Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan tsaye,
hasken kwan wutar dake makale a kofar
gidan ya hasko fuskarsa ta jike
jargaf da gumi jikinsa sai rawa
yake. Har sa'ar da Hilal ya tuka motar
ya bi duhun dare Dakta Sadi na
nan tsaye baki bude yana kallonsa.
Hilal ya yi imani da cewa dole ne
gobe war haka dakta Sadi ya yi jiransa. Koda ya hau kan
titi
sosai sai wani tattausan murmushi ya subuce masa a
ransa ya ce. Sauran matakin QARSHE********
D.P.O din jami'an tsaron ya dubi
fuskar kyakkyawan mutumin cikin shakka da zargi amma
acan cikin zuciyarsa ya fara
zuzzurfan tunani tabbas shekaru
ashirin da daya da suka wuce ya
taba jin wani kyas me kama da
irin labarin da wannan mutumin
yake bashi. A gurin tsohon D.P.O
na ofishin yan sanda ya taba samun labarin wanda D.P.O
din dan uwane a gareshi shi ne ma
ya yi sanadiyyarsa shiga aikin
dan sanda.
"Malam ka tabbata da abin da
kake fada? Domin idan fa muka
je muka kama mutumin muka ji
ba haka bane kai zamu rike?"
Hilal ya gyada kai sannan ya ce
"Yallabai na yarda ni dai abin kawai da nake son ku min
shi
ne." Hilal ya fara yi masa bayani da sauri da
sauri.*******
Sabanin ranakun baya yau tun karfe hudu Zuhuriyya ta
caba kwalliya ta fesa turare sannan ta
buda kundin hotunan ta ci gaba da kallo tana jiran
isowarsa.
Tabbas shi ne ni daman na san na taba ganinsa.
Zuhuriyya ta ce da kanta sa'ar da
ta ci gaba da kallon kundin hotunan. Hoton dake gabanta
tsohon hoto ne wanda aka dauka ranar bikin zagayowar
shekarunta hudu a duniya. Su uku ne a hoton
mahaifiyarta da kuma kyakkyawan saurayin da ya
dora ta a cinya yana mika mata
BINDIGAR ROBA
.
A kusa da kan saurayin an rubuta (HILAL)
Tabbas in dai har ba shi bane to
dan uwansa ne. Zuhuriyya ta ci
gaba da nanatawa kanta
Hawaye ya subuce mata sa'ar da
ta dubi hoton mahaifiyarta. Ina
ma tana raye.. Da ta tabbatar min
ko shi wane ne. Zuhuriyya ta ce
cikin zuciyarta.
Sannan ta dada kallon hoton ko
shakka babu wannan saurayin
da ya dorata akan cinya shi ne
mutumin da ta karewa kallo a
yammacin jya. In ba shi bane me
ya sa zai yi kira na da Zainab.
Hakan na nufin ya san
mahaifiyata kenan...me yiyuwa
kama na yi masa da ita. Zuhuriyya
ta ci gaba da zancen zuci. To
koma dai wane ne ko ta sanshi
ko bata san shi ba ita dai ganinsa
ya sa duk kaunar Dakta
Sadi ta fita daga ranta cikin
kwana biyu kacal.
Zuhuriyya ta ajiye kundin
hotunan sannan ta dubi agogo
karfe bakwai saura. Nan da nan
ta ji tsoro ya kamata kada fa ya
ki dawowa...shi da muka yi da shi
zai dawo. Haka nan zuhuriyya ta
yi ta jira
har karfe taran dare babu labarin
mutumin ta. Daga karshe dai
tana share hawaye ta nufi
daki za ta cire kayan kwalliyar da
ta caba, sai ga shafi'u ya sheko a
guje.
"Zuhuriy...ga wannan mutumin a
waje wai yana kiranki."
Hilal ya dubi zuhuriyya, ita ma ta
dubeshi. Sai yanzu ka ga damar
zuwa."
Zuhuriyya ta ce tana dubansa.
Cikin damuwa.
"Ki yi haku...wallahi mahaifiyata
aka kwantar a asibiti."
Zuhuriyya ta dafe kirji. Mamanka
aka kwantar...a wane asibitin?"
"A asibitin mahaifinki mana
yanzu ma can zan koma shi ne
nace bari na biyo ta nan mu nemi
alfarma tun dazu muke can babu
likita da zai dubata shi ne na ce
me yiyuwa za ki iya hadamu
da...mutumin ki...mijinki dakta
Sadi." Zuhuriyya jiki na rawa ta
ce.
"Bari to na shiga gida na fadawa
matar babanmu in da zani ka ga
dare ya yi, kuma babanmu yau
zai sauka karfe goma sha daya
na daren nan kada ya dawo ya
tarar bana nan ya yi ta fada."
"Je ki fada mata." Hilal ya ce
sannan sai ya dan hade fuska na
karya. Daman mamanki ba a
gidan
take ba?"
Nan da nan ya ga fuskar
Zuhuriyya ta yamutse, bai ji dadin
tambayar da ya yi mata ba to
amma dole ne ya tabbatar.
"Ni...babata tun ina karama ta
mutu
AKA KASHETA*******
.
Ya ya ka shiga ta nan?" Zuhuriyya
ta tambayeshi cikin mamaki sa'ar
da ta ga Hilal ya shiga ta kofar da
zata kai su rukunin gidajen
ma'aikata asibitin. "Na dauka ta
gidan Dakta Sadi
din za mu bi sai mu wuce da shi
cikin asibitin." Zuhuriyya ta dan yi
jim, domin ba ta son su je gidan
Dakta Sadi din tare.
"Na san abin da kike tunani." Hilal
ya ce da ita cikin murmushi.
"Idan mun je kya iya cewa da shi
ni kanen babarki ne." Zuhuriyya
ta harareshi ta ce.
"Ah, ni dai ba abin da kake nufi
nake tunani ba." Sannan sai ta
hade fuska.
"Me ye to in ma ya ganni da kai
din."
Suka fito daga cikin motar babu
magana sannan sai Zuhuriyya ta
wuce gaba Hilal ya bita abaya
suka nufi gidan. A daidai lokacin
da suka isa jikin jerin bishiyoyin
dake gidan ne to Jami'an tsaro
suka fito kamar aljanu suka
zagaye su. Zuhuriyya ta rike
numfashi a
tsorace ta dubi masu bakaken
kaya dake zagaye dasu bata iya
ganin fuskokinsu amma tana iya
ganin duzuzun gashin bakin
bakin katon dan sandan dake
tsaye a gabanta.
"Ka da ki ji tsoro yan mata ba
wani abu za a yi miki ba."
Zuhuriyya ta dubi Hilal a tsorace
tana neman taimako.
Ga mamakinta sai ta ga Hilal ya
matsa daf da ita da murmushi
sannan ya ce da ita cikin rada.
"kada ki ji tsoro Zuhuriyya, ki yi
duk abin da suka ce ki yi yanzun
nan ba da dadewa ba za ki ido
biyu da wanda ya kashe
mahaifiyarki tun kina karama".
Hilal na gama fadin haka sai ya ce
cikin wata murya kasa-kasa.
"Yallabai ka zagaya can bayan da
ita inda zaku iya sauraron mu."
jikinta na rawa, hawaye na zuba
saboda tsoro da rudewa
Zuhuriyya ta bi yansandan zuwa
bayan gidan, a zuciyarta tana
addu'ar Allah yasa ta farka ta ga
kawai mafarki take yi.********
Hannayensa cikin aljihu Hilal ya
karanta addu'arsa ta karshe ta
neman sa'a sannan sai ya danna
kararrawar gidan ko dakika
goma ba a yi ba kofar ta bude.
Dakta Sadi ya dubi Hilal a tsorace.
"Shigo daga ciki Hilal tun dazu kai
nake jira." Abin ya yi matukar
girgiza Hilal
saboda jin ya kama sunansa
haka nan ya lura babu alamun
tsoro sosai a cikin muryarsa. Hilal
ya bi shi a baya suka shiga wani
matsakaicin dakin shakatawa
mai dauke da kujeru sun yi masa
kuri sama da arba'in, daga
bangaren gabas, wata katuwar
talabijin ce mai kamar bango, a
kasa da ita (Video) ce da (VCD) da
kuma na'urar kamo tasoshin
talabijin na duniya. Dakin ya yi
matukar tsaruwa. "A kawo ma
lemo?" Dakta Sadi ya
tambaya.
"Hilal ya girguza kai cikin
kaduwa.
"Na san za ka yi mamaki jin na
kira sunanka kai tsaye, to idan
kana mamaki ma ka bari, domin
a cikin shekaru ashirin da daya
da suka gabata babu wanda
nake kwana nake tashi da shi a
rai sai kai, domin kai kadai ne
shaidar ido-da-ido wanda ya
ganni lokacin da na kashe
TSINANNIYAR KWARTUWAR NAN
HAJIYA ZAINAB
.
****Wash Nagaji Bari Na Huta****BINDIGAR KWALI-20
.
ƘARSHE......
.
Kai kadai ne shaidar ido-da-ido
wanda ya
ganni lokacin da na kashe
TSINANNIYAR KWARTUWAR NAN
HAJIYA ZAINAB
.......A can bayan gidan a tsaye
jikin tagar dakin Zuhuriyya ta ji
abin da ya ce, dan haka sai ta
bude
baki za ta kwalla ihu a rude, wani
dan sanda ya zaburo ya rufe
bakinta da hannu. "Lokacin da na
sami labarin an
neme ka an rasa na ji dadi domin
hakan ya ruda jami'an
tsaro masu bincike a wancan
lokacin.
Sun yi tsammanin kaine ka kashe
ta." Dakta Sadi ya dan yi shiru.
"Sai gashi yanzu ka dawo da jiya
yau. To abin da nake so ka sani
Hilal shi ne a yanzu haka idan aka
duba tsohon fayil na jami'an
tsaro kamannin wanda ake nema
naka ne wanda shaidu suka
bayar domin kaine mutum na
karshe da aka ga ya fita daga
gidanta a ranar da na kasheta."
Dakta Sadi ya bushe da dariya.
"Ka san duniya ba ta rabuwa da
yan tsurku irin su DAN BA'U me
tireda na kofar gidan Hajiya
Zainab a wancan zamanin." Dakta
Sadi ya dan yi shiru yana nazarin
fuskar Hilal akwai wani abu da ke
bashi tsoro a yanayin fuskar
saurayin da ya girma ya zama
mutum a halin yanzu ko kadan
mutumin bai tsorata ba. Dakta
Sadi ya ci gaba da cewa. Idan na
ga dama yanzun nan sai
in damkawa jami'an tsaro kai".
A karo na farko sai Hilal ya
dubeshi a murmushe ya ce.
"Kuma duk da kashe uwar da
kayi bai isheka ba shi ne kake
son ka auri yar ta itama kasheta
din
kake son ka yi."
Dakta Sadi ya yi murmushi
"Wannan duk fadin bakinka ne
anan amma baka da shaidar da
zaka nuna wa jami'an tsaro su
yarda da abin da ka ce ni kuwa
yanzu idan na ga dama sai in
mika ka garesu domin sun dade
suna sane da kai."
Hilal ya mike tsaye da faffadan
murmushi sannan ya dubi Dakta
Sadi ya ce.
"Ka san dai ai ba ni na kasheta ba
kaine ko ??"
"Kwarai kuwa ni na kasheta da
hannu na amma ba ka da shaidar
hakan ko kana da ita?"
"Kwarai kuwa." Hilal ya ce sannan
sai ya daga murya ya ce.
"Yallabai kuna iya shigowa."
"Kafin kiftawa da bismillah
jami'an tsaro sun cika dakin
shakatawar. Dakta Sadi ya rude
a tsorace ya dubi jami'an tsaro.
"Kun...kun san dai ba ni na
kasheta ba ko...shi ne ga shi
nan." "Idan mun je ka fadawa
alkali."
Shugaban jami'an tsaron ya ce
sannan sai ya mikawa Hilal
hannu ya ce.
"Ba ni abin da na baka." Daga
cikin aljihunsa Hilal ya dauko
wata yar karamar rediyo baka
wacce ke dauke da duk
maganganun da suka yi da Dakta
Sadi ya mikawa yan sandan. A
daidai lokacin da suka bugawa
dakta Sadi ankwa sai suka ji
motsi a bayansu. Suka juya baki
daya. Zuhuriyya ce ta shigo
idanunta cike da hawaye ta zo
kusa da Hilal tana rike da
hannunsa kamkam ta ce.
WALLAHI NA GANE KA HILAL"
Hilal ya dubeta da murmushi
sannan ya dubi dakta Sadi ya
nuna shi da dan yatsa ya ce. "Kin
ga wanda ya kashe mahaifiyarki
yau dubunsa ta cika." Sannan sai
ya dubi Dakta Sadi ido da ido ya
ce.
DA'ACE KANADA SAURAN YANCI DA
NA GAYYACE KA AUREN MATANA
BIYU 2
.
KARSHE
.
JIKAN SIDI MAI JAKA
(YARIMA GANGARIYA)
Kasancewar Paper Daya Wacce
Kuma ita ce ta karshe a cikin
wannan littafi ta bada matsala
ma'ana paper din tayi (damage).
dan abin da ya saura na daga
labarin wanda baku ji ba yana
cikin wannan paper din da tayi
damage duk da yake ma dai
babban abin da kowa yake so ya
ji bai wuce yadda Hilal zai auri
Mata biyu Rukayya da Zuhuriyya a
lokaci daya ba to amma idan
kuka yi la'akari da soyayyar da
Rukayya take yi masa idan ya
zauna ya bata labarin duk abinda
ke tsakaninsa da Mahaifiyar
Zuhuriyya wacca kuma itace
sanadiyyar barinsa gida har
tsawon Shekaru ashirin da daya
dakuma yadda akayi har aka
kama mijin da zata aura bazataki
amince masa auren
zuhuriyya ba ya hada su tare in
yaso tunda Rukayya ce babba sai
ta zama uwar gida ya fara
aurenta daga baya kuma sai ya
auri amarya Zuhuriyya.
. ALHAMDULILLAH
.... Godiya tabbata ga Allah dayabani ikon gama
kamumoku
wannan littafu mai suna BINDIGAL KWALI

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment