Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

direban
gidansu na nan yana jira amma gudun kada ta
batawa kabir rai sai tace Bakomai mu hadu goben.
To shikenan sai munyi waya kabir yace yana kallonta
da murmushin yaudara.
Zaka kirani awaya idan naje gida?
Me zai hana Faridata
cikin farin ciki farida ta nufi inda direbanta baba ali
yake jira saidai kuma duk wannan farin kafin ta zauna
abayan motar ne. Domin tana zama data kalli
hannayenta saita nemi bakin zanen kunshin sama da
kasa ta rasa.
Na shiga uku na lalace.
Farida ta fashe da kuka a tsorace.
.
Baki shiga ba matata keda nayi miki gata na fito miki
da adonki agaban wanda kike so wata kakkaurar
murya tace da ita daga sama. Wayyao Allah....waye ke
magana? Farida ta tambaya tana waige waige abayan
motar.
Wa kikaji yayi magana? Direbanta ne baba ali ya
tambaya yana kallonta cikin tsananin mamaki.
.
** ** ** **
Washegari da safe misalin karfe goma da yan
mintuna direba baba ali yakawo farida cikin jami'ar
bayeron
dan Allah Baba ali idan ka koma gida kace da mama
sai wajen magariba zamu tashi kaji? Kace da ita kuma
wata kawata ce zata dawo dani Farida ce ke fadi tana
kallon dattijon tausashe.
Basai na dawo ba kenan baba ali ya tambaya cikin
sauri farida ta gyada kai Eh basai ka dawo ba kuma
dan Allah idan baba yadawo da wuri koda yake dai
nasan me yiwuwa jirgin yamma zai biyo daga abuja
amma idan yadawo kafin nan sai ka nemeni awaya
dan in sani kaji baba Ali?
Baba ali ya danyi jim yana duban sitiyarin motar dake
gabansa.
.
Saidai fa kinsan wayar tawa tafi sati biyu babu komai
acikinta kwandala daya da yan kwabbai suka rage
dasu nake flashing.
Jin haka keda wuya farida ta fahimci abinda yake nufi
cikin sauri ta bude jaka ta zaro naira dari biyar guda
biyu sababbi kar ko kari babu ta mika masa
Ga wannan kasa katin harma ka samu na goro.
Yauwa 'yata ko kefa ai yana zuwa zan fada miki kuma
ina ganin ma ba saina kira ki ba idan ya tambayeki
zan iya cewa dashi sai wajen takwas zaku tashi zan
koma a dauko ki nasan bazai damu ba.
Yauwa baba ali na gode farida tace sannan saita bude
kofar motar ta fice cikin sauri ta nufi inda dakin
daukar darasinsu yake nan da minti arba'in zasu fara
daukar darasi.
.
Dattijo baba ali yabita da kallo yana yabawa da
abinda yagani azuciyarsa tun tana karama yake
kaunarta aransa sannu ahankali tana girma yana
kallonta har zuwa yanzu data girmewa duk wani
mafalkin sa. Akaro na farko arayuwarsa sai baba ali
ya fara tunanin ina amace saurayine shi dan shekara
shirin da biyar ko talatin da babu abinda zai hana shi
ya nemi Farida baba ali na tattare da masaniyar cewa
duk watan duniya sai farida ta sauya sabon saurayi ya
lura da hakane da irin samarin da kan rakata zuwa
wajen motar yau in ya ganta da wancan dan tsololon
bayan sati biyu ko uku kuma sai ya ganta da wannan
dan lukutin to amma har kullum yafi ganin laifin
samarin domin yayi imani da cewa da ace shi keda
yan kananan shekaru kamar nasu da babu yadda
za'ayi farida ta gagare shi.
.
Shekaru talatin da doriya da suka gabata Baba ali
tsohon direban babbar motace ta daukar shanu daga
arewacin najeriya zuwa kudanci azamanin da yake da
sauran kuruciya mayen karfe abokansa direbobi yan
bariki suke kiransa domin a tarihi ba'a taba ganin
karuwar daya tsaya da ita bai dauki hankalinta ba
koda bashida ko kwabo saita saurare shi domin allah
ya hore masa iya zance yana dan shekara arba'in
aduniya wani babban hadari ya rutsa dashi ahanyar
ikko shi kadai ya rage bai mut ba acikin jama'ar
motoci shidan da sukayi ta haduwa da juna amma
dai ya tare a asibiti da karaya biyar saida yayi shekara
biyu bata tuki bayan ya warke alokacin ne to wani
babban amininsa tsohon direba andace shi
nutsatstsene ba kamarsa ba ya hadashi da
kwamishina Ilyasu Na Gamdo wanda ya ya kasance
mahaifi agurin farida yau shekara goma sha biyu
kenan yana aikin direban hajiya da ya'yanta.
Baba ali na nan zaune cikin motar afilin fakin yana
kallon farida har saida ta bace sannan saiya tuka
motar ya nufi kofar fita daga cikin jami'ar cikin
takaici.
Me zai hana ka dawo daukarta in yaso sai kayi duk
abinda kake so? wannan kururuwar shaidan ce cikin
kunnensa yana dada karfafa masa gwiwa akan ya
aiwatar da wani tsohon kudiri daya dade yana yawo
cikin zuciyarsa tun sa'ar daya fahimci farida ta zama
cikakkiyar mace. Akullum baba ali ya dubi farida sai
ya fara tunanin me zai hana idan ya sami dama yayi
mata fyade kawai ya gudu abinsa. Dama tuni wannan
aiki ya isheshi domin dan abinda ake biyansa bai taba
isarsa ba. Abinda yakamata inyi kenan Baba ali ya
dada jaddadawa kansa. Tuni ya gama lissafin inda zai
tsere domin anfi shekara uku wani tsohon abokinsa
dake zaune a ikko nayi masa tayin sayar da kwaya.
Wahalar banza kakeyi wannan sa'ar tamu tafi wannan
direban hajiyar kanata wahalar banza yanzu da
karfinka yagama karewa zasu sallameka shikenan
kashiga uku.
Baba ali yayiwa kansa murmushi sa'ar daya tuno
kalaman tsohon abokin nasa tabbas wahalar banza
nakeyi amma yau din nan zan karbi ladan aikina na
karshe in bar musu tsiyarsu baba ali ya fadawa
kansa. Abinda ya rage kawai yanzu shine idan
magariba tayi nayi mata waya ince ta tsaya baba yace
inzo in dauketa.
Wani busashshen murmushi irin na yan duniya ya
subuce masa cikin nishadi sai ya zura hannunsa
aljihu domin ya dauko sigari abinda bai taba yarda
yasha agaban uban gidansa kwamishina ba sa
hannunsa keda wuya cikin aljihun sai yan yatsunsa
sukaci karo da sababbin takardun kudin da farida
tabashi ga mamakin baba ali saiyaji kudin sunyi sanyi
sanyi karai adaidai lokacin ne ya kawo wani dan
cunkoson motoci dake unguwar rijiyar zaki.
Wannan kamar yanzu kuka futo daga inji baba ali
yace sa'ar daya daga takardun kudin da hannunsa na
dama yayin kuma da hannunsa na hagu yake tuki.
Kamata yayi ace kunyi dumi ba sanyi ba baba ali ya
kuma cewa da kudin cikin nishadi sannan sai ya
mayar dasu cikin aljihu daga tafin hannunsa keda
wuya saiyaga tambarin zanen dake jikin naira dari
biyar din yafito rangadadau a hannunsa. Cikin
mamaki sai baba ali ya goge tafin hannunsa ajikin
riga da zummar ya goge fentin ga mamakinsa launin
bai gogu ba baba ali yasake murmushi kana ya mayar
da hankalinsa kan tukin da yake sannan yace.
Yar banza yarinyar nan ko injin buga kudi sukedashi
acikin gida? Naga wannan ko bushewa ma basuyi ba
to duk tsiyarsu dai saina kashe su
Da'ace dattijon mai cikakkiyar nutsuwa ne daya sha
jikin jikinsa tun a wannan lokaci domin gargadi ne na
farko a gareshi AMMA BAI SAN HAKAN BA.
** ** ** **
Kabir ya fito daga cikin motarsa shudiya kirar toyota
ya mayar da kofar cikin burga da budawa ya rufe
sannan ya nufi farfajiyar jami'ar yana tafiya yana
wani tsalle kamar ansa masa dunkulen tamaula
akasan takalmin sanye yake da wata damammiyar
riga mai dogon hannu fara sol da ita kamar auduga
sai sheki takeyi acikin dan abinda ya rage nadaga
hasken ranar wannan yammaci agaban rigar an
rubuta HUG ME cikin harshen turanci da wasu bakin
zare mai sheki bakin wandon jeans din yayi matukar
dacewa da farar rigar hakanan farin takalmin dake
kafarsa gami da bakin tabarau din dake zaune daraf a
saman doron hancinsa su suka kammala wannan
kwalliya ta musamman dayayi domin ya samu damar
karya zuciyar Farida.
Kabir ya shafi gashin kansa wanda ke sheki
sakamakon man da ya sha masa sannan ya gyara yan
kanan sifikun dake cikin kunnuwansa wadanke ke
dauko masa wani tattausan kidan zamani daga cikin
wayarsa kirar Nokia dake aljihunsa yana tafiya yana
bin kidan da bakinsa wata sa'ar kuma yana
kwaikwayon wakar da fito babu abinda ya dame shi
matsalar kudi babu duk abinda yake so hajiya zata
bashi.
.
Mahaifiyarsa HAJJO HABIBA tsohuwa yar kano zuwa
jidda ce hakanan ayanzu duk wani abu da zai kawo
kudi tana ciki jita jita kuma nata yaduwa cewa wai yar
damfara ce da yan daban take samun kudin domin
ma'abota iya tsegumi na unguwarsu sunce basu taba
ganinta cikin talauci ba hakanan duk bayan wata
shida sai ta sayi motoci biyu sababbi daya tata daya
kuma ta danta kwaya daya jal aduniya shima har yau
ba'asan ubansa ba daga Allah sai ita sau da dama
makwabtanta wadanda gulmarsu tafi karfin zuciyarsu
sukan tambayeta wai shin waye uban kabir wannan
tambaya bata taba batawa Hajjo habiba rai ba
hakanan kullum amsarta dayace.
Uban kabir yana sudan.
.
Sannu ahankali yana tafe yana fito kamar tsohon
bature kabir ya karaso tagwayen dakunan daukar
darasi anan ne sukayi kicibis da safiyya kabir baiji
dadin ganinta ba domin yau ba ranarta bace kuma
shi duk ya fara gajiya ma da ita domin tafiya naci.
Safiyya duniya...daga ina haka? Kabir yace da faffadan
murmushin karya lokaci guda kuma yana duban dan
siririn wuyanta azuciyarsa yana cewa in banda
shirmena ma ina ni ina wannan yarinya duk kashi duk
zaman da suke da ita kabir bai lura da kashin ba sai
jiya da farida ta matso kusa da shi ta rike hannunsa.
Kai nake nema safiyya tace da murmushi
gani kin samu...ya akayi?
Mu tafi cikin motata ko motarka in fadama safiyya
tace lokaci guda kuma ta kama hannunsa.
Cikin sauri kabir ya girgiza kai sannan ya zare
hannunsa daga cikin nata.
Sauri nake zan koma gida hajiya ce ke nemana.
Safiyya ta hade fuska.
Haba kabir yaya zakayimin haka rabona dakai fa tun
kusan jiya by this time ta karasa da turanci.
Nace dake hajiya ce ke son ganina ki jirani zandawo
na dauke ki in anjima da daddare sai mu tafi waje
musha iska.
Nan da nan fuskar safiyya ta washe cikin kwarkwasa
ta dora hannayenta biyu akan tace a tausashe
alkawari?
Eh Promise kabir yace gamida gyada kai lokaci guda
yana Allah Allah ta dauke hannunta daga kan
kafadarsa kada Farida ta hangesu garinsa yayi kasa.
Bari inje saina dawo kafin safiyya ta sami ta cewa tuni
kabir yayi nisa safiyya ta bishi da kallo cikin mamaki
me ke faruwa ne? Wannan baiyi kama da kabir din
dana sani ba tace cikin zuciyarta.
Yana tafe yana waige waige ko zai hangota kabir ya
nufi inda motarsa take ya riga ya sani babu abinda zai
hana farida zuwa domin yasan ta gama kamuwa dan
haka yana zuwa saiya bude kofar gidan gaba na
motar ya zauna yana yabar kofar a bude kafafunsa
awaje sannan ya kunna rediyon dake gaban motar
kidan zamani yafara tashi a tausashe sannan sai wani
mawaki mai katon makwogwaro yafara wani abu mai
kamar ihu matsayin waka. Baifi ko minti biyar da
zama ba ya hangota ta nufo inda yake.
Numfashinsa ya dauke cak sa'ar dayaga irin shigar da
tayi.
Saura kadan na cuci kaina ashe bebin nan haka tayi
bala'in haduwa. Daga can nesa dashi Farida ta hange
shi farin ciki yaso ya mamayi zuciyarta amma rufanin
datake addabar zuciyarta shiya dakushe dukkan wani
digo na farin cikin dake zuciyarta.
Yanzu kam farida ta riga ta gama yarda da cewa
batada lafiya matsala ta sameta tabbas tasan ta gamu
da aljani tasha ji abakin kawayenta cewa aljanu suna
hawa kan mata suyi ta wahalar dasu mahaifiyarta ma
tasha yi mata fada akan barin gashin kanta awaje
kokuma zama tsirara tsirara domin acewar
mahaifiyarta wadannan abubuwa suke baiwa aljanu
sha'awa har su hau kan mace suyi ta bugeta acikin
jama'a.
Farida tayi ajiyar zuciya a tsorace sa'ar data fahimci
cewa idan ba wani ikon Allah ba itama kwanan nan
aljanin zai fara bugeta tuni ta fara nadamar zuwa
gidan dan daudun nan domin yi mata zanen kunshi
akan tsaraicinta farida ta riga tasan wannan kunshi
shine sanadiyyar wannan bala'in dake faruwa akanta
daman mahaifiyarta tashafada mata cewa yawan fito da
tsaraici a fili na cikin abinda ke sa aljanu su hau kan
mata.
.
Farida ta dubi tafin hannayenta dakuma bayansu
batayi mamaki ba sa'ar dataga zanen kunshin yadawo
rangadadau kamar ma yanzu aka zana shi duk kuwa
da cewa ta tabbata har lokacin da baba Ali ya sauketa
hannunta babu zanen kunshin.
Farida tayi matukar kyau awannan yammaci ita kanta
ta sani domin inka dauke yan littattafan dake
hannunta duk abin dake jikinta sabo ne tun daga kan
riga da siket din da mahaifiyarta ta sayo mata a
landan zuwa ga takalmin dake kafarta da yan
kunnayenta da sarkoki kai hatta alkalamin rubutun
dake hannunta sabo ne domin dazun ta saye shi. In
banda farida ta riga tasan zanen kunshin dake
hannunta na aljanu ne da sai tace shima ya taimaka
wajen fito da kyawunta a fili.
.
Kai gaskiya yau kinyi bala'in haduwa.
Kabir yace sa'ar da farida ta karaso inda yake lokaci
guda kuma ya rage sautin kidan dake tashi.
Nagode farida tace a tausashe.
Naji dadi da kwalliyata tayi maka kyau Ah gaskiya
tayimin zagayo ki shigo ciki kabir yace sannan ya
mika hannunsa ya bude mata daya kofar.
Ahankali farida ta shigo cikin motar ta zauna sannan
ta rufo kofar, shima kabir ya rufe kofar ya kunna
na'urar sanyi kana ya dubeta farida ta lura da irin
kallon dayakeyi mata dan haka cikin bin umarnin
shaidaniyar kawarta Asma'u saita dan bude gaban
rigarta kadan domin kabir ya sami damar hango
tsakanin kirjinta sannan saita dan matsa kusa da
jikinsa ta dora kanta akan kafadarsa.
Ilove You Kabir.
Kabir yaji kama ta watsa masa ruwan sanyi azuciya a
wannan dan takin dakikar saiyaji kaunarta ta mamaye
zuciyarsa amma a iya lokacin nan kawai kafin shaidan
ya maye gurbin da sha'awa.
Daga nan idan mun tashi ina zamu?
Kabir ya tambayeta yana wani lumlumshe idanu
sannan ya kama hannayenta biyu yana kallon zanen
kunshin dake jiki.
Farida ta dubeshi cikin mamaki tace
Gida mana ba gida kace zaka kaini ba?
Kabir ya dubeta ido da ido ya girgiza kai yace, sai
mun fara biyawa ta gidan wani abokina kafin nakai ki
gidan domin can zamufi samun sake.
Farida taji gabanta ya fadi bata dauka abin zaikai ga
haka ba yaushe za'ace ta bishi wani gidan aboki.
Ina ganin muyi hirarmu anan dai zaifi kyau... Farida
tace a tausashe zuciyarta na harbawa tana tsoron
kada ta batawa kabir rai.
Kabir ya kamo tafukan hannayenta guda biyu ya
dorasu akan fuskarsa yace.
Ina kaunar ki ne farida shi yasa na nemi ki bini domin
in nuna miki yadda nake kaunarki.
Farida taji gabanta ya fadi ahankali ta zame
hannayenta a wayance daga kan fuskarsa.
Haba farida bakya.... Kalmar ta makale a fatar bakin
kabir sa'ar dayaga yanayin fuskar farida ta sauya nan
da nan da kabir ya kalli fuskarsa a jikin madubi
alokacin daya hangi irin zanen kunshin dake tafin
hannunta rangadadau a zane akan kumatunsa kamar
yi masa akayi.
.
Kada ki damu idan bakya son zuwa yanzu maje
watarana kabir yace da ita cikin sauri shi a haukansa
ya dauka abinda yace ne ya birkita kamanninta.
Farida ta gyada kai babu magana idanunta zuru akan
zanen fulawar dake kan kumatunsa.
Ganin haryanzu batayi fara'a ba sai kabir ya rankwafa
jikinta yana cewa haba farida....kiyi min murmushi
mana konaji dan dadi dadi yana gama fadin haka sai
ya zura hannayensa ya tallafo kanta sannan ya tura
bakinsa gaba da nufin zai sumbaceta anan ne to wani
abu mai kamar hannu ya zuro cikin motar kamar
daga sama ya kifawa Kabir Mari.
Wayyo Allah... Kabir yasa ihu sa'ar da yaga wani
haske kamar wuta ya gifta akan fuskarsa.
Wayyo... Wayyo dan Allah ki taimakeni za'a kasheni
kabir ya sake kwala ihu sannan a rude sai ya bude
kofar motar ya fada kasa yana birgima afilin ajje
motoci na jami'ar bayero.
Daga yau ka sake lalata ya'yan mutane dan banza
lalatacce an fadama matata irin matan da zaka iya
tabawa ce.
Wata kakkausar murya tace daga sama sannan sai
aka kece da kakkausar dariya.
Tsananin kaduwa da tsoro su suka hana farida yin
motsi tana nan zaune akan kujerar motar kamar
gunki tana hangen kabir yana ta murkususu adaidai
lokacin ne to ta lura da wasu fararen abubuwa masu
kama da kashi akan cinyarta hannunta na rawa farida
ta dauki fafaren abubuwan. Saida ta kura musu idanu
sannan ta gane ashe Hakoran mutum ne guda uku
wannan shiya sata bude kofar motar ta fice aguje
sannan tasa kabir agaba ta fara Ihu.
Nan da nan gurin ya cika da dalibai hadiman jami'ar
masu gadi da shara aka zagaye kabir an rasa mai
taba shi can sai wani kakkarfan dattijo mai shara ya
matso ya tashi kabir da kyar daga kan fuskarsa jini na
zuba nan da nan daliban dake zagaye dashi suka rike
numfashi a razane sa'ar da sukaga bakin Kabir ya
karkace ya koma baya gashi babu hakoran gaba.
Ku kamamin mu shiga dashi cikin makaranta ayi
masa addu'a ina zaton aljanu ne suka shafe shi.
Dattijon yace.
.
BABI NA UKU 3
Abayan katuwar sakatariyar gwamnati ta tarayya
abuja jama'a ne jingim maza da mata kowa nasha'anin gabansa wasu nata sunturi daga can
zuwa nan suna kokarin neman kwatancen ofishin
wanda suke nema domin neman aiki ko kuma maula
hakanan agefe guda lemomin masu wayar haya
acikin rana sunyi sahu sahu jama'a har jerin gwano
sukeyi suna sayen katin waya da kuma buga wayar
haya don su sami zantawa da wadanda suka zo
nema. Acikin wadannan mutane masu waya hardasu
MAMA.
Mama tayi tsaki sa'ar data danna lambar kawarta
Bebi a karo na ashirin ana cewa wayar a kashe.
Yaya bebi zatayimin haka? Mama ta tambayi kanta
acikin damuwa.
Mama tazo sakateriyar ne badon takira wayar haya
ba sai dan anan ne bebi tace idan tazo ta kirata zatazo
ta sameta agurin daga nan kuma su wuce gidan da
nata honorabil din ya ajiyeta aciki.
Mama ta sake danna lambar wayar bebi akaro na
ashirin da daya cikin damuwa domin idan har bata
samu bebi ba tashiga cikin matsala dan ko kudin da
zata koma kano batadashi adaidai wannan lokacin ne
wayar dake hannunta ta dauki kara cikin sauri mama
ta dubi lambar dake fuskar wayar ta dauka bebi ce
Mama tayi tsaki sa'ar da taga ashe lambar ALHAJI
BILYAMINU ce matsolon saurayinta na kano
Hello menene? Mama tace dashi a fusace kuma fada-
fada, bi ahankali kada ki fasa min dodon kunne Alhaji
Bilyaminu yace acan daya bangaren
kina inane? Nazo gidanku ance min wai tun da
sassafe kika fita.
Nayi tafiya ne mama tace a yatsine
Eh naji kinyi tafiya kina ina nace? Ni ganinki nake
sonyi.
Bazaka sami ganina ba ayau jibi ma albarka dan ina
abuja
Alhaji bilyaminu ya rike numfashi acan daya
bangaren haba mama yaya zakiyi tafiya batareda kin
sanar dani ba?
A'a yau kajini da mutum mama tace cikin wayar da
karaji aurena kakeyi kokuwa zaman daduro muke
dakai? Duk da babu ko daya dai acikin abinda kike
fada ai yakamata kisanar dani.
To banyi niyya ba kai ni kaga nafa gaji da hulda da
marowatan mutane irinka yar motar nan ma ka kasa
sayamin sai ka bushi iska kazo ka uzuramin.
Haba mama meye yayi zafi haka? Ba nace zan saya
miki motar acikin wannan watan ba?
Haka dai kace amma wa yaga sayen mama tace
gamida tsaki sannan sai tayi kamar zata katse wayar
da sukeyi
kada ki kashe wayar dan Allah mama yanzu yaushe
zaki dawo?
Idan naga kidin mota cash acikin bakina.
Babu komai Alhaji bilyamin yace cikin sauri ki dawo
gobe sai in saya miki
bazan dawo gobe ba domin ayanzu haka ma kofar
Nikon Hotel nake inajiran wani darling dina ya fito
dan majalisa ne wanda yasan abinda akeyi da kudi ba
irinka ba.
Alhaji bilyaminu yaji wani matsanancin kishi ya tuke
zuciyarsa kai kace wata matarsa ce ta aure.
Amma agaskiya mama baki kyauta min ba yanzu duk
irin wahalar da nakeyi miki sai kinbi wani mutum har
zuwa abuja.
Idan kaji haushi ka ajjeni daduro mana ko kuma ka
aureni idan zaka iya. Alhaji bilya ya dauke wuta na
yan dakiku sannan saiya tausasa murya yace.
Allah baki hakuri mama...yanzu yaushe zaki dawo.
Nan da sati guda idan naga dubu dari shida kudin
sayan mota acikin bankina idan kuwa naji shiru me
yiwuwa har abada bazaka sake ganina ba.
Har abada fa kikace?
Kwarai kuwa angaya ma kano garin mu ce ko ka
manta ni yar gombe ce?
Zan turo miki da kudin gobe kiyimin text din lambar
asusun bankin naki yanzu kuma dan Allah ina jiranki
din idan zi yiwu ma ki dawo nan da kwana uku.
To shikenan saika turo din mama tace a yatsine
sannan batareda ta sake bashi damar cewa kala ba
saita kashe wayar sannan ta dira kafa akasa cikin
murna lallai abin da malamin tsibbun nan ya fada
min gaskiyane daman saida yace shi maganin kadan
kadan yake ci na fi wata shida ina zuba mai magani a
abinci yanaci amma shegen ya kasa yimin koda
kyautar dubu arba'in sai gashi yanzu a banza zai saya
min mota. Duk da ya rude ya dauka bazai sake ganina
ba mama ce ke fadin haka cikin zuciyarta sannan
saita kudiri aniyar in har alhaji bilyaminu ya saya
mata mota saita sayawa malaminta mashin.
Mama taci gaba da lallatsa lambar bebi yanzu kam
damuwar dake tattare da ita ta ragu domin tasan in
babu nan akwai can idan hagu taki saita koma dama
tasan ko bata sami ganin bebi ba tana iya yin waya
Alhaji Bilyaminu ya turo mata koda katin waya ne ta
sayar domin ta sami kudin mota.
Wayar mama ta sake daukar ruri akaro na biyu
awannan karonma mama tayi zaton ko bebi ce amma
data duba fuskar waya sai taga ashe bakuwar
lambace yanzu haka ma wani wahalallan ne mama
tace gamida tsaki sannan ta kara wayar a kunne.
Hello wanene?
Nice bebi dan Allah mama kiyi hakuri wallahi wayata
na jefar yanzun nan wata wayar na aiaka aka sayomin
kina ina?
Mama tayi ajiyar zuciya ina nan Federal secretaria
inda kikace na tsaya nafi awa daya da sauka.
Oh kiyi hakuri kawata gamu nan zuwa yanzun nan ai
gidan babu nisa da inda kike.
Mintina goma da wannan sai gasu bayan mota kirar
fijo wata dunkulalliya mai kamar kwai wani dogon
direba mai dogon sanko kamar titin mota ne ke janta.
Fara tafiyarsu keda wuya sai direban motar yakunna
na'urar sanyi nan da nan sassanyar iska ta fara fifita
su. mama tayi ajiyar zuciya sa'ar dataji sanyin iskar
ya fara busar da guminta.
.
Kina hutawa kawata mama tace da bebi.
Toh ya muka iya haka nan hali yayi bebi tace sannan
ta kalli hannun mama tayi kasa kasa da murya yadda
direban bazai iya jinsu ba tace.
Shegiya kawata tsumma makunshin cuta mage mai
kwanciyar daurar rai a ina akayi miki wannan
hadadden zanen kunshin.
Mama ta dubi hannunta cikin mamaki sannan ne to
taji kamar na'urar sanyin ta fara huro mata zafi
mama tayi imani dacewa har sa'ar data shiga cikin
motar babu wani zane a hannunta amma sai gashi
yanzu ya bayyana rangadadau kamar ma yanzu aka
gama zana shi.
Meye naga kin hade rai? Shegiya wallahi da gaske
nakeyi ba tsokanarki nake yi ba wannan idan nayi
wasa ai saiki kwace har nawa honorabil din bebi ce
ke fadi sa'ar da taga yanayin fuskar mama.
Mama ta feso murmushin karfin hali tace aina dauka
tsokanata kikeyi
kokusa wallahi kai zanen naki yayi kyau idan muka
koma kano sai kin rakani inda akayi miki wannan bebi
tace lokaci guda kuma ta kama hannun mama tana
dubawa.
Kai yaya naji hannunki sanyi karau kamar kankara
lafiyarki kuwa?
Mama ta dubi kawarta da murmushin yake tace
Lafiyar kenan me kika gani?
** ** ** ** **
HONORABIL JATAU ya kurawa mama idanu baya ko
kiftawa kamar wani tsohon maye tabbas ya yaba da
abinda yagani.
Acikin wani katon dakin shakatawa suke a tsakiyar
wani gida wanda ke boye abayan wani munafikin
lumbun shakatawa su hudune acikin dakin daga
bangaren gabas bebi ce da kawarta mama
kowannensu sanye da wata irin doguwar rigar
Alatsine mai shara share kamar buhun algarara.
Abangaren yamma na dakin honorabil jatau ne zaune
da babban abokinsa HONORABIL SABO wanda shine
saurayin Bebi.
Tun sa'ar da mama ta sauka agidan shakatawa na
honorabil sabo saurayin bebi basu sami ganinsa ba
sai washegari da misalin karfe goman dare yashigo
gidan acewarsa in dai har ba karya yake ba wai tun
jiya suke gurin taro basu fito ba sai yanzu wannan
bata dami bebi da mama ba domin sun huta sun
wala abinsu katon gidan na alfarma babu kowa aciki
sai su da wani dan dukurkushin kare mai yawan gashi
irin na turawa da kuma masu dafa musu abinci idan
sunci abinci sai suyi kwanciyarsu suyita barci idan
sun farka su kunna talabijin suyita kallon fina finan
da ake watsawa a kasashen turai. Babu abinda ya
dame su duk abinda suke bukata magana kawai
zasuyi sai akawo musu.
Sa'ar da honorabil sabo ya dawo ne da misalin karfe
goma sai suka gaisa da mama shi kansa ya yaba da
abinda yagani to saidai kuma bai isa ya nuna hakan a
zahiri ba tun da dai ga bebi manne akusa dashi
kamar cingam bayan yayi wanka ya huta sai ya
bugawa abokinsa honorabil jatau waya domin ya
sanar dashi cewar bakuwarsa ta sauka kuma gasu
nan zasuzo gidansa yanzun nan.
.
Sannu da zuwa mama honorabil jatau yace yana
dubanta da yan mici micin idanunsa kamsu kama
dana maciji tabbas ayadda yaga mama azahiri har
tafi yadda yaganta a hoto burgewa.
Ina ganin saimu tafi ko? Tun da mun hadaku.
Honorabil sabo yace sannan ya mike tsaye gamida
yiwa bebi alamar ta mike tsaye
to kawata sai yaushe kenan mama ta tambayi bebi.
Zamuyi waya bebi tace gamida kashe mata idanu. Da
haka suka fice daga dakin fitarsu keda wuya ko
motarsu basu tayarba honorabil jatau ya dawo kusa
da mama ya zauna sannan ya dora hannayensa biyu
akan kafadarta yace.
Naji dadin zuwanki mama hotonki ya burgeni to ashe
azahiri ma har kinfi haka burgewa inason ki sani
cewa bazaki yi nadamar zuwan da kikayi ba.
Mama ta lumshe idanu irin na kwararriyar karuwa
sannan ta kwanta ajikinsa tace.
Kaima bazakayi nadamar gayyatata da kayi ba.
.
Abinda basu sani ba shine wani acikinsu yayi
kuskure.
.
Tashi mu shiga daki naga dare yayi sosai ko? Babu
musu mama ta mike tsaye sannan saita bishi abaya
zuwa cikin wani dakin kwana da bata taba ganin
irinsa ba koda acikin mafalki lokacin sanyi.
Lokacin da duk wannan ke faruwa karfe biyu saura ne
na dare.
.
Dare yayi dare birnin tarayya yayi shiru bakajin
komai sai jifa jifan haushin karnuka nan da can
dakuma kukan tsuntsaye shima jifa jifa haka nan da
mutum zai kasa kunne da kyau bazai rasa jin rurin
dubban na'urorin sanyaya dakunan dake ta famar aiki
ba'a acikin birnin.
Dan haka ba dole bane wadannan yan kananan
sautuka su dami honorabil jatau da mama ba
wadanda ke kwance abinsu akan gadon alfarma barci
har da munshari sannu ahankali dakiku na wucewa
lokaci na matsowa har dai dan gajeren hannun dake
fuskar wani kyakkyawan agogo na azurfa dake ajiye a
gefen gadon ya nuna karfe hudu na asuba.
Honorabil jatau ya matso adaidai wannan lokacin
sannan ya tashi zaune akan gadon daga shi sai
gajeren wando yana mutsutstsuka idanu.
Bayan wasu yan dakiku idanunsa suka washe

Please Login or Register in order to submit comment