Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a jikinta ta dubi udez tace maza ka cire hannunka daga jikina ko na tsinke maka wuyanka ka sadu da abar da kake tsoro
Dajin haka sai udez yayi sauri ya janye hannunsa daga jikin na gimbiya jikinsana
karkarwafaruwar hakan keda wuya sai gimbiya ta dako tsallo sama ta dira a tsakiyar dakarun
yan fashin ta hausu da sara da suka ya zamana
cewa tana taimakawa jarumin sai gashi suna ta ragargazar yan fashin kafin cikar dakiku
dari hudu yan fasin sun zama saura su sittin da biyar
a tsaye sauran sun zama matattu
da nakasassu
koda ganin abin dake faruwa sai bakin ciki ya turnuke shugaban yan fashin ya kwarara uban ihu karfin ihun nasane ya sa tsirarun dakarun nasa
sukaja da baya suka rugo izuwa bayansa
a wannan lokacine gimbiya da jarumin suka hada baya
ba tare da sun juyo sun kalli juna ba sai jarumin ya budi baki yace saboda me ka taimakeni kuma wanene kai??maimakn gimbiya ta bashi amsar
wadannan tambayoyi sai tayi shiru don kada tayi magana yaji muryar mace
a dai dai wannan lokaci ne shugaban yan fashin ya kurawa gimbiya muraisa idanu har izuwa tsawon yan dakiku
kawai sai ya tuntsire da dariya yace haba ranki ya dade
menene ya shigo dake cikin sabgar talakawa
haka
kada ki shiga harkarmu ta neman arziki kin sani cewa ko giya na sha ba zanyi
yunkurin zuwa sata gidanku ba ki koma gefe daya kiyi kallo wannan fada ba naki bane
amma idan kika ki zan iya salwantar da rayuwarki a nan na dauki abinda
nazo nema na bar nahiyar gaba daya idan kika mutu a nan sai mahaifinki ya dauki dubun nan
rayukan talakawa
sa adda shugaban yan fashin yazo nan a zancensa sai kowa
ya kamu da tsananin mamaki ita kuwa gimbiya jikinta yayi sanyi ta koma gefe daya ta tsaya hakanne yasa ko ya kura mata idanu
a wajan
Musamman jarumin da mahaifiyarsa kimaratu domin a sannan ne suke kokarin ganoko
wanene wannan bakon
jarumi da aka kirashi da matsayin ya mace
shugaban yan fashin ya dubi tsirarun dakarun nasa yace
kada ku shiga wannan yaki tsakanina da wannan yaron koda kuwa kunga
zan hallaka in kuwa kuka shiga to dukkaninku mutuwa
zakuyi
yana gama fadin hakan sai ya dubi saurayin jarumin
yace
yanzu zamuyi fadan karshe idan ka kashe ni ka tserar
da dukiyar wannan karuwar wacce ba ita ce asalin uwarka ba
koda jin haka sai idanun jarumin suka zazzaro ya kurawa kimaratu idanu ita kuwa kimaratu
sai tayi sauri ta sunkui da kanta kas a lokacin da hawaye ya subuto mata
koda ganin haka sai jarumin yayi kururuwa ya daga takobinsa
sama ya rugo izuwa kan shugaban yan fashin yana mai kururuwa
burinsa kawai ya gaggauta kashe shugaban yan fashin domin ya tuhumi
kimaratu gaskiyar al amarin matsayinsa a gareta
koda ganin tasowar jarumin sai shima shugaban yan fashin ya rugo gareshi ai kuwa suna haduwa sai suka kacame
da azababben yaki mai tsananin ban tsoro
wohoho ai duk sa adda tsohon gwani masanin yaki
da tuggu ya hadu da sabon jini mai jarumtaka
da juriya dole ne ayi mugun gumurzu mai ban sha awa da ban tsoro saboda
kowannensuyana da irin baiwar da Allah yayi masa
sai da shugaban yan fashin da jarumin saurayin suka shafe
sa a uku rir suna gabza yaki na tashin hankali wadda kowannansu ya galabaita ainun tamkar zasuyi ragas
wani irin salon yakin suka rinka yi ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka gami da kai naushi da bugu
hannu da kafa duk a lokaci guda, nan da nan suka hadawa juna jini da majina
da kyar jarumin saurayin ya sami nasarar yiwa shugaban
yan fashin rauni uku
shi kuwa sau shida yana yiwa jarumin rauni alhalin ga wasu
raunika ukun a jikinsa
hakan ne yasa jarumin saurayin ya galabaita ainun a lokacin
da jiri ke dibarsa sakamakon jinin dake ta zuba a jikinsa
kuma asannan ne idanunsa suka fara gani dishi dishi kawai sai ya yanke jiki ya fadi
kasa da ruf da ciki tamkar ya zama gawa koda ganin haka sai farin ciki ya lullube shugaban yan fashin ya bushe
da mahaukaciyar dariya ta murna yazo kan jarumin saurayin
ya tsaya yana mai raba kafafunsa a kansa sannan ya sunkuyo da nufin ya tallafo kan
jarumin yayi masa
yankan rago
ba zato ba tsammani sai akaga jarumin saurayin ya
yunkuro cikin bakin zafin nama na bazato ya gabzawa shugaban yan fashin wawan naushi a fuska
saboda karfin naushin sai da yayi sama yaje ya maku da bayansa a jikin bango ya fado kasa magashiyan
kafin ya samu damar motsawa tuni jarumin saurayin ya daka tsalle sama daga inda yake ya dira a gadon bayansa da kokon gwiwarsa ta dama
kowa dake cikin falon gidan abincin sai da yaji karar karyewar kashin bayan
shugaban yan fashin nan take ya baje a kasa matacce
Al amin Guyson sunana kenana koda ganin abinda ya faru sai wadannan tsirarun dakarun nasa suka zube
kasa suna masu mika wuya nan take dakarun kimaratu suka kamasu suka daddauresu
shikuwa wannan saurayin jarumi sai ya sulale kasa sumammc
e
lokacin da jarumin saurayin ya farfado yana bude idanuwansa sai yaga kimaratu tare da
bakon jarumin da ya taimakeshi da kuma bawa
udez sai sarkin yaki amzad tsaye a gefe guda a cikin daga daga cikin dakunan gidan abincin yana
bisa gado saurayin jarumin ya dubi raunikan jikinsa yaga duk an dinkesu kuma an sa musu magani kawai
sai ya dubi kimaratu ya ce wacece uwata ta gaskiya kuma wanene wannan baokn jarumin daya taimakeni??
Maimakon kimaratu ta bashi amsa sai ta fasa kuka
a sannan ne sarkin yaki amzad ya dubi saurayin
jarumin yace
mahaifiyarka itace matar marigayi sarki hisham na wannan birni namu babu wanda yasan
inda take a yanzu kimaratu ce ta reneka tun
kana jariri kuma nine na kawo ka gareta na baka horon
yaki ne domin ka dauki fansar ran mahaifinka akan sarki yanzu
wanda ya kasance kanin mahaifinka
wannan bakon jarumin dake gabanka wanda ya taimakeka ba kowa bane face
gimbiya muraisa ya ga sarkin yanzu kasani tsakaninka
da ita babu gaba kada ka kuskura kayi tunanin
daukar fansa a kanta......
..
A nan ne LITTAFIN KISAN GILLAH NA BIYU YAZO KARSHE
MARUBUCIN YACE MU HADU A LITTAFI NA UKU
wanda ni Al amin Ahmed Dan Mutan Misau Dake Bauchi Nayi hidimar rubuto muku shi
.
Guyson Inkiyata Kenan
Dan Garin Kd...
Nake cewa mu zama lafiya
KISAN GILLA 3
Littafi na uku
Na Abdulaziz sani madakin gini
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini

KISAN GILLA
Littafi Na Uku (3)
Part A.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
Lokacin da jarumin saurayin yaji wannan jawabi daga
bakin sarkin yaki amzad sai hankalinsa ya dugunzuma
ainun fiye da ko yaushe a rayuwarsa ya kurawa kimaratu idanu a lokacin
da kowa a dakin ke zubar da hawaye
ita kuwa gimiya Musaira kuka take yi sosai tamkar
ranta zai fita saboda bakin ciki da kuma takaici
bisa jin cewa wannan bakon jarumi dan uwanta ne
na jini amma aka rabata dashi tsawon shekaru
sannan kuma gashi mahaifinta ne ya kashe mahaifinsa
ya salwantar da rayuwar sa da ta mahaifiyar sa
bayan shafewar yan dakiku kowannan su na zub da hawaye sai saurayin
ya dago kai ya dubi kimaratu yace
yake ummina
kiyi sani cewa ban san kowa ba a wannan doron
kasa sama dake nononki nasha na rayu har na kawo iyanzu
tabbas uwa uwace amma ke ce uwata ta zahiri ina neman alfarma guda daya
a wajanki ina sonki yi mini izini na tafi neman
uwata ta jini saboda nafi son na dauki fansar ran mahaifina
a gaban idanunta tun ina yaro karami naji
kina kirana da sunan yarima ashe kuwa ni yarima ne
na gaskiya ban sani ba koda jin wannan batu
sai kimaratu ta rungumi yarima suna masu fashewa
da kuka a tare cikin kankame juna sannan ta numfasa
tace yakai dannan kayi sani cewa ni kaina bansan cewa kai
yarima ne ba sai bayan ka girma a ranar da sarkin
yaki yazo zai tafi dakai domin ya fara koya maka
yaki
A wannan ranane ya sanar dani ko kai waye sannan
ya umarceni da kada na kuskura na sanar dakai wannan
sirri
ka gafarceni yakai dana bisa renon dana baka a cikin
yanayin rayuwata wanda ya kasance mukaddari
ka sani cewa ban taba haihuwa ba a rayuwata kuma bani da wani dan uwa ko masoyi
wanda ya fika a doron kasa, na sani cewa
lallai akwai rana irin wannan da zata zo wato
ranar rabuwarmu don haka nayi maka izini ka
tafi neman mahaifiyarka,
koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube yarima ya sake kankame kimaratu a kirjinsa yana mai yi mata
godiya, daga can kuwa sai ya janye jikin sa daga
cikin nata ya tako kafafunsa yazo daf da sarkin yaki Amzad ya dubeshi yace nagode
maka bisa tserar da rayuwata data mahaifiyata da kayi,
kamar yadda kabani labarin cewar kai kanka yanzu
baka san a inda mahaifiyata take ba kuma babu tabbacin
tana raye, to kasani ni ina ji a jikina cewar mahaifiyata tana raye don haka
ina neman Taimako guda daya a wajanka, ta yaya zan
iya shaida mahaifiyata alhalin bantaba ganinta ba
itama baata taba ganina ba sa a dda sarkin yaki
Amzad yaji wannan batu sai ya shiga tunani
daga can sai ya dago da kansa ya dubi wata sarka dake
wuyansa yace mahaifiyarkace ta sanyata a wuyanka
kana jariri kuma itama tana da irinta sak duk
macen da ka gani da irin wannan sarka itace mahaifiyarka
koda jin wannan batu sai yarima ya kama sarkar dake wuyansa
ya kura mata idanu sannan ya sumbace ta yana mai lumshe idanu,
sa adda hawaye ya subuto masa sannan ya dubi
kimaratu yace nifa a daren yau zan bar garinnan
idan kin amaince, bani da ikon hanaka yin wannan
tafiya a duk sa adda kaso fatana kawai ka dawo lafiya.
Gama fadin hakan keda wuya sai kuwa Udex ya dubi
Gimbiya Musaira cikin alamun firgici yace ya shugabata
kizo muyi sauri mu koma gidan sarauta tun kafin mahaifinki ya gano fitarki
idan hakan ta faru kashina ya bushe musaira ta
dubi udez a fusace tace ya zan ga dan uwana na
jini a yanzu kace zaka yi gaggawar rabani dashi
caraf sai sarkin yaki Amzad yace ai babu mai rabaki dashi sai dai mutuwa to amma ya zakiyi idan kikaga ya kashe mahaifinki saboda zaluncin
sa da rashin tausayinsa akan talakawan kasarnan.
A yanzu da naji cewar ya kashe dan uwansa saboda
karagar mulki kuma ya tarwatsa iyalinsa sai naji
na tsaneshi fiye da komai inba don darajar uwataba da har abada ba zan sake komawa
wannan gidan sarautar ba
nayi sallama dashi kenan har abada Dajin wannan batu sai sarkin yaki ya dubi
gimbiya Musaira cikin alamun damuwa yace ya shugabata ai yanzuma ba zai yiyu ki koma gidan ba domin
tuni labari ya riski sarki bisa duk abinda ya faru a nan tsakaninku da wadannan yanfashi kai Udez rayuwarka na cikin
hadari haka kuma gimbiya, idan sarki bai cutar dake ba bisa sanin sirrinsa da
kikayi yanzu to zai kafa miki takunkumin fita
mai tsaurin gaske fiye da duk irin wanda ya sa miki
a baya shawara da zan baki itace kibi dan uwanki
ma ana ki rakashi neman uwarsa ni kuma zanyi kokarin
kare duk wata baraka da zata faso a gano inda kuke
bare har a cin maku kuma Udez dolene ka bisu in kuna son ku tsira domin tuni
yanzu sarki ya gane cewa kaine ka fitar da gimbiya
na iso nan don haka ku tashi mu tafi na saku a kan
hanyar sirri wacce babu mai ganinku yayin fita
daga garin
The Al Amin Ahmed Guyson, A Square nake magana
koda jin haka sai kimaratu ta sake rungume yarima
suka fashe da kuka na bakin cikin rabuwa nan dai
sukayi sallama kimaratu ta kawo musu kudi masu yawa
ta bashi sukayi bankwana
cikin hanzari sarkin yaki Amzad, Udez Gimbiya Da yarima suka fice daga cikin gidan abincin
suka nausa daji da gudu suna masu bin wata barauniyar
hanya mai sarkakiya, sai da suka shafe kusan rabin sa a suna gudu sannan
Kwatsam suka tsinci kansu a bayan gari nanfa Udez,
yarima da gimbiya suka kamu da tsananin mamaki
domin duk su ukun babu wanda ya taba sanin
wannan barauniyar hanya wacce ta fullo dasu bayan
gari.
Da isowarsu wannan wuri sai amzad ya tsaya
cak suma sai suka tsaya zuba masa idanu Amzad
ya dubi yarima cikin nutsuwa yace' to ni daganan
zan koma ku nufi yamma kuyi ta tafiya ba tsayawa
zaku riski wani karamin kauye a dai dai lokacin
da rana ta fadi zaku iya tsayawa a kauyan kuci abinci
ku huta amma kada ku kwana saiku sayi dawakai ku nemi guzuri ku kara gaba
kada ka fara neman mahaifiyarka sai kun fice
daga cikin wannan nahiya tamu gaba daya shawarar
da zan baka guda kada ka tsananta gaba da kowa kuma ka zamo mai
hakuri hakanne kadai zai taimakeka ka sami nasara bisa duk abinda zaka sa
a gabanka da wannan furuci nake yi muku bankwana
sai mun sake saduwa a ranar da zaku dawo wannan
birni namu mai albarka na Madinatul haswar sakona ga
mahaifiyarka shine ka gaya mata cewa ni Amzad na cika alkawarina na tserar
da rayuwarka da kuma damuwarku koda sarkin yaki amzad yazo nan a zancensa sai yarima ya
rungumeshi yana mai godiya yace tabbas ka ruke amanar
mahaifina, baka kasance butulu ba kamar sarkin
yanzu bani da abinda zan iya saka maka dashi bisa rike
amanar mahaifina dakayi
Amzad ya numfasa yace ina da alfarma guda daya
da nakeso kayi mini ina son ka ruke yar uwarka
gimbiya amana lallai kasota kamar yadda kake son kanka kuma ka tsare lafiyarta da mutuncinta kamar
yadda na tsare taka
sa adda yarima yaji wannan batu sai ya jinjina kai
yace lallai na dauki alkawari zan tsare rayuwar yar uwata da mutuncinta
kamar yadda ka bukata
yarima na gama fadar haka sai ya juya ya falfala da gudu izuwa yammacin dajin ai kuwa sai gimbiya da
bawa udex suka rufa masa baya ba tare da bata
wani lokaci ba shima sarkin yaki amzad ya ruga
yabi wata hanyar daban
kamar yadda sarkin yaki ya fada haka al amarin ya kasance wato rabin sa a na cika
sai ga sarki zamaru tare da dakaru kimanin dari shida
bisa dawakai acikin shigar yaki sun iso kofar
gidan abincin kimaratu duk wanda ya ga fuskar sarki
a wannan lokaci dolene ya firgita saboda kokadan babu
annuri a tare dashi saboda tsabar bakin ciki
har yatsine fuskarsa keyi kai tsaye sarki Zamaru da
dakarunsa suka sauko daga kan dawakansu suka shiga cikin
gidan da sauri a wannan lokaci kimaratu da yaranta na ta
kokarin gyara barnar da akayi a falon wato suna kwashe karyayyun kujeru da tebura
wasu na goge jinin da ya malala a kasa dama tuni an fice da gawarwakin yan fashi da kuma nakasassunsu koda ganin
shigowar sarki da dawakansa sai kimaratu ta rugo
da gudu izuwa ga sarki tana kuka ta zube kasa gabansa har kimaratu ta budi baki zata ce wani abu sai sarki ya zabga
mata wawan mari sabida karfin marin saida ta zube kasa, kimaratu ta dafe kuncinta da hannayanta biyu a lokacin
da wani zafi da zugi ya addabi mukamukinta taji kamar ya goce batasan sa adda hawayan wuya ya zubo mataba
sarki zamaru ya dakawa kimaratu tsawa yace kada ki
yaudareni da irin halinku na tsofaffin bariki lallai
jikina ya bani cewa akwai wani munafunci da ake kullawa tare dake na sami labarin cewa danki ya kashe shahararran danfashin nan Bazazga
yaushe danki ya koyi yaki har ya zama gawurtaccen jarumi
acikin birnina bansani ba? Na nemi yata gimbiya da kuma amintaccen bawana
Udez na rasa kuma ance anga udex anan dazu sa adda akayi gumurzu da yan fashin
lallai kuwa udez yna tare da gimbiya yanzu gashi babu dan naki anan kuma
babu udez da gimbiya ki sanar dani gaskiyar
lamari ko kuma ki gwammace mutuwa da rayuwarki
the Al amin Ahmed Guyson A Square nake magana
duk abinda kika mallaka zan kwace shi kuma zan sa ayi ta gana miki a zaba
kullum har ta zamo sanadin ajalinki
lokacin da sarki zamaru yazo nan a zancensa sai
kimaratu ta tkarkare ta bushe da dariyar Mugunta
al amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan a wajan
lokaci guda kuma sai ta tarbone fuskarta ta
dubeshi cikin gadara ba tare da jin wani tsoroba
ta ce yakai wannan sarki kayi sani cewa labarin da kakeso
kaji yanzu daga bakina dai dai yake da allura ta tono
garma zaifi kyau mukadaita dani dakai kasani cewa ni yanzu
bani da wani sauran buri a duniya domin idan ka kwace abinda
na ke dashi ma wannan gari naka ina da ninkin uku nashi
a can wani garin daban inda baka saniba, bani da da na cikina bani da wani dangi
a duk fadin duniyar nan babu abinda bangani ba a rayuwata nasha wuya
kuma nasha dadi aiko yanzu kasuwa ta tashi dan koli yaci riba ko ka kasheni ka ka barni a raye bani da asara
kuma babu wanda zaiyi asafa face wanda ya ke son jin labarin da kake so kaji daga bakina
shine kadai zai iya taimakonka ka tunkari makiyanka
kuma dole sai dani zaka iya riskar makiyan naka wannan babban kasuwancine a tsakanina dakai
Lokacin da kimaratu tazo nan a zancenta sai hankalin
sarki zamaru ya dugunzuma ainun ya rasa abinda zaiyi yau ya shiga tunani
daga can sai ya kama kafadun kimaratu da hannayansa
biyu yana murmushi ya tasheta tsaye ya kaita kan kujera ya zaunar da ita
sannan shima ya
Zauna daf da ita kawai sai yasa hannu cikin aljihunsa
ya dauko hankicinsa mai daraja ya goge jinin dake kan leben kimaratu da kansa
ya dubeta yace
ki gafarceni yake kimaratu hakika nayi kuskure da nayi
saurin kai hannuna fuskarki amma rashin sanine
ya janyo hakan yanzu zan tafi kuma zan aiko miki da dinare dubu dari
uku domin ki gyara abubuwan da suka lalace a gidan
nan zan dawo da kaina cikin dare domin mu
tattauna sai nazo ''......KISAN GILLAH
Littafi Na Uku (3)
Part B.
.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
Mun tsaya ne a inda sarki yace.. Ki zan aiko miki
da kudi ki gyara abubuwan da suka lalace a gidan
nan zan dawo da kaina cikin dare domin mu tattauna
sai nazoo.
Zamu cigaba.
Yana gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya fice
daga cikin gidan da sauri dakarunsa na take
masa baya tafiyarsa keda wuya sai kimaratu ta
kama kyalkyale dariya kamar bazata dainaba
daga can kuma saita fashe da matsanancin kuka har
gaba dayan yaranta suka kamu da matukar tausayinta
suka shiga rarashinta da kyar suka shawo kanta
ta daina kukan sannan aka tasheta tsaye ta tafi izuwa inda turakar take
Al amarin sarki kuwa lokacin da ya koma gida sai ya kasa
zaune ko tsaye yayi takai kawo cikin tsananin
tashin hankali bayan ya dan jima yana tunani da nazari
sai yasa aka shirya wani hawan na musamman ya debi
dakarunsa na musamman masu tsaron
rayuwarsa wadanda ya yarda dasu domin zakwakuraine kuma jajirtattu
su dari suka tafi izuwa birnin boka Hizainu
tafiyar sa a dayace da rabi tsakanin birnin sarki zamaru da birnin boka hizainu
koda su sarki zamaru suka shafa rabi wannan
tafiya sai kwatsam suka ga an harbo
wata kibiya dauke da wasika tazo ta cake a jikin wata bishiya
dake gabansu kadan
nanfa suka kama waige waige ko zasu ga wanda ya harbo
kibiyar amma ba a ga alamun mutumba
a gabas da yamma kudu da arewa nan take sarki zamaru ya yiwa daya daga cikin
dakarunsa inkiya yaje ya cire kibiyar daga jikin
bishiyar ya kawo masa wasikar har sarki zamaru
yayi nufi ya ajiye wasikar sai yaje can gidan boka
hizainu sai kuma ya sauya shawara ya warware
wasikar da hannunsa ya fara karantata a cikin ransa kamar haka.....
Takarda daga hannun sarkin Yakin ka Amzad yakai wannan
tsohon azzalumin sarki kayi sani cewa duk abinda
mutum ya shuka shi zai girba shekaru ashirin da biyar da suka gabata kaci
amanar dan uwanka sarki Hisham domin ka kashe
shi ka hau kan karagar mulki ka umarceni dana kashe
matarsa da dansa amma sai naci amanarka
maimakon naci amar sarki hIsham gawar dana kawo maka ta
matar marigayi da jaririnta basu bane, gawar
wadansu fatakene da yan fashi suka kashe kuma
tsafi akayi aka mayar da kawunansu irin na matar marigayi da jaririnta
shi wannan jaririn dan marigayi shine dan da
kimaratu ta raina ya girma har ya zama jarumi
a boye kuma ba kowa bane ya bashi horon yaki face ni,
mahaifiyarsa kuwa tuni tun a wancan lokaci ta bar wannan nahiya don haka wannan yaro yarima ne kuma ya
tafi neman mahaifiyar tasa duk ranar da yaga mahaifiyarsa
zai dawo nan birnin
madinatul haswar ya tsinke maka kai ya hau
karagarsa ta mulki a yanzu haka ni da iyalina da
kimaratu tuni munyi nisa ga birnin kasar ka
har abada ba zaka sake ganinmu ba, kai bayan ka fadi zamu dawo
kasani karshen azzalumi
maci amana shine kaskanci da mutuwa.
Koda sarki zamaru ya gama karanta wannan wasika
sai ya takarkare ya kwarara uban ihu ihun
da ya firgita gaba dayan dabbobi da tsuntsaye dake cikin dajin
saboda tsananin bakin ciki da takaici sai da
sarki zamaru ya fado kasa daga kan dokinsa ya kama
zubar da kwallah
jim kadan sai ya mike tsaye ya dubi daya daga cikin
manyan dakarun sa ya ce dashi maza ka koma gida
kasa a taro dakaru dubu dari biyu a basu guzuri
mai yawa su rabu gida hudu su bazama neman sarkin
yaki Amzad da iyalansa tare da kimaratu da
danta gabas da yamma kudu da arewa har zuwa
karshen iyakokin mu da zarar an gansu a kashesu a zo mini da
kowannansu duk
rundunar da tasamu nasarar aiwatar da wannan
aiki zan mai shesu attajiran da babu kamarsu a kasata
kuma zan daukakasu acikin majalisata
koda jin wannan umarni sai badakaren ya risina
da sauri jikinsa na bari yace an gama ya shugabana
cikin hanzari badakaren ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya ya nufi hanyar da
zata mayar dashi birnin madinatul hashwar
tamkar zai tashi sama saboda karfin gudu bacewarsa ke da wuya sai sarki
zamaru ya sake jagorantar dakarun suka ta
samma birnin boka hizainu da yake wannan
karon sarki zamaru a fusace yake kuma gudu yake bisa dokinsa a lokacin da
zuciyarsa ke tafarfasa kamar zata kone nan da nan suka isa birnin
da isowarsu kofar gidan sarautar sai suka iske boka hizainu tsaye
fadawansa sun kewayeshi fuskarsa a murtuke al amarin
da yasa zuciyar sarki zamaru ta buga da
karfi kenan tsoro ya darsu da mamaki suka baibayeshi
sarki zamaru da dakarunsa na gama shigowa
cikin harabar gidan sarautar sai dakarun hizainu
sama da dubu biyu suka kewayesu sukayi musu kawanya cikin rudewa
da rashin fahimta sarki zamaru ya dubi boka hizainu yace,
me zan gani haka? Akan wane dalili zakasa dakarunka
su ritsamu maimakon ka tarbemu hannu biyu?
Sa adda boka hizainnu yaju wadannan tambayoyi sai ya takarkare
ya bushe da mahaukaciyar dariya lokaci guda
kuma sai ya turbone tamkar an aiko masa da sakon
mutuwa ya dubi sarki zamaru a fusace yace akan wane
dalili zaka debo zakwakuran dakarunka ka kawo mini
ziyarar ba zato? Rabona da kai yau shekara ashirin da biyar kenan tunda ka
raba kasarka da dukiyarka ka bani rabi ka manta
dani ko sakon gaisuwa baka taba aiko mini ba
bare
ziyara babu mamaki yanzu ka zone da shirin
ka yakeni ka karbe abinda ka bani, sa adda boka
hizainu yazo nan a zancensa sai sarki zamaru yayi
murmushi sannan yace ai kai boka ne kasan abinda bansani ba me yasa bakayi bincike
ba ka gano dalilin zuwana gareka, tsawon shekaru ashirin
da biyar baya ina zaune lafiya cikin koshin lafiya
da kwanciyar hankali kaima haka tabbas ruwa baya
tsami banza kaima kasan cewa akwai abinda ya kawo ni
gareka babu wanda yasan sirrina sama da mutum
biyu a cikin fadin wannan duniya daga kai sai
sarkin yakina Amzad to ka sani yanzu sarkin yakina yaci amanata domin duk
abinda ya faru a baya yaudarata yayi
bani ya taimaka ba abokan gabaata ya taimaka
wannan yaro wato yarima dan marigayiii......
Kafin sarki zamaru ya gama fadin abinda ke bakinsa sai boka
hizainu ya dakatar dashi yana mai daga masa
hannu kawai sai ya kyalkyale da dariya sannan yace
nasan komai hatta tare ka da nayi yanzu dan kurum na gwada ka nayi don naga
karfin zuciyarka kazo ka iyayin abinda nakeso kayi ina son ka kwantar da hankalinka tamkar tsumma a randa
zo muje ka huta sannan saimu tattauna bisa
abinda zai fishshemu koda gama fadin haka sai farin ciki
ya lullube sarki zamaru ya sauko daga kan dokinsa da
sauri ya rungume boka hizainu suna masu kyalkyalewa
da dariya a tare.
The Guyson naci gaba da cewa Al amarin su
yarima da gimbiya kuwa tunda suka nausa cikin daji suna masu bin
yamma basu yada zango ba ko inaba har sai da suka iso wannan kauye.
Da

4 Comments On KISAN GILLA
avatar
daiy

2 years ago

Reply

Good

avatar
ibrahim-9-5

1 year ago

Reply

Nice thanks a lot

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to ibrahim-9-5

Aha thanks for feedback keep following our site and enjoying our new hot hausa novels

avatar
kabir-mariya

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment