Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan
sai
Ya mika hannu zuwa kan wani karamin teburi adab
da gadon ya kunna wata irin fitila mai malafa nan da
nan wani tattausan haske mara kashe idanu ya
mamaye dakin.
.
Honorabil jatau ya mike tsaye a tsakiyar dakin sannan
ya kurawa mama idanu wacce ke kwance akan gadon
tana barci abinta cikin nutsuwa
hakika nayi sa'ar yarinya jatau yace aransa sannan ya
nufi bandakin dake fuskantar dakin kwanan domin
mararsa tayi nauyi tun wajen karfe ukun dare yake jin
fitsari amma yakasa tashi yaje yayi.
Honorabil ya tura kofar bandakin ahankali ya shiga
sannan sai yayi turus akofar cikin mamaki sa'ar
dayaji zubar ruwa acikin bandakin. Mamaki da
fargaba suka mamayi zuciyarsa lokaci guda kuma
domin shi yasan su biyu ne kawai adakin haka nan ya
tabbata bai bar famfo a bude ba.
Shigo mana yaka tsaya anan nima fitsarin ne ya tashe
ni naso in tabaka sainaga kamar kanajin dadin barcin
wata MAMA ce tsaye acikin bandakin sanye da
doguwar riga irinta waccan Mamar daya bari yanzun
nan akan gado tana barci.
Cikin tsananin firgici honorabil ya dubi mamar dake
tsaye cikin bandaki yace bakinsa na rawa.
Bake na gani yanzun nan a kwance akan gado ba?
Mama ta girgiza kai cikin mamaki sannan ta haske shi
da murmushi
kodai tarin wannan katon bargon naka mai gashi ka
gani kake zaton nice?
Honorabil ya girgiza kai a tsorace sannan sai ya
dubeta yace Jirani anan ina zuwa.
Jiki na rawa ya nufi cikin dakin kwanansu tun kafin ya
karasa bakin gadon sai wata Mamar ta mike zaune
akan gadon tace.
Wallahi harka bani tsoro inaka tafi na farka ban ganka
ba?
Honorabil jatau ya dubi kofar bandakin a tsorace
sannan sai ya zauna akan gadon ya dubi mama yace
a firgice.
Bake nagani yanzun nan a bandaki ba?
Mama ta girgiza kai sannan ta matso ta kwanta akan
cinyarsa yan yatsunta akan katon tumbinsa tace.
Kaifa baka rabuwa da abin dariya yaya gani anan tare
dakai zakace wai ka ganni yanzu a bandaki.
Mama ina ganin.......Kalmar ta makale a
makwogwaron honorabil sa'ar dayaji wasu irin Farata
masu kamar karfe sun nutse acikin tumbinsa.
Honorabil ya bude baki zaiyi ihu amma sautin bai
sami fitowa daga bakinsa ba.
Aka kece da wata mahaukaciyar dariya sannan sai
wani farin hayaki ya turnuke dakin.
Waya fadama wani katon banza maci amanar iyalinsa
yana taba min mata wata kakkausar murya tace daga
sama.
Mama tafito aguje daga cikin bandakin a tsorace
sa'ar dataji mahaukaciyar dariyar tana zuwa bakin
gadon sai tayi turus.
Akwance akan gadon harshensa ya zazzago waje
hanjinsa awaje jini ko ina akan gadon Honorabil
Jatau Ne.
** ** ** ** **
Yaya zaka fita baka bada kudin yaran nan na zuwa
makaranta ba.
Wata katuwar matace uwar gidan Alhaji bilyaminu ke
fada masa wannan kalma.
Ke dai wallahi bakya gode Allah....
Yanzu kudin makarantar ma saina basu ke bazaki iya
basu ba.
Kaidai baka tsoron Allah alhaji yanzu tsakani da Allah
aikin me nakeyi da zan sami kudin da zan biya
dawainiyar makarantar yara haba alhaji wallahi ya
kamata ka rage irin wannan mugun hali naka yanzu
kadubi yarannan kanana sai yawo suke acikin
tsumma kamar ya'yan almajirai? Ka dubi manyan
ya'yanka nan duk abokansa da motocin hawa amma
kai dan mugun hali da matsolanci ko dan lifan babur
din zamanin nan ka kasa saya musu suna zuwa
makaranta.
Alhaji bilyaminu ya katseta ta hanyar daga mata
hannu
kinga dan Allah sauri nake ni ban tambayeki wa'azi ba
na rediyo ma danakeji kullum kwanan duniya ya
isheni yanzu dai ga naira dari hudu nan ki rarraba
musu su tafi in sunje sacewa malamin gobe za'a
kawo kudin makarantar.
Matar ta dubi kudin daya mika mata cikin takaici.
To in ka bada wannan yaya zamuyi da maganar abinci
kuma? Na fa fada ma tun jiya bamuda ko kwayar
shinkafa daya agidan nan waken ma yakare gashi ma
jibi za'a mayar dasu MAMI DA HAFSAT makaranta...
Zan turo yanzun nan akawo buhun masara dana
wake dakuma fulawa yana gama fadin haka sai ya
nufi gajeri inda motarsa take cikin sauri yana duban
agogo.
Karfe hudu da rabi na yamma.
Matar ta share hawayen bakin ciki dake sartu akan
kumatunta sannan saitace cikin sheshshekar kuka
Allah idan munada hakki akan wannan mutumin
dayake zaluntar mu Allah ka bi mana hakkinmu.
.
Acan cikin gareji Alhaji Bilyaminu ya bude motarsa
yashiga sannan yafice aguje wani yaro mukhtar yazo
da sauri ya rufe garejin.
Koda yafara tafiya cikin motar saiya dauki wayarsa ya
danna wata lamba sannan ya kara a kunne.
Hello mama kina jina
Eh ina jinka akace acan daya bangaren cikin
sheshshekar kuka
meya samiki naji kamar kina kuka?
Kaina ne ke ciwo...Mama tayi masa karya
Toh Allah ya sauwake Alhaji bilyaminu yace sannan
saiya dada dacewa kije bankinki ki duba na turo miki
da kudin sayen motar amma dubu dari biyar kawai
aka samu.
Da'ace jiyane da ba karamin farin ciki maganar zatasa
mama ba amma abin daya faru adaren jiya yagama
fitar mata da sha'awar komai aduniya.
.
Sa'ar da mama ta tabbata aljanin dayayi musu zanen
kunshine ya kashe Jatau saita hada nata ya nata gari
na wayewa ta baro abuja mama tayi sa'a domin ta
sami wata gantalalliyar
naira dubu acikin hular honarabil jatau dake falon
gidan. Duka duka batafi sa'o'i hudu da sauka ba Alhaji
bilyaminu ya bugo mata wayar.
Saukarta keda wuya ta kunna rediyo domin jin
labaran BBC na rana kamar yadda ta tsammata tun
farko sun fadi labarin rasuwar honorabil jatau
acewarsu ana zaton yan fashine suka kashe shi to
amma haryanzu babu tabbacin iya adadin kudin da
suka sata daga nan ba'a sake wani kwakkwaran
bayani ba akan rasuwat tasa sai jifa jifan bayanai da
aka dauka daga bakin wasu abokan aikinsa yan
majalisu.
Ayanzu haka da mama take zaune jira take taji
kawarta bebi ta bugo mata waya ko kuma saurayinta
honorabil sabo domin jin inda take amma ga
mamakinta har yanzu shiru haka nan dataji wayarta
ta dauki ruri ma ta dauka su ne sai kuma taga ashe
saurayinta ne na kano Alhaji Bilyaminu.
.
Yaya naji kinyi shiru ko bakiji dadin abinda nayi bane?
Naji. Mama tace dashi a takaice.
Yauwwa ko kefa Alhaji bilyaminu yace baki na rawa.
Yanzu sai yaushe zaki dawo din?
Na dawo ma.
Kina nufin yanzu kina nan kano? Eh ina gida
gani nan zuwa yanzu Alhaji Bilyaminu yace sannan
saiya karkata kan motarsa ya sauya hanya ya fasa
zuwa bikin saukar karatun kur'ani da aka gayyace shi.
***
Me ke damuna ne? Alhaji bilyaminu ya tambayi kansa
sa'ar da yayi fakin da motarsa akofar gidansu mama
dake Na'ibawa.
Shi kansa abin na bashi mamaki irin yadda yaga ya
damu da mama sosai a yan kwanakin nan. Adacan
lokacin da suka fara alaka sam sam bata gabansa ya
dai dauke ta ne kamar sauran matan da suke
mu'amala a hadu ayi harka a watse babu wata
dangantaka mai tsayi.
