Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma shi ne, ya yi
masifar kamuwa da ciwon sonta,
irin tsananin kaunar da ko
rabuwa da ita bai son yi, katsam
sai ya ji haka kawai ya tsani
mijinta, ba a dade ba kuma sai
zuciyarsa ta fara raya masa cewa
dama ace kada Hamisu Jumare ya
dawo garin, da ma ya makale a
can... Zuciyarsa ta buga, domin ya
san abin da take nuna masa, ko
shakka ba ya yi, fata yake yi dama
ace mijin zainab Alhaji Hamisu
Jumare ya mutu a can. Zuciyarsa
ta ci gaba da kawo masa hanyoyi
kala-kala, mota ta yi karo da shi a
ciki wata zuciyar kuma ta ce
dashi dama jirgi ya fashe dasu a
sama..
"Tunanin me kake yi ne? Hilal ba
ka ce dani komai ba, ko ba ka
kaunata ne?"
Hilal ya juyo firgigit ya yi ajiyar
zuciya ya dubeta
"Ina... Kaunarki Zainab, sai dai
kuma duk a banza." Zainab ta
dubeshi cikin kaduwa ta mike
tsaye ta dafa hannayensa. Hilal ya
yi sauri ya janye hannunsa. Ta
sake rankwafawa ta ce.
"Me kake nufi da cewa kana
kaunata a banza?"
"Saboda kina da miji". Zainab ta ji
kamar ya watsa mata wuta.
"Amma ai duk da hakan dai kana
kaunata ko?"
"Ki dubi idanuna Zainab kin san
ai ina kaunarki". Ya shafi
fuskarsa a hankali.
Suka dan yi shiru na dan lokaci,
suna duban juna, sannan sai
Zainab ta ce.
"In dai kana sona, to za mu ci
gaba da haduwa ko da kuwa
mijina yana gari" Hilal ya dubeta
cikin mamaki ya ce
"Ta ya ya?"
"Ta hanyar da ta ke bi idan tana
son yaudarar mazaje" Wata
kakkausar murya ta ce dasu daga
baya, sannan sai muryar ta dada
da cewa.
"Ja da baya Zainab kada ki
sumbaci kaninki, ba kya ganin
kin girmeshi"
Hajiya Zainab ta ji wani abu
kamar ruwan kankara ya surtato
daga goshinta
.
Mutanen biyu suka yi sororo
kamar wadanda suka yi gamo da
aljanu Abin da ya fara zuwa
zuciyar Hilal shi ne kashinsa ya
bushe domin ko shakka baya yi
ya san wannan muryar Alhaji
Hamisu Jumare ce To amma a
bangaren zainab abin
ba haka yake ba domin ita ta fi
kowa sanin mai muryar Ta juyo a
hankali tamkar sitiyarin mota
sannan suka yi ido biyu da mai
kakkausar murya. Dakta sadi ya yi
murmushi.
"ki yi hakuri Hajiya Zainab na saki
kaduwa ko? Wallahi nima ba
haka na so ba to amman dole ne
na ce wani abu in dai har zan yi
la'akari da irin kalaman abin
kunyar da ke fita daga bakinki
shin ke ba kya girma ne da hulda
da yara? "Fuskar Hajiya Zainab ta
sauya launi tun da take ba a taba
fada mata maganar raini irin
wannan ba
"Fice daga gidan nan' Ta ce cikin
fushi tana duban dakta sadi.
Dakta Sadi ya yi murmushi
sannan ya dubi Hilal wanda ke
zaune kamar gunki gumi na
kwarara ya ce. "Dan samari tashi
ka fice daga gidan nan tun kafin
mijinta ya rutsa da kai ni zan iya
rufa maka asiri a matsayina na
abokin
mijinta" Nan da nan Hilal ya mike
cikin
gaggawa bai ko dubi Zainab ba
ya nufi kofar gidan jikinsa na
rawa Dakta Sadi ya bushe da
dariya
Zainab ta bi abin son ta Hilal da
kallo cikin takaici domin
kwakwalwarta ta kasa tunanin
komai sannan sai ta dawo da
kanta ga duban Dakta Sadi tsana
da kyamarsa karara a fuskarta
Sadi ya yi mata murmushi ya ce.
"LOVER WOMAN" Dubanni da
kyau ko ki so ni ko ki kyamace ni
duk a banza domin ni yanzu na
gama dake kudin ki kawai nake
so "Idan na ubanka ne ba sai ka
dauka ba na ce dakai ka fice
daga gidan nan ba na son sake
ganin fuskarka ko da kuwa a
mafarki ne idan kuwa ka ki
wallahi zan sa a yi maka dan
banzan duka a fitar min da kai
Dakta Sadi ya sake fashewa da
dariya. Ka da ki yi haka Zainab
abin ai
bai kai da zage-zage ba na san
duk abin da kike fada ai ba ki isa
ki sa a aikata haka a kaina ba
yanzu ke kya so na bada labarin
holewar da muke yi ni da ke?
Hajiya Zainab ta ji jikinta yayi
sanyi ta dubeshi cikin takaici ta
ce
"Na ce da kai ka fita
"Na ce da ke ba zan fita ba" Dakta
Sadi ya ce yana zazzare idanu.
"To zan sa kuwa yanzun nan a yi
waje da kai" Dakta Sadi ya dada
bushewa da dariya Hajiya Zainab
ta ji
zuciyarta kamar za ta rabe gida
biyu.
"Na san duk abin da kike fada da
barazanar da kike yi wai za ki sa
a yi waje dani duk bindigar kwali
ce, harsashin ruwa, domin baki
da hujjar aikata haka a kaina dan
ke kika fara gayyata ta da na
zo gidanki, na tayaki jin dadin
rayuwa to kuma dan yanzu kin
samu dan kyakkyawan saurayi
da ya fi ni kuruciya sai ki a
wulakantani. To bari ki ji ko dai
ki saurari zancen da na zo miki
dashi yanzu ko kuma na bata
ruwa" Ya yi mata murmushin
mugunta "Kin san abin da nake
nufi da
bata ruwa?" Ta kalleshi cikin
takaici ba ta amsa ba ya ci gaba
da cewa
"Sai na raba ki da dan
kyakkyawan saurayi Hilal. Na san
kin mutu da kaunarsa ba za ki so
na rabaki da shi ba ba kya ganin
tuni ya fara tsorona ya dauka ni
fa da gaske abokin mijin ki ne."
ya dan yi shiru yana dubanta.
"Idan kuma kina son ki fitar da
kanki, to sai ki ce dashi ya daina
tsorona, ni ba abokin mijinki ne
ba masoyin ki ne a boye. Za ki
iya? Ya dubeta ya sake bushewa
da dariya ya buga kafa tim kamar
dan bori.***
"Yan sauran tsirarun samari da
yan matan da har yanzu suke
holewarsu a farfajiyar gidan suka
mimmike tsaye daga
mazaunansu. Suka daga
kawunansu kusan lokaci guda
suna masu duba izuwa ga
sararin samaniya cikin mamaki.
Hakan na da nasaba ne da
rugugin aradun da suka ji babu
zato ba tsammani ya ratsa shirun
dake makale a sararin samaniyar.
Duk da yake dai suna da
masaniyar cewa a tsakiyar
damina ake to amma ba su
tsammaci za su fara jin rugugin
aradu ba maimakon iska.
Hajiya Zainab ta dubi Dakta Sadi
shima ya dubeta, a daidai lokacin
da suka ga samari da yan matan
sun nufo inda suke. Daya daga
cikin yan matan dauke take da
Zuhuriyya. Dakta Sadi ya dubi
Zainab ya jefeta da fatalwar
murmushi ya ce da ita cikin
murya mai karancin amo. "Ki
sameni a dakin shakatawa
kafin Hajiya Zainab ta ce dashi
wani abu, tuni ya bi jerin
fulawowim da suka yi sahu-sahu
tun daga inda suke har zuwa
kofar da zata kai shi kofar shiga
babban falon gidan.
Hajiya Zainab ta ji wani abu mai
kamar gare-gare ya fara
mirginawa wur! Wur!! Wur!!! A
cikin kwakwalwarta kadan ya
rage tasulale a gurin ta fadi kasa
saboda bakin ciki. Ta zargi kanta
da kanta domin ita ta janyowa
kanta duk abin da ya faru. A haka
samari da yan matan suka
sameta kyakkyawar fuskarta
sharkaf da gumi kamar wacce ta
yi ido biyu da ifiritu.
"Hajiya mu za mu tafi". Anti Zaliha
ta ce da ita sannan lokaci guda
kuma ta mikawa Zainab
Zuhuriyya wacce tuni ta fara
gyangyadi akan cinyar Zalihar.
"To Zaliha na gode wallahi"
Sannan ta juya ga sauran samari
da yan matan
BINDIGAR KWALI--> 5
.
"To Zaliha na gode wallahi"
Sannan ta juya ga sauran samari
da yan matan wadanda mafi
yawa daga cikinsu duk malaman
asibitin su ne. Ta mika godiyarta
a garesu. Sannan ta sallamesu da
alakoron tattausan murmushin
da bai kai idanunta ba domin ba
su bane a ranta***
Ba karamin kaduwa ta yi ba
lokacin da ta shiga dakin taga
Dakta Sadi zaune akan daya daga
cikin luntsuma-luntsu man
kujerun alfamar da suke falon
sigari a hannunsa, hancinsa da
bakinsa na ta fitar da hayaki
kamar salansar jirgin kasa bugu
da kari kuma hannunsa na hagu
rike da kofin tangaran mai dauke
da tsaftataccen lemon alfarma
yana kurbawa abinsa. In ya busa
hayaki sama sai ya kurba lemo
kai kace gidan ubansa ne. Zainab
dauke da zuhuriyya a kirjinta ta
dubeshi cikin takaici ta ce.
"kana da gado a gidan nan ne?
Wai me ka dauki gidan nan ne?
Bariki kome? Dakta Sadi ya yi
murmushi sannan ya kurbi
lemonsa ya ce.
"To me ye marabarsa da barikin ?
Ko kuwa ni mijin ki ne ?" Cikin
kunar rai ta wuce zuwa dakin
zuhuriyya ta kwantar da ita
sannan ta dawo fuskarta a
murtuke ta ce.
"Tashi ka fita tunda ba gidan
ubanka ba ne!" Dakta Sadi ya
fashe da dariya.***
Tsawon lokaci suna duban juna
babu wanda ya ce da wani kala
Bugu da kari kuma gidan ya yi
tsit kai ka ce yan sa'o'i kadan da
suka wuce gidan ba a cike yake
da jama'a ba. Lokaci-lokaci
shuke-shuken gidan da iska ke
kadawa su suke bata shirun,
haka nan kuma suke dada sa
Hajiya Zainab kara tsanan Dakta
Sadi wanda ke zaune yana yi
mata fatalwar murmushi Zainab
ta dubi Dakta Sadi irin
duban da za ka yiwa kyankyason
da ya fada cikin abincin buda
bakinka yayin azumi "kada ki ci
gaba da yi min irin
wannan kallon zainab." Sadi ya ce
yana dubanta.
"Haba zainab, kin manta cewa
nima masoyinki ne, ki tuna ba ki
da kowa da zai taya ki jindadin a
rayuwa, na mika kaina garekim
na dauki dukkan hadarin dake
tattare da al'amarin duk fa
wannan domin jin dadinki ne
amma duk da haka ba zaki gode
min ba shi ne za ki saka min da
haka?"
"Hauka ne ya sameka?" zainab ta
ce jikinta na rawa.
"Ba hauka bace Hajiya Zainab ki
saurari abin da nake son fada
miki***
"Na ce ba zan saurara ba ko
kuwa dole ne?" Ta ce dashi tana
zazzare idanu.
"Ka da ki ci gaba da daga
muryarki har jama'a su jiyo na
san ba zaki so a sameki da mijin
da ba naki ba cikin wannan
daren". Ya dan yi shiru yana
dubanta. Akwai wani abu a
yanayin kallonsa dake kara
damun zuciyar zainab.
"Zainab maganar kudin nan da
nake so ce ta dawo da ni kin ga
dai ke Allah ya sa kina daga cikin
mutane masu sa'a." Ya yi shiru
yana dubanta sannan kuma yana
jira ya ji abin da zata ce.
"Zainab kin kasance daga cikin
mutane masu sa'a, domin tun da
kika tashi ba ki san wani abu wai
shi talauci ba sai dai ki ji ana
fadar sunansa ko kuma ki ga
wasu a cikinsa. Zainab ina son ki
sani cewa ni kuma ina daya daga
cikin marasa sa'a, domin tun da
na tashi nake shan wahalhalun
duniya iri daban-daban, a haka
har na fara karatu," Dakta Sadi ya
dan yi shiru yana duban sigarin
dake cin wuta a hannunsa, tokar
sai murmushewa take tana zuba
a kasa. Ya yi kamar zai zuki
sigarin to sai kuma ya fasa ya ci
gaba da cewa.
"Ka da ki tona ki ga wahalar da
na sha lokacin da nake karatuna
na likita a jami'a, na sha wuya ta
fitar hankali, Allah ne ma ya sa da
rabona, da tuni ma karatun ya
gagareni, zaki yi mamaki idan na
ce miki da kyar da kyar da
taimakon abokina na gama
karatuna. Wasu lokuta kudin
motar da zan koma makaranta
sai abokaina na gida suke bani,
haka nan kuma idan na je
makarantar ma to a gurin
abokaina nake dan samun
abincin da zan jefa a bakina.
Kada fa ki yi tunanin bani da yan
uwa zainab, ko kusa ba haka
bane ina dasu, to amma ganin
cewa bani da iyaye sai duk suka
watsar dani, bayan kuma a da
can wani zamani da ya shude
duk a gindin mahaifina suke a
tattare kuma..."****
"Malam ya isa haka, ni ban
tambayeka tarihinka ba, ka tashi
kawai ka fice min daga gida!"
zainab ta katse shi fuskarta a
murtuke.
"kada ki yi min korar kare zainab,
da sannu zan zo miki da
manufata domin kin ga irin
wannan hali
naki shi ya sa lokacin da na gama
karatuna da kyar sai na gane
cewa lallai mutane basu da
tausayi ko kadan, don haka nima
daga ran nan na kudiri aniyar
duk wanda ya fada cikin tarkona
ko kuma ya hadiyi fatsa ta, to ban
bari ya kufce min ban kuma
tausaya masa." Dakta Sadi ya
dubi zainab ido da ido ya ce.
"Zainab kin riga kin shiga
tarkona, domin tun sa'ar da na
gane manufarki, sai na ga dama
ce agareni ta karshe. Ban ga
kuma dalilin da zai sa na tausaya
miki ba, domin kema cin amanar
mijinki kika yi to mene ne aibu
kuma dan ni na ci taki amanar ?
Ina fatan dai yanzu kin gane
manufata ?"
"Ban gane ba!" Zainab ta ce.
"To abin da nake nufi shi ne ina
bukatar kudin nan da na bukata
gareki a kwanakin baya,
Miliyan uku kacal nake bukata Sai
ki zaba tsakanin miliyan uku da
kuma dan kyakkyawan saurayi
HILAL wa kika fi so ? Na ba ku
kwana uku ki yi tunani" Dakta
Sadi ya mike tsaye sannan ya fara
matsawa kusa da zainab "Zo mu
tafi daki ko" Ya kai hannu zai
kama hannunta Zainab ta kai
masa duka ta buge hannunsa
"Kada ka taba ni shege dan iska"
Sadi ya fashe da dariya. "Au yau
kuma har da duka to ai
iska bata da guda
Ya sake matsawa kusa da ita
Dakta Sadi bai kula ba a hankali
sai kyawawan siraran yan
yatsunta suka fara matsawa
izuwa kan teburin dake tsakar
dakin
"Kada ka tabani Zainab ta ce cikin
karaji lokacin da ta ga Dakta Sadi
da gaske yake yi sannan sai ta yi
wuf ta zari kwalbar Dakta Sadi ya
ji wani abu fus!
Kamar kofaton doki ya daki
tsakiyar kansa ya kwalla kara
cikin gigita ya rike kansa da
hannayensa nan da nan jini
yafara rine hannayen
"Ni...fice min daga gida" Zainab ta
ce bakinta na rawa har yanzu
akwai sauran wani bangare na
kwalbar da bai fashe ba a
hannunta.
"In kuma ba haka ba in kara ma
shege dan iska" Dakta Sadi ya
dubi Zainab cikin tsana rabin
fuskarsa a rine da jini ya ce.
"Na gode....zainab amma ina
tabbatar miki da cewa wannan
shine zai zamo karo na karshe
da zaki sake dukan wani da
namiji a doron kasa." Dakta Sadi
ya juya a fusace ya fice daga
dakin kansa rike a hannunsa "Na
tsaneka!" Zainab ta sake cewa
dashi cikin karaji Rugugin
aradun bai bari Dakta Sadi ya ji
abin da take cewa ba****
Kyakkyawan saurayin Hilal ya
motsa a hankali sannan ya turar
da zanin mayafin dake jikinsa ya
dafe kansa da hannaye biyu ya
rintse idanu gami da cije lebe. Da
farko ya dauka ciwon kan
dake sara masa na da nasaba ne
da tashinsa daga nannauyan
barcin to amma sa'ar da ya tashi
zaune ya jingina bayansa jikin
bangon dakin sai shakkar hakan
ta darsu a zuciyarsa Tun sa'ar da
ya baro gidan Hajiya
Zainab kansa ke ta sarawa Dum
Dum! Kamar ana kidan duma a
ciki shi kansa bai san ta yadda
aka yi ya karaso gida ba
zuciyarsa cike fa tunane-tunane
dauke kuma da fargaba kala
biyu.
Fargabar farko dake damun Hilal
ita ce ta mijin Hajiya Zainab. Duk
da ya ke mutumin da ya samesu
a daren jiya shi da Hajiya Zainab
ya ce zai rufa masa asiri amma
hakan ba ta sa ya daina fargaba
ba domin Hilal bai san mutumin
ba me yiyuwa ma kawai ya yi
masa haka ne domin ya
yaudareshi ya bar gidan kafin
kuma a zo daga baya da jami'an
tsaro. Hulda da matar babban
mutum kamar Alhaji Hamisu
Jumare ba karamin hadari ba ce.
Hakika na zama wawa wayona
da hankalina duk basu amfaneni
da komai ba domin in ba haka ba
me zai sa na fara soyayya da
matar aure? Hilal ne ke tambayar
kansa.
So! Amsar kenan da
kwakwalwarsa ta shimfida a
faifan tunanin zuciyarsa. Wannan
kalma ta "SO" ita ce babbar
fargaba ta biyu da ta mamaye
zuciyar saurayi Hilal. Matsanancin
so da begen Hajiya Zainab ya
gama mamaye bargon jikinsa
cikin dan kankanin lokaci dan
haka duk da tsoron mai gidanta
da yake idan ya tuna da cewa ba
zai taba mallakarta ba sai ya ji
duk duniyar nan ta dagule masa.
Hilal ya zuro kafafunsa kasa daga
kan gadon sannan ya dubi
agogon dake makale a jikin
bangon dakin a daidai lokcin da
aka sake kwankwasa kofar dakin
a karo na biyu. Hilal bai damu da
ya amsa ba bai kuma yi wani
yunkuri na ya bude kofar dakin
ba koda yake dai daman jiya da
daddare bai iya kulle kofar dakin
ba turo ta kawai ya yi Rashin
yunkurin bude kofar dakin na da
nasaba ne da ciwon da kirjinsa
yake yi. Hilal ya dafe kirjinsa
sannan kuma lokaci guda ya ji
wani abu mai kamar kibiya ya
soki kwakwalwarsa nan da nan
sai wani zazzafan gumi ya fara
wanke kyakkyawan fuskar
saurayin. Abin ya fara damunsa
domin Hilal bai taba gamuwa da
irin wannan matsala ba sai da ya
hadu da Hajiya Zainab kuma ya
lura da cewa kansa da kirjinsa
suna takura masa ciwo ne a duk
sa'ar da tunanin Hajiya Zainab ya
fado masa Irin wannan kauna
wacce iri ce? Hilal ya tambayi
kansa
A daidai lokacin ne to aka turo
kofar dakin a hankali. Hilal ya
dubi kofar dakin zuciyarsa cike
da masaniyar wacce za ta bude
kofar dakin. Bai yi kuskuren
tunani ba wacce ya ke
tsammanin ce wato mahaifiyarsa
"Wacce irin lalatar banza ce kuma
wannan Hilal ? Da girmanka da
komai ace makaranta ma sai na
tasheka za ka dubi fa karfe
takwas da kwata" Ta nuna
agogon dakin da hannunta
"kuma yau na lura ko sallar asuba
ba ka yi ba yanzu kana jin idan
mahaifinka ya ji za ku kare da
dadi? Ko kuwa dai kafi son ka
harzukashi ya zo ya yi ta fadan
nan nasa ba kai ba gindi." Ta yi
shiru tana duban Hilal
wanda ke yamutsa fuska. Ko
kusa bai fahimci yawa-yawan
kalmomin da ta fada ba abin da
kawai dake yawo cikin
kwakwalwarsa shi ne tausasan
kalamanta in da take cewa
"KAUNAR KA NAKEYI HILAL"
BINDIGAR KWALI--> 6
.
Ko kusa bai fahimci yawa-yawan
kalmomin da ta fada ba abin da
kawai dake yawo cikin
kwakwalwarsa shi ne tausasan
kalamanta in da take cewa
"KAUNAR KA NAKEYI HILAL"
"Ko ba ka jin abin da nake fada
ne ?
Hajiya Asma'u ta buga masa
tsawa Hilal ya yi firgigit
cikin tsoro ya dubi mahaifiyarsa
ya ce bakinsa ba rawa.
"Wal..Wallahi Ummi yau bana
jindadi"
Kamanin fuskar mahaifiyar tasa
suka sauya Ta matso kusa dashi
"Me ke damunka?"
"Kaina ne ke yi min ciwo tun jiya
da daddare" Hajiya Asma'u ta
dada matsowa kusa dashi ta
dafa kansa kamar
za ta yi kuka duk bambamin
fadan da take ya kare Ko kusa ko
alama ba ta son abin da zai taba
mata dan tilon danta tuni daman
ta yanke kauna da samun
Don haka sai hankalinta da na
maigidanta malam zubairu ya
tattaru gaba daya akan dansu
kwaya daya wato Hilal sabanin
wasu daga cikin mutane su basu
bata nasu dan ba duk kuwa da
cewa shi kadai suke dashi sun
tarbiyantar dashi sun bashi ilimi
na muhammadiya da kuma na
zamani.
Malam Zubairu tsohon soja ne
koda yake wannan tsohon
zancene domin yana daya daga
cikin
tsofaffin sojojin da suka hadu da
rashin sa'a a lokacin yakin
basasa hakan ce ma ta sa yanzu
kafa daya ce dashi kuma ido
daya to amma duk da haka idan
allurarsa ta motsa to fa ran nan
gidan babu kwanciyar hankali
kenan. Malam Zubairu dan karere
ne motsattse yana da tarin
gashin baki fari tas kamar gashin
tinkiya idanunsa jajaye ne
sakamakon kokinon da aka
zuzzuka a da duk da yake dai
yanzu girma ya kama shi to
amma lokaci-lokaci akan dan
taba shan kokino domin wai a
cewarsa maganin mura ne. Da
yawa daga cikin abokan aikinsa
a zamanin suna soja da DUJAL
suke kiransa.***
Hajiya Asma'u fara ce doguwar
bafulatana kyakkyawa kana
ganinta ka ga Hilal mutane da
yawa sun sha tsurku akan cewa
yaushe za a ce kyakkyawar mata
kamar Asma'u za ta auri wannan
kyamurarren tsohon sojan mai
kamar zanen yan koyo? To amma
kuma ai an ce matar mutum
kabarinsa. Mutane musamman
yan uwan Hajiya Asma'u sun yi
farin ciki lokacin da aka haifi Hilal
suka ga sam-sam ma shi bai yi
kama da ubansa ba domin wai a
cewarsu da ya yi kama da
ubansa da zai yi wuya in zai sami
matar aure a duniya.
"Sannu Hilal" Mahaifiyarsa ta ce
dashi kamar wani dan kankanin
yaro.
"Gashi kuma jarrabawa ya za ka
yi kenan?" Hilal ya dubi
mahaifiyarsa ya yi murmushi
yake ya ce 'Zan kokarta na tafi a
haka na
san me yiyuwa in na shiga dakin
jarrabawar na warware."
"To ai sai ka hanzarta tun da
kana ganin za ka iya kaga fa har
tara ta kusa kuma ka ce tara
kuke farawa" Hilal ya mike tsaye
zuciyarsa na ta zayyana masa
kyakkyawar fuskar nan ta Zainab
mai lallausan murmushi.
"Idan ka yi wanka sai ka je falo
abin karin kumallonka yana can
gashi ma ko sallah ba ka yi ba."
Hajiya Asma'u ta nufi kofar dakin
ta janyo ta a hankali zata bude
can kuma sai ta juyo firgigit
kamar wacce ta tuna da wani
abu ta ce. "Af, na manta wai wata
yarinya a waje tana sallama da
kai ta ce
wai yar makarantar ku ce." Hilal
ya hade fuska ya dubi
mahaifiyarsa ya ce "RUKAYYA CE
ko?" Mahaifiyarsa ta girgiza
kanta ta ce.
"A'a ai na san Rukayya wannan
fa ina jin har da mota ta zo wai
sunanta ZAINAB." Hilal ya ji kamar
an jefa masa
gwauron dutse a cikin zuciya.
Hilal ya fito tsakar gida dauke da
littattafan makarantarsa guda
biyu. Jarrabawa ce ta hana shi
dauko jakar makarantar baki
daya. "Ummi ni zan tafi". Ya ce da
mahaifiyarsa wacce ke tsaye
bakin famfon dake tsakar gidan
tana daukar ruwa a tukunyar
karfe. "To Hilal yi sauri kada ka
makara
yarinyar na nan waje tana
jiranka, nayi-nayi ta shigo ciki ta
ki". Ta dan yi shiru sannan ta ci
gaba "Da zarar an tashi kuma sai
ka
nufo gida kada ka tsaya zafin
rana ya sake tada maka ciwon
kan".
"To Ummi". Hilal ya amsa sannan
ya nufi kofar gida cikin sauri,
kirjinsa na dakan uku-uku. Tun
sa'ar da mahaifiyarsa ta ambaci
sunan Zainab sai ya ji duk zaman
gidan ya ishe shi, dokin sake
ganin kyakkyawar fuskar nuna
bai iya barin sa ya sa ko da loma
daya ba a bakin salatinsa to
amma Hajiya Asma'u bata takura
shi da sai ya ci abinci ba domin a
tunaninta rashin lafiyar daya
tashi da ita ce ta hana masa jin
dadin dandanon abincin. Fitarsa
ke da wuya, shekin jikin
dankareriyar marsandin fara ya
dauke masa idanu kofar motar ta
bude Hajiya Zainab ta fito tana
murmushi. Yawun bakinsa ya
kafe kamar yadda itama nata
yawun bakin ya kafe domin a
lokacin ko cikakken numfashi
bata iya yi sosai. Ga mamakinsa
sai ya sami kansa yana mai yi
mata murmushi.
Masoyan biyu suka dubi juna,
daya matar aure daya kuma
saurayi dan makaranta Zainab ce
ta fara magana bakinta na
rawa "Hilal....ka yi hakuri dan
Allah".
Halil ya yi mata murmushin yake
sannan ya juyo ya dubi kofar
gidan su domin tsoro ya ke ji
kada mahaifinsa ya samesu gurin
"Mu shiga mota". Hilal ya ce yana
duban kofar gidan. Hajiya Zainab
ta nufi motar ba ta yi musu ba
domin ta fahimci abinda yake
nufi.
Suka fara tafiya a hankali a daidai
lokacin ne to Hilal ya ji kamar an
zungureshi ta baya
yana juyawa sai ya ji an fashe da
dariya. Zuhuriyya ta dubeshi tana
kokarin sake zungurinsa da
bindigar wasanta.
"Ah, Zuhuriyya kada fa ki
harbeni". Hilal ya ce yana dariya.
Zainab ta yi murmushin yake ta
ce "Ke....kyaleshi haka kada ki
dameshi mana ke fa fitinarki
kenan". Zuhuriyya ta bata fuska
ta ce cikin shagwaba. "To Mama
ya dawo baya mana
mu zauna." Hilal ya fashe da
dariya gami da mamakin irin
wannan wayo na wannan
yarinya Zuhuriyya, sannan sai ya
dubi fuskarta mai sheki ya kuma
dubi ta mahaifiyarta sai ya ga
tamkar taurari ne biyu a sararin
samaniya masu hasken gaske
babba da karama.
"Hilal dan Allah abinda ya faru jiya
ka yi hakuri zan yi maka bayanin
duk abin da ake ciki."
Hilal ya dubeta sannan sai ya
jefeta da wani irin murmushi na
kauna mai narkar da zuciya.
"Zainab ina son ki sani cewa duk
wani bayani da za ki yi min a
yanzu in dai har ba na kaunarki
to ba zai sa na taba son ki ba.
Haka nan kuma an ce so hana
ganin laifi dan haka duk abin da
ya faru jiya bai isa ya hana ni
kaunarki ba in dai har ina yi din".
Hilal ya mayar da numfashi
sannan ya yi kasa da muryarsa ya
ce. "Zainab ina sonki fiye da duk
wata halitta dake doron kasa a
yanzu dan haka koda ba ki yi min
bayani ba begenki bai taba
girgiza a zuciyata ba
Hajiya Zainab ta rage gudu
sannan ta sa hannunta ta share
hawayen farin cikin jin cewa
yana kaunarta daga kan fuskarta.
"To amma kuma ina jin daga yau
mun rabu kenan ni dake domin
haduwar mu dake ba alheri
bace." kadan ya rage sitiyarin
motar
ya kwace daga hannun Hajiya
Zainab saboda girgizata da
kalamin ya yi "Haba Hilal kada ka
yi min haka kai fa yanzun nan ka
ce kana kaunata da bakinka to
kuma
mene ne ya kawo zancen Rashin
alheri a haduwarmu kana sona
ina kaunarka fiye da kaina to
mene ne aibun" Hilal ya muskuta
sannan ya dubi agogon dake
gaban motar tara
saura minti bakwai.
"Aibun haduwata dake shi ne ke
ba matata ba ce matar wani ce ki
tuna fa duk haduwar da muke
dake hatta zama da hirar da
muke dake a halin yanzu duk
haramun ne" Hajiya Zainab ta
dauke wuta na tsawon dakiku
tana ta karatun jaki hakika bege
da kaunar dan kyakkyawan
saurayin sun fitar da ita daga
cikin hayyacinta kai dama duk
hankalinta gaba daya.
Tara da minti daya suka kawo
farfajiyar makarantar tuni har
barci ya dauke Zuhuriyya wacce
ke kwance a bayan motar dauke
da bindigar robarta.
"Kafin ka fita Hilal ina son ka
taimakeni dan girman Allah ka
zo gidana yau da daddare ina
son magana da kai" Hilal ya
dubeta sannan ya girgiza kai
yace.
"A duk sa'ar da na dubeki sai
kaunarki ta dada mamaye
zuciyata ni kuma tunanin hakan
na da matukar hadari ga
rayuwata domin ba zan taba
mallakar ki ba tun da kin kasance
matar wani ki yi hakuri Zainab ni
zan tafi sai wata rana." ya juya ya
fara tafiya. "Hilal dan Allah ka
taimaki
rayuwata, dan Allah" Ya girgiza
kai "Ki yi hakuri ni da ke har
abada" Ya nufi dakin jarrabawa
da gudu-gudu. Har ya kule tana
kallonsa sannan sai ta kifa kanta
akan sitiyarin motar ta fara
matsanancin kuka. "Mama kukan
me kike?" Zuhuriyya ta tambaya
daga bayan motar.*****
Tun kafin duwawunsa ya gama
taba kujerar sai talafon ya dauki
ruri. Kamannin Dakta Sadi suka
sauya ya dubi talfon din cikin
takaici. Wane ne kuma wannan
ke son damunsa a daidai lokacin
da yake kokarin hutar da ransa
ya dan sha iska. Tun sa'ar da ya
fito daga dakin
tiyatar jikinsa ya fara bashi cewa
abubuwa yau ba sa tafiya yadda
ya kamata. Koda yake dai daman
tuni ya gane cewa sabanin da
suka samu tsakaninsa da
asirtacciyar masoyiyarsa Hajiya
Zainb ba karamin taba harkokin
rayuwarsa ya yi ba. A da can
kafin su sami sabani Dakta Sadi
ya dauka shi Hajiya Zainab take
so bashi yake sonta ba kuma
yana iya yi mata duk abinda ya
ga dama domin shi ne (Master)
dan shi ake so. Bai gane
kuskurensa ba sai a daren
shekaran jiya irin yadda Hajiya
Zainab ta ruguje shi da kwalba
kuma ta koreshi fata-fata kamar
kare shi ya karya zuciyarsa
sannan kuma ya aza zuciyar tasa
akan wani tsini na tsananin
FARGABA DAKUMA
BINDIGAR KWALI--> 7
.
Irin yadda Hajiya Zainab ta ruguje shi da kwalba kuma ta
koreshi fata-fata kamar
kare shi ya karya zuciyarsa
sannan kuma ya aza zuciyar tasa
akan wani tsini na tsananin
FARGABA DA MAMAKI Lokacin da
ya dawo gida sai ya
kasa fitar da tunanin kyawunta
daga cikin ransa sannan sai ya
sami kansa yana mai zubar da
hawaye domin ya san ya yi
rashin masoyiya a take a nan sai
ya gane cewa ashe tuntuni ya
kamu da ciwon sonta bai sani ba
sai da rabuwarsu ta zo Dakta
Sadi ya zargi kansa akan hadama
ta son mallakar abin da bai kai ya
mallaka ba Da ya san haka ne da
bai tambayeta kudin ba da kuma
yanzu zamansu suke lafiya
A washegarin ranar

Please Login or Register in order to submit comment