Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hilal ya
sauke gilashin motar domin ya
sami damar ganin irin sauyin da
aka samu a birnin kano
BAYAN TAFIYARSA BABU SHIRI.
Hilal ya yi mamakin ganin irin
manya-
manyan gidajen da suka dadu a
cikin garin idan ban da ya gani a
rubuce da ba zai taba imani da
cewa nan birnin kanon da ya
sani ba ce A zuciyarsa ya yi
mamakin irin
yadda yan jaridu ke karawa miya
gishiri domin a yadda ya ji suna
bada labarin yakin mai tatsine
bayan tafiyarsa bai dauka zai
tarar da kano a haka ba. Hilal ya
shafi aljihunsa a hankali domin
ya ji ko bindigar rabor tana nan
sannan sai ya kalli zoben dake
dan yatsansa na hagun ya ce a
sanyaye.
"Rabon ka da garin nan yau
shekaru ashirin da daya. tun
wacce ka fi so a duniya tana
raye." wani zazzafan hawaye ya
fara sartu akan kyakkyawar
fuskar da karin shekaru ashirin
da daya basu iya dakushe
kyawunta ba. Sa'ar da motar ta
shiga cikin layin
sai Hilal ya miko kansa ta cikin
tagar yana kallon gidajen dake
layin cikin kaduwa sannan har
sa'ar da motar ta ja birki ta tsaya
a kofar gidansu kaduwar bata
saki Hilal ba badan komai ba
kuwa sai don ganin a cikin
shekaru ashirin da dayan da ya yi
baya nan ba a sami wani
kwakkwaran sauyi na gani a
fada ba. Wannan ita ta sa motar
na tsayawa Hilal ya bude kofar ya
fito kana jikinsa na rawa ba tare
da ya dubi inda sabuwar
katangar gidansu take ba sai ya
kalli kudu ya kalli arewa, sannan
ya kalli gabas da yamma cikin
tsananin mamaki in ka dauke
wasu yan tsukakkun benaye
guda uku masu kamar hasumiyar
masallaci gami da wani katon
kwalbati mai tudun tsiya kamar
kabarin jaki gami da katangar
gidansu da aka sake ginawa
babu wani sauyi da aka samu da
layin sai tarin bolar data cushe
magudanan ruwa da kuma karin
kaji da agwagi da aka samu a
layin. Jikin Hilal na rawa ya nufi
kofar gidan makwabtansu Malam
Iliya, sai ya ga har yanzu dai
tsohon ginin nan ne mai kamar
bukka to sai dai kuma katuwar
rumfar kiwon awakin da Hilal ya
sani tana kafe a kofar gidan a
yanzu babu ita har ma an
sumunce gurin wani dan
tutturnan saurayi mai doguwar
keya da kyawawan idanu farare
gami da dogon bakin da ya bashi
siffar tsuntsu shi ne zaune a
gurin da wani dan teburi yana
sayar da kayan masarufi masu
rangwamen farashi.
"Sannu da zuwa." Dan saurayin
ya ce da Hilal, sannan lokaci guda
ya matso inda suke ya kamawa
direban suka fara sauke kayan
Hilal.
"Yauwa sannunka dai...sannu da
kokari." Hilal ya ce yana duban
saurayin sama da kasa domin ko
shakka Hilal ba ya yi yasan
saurayin dan Malam Iliya ne ko
kuma jikansa domin idanunsa da
kuma tsayin bakinsa sun nuna
hakan. Me yiyuwa bayan tafiyata
da kadan aka haifeshi. Hilal ya ce
cikin Zuciyarsa domin ya lura
saurayin bai fi shekaru goma sha
takwas zuwa Sha tara ba.
Saurayin da direban suka ci gaba
da sauke manyan akwatunan
Hilal yana kallonsu gabansa na ta
faduwa, bai san abin da zai tarar
a cikin gidansu ba bai kuma san
ta yadda zai fara neman gafara a
gurin iyayensa ba, tabbas ya san
ya gama jefa iyayen nasa cikin
bakin ciki marar misaltuwa
musamman ma mahaifiyarsa
hilal ya yi sauri ya share hawayen
bakin cikin dake kokarin subuce
masa sa'ar da ya tuna da safiyar
wannan mummunan
rana*********** ***
Ranar da ya rasa babbar
masoyiyarsa
Hajiya Zainab.
"....yau ba za ka je makaranta
bane ka ke kwance har yanzu ba
ka tashi ba... Wallahi bani da
lafiya ne..." Maganganun da suka
yi da mahaifiyarsa suka fara
dawo masa a safiyar ranar. Har
yanzun nan da yake tsaye Hilal na
iya tunawa da irin matsananciyar
kulawar da mahaifiyarsa ke nuna
masa a zamanin kuruciyarsa, sai
gashi lokaci guda ya bakanta
mata, a dalilin subucewar wani
abu da ba zai taba daina kauna
ba.
"Malam mun gama" Muryar
direban motar ta katse tunanin
Hilal. Cikin lalaci Hilal ya lalubi
aljihunsa ya zaro wasu adadi na
takardun kudi ya mikawa
direban. Cikin ladabi direban ya
karbi kudin sannan ba a dade ba
ya shiga motarsa ya fice daga
tsukakken layin.
Hilal ya yi tsaye cikin fargaba
yana kallon kofar gidansu, yayin
da dan tutturnan saurayin ya
kura masa idanu a zuciyarsa
yana tunanin duk yadda aka yi
mutumin bako ne kuma me
yiyuwa ma bai san takamaiman
inda ya zo ba.
"Gidan wa kake son zuwa?"
Saurayin ya tambayi Hilal gami da
matsowa kusa da Hilal cikin
niyyar taimako. Hilal ya dubi
saurayin, sannan ya jefeshi da
murmushin yake ya nuna
gidansu ya ce.
"Nan gidan nazo. mutanen gidan
suna nan?"
Saurayin ya yi jim na dan lokaci
"Ai daman babu kowa a gidan
sai Iya me waina."
To ina mahaifan nawa suke? Ya
tambayi kansa Sannan lokaci
guda ya dubi Saurayin.
"Taya ni to mu shiga da kayan
ciki." Kafin ya rufe bakinsa
saurayin ya kinkimi katuwar
akwati daya ya nufi cikin gidan.
Hilal ya yi kamar ya tsaya ya ga
dawowar saurayin, sai wata
zuciyar ta ce dashi shiga kawai
ka tambayi me wainar inda
iyayenka suka koma.
WANNAN ITA TASA HILAL YA
KINKIMI AKWATI Shima ya bi
saurayin a baya. A
daidai lokacinda ya shiga zauren
gidan ne ya ji wata murya na
cewa da saurayin
"Hamza wannan katuwar
akwatin fa ko tsintuwa muka yi?"
Hilal ya ji zuciyarsa ta harba
tsakanin hakarkarinsa sa'ar da
muryar ta daki dodon kunnensa
"Wani mutum ne ya ce na shigo
da ita." muryar Hamza ta ce da
me waina
"Wani mutum? Wane ne?"
"Nima ban san shi ba wallahi
bako ne amma na ga kin yi kama
dashi sosai wallahi"
Hilal ya dafe kirji wani zazzafan
hawaye ya fara kokarin subuce
masa. Ko shakka ba ya yi duk
duniya babu mai irin wannan
murya sai mahaifiyarsa. Dan haka
zuciyarsa na harbawa sai ya
shiga gidan janye da katuwar
akwati me taya
"Ya yi kama da ni fa ka ce, to
wannan wane..." kalamin matar
ya katse sa'ar da Hilal ya shiga
tsakar gidan da sallama cikin
rarraunar murya.
"Ameen wa'a..." Bata karrasa
amsa sallamar ba sa'ar da suka yi
ido biyu da mutumin. Hilal ya
dubi yamusasshiyar tsohuwar
wacce ke sanye da zanen shudin
leshi mai tsadar gaske wanda ya
sha dinki na zamani duk kuwa
da irin tsufan da ta yi. Abin ya
bashi mamaki. Koren dan kwalin
dake kanta ya zame gefe guda
wannan shi ya baiwa gashinta
rabi baki, rabi fari da furfura ya
sami damar burtsowa ta gefen
kyakkyawan dankwalin to sai dai
kuma fuskarta duk ta yamutse
tunani me yiwuwa da bakin cikin
rashin ganinsa sun gusar da
kyawun da annurin fuskar da
Hilal ya sani shekaru ashirin da
daya da suka wuce amma hakan
bai isa ya hana Hilal gane
mahaifiyarsa ba.
"Ummi!" Ya kirata muryarsa na
rawa.
"Hilal...kaine. ..wayyo Allah...Allah
nagode ma da ka dawo min
dashi" Tsohuwar ta fashe da
kuka.
Hamza cikin mamaki da tausayi
ya ci gaba da kallon diramar da
ake yi a gabansa. Shin ko
wannan shi ne dan mai waina da
ta sha ba shi labari? Hamza ya
tambayi kansa.
"Ummi daina kuka dan...Allah"
Hilal ya ce duk kuwa da cewa
shima kukan ya ke yi.
Jikin tsohuwar na bari ta matso
kusa da dan ta ta rike hannunsa
ta duddubashi tana rafsa kuka
kamar karamar yarinya wani
sa'in kuma sai ta fashe da dariya
kamar tababbiya, motsattsiyar
fuskarta ma'abociyar kyau da
annuri a wani shudadden
zamani ta jike sharkaf da
hawayen farin ciki a haka cikin
wannan hali tana kuka, yana
kuka makwabta suka fara
taruwa zuwa gidan domin su
ganewa idanunsu abin da ke
faruwa. Da mutum ya shigo sai
tsohuwar ta dubeshi ta ce.
"Wannan shi ne dana da na sha
baku labarin ya bata. Gashi yau
Allah ya dawo min da
shi."********** ****
Wannan ita ta sa gidan ya ci gaba
da dinkewa da yan uwa da
abokan arziki domin duk wanda
ya fita sai ya bai wa dan uwansa
labari. Wasu ma ba su san Hilal ba
wasu ko haifar su ma ba a
yi ba sa'ar da Hilal ya bar gida
amma sai zuwa gidan suke
domin su sami abin kai wa gaba.
Ana cikin wannan hargitsi ne,
Hilal ya dubi mahaifiyarsa ya ce.
"Ummi ban ga BABA ba?"
Mahaifiyarsa ta sunkuyar da kai
sannan ta ce a sanyaye bakinta
na rawa. "Shekararka daya da
tafiya Allah
ya yi masa rasuwa.. Yan mai
tatsine ne suka kashe shi a kofar
gidan nan ka san shi da taurin
kai!" Ta sake fashewa da
kuka.********** **********
Daga ita sai daurin kirji ta shigo
kawataccen dakin ruwa na diga
cikin tsefaffen gashin kanta
wanda ke kwance akan doron
wuyanta kafafunta sanye cikin
farin takalmin roba marar nauyi
fitowarta kenan daga wanka
Matar ta yi ajiyar zuciya kana ta
nufi kujera ta zauna a gaban
teburin kayan kwalliyarta wanda
ke dauke da kayan shafe-shafe
da manne-manne sama da kala
dari domin a duk wata guda na
duniya sai ta kashewa kayan
kwalliya naira dubu bakwai. Kudi
ba komai bane a gurin matar
domin ta mallake su an kuma
tara mata su a gida. Haka nan a
halin da ake ciki kudin da ta
tarama a shekaru goma sha biyar
da
ta yi tana aikin banki sun isheta
kashewa har iya rayuwarta ko da
kuwa bata gaji komai ba a wajen
mahaifinta marigayi Alhaji
Alawaisu. Wannan ita tasa aduk
karshen mako idan ta bushi iska
sai ta hada liyafar sanyaya rai ta
gayyaci kawaye irinta
shagwababbu su yi ta
rakashewa abin su domin talauci
ba abokin wasansu ba ne, ba su
ma san shi ba sai dai su ji labari.
Akwai wata rana, suna zaune ita
da wata kawarta sai suka ji wani
mai labarai a gidan rediyo yana
bayanin irin masifar wahalar da
talakawa ke ciki a kasar nan har
ma yana cewa mutanen da ke
kwana ba su ci abinci ba ba zasu
kirgu ba. Jin haka ke da wuya sai
matan biyu suka bushe da dariya.
Kawar matar ta dubeta ta ce.
"Oh! Masu labaran nan ba a
rabasu da QARYA.
.
BINDIGAR KWALI--> 11
.
Jin haka ke da wuya sai matan
biyu suka bushe da dariya.
Kawar matar ta dubeta ta ce.
"Oh! Masu labaran nan ba a raba
su da karya ki ji fa wai har akwai
wadanda ke kwana ba su ci
abinci ba." Matar ta yi murmushi
ba ta ce komai ba domin ita ta
san abin da mai labaran ke nufi a
kalla dai koda bata san menene
talauci ba to ta taba ganinsa
muraran a gidan mutumin da tafi
kauna fiye da kowa a duniya.
Matar ta dauki wani tattausan
shudin kyalle ta fara goge ruwan
dake cikin gashinta mai santsi a
zuciyarta tana cewa yau dai ya
kamata na je wankin gashi duk
kuwa da cewa jiya-jiyan nan ta je
wankin gashin da safe. Bayan ta
gama wanke gashin sai ta mika
hannu zata janyo kwalbar mai
kusa da ita sannan ne to ta tuna.
Cikin sauri ta zabura domin ta
tuna da cewa ta manta da al'adar
da ta saba yi a duk safiyar
duniya. Cikin sauri ta janyo lokar
da ke jikin teburin kayan
kwalliyar ta dauko wata farar
ambulan sannan ta zaro hoton
kwaya daya tak wanda a gurinta
ya fi komai muhimmanci a cikin
dakin domin da kyar ta sami
hoton. Matar ta kurawa hoton
idanu na tsawon lokaci hawaye
na zuba daga cikin fararen
idanunta har tsahon mintuna
goma sha biyar a zuciyarta tana
cewa
"Allah...Allah ka dawo min da
masoyina Hilal.
A daidai lokacin ne to ta ji motsi
a bayanta. Bata damu da ta juya
ba domin ta san ko wace ce.
"Um...hum kin fara abin ba ai sai
ki yi ta yi wahalalliya, soyayya da
matacce." Muryar mahaifiyar ta
ce. "Ke dai Rukayya wallahi kin
shiga
uku, ni na taba ganin irin
wannan masifa ki yi ta fama da
son mutumin da ya riga ya mutu
haba Rakayya. Yau fa shekarar sa
ashirin da daya kenan da barin
gida." Ta dan yi shiru sannan sai
ta fice a fusace tana cewa.
"In kin gaji da zaman haka ai kya
koma gidan mijinki."
Rukayya ta yi ajiyar zuciya sa'ar
da ta gama jin bambamin fadan
mahaifiyarta. Ba ta damu ba
domin har ta saba da irin
wannan fada, dan tun tana
budurwa take jin irin wannan
fada, har zuwa aurenta na farko
wanda ko shekara guda ba a yi
ba ta fito daga gidan mijin.
Daman sai da ta fadawa iyayen
nata cewa ita fa ba za ta auri
wani mutum ba a duniya sai Hilal,
idan kuwa Hilal ya mutu ba zai
dawo ba, to ita da aure har
abada.
Ba a fi shekara goma ba da
mutuwar aurenta na farko, wani
dan abokin mahaifinta ya nuna
yana kaunar zama da ita.
Rukayya ba ta ma san da
maganar ba sai bayan da aka
daura aurenta da mutumin.
A ranar da za su wayi gari na
farko da ango nata, ta dubeshi
tace.*********
"Bawan Allah ka rufawa kanka
asiri dan ban taba ganinka ba,
ban san da labarinka ba sai ji na
yi an daura min aure da kai, ka
ga ashe abu ne me wuya na iya
zama da kai dan ba na
kaunarka." mutumin dan gajere
fari kamar zabiya mai katon kai
da fadi kamar faranti ya dubeta
da dariyar keta ya ce.
"Ni ma kaina na san ba kya
kaunata, amma ai ni ina kaunar
ki dan haka da za ki yi hakuri mu
zauna da ya fi domin ina son
matata kuma ba zan sake ki ba."
A wayewar garin ranar da asuba
Rukayya ta rushe katon kansa da
kwalbar lemo. Kwanansa goma
a asibiti yana jinya. Fitowarsa ke
da wuya ya bata takarda yana
murna.
A shekarar da ta fara aiki a banki
ne, aka dada takurawa Rukayya
ta
auri wani dan kasuwa Alhaji
Mahmud. Auren ya so ya yi karko
domin Rukayya ta sami damar
yin shekara biyu tare da shi daga
karshe mutumin ya kamata tana
shan maganin hana daukar ciki.
"Dan me za ki yi min haka ba ki
san cewa son haihuwa ne ya sa
na aure ki ba." Rukayya ta
dubeshi a yatsine ta ce.
"Da ni ka dauka kaunarka ce ta
sa ni aurenka? Bin maganar na
gaba ne kawai ta sa ni aurenka
amma ni ina da wanda ke raina
har abada. Idan ba shi ba ba
zan iya haihuwa da kowa ba."
washegari mutumin ya sake ta.
A cikin shekaru ashirin da daya
din da suka gabata auren
Rukayya biyar a cikinsu babu
wanda ya taba wuce sama da
shekara biyu.
A yanzu da take zaune dauke da
hoton a hannunta shekara biyar
kenan rabonta da aure. Ba ta da
aiki sai hada liyafar kawaye da
tsofaffin abokanta yan boko
wadanda suka yi mutunci a
zamanin zaman su na jami'a.
Yaushe za ka dawo Hilal...yaushe
ne za ka dawo ka gusar da bakin
cikin raina? Rukayya ta ce tana
duban tsohon hoton da ke rike a
hannunta. Sannu a hankali sai ta
mike tsaye dauke da hoton ta
nufi madubi kana ta dubi hoton
sannan ta dubi kanta a madubin.
*HAKIKA KWANAKI NA SHUDEWA
*WATANNI NA WUCEWA
*SHEKARU NA KARA YAWAITA.
*ZAMANI NA DADA NISAWA.
*KYAWUNA NA DADA DAKUSHEWA
Rukayya ta ce da kanta. Ta lura da cewa fuskarta tafara
tsofewa kyakkyawan saurayin
dake jikin hoton. Shin yaushe
Hilal zai dawo? Rukayya ta kuma
tambayar kanta. A karo na farko
cikin shekaru ashirin da daya sai
ta ji tsoro ya cafki zuciyarta
sannan ta fara mummunan
tunanin da zuciyarta ba zata iya
jurewa ba.
"Anya kuwa Hilal bai dade da
mutuwa ba?" Ta tambayi kanta
da kanta, zazzafan hawaye na zuba akan
kumatunta.*********
Washegarin ranar da Hilal ya dawo da sassafe misalin
karfe
shida mahaifiyarsa Asma'u ta
nufi dakinsa domin su sami
damar tattaunawa dashi. Jiya ba
a bar su sun sake ba, don tun
dawowarsa yan uwa ke ta
tururuwa suna zuwa kallonsa
duk kuwa da cewa da yawa daga
cikinsu. Sun watsar da mahaifiyar
ta sa babu ruwansu da ita. Har
karfe goma sha biyun dare
jama'a ba su bar gidan ba,
wannan ita ta sa sai kusan biyu
saura Hilal ya sami damar
runtsawa.
Sa'ar da Hilal ya shiga tsohon
dakinsa a ranar sai ya ji kamshin
turare ya bugi hancinsa, sannan
ya ji kafarsa ta taka wani abu
tattausa, tabbas kilishin dakine.
Abin mamaki na uku kenan. Hilal
ya ce cikin zuciyarsa. Domin sa'ar
da ya fara shiga gidan ya lura
duk an gyara ginin gidan an
sumunce ko ina an kuma sake
fenti, hakika gidan ya sake kyau
nesa ba kusa ba fiye da yadda ya
bar shi shekaru ashirin da daya
da suka wuce. Mamaki na biyu
shi ne tufafin da ya gani masu
tsada jikin mahaifiyarsa, sai gashi
yanzu kuma ga dukkan alamu zai
sake ganin wani sabon abin
mamakin. Sannu a hankali Hilal ya
fara laluben inda makunnan
lantarkin take, bayan wasu yan
dakiku ya samu sannan ya
kunna, dakin ya gauraye da
haske Hilal ya dubi dakin a rude.........
BINDIGAR KWALI--> 12
.
Kamar yadda ya yi tsammani tun
farko, tabbas tattausan kilishin
daga bangaren arewa a jikin
bango wata katuwar katifa ce
dindimemiya, me yiyuwa sai ya
sa tsani zai iya hawanta. Katifar
lullube take da wani irin
tattausan zanen gado mai gashi
dauke da surar wani
kyakkyawan aku launin rawaya
zaune akan bishiya. Daga
bangaren kudu na dakin
teburine na gilashi mai bakaken
kafafu, dauke da fulawowi na
roba, da kuma sauran yan
littattafan Hilal na makaranta
wadanda yake amfani dasu
shekaru ashirin da daya da suka
wuce. Ko da Hilal ya duba
bangaren gabas sai ya hangi
wasu yan kujeru masu taushi
guda biyu. Tsawon mintuna biyar
Hilal na tsaye cikin tekun mamaki
yana kallon dakin. Shin wane ne
da wannan aiki? Ya tabbata a
yadda ya ga mahaifiyarsa a
motse a kode duk a rame babu
alamar jin dadi a gareta babu
wata hanya da zata iya kawata
wannan gida nasu haka, ga
kuma wani abin mamakin shi ne
babu alamar kura ko kankane a
cikin dakin.
Hilal ya zauna akan tattausar
katifar. Ga mamakinsa sai ya ji
lokaci guda gajiya ta lullube
gabobinsa, nan da nan ya fara
hamma, sannan ba a dade ba
zuciyarsa dauke da tambayoyi
masu tarin yawa sai barci ya
daukeshi. Tunani na karshe da ya
zo zuciyar Hilal a daidai lokacin
da barcin ke kokarin dauke shi
shi ne, shin me ya sa
mahaifiyarsa ramewa da
tsofewa, bayan kuma ga dukkan
alamu babu wahala a gidan?
Wata zuciyar ta ce da shi bakin
cikin rashinka ne Hilal?
***
"Salamu alaikum...Hilal ka tashi
ne?"
Mahaifiyarsa ta ce dashi Hilal ya ji
wani abu ya lullube zuciyarsa.
Wannan shi ne gidansu, wannan
shi ne mutuncinsa, wannan ita ce
irin kulawar da mahaifiyarsa ke
nuna masa tun yana karami. Hilal
ya tuna safiyarsa ta karshe a
gidan.
Hilal ya amsa sallamar a daidai
lokacin da mahaifiyarsa ta shigo
dakin ta zauna a gaban katifarsa
akan tattausan kilishin dakin.
Cikin sauri ya gaisheta, kana ya
ajiye tasbahar dake hannunsa a
gefe guda.
"Jiya ba mu sami damar tattauna
komai ba jama'a sun yi yawa."
Mahaifiyarsa tace tana dubansa.
A zuciyarta tana cewa Hilal ya
zama cikakken mutum.
Hilal ya sake duban kayan dake
cikin dakin sannan ya dubi
mahaifiyarsa alamun tambaya
karara akan fuskarsa,
mahaifiyarsa ta lura da hakan,
wannan ita ta sa ta dubeshi da
busasshen murmushi ta ce.
"Na san abin da kake tunani,
wane ne ya gyara gidan nan ko?
Wane ne kuma ya ba ni sutura
ko?" Hilal ya gyada kai cikin
mamaki domin kamar zuciyarsa
ta karanta.
"Kafin na baka amsa zan zo jin
inda ka tafi da kuma dalilin
tafiyar ka, ba ka dawo ba sai
yanzu bayan shekara ashirin da
daya." Ta dan yi shiru tana
dubansa sannan sai ta sunkuyar
da kai ta ce da shi a sanyaye.
"Hilal sace ka a ka yi, ko kuwa
wani ka yi wa laifi ya yi maka
kurciya?"
Hilal ya sunkuyar da kai cikin
tsananin tunani, bai san ta inda
zai fara ba, shin wai zai fada
mata labarin ne tun daga lokacin
da aka kashe babbar
masoyiyarsa Zainab, ko kuwa iya
labarin tafiyarsa kawai zai fada
mata. Zuciyarsa ta shiga cikin
rudani, dole ne in har yana son ta
fahimci dalilin barinsa gida ya
sanar da ita labarin Hajiya Zainab.
Hilal ya yi ajiyar zuciya sannan ya
dubi mahaifiyarsa lokaci guda ya
dauki tasbahar dake dab da shi
ya fara wasa da ita, yana duban
koren kilishin dakin.
"Ummi...kin tuna da wata Zainab
da ta taba zuwa nemana?"
Mahaifiyarsa ta gyada kai cikin
sauri ta ce.
"Ba zan taba mantawa da ita ba,
wata kyakkyawar mace da ta zo
nemanka a mota ko? Hilal ya
gyada kai, sannan ya dan yi shiru
yana tunanin kaset din tsohon
majigin dake cikin
kwakwalwarsa, sannu a hankali
sai ya fara tunanowa.
Ga shi nan ya fito kan titi cikin
sauri a firgice, yana kokarin
shigewa duhu domin baya son
motocin yansandan dake giftawa
ta gabansa a guje su hasko shi.
Hawaye na zuba kamar ruwa, ya
kasa imani da abin da ya gani
shin anya kuwa da gaske ne
Zainab masoyiyarsa ya gani a
mace cikin jini? Ko kuwa mafarki
ne yake. A daidai lokacin da ya
raba ta jikin doguwar katangar
wani gida ne wani katon kare ya
yi masa haushi. Hilal ya yi tsaye
cak a cikin duhun jikin katangar.
A lokacin ne ya tabbata abin da
ke faruwa gaskiya ne ba mafarki
ba.
"Ka yi min rai don Allah...ka kyale
ni na wuce kada ka sa a kamani
wallahi ba ni na kasheta ba.." Hilal
ya ce da katon karen mai bakin
kai da farar jela kai ka ce da
mutum yake magana. Tsawon
yan dakiku Hilal da karen suna
kallon juna, sannan kamar karen
ya fahimci abin da Hilal ya ce sai
ya fara ja da baya da baya sannu
a hankali har ya shige cikin gidan
mai katuwar kofar baka.
Hilal ya dafe kirji gami da ajiyar
zuciya sannan ya zura a guje ya
nufi bakin titi a rude
kwakwalwarsa a hargitse. Sa'ar
da ya kawo daf da bakin titin sai
ya tsaya gindin wata katuwar
bishiyar dorawar turawa yana
mayar da numfashi lokaci guda
ya dubi kwan dalelem agogon
robar dake hannunsa mai lamba-
lamba karfe bakwai na dare
saura mintuna. Hilal ya jingina da
jikin bishiya yana haki
"Na shiga uku! Na shiga uku!! Ya
ce a rude Sannan zuciyarsa ta
fara tsalle-tsalle tana tunanin abin da ya kamata yayi.
Abu na farko da ya fara zuwa
zuciyarsa shi ne ya kira yan sanda ya yi musu bayanin
cewa
abokin mijinta ne ya kashe masoyiyarsa Zainab.
"Kai shashasha." wata zuciyar ta
ce dashi "Yanzu idan yan sandan
suka tambayeka abin da ya kai ka
gidan wacce amsa za ka ba su?"
Wani zazzafan gumi ya barko
akan goshinsa. Sai in ce da su kwartanci ne ya kai ni. Hilal
ya
baiwa zuciyarsa amsa duk kuwa
da cewa ya san har abada ba zai
taba iya fadawa yan sanda haka
ba. To wacce hujja ma na ke da
ita da zan gamsar da su cewa
dakta Sadi ne ya kasheta? Hilal ya
tambayi kansa. Me yiyuwa ma su
yi tunanin cewa ni ne na kasheta
rudewa ta sa na kawo kaina.
Wannan tunani shi ya sa shi
kawar da tunanin zuwa gurin
yan sanda daga zuciyarsa.
"Ka tafi gida kawai abinka ka ci
gaba da addu'ar Allah sa babu
wanda ya ga shigar ku gidan
tare da ita." Zuciyar tasa ta ci
gaba da fada masa.
Jikin Hilal ya dauki rawa sa'ar da
ya tuna lokacin da suka zo kofar
gidan dazu.
"Sannu da zuwa Hajiya." Wasu
mutane guda biyu suka gaisheta,
sa'ar da Zainab ta tsayar da
motar a kofar gidan domin kofar
a rufe babu kuma me budewa
tun da ta sallami duk masu gadin
domin ta sami sakewa da tsohon
kwartonta dakta Sadi.
"Yauwa sannun ku dai. Dan Ba'u" Hajiya zainab ta ce da
daya
daga cikin mutanen biyu wadanda suka nufo gurinta a
rusune cikin fadanci Hilal ya dubi
yar rumfar kwanon dake daf da kofar gidan sai ya ga ashe
yar karamar tireda ce a gurin mafi yawa-yawan
abubuwan dake cikinta biskit ne da alewa kala
daban-daban. Me yiwuwa yaran
masu hali dake yankin unguwar
ne ke saya. Hilal ya ce cikin zuciyarsa.
"Bari a bude miki Hajiya ba ma
sai kin fito ba." daya daga cikin
mutanen wanda ta kira da Dan Ba'u ne yace hakan. Cikin
sauri ya nufi kofar ki-ki-ki-ki ya janye
kofar gefe guda sannan ya ce.
"Bismillah Hajiya." Zainab ta tuka
motar zuwa farfajiyar gidan.
Bayan ta tsayar da motar sai ta
fito daga cikin motar a daidai lokacin da dan ba'u ya ke
kokarin rufe kofar.
"Dan Ba'u." Ta kira sanansa Cikin sauri Dan Ba'u ya taho
inda
take ya durkusa "Gani Hajiya" Hajiya Zainab ta mika masa
takardar kudi ta ce. "Na gode, ga
wannan kwa raba da wannan aboki naka na waje." "Na
gode Hajiya." Dan Ba'u ya ce Duk wannan Hilal na zaune
cikin motar bai fito ba. A daidai
wannan lokacin ne ya ji Dan Ba'u yana cewa da Hajiya
Zainab.
"Ah.. Hajiya wannan dan uwan Alhaji ne..
naga kamar sun yi
kama." Hilal ya ji gabansa ya fadi
domin ya san irin wadannan mutane yan zaman sheda ne
ba kasafai suke manta fuskar duk
mutumin da suka gani sau daya ba.
"Oh! Hila....uhm...u hm....abokin... Aikina ne..." Ta fada
muryarta na rawa. Hilal ya ji abin da ta ce ya kuma ji irin
rawar da muryarta
take yi ya kuma tabbata Hajiya
Zainab ba gwana ba ce wajen iya karya
"Oh....to sai an jima Hajiya." Dan Ba'u ya ce. Sannan ya
dubi Hilal ta cikin gilashin motar. Mutanen
biyu suka kurawa juna idanu na dan lokaci sannan sai
Dan Ba'u ya juya cikin sauri ya nufi kofar
gidan ya fita daga waje Ya janyo
ta ya rufe Hilal ya lura kamar akwai alamar murmushi a
gefen
bakin mutumin Tun daga wannan lokaci Hilal ya san a
duk
inda suka hadu Dan Ba'u ba zai taba mantawa da shi ba
Dan haka a lokacin da Hilal ke jingine jikin bishiyar yana
tunanin tafiya gida sai ya ga bazata sabu ba wai bindiga a
ruwa. Tabbas ya sani idan an dade ba a
sami gawar zainab ba kwana biyu inda kuwa har yan
sanda
suka fara bincike ba za a dade ba su Dan Ba'u zasu bada
shaidar cewa sun ganshi da ita sun shiga gidan.
Gumi ya ci gaba da sartu akan goshin Hilal tuni har rigar
dake jikinsa ta fara mannewa a bayansa. Tunanin
mahaifiyarsa
ya fado masa. Idan har akwai abin da Hilal yake tsoro to
shi ne bacin ran mahaifin sa. Ya riga ya
sani idan allurar sojansa ta motsa
mahaifiyarsa ma ba kyaleta yakeyi ba ballanta na kuma
shi Hilal ya riga ya sani ko da kwartanci
za a tuhume shi zai da shi idan mahaifinsa ya sami labari
kashe
shi zai yi tabbas kashe shi zai yi !
Duk da yake dai mahaifin Hilal kafa daya ke dashi ido
daya amma Hilal na da wayo sa'ar da
mahaifinsa ya ke cewa sai ya harbe wani saurayi dake yi
musu ihu kullum akan kwanar layi in
ban da manyan unguwa sun sa
baki da abin ya baci Wannan shine tunanin da ya sa Hilal
barin gida kano.
Har yanzun nan da Hilal ke gaban
mahaifiyarsa yana bata labarin
tafiyarsa zuciyarsa na tuna lokacin da ya isa tashar motar
dogayen motoci dake zuwa kudu. A wannan lokacin dan
kudin dake aljihunsa basu taka kara sun karya ba a haka
ya isa
tashar ba tare da ya san inda zai dosa ba. Ya jima yana
zagaye a cikin tashar......
INA KUMA HILAL ZAIJE ???
BINDIGAR KWALI--> 13
.
Ya jima yana zagaye acikin
tsashar lokaci-lokaci ya kan duba
agogo a zuciyarsa yana tunanin
me yiyuwa yanzu an
tsinci gawar Zainab. a'a me yiwa
Zuhuriyya ta farka cikin dare ta
sami mahaifiyarta a kwance cikin
jini Hilal ya tausayawa Zuhuriyya
irin halin maraicin da zata shiga
Tsawon lokaci Hilal na ta zagaye-
zagaye cikin tashar tuni har
hankalin fasinjojim da ke shirin
tashi karfe bakwai ya fara kaiwa
gareshi.
A daidai lokacin ne Hilal ya hangi
wani bahaushe dan duniya
zaune a gefe guda sanye da
shudiyar riga ta "Jeans" da
wandonta, gashin kansa ya koma
tsakiya goshin na kyalli kamar
madubi saboda sanko a hannun
mutumin karan sigari ne yana
karawa sararin samaniya hazo
babu abin da ya dameshi lokaci-
lokaci ya kan dubi katon agogon
mai kamar ankwa dake
hannunsa, ga dukkan alamu ya
kosa motar ta tashi.
Hilal ya matsa kusa da mutumin
jikinsa na rawa ya ce.
"Wannan motar ina za ta?"
Mutumin dan duniya ya busa
hayaki sama kana ya jefar da
guntun tabar ya take da katon
bakin takalminsa ya dubi Hilal.
"Ikko za ta sai ka hanzarta. Ina
tsammanin akwai

Please Login or Register in order to submit comment