Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damuwa ba
sai ya tari Amzad ya rungumeshi, shi kuma sarki zamaru ya rungume shugaban makiyaya, bayan nan kuma sarki amzad
ya rungume sarki zamaru ai kuwa suna hada jiki sai boka
zamaru shima yaji zuciyarsa ta buga da karfi
nan dai aka kafa tantuna aka zazzauna aka kawo ababen ci dana sha aka kama
kimtsa ciki ana hira tamkar an dade da juna, ana cikin
wannan haline boka hizainu da sarki zamaru suka mike
tsam suka koma can gefe daya inda babu wanda zaiji
abinda suke cewa
'' Wai shin wane amfani zamanmu a nan zaiyi bare mu
bata lokaci muna baiwa makiyanmu damar kubuta daga shirinmu ? Lokacin da boka hizainu ya ji wannan batu sai yayi guntun murmushi sannan yace
ni ina ji a jikina cewar idan muka ci gaba da tafiya muka bar wadan nan mutanen a bayanmu tamkar mun kashe maciji bamu sare
kanshi bane
kasancewar a dazu da wannan sarki ya rungume ni sai da
naji zuciyata ta buga da karfi don haka ban yarda dashi ba , zarki zamaru yace
ai nima ina hada kirji dashi naji haka' boka hizainu yace
tabbas zargina zai zama gaskiya zai iya zama sarkin yaki
amzad ne ya juye zuwa siffar mutanen kasar hindu
ita wannan zukekiyar macen dake tare dashi zata iya
kasancewa gimbiya musaira ce ko abokiyar gabata
lasmin
sa adda sarki zamaru yaji wannan batu sai yayi shiru yana
gyada kai gami da nazari a cikin zuciyarsa daga can sai
ya dago kai ya kalli boka hizainu yace masa
to yanzu ta yaya zamu iya tabbatar da abinda muke zargi a kansu boka hizainu yace
Hanya biyu ce kawai, na farko sai mun taresu gaba da gaba munyi yaki, na biyu kuma sai dai mu dana musu tarko kayi galala da takobinka ina ganin
abinda ya kawo su kenan su sace, domin ceton rayuwar
yan uwansu to amman abin tambayar anan idan sunyi nasarar sace takobin tayaya
zasu yi nasarar shiga cikin gidan sarautarka har su tsoma takobin a cikin tsumin tsafinka
Al amin Ahmed Misau Ke magana,
alhalin nasan cewar
yana da tsaro koni ban isa zuwa na debo shi ba lokacin
da boka hizainu yazo nan a zancensa sai sarki zamaru ya bushe da dariyar farin ciki har ya zamana su sarkin
yaki amzad dake can cikin tanki a zaune sunjiyo dariyar
abinda su sarki zamaru basu sani ba shine makaho baya cewa ayi wasan jifa face ya taka hoge
bayan sarki zamaru da boka hizainu sun gama tattaunawa sai suka dawo wajen su amzad suka bukaci suma a kafa musu tanti domin kwana a wajen
ba tare da bata lokaci ba kuwa sai amzad yasa aka kafa musu
tanti mai kyau aka shirya shimfidu guda biyu a cikinsa masu taushin gaske kuma aka sake kai
musu abinci da abinsha mai daraja irin nasu na sarakuna
lokacin da boka hizainu da sarki zamaru suka shiga cikin
tantin nasu sukaga irin daular da aka shirya musu sai suka
bushe da dariyar mugunta boka hizainu yace, wai mu za ayi wa yaudaran zamani,
ai mu ba mahaukata bane da shagala da abincin su ko kuma
shimfidarsu a samu damar da za a cutar damu
suna gama fadar haka sai suka zauna a kasa dirshan suna hira suna tattaunawa akan
Yadda zasu gama gano komai a daren yau, suna cikin
haka sai sukaji sautin zubar ruwa a can bayan tantinsu tare da murya wata mace mai zakin
gaske tana rera waka mai dadin gaske, nan take boka hizainu
da sarki zamaru suka mike suka fice daga cikin tantin suka zagaya izuwa baya koda sukayi arba da macen da take yin waka
sai suka dimauce sakamakon ganin tsananin kyawun surarta gami da kyawun fuskarta tamkar wata dan daren sha biyu
sai sheki da walwali take yi budurwa ce yar kimanin shekaru sha shida zuwa sha bakwai
mai siffar mutanen kasar hindu, wanka take yi a bakin korama
tana watsa ruwa a jikinta
ba tare data cire farar doguwar rigar dake jikinta ba
wacce ta kasance shara shara mai baiyyana dukkan surorin
jikinta cikin rudewa da dimaucewa sarki zamaru ya yunkura zai ruga zuwa gareta sai boka hizainu ya yi caraf
ya rike shi yace masa
baka da hankali a ina ka taba ganin bil adama mai irin wannan azababben kyau diri da
fuska. Ai da gani kasan wannan aljana ce ta juye zuwa wannan kyakkyawar siffar domin a
yaudaremu idan har akwai wannan kyakkyawar budurwa a cikin wannan ayarin me yasa
tun farkon haduwarmu
dasu bamu ganta ba
Al amin Ahmed Misau Sunana, sa adda sarki zamaru yaji
wannan batu sai jikinsa ya yi sanyi yaji yayi wani dan guntun
tunani kafin yace wani abu............
.
Wow Nimafa Na rikirkice na rikide na rude na kasa cigaba da
wannan typing din sakamakon ganin tsananin kyan da wannan, kyakkyawar yarinya take
da ne ma yasa na dakata kuma nima na labe na ci gaba da
kallonta kawai tana rera wakarta...KISAN GILLA
Littafi Na Biyar (5)
Part C.
.
Takun Karshe °√The End√°
.
Hm Real AA Misau, yau dai munzo karshe..
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
SA'ADDA SARKI ZAMARU YAJI WANNAN BATU SAI JIKINS AYAYI SANYI YAYI WANI DAN GUNTUN TUNANI SANNAN YACE
Ai kuwa koda aljana ce sai naje na taba wannan kyakkyawar sura
saboda nasan ina da tsarin da bata isa ta cutar dani ba
koda gama fadin hakan sai sarki zamaru ya cire takobinsa
biyu daga jikinsa ya mikawa boka hizainu ya barba takobin
sai sarki zamaru ya kwabe rigarsa da rawaninsa ya ruga
a guje izuwa wajen da wannan kyakkyawar budurwa take
koda budurwar ta hango shi sai ta firgita ainun ta tsandara uban ihu nan take gaba daya jama ar
dake cikin ayarin suka fito daga cikin tantinsu suka rugo
izuwa bakin korama
shikuwa boka hizainu kunya ce ta kama shi lokacin da
jama a suka zo suka ganshi rikeda takobin sarki zamaru
kuma suka hango sarki zamaru tare da budurwa a cikin
korama suna kokawa, boka hizainu bai san lokacin daya saki takobin kasa ba amman yana kallonsu don kada
wani yazo ya dauke su, nan fa jama a suka rika wuce su suna wuce boka hizainu
wasu ma suna bangazarsa
a lokacin ne amzad ya ruga da gudu zuwa wajen sarki zamaru da karfin tsiya ya janye shi daga wajen kyakkyawar budurwar yayi jifa dashi gefe guda
kuma ya kalleshi a fusace yace, akan me zaka afkawa kanwar matata? Saboda tsananin
kyawunta ne na boyeta tun a farkon zuwan mu yanzu ma bansan sa adda ta fito wajen nan wanka ba
cikin hanzari amzad ya cire mayafin jikinsa ya lullube jikin budurwar ya tafi da ita
da sauri izuwa cikin tantinsu
a lokacin sarki zamaru ya mike tsaye cikin kunya ya nufi boka hizainu koda ya isa
wajen da yake yaga takobinsa zube a kasa sai ya dubeshi cikin firgici yace
ya akayi ka ajiye abinda na baka ajiya a kasa ? Cikin hanzari
sarki zamaru ya suri takubban ya zarosu daga cikin kubansu yana duddubawa, koda ya gama duba su sai ya takarkare ya kwala uban ihu yana mai cewa
sun sace min takubbana dajin haka sai boka hizainu ya ruga da gudu zuwa cikin tantinsu amzad
yana shiga yaga wayan babu su amzad babu kayansu
nan take shima boka hizainu ya kwarara uban ihu sannan ya
fito da gudu ya nufo inda sarki zamaru yake kafin ya karasa ya rikide ya zama wani babban tsuntsu, kawai sai sarki zamaru ya daka tsalle ya haye kan
tsuntsun ya tashi dashi sama suka luluka izuwa cikin gajimare
fara tafiyar tasu keda wuya sai sarki zamaru ya budi baki
cikin alamun tsananin fushi yace Al amin Ahmed Misau sunana
wai shin yanzu ina muka dosa, alhalin bamu san inda suka nufa ba boka hizainu yace
babu inda zamu sama da gidan sarautarka domin dole can zasu nufa kai tsaye domin
sato tsumin tsafinka suje su warkar dasu yarima da lasmin daga cutar dafin dake jikinsu, ka kwantar da hankalinka ya zamaru kayi sani cuk irin tsananin saurin da zasu yi kodai mu riskesu
a cikin gidan sarautar ko kuma mu riske su suna fitowa
gama fadar haka keda wuya sai boka hizaunu yaci gaba
da kada fuka fukansa da karfi yana mai kara karfin gudunsa a cikin gajimare
wannan shine abinda ya faru tsakanin boka hizainu da sarki zamaru bayan sun gano
cewar su amzad ne suka yi badda kama suka sace takubban
sarki zamaru
+++ ++ ++
AL AMARIN SU SARKIN YAKI, Amzad
kuwa lokacin da suka samu
nasarar sace wadannan takubban guda biyu suka bace bat
daga cikin tantinsu su uku basu sake bayyana a ko ina ba sai
a wannan gidan nasa na sirri dake tsakiyar daji, da bayyanarsu
ukun sai wannan goggon birin ya risina a garesu yana mai yiwa
amzad barka da zuwa, nan take amzad da musaira suka nufi kofar gidan zasu shige
amma sai wannan kyakkyawar budurwa da suke tare da ita ta noke taki bin bayansu
cikin tsananin mamaki amzad ya juya ya dubeta yace
yake Aljana ZURARA menene dalilinki na nokewa anan?
Kodajin wannan tambayar sai zurara ta murtuke fuskarta
tace
ina alkawarin dake tsakanina dakai, ba zanci gaba da taimakonka ba face ka cika alkawarin dake tsakaninmu yanzu take, kai da kanka kace
zaka karbi addini na bayan na taimaka muku kun samu
nasarar dauko wannan takubban guda biyu, ka sani
domin bukatarku ta biya na aikata wadannan laifuka da suka
sabawa dokar addinina
lokacin da aljana zurara tazo nan a zancenta sai hankalin
sarkin yaki amzad ya dugunzuma yace, shin bakya ganin idan na karbi addininki ba zan iya
ganin bayan sarki zamaru
da kuma boka hizainu ba ki sani ina karbar addininki sihirin
tsafina duka zai daina aiki
koda jin wannan batu sai aljana zurara tayi murmushi tace
ai idan ka karbi addini na na bautar Sarki Guda daya mahaliccin komai da kowa wato
ubangijin musulunci to tabbas a sannan nema nake da tabbacin
zaka sami nasara akan su sarki zamaru domin ubangijin
musulunci zai tallafa maka 'kafin amzad ya buda baki yace
wani abu sai ga yarima da lasmin, bawa uded da shamilat sun fito daga gidan, koda musaira ta hango yarima a tsaye cikin koshin lafiya sai ta ruga gareshi
cikin tsananin farin ciki ta rungumeshi tana mai cewa
nayi murna da samun lafiyarka yakai dan uwana koda ganin abinda ke faruwa sai
kishi ya turnuke lasmin, taji kamar tazo ta fincike musaira daga kan
kirjin yarima, musaira ta janye jikinta daga na yarima tana
mai dakawa Lasmin harara ita kuma lasmin sai ta mayar mata da martanin
murmushi a cikin ranta tana mai cewa, na gama dake tunda na
rigaki furta masa abinda yake cikin raina
kwatsam sai sukaga shamilat ta kalli aljana zurara tace mata
tabbas addinin musulunci shine addinin gaskiya, domin
mijina marigayi ya bani labarinsa tun sa dda mukayi auren
saurayi da budurwa yace mini shi bazai samu damar karbar
addinin musulunci ba amma yace min duk lokacin dana samu
dama na karba
gama fadin haka keda wuya sai shamilat ta taho zuwa
wajen aljana zurara ta durkusa bisa gwiwoyinta tace, maza
ki shigar dani cikin wannan addinin mai daraja nan take zurara ta fadawa shamilat
kalmar shahada ta maimaita, duk wannan abin dake faruwa
bawa udez , yarima da wannan katon gwaggon birin sun
kurawa aljana zurara idanu ko kiftawa basayi, ba komai ne ya tafi da hankalinsu ba face ganin tsananin kyawun zurara wanda babu wani da namiji
da zai yi arba da ita ba tare daya dimauce ba, saini AA Misau
Tunda ina da Wacce tafika Kyan hahahaha, shi kansa sarkin
yaki amzad da yake tare da ita tsawon shekaru danne zuciyarsa kawai yakeyi, saboda yasan
babu aure tsakanin MUTUM DA ALJAN, koda su amzad suka ga shamilat ta karbi
addinin musulunci, kuma suka ji kalmar da aka biya mata wacce basu taba jin
irinta ba sai dukkan su jikinsu yayi sanyi kuma suka ji
tsigar jikinsu na tsashi
nan take sai yarima shima ya taso yazo gaban zurara shima ya durkusa kamar yadda
mahaifiyarsa shamilat tayi ai kuwa sai itama kimaratu tazo daf da shi ta tsugunna ta
dubeshi 'nima nayi kafin ta gama rufe bakinta tuni bawa udez, musaira, lasmin da sarkin yaki amzad sun zo sun durkusa a gaban aljana zurara , cikin tsananin farin ciki zurara ta fada musu kalmar shahada suka maimaita, ta kalle su cikin murmushi tace musu
to daga yanzu bakwa bukatar taimakon kowa sai na ubangijin musulunci, ku tashi
ku tafi fadar sarki zamaru ku aiwatar da abinda ke gabanku
ko kuma ku jira shi yazo nan ya same ku ayi duk wacce za ayi, idan har zaku bkukaci taimakon ubangijin musulunci babu abinda zasu iya yi muku
kuma sai kunga bayansu da wannan furuci nake yi muku sallama ba zaku sake ganina ba sai a ranar da kuka tankwabe haramtacciyar karagar mulki ta sarki zamaru
ya zamana cewa yarima ya karbi mulkin birninsa, koda gama
fadin haka sai aljana zurara ta bace bat tamkar bata
taba wanzuwa a wajen ba, tafiyarta keda wuya sai amzad ya kama kalle kalle
ya rasa abinda zaiyi, ya kalli su yarima yace musu nifa ban yadda zamu iya zuwa birnin
madinatul haswar ba a cikin kankanin lokacin tunda tsafina ya daina aiki, jin haka sai shamilat ta dafa kafadar yarima tace masa
ya dana shin ka manta da bayanin da aljana zurara ne ?
Ai tace duk halin da muke ciki mu nemi taimakon ubangijin
musulunci dajin haka sai sarkin yaki amzad ya bude baki yace
ya ubangijin musulunci muna neman taimakon ka ka kaimu birnin madinatul haswar ka bamu sa a akan abinda zamu jeyi
a can ka doramu akan abokan gabanmu' gama fadin haka keda wuya sai wannan katon goggon birin yayi girgiza ya zama wani katon aljani yace
ya shugabana sunana NURUL HAIYAS kuma aljana zurara ce ta turoni gareka tsawon shekaru biyu baya domin nayi maka bauta nazo maka a siffar biri ba tare da ka san cewa ni aljani bane
ni musulmi ne kamar zurara dan haka kuzo ku hau bayana na kaiku ku duka da izinin uban gijin musulunci zan kaiku birnin madinatul haswar a cikin abinda bai wuce dakika dari da sittin ba cikin farin ciki su duka
suka yunkura suka durfafo aljani nurul haiyas zasu hau kansa
sai musaira tasha gaban yarima ta tsaida su sannan ta dubi
yarima ido cikin ido tace masa
yakai dan uwana na jini kayi sani cewar ina fama da ciwon
sanka da begenka dare da rana fiye da yadda lasmin take shaida maka, ka sani idan na rasaka ka tafi ka barni sai dai mu rabu har abada ba zan iya rayuwa a doron ka sa ba face ina matsayin
matarka ta aure, koda jin haka sai hankalin lasmin ya dugunzuma
ta dubi musaira a fusace tace
ai na riga ki furta masa soyayya saboda haka kece ya kamata ki hakura dashi , koda jin haka sai aljani nurul haiyas ya tari numfashin lasmin yace
ai duk wannan mai sauke ne tunda kun shiga addinin musulunci
saboda a cikin addinin musulunci namiji yana auran mata
sama da daya kubar wannan muhawarar yanzu sai munje bayan mun sami nasarar aiwatar da abinda yake gabanmu
Koda Aljani Nurul Haiyas yazo nan a zancensa sai ya rankwafa
fuka fukansa suka hau kansa su duka suka zazzauna shikuma sai ya bude fufafukansa ya tashi dasu sama ya rinka tsala azababben gudu na gaban kwatance tamkar tauraruwa mai
wutsiya Al amin Ahmed Misau Sunana, Ai kuwa a cikin dakika sittin daidai aljani Nurul Haiyas ya sauko kasa ya
dira a tsakiyar gidan sarautar birnin madinatul haswas koda dakaru suka ga sarkin yaki amzad tare da bawa udez
dakuma matar marigayi akan aljani nurul haiyasa
sai suka firhita ainun suka kasa tararsu, kai tsaye amzad ya wuce gaba izuwa cikin gidan
sarautar, shamilat da bawa udez na take masa baya har suka isa
inda tsumin tsafin sarki
zamaru yake da isarsu
wajen kwatanyar tsafin sai amzad ya zare takubban guda biyu daga cikin kubensu
ya tsoma a cikin tsumin ya zare sannan ya dauko kwatanniyar ya mikawa lasmin
ta kafa bakinta tasha ta mikawa yarima shima ya karba yasha,
nan take su biyu suka ji tamkar tafi bai taba shiga jikinsu ba, kuma suka ji wani
irin gagarumin karfi ya shigesu, Aski yazo gaban goshi fa
Al amin Ahmed Misau ne Jagoran Typing, sai yarima ya
kalli sarkin yaki amzad yace masa, hakika sihiri gaskiya ne kuma maganin ma haka
gama fadin haka keda wuya suka jiyo muryar sarki
zamaru daga can waje yana kwalawa amzad kira cikin
kakkausar murya koda jin haka sai ya kalli yarima da musaira
da lasmin yace abokan gabarmu sun iso, mu nemi taimakon
ubangijin musulunci muje mu tunkare su nan take su duka
suka kama kiran sunan
Allah suna neman taimakon sa a cikin zuciyarsu
su duka ukun suka zare takubbansu suka nufi babban filin dake tsakiyar gidan
sarautar da isarsu suka iske sarki zamaru a tsaye ya rike
wata sharbebiyar adda gami da garkuwa, fuskarsa na
yin gatsine saboda tsananin fushi , boka hizainu kuwa ya rike mashi guda biyu a hannayensa yasha damara fuskarsa a
murtuke babu annuri ko kadan, hizainu ya dubi zamaru yace ka barni da yarima
da yarka musaira, dan bana son ka kashe yarka da hannunka
zamaru ya gyada kai yace, hakan yayi kafin daya daga cikin
su amzad yace wani abu tuni su sarki zamaru da boka
hizainu sun rugo izuwa kansu an kacame da azababben yakin
WOHOHO ! a wannan ranar an fafata kazamin bakin gumurzun yaki kuma sai da
su yarima suka sha bakar wahala suka samu raunika da
yawa a jikinsu sannan suka sami nasarar kashe sarki zamaru
da boka hizainu
bayan an gama wannan yakinne an kashe manyan Azzaluman wato sarki zamaru da
boka hizainu
Kashe gari aka dora yarima akan karagar mulki kuma aka
daura auren sa da yan mata biyu wato Gimbiya Musaira
da Gimbiya Lasmin suka ci gaba da rayuwarsu cikin jin dadin
duniya da kwanciyar Hankalin yayinda Addinin musulunci ya kara yawaita a sassan duniyar ya ci gaba da yaduwa aka
bautar da bautar Gumaka....
.
Bayan nan kuma sai Aka Daura auren AA Misau Da Gimbiya...... Koda yake ba saina karasa ba nasan kunsan wacce nake nufi ai hhhhhhh
.
ALHAMDULILLAH !!!
A nan ne Littafin Kisan Gillah Yazo karshe kuma muna fatan
littafin ya kayatar daku an dauki darasi akanshi sosai,
Marubucin Littafin Wato Abdul aziz Sani M/Gini dake
garin Kano
Kuma The King Of Adventure Story
Saikuma Ni Al amin Ahmed Misau wanda nayi
Hidimar Typing din wannan Littafin Domin ya Nishadantar daku.
.
A KARSHE KA/KI AJIYE COMMENTS 3 NA DARASIN DA KUKA DAUKA CIKIN WANNAN LITTAFIN
karku manta Dai
Nidinne
Al amin Ahmed Misau
AA Misau Ke Magana
Admin Na
Zauran Labarai Page
Ke Cewa Sai kuma mun sake hadewa daku a cikin wani sabon littafin Insha Allah

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


4 Comments On KISAN GILLA
avatar
daiy

2 years ago

Reply

Good

avatar
ibrahim-9-5

1 year ago

Reply

Nice thanks a lot

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to ibrahim-9-5

Aha thanks for feedback keep following our site and enjoying our new hot hausa novels

avatar
kabir-mariya

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment