Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya karyatashi yanzu ma ganin abin yake
kamar ruda ido.
Farida ya kira sunan yarsa a sanyaye akwai alamun
nadama karara a fuskarsa
Farida ta dago kai daga inda take ta share hawaye
sannan ta fuskanci mahaifinta.
Kin tabbata duk labarin nan da kika fadawa
mahaifiyarki gaskiyane?
Farida ta gyada kai batareda tayi magana ba.
Gashi nan anyi ma agabanka Mahaifiyar farida ta
fada bakinta na rawa.
Na fadama tun farko baka saurareni ba dolene sai
mun tashi tsaye akan yarinyar nan in bahaka ba
wallahi da kyar zata auru.
Alhaji ilyasu ya sunkuyar da kai kasa na tsahon lokaci
yana tunani can saiya dago kai ya dubi farida yace da
ita a tausashe.
Ki shirya gobe zamu tafi kauye.
Mahaifiyar farida ta kalleshi a rude.
Akwai wani tsohon malamin mahaifinmu wai shi
MALAM NA KOGO Waliyi ne nasan in Allah ya yarda
ko ifiritu ne akan yarinyar nan sai ya barta Insha
Allahu ai ita addu'a tafi karfin komai. Yadanyi shiru
sannan saiya ci gaba da cewa.
To daman in banda lalacewar zamani ma yanzu ace
wai zanen kunshi ya wuce tafin hannu da sawu yatafi
har zuwa kan tsaraici wannan wacce irin masifa ce
yaushe za'a ace wai mace ta bude tsaraicinta agaban
wani kato yayi tayi mata zane zanen banza
.
Alhajin yasake yin shiru akaro na biyu sannan ya juya
inda farida take a takure yace.
Saurara da kyau kijini daga yau sai yau kada nakara
ganin kinsa wannan shegun kayan matsatstsu duk
kifito min dasu zansa a kone su idan kuma kika sake
na kara shigowa gidan nan natarar da gashinki awaje
saina sa wanzami ya aske kan ki Ja'ira.
Yana gama fadin haka sai ya dauki wayarsa ya
daddanna sannan yace.
Hello Alhaji Shu'aibu.... Nine dan Allah in anyi sallar
isha'i saimu hadu anan gidanka zamu tattauna
maganar auren yaran nan domin an sami wata yar
mishkila ina ganin dole sai mun kara watanni ya
danyi shiru yana sauraro.
Toh shikenan duk daya ne idan kai din ma kazo. Yana
ajiye wayar ne aka sake sallama akaro na biyu
Wannan Karon wani saurayi ne kyakkyawan gaske
yashigo dakin saidai shi anyi sa'a bashida kofato yana
shigowa sai yayi turus zai koma cikin jin kunya.
Ah...shigo...shigo mana Alhaji ilyasu yace lokaci guda
kuma ya dubi farida.
Farida ta dago kai ta dubi saurayin taji gabanta ya
fadi sa'ar dataga sunyi kama da kabir dinta. Ga
mamakinta saitaji tana addu'ar Allah ya rabata da
wannan masifa ta wannan Aljan indai har wannan
shine mijin da za'a bata to tayi dace ta fada acikin
zuciyarta sannan saita sunkuyar dakai kasa a kunyace
azuciyarta tana mai fatan Allah sa shima wannan
saurayin bazai koma gida karkataccen Baki ba.
.
MAMA
Motar kirar fijo tsohon yayi ta fito daga tashar ta nufi
arewa dauke da fasinjoji shida. Abayan motar a
zaune kusa da wani kyakkyawan saurayi mamace
idanunta sunyi jajur saboda kukan da taci da kuma
tashin hankali.
Ga alama mutum uku ne yakamata su zauna abayan
motar amma dayake kyakkyawan saurayin mai dogon
hanci ya biya kudin mutum biyu sai ya kasance daga
shi sai mama ne zaune aciki.
Mama ta dubi agogon dake jikin wayarta karfe shida
da yan mintina tuni hasken rana ya fara sallama
duhun dare yafara maye gurbinsa ahankali kamar
yadda suka saba akullum kwanan duniya.
Daga inda mama take zaune tana iya hangen yan
mata birjik abakin titin kurna asabe zuwa bachirawa
wasu na tafiya abinsu me yiwuwa unguwa zasu wasu
ko dauke da farantin talla wasu ko sanye da dogayen
riguna da hijabi sun taso daga islamiyyar yamma.
Mama taji wani bakin ciki marar misaltuwa ya
mamayi zuciyarta ga mamakinta saitaji tana mai
fatan inama ace tana daga daga cikin irin wadannan
yara inama ace itama agaban magabatanta take da
yanzu fa meyiwuwa tayi aure ko?
Me yiwuwa har da ya'yama da yanzu haka tana zaune
ita da mijinta lafiya cikin kwanciyar hankali babu
taraddadin wani aljani ko wasu jami'an tsaro akaro
na farko sai mama tafara Nadamar dukkan wani iya
shege data aikata adoron kasa yanzu ina ribar irin
wannan rayuwa mara manufa?
Mama ta tambayi kanta nan da nan sai hawayen
bakin ciki ya fara sartu akan fuskarta lokaci guda
kuma tana tunanin shin ko su bebi sun karaso gidan
tare da jami'an tsaron.
Ita kam ta riga tasan ta tafi zuwa duniyar da bata san
abinda zata tarar ba shin yaushe ne mai zai karewa
tsohuwar motar? Mama ta tambayi kanta a tsorace.
.
Kukan me kikeyi?
Wata tattausar murya ta tambayeta mama ta juyo
ahankali yayinda sukayi ido biyu da kyakkyawan
saurayin dake kusa da ita.
Ki daina kuka komai na duniya mai wucewa ne tunda
dai kina tare dani.
Saurayin yace sannan sai ya lalubi aljihunsa ya dauko
wani farin kyalle ya mika mata.
Goge fuskarki kada hawaye yabata miki kyawunki
Saurayin ya hasketa da murmushi.
Mama ta dubi kyakykyawan saurayin cikin mamaki
lokaci guda kuma taji zuciyarta na harbawa tsakanin
hakarkarinta
hakika kyakkyawa ne na gaske mama ta fara hasko
hotunan mazan data taba mu'amala dasu abaya ta
kasa tuna daya daga cikinsu daya kai koda rabin
kyawu na wannan dake kusa da ita.
Karbi mana ki goge.... Kada nima ki sani kuka.
Jikinta ta rawa mama ta karbi farin kyallen ta goge
fuskarta sannan ta mika masa.
Nagode. Tace da saurayin.
Nine da godiya ai da kika saurareni kika kuma karbi
kyallen dana baki.
Suka danyi shiru na yan mintina suna duban juna
direban motar ya dada kara gudu domin yagama fita
daga cikin gari.
Ina kika nufa?
Mai mujiya. Mama tace tana duban kyakkyawar
fuskarsa cikin shauki.
Kaifa ina zaka.
Guri daya muka nufa saurayin yace cikin murmushi.
Duk inda zaki muna tare don bana gajiya da ganinki.
Mama ta dube shi cikin mamaki.
Yanzu fa ka fara ganina.
Ke kike ganin haka ni na dade da saninki...... Ina kuma
kaunarki.
Mama taji kamar an watsa mata ruwan sanyi. Adaidai
wannan lokaci sai wani tattausan murmushi ya
subuce daga bakinta tayi murna da bata jefar da
layar dake makale akanta ba. Tabbas tasirin layar
bokance tafara aiki. Mama uwar gaggawar tare
mubarak tayiwu me yiwuwa alokacin layar ce bata
fara aiki ba babu mamaki ma da tabi ahankali har
gida mubarak zai sameta.
Mama ta haskake kyakkyawan saurayin dake zaune
kusa da ita lokaci guda kuma tana wasa da wayar tafi
da gidanka dake hannunta.
Tayaya daga ganina zaka fara..
.
Tayaya daga ganina zaka fara kaunata? Mama ta
bukata.
.
Haka daman abin yake kowa kinsan da irin abinda
yake so baki san ana kaunar mutum ba tun ma ba'a
ganin shi ba.
Mama ta lumshe idanu kana ta shafi layar dake kanta
awayance
Kaidai fadi gaskiya yanzu danace ka aureni guduwa
zakayi.
Saurayin ya matso dab da ita yace
Auren ki shine abu mafi soyuwa agareni gwada ni ki
gani in ban aureki ba.
Mama taji wani farin ciki ya lullubeta. Tabbas
maganin bokan yaci ta dada jaddadawa kanta gashi
ma nayi sa'a wannan yafi mubarak kyawun sura nesa
ba kusa ba.
Zaki Aureni? Saurayin ya tambayi mama a tausashe
kamar wanda yake tsoron kada na kujerar gabansu
suji.
Gwada ni ka gani mama tace lokaci guda suka fashe
da dariya me yiwa dariyar da takeyi ne yasa wayarta
subucewa daga hannunta ta fada kasa inda kafarta
take babu mamaki kuma wata gargada da motar ta
fada ne.
Oh wayarki ta fadi ko bari na dauko miki.
Cikin dariya mama ta girgiza kai sannan tayi masa far
far da idanu irin na kwararriyar yar duniya lokaci
guda kuma ta dafe hannayensa tace.
Bari na dauko kayata kada na baka wahala darling.
Tana gama fadin haka saita sunkuya domin ta dauko
wayar sannan ne to taga abinda ya tsayar da bugun
zuciyarta ya kafar da yawun dake bakinta sannan yasa
yasa tunaninta a rudani.
Da farko da mama taga abin ta dauka wanine daga
cikin fasinjoji ya ajje musu akuya akasa amma data
duba da kyau sai taga ba kafar akuya bace kafar
kyakkyawan saurayin da zata aura ne har da kofato
kamar kafar doki.
Mama ta dago kai a gigice ta kwalla ihu nan da nan
motar ta hade da farin hayaki.
.
FADILA
Da yamma misalin karfe saura yanayin garin ya sauya
nan da nan gashi dai lokacin sanyi ne amma sai garin
ya daure aka fara zafi.
A zaune cikin dakin shakatawa na alfarma masoyan
biyu ne zaune yau kwana uku kenan kacal da mayar
da aurensu. Tun da suke arayuwarsu basu taba shiga
farin ciki irin na wannan kwanaki ukun ba. Kullum
suna tare faisal yace ba zaifita nan da can ba sai nan
da sati biyu.
Don haka koda yaushe suna tare da amaryarsa fadila
ko dai suna tare da amaryarsa fadila kodai suna kallo
ko kuma wasan ludo ko kuma wasanninsu irin na
masoya masu sabon aure.
.
Kai ni fa nagaji da ludon nan.
Faisal yace lokaci guda kuma ya aje dan kofin ludon
akan faifan gilashin
Fadila ta dubeshi tayi far far da fararen idanunta tace
cikin shagwaba.
Me to zamuyi?
Faisal ya matso kusa da ita yace zauna kawai nayita
kallon ki my love
cikin farin ciki sai fadila ta karkace ta kwanta akan
cinyarsa tana fuskantarsa.
Sai kayi ta kallona har barci ya daukeni.
Faisal yasa hannu yaja dogon hancinta
Kada fa ka tsine min hanci don kaga yafi naka kyau
ko?
Ba wani nan ai wallahi nawa yafi naki kyau. Faisal
yace yana jan hancin.
Fadila ta tashi zaune firgigit cikin tsiwa ta wasa.
Allah ya sawwake ace kafini kyau kana kallon madubi
kuwa?
Faisal ya mike tsaye ya dubeta da murmushi yace In
ba tsoro ba ajje daki aduba madubin mana.
Fadila ta zunkuda kafada tace
Naki aduba dai anan ga madubi can.
Faisal ya girgiza kai ban yarda ba bayan wancan
madubin zo muje daki agani yana gama fadin haka
sai ya ruga da gudu ya shiga daki daga cikin dakunan
kwanansu na alfarma.
Faisal na shiga dakin sai yayi turus cikin tsananin
kaduwa. A kwance akan gadon kwanansu wata
santaleliyar budurwa ce sanye da wata irin doguwar
riga ta bakin gashi. Faisal bai taba ganin irin rigar ba.
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un.
Faisal yace a fili sannan saiya dubi budurwar cikin
hali yace.
Ta Ina kika shigo mana daki kuma me ya kawo ki?
Budurwar ta mike zaune akan gadon ta kashewa
faisal idanu tace.
Yar zaman daki ce aka kawo muku amma tun da naga
baka farin ciki da zuwana bari inyi tafiyata kada ku
isheni da surutu. Tana gama fadin haka saita zama
farin hayaki.
Adaidai lokacin ne fadila ta shigo dakin a guje tana
zuwa saita rungume mijinta faisal tana dariya tace.
Ilove You Faisal.
Nima ina kaunar ki fadila tsahon dakiku suna tsaye
ahaka can sai fadila ta dada kankame shi tace.
Faisal ina son kayi min alkawari.
Faisal ya dubi fuskar amaryarsa a rude yace
alkawarin me?
Fadila ta lumshe idanu tace Alkawarin bazamu sake
rabuwa ba har abada kaga wancan karon saki biyu
kayimin yanzu saura daya.
Faisal ya dada janyoya jikinsa idanunsa na kan farin
hayakin dake bayansu yace a tausashe.
Nayi miki alkawarin ba zamu sake rabuwa ba.
Fadila tayi ajiyar zuciya cikin farin ciki sannan ta kalli
fuskarsa tace.
Kishiya fa ita ma ka dauki alkawarin bazakayi min ba?
Faisal ya kuma kallon amaryarsa ido da ido sannan
ya kalli dan sauran farin hayakin da har yanzu yake
makale a sararin samaniyar dakin yace da
murmushin Yake.
BANSANI BA ME YIWUWA NAN GABA IN AURO MIKI
ALJANA.
Masoyan biyu suka fashe da dariya.
.
KARSHE.
.
NAZIR ADAM SALIH
Abinda Nayi kuskure a gafarceni masu karatu
Mutum Ne Ni Ajizi
A Aiko Min Da Gyaran Kura Kurai Na.
.
NAGODE SAI MUN SAKE HADUWA IN ALLAH YA
NUFA.
ZAYYANA 1 and 2
Littafin Nazir Adam salih
(c) Nazir Adam Salih
Created and design by :- Shuraih Usman
.
Publish:- http://shuraih.xtgem.com
.
This Ebook is available in our website just click here and download it , http://shuraih.waphall.com
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment