Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

guntun tikiti
bai kare ba da ma ba za ka same
mu ba."
Ikko. Hilal ya maimaita sunan a
zuciyarsa. Sannan cikin sauri sai
ya nufi inda ake sayar da tikitin
motar. Karfe bakwai da rabi suka
bar tashar.
Kusan sa'arsu guda suna tafiya
babu wanda ya ce da wani kala
tsakanin dan duniyar da Hilal.
"Hala wannan shi ne zuwanka
Ikko na farko?" Dan duniyar ya ce
da Hilal a karo na farko tun sa'ar
da motar ta fara tafiya. A
zuciyarsa yana mai mamakin
abin da zai kai wannan
kyakkyawan saurayi Ikko babu
ko jaka a hannunsa.
"Uhm...shi ne zuwana na farko."
Hilal ya ce da shi muryarsa na
rawa. Dan duniyar ya gyada kai
xikin fahimta. Tuntuni, tun sa'ar
da saurayin ya zo gare shi da
tambaya ya san yaron na cikin
bala'i. To amma kwarewa da
gogewar yawon duniya su suka
sa shi yin gum da bakinsa a
zuciyarsa yana cewa.
Me yiyuwa sata ya yi. ko kuma
wani babban abin kunyar.
Hilal ya jingina kansa a majiginin
motar bai yi mamaki ba sa'ar da
ya ji duk lakar jikinsa ta mutu
gajiya ta lullube shi ba a dade ba
sai ya ji idanunsa sun fara
rufewa sannan sai sarkin
barayi ya lallabo ya sace shi
(Barci)
Bai san iya adadin sa'ar da ya
kwashe yana barci ba sai kawai
yaji kamar ana girgiza shi. Cikin
sauri ya bude idanunsa a firgice
a tunaninsa abokin tafiyarsa ne
me dogon sanko yake girgiza shi.
Bude idanunsa ke da wuya sai ya
ji mutane sun fara kururuwa
motar sai tangal-tangal take yi ba
a dade ba sai yaji karar fashewar
wani abu tus!! Iya abin da yaji
kenan sakamakon jifan da aka yi
da shi kansa ya daki wani abu
me kamar dutse sannan wasu
bakaken taurari marasa adadi
suka lullube Idanunsa.******
****
"Lah! Alhaji ka ga ya fara bude
Idanunsa...yana motsi!" Da farko
Hilal bai fahimci abin da
muryar take cewa ba sai daga
baya sannan ya fara fahimtar
kalaman. To sai dai kuma sama-
sama ya ke jiyo murya kamar me
maganar a can nesa yake da shi.
Sannu a hankali Hilal ya bude
idanu, sannan ya fara kokarin
fahimtar dashi-dashin surorin
dake tsaye akansa. Ba a dade ba
idanunsa suka samu saiti sannan
ne ya dara idanu biyu da su.
Wani dattijo ne da wata Hajiya
tsaye a kansa. Dattikon fari ne
dogo mai dogon gemu fari me
yiyuwa zai kai kimanin shekara
sittin babu kadan. Matar dake
kusa dashi ita ma doguwa ce
amma ba ta kai mutumin fari ba
to sai dai kuma mutumin ya dan
girme mata zai yi wahala ko iya
fadin shekarunta me yiyuwa
arba'in da biyar in har za a yi
la'akari da busassun idanunta
me yiyuwa kuma talatin da wajen
takwas idan aka yi la'akari da
cikakkiyar fuskar da ke dauke da
tsohon alkawarin annurin
kuruciya. A lokacin Hilal ya
tsammaci yar mutumin ce ko
kuma kanwarsa.
Sai bayan mako guda da
sallamarsa daga asibitin ne ya
fahimci ashe wai matar mutumin
ne. Kwanansa ashirin da uku a
asibitin yana jinyar yankan dake
kirjinsa da kuma dan raunin
dake tsakiyar kansa. Hilal ya lura
da cewa a kullum kwanan duniya
sai sun zo duba shi su ke biyan
kudin jinyarsa su kuma ke kawo
masa kayan lashe-lashe. A ranar
da aka sallame shi su suka zo da
mota marsandi shudiya mai
dauke da karfen lambar APAPA
tare da direba yana tukasu suka
dauke shi zuwa wata unguwa
wacce daga baya Hilal ya fahimci
cewa ashe a cikin garin Ikko
take. Duk abin da ake yi Hilal bai
taba tambayar wani labari a
game da dawainiyarsu ba to
saidai ya kan gaishe su kuma ya
kance da su. "Na gode Allah saka
da alheri."
Dan haka a ranar da aka
sallameshi bayan sun isa gidan
sai suka shiga da shi cikin wani
falo to amma tun daga farfajiyar
gidan Hilal ya lura da tarin samari
kusan ashirin duk majiya karfi
wadansu na wankin sutura
wasu mota wasu na baiwa
shuke-shuke ruwa wasu kuwa
na gefe suna kada karta abin su.
"Ina fatan ka san a inda kake a
yanzu?" Dattijon ya tamabayi Hilal
bayan sun zauna a dakin
shakatawar.
Hilal ya girgiza kai. Ban sani ba, a
ina na ke?" Mutumin ya dubeshi
da tattausan murmushi ya ce.
"Ederaba ne...ina datan ka san
abin da ya sameka a hanya? Hilal
ya dubeshi cikin shakka.
"Ina tsammanin hadari na yi."
Mutumin ya sake dubansa da
murmushi ya ce.
"Gaskiya ne me yiyuwa za ka so
ka ji yadda aka yi muka same ka?
Hilal ya gyada kai. Sannan ne to
mutumin ya dubi matarsa da ke
gefe ya ce.
"Mun je ziyarar wani dan uwa ne
a asibitin, muka iske an kawo ka
tare da gawawwaki."
"Gawawwaki!" Hilal ya maimaita
kalmar cikin kaduwa
Mutumin ya gyada kai "Kwarai
kuwa gawawwaki, domin kai
kadai ne a motar ka tsira da rai,
mun sameka a kwance duk an
zubar da ku a farfakiyar asibitin
tare da gawawwaki, shi ne
matata da ta ga kana da rai ta
tausaya ma ta nemi na taimaka
maka."
"Kai ne wa?" Hilal ya ce a
zuciyarsa, amma bai fadi hakan a
fili ba.
"Na gode Alhaji..."
"Kada ka gode min." Mutumin ya
ce yana duban matarsa da
murmushi.
"Ka gode mata, domin ita ta sa na
dauki nauyin komai naka, duk
abin da take so shi zan yi."
Aka yi shiru a dakin na dan lokaci
sannan sai mutumin ya dubi Hilal
ya ce.
"Daga wacce jiha kake, kuma ina
za ka?"
Hilal ya ji gabansa ya fadi, ya
bude baki zai yi magana, bayanin
ya ki fitowa. Nan da nan sai
mutumin ya daga hannu ya ce.
"Shi kenan...shi kenan ya isa ba
sai ka ce komai ba, barka da
zuwa Ikko, muna da irinka da
yawa anan, wadanda ba sa son a
san daga inda suke....duk
wadannan samarin da ka gani a
farfajiyar gidan nan irinka ne."
Mutumin ya dan yi shiru. A karo
na farko sai matar ta dubi Hilal ta
ce.
"Yanzu me kake son yi a garin
nan?"
Hilal ya dubi matar cikin
girmamawa ya ce.
"Duk sana'ar da...na samu... In
kuma na sami dama nan gaba
zan so ci gaba da karatu."
Matar ta dubeshi cikin mamaki ta
ce "Ka taba yin makaranta
daman?"
Hilal ya tuna da jarrabawarsa ta
karshe da ya bari a gida ko
sakamako bai zo ba. "Na taba yi
amma ina shekarata ta karshe a
sakandare na bari."
Matar ta girgiza kai cikin
tausayawa, sannan sai ta dubi
mijinta ta ce "Alhaji...ina ganin
wannan dan bangarena ne a
sashi a makaranta."
"An gama...gimbiyat a."
mutumin
ya ce. To sai dai kuma Hilal ya lura
da alamun fuskar mutumin bai ji
dadin abin da matar ta ce ba.
"Oh..wacce irin rayuwa kuma na
jefa kaina? Hilal ya tambayi kansa
***
Tun daga wannan lokacin Hilal ya
fara karatu. Da farko ya karasa
sakandare, ya wuce jami'a inda
ya yi shekaru bakwai yana
karatun koyon aikin likita, a
shekarasa ta karshe ne ya yi
gamo da tsautsayi aka kore shi a
dalilin wata yarinyar bayarbiya da
aka kama shi yana bata satar
amsa. Yan ajinsu da duk wani
mai kaunar Hilal ya yi bakin ciki
da wannan kora da aka yi masa a
jami'a, amma duk wani mai jin
haushi a bayan Hajiya Uwar
dakin Hilal yake.
"Ka yi hakuri Hilal, Haka nan
rayuwa ta ke kada ka damu ai
faduwar da namiji ba ita ba ce
karshen rayuwarsa. Bayan
wannan kalami nata sai da Hilal
ya shafe sama da shekara hudu
yana zaman banza. Ba shi da
aikin komai sai dai ya yi wanka
ya ci abinci. Idan bokon ya motsa
sai ya dauki tuma-tuman
littattafansa na karatun likita ya yi
ta karantawa cikin bakin ciki.
Wata sa'ar kuwa idan ya tuno da
mahaifansa musamman ma
mahaifiyarsa sai ya shige wani
lungu a cikin katon gidan ya yi ta
kuka duk kuwa da cewa a
lokacin shekarunsa kusan sha
daya kenan da barin gida. A cikin
wannan shekaru Hilal ya fuskanci
abubuwan girgiza zuciya da
yawa a gidan da ya sauka. Hilal ya
gane cewa a she dai dattijon
mutumin nan mai tarin farin
gemu turun barayi ne. Al'adarsa
ita ce duk saurayin da ya ga ya
isa Ikko ba shi da gata, ba kuma
ya son a san daga inda yake, sai
mutumin ya dauki nauyin mutum
na ci da sha da sutura da zarar
ya fahimci ka sakankance ya
kuma lura da cewa kai ma
lalatacce ne, sai ya rude ka ya sa
ka a hanya. Dan haka sama da
karti majiya karfi talatin ne a
gidan, kuma duk karnukan
farautar mutumin ne na harkar
fataucin dare Akwai sa'ar da Hilal
yana kwance cikin dare zai tashi
ya ji ana ta shigowa da buhuna
dauke da wasu abubuwa da bai
san ko mene ba Tun Hilal na
kawar dakai har dai ran nan ya
gaji ya tambayi uwar dakinsa
abin da ke faruwa a gidan
"ka rufawa kanka asiri ka yi
zamanka a yadda kake. Ka iya
bakinka ka fita daga harkar abin
da ake yi a gidan nan tun da ba a
kasa dakai ba" Matar ta ce dashi
tana kallonsa akwai alamar
gargadi karara a cikin kwayar
idanunta
"Ina son ka sani Hilal duk fadin
gidan nan
NI KADAI NAKE SONKA
BINDIGAR KWALI--> 14
.
......"Ina son ka sani Hilal duk fadin
gidan nan NI KADAI NAKE
QAUNAR KA gani daya na yi ma a
cikin jini na ji ya kamata in
taimaka ma domin ka yi matukar
kama da dana daya kwallin kwal
da shima ya mutu a hadarin
mota Kamar ku daya da shi
ganinka shi ya tuna min da shi
idan ina kallonka sai in ga kamar
shi nake gani saboda haka ina
son ka iya takunka a gidan nan
domin samin dorewar farin
cikinka da kuma farin cikina ina
fatan ka fahimce ni?
Hilal ya gyada mata kai kamar
kadangare a tsorace Tun daga
ranar bai kara yi mata zancen
abin da ke faruwa a gidan ba
Wata sa'ar ko barci yake yi idan
ya ji ana shigowa da buhuna
gidan sai ya dada runtse
idanunsa ko kwakkwaran motsi
ba ya yi dan kada ma a ga kamar
yana sauraren abin da ake yi
A shekararsa ta sha bakwai ne a
Ikko Hajiyarsa ta bashi jari tun
da dai karatun ya gagara. Hilal ya
bude shagon sayar da kayan
wutar lantarki a unguwar koyi
Sannu a hankali rumfar ta fara
habaka har dai tsawon kimanin
shekaru uku. Ran nan da
daddare sai suka sami labarin
cewa wata mummunar gobara ta
tashi a rukunonin da shagunan
su Hilal suke ta kone shagunan
kurmus
A ranar Hilal kwana ya yi yana
kuka. A karo na farko cikin
shekaru ashirin da doriya tun
barinsa gida sai Hilal ya yi
mafarki da mahaifiyarsa. A
washegarin ranar da aka yi
gobarar ne to Hajiyarsa ta kira
Hilal dakin shakatawarta ta
dubeshi ta ce.
"Hilal ina son yau dai na san
tarihinka shin me ya fito da kai
daga garinku?" Hilal ya dubeta a
rude domin tambayar ta zo masa
a bazata don ya yi tsammanin
maganar shagonsa da ya kone za
ta yi masa. Hilal ya so ya boye
mata to amma mafarkin da ya yi
da mahaifiyarsa a daren jiya shi
ya raunana niyyar karyarsa. Hilal
ya ba ta labarin tun daga farko
har karshen dalilin barinsa gida.
Tsahon lokaci Hajiya na kallonsa
cikin kaduwa da abin da ta ji.
Hawaye ya fara sartu akan
kamatunta.
"Ni daman. da ganinka na san ba
mutumin banza bane..amma
ka dauki hakkin mahaifiyarka...
na san yadda rashin da yake
kona zuciyar uwa." Ta fashe da
kuka. Bayan wasu yan dakiku ta
share hawaye sannan ta dubeshi
ta ce.
"Ka shirya gobe ka tafi gurin
iyayenka ka nemi gafararsu Allah
sa suna da rai in kuwa ba
gafararsu ka nema ba duk abin
da ka taba da wahala ya yi
albarka...ka yi kuskure Hilal dan
me ya sa za ka bar iyayenka
bayan ka tabbata ba kai ka
kasheta ba?" Washe gari tun da
asuba ta tashi
Hilal a asirce sannan ta mika
masa wata katuwar jaka
kodaddiya ta ce.
"Tashi ka tafi neman gafarar
iyayenka ko ka yi albarka." Ta dan
yi shiru tana duban jakar "Ga
kudi nan naira dubu dari biyar
ne kawai... Ita ce gudunmawata
ta karshe a gareka zan kuma yi
maka gargadi daga yau kada ka
sake yin abin da zai batawa
iyayenka rai in ba so kake ka
lalace ba."
Hilal ya dubeta cikin hawaye ya
ce "Na gode...Hajiya.. .na gode
kuma in Allah ya yarda zan koma
gida yau din nan...Allah sa dai
suna da rai."
Sa'ar da suka zo rabuwa sai ta
dubeshi ta ce.
"Hilal ina son bayan mun rabu ka
yi min abu guda biyu..."
ya dubeta cikin mamaki, "Me kike
so Hajiya?"
"Ina son idan ka koma gida ka
bincika in dai har yanzu wannan
mutumin da ya kashe zainab din
da ka bani labari yana da rai ka
yi duk abin da za ka yi ka
tabbatar wa jami'an tsaro laifinsa
domin a hakunta shi."
Hilal ya gyada kai ya ce "Na yi
miki alkawarin haka daman
kuma abin dake raina kenan duk
tsawon shekarun nan da shi
nake kwana da shi nake tashi."
"Sai kuma abu na karshe da nake
son ka yi min."
Hajiya ta ci gaba da cewa.
"Ina son Hilal a duk lokacin da ka
sami dama ka yi min addu'ar
Allah ya rabani da auren tshohon
barawo!"******* ***
Mahaifiyar Hilal ta fashe da kuka
sa'ar da Hilal ya kawo karshen
labarin.
"Haba Hilal...haba dan me za ka
tafi ka bar ni bayan ka san ba kai
ka aikata laifin nan ba."
"Ki yi hakuri mama yarinta ce da
rudin shaidan...ki yafeni."
"Ban taba fushi da kai ba Hilal
haka ma mahaifinka har ya mutu
yana cewa. Hilal yaron kirki an
rabani da shi...idan mutuwa ya yi
Allah ya ji kansa idan kuwa yana
da rai to Allah ya dawo mana da
shi." Ta sake fashewa da kuka.
Bayan an sami yan dakiku suka
nutsu. A daidai lokacin ne suka
lura ashe har rana ta fito sosai.
Hilal ya dubi agogon dake
hannunsa "Har karfe tara ta yi." A wannan
lokacin ne mahaifiyar tasa ta
dubeshi da jajayen idanu ta ce.
"Zan so ka je har gida ka yiwa
yarinyar nan godiya, domin tun
da ka bace, mahaifinka ya rasu
duk yan uwa suka guje ni, babu
me taimaka min sai ita, ka ga ita
ta sa aka sake ginin gidan nan da
har na fara waina ta sayarwa
saboda talauci ita ta hanani duk
karshen wata sai ta kawo min
kudi da sutura."
Hilal ya bude baki yana kallon
mahaifiyarsa a rude domin bai
san wacce yarinya take nufi ba.
"Wai mama...wacce yarinya kike
nufi?" kamar amsar tambayarsa,
sai suka ji wata siririyar murya ta
ce daga kofar daki.
"Assalamu Alaikum....mama ke
kadai ce a dakin ko kuwa baki
kika yi...?"
Mahaifiyar Hilal ta dubeshi da
murmushi sannan ta dubi kofar
dakin ta daga murya cikin farin
ciki muryarta kamar za ta yi kuka
tace.
"Yar halak kin ki ambato...yanzun
nan muke zancenki sai ga ki...zo
ki taya ni farin ciki yau Allah ya
dawo min da dana Hilal....shigo
RUKAYYA.******* ****
Sa'ar da ta shigo dakin sai ta
kasa zama ta zura masa idanu
cikin tsananin kaduwa tana
kallon fuskar da ba zata bata
mantawa ba fuskar da ke yaye
mata bakin ciki.
Hilal ya kura mata idanu cikin
tsananin mamaki, domin kwata-
kwata ko a mafarki bai taba
ganinta ba ya mance da ita to
amma da yake ta dade tana naci
akan sai ta sami soyayyarsa bai
mance da fuskar ba rabonsa da
ita yau shekara ashirin da daya
kenan tun a farfajiyar makaranta.
"Hilal..."
"Na'am....Rukay ya."
jin ya kira sunanta, sai dadi ya sa
ta fashewa da kuka.
"Hilal ashe ba ka manta da ni ba."
Ganin haka sai mahaifiyarsa ta
mike tsam ta fice daga dakin
domin ta riga ta san abin da ke
tsakanin tsohuwar soyayyar. A
zuciyarta tana cewa Allah ka
daidaita tsakaninsu. Ta riga ta
san cewa ko kusa ko alama Hilal
bai taba damuwa da Rukayya ba.
"Zauna Rukayya.." Hilal ya ce da
ita. Jikinta na rawa ta zauna a
gabansa.
Hilal ya kurawa yar karamar
budurwar da ya sani a da yanzu
ta zama cikakkiyar mace amma
idanunta
da bakinta mai yawan son
murmushi
da kuma dogon hancinta su suka
tabbatar da tsohuwar kamarta
duk kuwa
da kibar da ta dan yi.
"Rukayya kin girma."
"Shekara ashirin ba wasa ba Hilal
kaima ai ka girma sosai Hilal dubi
fa
yadda ka zama...sai ka ce
malamin
turancinmu malam Kabiru." suka
dan
fashe da dariya. A karo na farko
cikin shekara ashirin da daya sai
Hilal
ya ji tausayin Rukayya ya kama
shi
tabbas ya san duk mutumin da
zai iya son ka har na tawon
shekaru ashirin ba
tare da yana ganinka ba wannan
ba karamin masoyi bane.
"Umma ta fada min duk abinda
kike yi
mata...Allah saka da alkhairi.
"Haba Hilal mahaifiyarka ai
mahaifiyata ce."
suka sake yin shiru na yan
dakiku. "wane
ne mijinki yanzu?" Rukayya ta
dago kai ta kalleshi ta ce. "Ba ni
da miji yanzu...bayan tafiyarka dai
aurena biyar amma babu
wanda ya dore."
"Aure biyar? Hilal ya maimaita
cikin
kaduwa.
"Haba Rukayya dan me za ki yi
haka?" Rukayya ta dubeshi ido
da ido ta ce.
"Saboda na rasa soyayya
Hilal...daman
kai kadai nake gani na ji dadi
duk kuwa da
cewa ba wani damuwa kayi
da ni ba."
Hilal ya sunkuyar da kai domin ba
shi
da abin cewa. Dan lokaci ya dago
kai.
"Wannan duk wani abu ne da ya
wuce Rukayya." Cewar Hilal.
Rukayya ta ji
wani irin dadi ya lullube
doron zuciyarta, shin kalamin da
ya yi
yanzu nan na nufin cewa Hilal ya
fara kaunarta ne ko kuwa mene
ne?
"Wai....Hilal ina ka tafi ne duk
tsawon
shekarun nan? Hilal ya dubeta
"Labarin na
da tsayin
gaske Rukayya amma nan gaba
idan
lokacin da ya dace ki sani yazo
zan
fada miki'.
Rukayya ta dubeshi zuciyarta na
harbawa shin ko har yanzu baya
kaunata
ne? Ta tambayi kanta
sannan sai ta ce da sauri. "Wane
lokaci ne ya dace ka fada
min?"
Hilal ya dan saurara kadan. Ya
lura tun
shigowarta dakin ya hade da
wani
daddadan kamshi. Haka nan Hilal
ya lura da cewa
hankalin Rukayya a kwance yake
ko
da can ma zamanin da suke
makaranta Hilal ya riga ya san
cewa Iyayen Rukayya masu
hannu da
shuni ne to amma bai dauka
bayan duk
tsayin shekarun nan zai sami
Rukayya da sauran kuruciya ba.
Hilal
ya yi mamaki domin a fuska
Rukayya
ba tafi yar shekara ashirin da
tara ba
duk kuwa da cewa a yanzu haka
ta
doshi talatin da hudu. "Lokacin
da zamu
zama daya
Rukayya." Hilal ya ce, a zuciyarsa
yana
cewa. Ita ce daidai dani sannan
sai ya fara tunanin yawan
shekarunsa a
duniya. A yanzu kam yana da
kusan
shekaru talatin da tara a duniya.
Rukayya
ta dubeshi cikin farin ciki da
faffadan murmushi sannan ta ce
"Yaushe ne zamu zama dayan?"
"Nan da dan lokaci
kankane....akwa i
wani abu da nake shirin
karasawa!"
Hilal yace da ita yana kallon
kilishin
tsakar dakin lokaci guda kuma ya
fara tambayar kansa.
"SHIN....... ???
.
****kash masu karatu wayata babu chaji ku jira nepa su
kawo wuta****
BINDIGAR KWALI--> 15
.
"Yaushe ne zamu zama dayan?"
"Nan da dan lokaci
kankani....akwai
wani abu da nake shirin
karasawa!"
Hilal yace da ita yana kallon
kilishin
tsakar dakin lokaci guda kuma ya
fara tambayar kansa.
"SHIN.... a ina zan sami mutumin
nan da
ya kashe Zainab?" Sai da suka
kwashe
sa'o'i uku suna
hira daga karshe Rukayya ta yiwa
mahaifiyarsa sallama. Hilal ya
rako ta
kofar gida. Suna fitowa sai Hilal
ya
rike numfashi cikin kaduwa.
Dankareriyar motar baka wuluk
tana
sheki a cikin rana ita ta fara
gaishe da
idanunsa. Abin da ya sa Hilal rike
numfashi shi ne motar da
Rukayya ta
zo da ita irinsu daya da motar
maigidansa dan tsohon nan
turun
barayi na Ikko. "Tana da kyau?"
Rukayya
ta tambayeshi da murmushi sa'ar
da ta ga ya kurawa motar idanu.
Hilal ya yi sauri ya dauke
idanunsa
daga kan motar gami da ajiyar
zuciya,
ya ce "kai kyawun ma ai ya isa."
kadan ya
rage ya ce mata irinta
ubangidana yake hawa a ikko.
Sai
kuma ya tuna da cewa lokaci bai
yi ba da ya kamata ta san komai
a game da
tafiyarsa Ikko Domin labarin da
saura
bai kare ba tun da dai har yanzu
bai san matsayin da mutumin
nan da ya kashe Zainab ya ke ciki
ba.
"Irin wannan motocin guda uku
na ke da su." Rukayya ta ci gaba
da cewa.
"Kana son irinta ne?" Hilal ya
tabbata
da wasa take don haka sai ya
girgiza kai cikin sauri ya ce.
"Haba Rukayya ina ni ina hawa
motar
manya. Wannan ai ta yayan
sarakuna
ce da masu abin duniya irinku."
Rukayya ta fashe da wata
zazzakar
dariya. "Ka ga Hilal daina
tsokanata...kai
ma ya dace ace ai kana hawan
wannan."
Ta dan yi shiru "Bari na koma
gida zan
turo direban mu ya kawo maka
ita
har ma da takardunta na baka
ita."
Hilal ya fashe da dariya ya ce "Ke
kuwa Rukayya wallahi ba kya
rabuwa da
tsokana kyautar irin
wannan mota sai ka ce wata
riga."
Sannan ne to ya ga Rukayya ta
hade
fuska kana ta matso daf da shi ta
dubi kwayar idanunsa ta ce a
tausashe. "Na fi karfin dari na irin
wannan karamar motar Allah ya
hore min duk abin da nake
bukata na duniya
abu daya na rasa a duniya shi ne
soyayya...kai ne abin so na Hilal
Allah
ya dawo min da kai bayan tsayin
shekaru
masu yawa, a yanzu haka ni na
rasa ma abin da zan yi maka."
Ta sunkuyar da kai na yan
dakiku. "Idan kana ganin kyautar
da nayi maka da wasa nake ka
tsaya
anan, nan da minti ashirin za a
dawo
maka da motar nan domin ka fita
a
gurina."
Tana gama kalaminta sai ta juya
da murmushi ta shige motar
alfarmar ta rufe sannan ta leko
kai ta cikin tagar motar ta ce.
"To sai na dawo...in an jima da
yamma." Da haka ta tuka motarta
ta fice daga layin. Yara dake wasa
a gefen kwatocin dake layin suka
bi motar da kallo. Daya daga cikin
kananan yaran ya dauki bawon
gyada ya jefi motar a daidai
lokacin da ta wuce su. Sauran
yaran suka dauki sowa
"Lah...Habu ya sameta wallahi."
Hilal bai lura da su ba sai ya juya
zuwa cikin gidan a zuciyarsa
yana cewa.
"Oh, wannan mata da kuri ta ke
wanene ya isa ya yi kyautar irin
wannan mota a wannan zamani
da talauci ya yawaita?"
ko mintuna talatin Hilal bai yi da
shiga gida ba sai wani yaro ya yi
sallama.
"Wai ana sallama da Hilal a waje."
Mahaifiyar Hilal na tsakar gida
tana wanke-wanke sa'ar da
yaron ya shigo.
"Je ka ce yana zuwa." Ta ce da
yaron. Sannan sai ta daga murya
"Hilal!" Cikin sauri Hilal ya fito
daga dakin ya nufo inda take
wanke-wanke.
"Wai ana sallama da kai a waje."
Hilal ya dubeta cikin mamaki. "Ni
kuwa wazai yi kirana...bayan
kusan duk an manta ni ma." "Je
ka gano mana...yanzu haka
ma tsofaffin abokanka ne na
makaranta suka sami labari
kasan fa duk labarin dawowarka
ya hada unguwar nan kamar
wutar daji."
Hilal ya dan yi jim, sannan sai ya
nufi kofar gidan. Tun kafin ya
karasa fita ya hangi hancin
dankareriyar Honda wani dan
tsoho motsattse ya fito daga
cikin motar cikin sauri sannan ya
durkusa a gaban Hilal ya mika
masa dan mukulli da wata jakar
wasika fara ta roba ya ce.
"Yallabai ga wannan Hajiyace
tace nakawo ma...wai takardun
motar yana ciki." Hannunsa na
rawa kamar ana yi
masa gangi Hilal ya karbi dan
mukullin da jakar da kuma wata
yar guntuwar takarda da rubutu
a jiki. Hilal ya kara karanta
gajeran jawabin kamar haka.....
.
Na san dazu ka dauka kyautar da na ce zan yi ma ka duk
BINDIGAR KWALI ce
HARSASHIN RUWA ko?
To ba haka bane dan ka raina ne idan kana so kuma ina
da iko zan iya ba ka Hilal. Ga
motar nan na baka kyauta nasan za ka so ka dan zaga gari
domin gaisawa da tsofaffin abokanka...kada ka yi kokarin
zuba mata mai domin tankinta a
cike yake... Na gode, sai na zo.
MATAR KA RUKY.***
.
Tun misalin karfe hudu da rabi Rukayya ta dawo gare shi,
cikin wata motar kirar marsandi. Sun
yi hirar bayan rabuwa. Hilal ya yi
kokarin yin godiya sai Rukayya ta bata rai ta ce.
"Don Allah Hilal kai ka cika mita Wallahi nawa kyautar
take da
har za ka yi ta damun kanka?" Bata bar gidan ba sai karfe
shida da rabi, tare da alkawarin za ta
dawo gobe da safe, domin ta kai shi ya gaishe da
mahaifiyarta.
Tafiyarta ke da wuya sai Hilal ya
shiga wanka bayan ya fito sai ya
yi alwala ya nufi masallacin dake
can karshen layinsu. Bayan an idar da sallar magriba ne
ya
dawo dakinsa ya sauya kayan da
ke jikinsa, sannan ya zauna ya
zubawa bangon dakin idanu
yana mai tambayar kansa.
Tambayar da ya fara yiwa kan nasa ita ce "Shin...ta ina
zan fara
neman wannan azzalumin mutum da ya kashe Zainab?"
"Ta inda al'amarin ya fara mana." Wata zuciyar ta ce
dashi.
Wani zazzafan gumi ya karyo masa. Shin ko a wane hali
gidansu Hajiya Zainab yake a yanzu, shin ko mijinta Alhaji
Hamisu Jumare na nan da rai?
Shin ina yar karamar yarinyarta da ya sawa zobe?....me
yiyuwa tayi aure, ya baiwa kansa amsa.
A daidai wannan lokacin ne to
zuciyarsa ta fara kwadaita masa
cewa ya koma gidan Hajiya Zainab ya ga irin halin da yake
ciki, me yiyuwa idan ya yi dace
yana iya samun hanyar da zai bi
ya gano inda azzalumin nan yake.
Jikinsa na rawa Hilal ya dauki dan
makullin motar sannan ya nufi
dakin mahaifiyarsa.
"Mama za ni unguwa?"
"Ina za ka?" ta tambayeshi tana
kallonsa a tsorace, domin gani
take yi kamar idan ya tafi ba zai dawo ba.
"Gidansu abokina Aminu...zan je
mu gaisa...Allah sa ma ya ganeni." Hilal ya yi mata karya.
Mahaifiyarsa ta yi ajiyar zuciya ta
ce cikin murmushi "Me zai hana
ya gane ka, ai aboki baya manta
aboki duk tsahon zamanin da aka yi ba a hadu ba. A dawo
lafiya, kada kuma ka dade."
"Ba zan dade ba."
Karfe takwas saura kwata daidai
Hilal ya bar gida. A hankali yake
tuka dankareriyar motar da bai
taba mafarkin za a rage masa
koda hanya ne a cikinta ba. A
zamansa na Ikko ya sha addu'ar
ina ma wata rana Hajiyarsa ta
aike shi cikin motar Alhaji ko ya
taba hawa. Amma maimakon
haka kullum in za ta aike shi wata tsohuwar Toyota take
bashi. Hilal ya yi mamaki sa'ar da ya ga yana fahimtar
hanyoyin da ya
dade bai bi su ba. Sannu a hankali yana tafiya, yana lura
gami da mamakin irin yadda
babura suka cika garin kano, har
dai ya kawo kan kwanar gidan
marigayiya tsohuwar
masoyiyarsa matar wani, Zainab.
Hilal ya shiga cikin layin a hankali,
kusan cikin sanda ma yake tuka
motar. In ba dan doguwar hasumiyar masallacin dake
kan
kwana ba da har abada Hilal ba
zai taba gane titin ba. Kome ya sauya a titin, gidajen duk
an sake
gininsu, da tsarin rufinsu an maida su kamar tsarin
GIDAJEN KASAR SIN....
BINDIGAR KWALI--> 16
.
Hanjin cikinsa ya kulle sannan
yaji kamar zazzabi zai rufe shi
don har yanzu tunani yake yi
kamar idan ya koma gidan zai
samu su dan Ba'u me tireda a
kofar gidan, sannan kuma idan
ya shiga cikin gidan zai sami
gawar Hajiya Zainab kwance
cikin jini yarta a gefe a kwance.
Wannan tunanin shi ya sashi jin
kamar bashi da lafiya. Kwantar
da hankalinka Hilal. Wata Zuciya
ta ce dashi. Wannan duk wani
abu ne da ya
riga ya faru a wani shudadden
zamani.
Hilal ya ci gaba da tuka motar
zuwa cikin layin, idanunsa wuri-
wuri kamar na barawon akuya.
Yana tafe yana kallon
kyawawan gidajen zamanin da
suka yi sahu-sahu a gefen layin
fitilun lantarki na ci tarwai a kan
katangunsu kamar rana. Kusan
ko wace kofar gida a rufe take
sai dai jifa-jifa ya kan hangi kan
masu gadi suna dan lekowa.
Hilal ya gama dube-dubensa bai
hangi tiredar su Dan Ba'u ba
ballantana ma ya gane gidan
marigayiya Zainab. Zuciyarsa ta
fara shakkar anya kuwa nan ne
layin. Tabbas masallacin dake
can kan kwana ya nuna hakan
domin shi kadai ne bai canza ba
hatta gurbin famfon dake daf da
masallacin nan alwala yana nan.
Sa'ar da Hilal ya tabbata ya isa
tsakiyar layin sai ya tsayar da
katuwar motar. Sannan ya
jingina bayansa sosai a tattausar
kujerar mota yana tunanin abin
da ya kamata ya yi. Na bata lokaci
anan a banza. Ya
ce da kansa domin ya tabbata ba
zai taba iya gane gidan
marigayiya Zainab ba.
A daidai wannan lokacin ne kofar
wani gida ta bude wani dan
siririn yaro, dogo fari dan
kimanin shekaru goma ya fito
sanye da bakar shat da gajeran
wando kore hannunsa na dama
dauke da dutsen guga wani dan
dukurkushin kare mai yawan
gashi na bin sa a baya.
Hilal ya sauke gilashin motarsa
yana kallon yaron da ya nufo
inda yake, a wannan dan takin
lokacin

Please Login or Register in order to submit comment