Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga kan tsuntsun ya dubi nasmirat yace
maza ki hau wannan tsuntsun nawa zai kaiki
maboyata inda zaki samu nutsuwa da kwanciyar hankali lallai idan muka
gama wannan yakin zamu riskeki a can kidi duk
abinda ya faru ba tare da wata gardama ba kuwa sai
gimbiya nasmirat ta haye kan wannan tsuntsun ya tashi
da ita sama yana mai juyawa da baya, A dai dai
wannan lokacin ne gimbiya nasmirat ta juyo ta hada
idanu da mahaifinta sarki zamaru taga fuskarsa a murtuke take babu ko annuri koda yaga
wannan tsuntsun zai tafi da ita sai ya kwalla mata kira yace
mata, kawai sai gimbiya nasmirat ta kauda kai da
fuskarta ga barin kallonsa a lokacin da hawaye ya sake
subuto mata a karo na biyu nan da nan tsuntsun ya
luluka da ita cikin sararin gajimare ya bace bat tamkar
bai taba wanzuwa ba a wajen, faruwar hakan ke da
wuya sai sarki zamaru ya zare takobinsa guda biyu yana mai saukowa kasa
daga kan dokinsa ya tunkari yarima da lasmin gadan
gadan
boka hizainu da sarkin yaki amzad kuwa sai suka taho ga juna
kowannansu fuskarsa na yin gatsine saboda tsananin
fishi gami da kiyayyar juna koda ya rage sauran baifi
taku shida ba su hadu sai boka hizainu ya rikide
ya zama wata shirgegiyar kada mai tsawo da
kaurin gaske
a iya yawon duniyar amzad bai taba ganin kada mai
girman taba
koda ganin haka sai shima amzad ya rikide ya zama wata
narkekiyar macijiya wacce kaurinta da tsawon ta
ya ninka na kadar sau uku
koda ganin haka sai nima Al amin da nake typing na
rikide na zama zaki domin cigaba da ganin wannan
gumurzu
Ai kuwa sai kadan ya nufi cikin wannan korama
itama sai tabi kadan suna haduwa a cikin koramar suka
kacame da masifaffen fada
Al amarin yarima da lasmin kuwa koda suka ga sarki
zamaru ya zare takobinsa guda biyu ya durfafo su
sai suma suka zare na su takubban suka tsaya cak
a inda suke suna jiran karasowarsa a nan ne yarima ya dubi lasmin yace
ranki ya dade kiyi amfani da duk irin salon yakin da
kikaga ina yi domin ta haka ne kadai za mu iya kare
kanmu daga sharrin wannan tsohon makiyin namu
lasmin tace
idan kuma shi yazdo da wani salon wanda yafi
namu yarima yace
ai duk irin salon da yazo mana dashi muma shi zamuyi
kinsan na samu horo a wajen sarkin yaki kuma babu
salon da ban iya ba
lasmin ta danyi guntun murmushi tace masa, ashe malamin mu
daya ne domin nima a wajen sarkin yaki amzad na samu
horona
ina dai haka ne bamu da matsala amma fa ka sani
wannan mutumin ba karamin annoba bane a tare
da mu
kuma shirinsa ya wuce duk yadda muke zato kawai
dai muyi iya yinmu wajen ganin mun gama dashi
kafin yarima ya budi baki ya kara magana sai kawai suka
hango sarki zamaru a sama kamar an harboshi
kafin suyi wani abu ya daki kirajensu da kafafunsa
guda biyu saboda karfin dukan sai da kowannansu yayi
sama suka yi baya suka fado kasa tim bisa gadon
bayansu sai gashi ko wannansu ya furzar da jini daga
cikin bakinsa
A WANNAN LOKACI TUNI SARKI zamaru ya dira a kasa bisa kafafunsa biyu
yana mai kura musu idanu kawai sai sarki zamaru ya
bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma ya turbune
fuskarsa yace
yanzu a haka ne kuke tunanin zaku iya samun galaba
a kaina? Na rantse da darajar karagata ko shi
malamin naku ne ya kusance ni sai dai a dauki
buzunsa domin shirina yafi nasa ni murucin kan dutse ne
wanda ban fito ba sai dana shirya babu wani makiyana
wanda banyi tanadin ganin bayan sa ba, Yanzu take
anan zan yi muku kisan gilla irin wanda ba'a taba yiwa
wani ba a wannan nahiyar tamu koda jin wannan batu sai
lasmin da yarima suka dubi junansu kawai sai suka yi
wata irin tasowa sama daga tsaye kamar an saki majajjawa
kafin sarki zamaru ya sake yin wani yunkuri
sun dako tsalle sama zuwa kasa ai kuwa sai yarima
ya daki fuskar shi da kafarsa ita kuma lasmin ta daki
kirjinsa
Al amin Ahmed Misau, da kafafunta guda biyu
saboda karfin dukan sai da sarki zamaru yayi baya
kamar an janye shi da majajjawa, bayan shi ya gwaru
da jikin wata bishiya ya fado kasa a galabaice yana mai tofar
da gudan jini daga bakinsa amman hakan bai saka ya yadda takubban da suke
hannunsa ba
kawai sai ya mike tsaye zumbur kamar babu abinda
ya same shi yana mai gyara tsayuwarsa, da ganin
haka sai suma suka rugo izuwa kansa aka kacame da
sabon azababben yaki ya zamana cewar suna kai masa
sara da suka cikin tsananin zafin nama shima yana maida
martanin sai dai kaji karar haduwar takubbansu
tamkar ana dukan karafa a makera, Al amin Misau wani lokacin har tartsatsin
wuta ke tashi gami da hayaki sakamakon
gogaiyar takubban uku
babu abain da zai baiwa mutum tsoro a cikin wannan
yakin face yadda jaruman uku suke yaki da matukar
zafin nama kuma da dukkan karfinsu cikin burin
Gaggauta ganin bayan junansu, kai da ganin yanayin
gumurzun kasan cewar duk wanda yayi kuskure kadan daga cikinsu tasa ta kare
kamar yadda ake yin wannan mummunan artabu
a tsakanin su sarki zamaru dasu yarima, haka ake yinsa
tsakanin amzad da boka hizainu a cikin wannan korama, duk
sa'ar da wannan kadar ta samu sa'ar laftar
jikin wannan macijiyar da bakinta idan ta gatsa da hakoranta
sai taji kamar karfe ta gatsa ko alamar kwarzane babu
haka itama katuwar macijiyar idan ta samu nasarar
fara hadiye kadan sai taji kamar wuta take hadiya don
haka ba shiri take amayar da ita, Al amin Ahmed Misau,
idan kuma maciyar ta samu nasarar kanannade
jikin kadan da nufin ta matse shi ta karairaya dukkanin
kasusuwan jikinsa sai taji ta kasa domin ji take kamar
dutsen lu'u lu'u take matsewa
wohoho tabbas masu iya magana sunyi gaskiya da
sukace
bala'i ba a sa masa rana kuma duk mai rabon shan duka sai
ya shata
sai da wannan kada da macijiya suka shafe sama da sa'a uku suna kokawa da
birgima gami da cizon junansu a cikin wannan korama
wani lokacin ma idan suka rukunkume jikin juna sai kaga sun nutse izuwa kasan
koramar sun sake tasowa sama suna hargitsa ruwan
koramar
gaba dayansu tamkar zasu karar dashi, wuya mai saka
dole kanwar naki
lokacin da macijiyar da kadan sukaji sun galabaita
ainun domin sun sha ruwa sun gaji kuma jiki ya
jigata sai suka saki junansu ba shiri suka fado daga cikin
koramar kowannansu ya koma gefe daya a sannan ne kuma
kowanne ya rikida zuwa ainihin halittar sa ta bil'adama
gashi dukkan su suna haki kamar ransu zai fita ko
mikewa tsaye basa iya yi a haka suka tsaya suna kallon kallon juna kamar zasu cinye
kansu har izuwa kimanin dakika dari da sittin sannan suka mike tsaye atare suna yin
murmushin mugunta...KISAN GILLA
Littafi Na Hudu (4)
Part B.
.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
SANNAN SUKA MIKE TSAYE A TARE SUNA MASU YIN
MURMUSHIN MUGUNTA
boka hizainu ya dubi sarkin yaki Amzad yace
tabbas ka samu babban shiri , gumurzun da muke yi
yanzu ya tabbatar min da cewar ba zamu iya hallaka
junan mu da karfin sihirin tsafi, don haka yanzu lokaci
yayi da za mu jarraba juna da karfin damtse, daman kai
kadai ne jarumin da ban taba yin gumurzu da shi ba gaba
daya a wannan nahiyar tamu daga cikin fitattun
jaruman da suka yi shuhura sa ar da boka hizinu yazo nan
a jawabinsa sai sarkin yaki amzad ya kamu da mamaki kuma
ya dubeshi cikin alamun rashin yadda yace
yaushe ne ka fafata da gaba daya fitattun jaruman wannan
nahiyar tamu ? Koda jin wannan batu sai boka hizainu ya
bushe da dariyar mugunta sannan yace,
ashe ka manta da jarumi mai bakar hular karfe kenan
wanda ya hanaka amsar kambun gasar jarumta shekaru bakwai da suka gabata a can birnin
shamshal ?
Koda jin wannan tambayar sai mamaki ya kara turnuke sarkin yaki amzad yana mai
nuna hizainu da dan yatsansa cikin alamun kaduwa yace
daman kaine wannan jarumin mai bakar hular karfe wanda
har aka gama gasar babu wanda yaga fuskarshi, boka hizainu
ya gyada kai yace
tabbas nine wannan jarumin kuma ka sani cewar ragas
muka yi ni da kai a wannan gasar babu wanda ya
tafi da wannan kambu abinda nake nufi bamuyi yaki
gaba da gaba ba shine bamuyi yaki ido na kallon ido ba
sai yanzu za muyi , lallai yau ne zamu fidda raini
a tsakanin mu gama fadin haka keda wuya sai boka hizainu
ya mike tsaye yana mai zare takobinsa kuma ya
buda hannayansa yana mai kallon sarkin yaki Amzad
yace
maza ka mike mu fafata ba tare da wata gardama ba sai
sarkin yaki amzad ya mike tsaye shima ya zare tasa
takobin yana mai gyara tsayuwarsa sannan ya dubi
boka hizainu yace
tabbas ka burgeni daya zamana cewar baka fito ba sai
daka shirya ai ba a samun duniya a banza sai dai kash !
Baka kama turba mai kyau ba domin shi zalunci baya
daurewa ka tambayi masana tun daga farkon wannan duniyar kawo yanzu babu wani
azzalumin sarki ko boka ko kuma jarumin da dauwama a doron
kasa sai dai kawai yaci zamaninsa ya shude kamar
bai taba wanzuwa ba, Al amin Ahmed Misau Guyson,
amzad na gama fadin hakan sai ya afkawa boka hizainu suka
kacame da sabon masifaffen yaki
wohoho !
Idan tsohon hannu ya hadu da takwaransa dolene aga
tuggu, wayo gamai da makircin yaki kuma dolene aga
kwarewa jajurcewa da sanin dabarun salon yaki kala uku
ma ana sai gashi suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama gami da naushi da bugu
hannu da kafa da kuma yin tsalle
tsalle suna yin alkafira suna shallake juna tamkar sun kasance tsuntsaye masu fuka fukai
inda ace akwai yan kallo lokacin da ake yin wannan bakin
gumurzun to da ihunsu da shewarsu ne zai cika dajin gaba daya domin basu taba ganin
jarumta da jarumtaka irin
wannan ba
bugu da kari duk wanda ya tsaya yana kallon wannan
fafatawa to ba zai taba samun nutsuwa da kwanciyar
hankali ba saboda bala in dake faruwa a wajen zai iya
samunsa kuma ya sami duk wata halitta mai rai dake wajen
kamar yadda ake wannan yakin a bangaren sarkin yaki
amzad da boka hizainu haka abin ya kasance a
bangaren sarki zamaru dasu yarima amman koda aka
shafe awa guda ana gumurzu sai labari yasha banban
komai ya sauya, ba komai ne ya haddasa haka ba face
alamar gajiya a jikinsu amma shi sarki zamaru sai ya zamana
sannan ne ma yake jin sabon karfi a jikinsa, hakan ne ya tabbatar
musu da cewar ya fisu samun horo a jikinsa na jarumta da kuma juriya da dadewa ana
gumurzu
Al amarin daya matukar dugunzuma hankalin yarima
kenan domin ya tabbatar idan har aka ci gaba da wannan
gumurzun a haka har tsawon wata rabin Sa'ar to koda bai
samu nasara akan su ba to zai yi musu babbar illah.
Nan fa yarima ya soma tunanin dabarar da ya kamata
suyi dan ceto kansu da kuma samun nasara akan
makiyinsu
yana cikin wannan tunanin ne sarki zamaru ya
shammacesu yayi wata irin katantanwa a tsakiyarsu
tamkar an murza mazari, ai kuwa sai yayi nasarar yankan
lasmin a cinyarta kuma ya yanki yarima a kafadarsa
ta hadu duka su biyun sai suka kwala ihu sakamakon
zafi da zogin da suka ji a lokacin da jini yayi feshi
daga cikin jikinsu
koda sarki zamaru yaga ya samu wannan nasarar
sai ya kara yunkurawa cikin zafin nama da shammace
ya kawowa yarima suka da takobi a ciki, ita kuma
lasmin ya kai mata sukar a gadon bayanta, koda lasmin
taga takobin zata soke yarima sai ta yunkura da dukkan
karfinta tasha gaban yarima ai kuwa sai tsinin
takobin ya soketa a saman kafadarta ta baya daya takobin kuma ta soketa
a gadon bayanta ya zamana kenan ta kubutar
da rayuwar yarima, kawai sai ta durkusa kasa cikin
mugun yanayi mai kama da suma, ganin yanayin
data shiga ne ya saka yarima ya kurma uban ihu
mai firgitarwa ya daka tsalle sama ya doki kirjin
sarki zamaru da kafafunsa biyu saboda karfin dukan
sai da sarki zamaru yayi tsalle sama da baya tamkar
an janye shi da kugiya ya fadi can gefe daya, Al amin
Ahmed
Misau sunana kenan, nake typing, kafin ya mike tsaye
sai yaga wata guguwa ta lullube yarima da lasmin
tayi sama dasu sun luluka, kafin kiftawar ido sun bace
bat, koda sarki zamaru ya juya ya duba wajen da ake
gumurzu tsakanin boka hizainu da Amzad sai yaga
babu sarkin yaki sai boka hizainu yana ta tsafe tsafensa
don yaga inda Amzad yake amma abu ya gagara, koda
ganin haka sai sarki zamaru ya takarkare ya kurma
uban ihu cikin tsananin bakin ciki.
Wannan shine abinda ya faru tsakanin su
sarkin yaki Amzad da kuma sarki zamaru a lokacin
da suka kawo musu farmaki na farko a cikin farautar
da suke yi musu
++ ++ ++ ++ +++
AL AMARIN GIMBIYA Musaira kuwa lokacin da ta hau
wannan tsuntsun na sarkin yaki Amzad ya tashi da ita
sama ya luluka a cikin gajimare sai yayi ta tsala gudu da
ita, suka yi ta keta gajimare ba sassauci har tsawon
kimanin rabin sa'a kawai sai gani tayi sun iso wani
babban daji mai tarin ni'ima , akwai bishiyoyi kala kala gami da tarin 'ya 'yan itatuwa
naci iri iri koramai kuwa da koguna ga sunan birjik gami da manyan duwatsu da
tsaunuka
Kwatsam sai Musaira ta hango wani babban gida
ginin dutse da dutse a tsakiyar dajin shi dai wannan gidan
anyi masa gini na kawa wanda komai isar mai mulki
ko attajiri sai an burgeshi, kai tsaye tsuntsun ya
tunkari kofar wannan gidan ya dirgo kasa ya sauka
bisa turba da farko sai musaira ta firgita bisa ganin
wannan katon gwaggwan biri kikam a kofar gidan,
tunda tazo duniya bata taba ganin gwaggwan biri mai
girman wannan ba domin tsawon shi yakai kamu talatin
da uku kuma fadin kirjinsa yakai kamu shida, can sai ta
tuna ai sarkin yaki Amzad ne ya saka aka kawota wannan
gidan dan haka sai taji hankalinta ya kwanta ta cire dukkan tsoro daga cikin
zuciyarta, ba tare da wata fargaba ba sai musaira ta
yunkura domin ta sauko kasa daga kan tsuntsun da take
zaune amman sai ta kasa saboda nisan kasa daga kan
tsuntsun idan tace zata dirko zata iya karyewa ko kuma
ta samu targade, bisa ga mamaki sai taga wannan
katon gwaggwan birin ya tunkarota, da zuwan shi gaban wannan tsuntsu
sai ya mika hannunshi biyu ya kamo kafadun musaira ya daukota cak ya sauketa kasa
a hankali sannan ya wuce gaba izuwa cikin wannan
gidan tana biye dashi.
Gidan yana da zurfi sosai kuma Al amin Ahmed Misau
saida suka keta ta cikin fadoji biyar sannan suka iso
wani babban falo wanda ya kawatu ainun
duk irin kawar da ake shirya a gidan sarautar sarki
zamaru sai gashi ta zama yar kauye a cikin wannan gidan domin kawar ta
nunka ta gidansu sai uku nan take musaira tayi arba da
abinda yayi tsananin kadata ba kowa ta gani ba face
Kimaratu
tana tsaye a wajen wani faffadan teburi wanda ke cike
da kwanukan abinci kala kala kamshin abincin ya
cika falon gaba daya da isowar gwagwan birin tare
da gimbiya musaira sai birin ya risina ga kimaratu
sannan ya juya ya tafi ya barsu su biyu kacal a tsaye, kimaratu
ta risina ga musaira cikin biyayya ta kwashi gaisuwa
sannan tace
barka da zuwa ya shugabata ga kujera ki zauna ki
fara cin abinci kafin su sarkin yaki su dawo sa ar da taji
wannan batun sai ta dubi kimaratu
cikin tsananin mamaki tace mata, ya akayi kika tabbatar
da cewar zasu dawo nan a raye ? Ni kaina ban dauka
zan zo nan wajen a raye ba, kuma yanzu babu wanda
yasan halin da suke ciki tund asarki zamaru da boka
hizainu sun tare su koda jin wannan batun sai kimaratu ta bushe da dariya
al amarin daya kara baiwa musaira mamaki kenan,
maimakon ta kara bata amsa sai ta kama hannun
gimbiya musaira ta jata izuwa kan kujera ta zaunar da ita
ta zuba mata abinci tace mata, ya shugabata ki soma
cin abinci domin ki samu nutsuwa sannan sai muyi
hira cikin kwanciyar hankali ba tare da wata gardama
ba sai gimbiya musaira ta fara cin abinci itama
kimaratu sai ta zauna ta zubawa kanta abinci ta fara ci
tsawon yan dakiku suna cin abincin dayansu baice
uffan ba
daga can sai gimbiya musaira ta ajiye cokalin ta daina cin
abinci koda kimaratu taga haka sai ta ajiye nata
cokalin ta dubeta tace mata, shugabata tunanin me kike yi ne ? Musaira ta girgiza
kai tace.
Nayi babban kuskure dana baro su yarima a wancan dajin
kamata ya yi na tsaya ayi komai a kan idanuna koda jin
wannan batu sai mamaki ya turnuke kimaratu tace
kekuwa menene dalilin daya sa kika ce kinyi kuskure da
kika baro su yarima a can dajin musaira tace
Akwai abinda nake zargi nake son na tabbatar dashi,
kiyi hakuri ba zan iya sanar dake wannan al amarin ba,
amman idan lokacin daya dace ki sani ya yi zaki sani
koda jin wannan batu sai kimaratu ta kasa gane abinda musaira ke nufi don haka
sai ta sake bude baki da nufin tayi mata wata tambayar
amman sai musaira ta tari numfashinta da cewar
wai shin idan banda biri babu kowa a cikin wannan katon
gidan ?
Kimaratu tace
A'a akwai hadimai, amman ba a ganinsu sai idan lokacin
yin aikinsu yayi
da zarar sun gama za a neme su a rasa, shi kuma wannan birin
duk da rana da dare yana nan baya gusawa ko ina saboda shine mai gadi,
musaira tayi Ajiyar zuciya tace,,,,
Nidai hankalina bai kwanta
da zaman mu Anan ba saboda na fahimci shirin mahaifina dana boka
hizainu ya wuce tunanin sarkin yaki Amzad domin kuwa zasu iya kawo mana hari har nan din a ko yaushe, ke ni yanzu ma zuciyata bugawa take yi
da karfi saboda tsoron abinda ka iya faruwa ga su
yarima , kafin musaira ta gama rufe bakinta sai sukaji
an turo kofar falon
cikin kaduwa da firgici suka waiga domin suga ko
su waye suka turo wannan kofar..KISAN GILLA
Littafi Na Hudu (4)
Part C.
.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
CIKIN KADUWA DA FIRGICI SUKA WAIGA SAI SUKA GA ASHE
SARKIN YAKI AMZAD NE SUKE SHIGOWA, cikin matukar farin ciki musaira da kimaratu suka
mike zumbur suka ruga zuwa garesu, suka tarye su amman koda suka hango yarima a can baya goye da
gimbiya lasmin ga rauni a kafadarta kuma tana cikin wani irin mugun hali mai
kama da suma sai hankalinsu ya dugunzuma cikin
hanzari amzad ya kai yarima cikin wani dakin barci aka
kwantar da lasmin bisa wani shamfidadden
gado na Alfarma.
Take Amzad ya tafa hannun sa sai ga wata budurwa
Aljana yace Dunaila maza ki ceto rayuwar gimbiya ki
sani cewar sarki zamaru ne ya soketa da takobinsa
a kafada da gadon bayanta koda jin haka sai Dunaila
ta dubi raunikan da sauri sannan ta girgiza kai cikin alamun
damuwa tace
hakika rayuwar lasmin na cikin mugun hatsari, zan iya
yi mata magani ta samu sauki na tsawon kwanaki bakwai
kacal amman ciwon zai kuma dawowa ya zama ajalinta
farat daya koda jin wannan batun sai hankalin kowa ya
dugunzuma har dani kaina Al amin Misau
Amzad ya kama kafadun Dunaila ya girgiza kuma ya dubeta
cikin daga murya yace duk yadda za ayi ki ceto rayuwarta
in banda haka ina amfanin ki na uwar likitocin aljanu, ki
tuna fa ke yar gado ce, kakan kakanki ma har ya bar duniya ba a sami kamarsa
ba cikin likitocin aljanu, Dunaila ta gyada kai gami da ajiyar
numfashi sannan tace
duk abinda ka fada gaskiya ne hanya daya za a bi
idan ana son ceto rauuwar lasmin dole a tsoma wadan
nan takubban guda biyu wadan da sarki zamaru ya
soketa da su a cikin ruwan tsumin tsafinsa a debo tsumin a
baiwa lasmin tasha,
wannan shine kadai makarin wannan dafin dake
jikin takobin, wanda a halin yanzu dafin ya shiga cikin
jinin jikinta koda Aljana Dunaila ta zo nan a jawabinta sai
hankalin kowa ya sake dugunzuma musamman hankalin bawa udez domin komawa
yayi gefe daya ya zauna ya fara kuka
nan fa aka yi jugun jugun ana tunani da nazarin
al amarin har izuwa tsawon yan dakiku dayansu baice
uffan ba, zuwa can dunaila ta dubi yarima tace masa, ya aka yi
sarki zamaru ya soki lasmin da takubba biyu a
lokaci guda alhalin kana tayata yakarsa ?
Yarima yace
ai a lokacin ni yake so ya kashe shine tasha gabana
don ceton rayuwata, koda jin haka sai musaira tace
akan wane dalili lasmin zata sallama rayuwarta don ceton taka rayuwar alhalin
bata kasance yar uwarka ba, hasali ma yau kwanaki kadan
da haduwarku da juna?
Koda jin wannan batun sai kowa ya kurawa musaira
idanu nan take taji kunya ta kamata, don haka sai ta
sunkuyar da kanta kasa bata kara cewa komai ba, nan take
Dunaila ta hada wasu Al amin Ahmed Misau, magunguna
aka durawa lasmin a baki tasha kuma aka shafa mata
shi akan raunikan biyu gama haka ke da wuya sai ta
dawo cikin hayyacinta har ta iya buda idanunta, koda
ta hada ido da yarima sai ta kama murmushin farin ciki,
ita kuwa gimbiya musaira sai taji kishi ya turnuke ta
amma sai ta dake bata nuna kishin nata ba, dunaila ta
dubi sarkin yaki Amzad tace
to ni zan tafi amma ku tabbatar da cewar kunje kun
sato wadan nan takubban biyu dake hannun sarki
zamaru kunje kun tsomasu a cikin wannan ruwan na
tsumin tsafinsa kun debe shi kun baiwa lasmin tasha
kafin cikar kwanaki bakwai masu zuwa don kashe
dafin dake cikin jikinta, nasan kuna tunanin yadda zaku
iya samun wannan nasara, zan baku shawara guda biyu
ku nemi mutum biyu wadan da suka san sirrin gidan
sarautar tsawon shekaru, daya daga cikinsu ya kasance
jinin gidan ne, dayan kuma ya kasance babban hadimi
ne na gidan da wannan furucin nake muku sallama
sai an kawo wannan tsumin za a sake nemana ya
shugabana Aljana Dunaila tana gama fadin haka ta bace
bat Tamkar bata taba wanzuwa a wajen ba,
Amzad yayi shiru yana kallon kowa a wajen daya bayan
daya koda yazo kan bawa udez sai yaga jikinsa na tsuma kuma idanunsa sun
zazzaro, alamun tsananin tsoro sun bayyana karara a
tare dashi koda ganin haka sai sarkin yaki yazo gaban
shi ya durkusa kuma ya dube shi a cikin nutsuwa yace
duk yadda zanyi na tserar da lafiyarka da rayuwarka
sai nayi, yanzu dai ku biyu ne rak zaku iya taimakawa lasmin
a ceto rayuwarta, da kai da mahaifiyar yarima ne kadai kuka san sirrin gidan sarautar
sarki zamaru fiye da kowa
kunsan a inda sarki zamaru yake ajiye tsumin tsafinsa kuma kunsan masu kula da tsumin
da kuma lokacin da za a iya fakar numfashin shi a debo tsumin
ni kuma zan yi kokarin sato takubban guda biyu
kunga kenan nawa aikin shine farko sannan naku, sa armu daya babu yadda za ayi
boka hizainu da sarki zamaru su taba gano nan
inda muke yanzu bare har su kawo mana hari
Al amin Misau amman akwai dokokin da zaku kiyaye
idan har kuna son mu kare kanmu, yanzu aikin dake gabana dole ne na kera takubba
da suke iri daya sak dana sarki zamaru lokacin
da sarkin yaki Amzad ya zo nan a maganarsa sai
gimbiya musaira ta turbune fuskarta tace
to waishin duk dan mu ceto rayuwar lasmin zamu jefa
rayuwarmu cikin hatsari, kai zaka tafi sato takubban
sarki zamaru wanda a dalilin haka su sarki zamaru zasu iya tarbarka su cutar dakai
mahaifiyar yarima
Da bawa udez kuma zasu sayar da rayuwarsu
su tafi izuwa can gidan sarautar sarki zamaru don
debo wannan tsumin tsafi alhalin sarki zamari yana neman su
ya kashe su,
ai wannan ma ganganci ne domin za a salwantar da rayuwar
uku kenan saboda guda daya. Koda jin haka sai ran yarima ya baci bai san sa adda ya dakawa gimbiya musaira tsawa
ba yace
'shin ke baki ga yadda lasmin ta saida rayuwarta bane
domin ceto rayuwata ? Ko godiya baki yi mata ba a
matsayinki na yar uwata kafin yarima ya gama rufe bakinsa sai idanunsa
suka kama lumshewa a lokacin da jiri ya debeshi, sai gani suka yi ya
yanke jiki ya fadi kasa
gaba dayan su suka ruga izuwa kansa a dimauce, cikin sauri sarkin yaki amzad ya duba jikinsa sannan yayi masa magani
aka dauke shi aka shigar dashi cikin wani daki mai kyau aka kwantar dashi a sannan ne sarkin yaki ya tura aka dauko shamilat mahaifiyar
yarima daga can wani bangare na daban da aka kwantar da yarima
koda shamilat taga danta a kwance cikin mawuyacin
hali sai hankalinta ya
dugunzuma ta fara kuka, koda ganin haka sai sarkin yaki amzad ya dubeta cikin
murmushi yace
kwantar da hankalin ki ya shugabata danki zai warke sumul irin halin da lasmin ta
shiga shine ya same shi, ma ana dafin takobin
sarki zamaru ne a jikinsa saboda ya yankeshi da takobin
gama fadin haka ke da wuya sai sarkin yaki amzad ya
dauko wannan maganin da aljana Dunaila ta hadawa lasmin
ya baiwa yarima yasha kuma ya shafa masa akan ciwukan da aka yi masa sannan ya dube
shi yace masa
yanzu kaima zaka tsira daga sharrin wannan dafin iya
tsawon kwana bakwai don haka kai da mahaifiyarka sai ku
tayamu da addu ar Allah ya bamu sa ar
samo wadan nan takubban na sarki zamaru gama fadin haka ke da wuya sai
sarkin yaki Amzad ya dubi gimbiya musaira yace
zo muje mu tattauna domin ni dake ne zamuyi wannan
aiki na sato takubban sarki zamaru in babu ke ba
zamu samu nasara banan take sarkin yaki amzad ya juya ya fice daga cikin dakin
ita kuwa musaira sai ta bishi da sauri tana waigen yarima dake kwance tana mamakin
yadda za ace wai in babu ita ba za a iya sato takubban
sarki zamaru ba
sai da suka yi yar doguwar tafiya a cikin gidan suka iso
wata katuwar fada ta musamman suna isowa daf da kofar
shiga fadar sai musaira taga wadansu kyawawan kuyangi na aljanu guda biyu a
tsaye
nan

4 Comments On KISAN GILLA
avatar
daiy

2 years ago

Reply

Good

avatar
ibrahim-9-5

1 year ago

Reply

Nice thanks a lot

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to ibrahim-9-5

Aha thanks for feedback keep following our site and enjoying our new hot hausa novels

avatar
kabir-mariya

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment