Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mance ne ban tambayeki inda akayi miki wannan
zanen kunshin ba.
.
Har zuwa lokacin da farida ta shiga farfajiyar dan
daudu Amara idanunta basu daina nuna mata
hannayen safiyya akan kafadar masoyinta ba.
.
Salamun Alaikum......sannunku farida tayiwa Fadila da
mama sa'ar data shigo falon.
Dan Allah anan ne ake kunshin nan?
Fadila ta dubeta da murmushin yake domin haryanzu
sanyi takeji.
Eh nan ne kema saiki jira mu ma shi muke jira.
Zaman farida keda wuya saitaji wata irin iska mai
sanyi ta fara ratsa kashi da bargonta nan da nan taji
jikinta ya fara rawa.
Kai wannan wane irin sanyi ne?
Mu ma haka muka tarar dashi mama tace cikin
damuwa sannan saita dada da cewa ko waje zamu
fita mu jira shi
Ina ganin dai gaskiya zaifi fadila tace ta fara mikewa
kenan.
.
Sai sukaga wani irin farin hayaki ya rufe kofar dakin
sassanyar iska taci gaba da hurowa cikin dakin.
.
Me kuma zakuyi awaje bayan gani nazo ko bani kuke
jira ba kanne na?
Wata zazzakar murya tace dasu daga cikin hayakin.
** ** ** ** **
Matan uku suka dubi kofar dakin a tsorace cikin
tsananin firgici sannan ga mamakinsu sai sukaga
hayanin ya washe kamar ma ba'a halicce shi agurin
ba.
Sannunku da zuwa.
Amara dan daudu yace dasu shine a tsaye akofar
dakin maimakon farin hayakin. Nashiga uku mama
tace tana duban amara a tsorace wannan wane irin
hayaki ne amara duk kabi ka tsorata mu.
Kuyi hakuri kannena dan daudu amara yace dasu.
Wani sabon sinadari ne mai sanyin hayaki nake
turara mutane dashi kafin nayi musu zane idan akayi
haka yafi fitowa rangadadau. Da kuka shigo bakuji
sanyi ko ina ba?
Matan uku suka dubi juna sannan sukayi ajiyar zuciya
munji suka amsa baki daya. Amara ya dube su da
murmushi wacece tafara zuwa acikin kannen nawa?
Fadila ta mike tsaye gamida duban agogonta har
yanzu jikinta rawa yakeyi batasan abinda yasa ba
amma har yanzu a tsorace take duk da yake wannan
shine karo na kusan hudu da za'ayi mata kunshin
sa'ar data dubi Amara saitaji gaba daya hankalinta
bai kwanta dashi ba.
Muje to nafara dake kanwata Amara yace da fadila
sa'ar da yaga ta mike tsaye Suna nan zaune acikin
Dakin Amara yagama zane kirjinta yadawo zuwa kan
cinyoyinta. Yau naga kamar baka son hira Amara
kamar ba kai ba ko baka ganeni bane?
Fadila tace dashi
yi hakuri yar uwata ai ina shigowa na ganeki....wallahi
dan karin kudin sinadarin aikin nan ne aka samu duk
yabata min rai.
Bayan wani lokaci mai dan tsayi Amara yagama zane
Fadila da mama wadanda suka dawo dakin jiran
kusan jikinsu tsirara suka zauna akan wani kilishi mai
taushi acan karshen falon domin su jira zanen ya
bushe kafin kuma daga baya su wanke sannan sai a
goga musu sinadarin Hydrogen wanda shike sa zanen
yayi baki adaidai lokacinda amara yana can cikin daya
dakin yana zane Farida.
Ana cikin wannan hali ne kofar falon dake fuskantar
waje ta bude sannan Fadila da mama suka yi duba I
zuwa abunda ya dada sasu cikin firgici a tsaye abakin
kofar dakin AMARA ne sanye da doguwar
Jallabiya fara.
.
Sannunku da zuwa Amara yace dasu yana kallon
zanen kunshin dake kan cinyoyinsu da kirjinsu.
Mama ta dube shi cikin kaduwa tace Sannunmu da
zuwa ina...yaushe ka fito daga dakin harka fice waje
bamu ganka ba?
Amara ya dubi mama cikin mamaki yace Ke Ja'ira
kada kiyimin sharri ni rabona da gidan tun safe ina
kasuwa ruwa ya rutsani sannan sai ya kalli zanen
kunshin dake jikinsu yace.
Wanene yayi muku wannan ku kukayi da kanku? Kada
ka raina mana hankali mana ba kai ka gama yi mana
zanen ba ina dayar da kakeyiwa? Inka gama mata ai
gara kazo kasa mana Hydrogen din nan ko ma tafi
mun dade anan mama tace.
Ki rufamin asiri in mutu yan mata su kaini kinga ni
tun da gari ya waye yau banyiwa kowa zanen kunshi
ba.
Jin haka keda wuya sai Fadila ta mike tsaye a tsorace
ta dubi Amara tace.
Kana da dan uwane yan biyu?
Amara ya girgiza kai kafin tagama magana sai sukaji
acan daya dakin Farida ta kwala ihu nan da nan su
uku suka nufi dakin a tsorace suna shiga dakin suka
tarar da Farida rabin jikinta tsirara an gama zaneta
cinyarta dayace kawai ta rage babu zane.
A ina yake mama ta tambaya a tsorace farida ta
dubesu cikin kuka tace YA ZAMA HAYAKI.
.
Amara ya dubi sararin samaniyar dakinsa sai ya
hangi sauran farin hayakin a makale.
Na fada muku bani bane
to in ba kaibane wanene? Fadila ta tambaye shi
kamar zata fashe da kuka.
Hahahahhaha wata kakkausar murya ta fashe da
dariya sannan sai sukaji daga sama ance
KUNYI KUNSHIN KARSHE YAN' MATA.
.
BABI NA DAYA 1
Hayaniyar biki gamida farin cikin ganin Faisal ya zama
nata su suka mantar da Amarya Fadila rudanin daya
faru agidan dan daudu Amara da farko sa'ar da aka
shiga hayaniyar bikin duk kusan minti biyar sai gaban
Fadila ya fadi idan ta tuna sa'ar da kakkausar muryan
nan ta kece da dariya to amma daga baya sa'ar da
kawaye da yan uwa gami da abokan arziki suka
zagayeta sai zuciyar Fadila ta shagalta izuwa shagalin
bikinta to amma fa duk da haka jifa jifa takan tuna
kalmar Amara sa'ar da kakkausar muryar ta kece da
dariya.
Meye naga kunyi wani zuru zuru daku kamar kunyiwa
sarki karya? Amara yace dasu sa'ar dayaga matan
ukun sun dubi saman dakin a firgice.
Kaga dan Allah amara idan wani ka boye yake bamu
tsoro to kace ya bari ni wallahi bana son irin wannan
wasan mama tace dashi.
Yau na shigesu ni Amara kinjini da yan mata wai
maganar me kuke ne?
Kai kurma ne bakaji dariyar da akeyi a saman dakin
nan ba?
Duk abinda akeyi Fadila na gefe jiki na rawa kamar
mazari ita ko magana bata iyayi jim kadan da gama
maganar mama sai farida ta ruga aguje ta fice daga
dakin ganin haka sai fadila da mama suma sukabi
bayanta a gurguje suma suma fice daga cikin gidan.
Yau Allah ya hadani da mahaukatan mata oh ni 'yasu
in da ranka kasha kallo amara yace sannan ya taba
cinya gami da shewa abinsa.
.
Kanwata. Mama tace Fadila a daidai lokacin da suka
zo karshen munafikin lungun in ba damuwa ki bani
lambar wayarki mana make gaisawa ba dan komai
mama ta tambayi lambar wayar fadila ba sai don
kawai taji aranta tana kaunarta domin tana son taga
farar mace kyakkyawa domin wannan shine kawai
abinda ya ragu a jarinta na karuwanci.
Kawo wayarki nasa miki fadila tace da mama tana
kallonta rabi a tsorace rabi kuma a yatsine tabbas
mama bata kwantawa fadila azuciya ba domin tun
sa'ar da mama ta shigo ta sameta a falon dan daudu
fadila ta lura da tambarin bariki akan fuskar mama.
In badan rudanin daya samesu tare ba da babu
abinda zaisa fadila ta baiwa mama lambar wayarta.
Nagode bari nayi miki Flashing saikiyi sebin din
lambata mama tace sa'ar da fadila tasa mata lambar
wayar.
Mintuna uku da faruwar haka fadila shiga cikin Jeep
dinta ta wuce mama tsaye abakin titi tana jiran tasi.
Mama ta dagawa fadila hannu amma fadila bata
damu da ta rama mata ba.
.
Duk wannan al'amura sun zama tarihi a gun amarya
fadila anyi biki lafiya an tashi lafiya an kaita dakin
mijinta babban masoyinta Faisal mutumin da take
kauna fiye da kowa aduniya. Adaren amarcinsu na
farko bayan kawaye da abokan ango sun tafi sun
barsu su kadai daga fadila sai angonta faisal wanda
shima mahaifinsa na da abin hannu amma bai kai
mahaifin Fadila ba.
Awannan dare ne to abinda Fadila ta dauka tamkar
wani shudadden mafarki kokuma wata binnanniyar
gawa ya fara FATALWA.
Zaune suke a dakin kwanansu akan wani fankadeden
gado na alfarma wanda akalla zai iya daukan mutum
biyar batareda kowa yaji hucin dan uwansa ba.
Fadila ta dubi faisal sannan faisal ya dubi fadila sai
suka fashe da wata tattausar dariya lokaci guda cikin
farin ciki.
Dariyar me kakeyi?
Ke dai zan tambaya dariyar me kikeyi? Masoyan suka
sake yiwa juna murmushi
Faisal barci nakeji.
Fadila tace dashi tana lumshe idanu cikin wata
shagwababbiyar murya.
To ki kwanta mana ko so kike na kwantar dake
Uhm fadila tace gami da gyada kai.
Faisal ya matso kusa da ita ya dora hannayensa
akan kafadarta cikin
murmushi sannan yafara kokarin kwantar da ita.
Uhm Uhm ni ba anan zan kwanta ba Fadila tace tana
wata girgiza cikin shagwaba.
To fadila a ina kike son kwanciya?
Anan fadila tace gamida nuna cinyoyinsa.
Faisal ya fashe da dariya fadila kenan duk fadin
gadon nan ki rasa inda zaki kwanta sai akan cinayata.
Nidai anan zan kwanta fadila ta kuma fadi cikin
shagwaba
faisal yayi ajiyar zuciya sannu ahankali sai fadila ta
kwanta akan cinyarsa ta yadda fuskokinsu zasuke
kallon juna fuskar faisal dauke da faffadan murmushi
ya kamo santala santalan hannayenta Fadila.
Ya kallesu sannan sai ya dubeta cikin mamaki.
A ina zanen kunshin da nace inason kiyi min duk
ranar da za'a kawomin ke?
Fadila taji gabanta ya fadi ras da faisal yasan abinda
maganar zata janyo da baiyi ta ba. Nan da nan sai
wani zazzafan gumi ya fara sartu akan dogon wuyan
fadila hankalinta ya tashi tunaninta ya yamutse lokaci
guda kuma ta fara tunanin irin karyar da zatayiwa
faisal domin tasan haryanzu akwai shatin zanen da
aljanin nan yayi ajikinta to saidai bai fito sosai ba
domin ba shafa masa sinadarin hydrogen ba sa'ar da
gayyar ta watse gashi kuma bata san ta sabawa faisal
dan tasan yanada zafin zuciya idan ranshi ya baci.
.
Yaya naji kinyi shiru? Faisal yace da ita cikin
murmushi da kuma mamaki domin ya lura kamar
yanayin fuskarta ya sauya haka nan ta sandare
ajikinsa shagwabar da takeyi baki daya ta bar jikinta.
Nayi ma laifi my darling fadila tace cikin wata
sassanyar murya alokaci guda kuma kwakwalwarta
na kokarin nemo abin fada.
Haba fadila laifin me kikayi min?
Kisan fa ance wai amarya bata laifi koda ta kashe dan
masu gida.
Kunshin da kace nayi ma ne ba'a gama ba muka baro
gidan an gama zanen kenan za'a sa hydrogen
sinadarin dayake sa shi yayi bakin nan sai mama tayi
min waya tace nayi maza na koma gida ana jirana
duba ka gani zaka ga ma shatin zanen Fadila tace
lokaci guda kuma ta mika masa hannayenta tana
daga kwance.