Ayanzu da Alhaji yayi fakin da motar a kofar gidan ji
yake yi kama ma zai iya auren mama saboda irin
kaunar da yaji tana kwarara acikin zuciyarsa.
Alhaji bilyaminu yafito daga motar ya rufe sannan ya
nufi cikin gidan kai tsaye abinka da wanda ya saba
shiga. Ya riga yasan mata biyu ne kawai acikin gidan
daga Mama sai wata inyamura wacce ke aiki a
kamfanin magani. Mafi yawan lokuta baifiye isketa
agidan ba amma duk sa'are da akayi dace ya sami
inyamurar agida in zai fito sai ya jefe ta da dari biyar
badan komai ba sai don kawai yana son ya burge
mama.
Kwan...kwan kina ciki ne Alhaji bilyaminu yace sa'ar
daya shiga farfajiyar gidan yana wani bubbudewa
waishi ga dan duniya
ina nan shigo ciki mama tace jikinsa na rawa gamida
dokin ganinta alhaji bilyaminu yashiga dakin sannan
ya zauna akan gado kusa da mama
Kai yau ana zafi ki kunna AC mana
jiki ba laka kamar kazar da kwai ya fashewa aciki
mama ta mike sannan ta nufi makunnin na'urar
sanyaya dakin ta kunna.
Tun da yanzu mun gama da maganar mota kamata
kuma yayi ace na saya miki gida Alhaji bilyaminu yace
yana kallon irin kirar da Allah yayi mata sai yaga
kamar ta kara kyau. Azuciyarsa yana cewa idan na
rabu da mama bazan sake samun wata mace aduniya
kamarta ba.
Mama ta dawo kusa dashi ta zauna.
Kai din ne zaka iya sayawa mutum gida? Wannan ma
sa'a akayi kasa kudin shima saida ka Kwangemin
naira dubi dari
Alhaji bilyaminu ya cire babbar riga gamida hularsa
ya ajiye agefen gadon sannan ya shafi dogon
sankonsa daidai lokacin da sassanyar iskar ta fara
fifitashi
Da'ace hajiya mai gidan nan zata amince da wannan
gidan da kike ciki zan saya miki.
Allah sa. Mama tace a yatsine sannan ta dubi wayarta
tana mai mamakin abinda yasa haryanzu su bebi
basu nemeta ba anya kuwa yan sanda ba nemanta
sukeyi ba tasan babu abinda zai hana ace ita ta kashe
shi.
Tunanin me kikeyi naga kinyi shiru?
Alhaji bilyaminu ya bukata
Tunanin rayuwa mana
Haba mama kedai kin fiye damun kanki wallahi
menene yayi zafi haka da har ya gagari ruwan sanyin
da zamu zuba masa?
Mama tayi shiru bata bashi amsa ba lokaci guda
kuma tana dan wasa da yan yatsun hannunta
zamansa adakin tuni ya gama gundurarta domin duk
hankalin ta yana abuja. Saidai babu yadda ta iya
tunda dai ya zuba mata naira dubi dari biyar a
asusunta in banda wannan da tuni ta fatattake shi
nan da nan saita sami kanta tana mai addu'ar inama
dai ya gaggauta yayi abinda zaiyi ya fice ko ya kyaleta
da abinda ke damunta.
Na dade banga murmushin ki ba dan Allah ki saki
fuskarki mana ko ayi mana ruwan sama.
Mama ta saki wani busashshen murmushin yake ta
dubi Alhaji mai dogon sanko tace
Kaidai Alhaji baka girma
Alhaji bilyaminu ya kwanta ajikinta sannan ya kama
hannayenta yace in har zan tsufa da wannan harka to
kuwa ina tabbatar miki cewa harshe ma zai tuba da
yawan surutu.
.
Amma kuwa kayi asara mama tace cikin zuciyarta in
banda sha'anin karuwanci mace batada zabi da babu
abinda zaisa ta mu'amala da dattijo kamar wannan
dan kusan shekara sittin shi yasa a kullum ta tuna da
tarihin da ake ta fada mata tun tana karama saita
jinjinawa mahaifinta domin akalla dai shi bai yarda
sunyi zaman banza da mahaifiyarta ba aurenta yayi.
.
Kai amma fa zanen kunshin nan naki yayi kyau Alhaji
bilyaminu yace lokaci guda kuma ya tura mama
ahankali ya kwantar da ita akan gadon sannan ya
sake duban hannunta yace kai kunshin nan naki ya
zanu ZIZI.
.
Yana gama fadin haka sai yasa hannunsa ya shafi
zanen dake hannunta awannan lokacin ne to yaga
kakkauran hannunsa ya zuke yakoma kamar lawurjen
wando.
Kai-Kai meye haka?
Alhaji Bilyaminu yace a tsorace yana kallon
hannunsa.
Mama ta tashi zaune a tsorace domin tariga tasan
abinda ke shirin faruwa tashinta keda wuya sai taga
hannun Alhaji Bilyaminu ya shanye yakoma kamar
maburgi sannan ahankali sai na hagun ma ya zuke
nan take.
Wayyo Allah... Wayyo na shiga uku Alhaji bilyaminu
yasa ihu agigice sannan ya mike tsaye zaifito aguje
daga dakin.
Taku uku kawai yayi sai ya zame ya fadi kafafunsa ma
sun shanye bazasu iya daukar nauyinsa ba.
.
Aka kece da mahaukaciyar dariyar nan sannan sai
kakkausar muryar tace
Daga yau bazaka sake shafar hannun matar kowa ba
ballantana tawa.
.
BABI NA HUDU 4
Faisal yayi fakin da motar akusa da sauran motocinsu
guda uku ya bude kofar motarsa yafito da lema
ahannu domin ruwan saman ya dada kecewa kamar
da bakin kwarya
Tabbas laifina ne faisal ya fadawa kansa sa'ar daya
nufi inda ginin gidan yake agaggauce yana tafiya iska
na dawo dashi baya sakamakon lemar dake
hannunsa kodayake dai lalura ce ta kawo haka. Faisal
ya kuma fadawa zuciyarsa idan ba rashin lafiyar
mahaifiya ba me zaisa na in tafi nabar sabuwar
amarya ta kwana daya kacal da tarewa har kusan
goma sha biyun dare ban dawo gida ba gashi nan
yanzu na barta ana neman a tsorata min ita yaya
zatace wai nine kwance kusa da ita?
Ahaka yana wannan tunani har ya shiga cikin dakin
kwanansu.
Sannan ne to yayi turus yana kallon Fadila wacce ke
zaune akan matashin kai ta takure ajikin bango daga
can kuryar daki tana sharbar kuka.
.
Daina kuka gani nadawo... Fadamin duk abinda ke
faruwa
fadila ta dubi fuskar mijinta a rude tasan abin kenan
da yakamata tayi ta fada masa dukkan abinda yafaru
tun daga ranar da sukaje kunshi gidan dan daudun
har zuwa yanzu sai dai tambayar anan itace anya
kuwa faisal zai iya amincewa da wannan labari mai
kamar tatsuniya.
Faisal ya matsa kusa da amaryarsa ya zauna sannan
ya mika hannu zai janyota jikinsa sai yaga ta janye
jikinta cikin sauri.
Meye kuma haka wai meke damunki ne ki fadamin
mana.
Fadila ta dubeshi cikin sheshshekar kuka wani aljani
ne ke damuna faisal shine yazo min a siffarka.
Faisal ya dubi fadila a rude azuciyarsa yana cewa
anya kuwa yarinyar nan ba tabuwa tayi ba.
Aljani fa kikace mai siffanta a kwance akusa dake to
yanzu yana ina? Faisal ya tambayeta akwai alamun
zargi karara akan fuskarsa.
Ya bace... Kanayi min waya ya bace
Faisal ya girgiza kai sannan ya dubeta da murmushi
yace
Kinga fadila kin kwantar da hankalinki kawai babu
wani abu da zai sake faruwa tunda gani na dawo ina
ganin tsorata kawai kikayi ganin bana nan shine kika
fara gane gane.
Daman na sani wannan ma bai yarda ba to yaya
kuma idan na bashi labarin gidan kunshi fadila ta
fada aranta.
Come On fadilata zo nan ki kwanta faisal yace yana
nuna mata kan cinyarsa cikin lallashi
Cikin sauri fadila ta dada janye jikinta ta dada
mannewa da bangon kamar zata huda bangon ta
shige ciki
Faisal ya dubi amaryarsa cikin tsananin mamaki
sannan saiya mike tsaye akan gadon a dudduke ya
nufi inda take zai janyota jikinsa lokaci guda kuma
yana cewa zo nan mana kefa wallahi kin cika rudewa
da yawa.
Kada ka tabani dan Allah fadila ta roke shi cikin karaji
yanzu kam ta riga ta sani rayuwarta data mijinta suna
cikin hadari.
Me kike nufi ba zan tabaki ba fadila?
Faisal ya tambaya akwai alamun sosuwar zuciya akan
fuskarsa.
Nidai nace kada ka tabani dan Allah zanyi ma bayani
cikin fushi sai faisal yakai mata cafka ya fizgota jikinsa
tana fadowa zai zanin dake jikinta ya fadi sannan ne
to faisal yayi sororo yana kallon abin mamaki tun
daga kasanta har zuwa kan kirjin amaryarsa fadila
zanen furanni ne kunshin zamani irin wanda yace tayi
masa kafin akawota batayi ba.
.
Tambayar farko data fara zuwa zuciyarsa itace
yaushe har farida ta fita akayi mata wannan zanen ita
da aka kawota gidan jiya jiyan nan faisal ya dubi
amaryarsa fadila wacce ke kwance rub da ciki akan
cinyarsa tana kuka.
Yaushe kika fita akayi miki wannan? Ya tambayeta
akwai alamun zargi karara a yanayin sautin
muryarsa.
Fadila tayi ajiyar zuciya ta riga tasan an rutsata bata
da mafita dolene ta fada masa gaskiyar al'amarin ko
ya yarda ko kada ya yarda.
Kayi hakuri Faisal.... Wallahi agidan wani dan daudu
mukaje yayi...
Me faisal ya daka mata tsawa cikin kaduwa gidan dan
daudu....kai amma fadila kin cuceni yanzu daga kawo
min ke jiya shine har kika fita unguwa batareda kin
fadamin ba kikaje kika budewa wani katon banza
tsaraicinki yanayi miki zane
Wallahi kin cuceni yana gama fadin haka sai ya turar
da ita gefe guda ya tashi tsaye.
Fadila ta fashe da kuka tsaya kaji dan Allah faisal bari
na karasa maka abin....
Babu wata magana da zan sake saurara daga bakin
kifaisal yace bakinsa na kumfa saboda tsabar zafin
zuciya.
Shine da kika fake da aljani zakiyi masa karya.... Waya
sani ma ko dan daudun kika kawomin gida kikace wai
aljani ne a kwance kusa dake... Allah ya isa tsakanina
dake fadila.
.
Fadila ta kife kai akan gadon ta fara rusa kuka
Ahaka suka wayi gari ita tana cikin dakin kwanansu
tana rusa kuka shi kuwa yana falo zaune akan kujera
hawayen bakin ciki na zuba akan kumatunsa gari na
wayewa ya mika mata takarda.
NA SAKE KI SAKI BIYU 2.
** ** ** ** **
Farida na zaune agefe guda tana sheshshekar kuka
yayinda dalibai keta tururuwa daga dakin kwanan
dalibai zuwa kallon kabir wanda ke kwance akan wani
daben siminti wasu tsofafaffi uku sun zagaye shi suna
tofe shi da yawu daga baya bayan cincirindon daliban
wasu masu karancin kunya sun fara gunaguni me zai
hana a tafi dashi asibiri tunda dai ga bakinsa nan har
jini yakeyi.
Duk wannan rudani da akeyi farida na can gefe nesa
dasu bama kowa yake lura da ita ba domin hankalin
jama'a na kan kabir wanda ke kwance yana
murkususu gashi kuma daman ma duhun dare tuni
ya gama shigowa dan haka su kansu tsofaffin dakeyi
masa addu'a saida wasu samari suka taimaka wajen
haske gurin da fitilolin dake jikin wayarsu.
.
Ana cikin wannan rudani sai farida taji wayarta ta
fara ruri ajakarta hakan shi yadawo da ita cikin
hankalinta akaro na farko tasan cewa daga gidane
meyiwa ake nemanta jiki na rawa ta zaro wayarta
daga cikin jaka sannan ta kara a kunne.
Hello tace da wata malalaciyar murya
Farida...Farida nine baba ali Alhaji yadawo na fada
masa abinda kikace na fada shine yace in taho yanzu
yanzun nan na mayar dake gida kina ina?
Farida ta lumshe idanu tana sauraron sa har sa'ar
daya gama sannan sai ta kuma cewa cikin malalaciyar
murya
Taho mu tafi zan jiraka a filin fakin.
Gama fadin haka keda wuya saita zagaye taron
jama'a tabi duhun dare ta wuce kai tsaye zuwa filin
fakin. Ayanzu duk abubuwan da suke faruwa sun fara
dawowa cikin zuciyarta garai garai tabbas tasan da
kabir bai matsanta mata ba
daya bari sun zauna hirar arziki batareda yayi kokarin
turo bakinsa izuwa sumbatarta ba to da yanzu yana
nan lafiyarsa kalau. Kabir shi ya janyowa kansa... Ba
laifina bane farida ta kuma jaddadawa kanta amma
duk da haka dai ta tausayawa kabir musamman da
taga bakinsa ya koma baya.
Tana nan tsaye ita kadai a tsakankanin daidaikun
motocin da suka rage a filin fakin din zuciyarta
lullube da duhun rudanin dake tattare da rayuwarta
ta kasa tunanin komai ahaka direbanta baba ali ya
sameta.
Tunanin me kikeyi ne? Ya tambayeta cikin mamaki
sa'ar daya tsaya akusa da ita domin yaga hon dinsa
uku bata juya ba farida tayi firgigit kamar wacce ta
tashi daga wani nannauyan barci ta dubeshi sannan
ta juyo tayiwa inda kabir ke kwance ganin karshe.
.
Kace baba ya dawo?
Ta tambaya batareda ta kalli baba ali ba lokaci guda
kuma ta bude gidan baya na motar ta shige ta zauna
Tun dazu ya dawo...misalin biyar da rabi na dauko shi
a filin saukar jirage ya tambayeni ke sainace dashi
jarrabawar gwaji kikeyi ba zaku tashi ba sai karfe
takwas baba ali ke fadin haka amma bai yarda sun
hada idanu da ita ba.
Uhm abinda farida tace kenan azuciyarta tana
mamaki domin bata taba ganin mahaifinta yadawo
karfe biyar da rabi ba.
Dattijo baba ali ya tuka motar ahankali ya nufi kofar
fitar daga sabuwar jami'ar bayero ta kano lokaci guda
kuma ya gyara madubin gaban motar na sama ta
yadda zaike iya samun damar satar kallon fuskar
farida shirun da tayi da kuma irin yanayin fuskarsa
awannan lokaci yafara damun zuciyarsa duk da yake
dai har yanzu nan zuciyarsa bata karaya ba tun da dai
daman kome zai faruma ai ba'a son ranta za'ayi ba.
Sannu ahankali suka kawo kofar fita daga sabuwar
jami'ar bayaro direba baba ali ya mikawa mai gadi
balgacaccen jar roban da ake baiwa duk wanda zai
shiga jami'ar amatsayin shaida yana fitowa daga
kofar jami'ar sai ya karkata hannun dama yabi hanyar
da zata kaishi Gwarzo maimakon yabi wacce zata
dawo dashi cikin birnin Kano.
Ina kuma zamu? Farida ta tambaya cikin mamaki.
Baba ali ya shafi doguwar hular dake kansa mai
kamar ribabbiyar dankali yace ranki yadade yimin
afuwa muje nan gaban jan guza musha mai.
Haba baba ali duk man dake cikin gari bai isheka ba
har sai munje gaban wani jan guza?
Baba ali ya karawa motar giya daga daya zuwa biyu
sannan ya kaiwa wani nacaccan kuda duka dake ta
faman zarya agefen kunnensa na hagu
Mai yafi araha awajen gari shiyasa nake neman ki
rufa min asiri kamar yadda nima na rufa miki kinga
dan ragin da muke samu da shine muke dan rage
zafin garin nan.
Baba ali yadanyi shiru yana satar kallonta cikin
madubin dake saman motar.
Shikenan farida tace dashi sannan ta dauke kanta
gefe guda tana kallon korayen ciyayi da tafasa da
sukayi sahu sahu agefen hanya abin gwanin ban
sha'awa daga inda take zaunen acikin hasken fitilun
motocin dake ta wuce su tana iya hango koramu inda
ruwan damuna ke taruwa wasu kananan
kwari sai sunturi sukeyi a saman ruwan
acikinsu har dani dan tsololin kwaro mai siffar jirgi
mai saukar ungulu. Wata kawar farida ta taba cewa
da ita siffar wannan kwaron nasara ya kwaikwaya
lokacin da zai kera jirgi mai saukar ungulu.
.
Na fuskanci kamar kina sha'awar ganin korayen ciyayi
acikin hasken fitilu direba baba ali ya tambaya sa'ar
daya lura da cewa tunda suka baro kofar jami'ar
idanunta waje suke kallo.
Uhm suna burgeni musamman da yamma likis kafin
rana ta gama faduwa
Harzuwa lokacin da farida ke wannan batu zuciyarta
bata daina hasko mata jifa jifan hoton al'amarin daya
faru akan kabir ba.
To amma tafiyar da suke yanzu ahankali ta fara
samun saukin kaduwar dake dabaibaye da
kwakwalwarta musamman ma lokacin da ta sauke
gilashin motar daddadar iskar damuna mai dauke da
kamshin kasa da tsirrai ta daki fuskarta.
Haryanzu bamu karasa gidan man bane? Farida ta
tambaye shi ganin cewa tafiya ta mike har sun wuce
kwanar jun guza
yana nan gaba kadan awani dan kauye dattijon
direban yace batareda da ya dubi fuskarta ba.
Sannu ahankali suna tafiya har mintina biyar suka
shude adaidai lokacin ne dattijon direban ya ragewa
motar wuta adaidai wasu dogayen duwatsu dake
gaban wani gulbi ma'abocin tarin ciyayi masu tsaye
baba ali ya karkata kan motar lokaci guda ya kutsa ta
cikin ciyayin zuwa bayan dutsen sannan ya tsayar da
motar.
Me....me kuma zamuyi anan? Farida ta tambaya a
tsorace akwai alamun firgici karara akan kyakkyawar
fuskar budurwar
Dan Allah baba ali ka fitar damu daga cikin wannan
kungurmin dajin..... Ya zaka shigo damu nan acikin
wannan duhun dare
Baba ali ya dubeta da wani kekasasshen murmushi
lokacin bada umarninki ya rigaya ya wuce yanzu nike
da ikon bada umarni.
Ban...ban fahimce ka ba? Farida tace a tsorace lokaci
guda kuma tana duba izuwa cikin duhun daren da
kuma dogayen duwatsu da ciyayin dake zagaye dasu.
Tuni ta fara tunanin mafarki takeyi tabbas wannan ba
gaskiya bane awata duniyar dai take.
Abinda nake nufi shine duk abinda nace kiyi sai kiyi
baba ali yace lokaci guda kuma ya bude gidan gaba
na motar ya fito waje sannan saiya bude gidan baya
na motar inda farida take zaune ya zauna akusa da ita
cikin sauri kamar wacce maciji ya rabeta ta matsa
can jikin daya kofar motar a tsorace.
Kaga baba ali wannan in wasa ne ni bana so dan
Allah ka fitar dani daga cikin dajin nan.
Ba wasa bane farida wannan al'amari gaske ne na
dade ina fatan samun wannan dama ban samu ba sai
yau....
Me.... Kake nufi farida ta tambaye shi a fusace kuma
rabi a tsorace
Abinda nake nufi shine ki cire kayanki ahankali tun
kafin na cire miki su.
Haba... Baba ali ya zakayimin haka ?
Kamar yaya na cire kayana?
Nace ki cire kayan jikin mubi abin nan ahankali ko so
kike na takura ki da karfin tsiya?
Na shiga uku farida tace cikin shashshekar kuka dan
Allah ka rufa min asiri....wallahi ni ban tabayin abinda
kake nufi ba.
Yau zaki fara cire kayanki kigani baba ali yace sannan
ya matsa kusa da ita ya dora hannunsa akan
kafadarta.
Cire mana yar 'yata yanzu zamu gama
farida ta rike numfashinta cikin tsananin kaduwa
hannun dattijon direban dake kafadarta tamkar wani
kan bakin maciji take jinsa.
Kada ka tabani dan Allah... Matsa daga kusa dani
farida takuma mannewa ajikin kofar motar lokaci
guda muka ta rufe hancinta da tafin hannu domin
duk lokacin da dattijon yayi magana sai taji bakin sa
na hamami kamar bakin kura tabbas tasan kowane
lokaci daga yanzu zata iya fara amai.
Zan lissafa miki uku baba ali yace kana yayi wuce ya
kama gefen rigarya da busassun hannayensa masu
kamar itace.
Idan baki cire ba ni zan cire miki.
Farida ta kwalla ihu a razane sa'ar dataji ya fara ja
mata riga har wuyan rigarta ya sauko zuwa kafada
duwatsun dake zagaye dasu suka amsa kuwwar
datayi wani kurege ya ruga aguje ya shige cikin
raminsa a tsorace sakamakon ihun.
.
Duk wannan bazata kaiki ba fitananniya ai ba akaina
kika fara ba yana fadin haka sai ya cafko hannunta da
zummar ya janyota jikinsa ga mamakinsa sai yaji
kamar ya cafko tubakin kankara nan da nan yaji
hannunsa ya sandare sannan sai jinin jikinsa yafara
tafiyar hawainiya acikin jijiyoyinsa adaidai lokacin da
wata sassanyar iska mai karfin gaske ta fara fifita su
acikin Motar.
Baba ali yaji hannayensa sun dada sandarewa cikin
gaggawa ya saki hannayen a tsorace kana ya dubeta
Me kikayi min naji hannuna kamar zai tsinke? Kafin ya
rufe bakinsa sai yaji wani abu kai karfin gaske kamar
kofaton doki ya daki tsakiyar fuskarsa.
Wayyo Allah Wayyo Allah.
Farida tayi sororo ciki rudani tana kallon ikon Allah
tabbas yanzu tasan abinda ke faruwa abin nan mai
kamar kofaton doki ya kuma dungurowa ta cikin tagar
motar ya daki gefen fuskar baba ali.
Wayyo Allah... Na shiga uku.
Sai ka shiga talatin ma idan ka kara tabamin matata
kakkausar murya mai amsa amo tace adaidai wannan
lokacin ne to farida taji lema lema ajikin sangalalin
hannun tatana tabawa sai taji wani abu mai laushi laushi dago
shi sama keda wuya saita jefar dashi sannan cikin
tsananin razana sai hannunta ya kai izuwa mabudin
kofar motar farida ta bude sannan ta nufi hanyar da
take tunanin zata kaita izuwa bakin titi aguje tana ihu
kamar mahaukaciya.
Abinda yasata wannan firgici abinda yasata wannan
gudu tana ihu shine kunnen direbanta Baba Ali
datagani akan sangalalin hannunta yana mots kamar
kosai mai rai.
** ** ** **
Bebi ta wangame baki tana hamma babu kalmar
shahada sai wani dan ihu da tayi kamar tsuntsuwa
sannan taja wata doguwar mika akan tattausan
gadon alfarmar ta mirgina kamar yadda jaki yakeyi
idan yana wanka acikin toka.
Kai ashe rana tayi haka. Tace da kanta sannan cikin
lalaci acikin tattausan kilishin dake mamaye da tsakar
dakin.
Ahankali kamar kazar da kwai ya fashewa aciki bebi ta
nufi gindin tagar dakin dake fuskantar koren lambun
shakatawar gidan honorabil sabo dake bayan dakin ta
zuge labulen sannan ta bude tagar dakin sassanyar
iska tsabtatacciya daga cikin lambun ta bugi fuskarta.
Bebi tayi ajiyar zuciya domin taji sanyin iska yafara
yawa
Da gaske dai sanyin za'ayi kenan? Ta tambayi kanta
da kanta ganin cewa har kusan biyu amma kamar
goma sannan saita bar jikin tagar ta dawo kan gado
ta zauna tana tunanin makomarta lokaci guda kuma
ta dubi fuskarta acikin dan madubin dake daf da
gadon ba karamin kaduwa tayi sa'ar dataga fuskarta
ta fara tauyewa hakanan baki baki shudi shudin
tambarin Bilicin yafara bayyana a fuskarta.
Na shiga uku bebi tace a tsorace ta riga tasan bayan
kyan kirar jikinta da take takama dashi abu na biyu
dake fizgo hankalin mazaje izuwa

Please Login or Register in order to submit comment