Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigowa kauyen suka gane cewa sun shigo wata nahiyar daban domin
yanayin mutanen da yanayin shigarsu da
al adonsu ya fita daban da irin na mutanen tasu nahiyar
su dai mutanen wannan kauyen suna kama da mutanan birnin hindu kuma
kyawawane kuma fatar jikinsu wankan tarwadace amma kuma wani
irin yare sukeyi wanda su yarima suka kamu da tsananin
mamaki bawa udez ya dubi yarima da
gimbiya yace waishin ta yaya muka iya isowa wata nahiyar haka
acikin kankanin lokaci ku dubi mutanan nan fa ku gani sai kallonmu sukeyi kamar baso kasance mutane
irinsu ba dajin wannan batu sai gimbiya musaira
tayi murmushi ba tac komai ba shi kuwa yarima
sai ya numfasa yace shin ka manta da wanda ya
bamu umarnin hanyar da za mubi acikin tafiyar
tamune?
Tabbar tafiyar tamu aikine na tsafi bako karinmu bane gimbiya koba haka bane?
Maimakon gimbiya tace wani abu sai ta tabe fuska
ta kau da kai Al amarin da yasa yarima yaji
haushi kenan yace wai me wannan yarinyar take nufine?
Idan takamar ta sarauta ai nima dan sarkine
kuma gashima ni da ita yan uwane ko kuwa jan aji take yi mini irin nasu
na mata to ai ban nuna ina sonta ba duk da cewa
ban taba ganin mai kyanta ba ni kam bazan taba son macen
da ba itace ta nuna mini so ba wannan shine Ra ayin Guyson nima,
gama aiyana hakan keda wuya sai bawa udex
ya dubi yarima yace ya shugaba na muje muci abinci
sannan mu sayi dawakai kamar yadda sarkin
yaki ya umarcemu don ya gargademu akan kada
mu kuskura mu kwana a nan
koda jin haka sai yarima ya gyada kai yace kwarai
kuwa gwara daka tuna mana kuzo muje nan take
yarima ya nufa wata rumfa inda ake siyar da abinci cikin
hanzari
bawa udex ya bishi sannan musaira tabi
bayan udex tana yanga a lokacin da gaba dayan
mutanan dake wajan suka kura mata idanu ba komaine
yasa mutane ke kallon gimbiya ba face yadda tayi
shigar mza a matsayinta na ya mace a wannan lokaci
ta saki gashin kanta ya zuba har kasan kankwasonta
kuma ta cire rawanin da ya rufe fuskarta kuma ta
cire mayafin da ya lullube jikinta wanda ya rufe dukkan
siffofin jikinta na 'ya mace da isarsu sai suka iske wata tsaleliyar budurwa tana
rabawa kwastomominta abinci musaira na ganin
wannan budurwa sai zuciyarta ta buga da karfi
nan take taji kishi ya turnuketa saboda bata taba
ganin mace mai kyan taba
budurwar ta kasance doguwa abar kwatance
wacce babu 'da namijin da zai ganta bai dimauceba
koda budurwar taaga shigowar su yarima sai ta
taho da sauri taryesu kamar wacce taga shalakinta,
cikin girmamawa ta gaishe su a cikin yarensu tana mai cewa lale marhaba da mutanan
birnin madinatul haswar cikin tsananin mamaki suka kyra mata idanu
duk su ukun yarima ya dubeta yace ya akayi kika iya yaranmu kuma ta yaya kika san daga inda mukazo
koda jin wannan tambaya sai budurwar tayi dariya
sannan tace uba na bafatake ne tun ina da shekaru bakwai yake zuwa dani
ga rinku fatauci akwai lokacin da muka shafe shekara
biyu da rabi a birninku a lokacinne na iya yaranku amma fa kunsha tafiya domin
daga birninku zuwa nan tafiyace ta kwana sitttin
da
uku koda jin wannan batu sai su yarima suka sake
kamuwa da tsananin mamaki amma sai sukayi shiru basu ce da ita komai ba
budurwar ta dubi yarima cikin tattausan murmushi wanda ka iya sabauta matashi
tace ammafa kai da wannan budurwar kona kama yar uwarka ce ko?
Kafin yarima ya budi baki ya bata amsa sai gimbiya
ta tari numfashinta tace kinga ba hirace ta kawo mu
ba abinci zaki bamu muci a kan hanya muke
dajin haka sai budurwar ta bata rai tace kwantar da hankalinki ba son dan uwanki nake ba
sanin darajar kwastomoni ce tasa kikaga
Ina magana dashi anan garin nafi zinare daraja maza
da yawa sun mutu saboda ni ki bincika kiji
koda jin haka sai gimbiya ta bushe da dariya tace
ai banyi mamaki ba tunda nan kauyene
budurwar tace kwarai kuwa ai a birnima babu
kamata idain kuma akwai kaini na gani sama da sarakuna
dari sunzo daga birane neman aurena basu samuba
cikin mamaki yarima ya dubi budurwar yace meye sunanki?
Budurwar tace bazaka jishi ba daga bakina ba
ka tambayi kowa koda yara kuwa domin ni fitacciya ce a wannan nahiya gaba daya
duk fadin kauyan nan babu mai arziki na kaso
tamanin na kasuwarnan tawace yarana ke gudanar da ita
dajin haka sai gimbiya tayi dariya tace amma
kika boye da siyar da abinci
budurwar tayi murmushi tace kamar yadda mahaifinki ya buge da nunawa dan uwansa kauna
har yaci amanar sa ya kashe shi don ya hau
karagar mulki haka nima na buge da wannan sana'a
don cika wani babban burina na duniya ni
marainiyace ba uwa ba uba sai dukiya dolene
na cika burin da iyayena suka mutu a kansa.
Koda jin wannan batu sai jikin su yarima yayi
sanyi matuka musamman gimbiya musaira domin
sun kuyar da kanta tayi kas tayi shiru bata kara
cewa uffan ba saboda tsananin mamaki har budurwar ta kawo musu abinci suka gama kimtsawa dayansu bai kara cewa
ko mai ba.KISAN GILLA
Littafi Na Uku (3)
Part C.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa... sun kare cin abincin ne yarima ya yafito
kyakkyawar budurwar da hannunsa ta taho gareshi fuskarta cike da annuri
da murmushi nan take a karon farko yaji kibiyar
soyayya ta sokeshi domin kyawunta ne ya riba ceshi baisan sa adda ya mike tsaye ba
kuma ya risina a gareta yace ranki ya dade nawa ne
kudin abincin mu?
Koda jin wannan tambaya sai budurwar tayi
murmushi tace bana bukatar ko sisi daga gareku nasani
cewa zaku sayi dawakai guda uku don ci gaba
da tafiyarku zan baku kosassun dawakai kyauta
ya kai yarima ka bar kudinka hatta guzuri ni zan baku duk abinda kuke bukata
har yarima ya budi baki zaice wani abu sai budurwar ta
tari numfashinsa tace kar kace komai saimun isa gidana ku biyoni muje
cikin fushi gimbiya musaira ta dubi yarima tace
wai akan wani dalili zaka dauki amincinka ka bata alhalin yau ka fara ganinta
shin kasan irin nufin da take dashi akanmu dajin yadda tasan komai akanmu
matsafiyace baka tunanin cewa zata iya cutar damu?
Har yarima ya budi baki zaice wani abu sai
budurwar ta tari numfashinsa tace ni bana tsafi amma kusani wanda ya umarceku
da zuwa nan kauyan shine ya sanar dani komai
naku kuma zan taimakekune bisa wani alkawari dake tsakanina dashi bisa wani
taimako da zaiyi min akan cika burina
koda jin wannan batu sai jikin gimbiya yayi sanyi tayi shiru bata kara cewa komai ba
nan take kyakkyawar budurwar ta kirawo wadansu yaranta mata su uku ta basu umarnin
yadda za a tafiyar da komai ba tare da bata lokaciba
matan suka risina suna masu amsa umarni daya daga cikin su ta dubeta tace ranki
ya dade gimbiya yaya batun bakon ki dake can bayan gari
koda jin wannan tambaya sai budurwar tayi murmushi
tace duk abinda ya bukata ayi masa koda bana gari
gama fadin hakan keda wuya sai ta juya ta nufi har cikin garin kauyan cikin hanzari
yarima da bawa udez suka bi budurwar ita kuwa
gimbiya musaira sai ta dan noke ta dubi daya daga cikin yaran nata tace me yasa
naji kin kirata da suna gimbiya
matar tayi murmushi tace ai sarkin garinmu kanin uwartane
musaira ta gyada kai tace to menene sunan ta na asali budurwar tace sunanta Gimbiya Lasmin.
Musaira ta tabe baki cikin alamun kishi ta kara gaba
yar doguwar tafiya kadan sukayi suka iso gidan gimbiya
lasmin a gaba daya kauyan babu wani gida mai
girma da kawatuwa kamarsa, babban abinda ya daurewa su yarima kai shine duk
inda suka ratsa a kauyan sai suga ana zubewa Gimbiya ana kwasar gaisuwa duk inda suka iske tsofaffi ko almajirai sai suga lasmin na ta fiddo kudi a jikinta tana rabamusu
suna tay mata godiya kamar za suyi mata sujjada
da isowarsu gidan nata sai ta wuce da su kai tsaye zuwa inda bargar dawakar take da shigarsu cikin
bargar suka iske wadansu kosassun fararen dawakai guda hudu lasmin ta dubi
udez da gimbiya musaira tace kowannan ku
ya zabi doki guda daga cikin guda hudunnan
ba tare da gardamar komai ba kowa sai dukkaninsu
suka zaba nan da nan aka daurawa dawakan siddi
har da guda dayan da ya rage kuma aka kawo jakunkunan guzuri guda
hudu ko da ganin haka sai yarima ya dubi gimbiya lasmin cikin alamun rashin fahimta yace waishin kina nufin tare dake zamuyi
wannan tafiya dajin wannan tambaya sai
lasmin tayi murmushi tace
ai dolene ma ayi wannan tafiyar tare dani saboda nice kadai nasan inda zamuga mahaifiyarka
tabbas nasan garin da take amma bansan a inda zamu ganta ba duk da cewar
sarkin yaki ya kwatan ta mini kamanninta abune mawuyaci na shaidata abu daya ne zai taimaka mana mu sameta muga irin
sarkar wuyanka a wuyanta ka sani cewa dole sai na biku sannan zan iya cika nawa
burin bamu da wani isashshen lokaci yanzu domin nan da cikar sa a biyu dakarun sarki zamaru masu farautarku zasu iya
isowa garin idan kuma suka riskeku anan komai ya rushe
koda jin wannan batu sai yarima gimbiya da bawa udex sukayi sauri suka kama dawakansu suka haye suka rataya
jakunkunan guzirinsu a gadon bayansu itama lasmin sai tayi hakan ta wuce kan gaba suka
bita a baya suna masu zaburar dawakansu da gudu
kamar yadda gimbiya lasmin ta fada haka al amarin ya kasance.
Wato suna barin kauyen da ta zarar sa a biyu da rabi sai ga
rundunar dakarun sarki zamaru sun iso dauke da zanen
fuskokin su yarima
nan fa sukayi ta yawo a cikin kauyan kwararo kwararo lungu da sako suna nemansu
amma saboda an ga su yarima tare da lasmin babu wanda ya
amsa cewar ya gansu haka dai suka gaji da yawon nema suka hakura
sai da su yarima suka shafe kwanaki biyar
suna ratsa dazuzzuka kuma basa ya da zango face
idan dare yayi da yammaci kwana suke iske wani babban birni
da ake kira
Darul Kushuf
birnine babba wanda yafi birnin madinatul hashwar girma da kawatuwa suna
shiga farkon garin suka gane cewa mulkin zalunci akeyi domin bayi suka gani maza da mata suna ta aikin bauta
na gina wani dogon gida dakaru na tsaye a kansu duk wanda ya sare sai kaga an zabga masa wata murtukekiyar bulala mai kaurin gaske sai
dai kaga bayan bawa ya kwaile jini
na zuba yana ihu nan take su yarima suka kamu da tausayi
da takaici cikin hanzari
lasmin ta juya ta dubesu tace A cikin rada duk abinda ya faru kuji ku gani
amma babu ruwanku da kowa da isowar su bakin kofar
birnin sai dakaru suka tare su cikin hanzari gimbiya lasmin ta zuba hannu cikin
aljihunta ta fiddo zinare dubu ta mikawa masu gadin kawai sai
aka bude musu kofa suka kunna kai ciki ba tare da an caje suba don tabbatar da tsaro kai tsaye suka nufi cikin birnin lasmin nayi musu jagora
kai da ganin yadda lasmin ke kutsawa dasu
ta cikin lunguna kasan cewa ita yar gari ce
haka kuma Al amin Guyson ma Dan garine
wajan son kawo muku labarai na litattafan yaki, sai da sukayi tafiya ta a kallah
rabin sa a sannan suka iso wani bakatafaren gida
zaune a kofar gidan wani attajirine bisa wata kujera ta alfarma hadimai
sun kewayeshi koda attajirin ya hango su
gimbiya lasmin sun durfafeshi sai ya mike tsaye
zumbur da sauri cikin matukar farin ciki ya
nufosu da gudu har yana tuntube cikin girmamawa
attajirin ya kamawa lasmin dokin ta ta sauka tana mai
yi masa marhaba nan take aka kaisu masauki
suka zauna suka huta kuma suka ci suka sha
bayan sun huta attajirin ya shigo babban falon dasu
gimbiya lasmin ke zaune ya zuba a gabanta wanwar yana mai
tankwashe kafafunsa yace ranki ya dade yau kuma
wace bukata kikazo da ita kin sani cewa a shirye
nake na biya miki ita koda kuwa zan rasa rayuwata
a dalilin haka sa adda lasmin taji wannan tambaya
sai tayi murmushi tace na zone neman wata bakuwar
mace a garinnan wacce a halin yanzu ta shekara ashirin da biyar anan tana rayuwa
kuma ta zone daga birnin madinatul hashwar sunanta shamslat ta kasance matar marigayi sarki hisham kuma gudun hijira tayi daga can birnin don tserar da rayuwarta
koda jin wannan batu sai attajirin yayi shiru
yana jinjina kai gami da tunani har izuwa tsawon
yan dakiku sannan ya dago kai yace ranki ya
dade gano wannan matar sarki acikin wannan
babban birni namu abune mai wuyar gaske tunda
ma babu tabbacin tana nan a raye inda ace akwai
wata shaida da za a iya shaidata to da bamu da matsala
caraf sai yarima yace akwai shaida tana da wata irin sarka irin wannan dake wuyana
nan take yarima ya zaro sarkar daga cikin wuyansa
sarkace wacce aka yita da zallan karfen lu u lu u kyan hatimine na gidan sarautar birnin
madinatul hashwar a jikinta koda ganin wannan sarkar sai attajirin ya kurawa sarkar
idanu ya fada kogin tunani daga can sai ya dago
kai yace na taba ganin wata baiwa da irin wannan sarka a can gonar sarki dake bayan gari
kimanin shekaru takwas baya tana aikin bauta a wannan lokaci wani badakare ya cafi sarkar a wuyanta ya fisgeta saboda
tsananin fusatar da tayi sai ta gabza masa wawan naushi ya zube kasa sumamme nan fa dakaru suka
rufeta da duka suna neman sumar da ita nine na ceceta
na basu kudi suka kyaleta koda na tambayeta
matsayin sarkar a wajanta sai tace dani gwara a raba ta da ranta akan a rabata
da wannan sarka
Al amin Ahmed Nake Guyson Kenan A square
koda jin wannan labari sai yarima ya rugo ga attajirin yace
yanzu a ina kake ganin zamu iya ganin wannan mata
attajiri yace ai duk bawan da aka kaishi bauta
wannan gidan gona ta sarki sai dai gawarsa ta
fito
abu daya ne zai iya sawa a fito da ita ba komai bane
face kudi
a garin nan kudi yafi komai daraja shi kansa sarkinmu
ana siyan sa da kudi
koda jin haka sai farin ciki ya kama su yarima
gimbiya lasmin tace gobe da safe zaka kaimu wannan gidan
gona ta sarkinku bana son mu baiyana bukatarmu
kai tsaye kawai mu siye dukkanin dakarun dake aiki
a gidan gonar mu samu izinin ganin gaba dayan bayin
dake gidan da zarar mun sami damar hakan kai yarima
zaka fito da sarkar wuyanka fili yadda matar zata iya gani
Attajirin yayi murmushi yace tabbas wannan
itace kadai hikimar da zamuyi mukai ga nasara
kashe gari kuwa tun kafin alfijir ya keto su gimbiya
lasmin suka yi shiri attajiri yayi musu jagora suka durfafi gonar sarki da isarsu
aka kirawo shugaban dakarun dake gidan gonar tare da duk kan yaransa
tashin farko sai lasmin ta kebe da shugaban ta bashi
kyautar dinare dubu goma sannan ta bashi
wadansu dinaren dubu uku tace ya rabawa yaransa saboda murna da mamaki
sai jikin shugaban ya kama karkarwa ya zube kasa yana godiya lasmin na fada masa
bukatarsu ya amince nan take aka bude musu gidan gonar suka shiga sannan aka
tara gaba dayan bayin a gabansu
nan take yarima ya fiddo da sarkarsa waje
tana reto akan kirjinsa ya shiga duba bayin a lokacin da suka jeru a kan sahu
amma sai ya nufi bangaren da aka tara mata zallah ya kama kewayasu
sai da ya rage saura sau uku kacal ya gama kewayasu
sai ya tsaya cak a lokacin da ya gifta wata babbar mace
wadda yaga ta kura masa idanu ko kiftawa batayi
nan da nan idanuwa suka ciko da kwallah jikinta ya kama tsuma
amma kuma bakinta na karkarwa ta kasa magana
yarima ya dawo da baya ya tsaya cak a gabanta
matar daf da daf yadda suna iya jin numfashin juna suka ci gaba da kallon juna kawai
daga can sai matar tayi wuf ta bude rigarta saiga sarka
irin ta yarima a kirjinta kawai sai ta rungume yarima ta fashe da
kukan farin ciki tana mai cewa tabbas na sani cewa
indai ina raye sai na sadu da
Kai ya dana yau shekara ashirin da biyar kenan ina
begenka a zuciyata kuma kullum ina mafarkinka a barcina ko
yanzu na mutu burina ya cika bani da sauran takaici
koda jin wannan batu sai yarima ya fashe da matsanancin
kuka yana mai rungume ta a kirjinsa yace
nima haka na kasance a cikin begenki da son ganinki tun da naji labarinki
ban san dadin uwa ta jini ba amma yanzu da na sameki zan sanshi nan
take kowa dake wannan wuri ya kamu da tausayin
yarima da mahaifiyar sa sakamakon jin irin kalaman da suke furtawa
duk tsananin rashin imani na dakaru dake tsaron wannan gona sai gashi wasunsu na zubar da hawaye wasunsu idanuwansu sun ciko da kwallah
nan take shugaban dakaru ya dubi yarima yace
yakai wannan saurayi ma abocin sadaukantaka
kayi sani cewa bawa baya fita daga gidannan idan ya shigo idan bawa daya ya bace indai ba gawa ya zamo ba ne da dakarun zamu iya rasa rayuwarmu
amma domin mu hada wannan da da mahaifiyarsa
wadanda suka rasa juna tsawon shekaru ashirin da biyar da
sadaukar da rayukanmu koda jin wannan batu
sai gidan gonar ya rude da shewa shugaban dakarun ya daga
hannu akayi tsir sannan yace kai a yau mun sallami gaba dayan bayin
gidannan mun basu yancinsu munma duk tarwatsewa zamuyi yana gama fadin
haka sai aka bude gidan gonar bayi suka fice
suna ihu da murnar samun yanci wasu bayinma
saboda farin ciki sai suka zube kasa suna suna kuka
ba tare da wani bata lokaci ba sai yarima ya dora
mahaifiyarsa akan dokinsa lasmin munaira da bawa udez
suka rufa masa baya suka juyo da baya izuwa hanyar da
zata kaisu wani birnin daban don kada sarkin wannan gari ya sami wannan labari ya turo a kamasu
cikin tsananin farin ciki
sukayi ta tafiya ba sassauci har rana ta fadi a sannan ne suka yada zango
a bakin wata korama domin su kwana a wurin
in yaso kashe gari ya soma duhu amma idanu na shaida komai
bayan sun daure dawakansu sai suka gangaro gaban wannan korama
domin su sha ruwa kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaji sukuwar dawakai
gua biyu daga cikin duhuwar daji an durfafosu kafin
suyi wani yunkuri sai ga mahayan biyu sun riskesu sunyi turjiya a gaban su
nan fa aka tsaya ana kallon kallo ba wadansu bane wadannan mahaya face sarki zamaru
da boka hizainu nan take hankalin mahaifiyar yarima ya dugunzuma ta fashe da
matsanancin kuka
shi kuwa sarki zamaru sai ya takarkare ya bushe da
mahaukaciyar dariya yace ke tsohuwar banza ai yanzu kika fara kuka kuma ba
zaki daina ba har izuwa karshen kwanakinki na duni
.
A nan Littafin Kisan Gillah 3 yazo karshe Marubucin
Littafin Yace Mu hadu a Littafi Na hudu Domin jin cigaban wannan labari
amma kafin nan ku meye
ra ayinku dangane da wannan haduwar da akayi
shin suwaye zasu sami Galaba nidai nacee,...... Sai naji daga gareku
,
nidinne dai
Al amin Ahmed Misau
Guyson ko AA Misau
nake cewa mu zama
lafiy
KISAN GILLA 4
Littafi na hudu
Na Abdulaziz sani madakin gini
Ebook creator:- Shuraih Usman 99%
Domin download na wasu kayatattun littatafan Hausa a matsayin Hausaebooks tayadda zaku iya saukewa ku karanta acikin wayoyinku sai ku ziyarci wannan shafi www.shuraih.waphall.com Sannan ku zabi littafin da kuke so

For more download of some non- fictional hausa books as a hausaebooks so that you can download it to your phone and read it at any time (offline reading) then visit our wepsite at www.shuraih.waphall.com Adress and select your books for offline reading
Gargadi:- wannan ebook din bana sai ruwa bane kuma ba anyishi bane don batanci ga wani koh ga wata
Sannan ni shuraih Usman 99% bana tura littafi ta private kuma bana whattsapp sannan banda group a whattsapp ga wanda yaga wani kuskure da muka making acikin wannan littafi sai kiramu akan wannan nombar 08170707521

Ga duk wanda baisan yadda ake downloading na littatafanmu ba sai ya ziyarce mu akan wannan adireshin yanar gizo gizon http://keffians.xtgem.com/forum Sannan yayi tambaya in sha'Allah muku ma zamu mai bayani dalla dalla akan yadda ake sauke littatafanmu
Sannan ina kara maimaitawa bana whattsap kada wani ya ha'ince ku ta hanyar amfani da sunana a whattsap asha karatu lafiya
Hakkin mallaka (m) Abdulaziz sani madakin gini

KISAN GILLA
Littafi Na Hudu (4)
mPart A.
.
.
Marubucin Littafin
Abdul Aziz Sani M/Gini
Typing AA Misau
Ke Magana
.
Labari ya isowa AA Misau cewa...
Kafin sarki zamaru yagama rufebakinsa saiyaji wata murya
daga bayansu tadaka masa tsawa cikin hanzari shida boka hizainu
suka waiga baya dansuga kowaye
bawanibane sukayi arba dashiba
face sarkin yaki amzad bisa wani
gabjejen tsuntsu asama cikin iska
yayi shigar yaki
amzad na sanye dabaki sulke yarataya wata shimfidediyar
takobi agadon bayansa akuibins cinyoyinsa biyu
wadansu gajerun adduna ne guda
biyu rike ahannunsa nahagu wata
farar sandace sandce siririya anyiwa marikanta
siffar kwarangwal nakan bil,adama komai dayake jikinsa
bakine hatta takalmansa da garkuwarsa
kuwa shikansa sarki zamaru saidaya dan firgita daganin sarkin yaki amzad
acikin wannan gagarumar shirin yaki don baitaba ganin yayi
irintaba duk irin yake yaken dayake fita nanfa aka fara kanlan kallo shamilat da sarki zamaru suka kurawa juna
ido tanamaida dakamada harara
cikin tsananin kiyayya saboda sanin cewar shine yakashe mata
miji yarabata da danta kuma ya
jefa rayuwarta cikin kunci
dawuya tsawon shekaru ashirin
dabiyar shima sai yarinka yiwa sarki zamaru irin wannan
kallon har jikinsa yasoma tsuma
yarinka kamar yazare takobi
ya afkamasa shidai sarki zamaru
babu wanda yake jin haushi kamar sarkin yaki
amzad domin tunda ya kura masa ido ko giftawa baya yi
kuma saboda tsananin kiyayya a zuci sai da fuskar
sarki zamaru ta rika yin gatsine
bayan anyi wannan kallon kallon na tsawon
yan dakiku sai sarki zamaru da boka hizairu suka
dubi junansu suka bushe da dariyar mugunta
sannan boka hizainu ya dubi sarkin yaki amzad yace
kai karamin kwaro kayi wani cewa ai tunda ka kasa hanamu
ganin bayan mai gidanka marigayi sarki
hisham to kaima ba zaka gagaremu ba ina mai tabbatar maka da cewar
anan wajen zamu gama da kai sannan mu gama da
wadannan yan tsakin na rantse da darajar tsafi a halin
yanzu babu wani mahaluki a doron kasa walau
mutum ko aljan wanda ya isa ya hanamu kammala
cika babban burin mu a rayuwa, koda boka hizainu
yazo nan a zancensa sai sarkin yaki Ya numfasa
yace
kai tsohon azzamuli maci amana kuma butulu
kayi sani cewar ramin karya kurarre ne kuma komai nisan jifa kasa zai
fado ina mai tabbatar maka da cewar kafin nabar
wannan duniya sai na tabbatar da cewar wannan yaron
ya dauki fansar ran mahaifinsa a kanku kuma sai
ya tarwatsa wannan burin naku na banza wanda
dai dai yake da mafarki gama fadin haka ke da wuya
sai boka amzad ya zunguri cikin tsuntsun da yake zaune
akai take tsuntsun yazo gaban su yarima ya sauka wato
ya fuskanci su sarki zamaru sannan ya dubi bawa udez da shamilat yace musu
ku koma can jikin dotsen dake bayan bishiyar can ku
zama yan kallo kada ku kuskura ku motsa daga wajen
da kuke duk bala 'in da za a yi kada ku firgita kuyi
yunkurin guduwa domin kuwa yunkurin yin hakan zaku
fada hannun wadan nan makiyan namu da jin wannan
batu sai bawa udex da shamilat suka bi umarnin suka
ruga can wajen da sarkin yaki amzad ya umarcesu jikinsu
yana rawa suka waiga cikin alamun matukar tsoro
bayan sun isa jikin bishiyar sai sarkin yaki amzad
ya dubi lasmin yace
Ranki ya dade ga wanda kika shafe shekaru goma kina
farautarsa wato makashin mahaifinki gashinan
a gabanki wato sarki zamaru kamar yadda na baki
labari a baya cewar wanda ya kashe mahaifinki na jikinsa
ne kuma amininsa wanda ya yarda dashi fiye da kowa
a harkokin kasuwancinsa ki sani cewar domin ya
danne dukiyarsa ne kimanin dinare miliyan dubu
casa'in da biyar ya kashe shi har izuwa yanzu babu
wanda yasan komai akan lamarin face ni kadai kuma ina
da cikakkiyar shaida har guda biyu akan kisan gillan da
yayi wa mahaifinki da kuma shaidar kudin da ya bashi
har da lokacin daya bashi da wurin da suka hadu
domin
Al amin Ahmed Misau, gabatar da wani babban
kasuwanci a birnin sin
ranki ya dade kinga kenan yanzu abu biyu ki ke nema
a wajen sarki zamaru na farko kina neman kudinki
da kika gada a wajan mahaifinki sannan kuma kina
neman fansar ran mahaifinki don haka babu abun
bukatar mu fara kashe sarki zamaru a yanzu har
sai kin fara karbar wannan dukiyar taki abinda yanzu nake da bukata mu kamashi
a raye mu tsare shi a wajen mu muyi ta gana masa azaba
har sai ya fadi inda wannan dukiyar take daga nan sai
mu farwa karagarsa
shi kuma wannan tsohon azzalumin boka
hizainu dake tare da shi yanzu take zamu maida labarinsa
tarihi koda sarkin yaki amzad yazo nan a jawabinsa
sai sarki zamaru tare da bokan hizainu suka bushe
da dariyar mugunta a lokaci guda tsawon yan dakiku
suna dariyar sannan sarki zamaru ya turbune fuskarsa
yace
Ai inda ba kasa a nan ake gardamar kokawa kawai
ku zo muyita a kare a nan domin banga amfanin hutun
jaki da kaya ba koda jin wannan batu sai sarkin yaki
amzad ya dubi yarima da nashmirat yace
ni ku barni da boka hizainu ku kuma ku tari sarki
zamaru ke kuma gimbiya sai dai ki zama yar kallo kuma
kada ki kuskura kice zaki saka hannunki a cikin wannan
gumurzu da za ayi komai rintsi da tsanani kada ki ce zaki
yaki mahaifinki saboda na
Tabbatar da cewar shima ba zai taba cutar dake
ba ko rayuwarki koda sarkin yaki amzad yazo nan a
zancensa sai idanun gimbiya nasmirat suka ciko da
kwalla har hawaye ya subuto mata kawai sai ta
dubi amzad tace
bazan iya kallon abinda zai faru ba a nan zanso na bar
wajennan in da hali sarkin yaki ya numfasa yace
ai wannan ba matsala bane nan take tsuntsun amzad ya
sauko bisa turba ya sauko

4 Comments On KISAN GILLA
avatar
daiy

2 years ago

Reply

Good

avatar
ibrahim-9-5

1 year ago

Reply

Nice thanks a lot

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to ibrahim-9-5

Aha thanks for feedback keep following our site and enjoying our new hot hausa novels

avatar
kabir-mariya

1 year ago

Reply

Tnx alot

Please Login or Register in order to submit comment