Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gareta shine
kyawun fuskarta.
Bebi ta sake zubawa fuskarta idanu cikin kaduwa
domin ta lura duk ta lura fatar ta fara saki kamar
fatar dadadden mangwaro duk da yake dai bebi tai
imani da cewa ta gama kama ruhin honorabil sabo
amma abin ya bata tsoro domin ta sani idan batayi
hanzari ba honorabil sabo na iya sauya aniyarsa ta
aurenta dayafara yi duk da yake dai tasan cewa ba
ra'ayin kansa bane ya aure ta malaman tsibbunta da
bokayenta ne ke ta aiki akansa amma yanada kyau
ace idan kanada kyau ka kara da wanka wannan
tunanin shiyasa bebi ta sake kallon kanta ajikin
madubi akaro na uku sannan saitace da kanta cikin
takaici.
Haba fuskata... Ya zakiyi min haka? Tana gama fadin
haka sai bebi ta lalubi wayarta akasan matashin kai ta
daddanna wasu lambobi sannan ta kara wayar a
kunne acan jimawa saitace.
Hello.... Malam ina kwana?
Lafiya lau. Akace adaya bangaren
kudin nan dana turo ma yazo ko? Kwarai kuwa yazo
masha Allah Allah yasaka da alkhairi aka amsa adaya
bangaren shiru na dan lokaci.
Dan Allah malam sai akuma dage min kaga haryanzu
dai zancen auren nan namu shiru kwata kwata ma ya
daina zancen rabon da yatada zancen tun kafin
mutuwar abokinsa honorabil jatau kaga yau kusan
wata uku kenan fa Malam.
Kada ki tashi hankalinki 'yata. Akace da wata
kakkausar murya acan daya bangaren
nafada miki tunda mukayi wannan aikin na farko
babu abunda zai hanashi aurenki.
To ai malam ni abin ne da ban tsoro kaga fa da ba'a
sama da kwana biyu banganshi ba amma yanzu
tunda abokin nan nasa ya rasu sai inyi kwana goma
ban ganshi ba ya ajiyeni kawai sai kiwatani yake
kamar akuya kullum yana shagwaba ni da jin dadi
amma ni duk wannan bashine agabana ba nidai
burina shine ya aureni kuma idan da hali ma so nake
matarsa uwar ya'yansa tabar gidan.
Kada ki damu babu abinda ya gagari malam. Aka
danyi shiru acan daya bangaren yanzu yaushe rabon
da ku gana dashi?
Ido da ido dai yau anfi kwana shida amma kullum
muna waya kamar sau uku zai tambaya idan kayan
abincina ya kare sai a karomin akwai wanda yake
aikowa.
To shikenan Allah rufa asiri yanzu ina ganin wani
aikin zamu sake.
To malam bebi ta amsa cikin gaggawa zamu bukaci
bakaken tinkiyoyi guda goma wadanda babu sofaren
fari a jikinsu
To malam nawa ne kudin saina kawo ma gobe da
kaina.
Yan kanana dai basa wuce dubu shida shida....
Kada ka damu zan kawo ma dubi dari gobe sai ayi
duk abinda yakamata nidai burina shine......
Bebi tayi shiru sa'ar dataji motsi da surutun Jama'a a
farfajiyar gidan.
Zan kiraka in an jima bebi tace da malamin kafin ya
amsa ta kashe wayar.
Lokaci guda kuma ta koma kan gadon ta kwanta lamo
kamar tashinta kenan daga barci batayi minti guda da
kwanciya ba aka banko kofar dakin da karfin tsiya aka
shigo bebi ta dago kai a firgice cikin mamaki sai taga
honorabil dinta sabo tsaye a tsakiyar dakin kallo daya
tayiwa fuskarsa tasan cewa tabbas ba lafiya jiki na
rawa ta tashi zaune akan gadon ta dube shi amma
batace uffan ba.
Tashi kisa kayanki ina san magana dake akwai
alamun karkarwa acikin muryarsa haka nan bebi ta
lura da fuskar honorabil sai naso take da gumi
Lafiya..... Me yayi zafi haka? Bai amsa mata ba sai ya
nufi bakin gadon ya zauna sannan ya dubeta
.
Abinda Nake Gudu Ne Bebi Shiya Faru Honorabil
Yace Yana Girgiza KaiMaganar kawarki ce mama gashi nan yanzu ita
jami'an tsaro suke nema.
.
Bebi taji gabanta yafadi kana nufin kace dani ita ta
kashe shi?
Honorabil ya girgiza kai cikin damuwa babu tabbas
amma sunanta ne a shafin zargi na farko honorabil
ya danyi shiru sannan sai ya dago fuska ya dubi bebi
ido da ido yace.
Nayi Nadamar haduwa dake bebi da nasani daban
dora idanuna akanki ba
Bebi gashi yanzu kin sani acikin masifa bebi ta dafe
kirji cikin kaduwar jin bakaken kalaman dake fitowa
daga bakinsa.
Haba darling me yayi zafi haka sai kace ni na kashe
shi ni meye laifina acikin wannan al'amari ?
Da bansanki ba da bazan taba mu'amala da mama ba
abinda baki sani ba shine masu gadin gidan marigayi
jatau ne suke bada shaidar sun ga mun shiga mu uku
sannan mun fito nidake sun tabbatarwa da jami'an
tsaro cewar acan gidan mama ta kwana. Akan dole
aka takura ni na amsa cewa eh lallai haka akayi...
Honorabil sabo yayi shiru ga mamakin bebi saitaga
hawaye ya fara sartu akan fuskarsa.
Kin cuceni bebi kin zamo sanadin barin kujerata
domin idan wannan abun kunya yafito fili idan ya
tabbata cewa mama ce ta kashe shi dole ne a tsigeni
daga kujerata.
.
Mama bazata iya kashe mutum ba.... Wallahi nasan
ko bera mama bazata iya kashewa ba.
Honorabil sabo ya mike tsaye a fusace ya dubi rabi
saikifito ki fada musu haka dan suna dakin shakatawa
suna jiranki. Bebi taji gabanta ya fadi. Su wanene? Ta
tambaya a tsorace.
Jami'an tsaro zasuyi miki tambaya ki kuma kaisu inda
zasu sami mama
yana gama fadin haka saiya lalubi aljihunsa ya zaro
naira dubu biyu ya jefa mata akan gadon sannan
yace.
Na baki minti goma ki hada kayanki gaba daya kifito
ki bisu daga yau bana kara son ganin kodaddiyar
fuskarki agidan nan
Bebi ta fashe da kuka haba.... Darling kai da kace zaka
aure ni yanzu duk zaman da mukaiyi da wannan zaka
sakamin dubi fa wai da dubu biyu ma zaka sallameni.
Honorabil jatau ya dubeta da murmushin yake
sannan saiya sunkuya ya dauke dubu biyun daya
bata. Sannan yace
Idan bakyaso ni inada bukata domin banzan abinda
gobe zatayi ba saikiyi sauri kada su gaji da jira yafice
daga dakin cikin gaggawa.
.
BABI NA BIYAR 5
Fadila ta kalli fuskar wayar tafi da gidanka dake
gabanta sannan saita rufe idanu ta fashe da kuka
wayar taci gaba da ruri gashi dai tana ganin Faisal
dinta ne ke kira amma batada ikon ta amsa wayar.
Umarni ne na mahaifanta.
Kada ki kara amsa wayarsa har sai mun gama aikin
da zamuyi akanki.... Bakida lafiya fadila tabbas kin
hadu da lalura babba.
.
Fadila ta tuno da maganar mahaifiyarta sa'ar da
wayar taci gaba da ruri agabanta hawaye na zuba
akan kyakkyawar fuskarta hannu na rawa ta dauko
wayar ta danna gurin amsawa amma batace kala ba
sai kawai ta kara a kunne tasan yanzu haka wani yana
labe akusa da kofar yana sauraro datace Hello
mahaifiyarta zatashigo ta hauta da fada dan haka sai
fadila ta lumshe idanunta tana sauraron tattausan
muryar faisal dinta acan daya bangaren kamar zai
fashe da kuka yana cewa.
.
Fadila... Fadila yanzu bazaki amsa min ba nasan kina
sona nima ina sonki Wallahi kuskure ne fadila... Hello
dan Allah ki amsa min ko naji muryarki na sami
saukin kunan zuciya..
Halo... Fadila.
Fadila taji kamar ta amsa masa amma maimakon
haka saita lumshe idanunta taci gaba da sauraron
muryarsa tasan yasan tana sauraronsa kuma tasan
tana son itama tayi magana dashi amma tasan baisan
abinda ya hanata amsa masa ba. Idanunta a lumshe
yanata surutunsa har kudin wayar suka kare.
Maimakon fadila ta bude idanunta saita kara
runtsesu zuciyarta tafara dawo mata da majigin
rudanin da suka biyo bayan watanni uku da suka
shude masu kama da shekaru uku agurin fadila.
.
Watanni uku sun shude kamar wasa abubuwa
dayawa sun faru acikinsu harda takunkumin magana
da ake sawa fadila.
.
Kin cuceni Fadila na sake ki saki biyu taji amsa
kuwwar muryar datafi kauna fiyeda komai aduniya
tana ruri cikin kwakwalwarta.
Fadila bata taba ganin masifa irin ta wannan safiyar
ba domin faisal dinta na gama furucin sakinta saiya
rubuta a takarda ya jefa mata sannan ya fice abinsa
fitarsa keda wuya aka fara tafka ruwan sama kamar
da bakin kwarya sai da fadila ta shafe sama da sa'a
guda tana kuka daga karshe dai ta fahimci cewa koda
fa kukan jini zatayi saidai jinin jikinta ya kare dan
haka jiki na rawa zuciya na kuna ido na yararin ruwan
hawaye fadila ta dauki yar karamar jala irin ta mata
sannan ta kwashe duk hotunan da suka dauka ita da
faisal dinta tun farkon soyayyarsu har zuwa daurin
aurensu ta zuba acikin jakar daga wannan jakar bata
dauki komai ba sai lemar faisal saboda ruwan da ake
makawa.
Ruwa na dukan rabin jikinta lemar dake hannunta
kuma na kare wani bangaren a haka ta iso bakin titi
neman mota duk kuwa da cewa filin fakin din katon
gidansu na alfarma akwai manyan motoci sama da
guda uku. Titunan babu kowa sai jifa jifan motoci da
kuma yan kabu kabu da ruwan yagama jikawa ba'a
dade ba fadila tayi sa'a wani dan mashin mai
rumfa da taya uku launin rawaya ya tsaya agabanta
jikinsa an rubuta
ADAIDAITA SAHU
wani bawan allah mai siffar kamala da dan gemu
tsurut kamar jelar dawisu shike tuka wannan mashin.
Tun kafinma fadila tagama bayanin inda zata mai
mashin din yace ta shiga domin ya lura tana cikin
matsanancin hali.
Lokacin da fadila ta shiga babban dakin shakatawar
gidansu ba karamin kaduwa tasa mahaifanta da
kuma yan uwanta ba domin kannenta da wasu yan
uwanta guda hudu sunci kwalliya jira sukeyi kawai a
dauke ruwa akaisu gidan amarya kwatsam sai gata
acikin dakin shakatawar ta jike shakaf da ruwa kamar
algarar goro idanunta sunyi luhu luhu saboda kuka
tana zuwa saita wuce gurin mahaifiyarta aguje ta fada
akan cinyarta ta fashe da kuka.
.
An dauki sama da awa guda kafin ashawo kanta daga
karshe dai mahaifiyarta da wata kanwar mahaifinta
suka shiga da ita wani daki inda ta ZAYYANA musu
wannan labari mai kama da Almara matan suka
kwashi salati sa'ar da tagama basu labarin.
Ba'afi sa'a biyu da zuwanta gida ba saiga mahaifin
faisal da wani abokinsa sunzo gidan abubuwa suka
dada rincabewa to Amma sa'ar da sukaji wannan
labari sai suka baiwa iyayen fadila hakuri akan cewa
shashanci ne irin na yaran zamani acewarsu duk da
yake dai akwai matsala bai kamata dansu ya saketa
ba to amma sun bada shawarar lallai adage mata da
addu'a daga karshe mahaifin faisal yace zai dawo da
magariba domin su tattauna yadda za'a shawo kan
wannan al'amari don alokacin mahaifin Fadila baya
nan haka nan mahaifin na faisal ya dada da cewa
kada a sake a dauki koda Allura daga gidan yaran.
Washegari aka tura malamai sukayi ta addu'o'i akan
fadila baji bagani tun daga wannan rana kullum sai
anyi mata addu'a watan farko daya biyo bayan
faruwar al'amarin anso a mayar da auren faisal da
fadila amma sai wani malami yabada shawarar abari
tukunna agama yi mata addu'o'i domin in bahaka ba
sai aljanin yaci gaba da wahalar da ita.
Yaran zamani saidai hakuri amma suna da sakaci
malamin ne ke yiwa mahaifin fadila bayani.
Kaga yara ne idan zasu kwanta barci basusan suyi
addu'a ba gashi Ayyatulqursiyyun nan duk kusan
yaron dayan taba zuwa islamiyya ya haddaceta amma
bazasu iya karantata ba idan sunzo kwanciya saidai
suyita kallace kallacen fina finan banza su raba dare
suna yi kuma da zarar sun tashi kwanciya kawai
zasuyi babu wata addu'a.
Wai to Allah gafarta malam meke faruwa ne
matanmu ke fama da matsalar aljanun nan yanzu fa
duk acikin mace goma baka rasa akalla guda biyar
masu fama da matsalar aljani? Mahaifin fadila ya
tambayi malamin.
Wato Alhaji mafi yawan matan da jinnu ke hawa
kansu sakaci ne kaga na farko da akwai zama da
sukeyi cikin kazanta da rashin tsarki sun iya shafa mai
da hota da turare amma jikinsu babu tsarki na biyu
kuma akwai bayyana tsaraicinsu a fili wasu ma tsirara
suke kwana wasu ko suyi ta yawo da kaya rabinsu
tsirara ga barin gashi a waje duk wannan suke janyo
hankalin aljanu su sami damar shiga jikinsu.... Wato
abin dai Alhaji saidai addu'a yanzu in ba lalacewar
zamani ba yaushe ne za'a ce wai ZAYYANA na kunshi
ta wuce tafin hannuwa da kafafuwa ta kai har tsaraici
kai Allah yayi mana tsari da wannan shaidanci.
Ameen malam... Amin wannan duk ya farune watanni
uku da suka shude.
A tsayin wannan lokaci kullum sai anyiwa fadila
addu'a da yan rubuce rubuce nasha.
Mako guda da faruwar al'amarin ne watarana da
yamma sai faisal ya bugowa fadila waya alokacin
suna tare da mahaifiyarta fadila ta dubi wayar cikin
tsanancin mamaki domin bata taba tsammanin bayan
abinda yafaru faisal zai nemeta ba.
Faisal ne tace da mahaifiyarta baki na rawa.
Kada ki amsa... Rabu dashi dan banza marar mutunci
sukayi shiru a dakin na nyan dakiku wayar nata ruri.
Kada ki sake inji kin amsa wayarsa in ba rashin
mutunci ba ko kwarto ya kamaki dashi a daki ai ya
shawarci na gaba dashi kafin ya sakeki amma kwana
daya kacal agidan ya sake mana ke dan wulakanci
rabu dashi yayi tayi ko za'a mayar da auren nan saiya
san darajarki tukunna dan banza mai manyan
kunnuwa.
Tun daga wannan rana har zuwa yanzun nan da fadila
ke zaune tana tuna baya bata amsa masa waya ba.
Sau daya dai hana rantsuwa ta taba kokarin ta amsa
wayar sai mahaifiyarta ta kamata.
Bakiji abinda nafada bako? To wallahi duk ranar da
kika amsa saina kwace wayarki kin daina magana da
kowa ma kuma babu inda zaki fita ko nan da kofar
gidan har sai an gama yi miki addu'o'in nan uwar
shegen taurin kan tsiya babu yadda banyi dake ba
akan wannan shegen kunshin tsaraicin amma saida
kikayi yanzu gashi nann kin hada mu da wahala da
ganin wulakanci.
.
Fadila tayi ajiyar zuciya sa'ar data gama wannan
dogon tunani adaidai lokacin ne kofar dakin ta bude
mahaifiyarta ta shigo dauke da wani dan kofin
tangaran a hannunta kamar jira ake ta shigo. Wayar
ta sake daukar ruri
Fadila ta kalli fuskar wayar Faisan ne ke kira. Shi din
ne? Mahaifiyar ta tambata tana kallon yarta
tausayinta ya kamata yau saura kwana biyu a gama
mataaddu'o'in Da Akeyi.
Wayar Taci gaba da ruri fadila taci gaba da zubar da
hawaye.
Amsa masa. Mahaifiyarta tace da yarta a tausashe
sannan saita fice daga dakin.
** ** **
Safiya ce mai dauke da kurar hazo ga iska abin babu
dadi ga sanyi kamar ya tsaga kashi jama'a sai korafi
sukeyi kamar yadda suka sabayi akowane irin yanayi
duk da cewa dai sanyin ya uzurawa kowa ya hana
kowa sakat amma akwai wasu tsirari da suka dage
akan cewa sufa har yanzu suna nan akan bakarsu
cewa sunfi jin dadin sanyin nan akan zafi.
Mama bata yarda da wannan ra'ayi ba domin
katuwar rigar sanyi mai gashi kamar buzun malam
data rufa akan damammun kayanta sun nuna hakan.
Abakin titi take tsaye tana jiran tasi akan titin
na'ibawa kanta boye cikin wata irin hular gashi haka
nan kafafunta ma boye suke cikin takalmi sau ciki irin
na mata hatta hannayenta boye suke cikin bakaken
safa ka karamar kaduwa Mama tayi ba sa'ar dataga
wani dan cuwa cuwar Mai abakin titi ya dauko jarkan
mai daga shi sai gajeren wando da wata yar jeleliyar
riga singileti mai kamar hanci yana tafe abinsa yana
fito kai kace abakin kogi yake lokacin zafi.
Oh... Inda ranka kasha kallo mama tace azuciyarta
tana kallon saurayin cikin mamaki sannan saita dawo
da hankalinta kan matsalar dake gabanta ba'afi
mintina biyu da faruwar hakan ba dan tasi ya tsaya
agabanta mama ta fada masa inda zai kaita dan tasi
ya cajeta kudi da yawa domin inda zai kaita mota bata
zuwa gurin domin gindin wani dutse zai kaita gurin
wani BOKA dake bayan wani kauye ahanyar Wudil.
Mama ta shiga bayan motar ta zauna bata damu da
yawan kudin daya cajeta ba domin kudi ayanzu ba
matsalarta bane tun da dai haryanzu akwai sama da
naira dubu dari hudu acikin asusunta kudin da Alhaji
Bilyaminu ya bata domin ta sayi mota abinda yafi
damunta ayanzu shine ta kubuta daga hannun mugun
aljanin daya sata gaba tuni kasuwarta ta gama
mutuwa a jihar kano duk wanda kaga ya kulata to
rashin sani ne shima da an fada masa zai tsere ya
barta.
Jikin mama ya dauki rawa abayan motar sa'ar da tuna
wannan muguwar rana watanni uku da suka wuce
Ta tuno sa'ar da Alhaji bilyaminu ya fadi a tsakar
dakinta yana ihu hannu da kafafunsa duk sun shany
sun koma kamar maburgin miya.
A lokacin mama tasan abinda ke faruwa musamman
ma sa'ar dataji an kece da mahaukaciyar dariyar nan
acikin firgici sai mama tasa kururuwa sannan ta fito
daga cikin dakin aguje ta nufi kofar gida tana ihun
akawo mata agaji kafin kiftawa da bisimilla gidan ya
cika da jama'a wasu ko sukace bazasu motsa ko nan
da can ba dan daman rashin kunyar mama ta gama
isarsu.
Aranar da daddare a filin INDA RANKA na gidan radio
Freedom suka yayata wannan labari mai kamar
almara harma sun sami damar zantawa da mama
wacce tayi bayanin wannan masifa data sameta daga
yin wannan kunshi na zamani jama'a sukayita fadil
ra'ayoyinsu akan wannan al'amari wasu suka
tausayawa mata wasu ko sukace Allah ya kara ai
yanzu ta daina karuwanci tunda aljani fara buge
manemanta saida aka shafe sama da sati guda
jama'a na sunturi zuwa gidan mama domin su ganta.
Dan haka saida takai idan mama tabar gidan da
sassafe bata dawowa sai tsakar dare mama tariga
tasan in badan kudin da Alhaji Bilyaminu ya bata ba
da sai zaman kano ya gagareta watanni uku da suka
shude ko kuda baya sunsunata idan kaga dan duniya
ya kulata to bako ne.
Wannan al'amura su suka taru suka dami mama
domin ta riga tasani bata da wata sana'a data wuce
karuwanci takuma riga tasani duk namijin daya
rabeta ya shiga uku shin kudin dake hannunta kwana
nawa zasuyi kafin su kare idan kuma sun kare din
tayaya zata sake samun wasu? Wannan sune
tambayoyin da suka addabi zuciyar mama da farko ta
yanke shawarar tun da yanzu tanada yan kudi ta
samo dan yaro kawai ta aura ta huta da wannan
masifa Nan da nan wannan tunani ya rushe kamar
yadda ruwa ke rusa tubalin toka tabbas idan har ba
Aljanin nan aka rabata dashi ba mama tasan wani
namiji bazai kara rabarta ba.
Wannan shiya tashi hankalin mama ta tashi tsaye
wajen neman magani. To saidai kuma a tunanin
mama bokaye ne kawai zasu iya rabata da wannan
aljani wata kawarta ta taba cewa da ita wai bokaye da
aljanu suke kwana a dakunansu wai har da akwai
bokan da yake kwana da aljanu miliyan guda hakan
kawar mama ta dada cewa wai boka na iya kiran
kowane irin aljani ne ke damunta ya tsawatar masa
cewa kada ya kuma damunta idan aljanin yayi
gardama wai za'ayi zane shi.
Imani da wannan tatsuniya su suka sa mama bin
bokaye wannan boka da mama ta nufi gidansa
ayanzu shine boka na goma sha daya da zataje
gurinsa acikin watanni uku da suka wuce tuni mama
ta sayi saji sama da guda dari biyu.
.
Karfe sha biyu saura suka isa gindin dutsen tsaya nan
ka jirani mama tace da direban ma'abocin tarin
gashin baki kamar tsohon soja
zaki dade acan ne?
Meya shafe ka kaidai ba aikin kudi kakeyi ba? Direban
ya dubeta da murmushi cikin jin dadin cewa tata Fadi Gasassa.
.
Gaskiya ne ranki ya dade ina nan ina jira nasan dai ai
ma tafi nan da magariba ko?
Waya sani ko anan zamu kwana mama tace cikin
gatse sannan ta nufi gindin dutsen cikin sauri
Tuni mama ta riga ta gama yanke shawarar cikin
zuciyarta cewa idan har wannan boka bai rabata da
wannan aljani ba to kasar nijar zata shiga me yiwuwa
ko zata dace acan tun da dai gashi yau kusan sati uku
kenan babu ko saurayi daya daga cikin tsofaffin
samarinta daya mata waya. Wannan abu na tada
hankalin mama domin ada kullum ba'a kirata ba a
kirata sau saba'in sai gashi yanzu ko flashing ya
gagara.
.
Sannunki da zuwa tun jiya daman na ganki tafe.... Yar
mitsitsiya ce ta kawomin labarinki ta fada min abinda
ke tafe dake amma duk da haka dai zanso inji
matsalar daga bakinki. Bokane ke fadin haka.
Mama ta zube agaban bokan kamar zata fashe da
kuka tace cikin karyayyar murya.
Malam... Boka wani aljani ne ke damuna kwata kwata
ya hana maza su saurareni mama taci gaba dayi
masa dogon bayanin abubuwan dake faruwa akanta
kamar yadda ta saba yiwa sauran bokayen da taje
gurinsu abaya.
Baibayau ne.... Dan banza tabbas Dabaibayau ne ai
dan banzan aljani sa'a ma kikayi ai da kika zo nan
amma da kin kara wata guda baki zo ba gurgunta ki
zaiyi tunda kikace har cinyoyinki ya taba lokacin da
yakeyi miki Kunshin.
Mama ta rike numfashi a tsorace
gurgunta ni fa kace?
Kwarai kuwa... Amma kada ki damu ai kinyi sa'a
tunda kikazo gurina rufe idanunki bokan ya umarce ta
Jiki na rawa mama ta rufe idanunta
Bude su bokan ya sake umartarta mama ta bude
sake rufewa
Mama ta sake rufe idanunta akaro na farko.
Sake budewa
mama ta sake bude idanu ga mamakinta sai taga
wani katon koko agabansa cike da layu iri iri wasu
kamar kuli kuli wasu kamar ya'yan barkono wasu
kuwa manya manya masu siffar makani.
Sake rufe idanunki ki dauki daya bokan ya umarce ta
cikin karaji.
Jiki na rawa mama ta rufe idanu sannan ta tura
hannunta cikin kokon ta dauko laya daya.
Bude idanunki ki bani ita
mama ta bude idanu lokaci guda kuma ta mika masa
layar.
Tsawon dakiku bokan ya jujjuya layar a hannu can sai
yayi ajiyar zuciya ya dubi mama.
Kin hadu da dan banzan aljani mai nacin tsiya amma
daga yau din nan kin rabu dashi. Bokan ya danyi
shiru yana kallonta.
Zamu bukaci ayanka fararen zakaru goma jajaye
goma bakake goma dole ne kuma ayankawa aljani
dabaibayau burgun gafiya biyar da zomaye uku.
Mama tayi ajiyar zuciya ta dubi bokan baki na rawa
tace Ko nawa ne zan biya sai asaya in dai zan rabu da
wannan jaraba.
Ungo rike nan bokan ya mika mata yar karamar layar
data zabo mai kamar barkono.
Idan kinji gida yanzu kisa ayi miki kitso da wannan
layar a tsakanin gashinki kada ki sake ki tsefe sai
bayan kwana bakwai alokacin ne zanyi miki duk aikin
da kike bukata idan muka yanka duk abubuwan dana
lissafa miki abaya aljani dabaibayau zai shanye jinin
shikenan kun rabu dashi har abada in dai kina tare da
wannan layar.
Kana nufin da layar zanyi ta yawo akaina har abada ?
Boka ya girgiza kai zaki iya cirewa bayan kwana
bakwai amma ki tabbata duk inda zaki kina tare da
wannan layar.
Na fahimta mama tace baki na rawa sannan saita
bude jaka ta kirgi wasu adadin kudi masu yawan yan
dubu dubu ta mika masa.
Ajje anan bokan yace da ita sannan saiya dubeta ido
da ido yace.
Idan kwanaki bakwan nan sun cika kina iya kiran duk
namijin da kikayi niyya zaizo kuma idan kin nemi
aurensa ma zai yarda.
Adaidai wannan lokaci sai MUBARAK yafadowa
mama arai
kana nufin kowa nace ya aure ni sai yayi?
Kwarai kuwa dan dole mutum ma sai ya aureki domin
ai aljanin ne ke hanasu zuwa shi yake dabaibaye su.
Mama ta lumshe idanu cikin jin dadi duk duniya babu
wanda take so kamar wani takadirin saurayi alayinsu
waishi Mubarak to saidai kuma ya tsaneta domin ko
gaida shi tayi mubarak baya amsawa. Wani
busashshen murmushin mugunta ya subuce a gefen
bakin mama.
Shege uban girman kan tsiya shi zan aura mama tace
da kanta.
*** ** ** **
Acikin wani katon dakin shakatawa ma'abacin yalwa
wanda ke dauke da kujerun alfarma sunyi sahu sahu
kamar a filin fareti wani tsohon kwamishina ne zaune
daga shi sai farar singileti da farin wando na shadda
mai tazuge jarida a hannunsa yana dubawa ta saman
dan siririn tabarau fari wanda ke zaune daraf a
saman dogon hancinsa mai kamar na aku. Lokacin da
yana saurayi kafin zamani da tsufa su cimmasa wata
kyakkyawar budurwa ta taba cewa dashi.
Wallahi kana burgeni... Saboda dogon hancin nan
naka.
Ai kuwa kya yi kya bari an ni ko burge ni bakyayi. Ya
mayar mata da martani a takea agurin mutum ne mai
son gwale mutane sam sam ba'a yi masa daidai gashi
baha'i murdadde duk lokacin da jama'a suka karkata
dama shi sai yayi hagu idan akayi gaba shi sai yayi
yamma. Wannan fa duk mai sauki ne idan aka
kwatanta da halayarsa ta muguwar gardama domin
idan ya tsaya akan ra'ayi babu wanda ya isa ya sauya
masa tunani koda kuwa abinda ya tsaya akai ba
daidai bane. Wannan tsohon kwamishina sunansa
Alhaji Ilyaskuma shine mahaifin Farida.
.
Mutumin ya dago kai daga kan jaridar da yake
karantawa sannan ya dubi inda farida take a takura
agefen wata kujera tana sharbar kuka tun idanunta
na zubar da hawaye har sun kafe babu komai sai
majinar datake zuba daga hancinta.
Ko kukan jini zakiyi sai kin aure shi tunda kin raina
mutane.
Farida ta sake fashewa da kuka. Adaidai wannan
lokacin ne mahaifiyarta tashigo dakin fuskarta a
murtuke yar gajeriyar mata ce fara kyakkyawa tana
dauke da zanen kalangu agefen fuskarta hagu da
dama.
Alhaji ni dai wallahi abin nan ba sonsa nake ba kai
kuma idan ka kafe akan abu ka kafe kenan saikayi
amma in ba haka ba kasan lalurar dake kan yarinyar
nan ka bari ayi mata magani kaki kuma gashi sai
kokari kake ka hadata da wanda bata so mutumin da
ko ganinsa bata tabayi ba.
Alhaji Ilyasu ya ajje jaridar dake hannunsa ahankali
agefen kujerar ya dubi matarsa sannan ya dubi yarsa
cikin kunan rai
Idan ma bata taba ganinsa ba yau zata fara zaman da
nake yanzu shi nake jira su gana dan ko tana so ko
bata so nan da sati guda za'a daura musu aure.
Mahaifiyar farida ta rike numfashi cikin kaduwa.
Rana ita yau fa kace?
Haba alhaji wannan abu kamar kasha kwaya yarinyar
da......
.
Alhaji ilyasu ya katseta ta hanyar daga yan siraran
hannunsa masu kama da muciya
babu wanda ya isa ya saura min ra'ayina kinaji ko?
Daman ai ke kike daure mata gindi take duk iya
shegen da taga dama kullum tana tara mana yan iska
a kofar gida to wallahi ko mutuwa zatayi saina daura
mata aure rana ita yau Aljanin karyar da take baki
labari saidai ya kasheta karyar banza karyar wofi in
ba ta raina mutane ba ke kintaba ganin inda Aljani
yayiwa mutum Kunshi?
Farida dake zaune agefensu ta fashe da kuka kasa
kasa sannan ta runtse idanunta kana ta rufe
kunnuwanta da tafin hannayenta ko kusa ko alama
bata kaunar kalaman dake fita daga bakin mahaifinta
dan me zaice labarinta karya ne kodon baiga abinda
ya samu kabir bane kuma baiga abinda ya sami baba
ali ba.
.
Zuciyar farida ta hasko mata bakin titin gwarzo
watanni uku da suka wuce sa'ar data rugo aguje zuwa
bakin titin.
Wayyo Allah dan Allah ku taimakeni
farida ta kwalla ihu sa'ar data hangi wasu mutane
hudu suna gudun motsa jiki nan da nan mutanen
hudu suka dawo izuwa gareta.
Ke menene? Wani daga cikinsu ya daka mata tsawa
da wata kakkausar murya.
Shine... Yana ciki. Fadila tace a rude tana nuna bayan
dutsen cikin duhun daren.
Tsaya nan muna zuwa katon mutumin yace da ita
sannan sai suka ruga aguje zuwa bayan dutsen
abinda Farida bata sani ba shi kartin mutanen wasu
sojoji ne daga

Please Login or Register in order to submit comment