Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

barikin janguza suke motsa jiki basu fi
ko mintuna uku da bacewa daga dutsen ba sai farida
taji ihun baba ali ya ratsa dajin abin ya kada mata
hantar ciki domin tun da take bata tabajin dan adam
yayi irin wannan ihun ba.
Har zuwa lokacin da sojojin suka kawota gida farida
bata daina jin amsa kuwwar ihun baba ali acikin
kwakwalwarta ba.
.
Washegari da safe ne take samun labari agurin
mahaifinta cewa sojoji sun cirewa baba Ali idanunsa
guda biyu yanzu haka yana asibiti kuma ya amsa
cewa yayi kokarin yi mata fyade.
Farida ta labartawa mahaifiyarta irin masifun dake
faruwa akanta tun daga lokacin da akayi mata zanen
kunshin nan.
Ai kinga irinta in banda shaidancinku na ya'yan
zamani ina ke ina zuwa ki budewa wani kato
tsaraicinki wai yayi miki zanen kunshi gashi nan
yanzu kin dauko jaraba in ba tashi mukayi tsaye ba ko
aure ba zai barki kiyi ba. Mahaifiyarta ce ke fadin
haka Rabi a fusace rabi a tsorace cikin tsananin
kaduwa
Awannan yammacin tayiwa mahaifin farida bayanin
duk abinda ke faruwa akan yarsu ga mamakinta sai
taga ya fashe da dariya.
Wannan ai tatsuniyace haba TASALLAH haryanzu
daman kina imani da tatsuniyoyin yaran zamani.
.
Kada kace haka Alhaji matarsa tasallah tace a tsorace
domin tasan halinsa Alhaji ba karya bane kuma......
Bance dake Aljani karya bane amma saboda tsabar
sake shine har ya zama mutum yakeyiwa mata zanen
kunshin akan tsaraici haba Tasallah kada ki biye
karairayin yaran zamani Wallahi sa kakiki su baro ki.
Abin kawai daya kamata muyi shine mu aurar da
yarinyar nan kawai mu huta.
.
Matar ta dube shi a rude tace bazasu barta tayi
zaman aure ba. Dubi fa har baba ali suka cirewa
kunne dayayi kokarin mata fyade.
Alhaji Ilyasu ya fashe da dariya kada fa kema ki zama
sokuwa kamar yarki in banda abinki ko jaki sojoji
hudu suka jibga ai sai sun fitar masa da kunne
ballantana mutum.
Wannan duk yafaru ne watanni uku da suka wuce dan
haka ayanzu da farida ta fashe da kuka sai
mahaifiyarta ta dube shi tace.
Dan Allah Alhaji nidai ina rokarwa yarinyar nan
ahuwa abata nan da wata guda domin ta fito da
wanda take so tun da dai samarin nan tana dasu
bawai bata dasu bane.
Alhaji ilyasu ya gyara tabaransa sannan ya dubi
matarsa yace
Bazan iya sabawa babban aminina alkawari ba kuma
kada ki damu yaron nan kyakykyawa ne shima idan ta
ganshi zata so shi dan gidan alhaji shu'aibu ne wanda
muka zauna gida daya dashi a
london.
.
Kamar jira ake ya iddar da zancensa kwatsa sai sukaji
sallama wani kyakkyawan saurayi ne dogo ya shigo
dakin farine mai manyan idanu farare.
Baba Ina kwananku ya zube agaban su mahaifiyar
farida ta dubi saurayin sannan ta dubi farida daga
karshe kuma ta dubi mijinta baki na rawa tace.
Shine wannan? Bata taba tsammanin saurayin zaikai
kyawun haka ba.
.
Ba shi bane Wallahi shine. Farida tace da mahaifanta
cikin karaji a tsorace mahaifan nata suka dubi
saurayin a rude cikin rashin fahimtar abinda take nufi
sannan ne to suka lura da cewa kafar kyakkyawan
saurayin dake gabansu KOFATO
Ce.
.
BABI NA SHIDA 6
Nayi zaton zamu kai magariba ashe da wuri ma zaki
fito direban yace da mama sa'ar data fito daga gurin
bokan ta shiga gidan baya.
To ko tsayawa zamuyi mu kwana anan? Mama ta
tambaye shi cikin gatse.
Wani tattausan murmushi ya subuce daga bakin
direban sa'ar daya sawa motar giya suka fara tafiya.
Ni bance ba ranki yadade Allah yabaki hakuri
Da Hakurin ta mutu nawa ka bayar kudin sadaka?
Mama ta sake mayar da martani cikin tsiwa. Direban
yayi shiru daga wannan bai sake cewa da ita kala ba
har sa'ar daya ajeta a kofar gidanta.
Mama na fitowa daga cikin motart bata jira sun sake
sabon ciniki ba saita kirgo kudin data tabbata sun
lunka kudin da sau biyu ta mika masa
Jiki na rawa direban ya karba.
Nagode ranki yadade yace da ita cikin murmushi Ga
mamakinsa sai yaga mama ta sassauta fuska ta
haskake shi da murmushi tace.
Nima nagode suka danyi shiru na dan lokaci shi bai
tafi ba ita kuma bata juya ba.
Bani lambar wayarka kodon gaba idan kana da lokaci
sai in kiraka kana kaini unguwa
to ranki yadade direban yace yana rawar jiki lokaci
guda kuma ya fadawa mama lambar wayarsa ta
shigar atata wayar.
To shikenan sai na kira mama tace sannan ta juya
cikin sauri ta nufi kofar gidan.
Adaidai lokacin ne tayi Turus. Sa'ar data hangi
Mubarak saurayin da take mutuwar kauna tsaye
ajikin wani dan kanti na katako dake dab da kofar
gidan mama taji zuciyarta ta harba atsakankanin
hakarkarinta numfashinta ya dauke yawun bakinta ya
kafe tun da take aduniya bata taba kamuwa da ciwon
son wani 'Da namiji ba sai Mubakar agurin mama
maza tamkar kasuwa ne kashige su a lokacin dakaga
dama ka sayi abinda kake so ka fice. Ayanzu data kalli
mubarak sai mama ta gane kuskurenta a fili ashe dai
maza sun wuce kasuwa saidai Gidan kwana.
Sannunku mama tace dasu Mubarak da kuma mai
tsawon kantin sannan saita dubi cikin kantin tace
Kanada kwan wuta ne? Mama ta tambaya tana kallon
kayan kantin lokaci guda kuma tana satar kallon
Mubarak ta gefen ido
Akwai naira hamsin. Mai tsaron kantin yace
Ba musu ballamtana ta nemi ragi mama ta biya
sannan saita kuya kamar zata tafi saita tsaya agaban
Mubarak tace dashi a tausashe.
Mubarak ko gaisuwa babu? Mubarak ya dubeta
shekeke sannan ya shafi kwanjinsa yace
Kin Ajeni anan ne domin kullum ina gaisheki?
Mama taji kamar ya watsa mata wuta kunyar daya
saurayin mai tsaron kantin ta lullubeta.
Allah baka hakuri.... Ina kwana to ni na gaisheka
Lafiya lau mubarak yace sannan cikin sauri sai yabar
gurin ya nufi bakin titi.
Mama ta bishi da kallo cikin kunan rai har saida ya
bace sannan saita matsa jakarta daidai inda laya nan
da boka ya bata kana tayi murmushin yake.
Sai hakuri Mubarak dole ne saika aure ni tace da
kanta sannan saita dada matsa layarta cikin jaka.
** ** ** **
Duk wannan al'amura sun faru ne kwanaki bakwai
kafin honorabil sabo ya kori bebi daga gidansa.
Awannan ranar yan yansandan ciki suka sa bebi cikin
wata katuwar mota jeep kirar kamfanin Fodi bakikitin
da ita kamar shuni suka nufi kanon dabo daga abuja
su biyar ne acikin motar baya mutum uku ne babi da
wasu karti biyu sanye da bakaken kwat da bakaken
tabarau sun sata a tsakiya gaba kuma direba ne da
wani katon shima sanye da bakin tabarau da shudiyar
kwat.
Motar nata kwarara gudu bebi na tsakiyar kartin tayi
zuru da ita bata ko kwakkwaran numfashi da motsi
domin ta lura suma mutanen dake zaune akusa da ita
kyam suke basa motsi kamar busassun itatuwa
abinda yafi damun bebi shine da bata iya ganin
kwayar idanunsu.
Suna nan tafe zuciyar bebi nata sake sake na gargadi
mama. Bebi tace cikin zuciyarta tayi imani da cewa
mama bazata taba iya kashe mutum ba bera ma
tsoronsa takeyi ballantana har ta huda cikin mutum
kuma ma me zaisa ta kashe honorabil jatau? Bebi ta
tambayi kanta Yau da ace kudi sun bata adakin to da
sai ace ko kudin tazo sata yakamata ai ta ya kuma ta
kashe shi.... Kai bazaiyiyu ba ai mama ko kamata yayi
tana satar kudinsa babazata iya marinsa ma ba
ballantana har ta kasheshi to saidai kuma me yasa
har tsawon wannan lokaci mama bata yi waya ba?
Wadannan tarin tambayoyi su suke cunkushe
kwakwalwar Bebi.
.
Ance ki kwantar da hankalinki. Daya daga cikin kartin
yace da ita batareda ya dubi fuskarta ba. Babu laifin
da kikayi mana so muke kawai ki kaimu gidan da take
shikenan sai sai mu sallame ki.
.
Bebi tayi ajiyar zuciya sannan jikinta ya dauki rawa
kamar wacce zazzabi ke shirin hawa.
Ka... Kama ta zakuyi? Ta tambaye su cikin karfin hali
Yan tambayoyi kawai zamuyi mata daya daga cikin
karyin yace a takaice. Har yanzun nan bai jiyo ba
ballantana ma ya dubeta akwai wani abu a tattare da
yanayin mutanen dake baiwa bebi tsoro tabbas
ayanzu tasan ya zama dole ta gargadi mama halin da
ake cikin shin wai da tun farko ma meyasa batayi
tunanin tayi kiranta ba.
Kibar kaza acikin gashinta ki kaddara aranki cewa
bakima taba haduwa da mama ba kada ki kirata idan
kuma ita ta kira kice da ita kada ta sake ta dawo
Abuja.
Bebi ta tuna maganar honorabil sabo lokacin dayake
fatan Allah yasa wani bai lura da shigarsu gidan
honorabil jatau ba. Ashe ya maka masu gadi sun
lura.
Bebi ta muskuta abayan motar sannan ta takura
lokaci guda ta dubi daya daga cikin kartin tace a
tsorace.
Zaku iya tsayawa nayi fitsari?
Kwarai da gaske
ki saki ranki dan Allah duk kinbi kin rude ba wani abu
zamuyi miki ba.
Bebi ta dubi mai maganar da wani busashshen
murmushi sa'ar da direban motar ya tsaya dasu
acikin dajin.
Tsallaka can kiyi ga wata duhuwa can amma kada kiyi
nisa kinsan dajin da macizai
Bebi ta nufi bayan wasu dogayen ciyayi dake gefen
kwaltar amma daga can ciki ta tsugunna abayan
ciyawar. Saida ta tabbata babu mai ganinta Jiki na
rawa ta bude jakarta ta dauko waya tafara daddanna
lambobi wayar ta kwace ta fadi a kasa saboda rawar
da hannunta keyi cikin sauri bebi ta sake rarumar
wayar ta daddanna sannan ta kara a kunne tsahon
dakiku masu kamar sa'o'i uku agun bebi sai mama ta
dauki wayar acan daya bangaren.
Mama.... Bebi ce..... Saurara da kyau ki ji bamuda
lokacin gaisuwa.........
*** *** *** ***
FADILA ta dubi kan wayar tana mai shakkar abinda
taji daga bakin mahaifiyar tata duk da an bata izini ta
dauki wayar batayi hakan ba harda da tabbatar
mahaifiyarta ta gama fita daga dakin ta kuma rufe
kofar abayanta.
Hannunta tareda duk wani bangare na jikinta na rawa
fadila ta ganna abin amsa wayar sannan saita lumshe
idanu ta kara a kunnenta.
Fadila... Fadila ce? Don Allah kiyimin magana faisal
yace acan daya bangaren bakinsa na rawa kamar zai
fashe da kuka.
Faisal.. Fadila ta kira sunansa da wata rarraunar
murya.
Acan daya bangaren faisal yaji kamar an kwarawa
ruhinsa ruwan sanyi sa'ar dayaji muryar fadila.
Yanzu kam ya tabbata duk duniya babu wanda ya isa
ya rabashi da Fadilarsa domin yanzu ne yake
kaunarta fiyeda lokacin daya aureta ma.
Na'am fadilata kina ina? Ya tambaya cikin wata
tattausar murya.
Ina gida Faisal.
Me kike yi?
Azaune nake ni kadai ina kuka ina tunaninka....
Muryar fadila ta karye ta fara sheshshekar kuka.
Daina kuka dan Allah fadila kada kisa jinina ya hau.
Toh faisal.... Na daina fadila tace a raunane haryanzu
akwai alamu sheshshekar kuka a muryarta sukayi
shiru na yan dakiku.
Hello Fadila... Kina jina?
Ina jinka Faisal.
Kiyi hakuri don Allah ki yafemin abinda nayi miki.
Fadila ta danyi shiru acan daya bangaren.
Bazaki yafemin ba fadila? Aka sake shiru na dan
lokaci.
Na yafe maka faisal... Kaima kayi hakuri kaji?
Bakiyi min komai ba fadila Ilove you... Kinji?
Fadila ta dada lumshe idanunta acan daya bangaren
cikin wani irin farin ciki da bata taba jin irinsa ba.
Ina kewarka faisal... Yaushe zan ganka.
Gani nan zuwa yanzu. Adaidai wannan lokaci sai kofar
dakin Fadila ta bude mahaifiyarta ta shigo
idan kun gama hirar saiki fito falo su malam sunzo
zasu karasa miki addu'ar ki.
Faidla ta gyada kai lokaci guda kuma tace da faisal
acan daya bangaren.
Kabari sai nan da awa biyu
Tayi min tsayi faisal yace.
Zan dai zo saina jiraki a kofar gida har sai lokacin ya
cika.
** ** ** ** ** **
Dayake haryanzu fadila bata sa ko kashi daya daga
cikin takwas na kayan lefenta ba sa'ar data fita daga
wanka ta gama kwalliya saita kasa zaben irin kayan da
zata tari tsohon mijin nata dashi saida ta shafe sama
da rabin sa'a kafin daga karshe dai ta samu ta zabo
wani bakin siliki siliki mai sheki wanda akayiwa dinkin
riga da siket matsatstsu irin na wannan zamani tasa
Tuni Faisal ya dade adakin shakatawa na musamman
da aka ware dan manyan baki abokan mahaifinta.
Fadila ta gama feshe feshen turare kenan sai
mahaifiyarta ta shigo dakin sannan ta dubi irin kayan
da fadila ta sa sannan ta girgiza kai tace.
Oh Ya'yan zamani to daman yaya za'ayi ma ku rabu
da aljanu? Saiki nemi gyale mai fadi ki yafa karki kije
masa ahaka sinki sinkin kamar doya.
Fadila ta fashe da dariya wannan itace dariyarta ta
farko cikin wata uku rabonta da dariya tun yammacin
da sukayi sallama da faisal dinta yatafi yiwa abokansa
ban gajiya.
Baba kenan kuma dan nasa wannan sai aljanu su fara
bina.
Keda Allah can rufe min baki har zaki fara kaudi dan
kinga yazo.
Kinga mama ni dai ki daina janyo min su Fadila tace
cikin shagwaba
Dazan janyo miki su ai da ban sa anyi miki addu'ar
rabaki dasu ba mahaifiyarta tace sannanDa zan janyo miki su ai da ban sa anyi miki addu'ar
rabaki dasu ba Mahaifiyarta tace sannan saita matsa
kusa da yar tata tace a tausashe.
Ina fatan dai yanzu kin warware babu matsala?
Fadila ta gyada kai.
Har yan gane ganenma yanzu bakyayi ko? Fadila
takuma gyada kai mahaifiyarta tayi ajiyar zuciya
sannan tace ai saikije yana jiranki.
.
A dakin karbar baki na musamman faisal ya mike
tsaye cikin tsananin farin ciki sa'ar da masoyiyarsa
tsohuwar matarsa fadila ta shigo dakin.
Masoyan biyu suka zauna lokaci guda akan kujera
guda sannan suka fuskanci juna da wani narkakken
murmushi.
Fadila daga yau babu wanda ya isa ya rabani dake
Fadila ta lumshe ido cikin jin dadi tace kaidai fadi
gaskiya.
Gaskiyar kenan fadila ko Aljanin nan ne zai sake
dawowa bai isa ya rabani dake ba.
Fadila ta dube shi cikin mamaki tace kana nufin yanzu
ka yarda da abinda nafada wancan karon?
Cikin murmushi faisal yace ai bake kika fada min ba
agida na sami labarin a gurin MAMA
Masoyan biyu sukayi shiru suna kallon juna cikin
shauki na tsawon dakiku can sai faisal yayi ajiyar
zuciya a tausashe yace Matata.
Fadila ta lumshe idanu ta kuma bude su lokaci guda.
Umhm Mijin
Faisal ya mika hannu zai tabata sai fadila ta janye
jikinta cikin sauri tana dariya tace.
Kada ka manta ada nake matarka yanzu allura cikin
ruwa ce mai rabo ka dauka.
Faisal ya hade fuskarsa cikin wasa yace
Dan Allah ki bari kada kisa jinina ya hau yanzu yaushe
za'a mayar da auren namu?
Fadila ta dube shi ido da ido tace
Najisu mama suna cewa sai nan da shekara biyar.
Faisal ya kai mata duka suka fashe da dariya cikin
farin ciki.
** ** ** **
MAMA Tayi mika akan gadon sannan ta harba
kafafunta har sau biyu kamar mai hawan bori sannan
saita mike zaune a hankali ta dubi agogo karfe uku da
minti ashirin na yamma.
Tun karfe goma na safe data tashi ta wanke bakinta
tayi karin kumallo saita koma ta kwanta abinta bata
farka ba sai yanzu to me ya dameta? Daman aljanin
nan ne gashi kuma yau kwanaki bakwa da bokan nan
ya daukar mata sun cika.
Dan Haka mama ta gama imani da cewa daga yau ta
rabu da shegen aljanin nan.
Cikin murmushi saita lalubi kanta tsakanin kitso ta
shafi layar da bokan ya bata sannan ta fara tunanin ta
inda zata bullowa Mubarak idan anjima.
Idan har abinda bokan yafada mata ya kasance
gaskiya babu abinda zai hanata auren Mubarak
mama tagama yanke shawarar kawai ta auri Mubarak
tun dai tana kaunarsa tuni ta gama yanke kauna da
wannan harka ta karuwanci badon komai ba sai dan
kawai tana kaunar mubarak hakanan kuma tasan in
har ba garin kano zata bari ba cigaba da karuwanci
zai yi wuya tunda dai labarinta ya watsa ko ina gashi
wani abin kara tonon silili har masu sayar da hotuna
da kalandu ne ke yawo da hotunanta a kalanda da
kuma na likawa a kasan hoton an rubuta MATAR
ALJAN.
Zuciyar mama cike da wannan sake sake ta shiga
bandaki ta fesa wanka kana ta dawo ta zauna agaban
dogon madubin dake dakinta ajikin bango ta fara
goge goge da shafe shafe irin na kwararriyar yar
duniya bayan tsayin mintina tagama sannan ta kalli
surarta ajikin madubi mama tayiwa kanta murmushi
danjin dadin abinda tagani haryanzu nan ashe dai
fuskarta na nan dauke da TSOHON ALKAWARI kyawu
nan nata duk da yake dai yawan bilicin datake yafara
samun tasirin sauya launin kudukukinta amma
fararen idanunta da dan bakinta faffada gwanin iya
shan (Ice Cream) Madarar kankara su suka kara mata
kwarin gwiwa tabbas babu abinda zai hana Mubarak
kamuwa da sona idan ya ganni. Mama ta fada cikin
sauri dauke da nishadi sai mama ta nufi bakar
akwatinta mai kaya ta fara lalube laluben irin kayanda
yakamata tasa. Ta bude can ta leka can ta bincika can
daga karshe dai hannunta yakai kan wata bingilalliyar
riga tsawonta baifi iya cibiya ba shudiya ce kusan
rabin kirjin rigar duk a wawake yake hakanan rigar
tana da doguwar siket wacce idan mamatasa har
kasa take ja.
Mama tayi murmushi sannan ta dauki rigar.
Har ta fara sa rigar saikuma ta tsaya kai da wahala
mubarak yaso rigar nan dan naga ustazu ustazu ne
mama tace da kanta cikin murmushi. Duk da yake dai
tasan takadiri ne wasu ma nayi masa kallon dan daba
amma mama nada yakinin baya harka da mata.
Mintina ashirin suka shude daga karshe dai da kyar
mama ta zabo wata doguwar riga launin zuma da
dishi dishin fari kamar fatar damisa rigar na da
wando me dauke da wata beza beza ta farin leshi
daga can kasa kamar kafar namijin tattabara.
Karfe biyar saura yan mintuna mama ta gama
shirinta tsaf sai kamshi take yi tun daga sama har
kasa domin ta feshe jikinta da turare sama da kala
biyar mama tayiwa kanta kallon tsaf na karshe ajikin
madubi sannan saita dauki farar jakarta ta nufi kofar
gida inda Dabar su Mubarak take.
.
Mubarak na zaune shi kadai akan wani benci
karyayye agindin wata bishiyar darbejiya saiyaji
kamshi ya buhi hancinsa kamshin ya dadada masa
hanci matuka cikin sauri ya dago kai ahankali domin
yaga daga ina kamshin ke tashi dago idanunsa keda
wuya sai sukayi ido biyu.
Sannu da hutawa mubarak dama
Sannu da hutawa mubarak dama gurinka nazo.
.
Mubarak zuciyarsa ta harzuka wai shin dan uban
karuwar nan meyasa ta rainani ne? Mubarak ya
tambayi kansa rashin duka ne shaidaniyar zuciyar ta
shawarceshi nan da nan kamshin turaren dake tashi
yakoma kamar warin mushe agurin mubarak domin
aduk matan duniya babu wacce ya tsana irin mama
duk da yake dai daman shi mata basu dame shi ba
abinda ke gabansa shine kallon kwallo da yawon
farauta idan ta samu.
.
Kikazo kiyi min me?
Mubarak ya tambaya yana kallonta a fusace yana
ciccije baki.
Mama taji zuciyarta ta harba tsakanin hakarkarinta
bata tsammaci irin wannan daga bakinsa ba dan haka
saita sa hannu kamar zatayi susa ta shafo layar dake
tsakanin kitsonta awayance sannan ta dubi Mubarak
ido da ido
Gani nayi kamar gurin babu kowa shiyasa nazo in
tayaka zama.
Mubarak yaji zuciya ta tuke shi.
.
Kebace kar in barar dake an fada miki ni abokin
kazamai ne irinki?
Wannan kalma itace mafi muni da mama ta taba ji
arayuwarta abinda ya harzukata mama bata bari ya
bayyana a fuskarta ba.
Maimakon hakan sai mama ta dada shafar layar a
karo na biyu sannan babu zato babu tsammani sai ta
matsa inda mubarak yake ta zauna akan bencin bata
kura dacewa bencin gurgu bane tana zama sai
nauyinta ya rinjayesu nan da nan suka fadi da baya.
Wasu yara acan gefe na wasa suka fashe da dariya
harda sowa.
Mubarak ne yafara tashi a fusace sannan ya zare
bakin BELT
din dake kugunsa.
Kayi hakuri mubarak bansan a..... Kafin ta karasa
mubarak ya hauta da duka da farko mama ta dauka
abun wasa ne daga karshe kuma saitaga Mubarak
yasa kafa yayi bal da ita harsada ta fada KWATA.
Wayyo na shiga uku mama tasa ihu sannan ta mike ta
ruga aguje Mubarak ya rakata yana duka sai saida ya
rakata har kofar gida.
Akace bakya jin duka wai kina da aljani yanzu uban
wa na daka?
Mubarak yace yan ciccije baki sannann saiya juya
yana bubbudawa lokaci guda kuma yana mayar da
belt dinsa cikin wandonsa ya nufi inda mai dan kantin
nan na kusa da gidansu Mama yake.
Bani sigari yace da mai kantin yana muzurai.
Acan cikin gida mama tafada cikin daki tayi rub da
ciki akan gado ta fara rusa kuka. Ba kukan zafin dukan
da mubarak yayi mata ba takeyi ba kukan wulakanci
da nuna mata kyamarta da yayi takeyi. Mama ta tashi
zaune akan gadon hawaye sharaf shafar ta lalubi
kanta tsakanin kitson da niyyar ta dauko layar nan da
boka ya bata tayi jifa da ita adai wannan lokaci sai
wayar tafi da gidanka dake gefenta ta katse mata
hanzari sakamakon ruri data fara.
Da farko mama batayi niyyar amsa wayar ba dan
haka saita dauki wayar a fusace da niyyar ta kashe sai
kuma tayi turus sa'ar da taga sunan kawarta BEBI ya
bayyana a fuskar wayar. Nan da nan mama taji duk
damuwar dake tattare da ita ahalin yanzu an zare
mata ita kamar cirar kaya sannan alokaci guda wata
sabuwar damuwa ta maye gurbin wanccan. Cikin
sauri mama ta share hawaye sannan ta danna abin
amsa waya tace cikin wata malalaciyar murya.
Hello.
Mama bebice saurara da kyau kinsan bamuda lokacin
gaisuwa..... Ki tattara naki ya naki kibar kano kafin mu
karaso nan da awa biyu zamuzo da yan sanda wai
zasuyi miki tambayoyi akan mutuwar honorabil....
Dan Allah mama fadamin gaskiya ke kika kashe shi?
Mama taji wani zazzafan gumi ya fara sartu akan
gashinta tuni dama kukan dukan da tasha ya wanke
kwalliyar data shafe sama da sa'a guda tanayi.
Haba Bebi.... Wallahi bani na kashe shi ba...
Ke kinfi kowa sani na
Nida bera ma tsoroyake bani tayaya zan iya kashe
mutum..... Amma dai nasan ta yadda...mama ta danyi
shiru.
Kinsan me? Bebi tace acan daya bangaren cikin
kaduwa,
bani na kashe shi ba.... Amma akwai labari dai me
tsayi akan..... Kinga mama saurara bebi takatse ta
acan daya bangaren.
Koda bake kika kashe shi ba idan kinsa bakida gaskiya
kigudu kawai kuma amatsayin kawa domin na rama
irin mutuncin da kika nuna min lokacin dana fara
zuwa kano
ke kika fara bani sababbin kaya kyauta.... Sai wataran
kawata.
.
Layin ya katse daga can daya bangaren cikin tsananin
firgici zuciyar mama ta kankame gawar wayar a
kirjinta domin numfashinta ya fara daukewa tsahon
mintina tana nan azaune kwakwalwarta ta kasa
tunanin komai sai bayan mintina goma sannan ta
fuskanci halin da take ciki ta riga tasan har kullum
daman wannan al'amari kandarsu acikin ranta amma
matsalar wannan aljani dake addabarta su suka
dauke tunaninta daga kan duk wani hadari dake iya
samunta a sakamakon katuwar honorabil jatau. Da
farko mama ta yanke shawarar tayi zamanta kawai ta
jira zuwansu bebi tunda dai ai ba ita ta kashe shi ba
Jimawa kadan kuma sai wata zuciya tace da ita idan
suunzo kuma kuma kice dasu me? Kice dasu wani
aljani ne yafito atsakiyar dare ya kashe shi kina
kwance?
Mama tayi ajiyar zuciya tasan wannan zance ba mai
yiwuwa bane duk duniya wanene zai yarda da
wannan tatsuniya? Mama tasan tana fadin haka zata
fada hannun hukuma domin har yau din nan ita kanta
gani takeyi kamar mafarki.
Jikinta na rawa mama ta mike tsaye cikin zafin nama
naban mamaki ta hada duk suturarta cikin jakankuna
guda biyu sannan ta nufi bandaki ta wanke fuskarta
tana dawowa saitaci gaba da laluben sauran
abubuwan da take tsammanin zasuyi mata amfani
agaba da wannan karon mama bata damu da ta shafa
koda farar hoda ba ballantana ta tsaya doguwar
kwalliya tuni tagama yanke shawarar inda zata gudu
garin da aka dade ana bata labari aka kuma dade ana
shawarartar ta data tafi tun lokacin da aka kaddamar
da shari'ar musulunci a kano.
Ai saikiyi ta zama baki gaji da wahala bane kullum
ana binki ana takura rayuwarki kamar barauniya ance
kizo mu tafi inda zamu fantama babu mai rakura
mana.
Wata kawarta ce ke bata wannan shawara.
Wai wane gari ne wannan? Mama ta tambayi kawar.
Wani garine tsakanin bodar najeriya da nijar harka
agarin ba magana kizo kawai muyi tafiyarmu can inda
babu tsangwama.
Ayanzu da mama ta dauki jakankunan ta cikin sauri
can ta yanke shawarar guduwa babu abinda mama ta
tsana irin karuwancin kauye to amma yanzu batada
zabi akalla dai zan bace na dan lokaci kafin kura ta
lafa waya sani ma ko aljanu basa iya tsallaka boda
ballantana su dameni. Mama ta fadawa kanta domin
ta dada samun kwarin gwiwa abinda yafi damunta
ayanzu shine kudadenta dake banki kodayake tuni
mama tasan idan ta kwashe kudinta gaba daya daga
bankin zata iya damkasu a hannun wani dan canji a
wafa wanda take canjin kudin kasashen ketare
agurinsa tasan duk inda take zai iya tura mata da
kudinta.
Mama ta dubi agogo sa'ar data fito kofar gidan karfe
biyar saura tasan idan tayi sauri zata iya samun banki
ba'a rufe ba.
Mutane suka zuba mata idanu sa'ar da sukaga ta fito
da jakankuna a tunaninsu dukan da mubarak yayi
mata ne yasa zata tafi.
Mama ta isa bakin titi kafin ta tsayar da dan tasi sai ta
dandanna wasu lambobi awayarta. Sannan ta kara a
kunne tace
Hello.. Mu'azu... Nice mama dan Allah mu hadu
yanzun nan a OCEANIC BANK zan baka wasu kudi da
zakayi min sako dasu ta danyi shiru sannan saitace.
To shikenan amma kayi sauri don tafiya zanyi.
.
Wani da adaidaita sahu ya tsaya akusa da ita da
mashin mai kafa uku mama ta jefa jakankunanta biyu
aciki sannan ta shiga tace da direban
Oceanic bank zaka kaini daga nan kuma zamu wuce
tasha kofar ruwa.
Direban yaja mashin din ahankali.
Koda suka fara tafiya sai mama ta hangi mubarak
tsaye abakin titi kusa da wasu sayar da bakin Mai.
Batasan abinda yasa ba sai kawai ji tayi bakinta ya
subuce Yace. Mubarak
Mubarak ya juyo sai yaga mama tana daga masa
hannu cikin mashin mai taya uku.
Kai yau na hadu da mayya mubarak yace sannan ya
tsartar da yawu.
.
FARIDA
Dakin shakatawar yayi shiru bakajin motsin komai
kamar anyi ruwa an dauke.
Alhaji Ilyasu ne yafara magana cikin karfin hali yana
kallon kyakkyawan sauri me kafar Kofato.
Bawan Allah daga ina kake?
Farida acan gefe guda a takure ta dada runtse
idanunta da kunnuwanta bata son ji ko ganin abinda
ke faruwa idan su basu san kowanene saurayin ba ita
tasan shi.
NINE MIJIN FARIDA. Kyakkyawan saurayin yace dasu
sannan sai ya fashe da wata kakkausar dariya mai
kamar aradu wata iska mai karfi da sanyin gaske ta
fara fifita cikin dakin sannan sai wani farin hayaki ya
turnuke dakin.
Mahaifiyar Farida ta dauki satali a razane nan da nan
taji kafafunta bazasu iya daukar nauyinta ba cikin
sauri ta lalubi daya daga cikin kujerun ta lume aciki
domin bata iya ganin komai sai farin hayaki.
Tsahon lokaci kafin hayakin ya washe
.
Na shiga uku..... Yau mun hadu da jaraba Alhaji kaga
abinda nake fada ma ko? Mahaifiyar farida ce ke
magana
Alhaji Ilyasi yayi kasake na tsahon mintuna cikin
tsananin mamaki da fargaba yan mici micin idanunsa
suna kallon bangon dakin da wani yabashi labarin
abinda yafaru yanzun nan agabansa da babu abinda
zai hana

Please Login or Register in order to submit comment