Faisal ya dubi hannayenta cikin murmushi yana
nazarinsu
Fadila kenan ke dai in bakiyi ba kawai shikenan ba sai
kinyimin karya ba ni banga sanen komai ahannunki
ba.
.
Jin haka keda wuya sai fadila ta bar jikinsa ta tashi
zaune.
Haba Darling yaya zanyi ma karya bayan ga.....kalmar
ta makale acikin fatar bakinta domin ta lura ko sama
ko kasa Allah masani amma zanen dake hannunta ya
bace baki daya kamar ma ba'a taba zana shi ba.
Faisal ya dubeta cikin murmushi sa'ar dayaga
kamanninta sun sauya ta firgice cikin sauri ya janyota
jikinsa yana cewa.
Haba Fadila me yayi zafi haka da har zaki tashi
hankalinki adaren amarcinmu na farko? Dan bakiyi
kunshi ba ai ba wani laifi bane nan gaba idan inaso
basai muje duk inda kike so ayi miki ba.
Fadila ta kankame shi gamida ajiyar zuciya ta tabbata
mintuna biyu da suka gabata kafin ta kwanta akan
cinyarsa ta lura da zanen ahannunta tayaya kuma
za'ace ya bace cikin mintina biyu? Tambayar kenan
datayiwa kanta babu Amsa.
** ** ** **
Washegari da la'asar sakaliya misalin karfe biyar da
rabi amarya fadila ta fito daga wanka daure da wani
farin tawul tattausa ajikina tana tafiya tana yauki
kamar zata tsinke ta zauna akan waata doguwar
kujera dake gaban wani kyakkyawan madubi na
musamman da akayi mata shi don Kwalliya.
Tun da garin Allah ya waye fadila ke tare da angonta
suna ta wasanni na soyayya bashi ya fita ba sai karfe
hudu acewarsa abokai zaije yiwa bangajiya.
Kada ka dade don Allah.....ni banason zama ni kadai
awannan katon gidan fadila tace dashi sa'ar daya
shirya zaifita kanta akan kafadarsa.
Bazan dade ba my....karfe takwas ina gida.
To shikenan fadila tace cikin shagwaba
kataho min da wani abu mai dadi
karkiji komai idan zan dawo zan zo miki da TUBANI.
La.. Me zanyi dashi fadila tace cikin dariya tubani ba
shine wanda na karanta a littafin KARYA LINZAMIN
SHAIDAN wai wani tsoho yanaci ba. Ko bashi kake
nufi ba?
Shi nake nufi mana my darling faisal yace cikin
dariya.
Cab. So kake kenan in mutu idan na hadiyi wannan
abin ai sai ankaini asibiti.
Suka fashe da dariya lokaci guda da haka suna tafiya
suna hira hannayensu kamar zasu shafi juna ta
rakashi har farfajiyar gidan inda motocinsu na hawa
guda hudu ke tsaye sunyi jerin sahu faisal ya zabi
wata karama kirar honda ya hau.
Fadila na tsaye a farfajiyar gidan tana daga masa
hannu har saida ya fice.
Lokacin data dawo fankacecen dakin shakatawar na
alfarma saitaji duk kadaici ya lullubeta hakanan duk
saitaji gabanta nata faduwa hakan shiyasata kunna
talabijin sannan ta kamo tashar kasar larabawa wata
balarabiya yar masa masar ce mai katon baki take
cashewa amma katon bakinta bai hana
makwagoronta feso waka mai dadi ba.
Fadila ta lume cikin daya daga cikin kujerun alfarma
da suka zagaye dakin kofin tangaran dauke da
tacaccen lemo ahannunta na hadun taci gaba da
kallon wake waken larabawan wannan shiya dauke
mata damuwa har zuwa sa'ar da taga yakamata ta
tashi ta sake wanka domin taren mijinta faisal tana
fitowa daga wankan sai saita nufi Madubi.
.
Daga inda take zaune ayanzu tana fuskantar madubin
fadila na iya jiyo rugugin aradu sakamakon hadarin
dake lillibe da sararin samaniya hakanan amaryar na
iya hangen shuke shuken alfarma da furanni na
zamani wadanda ke jere sahu sahu a farfajiyar gidan
abin gwanin ban sha'awa sunata rangaji cikin iskar
daminar kamar yan amshin shata.
Fadila ta dawo da hankalinta kan madubin ta fara
nazarin hannayenta da kafafunta da kuma kirjinta
cikin mamaki da fargaba domin ko kusa ko alama duk
shacin zanen nan da akayi mata ya bace babu
alamunsa ko da kankane.
Na rabu da jaraba fadila tace gamida ajiyar zuciya
kana saita shafi goshinta ga maminta saitaga kamar
ta fara gumi sannan ne to ta lura shema na'urar
sanyaya dakin ba'a kunne take ba gashi kuma garin
ya daure babu iska sakamakon bakin dake ta haduwa.
Fadila tasa wani farin mataji ta korashi tsakanin
siraran gashinta sannan ta mike ahankali ta nufi inda
makunnar na'urar sanyaya daki take ta kunna sannan
ta dawo gurin zamanta ta zauna taci gaba da shafe
shafe irin na mata batafi k minti guda da zama ba
saitaji iskar na'urar ta fara sanyaya dakin fadila tayi
ajiyar zuciya sa'ar da sassanyar iskar ta fara ratsata
lokaci guda kuma taci gaba da nazarin surorin jikinta
a fuskar mudubin tana yabawa da abinda ta gani ita
kanta tasan kyakkyawa ce wata sa'ar tana kwalliya ne
kawai saboda dai wai ance sabo da tayi wai gawa da
yatsine amma fadila tasan ko batayi kwalliya ba ita
kyakkyawa ce.
Iskar na'urar sanyaya dakin taci gaba da fifita fadila
ganin ruwan wankan dake jikinta yafara bushewa sai
fadila ta matso wani tattausan mai fari daga cikin
wata doguwar roba mai kamar jallo ta fara shafawa
ahannunta daga nan sai kirjinta sai kuma kan
cinyoyinta zuwa sangalalin kafadunta bayan ta gama
saita dago ta sake nazarin jikinta a fuskar madubin
sannan ne to taga abinda yasa numfashi da yawun
bakinta daukewa.
A zane radau radau tun daga kan hannayenta da
kirjinta zuwa kan cinyoyinta zanen kunshin nan ne na
surorin furanni baki sidik ya bayyana a fili abin
gwanin ban sha'awa saidai kuma fadila bata san daga
inda zanen ya bullo ba.
.
Na shiga uku fadila tace a firgice gami da dake kirji
lokaci guda kuma ta dauke fuskarta daga kan
madubin a tsorace ta dubi sassan jikinta a zahiri har
yanzu zanen kunshin na nan randagagu ajikinta ba
wai madubin ne ke fada mata karya ba.
Na shiga uku....wayyo Allah fadila tace cikin karaji
sa'ar data fara ja da baya da baya a tsorace tana
barin jikin madubin.
.
Baki shiga uku ba matata.... Ki kuma bi ahankali kada
ki takani don gani nan tsaye abayanki ina yabawa da
abinda na aura.
Wata busashshiyar murya ce ke fada daga bayanta
fadila ta rufe baki domin ihun ma yakasa fita daga
makogwaranta ta juya ta dubi bayanta cikin tsananin
firgici wayam bataga kowa ba.
Wanene? Fadila ta tambaya cikin wata murya data
kasa ganewa amatsayin tata.
Wani mai sha'awar surar jikin ne.... Zanen kunshin
nan ya karbe ki bazan taba daina kaunarki ba muddin
ina kallonsa.
Aka sake kecewa da kakkausar dariya sannan sai farin
hayaki ya turnuke dakin.
Acan wani bangare na sararin samaniyar birnin kano
aka saki rugugin aradu mai karar gaske fadila ta
toshe kunnuwanta sannan ta fadi rub da ciki akan
tattausan kilishin dake daben dakin.
** ** ** **
Fadila ta farka agigice daga nannauyan barcin
rudanin daya dauketa sannu ahankali ta mika hannu
ta dauko wayarta dake ajje akan gadon kusa da ita ta
duba lokaci. Karfe takwas da minti arba'in nan da nan
sai fadila ta mike zaune zumbur a tsorace tana waige
waige akan faffadan gadon.
Ina faisal me ya hanashi dawowa haryanzu shida
yace karfe takwas zai dawo. Tambayar kenan data
farayiwa kanta sannan ne to abubuwan da suka a
yammacin suka fara dawowa kwakwalwarta.
Ita kanta fadila batasan ta yadda akayi ta kawo kanta
cikin dakin kwanansu daga falon gidan ba. Abinda
kawai da zata iya tunawa shine bayan farin hayakin ya
washe ta tallaba a tsorace ta fada kan gado ta fashe
da kuka batasan sa'ar da barci ya dauketa ba.
.
Fadila ta muskuta akan gadon a tsorace adaidai
lokacin ne to taji an sake sakin wata katuwar tsawa
sannan saitaji saurin ruwan sama ya fara sauka ajikin
tagogin dakin fadila ta sake kallon lokaci ajikin
wayarta. Tara saura minti biyar sannan ne to fadila ta
yanke shawarar karshe aranta. Tabbas in har taran
dare tayi faisal bai dawo ba to ko me zai faru kome
aljanin nan zaiyi mata saidai yayi amma ficewa zatayi
daga gidan gara ta koma gidansu.
Wani zazzafan hawayen takaici ya fara sartu akan
kumatun fadila yaya kwana daya kawai agidan
masoyinta duk wannan bala'in zaiyita faruwa akanta
ta tambayi kanta sannan ta dauki wayarta ta fara
buga lambar faisal kwata kwata tsoro da fargaba sun
raunana tunaninta abinda ya kamata fa ace tayi
kenan tun dazu ta neme shi awaya domin tasan inda
yake.
Tafara danna lambar kenan saitaji an kwankwasa
dakin sannan aka fara turowa zuciyar fadila ta harba
tsakanin hakarkarinta nan da nan ta jefar da wayar ta
nufi kofar dakin
aguje.
.
Gani nan darling bari na bude maka.
Fadila tace muryarta na rawa kamar zata fashe da
kuka
fadila tayi tsalle ta rumgume faisal sa'ar data bude
kofar cikin kuka faisal ya dauketa kamar yar tsana ya
ajjeta akan gado sannan ya dubi fuskarta a tausashe
Kukan me kikeyi?
Kadan ya rage fadila ta fada masa abinda ke faruwa
to sai kuma tayi tunanin me yiwuwa ma in ta fada
masa yace ko zautuwa tayi adaidai wannan lokaci
kuma sai fadila ta tuna da zanen kunshin daya dawo
jikinta gabanta ya kuma faduwa shin yanzu idan faisal
ya tambayeta inda akayi mata kunshin tace dashi me?
Ita dai tasan bazai yiyu ba tace dashi bayan yafita
itama ta fice domin ayi mata zanen kunshi ba.
Wannan na iya harzukashi domin tasan zuciyar faisal.
Kinyi shiru kina kallona kukan me kikeyi? Faisal yace
da tattausan murmushi lokaci guda kuma ya dubi
hannunta kamar zai kama koda fadila ta dubi
hannayenta sai taga zanen kunshin ya bace babu shi
babu alamarsa jikinta ya dauki rawa sannan saitayi
ajiyar zuciya ta kalli faisal tace a tausashe.
Rashinka ne yasani kuka don me zaka tafi ka barni
kaida kace dakayiwa abokanka bangajiya zaka dawo
karfe takwas dubi agogo yanzu karfe nawa?
Am Sorry faisal yabata hakuri cikin harshen turanci
sannan sai ya janyo amaryarsa ta kwanta a kirjinsa
.
Ango da amarya na kwance abinsu cikin kwanciyar
hankali bugun zuciyoyinsu na bugawa lokaci guda da
dakikar katon agogon dake magale a bangon dakin
adaidai lokacin da agogon ya buga karfe goma sha
biyun dare wayar Fadila dake gefen gadonta ya dauki
ruri.
Fadila ta farka a firgice kirjinta na harbawa gamida
tsaki da kuma nadamar ma meyasa tun farko bata
kashe wayar ba Fadila ta dauki wayarta ta kara a
kunne.
Hello wanene? Fadila ta tambaya
Hello my darling mijinki ne faisal dan Allah kiyi hakuri
yanzu zan dawo Wallahi gida naje na tarar mama
batada lafiya shine muka kaita asibiti amma gani nan
yanzu zanzo.
Fadila taji kamar wata katuwar katanga ta fado mata
a tsakiyar baya Fadila ta dubi mijinta dake kwance a
kusa da ita sannan ta dubi kan wayar a tsorace.
Kaga Malam nifa matar aure ce ga kuma Faisal dina
kwance kusa dani.
Aka kyalkyale da wata tattausar dariya acan daya
bangaren Haba darling na dai fahimci haryanzu fushi
kikeyi dani kiyi hakuri gani nan zuwa.
Fadila taji kamar tasa ihu tabbas muryar faisal dinta
takeji acan daya bangaren yawun bakinta ya kafe
sa'ar dataga sunan Faisal din ne a saman wayar.
Faisal dan Allah da gaske kaine?
Fadila tace a tsorace tana kallon daya faisal din dake
kwance a kusa da ita.
.
Kun hanani barci da shegen surutu wai ku masoya an
fada miki shi kadai yake sonki idan ba barin dakin
nan nayi ba bazaku barni nayi barci.
Faisal din dake kwance akusa da ita ne ke wannan
bayani cikin kakkausar murya yana gama fadin haka
sai farin hayaki ya turnuke dakin.
Wayar dake hannun Fadila ta Subuce.
.
BABI NA BIYU 2
.
Adab da babban dakin karatu na sabuwar jami'ar
bayaro agindin wata yar dukurkusar bishiya dake
fuskantar tagwayen dakunan darasi daga gabas
FARIDA ce zaune tana kallon ikon Allah zuciyarta
kamar zata fashe ta fito ta tsakanin hakarkarinta.
Daga inda take zaune tana iya hangen Kabir dinta
zaune akan wani benci na farin dutse SAFIYYA zaune
akusa dashi suna hira abinsu jifa jifa kuma saita bude
baki kabir ya jefa mata alawa aciki duk sa'ar da hakan
ta faru sai Farida taji kamar sun watsa mata wuta a
fuska.
Tun karfe hudu na yamma direbanta Baba Ali ke
zaune a filin fakin yana jiranta amma har zuwa karfe
shida na yamma farida na nan zaune domin ta gama
rantseewa yau ko me za'ayi saita yiwa kabir magana.
Farida na nan zaune kusan dakika ashirin saita dubi
agogo sannan saita dago kai ta dubi kabir tabbas
maganar Asma'u gaskiya ce da dai bata yarda ba
amma ayau ta yarda domin duk da yake abinda
Asma'u ke bata shawara tayiwa kabir nau'i ne na
shaidanci to amma shine kawai mafita in har tana so
ta kwato kabirunta Farida ta fadawa kanta sannan
saita dada da cewa cikin zuciyarta ai shima kabir din
shaidani ne domin idan bahaka ba yaushe ne za'ace
wai sai nayi shaidanci zai damu dani.
Farida na nan zaune tana kallon ikon Allah duk kusan
daliban dake gurin sun tafi gida sai jifa jifan wadanda
ke kwana a makaranta dake yar zirga zirga nan da
can.
Karfe shida da rabi daidai lokacin da farida ta fara
tunanin ko anan zasu kwana sai taga su kabir sun
mike tsaye safiyya na kokarin kama hannayensa biyu
duk da yake farida bata iya jin abinda safiyya ke
fadawa kabir amma ga yadda motsin bakin da
yanayin fuskarta ya nuna tabbas kalamai masu dadi
take fadawa kabir.
Farida taji zuciyarta tayi kuna ana cikin hakane
saitaga kabir ya tashi ya nufi hanyar da zata kaishi
zuwa dakin kwanan dalibai yayinda ita kuma safiyya
ta nufi hanyar da zata kaita filin da aka tanada dan
ajiye motocin dalibai
Suna tafiya suna waige suna waige
suna dagawa juna hannu.
.
Cikin sauri tana tafiya gabanta na faduwa kafafunta
na hardewa fadila tabi kabir abaya.
Kabir farida takira sunansa cikin wata rarraunar
murya adaidai lokacin dasuka kawo kusa da wata yar
rumfa da dalibai ke hutawa
kabir ya juyo cikin mamakin jin muryar mace tayi
kiransa.
Oh farida kece haryanzu baki tafi gida ba? Kabir yace
sa'ar daya juyo.
Ina nan ban tafi ba farida tace gamida danyin shiru
domin ta lura kallonsa yatafi izuwa hannayenta.
.
Kai nake jira tun dazu ina can azaune farida tace
lokaci guda ta nuna karkashin bishiyar data baro
haba farida amma kuma kika ki yi min magana
wallahi banganki ba.
Farida ta sunkuyar dakai naga kuna hira mai dadi ne
shine nace bari na jira dan kada na bata muku
hirarku
haba dai ai dama kinzo ba wata hirar kirki mukeyi ba
maganar jarrabawa mukeyi.
Farida ta dago kai a yatsine ta dubeshi tace Au
jarrabawar bana hardasu sa alewa abakin budurwa?
Lallai bana makin din jarrabawa sai a barwa su
Shazumamu.
Kabir ya fashe da dariya Kai lallai farida yau kin
samin idanu
farida ta waiga hadu da dama bata hangi kowa akusa
dasu ba sai daga can bangaren shiga dakin kwanan
dalibai take iya hango kawunan jama'a jifa jifa hakan
ita ta kara mata karfin gwiwar matsowa kusa da kabir
ta yadda har yana iyajin numfashinta fuskarta dab da
tasa ta dubeshi ido da ido tace.
Kabir me yasa kake guduna ko dan kaga na mutu
akanka? Kabir ya dago kai ya dubi farida cikin mamaki
da kaduwa amma da yake kwararren mayaudari ne
bai bari kaduwa ta nuna a fuskarsa ba. Abinda ya
bashi mamaki shine kama hannunsa da yaga farida
tayi yasan cewa wannan ba al'adar farida bace ita dai
ka barta da sauya samari kamar riga amma
shashanci ba aikinta bane.
Tsahon lokaci suna tsaye ahaka kabir yayi ajiyar
zuciya kana idanunsa sukayi duba izuwa hannayenta
akaro na biyu.
Ba gudunki nakeyi ba farida.
In ba guduna kakeyi ba me yasa ka daina kirana
awaya kuma sai in nemeka in rasa amma dana ganka
sai in ganka tare da safiyya farida tace sannan sai ta
dafa hannunsa.
Kabir yaji wani irin sanyi ya ratso daga hannun farida
ya soki hannunsa kamar an rike shi da hannun
kankara.
Ke yaya naji hannunki sanyi karau haka?
Sanya fa kace? Farida ta dube shi cikin mamaki
kaga ni hannuna dumi ne dashi saidai ko in hannun
safiyyarka ne keda sanyi
kabir yayi murmushi yace kinga ga dan Allah mu bar
wannan zancen ya wuce daga yau in Allah yaso kin
zama tawa my only one.
Kaidai fadi gaskiya safiyya fa?
Kada ki damu da wannan shirmenta kawai take.
Kabir yace azuciyarsa kuma yana cewa wannan ma
rabo na minallahi ce wai tsuntsu daga sama
gasashshe.
.
Kai amma fa zanen kunshin nan naki yayi bala'in kyau
a ina akayi miki kabir ya fada a fili.
Gaban farida ya fadi cikin sauri ta dubi hannayenta a
iya saninta zanen dake hannunta ko baki baiyi ba
amma sai gashi yanzu rangadadau yayi baki kamar
yanzu aka zana shi.
Wata...wata kawata ce tayimin farida tayi masa karya
a tsorace kabir ya lura da sauyin yanayi na lokaci
guda akan fuskarta dan haka cikin sauri sai ya saki
hannunta azuciyarsa yana cewa bi ahankali dan
samari wannan farin shigace ba irin su safiyya bace.
Yanzu yaushe zamu sake haduwa mu tattauna sosai?
Farida ta dubi zanen dake hannunta a tsorace tace.
Duk lokacin da kake so
mu hadu gobe a filin fakin idan mun tashi daga
karatu saina kaiki gida.
Tunda farida tazo jami'ar bayero bata taba bari wani
saurayi ya kaita gida ba domin kullum

Please Login or Register in order to submit comment