Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take kuyangin suka risina ga sarkin yaki amzad suka
kwashi gaisuwa sannan suka bude musu kofa suka shige
suna shiga fadar sai musaira ta zama cikakkiyar yar kauye ta kama kalle kalle
saboda kawar dake cikin wannan fadar ya ninka na can
inda suka baro sau goma me yasa sarkin yaki Amzad
ya zauna yana yin bauta a gidan mu tsawon shekaru
alhalin yana da irin wannan daula a gidan duniya?
Al amin Ahmed Misau tambayar da musaira tayi wa
kanta a cikin zuciya kenan kuma ta kasa baiwa kanta amsa
kai tsaye sarkin yaki amzad yaja gimbiya musaira izuwa
kan wadansu kujeru na alfarma wadan da aka yi su da farin lu'u lu'u suka zauna, zamansu ke da wuya sai taga fadar
ta cika makil da hadiman aljanu sama da su dubu, dukanninsu sai suka zube kasa gaban amzad suka kwashi gaisuwa
sannan ko wannen su ya samu kujera ya zauna wajen yayi tsit tamkar mutuwa ta gifta
a wannan lokacin ne sarkin yaki amzad ya dubi wadan nan hadiman aljanun gaba dayansu cikin nutsuwa yace
yaku dirkokin wannan gida nawa kuyi sani cewar ban taraku
anan ba domin komai ba sai domin sanar daku cewar
zan tafi aiwatar da wani babban aiki mai mugun hatsari
domin dauko takubban sarki zamaru, ina son
ku sake tsaurara tsaro a gidan nan fiye da koyaushe domin
idan kuka bari wata halitta guda daya ta samu nasarar
shigowa gidan bayan bana nan ko a lokacin dana dawo to a
lokacin ayyukan ku koda jin haka sai gaba daya hadiman
suka sunkuyar da kansu
kasa
shugaban su ne ya dago kai ya dubi sarkin yaki amzad cikin ladabi da nutsuwa tace
ya shugabana kamar yanda muka yi tsaro wannan gida tun
zamanin iyayenka da kakanninka haka zamu ci gaba da
tsaron shi har izuwa zuri'arka ta karshe, dan haka ka kwantar
da hankalinka ka tafi izuwa aikinka zamu tafiyar da komai bisa ka'ida alkawari da amana, koda jin wannan batun sai farin ciki ya lullube sarkin yaki amzad nan take ya daga
hannunshi na dama zuwa sama yana baiwa hadiman
inkiya
ai kuwa sai suka bace bat daga cikin fadar kamar basu
taba wanzuwa ba a wajen
faruwar hakan keda wuya sai sarkin yaki amzad yayi ajiyar numfashii sannan ya dubi
musaira yace
ya shugabata ki gafarce ni bisa sanyaki a cikin
wannan aiki na sato takubban mahaifinki dalili kuwa
babu wanda zai iya taba takubban face ya kasance jinin
sarautar gidanku, asalin wadan nan takubban gado ne tun daga sarkin farko na birninku
kuma an sihirce su da jinin zuri arku duk wanda bai kasance zuri arku ba
indai ya taba wadannan takubban ko kuma suka sareshi ko suka yanki
jikinsa sai dafinsu ya zama sanadin ajalinsa,
Don haka ni kaina ban isa na taba wadannan takubban ba kcece
kadai zaki iya dauko
su a lokacin da muka sami damar satosu, lokacin da
sarkin yaki amzad ya zo nan a jawabinsa sai gimbiya
musaira ta firgita ainun tace
kai
Sarkin yaki amzad yanzu ta yaya zamu iya sato wadannan
takubban alhalin ko yaushe suna jikin mahaifina kuma kome kake takama dashi na sihiri
ba zai iya tasiri akansa ba tunda yana tare da boka hizainu
sa dda amzad yaji wannan batu sai ya gyada kai yace
tabbas duk abinda kika fada gaskiya ne amman kinsan suma babu abinda zasu
iya yi mana na cutarwa kuma ki sani shi yaki dan
zanba ne, da izinin abin dogaro sai mun samu nasarar sato
wadannan takubban na mahaifinki don ceto rayuwar gimbiya lasmin da yarima,
in kuma shawartarki da kiyi taka tsantsan da alakar ki da
lasmin kuma ki iya sanin lafazin da zaki yi mata
magana saboda akwai alamar kishi zai iya hadaku akan
yarima
koda jin haka sai dariya ta kwace wa gimbiya musaira tace
haba sarkin yaki shin ka mantane cewa yarima dan
uwa nane na jini akan wane dalilin zan yi kishi da lasmin? Amzad yayi murmushi yace
tabbas yarima dan uwanki ne na jini ammah nasabar taku ba zata hana faruwar
soyayya ta kullu a tsakaninku ba
tunda iyayanku ne yan uwa
juna, ko kuma kema kin manta da hakan ? Musaira tana jin haka
sai ta sauya hirar tasu tace
yanzu dai kayi min bayanin ta yadda zan iya zuwa inda
sarki zamaru yake har na sato wadannan takubban yayin da
sarkin yaki yaji wadan nan tambayoyin sai ya kawo gwauron numfashi ya ajiye
sannan ya dubi
musaira cikin nutsuwa yace Al amin Ahmed Misau, A halin yanzu sarki da boka
hizainu suna nan a cikin dajin da muka baro su suna ta binciken akan yadda zasu gano
inda muke bisa binciken da nayi sai sunyi kwana bakwai
suna bincike sannan zasu gano inda wannan gidan na
sihiri da muke ciki yake wanda na gaje shi tun iyaye da
kakanni, a halin yanzu naga wani ayari na makiyaya suna kan
hanyar zuwa dajin dasu
sarki zamaru suke dan haka ya zamar mana dole mu batar da kamanni muje mu riski wadanannan
fataken mu shiga cikinsu don mu isa inda su sarki suke
dole za a samu wata mu amala da zata hada tsakanin sarki
da wadan nan fataken, damar da zamu yi amfani kenan da
ita mu sace wadan nan takubban lokacin da sarkin yaki Amzad yazo nan a cikin byaninsa sai musaira
ta jinjina kai cikin matukar tsananin damuwa
.
TO ANAN NE KUMA LITTAFIN KISAN GILLA NA HUDU YAZO KARSHE MARUBUCIN YACE MU HADU A CIKIN LITTAFI NA BIYAR 5 DOMIN JIN CI GABAN WANNAN KAYATACCEN KASAITACCEN LABARI
DAGA MAI DEBE MUKU KEWA ABDUL AZIZ SANI MADAKIN GINI
KARKASHIN JAGORANCIN TYPING DIN AL AMIN AHMED MISAU INKIYA GUYSON KO A SQUARE DAN GARIN KADUNA NAKE CEWA MU ZAMA LAFIYA ALLAH YA KAIMU GOBE DOMIN JIN CIGABAN WANNAN LABARI
its Real Al amin Ahmed Misau
KISAN GILLA 5
Littafi na biyar
Na Abdulaziz sani madakin gini
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini
KISAN GILLA
Littafi Na Biyar (5)
Part A.
.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
BAYAN MUSAIRA TA DANYI GUNTUN TUNANI SAI TA
DUBI SARKIN YAKI AMZAD TACE, shi kenan kawai ka tashi
muje mu riski wadan nan makiya da wuri domin kwanaki
bakwai kacal kadanne akan wannan gagarumin
aiki dake gabanmu mai matukar hatsari koda jin haka
sai Amzad ya yi murmushi yace, tabbas kinyi zance mai kyau
ya shugabata, yanzu kema ki shiga wancan dakin zaki
ga tufafi irin na birnin hindu ki dauka ki sanya su ki dubi
kanki a cikin madubi sannan ki fito ki sanar dani yadda
kika ga kyawunki a cikin madubin, cikin zumudi da walwalar fuska musaira ta mike
da sauri ta nufi cikin dakin da sarkin yaki amzad yayi
mata nuni
dakine na barci mai dauke da gadon barci guda daya rak
sai wata doguwar kabet ta karfe gami da dogon madubi
like a jikin bango tun daga kasa har sama, da shigowar musaira cikin wannan dakin sai
ta nufi inda wannan doguwar kabet din take ta bude
sutura irin na kasar hindu sama da kala dari a jibge a ciki,
nan take ta dauko wata shudiyar doguwar riga da wando gami da dankwali da
mayafi duka shudaye nan take musaira ta cire kayan
jikinta ta sanya wadannan data dauko sannan ta je gaban
madubi ta tsaya taga yadda kayan suka yi mata kyau
Al amin Ahmed Misau, da farko hankalinta yana kan kayan,
amman ganin yadda kayan suka yi tsananin mata kyau
sai tayi murmushi da farin ciki amma koda ta kalli
fuskarta a cikin madubin sai nan take zuciyarta ta buga
da karfin gaske,
tsoro ya kamata saura kiris ta kurma uban ihu sai ga sarkin yaki amzad ya shigo
cikin dakin ganinsa yasa ta kasa yin ihu, ba komai ne ya
firgitata ba face ganin kamannin fuskarta sun sauya izuwa
wata fuskar daban wacce bata sani ba, fuskace irin
ta matan hindu mai matukar kyawun gaske cikin hanzari sarkin yaki amzad yazo daf
da ita sannan yace mata, kwantar da hankalinki ya
shugabata fuskar ki zata dawo yadda take bayan mun kammala wannan aiki
na sato takubban mahaifinki, yana gama fadar haka sai ya
dafa madubin
dake gabansu faruwar hakan keda wuya sai kamanninsa
da kayan jikinsa suka sauya ya zamana cewar shima ya
zama ba indiye a cikin gagarumar shiga irin ta manyan
attajiransu, kawai sai ya sake daafa kafadar musaira suka bace bat daga cikin dakin
basu sake bayyana ba sai a cikin wani jeji kuma a cikin
keken doki na alfarma ga dakaru masu tsaronsu kumanin
mutum dari har da hadimai hudu nan take aka sa keken dokin nasu a tsakiya aka ci gaba da tafiya aka durfafi dajin dasu
sarki Zamaru suke
+++ ++++ *****
AL AMARIN SU BOKA HIZAINU KUWA, tun daga wannan lokaci da sarkin yaki amzad
ya dauke su yarima suka bace daga cikin daji a lokacin da ake fafata wannan mugun yakin
sai takaici ya turnuke sarki zamaru da boka hizainu bayan sunyi
iya yinsu basu gano inda su amzad suke ba sai suka zauna a kasa dirshan suka yi
tagumi, zuwa wani lokaci daya bai ce uffan ba, daga can sai
sarki zamaru yace da boka hizainu cikin alamun fushi da
damuwa yace
Yanzu daman amzad yafika karfin tsafi? Idan nasan haka ne
da tun wuri bamzo wajenka neman wani taimako ba
sa adda boka hizainu ya ji wannan magana sai ya takarkare
ya bushe da dariyar mugunta, lokaci guda kuma sai ya turbune fuska ya kalli sarki zamaru yace
idan da yafini karfin sihiri ai da ba zai gudu ba ka sani shi
tsafi kogo ne dai dai da rana daya idan mutum ya barshi to shi kuma zai barshi da shekara kada ka damu abokina
nan da kwana bakwai zan gano maboyar amzad da makiyanka
kuma zamuje har can muyi musu kisan gilla koda jin haka sai
hankalin sarki zamaru ya dugunzuma ainun kuma zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar
zata kone, Al amin Ahmed Misau, AA Misau Ke magana, sai ya
kalli boka hizainu a fusace yace masa ai sai ka tashi na koma kasata na ci gaba da mulkina idan yaso idan ka gano su
sai mu kai musu harin ba zato, dajin haka sai boka hizainu
ya bushe da dariya al amarin daya baiwa sarki zamaru mamaki
kenan yace masa
Menene kuma ma anar wannan dariyar ? Boka hizainu yace
ai jarumi na kwarai idan ya fito filin daga baya gudu
kuma baya ja da baya lallai ba zamu koma kasashenmu ba face mun kammala da makiyan mu
mun aika da su barzahu hm Idan kuwa ba haka ba
zasu shammace mu su gama damu yanzu zamu ci gaba da tafiya a cikin wannan dajin ni kuma ina ci gaba da
bincikena domin gano wajen da suke mu kai musu mamayar ba zato komawar mu
gida tamkar hutun jaki da kaya ne ko nace maka rufe kofa
da barawo kasan ance ka kashe makiyinka kafin makiyin
naka ya samu damar kasheka
ka sani kamar yadda muke shiri akan makiyan nan namu haka suma suke yi akan mu
koda boka hizainu yazo nan a jawabinsa sai jikin sarki
zamaru yayi sanyi ya aminta da wannan shawarar ta boka
hizaimu ba tare da bata wani lokaci ba suka ci gaba da tafiya suna masu kutsawa cikin
daji
A CAN WANNAN GIDAN SARKIN YAKI AMZAD KUWA, BAYAN TAFIYAR SU Amzad da Musaira sai gimbiya Lasmin ta samu kwarin jikinta tamkar
babu sauran wani dafi a jikinta kawai sai ta fito daga
cikin dakin da take kwance ta nufin dakin dasu yarima
suke
kai tsaye saboda dama tasan ko'ina a cikin wannan
Gidan sakamakon amincin su da sarkin yaki Amzad da shigarta
cikin dakin sai ta iske har yanzu yarima yana kwance akan
gado yana bacci, mahaifiyarsa shamilat na zaune daf dashi a gefen gadon ta kura masa idanu a lokacin data fada kogon
tunani, ba komai take tunawa ba face al amuran da suka faru
a baya tsakaninta da mahaifinsa marigayi tun daga lokacin
data sami juna biyu kawo izuwa rabuwarsu, A wannan
lokacin bawa Udex na zaune a can gefe guda shima yayi
tagumi yana ta tunani bisa yadda za ayi su kubuta daga
sharrin sarki zamaru
Kuyi Hakuri Babu Page daya daga cikin littafin saboda haka
zakuga kamar anyi tsallake
ina ji a jikina zamuyi nasara akan wannan azzalumin sarki
kuma zamu kubuta daga sharrinsa, ni yanzu abinda nake so dake da bawa udex ku soma tunanin hanyar da zamu bi domin debo tsumin tsafi na sarki
zamaru tunda dai kune kuka fi kowa sanin inda yake da kuma yadda za a iya debo shi
sa adda lasmin ta zo nan a zancentsa sai shamilat da bawa udex suka dubi junansu
suka yi shiru kawai sai shamilat ta dubi bawa udex tace
zomuyi tattaki zuwa kofar gidan nan ba tare da wata gardama
ba bawa udex ya mike ya nufi kofar fita daga cikin dakin
har shamilat ta bisu sun fita daga cikin dakin sai ta waigo ta kalli lasmin tace
kada ki fice kibar dana shi kadai saboda a koda yaushe zai iya
farkawa ya bukaci wani abun , dajin haka sai lasmin tayi
dan guntun murmushi tace, zan kula dashi kamar yadda zan kula da kaina bisa
amana shamilat ta mayarwa Da lasmin murmushi kamar
yadda tayi mata fitarta keda wuya sai lasmin ta zauna a wajen da
shamilat ta zauna kuma ta kurawa yarima idanu kawai tana murmushi
Al amin Ahmed Misau, AA Misau Ke magana, kamar wanda yayi
mafarki na ban tsoro haka yarima ya farka daga barci a
firgice yana mai mikewa zaune koda yayi arba da lasmin
zaune a gabansa ya dubi gabas da yamma kudu da arewa
dakin yaga su biyu ne rakm ya kalleta cikin mamaki yace
wai shin menene ya faru gare mu ina sauran abokan
tafiyarmu lasmin ta kalli yarima cikin alamun damuwa tace
kada ka damu duka zan baka amsar wadannan tambayoyin amma yanzu ya ya kake jin
jikinka kuma me kake da bukatar kaci ko kasha? Yarima ya saukar da ajiyar zuciya yace mata
ina jin kishir ruwa dajin haka sai lasmin ta tafi zuwa ga wani
teburi dake gefe daya jikin bango ta daga wani tambulan na zinare ta tsiyaya ruwan ciki a cikin
kofi ta dawo sai ta bashi ruwan da hannunta ya shanye kuma ya bukaci kari ta sake bashi da hannunta sannan ya gamsu, lasmin ta koma ta zauna suka sake fuskantar juna tsawon yan dakiku dayansu baice komaiba kuma ita ta kura masa
idanu ko kiftawa bata yi shi kuma sai yaji kunyarta ta
kama shi don haka sai ya rinka sunkuyar da kansa yana kauda kai ga barin kallonta
daga can sai ya bude baki ba tare da ya dago kai ya dubeta
ba yace
me yasa kika sallama rayuwarki don ceto tawa ? Koda jin wannan tambayar sai
farin ciki ya turnuketa tace masa, idan kana son jin amsar
wannan tambayar sai dai ka dago kanka ka kura min idanu
cikin mamaki yarima ya dago kansa yabi umarninta tace masa
So shine sanadin sallama rayuwata domin ceto taka a rayuwata ban taba tunanin
haka zata faru ba a kaina ba domin kaine da na miji na farko wanda naji na kamu da
tsananin sonsa a gani na farko babu wata shaida da zata tabbatar da tsananin kaunata a gareka sama da
sallama rayuwata domin taka, tabbas idan na boye maka
soyayyata lafiyata da rayuwata zasu iya salwanta saka makon tsananin
begenka da nake fama dashi dare da rana, babban dalilin
daya saka na bayyana maka soyayya ta a fili haka karara ba tare da shakkar komai ba
shine naga yar uwaraka gimbiya musaira ta kamu da sonka
matuka dolene na rigata furtawa domin na rigata mallakarka komai kankantarsa ka fada min iyakacin gaskiyarka shin kaji kaunata
a cikin zuciyarka ko kuma babu wani abu mai kama da haka ?
Lokacin da lasmin tazo nan a cikin zancenta sai yarima ya gyada kai cikin murmushi
daga can kuma sai ya turbune fuska kamar zai fashe da kuka yace
tun a ranar farko da nayi arba dake naji zuciyata ta buga da
karfin gaske, hakane ya tabbatar mini da
cewar na kamu da soyayya amman sai na danne zuciyata saboda ban yarda naso abinda zai wahalar da niba ko kuma naso abinda bani da tabbacin samunsa, tun da farko na
fahimci ke mai arziki ce kuma yar sarauta mai ji da kanta don haka sai na yanke
shawarar na tsare mutuncina don tserewa wulakanci tabbas yanzu da kike baiyanamin
sirrin zuciyarki sai naji nafi kowa farin ciki a cikin wannan
duniyar koda yarima yazo nan a zancensa sai hawaye ya
subutowa lasmin don haka bata san sadda ta fada kan
kirjin yarima suka rungume juna ba,
hm A A Misau, a can kofar wannan babban gida kuwa koda
fitowar bawa udex tare da
shamilat sai wannan katon goggon birin yasha gabansu ya hana su fita waje
al amarin da ya dan razanar dasu kenan suka dan ja
baya suka tsaya ana kallon kallo tsakaninsu da birin, bawa udex yayi dan tunani sannan ya dubi shamilat yace...KISAN GILLA
Littafi Na Biyar (5)
Part B.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
BAWA UDEX YA YI DAN TUNANI SANNAN YA DUBI SHAMILAT
YACE,
Ranki ya dade ai mantawa nayi daga cikin dokokin da amzad
ya bar mana yace babu fita daga cikin gidan, yanzu abinda zaifi mana mu koma da baya
mu samu wani waje can mu zauna mu tattauna, koda jin haka sai shamilat tayi murmushi
tace
hakika kayi gaskiya haka za ayi nan suka juya suka koma
wani bangare na gidan suka zauna,
AL AMARIN SARKIN YAKI AMZAD KUWA, tare da musaira saida suka shafe sa a shida cur suna tafiya a cikin daji tare da
dakarunsu da kuma hadimansu sannan suka riski wadannan
makiyayan wadanda adadinsu sunkai dubu sittin da doriya, a lokacin wannan makiyayan sun yada zango a gefen wata korama sun kafa tantuna
dabbobinsu suna shan ruwa koda suka hango dawakan
dakarun amzad daga can nesa sai suka kama shirin ta kwana
saboda a irin wannan lokaci ne yan fashi suke kawo musu harin bazata
nan take shugaban makiyayan ya tashi manzo daga cikin jama arsa ya hau doki ya tunkari tawagar su amzad
koda karasawar manzo ya karewa dakarun kallo yayi arba da
keken dokin wanda su amzad suke ciki sai ya risina yace mace
ya shugabana ni manzo ne daga ayarin makiyaya dake can gaba an aiko ni ne domin naga
ku din su waye? Koda jin haka sai amzad ya bushe da dariya
yace masa
ka koma ka fadawa shugaban ku cewar nine sarki Dilwal na
birnin Hadsham kuma hanyace ta ratso dani ta cikin
wannan dajin amma bani da wata manufa ta cutar da wani
koda jin haka sai murna ta kama manzon ya yi godiya kuma yayi sauri ya kama dokinsa
ya haye ya juya da sauri ya koma wajen jama ar tasu ya
isar da sakon, hankalin makiyaya ya kwanta suka karbisu amzad cikin farin ciki har suka kawo musu
madarar shanu suka sa aka ya da zango a wajan
ana hira, ana cikin hirar sai amzad ya lura da wata cuta
wacce ta haddasa mutuwar kimanin shanu biyar da rakuma uku nan take cikin
alamun damuwa sarkin yaki amzad ya kalli shugaban
makiyayan yace A A Misau Sunana yaushe dabbobinku suka
soma wannan cutar yace mac, kimanin sati guda
kenan tunda muka shigo farkon wannan dajin suka kamu
da wannan annobar kuma munyi iya bakin kokarinmu
dan maganin wannan cutar abin ya gagara koda jin haka
sai amzad ya mike yaje ya dudduba dabbobin da suka kamu da wannan cutar yayi nazarin cutar sosai kawai sai yayi
guntun murmushi yace
kunyi sa a da zuwana nan nasan irin wannan cutar kuma
nasan makarinta, amman badan haka ba to gaba daya
dabbobinku sai sun halaka saboda cutar ci gaba take da kara
yaduwa kuma kwana uku kacal take yi a jikin dabba ta
halakashi, nan take amzad ya fadi wasu itatuwa uku da wasu
saiwowi guda hudu yace a shiga daji aje a samosu ai
kuwa sai makiyaya suka tashi wasu masana abin su uku suka nausa daji kafin sa a guda sun dawo dauke da
abinda aka tura su amzad ya saka aka hada wuta karkashin murhun duwatsu aka dora tukunya
sannan aka wanke wannan itatuwan da saiwoyi aka zuba a cikin tukunyar gami da ruwa
Al amin Ahmed Misau ke Magana
Bayan Magani ya dahu kuma ya huce sai aka zo aka zubawa
dabbobin maganin, ko dakika talatin ba a yi ba sai gashi dabbobin dake kwance
magashiya sun mike sun warke sumu, ba wai makiyayan ba
hatta gimbiya musaira sai data kamu da tsananin mamaki nan take shugaban makiyayan
da jama a suka yi ta zubewa
kasa gaban amzad suka yi godiya cikin matukar farinciki kamar ba zasu dainaba
wannan ce tasa nan take zumunci mai karfi ya kullu tsakanin
su amzad da ayarin makiyayan tamkar daman can sun
dade a tare
a wannan wuri dai ayari biyu suka kwana sai washe gari
aka dunguma gaba daya aka ci gaba da tafiya, da yake amzad yasan su sarki zamaru suna gabansu sai ya saka dakarunsa suka kara kaimi wajen
tafiya ai kuwa suka zaburi dawakansu da gudu kai kace so ake a cemma wata dabbar da aka
fito farauta, koda ganin haka sai suma ayarin makiyaya
suka sakarwa dawakan su linzami suka mayar da abin
tamkar gudun tsere ake yi, nan fa karar sawun dawakai
ta cika dajin gaba daya hakanne ya firgita tsuntsaye da sauran kananan dabbobi suka kama
guje guje da sauya sheka
sarki zamaru tare da boka hizainu suna cikin tafiya sai
suka hangi tsuntsaye nata sowa daga inda suke sannu
a hankali kuma sai suka soma jiyo sautin sawayen dawakai
kawai sai boka hizainu yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak cike da damuwa da kuma mamaki
sai sarki zamaru yace masa
wai shin menene amfanin tsayuwarmu anan alhalin kasan akwai gagarumin aiki a
gabanmu na gano inda makiyanmu suke boka hizainu ya sauko ya debi kasar wajen
ya shinshina yace masa
yana da kyau mu tsaya musan rundunar dake zuwa don kada mubar baya da kura
babu mamaki wani tuggu ne makiyanmu suka shirya
mana bamu saniba
sarki zamaru yaja tsaki sannan ya sauko daga dokinsa yace
amma ai kace makiyan mu suna gabanmu taya kuma zasu
bullo ta bayanmu ? Boka hizainu ya gyada kai yace
ai kofofin sharrin makiya yawa garesu babu ta inda ba
zai iya bullo maka ba dan haka yana da kyau muyi taka tsantsan bisa ga duk
wani bakon al amari da zai bijiro mana kada ka manta
gumurzun
Da mukayi da makiyan mu mune muke da nasara tunda har
ka samu nasarar yankar jikin yarima da lasmin, babu yadda za ayi su tsira daga dafin
jikin takobinka dole su zama gawa nan da cikar kwanaki bakwai koda jin haka
sai ya bushe da dariyar farin ciki yace masa, hakane nan dai boka hizainu da sarki zamaru suka tsaya rike da
dawakan su suna jiran zuwan abinda yake bayansu , dakika dari bata cika ba kuwa sai ga ayarin makiyaya da na su sarkin
yaki amzad sun iso, tun daga nesa da boka hizainu ya hango su
sai yayi sauri ya dauko madubin tsafinsa sai yaga madubin
tsafin yayi duhu yaki ya nuna masa komai, koda yaga haka sai ya kalli sarki zamaru cikin
alamun damuwa yace masa
ban yadda da wadan nan mutanen ba saboda suna da karfin sihirin tsafi, kodai sun kasance gawurtattun yan fashi masu badda kama, ko kuma
sun kasance hadiman makiyanmu, ya zama dole muyi
taka tsantsan dasu babu maganar mu saki jikinmu dasu,
idan kuma sunzo mana da wargi kawai mu yake su mu
sharesu daga doron kasa' kafin sarki zamaru ya buda baki yayi magana sai suka hango
ayarin biyu sun tsaya cak a can baya kadan kuma sai suka tazo manzo ya
taho gasu sarki zamaru yace musu
Al amin Ahmed Misau Sunana
yaku wadannan matafiya ma abota daraja da daukaka
kuyi sani cewar waccan tawagar da kuke gani guda biyu
dana fito daga cikinsu ayari ne na makiyaya dana sarki Dilwal na birnin Hadsham dake can
kasar hindu, kuma hanya ce ta ratso dasu ta cikin dajin
nan muna fatan ba zaku zama masu cutarwa a garesu ba koda jin wannan batu sai boka
hizainu da sarki zamaru suka kalli juna suka kyalkyale da
dariya a lokaci guda ya dubi manzon yace masa
ka koma ka fadawa sarkin ka cewar nine sarki zamaru na birnin madinatul haswar tare
da boka hizainu , mun fito ran gadi ne dan haka muna yi masa barka da zuwa cikin
yankin kasarmu dajin haka sai manzon ya juya yaje ya isar da
sako cikin farin ciki su Amzad suka iso wajen su sarki zamaru ai kuwa ana haduwa sai boka hizainu yaji zuciyarsa ta buga
da karfi a lokacin daya hada ido da amzad wanda a halin yanzu kamaninsa irin na
mutanen hindu ne, boka hizainu bai nuna wata

4 Comments On KISAN GILLA
avatar
daiy

2 years ago

Reply

Good

avatar
ibrahim-9-5

1 year ago

Reply

Nice thanks a lot

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to ibrahim-9-5

Aha thanks for feedback keep following our site and enjoying our new hot hausa novels

avatar
kabir-mariya

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment