da komai kawai ya wuce gaba masu gadin kofar garin
ba tare da jaririn yayi kuka ba
ai kuwa yana isowa bakin kofar sai masu gadin suka tare shi saboda basu gane shiba
sakamakon yana sanye ne da bakaken kaya kuma basu ga sa adda ya fice daga cikin garin ba tare da dubun nan daakarunsa saboda ta wata barauniyar hanya suka fice
masu gadin na tare shi sai yayi sauri ya bude
fuskarsa don kada su bata masa lokaci koda suka dallare fuskarsa da madubi
sukaga shine sai suka yi sauri suka bude masa kofa ya shigo suna masu binsa da kallo cikin alamun tsananin mamaki domin su dai basu ga lokacin da ya fita daga cikin garin ba kuma tunda suka ganshi a cikin shiga ta
bakaken kaya lallai sun san cewa wani aiki ne na sirri yaje ya gabatar
amzad na shiga cikin gari bai zame ko ina ba sai gindin wata karuwa wacce ake kira kimaratu
a wannan lokaci dare ya fara nisawa kuma sawu ya dauke ba a jin sautin komai face haushin karnuka amzad ya kama buga kofar gidan da karfi
a fusace kimaratu tazo ta bude kofar tace wanene nan yake neman fasa mini kofar gida ka kama gabanka
ina da abokin kwana a ciki
koda jin haka sai amzad ya daka mata tsawa yace bude kofar na shigo nine
sarkin Yaki Amzad
jikin kimaratu na karkarwa tayi sauri ta bude kofar nan take amzad ya mika mata
jaririn sannan ya danka mata jakar
kudi
cike da dinare yace wannan kudine dinare dubu dari uku ki rike su ki reni wannan jariri har izuwa lokacin da na bukaceshi
idan wani abu ya tafa lafiyarsa a bakacin ranki
.
SHIN SARKI ZAMARU ZAI CIKA ALKAWARIN DAKE TSAKANINSA DA BOKA HIZAINU.??
.
YAUSHENE SHAMILAT ZATA SAKE GANIN DANTA???
.
ME ZAI FARU IDAN DAN SHAMILAT YA GIRMA ???
.
MU HADU A LITTAFI NA BIYU
DON JIN CI GABAN WANNAN LABARI
DAGA MARUBUCIN LITTAFIN
ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI KANO
WANDA NI AL AMIN AHMED MISAU
INKIYA GUYSON
NAYI TYPINGDINSHI
NAKE CEWA SAI MUN HADU A NA BIYUN
KISAN GILLA 2
Littafi na biyu
Na Abdulaziz sani madakin gini
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini

KISAN GILLA
Littafi Na Biyu (2)
Part A.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
Filine mai fadi wanda aka kewayeshi daragar karfe musamman sarki zamaru yasa aka shirya
wannan wuri domin baiwa kansa horon yaki
tsawon shekaru ashirin da daya kullum sai sarki
zamaru ya jarraba jarumtakarsa akan dakarunsa acikin wannan fili kuma yana yin yakine da mutum arba in shi kadai
yake ragargazarsu a cikin kankanin lokaci saboda jarumtakarsa
da iya yakinsa, mutum daya daga cikin arba in din baya tsira
da lafiyarsa wani lokacin ma idan tsautsayi ya ratsa wasunsu
na rasa rayuwarsu
banda sarkin yaki Amzad babu wani sadaukin daga cikin mayakan kasar wanda
sarki zamaru bai kaishi kasa ba shima din don
basu taba kafsa wa bane
yauma kamar kullum sarki zamaru ya tunkaro wannan filin jarumta a cikin gagarumar
shigar yaki yana rike da wata zabgegiyar takobi gami da wata garkuwa irin ta
gidan sarauta mai tambarin karagar mulkin birnin
madinatul hashwar bisa mamaki sai sarki zamaru ya hango
filin yakin wayam babu ko badakaren guda
cikin tsananin mamaki da fishi sarki zamaru ya buda baki ya kwallawa wani
hadimin kira mai suna zabbaru nan da nan saiga zabbaru ya rugo har yana sassarfa
don biyayya da isowarsa gaban sarki zamaru sai ya zube kasa
bisa gwiwoyinsa cikin biyayya sarki ya dubesu
da kakkauran murya yace menene
dalilin da yasa yau sarkin yaki bai turo da dakaru arba in wadanda zan yi yaki dasu ba?
Zabbaru ya risina cikin biyayya kansa na sunkuye a kasa yace ya shugabana ai amzad ya zo da dakaru arba in
kamar kullum amma sai gimbiya ta sallameshi tace
itace zata fuskance ka
cikin tsananin kaduwa da mamaki sarki zamaru yace wannan wace irin maganar banzace
kake mini haka ?
Tayaya gimbiya zatace zata tareni da yaki alhalin
bata taba rike takobiba a rayuwarta kafin sarki zamaru ya gama rufe bakinsa sai ya jiyo
sukuwar doki a bayansa koda ya waiga sai yayi arba
da yarsa gimbiya Musaira bisa wani farin ingarman doki tayo shigar yaki na bakin sulke bata
rufe fuskarta ba da hular karfe kuma ta tattare gashin
kanta ta daure ya zubo har kasan kwankwasonta
duk inda ake neman mace mai kyau da sura gimbiya musaira ta kai ta wuce misali
sai abinda ido suka gani
kafin sarki zamaru ya ankara tuni musaira ta dako
tsalle a sama tana mai barin kan dokin kawai sai ta zare takobinta ta
kawo masa wawan sara a wuya saboda karfin saran sai da sarki zamaru ya durkushe kasa a lokacin da yayi wuf ya kare harin da
takobinsa musaira na dira a kasa bisa kafafunta
sai taci gaba da kaiwa sarki zamaru sara da suka cikin zafin nama juriya da bajinta nan fa suka kacame da azababben
yaki
tamkar tsofaffin abokan gaba, sai da suka shafe kusan
dakika dari da arba in suna bakin gumurzu dayansu bai samu nasarar kowa
lakutar jikin daya ba
Al amarin da ya matukar fusata sarki zamaru kenan
kawai saiya shammaci gimbiya musaira ya sauya salon yaki ya fyalli kafarta tayi katantanwa a sama sannan ya
doki kirjinta da kafarsa guda ta fado kasa a matukar galabaice ta mike zaune da
kyar ta tofar da yawun jini
kawai sai sarki zamaru ya kyalkyale da dariya sannan ya mikawa gimbia musaira
hannunsa ta kama ya tashe ta tsaye ya dubeta yace yaushe ne sarkin yaki amzad ya baki horon yaki haka bansani ba
a tunanina ko rike takobi baki iya ba menene dalilin
da yasa kika bata lokacinki kika koyi yaki haka kuma me yasa
kika boye mini
koyon yakin naki sa adda gimbiya musaira taji wadannan tambayoyi sai tayi murmushi
a lokacin da tasa tafin hannunta ta share dan jinin
dake kan lebanta tace yakai abbana na sani cewa zaka iya kare rayuwata da lafiyata a ko da yaushe to amma ranar da babu kaifa waye zai
kareni
a matsayina na yarka guda daya jal a wannan duniya
mai shirin gadon karagar mulkinka wata rana ya kamata ace na zama
jaruma kamarka
tun ina karama na gane cewa nasha jarumtaka a nonon uwata kuma na gajeta
a cikin jininka, don me bazan koyi yaki ba in zama
cikakkiyar jaruma
ka sani cewa wannan duniya cike take da masoya da makiya
ba mamakima a cikin

4 Comments On KISAN GILLA
avatar
daiy

2 years ago

Reply

Good

avatar
ibrahim-9-5

1 year ago

Reply

Nice thanks a lot

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to ibrahim-9-5

Aha thanks for feedback keep following our site and enjoying our new hot hausa novels

avatar
kabir-mariya

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment