Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da abin ya
faru Dakta Sadi bai moru ba
kuma duk abin da ya taba a
ranar sai tsautsayi ya afkawa
abin misali da safe zai shiga
wanka ya dauko bokitin roba
cike da ruwa sai tunanin zainab
ya fado masa a take anan ya jefar
da robar ya dafe kirji cikin bege
da bakin cikin ganin shi da
ita sunyi hannun riga kenan.
Bokitin robar fashewa ya yi sai
da ya sayi wani. A ranar dai kuma
kadan ya rage mota ta kade shi
yazo tsallaka titi a daidai lokacin
da ya hango wata mata za ta
shiga asibitin awon ciki matar
kamar su daya da Hajiya Zainab.
Haka dai abubuwan tsautsayi
suka yi ta faru a kansa har zuwa
safiyar yau wadda rana ce da zai
yiwa wani bawan Allah mai
hannu da shuni tiyata. Kadan ya
rage Dakta Sadi yace ba zai yi
aikin ba to amma kasancewar
duk likitocin dake asibitin babu
wanda ya yi kwarewarsa kuma
mutumin da za a yiwa mai fada
aji ne ya ce shi baya son kowa ya
tabashi sai likitan da ya fi kowa
kwarancewa a asibitin wannan
shi ya tursasa Dakta Sadi yin
tiyatar. To ganin irin yadda
tsautsayi da jarabobi suka yi ta
samunsa duk sakamakon begen
matar da a yanzu ya tabbata ya
kamu da ciwon sonta su suka sa
shi fargaba lokacin da ya fito
daga dakin tiyatar A da can
lokutan baya idan Dakta Sadi ya
fito daga dakin tiyata za
ka sameshi ne cikin fara'a da
annashuwa domin ya san bai
taba yin aiki an sami kuskure ba
to amma a karo na farko cikin
shekara kusan tara kenan sai
Dakta Sadi ya sami kansa yana
mai shakkar aikin da ya yi dan
haka koda talfon din ya sake
daukar ruri sai Dakta Sadi ya ji
gumi ya rufeshi nan da nan ya
nufi kan talfon ya dauka. "Hello,
wa ke magana?" "Amburus ne"
Aka ce dashi.
"Sadi ka yi sauri ka dawo asibiti
yanzun nan domin ana son
ganinka da gaggawa." Dakta Sadi
ya ji numfashinsa ya dauke tuni
har tafin hannunsa ya fara
jikewa da gumi da kyar ya ke rike
talfon din.*****
"Am....Amburus in ce dai ko
lafiya?" Dakta Sadi ya tambaya
"Uhm....to lafiyar kenan amma
can daya bangaren iyalan wanda
ka gamawa tiyata yanzun nan ba
lafiya ba domin ka manta ka
dinke tumbinsa dauke da
kyawawan almakasanka guda
biyu. Sadi ya rike numfashi cikin
kaduwa ba zai yiyuwa ba sam-
sam ba zai yiyu ba ace ya manta
almakashi a cikin mutum haba
dai kamar wanda ya fara aikin
yau wannan dai kawai wasa ne
Amburus ke son yi domin daman
ya dade yana yi masa hassada
akan aikinsa saboda ganin ya
fishi kwarewa.
"Amburus saurara da kyau ni ba
wasa na tambayeka ba".
Amburus dake bangaren ya
gimtse dariya da kyar sannan
yace. "Da gaske nake wallahi
almakashi biyu ka manta a
cikinsa." Dakta Sadi ya yi shiru
gumi na kwarara akan fuskarsa
kamar ruwa can ya nisa ya ce.
"To ku bar shi yadda yake kada
ku taba shi gani nan zuwa."
Amburus ya yi ajiyar zuciya ya ce.
"Ai tabashi ko rashin tabashi ba
zasu amfaneshi da komai ba
domin yanzu ya kusan mintuna
biyar kenan a kiyama, ya tafi tare
da almakasan ka guda biyu a
tumbinsa Dakta Sadi ya yi jifa
da kan talfon din cikin fushi da
fargaba
Karfe biyar da yan mintuna Hilal
ya fito dauke da farar takardar
tambayoyin jarrabawar a
hannunsa. Hilal ya dubi sauran
dalibai dake ta faman ife-ife da
hayaniya gami da kade-kade
wasu kuwa har da yaga kayan
makarantar dake jikinsu domin
wai duk murna ce ganin daga
yau sun yi sallama kenan da
makarantar sakandare. Hilal bai
kula dasu ba domin shi
rayuwarsa cikin tashin hankali
take kuma shi kansa ya san
jarrabawar da ya zana a yau sai
wani gyaran Allah amma zai yi
wuya in zai ci. Hilal ya bi ta gefen
yan uwansa dalibai wadanda tun
suna janyoshi akan ya shigo su
dauki hoto har sun gaji sun
kyaleshi wasu har da zaginsa wai
daman mugun hali ne dashi baya
son mutane wasu masu hankali
kuma daga cikinsu suka ce a'a
duk yadda aka yi dai Hilal yau ba
lafiya ba domin ai ada ba haka ya
ke ba.
.
To koma dai mene ne Hilal ko a
jikinsa wai an mintsini kakkausa.
Ya bi ta gefen samarin a hankali
ya nufi gindin wata katuwar
bishiya ta dorawar turawa ya
zauna, yana tunani ko kusa ko
alama bai son tafiya gida ba don
komai ba kuwa sai don ya san
idan ya je din ma ba shi da
sauran kwanciyar hankali Tuni ya
fara nadamar abin da ya
fadawa Zainab Duk da yake dai
yace da ita ba za su sake haduwa
ba hakan bai hanawa zuciyarsa
tunaninta ba a wannan karon ma
har abin ya fi na da Allah ka cire
min kaunarta na huta Hilal yayi
addau'a cikin zuciyarsa domin
ya san abin da ya yi shi ne daidai
ba'a dade ba sai ya ji hawaye ya
fara cika masa idanu ya yi sauri
ya kifa kansa akan cinyarsa don
gudun kada wani dalibi ya
hangoshi ya zo ya dami
rayuwarsa Kusan mintuna biyar
yana zaune a haka fuskarsa cikin
hannunsa yana ta begen da ba
zai amfane shi da komai ba sai
tashin hankali. A daidai lokacin
ne to yaji kamar motsi a daf
dashi "Hilal." Wata sassanyar
murya rarrauna ta kira sunansa.
Numfashinsa ya tsaya cak a
tsakanin kirjinsa. Duk duniya
babu mai irin muryar sai Hajiya
Zainab Hilal ya dago kai a hankali
idanunsa jajur dasu
kamar garwashim wuta "Ha
Hajiya zainab me ya dawo
dake kuma gurina." Hilal ya ce
bakinsa na rawa. Hajiya Zainab ta
dubeshi a tausashe ta ce.
"Kaunarka ce Hilal ta dawo dani
gareka Wallahi na kasa komai
saboda kai na je gida nemanka
shi ne Umminka ta ce dani kana
makaranta ba ka dawo ba" Hilal
ya katseta. "Amma...kin san na
fada miki bai kyautatu ba abin da
muke yi." "Hilal kada ka zalunci
kanka na
san kaima kana sona tashi muje
gida in fada maka maganin
matsalar mu ai komai yana da
magani" Kafin Hilal ya sami
damar musu Hajiya Zainab ta juya
ta nufi inda ta ajiye motarta.
Bazai iya rabuwa da ita ba ba
kuma zai iya jure kunan rai na
begenta ba don haka sai ya mike
ya bi ta
a baya da yan littattafansa a
hannu iskar yammacin na
karkada su kamar tutar
Najeriya****
Dakta Sadi ya yi tagumi fuskarsa
na ta faman naso kamar waina
Kusan sa'o'i biyu kenan suna ta
tattaunawa tsakaninsu da
likitocin daga karshe dai suka
yanke cewa a rufe maganar kada
a sake ta fito fili domin yin hakan
zai ceto sunan asibitin daga
sharrin yan jaridu. Don kuwa ba
karamin abin kunya ba ne ace a
fitaccen asibiti kamar wannan
ace wai likita ya manta almakashi
a cikin majinyaci kuma wai har
hakan ta yi sanadiyyar mutuwar
majinyacin Wasu daga cikin
daktocin dake gurin asirtaccen
taron sun so a fito da maganar
fili musamman ma Amburus an yi
kiyasin cewa Dakta Sadi yayiwa
majinyata
sama da dari tiyata a cikinsu
kuma ba a taba samun wanda ya
mutu ba yayin gudanar da aikin.
Hakan ce ta sa da yawa daga
cikin daktocin ke jin haushinsa
saboda ganin nasibin da Allah
yayi masa.
Sai wajen karfe shida da rabi na
yamma Dakta Sadi ya dawo gida
wujiga-wujiga kai kana ganinsa
ka san ya ji jiki.
Dakta Sadi ya shiga bandaki ya
watsa ruwa sannan ya fito ya
bude firjinsa ya dauko ragowar
rabin gasasshiyar kazar da ya
ajiye tun jiya ya zauna akan
kujera sannan ya yagi tsoka daya
ya kai bakinsa ga mamakinsa sai
ya ji naman babu dadi. Ya yi sauri
ya ajiye kazar akan farantin
tangaran sannan ya nufi firjin a
karo na biyu ya dauko tataccen
lemo a cikin kwalba ya tsiyaya ya
kai bakinsa ya hadiye da kyar ji
yake yi kamar yana hadiyar
ruwan allura. Dakta Sadi ya yi
ajiyar zuciya sannan ya jingina
bayansa a makarin kujera ya
kurawa bango ido kamar yadda
malamin kimiyya kan kalli
sabuwar kwayar halittar da bai
san da ita ba a da. "Zainab" Ya ce
a sanyaye kai kace daman a
dakin take zaune kusa dashi. Ba
zan iya rabuwa da ita ba ya ce da
kansa.
"Kada ka sake na kara ganin
mummunar fuskarka a gidan
nan" Ya tuna bakaken
magagannun da ta ta jifansa
dasu. Dakta Sadi ya sake tashi
tsaye ya nufi tagar dakin ya leka
waje
sannan ya dawo dakin ya kunna
talabijin. Wata mata inyamira ce
ke tikar rawa kusan tsirara daga
ita sai dan kamfai wagagen
bakinta a washe tana ta ihu ita a
tunaninta wai waka take yi.
Dakta Sadi ya yi tsaki ya kashe
talabijin din sannan ya maida
kayan jikinsa yasa takalminsa
cikin sauri ya nufi kofar gida.
"Babu abin da zai rabani da ita,
wallahi idan na yi wasa kaunarta
kashe ni za ta yi ko dai ban mutu
ba to tunaninta zai bata min
kyakkyawan aikina na kwararren
likita gara in je in baiwa zuciyata
magani" Dakta Sadi ne ke fadin
hakan cikin zuciyarsa. Ya shiga
motarsa kirar honda cikin
gaggawa ya nufi gidan Hajiya
Zainab a lokacin karfe bakwai da
rabi na yamma. Ya kudurce a
ransa cewa dole ne ma ya shawo
kanta ko ta halin kaka domin
idan har ya kasa shawo kanta to
shi rayuwarsa bata da wani
amfani tuni fa har ya kashe rai
guda sakamakon tunaninta. To
wa ya san kuma me gobe zata
haifar ?
BINDIGAR KWALI--> 8
.
Tuni fa har ya kashe rai guda
sakamakon tunaninta. To waya
san kuma me gobe zata
haifar ???
A daidai lokacin da duk wannan
ke faruwa a can filin saukar jirgin
sama na Malam Aminu
Kano jirgin misara ne (Egypt) ke
kokarin sauka. Tun kafin ya gama
samun gurin
tsayawa motocin agaji na
hukumar kashe gobara da kuma
motar nan mai dakon tsani suka
nufi inda jirgin yake.
Ba'a dade ba sai fashinjojin dake
saukowa Larabawa ne da kuma
bakake yan kasuwa, miliniyoyi.
Daga cikinsu kuwa har da ALHAJI
HAMISU JUMARE.
Alhaji Hamisu Jumare dogo ne
kakkaura garsakeken kato baki,
amma fuskarsa tana da kyawun
gani kuma da yawa daga cikin
mutane basa ganin bakinsa
saboda irin nairorinsa. Alhaji
Hamisu ya biyo jerin gwanon
mutanen yana tunane-tunane.
Sau hudu kenan yana bugo waya
gida domin ya sanar da Hajiya
Zainab cewa karfe bakwai da
rabi na dare zasu sauka amma
ga mamakinsa babu amsa. Me
yiyuwa yawace-yawacen nata na
banza ta fita. Ya ce cikin
Zuciyarsa me yiyuwa kuma
matsalolin da iska ta saba
kawowa ne akan injinonin
sadarwa na Najeriya ya kawo
haka me yiyuwa ma talfon din
gidan ne ya lalace.
Mintuna biyar da saukowarsa
wata katuwar marsandi baka
taja birki agabansa kamar an
jefota. Alhaji Hamisu Jumare ya
dubi
motar cikin mamaki sannan ne to
kofar motar ta bude, wani
kurtun dansanda ya fito ya sara
masa sannan kuma sai daya
kofar ta bude. Nan da nan fuskar
Alhaji Hamisu
Jumare ta washe Cikin fara'a.
"A'a kwamishina Mahmud yau da
kai kuma Allah ya fara hadani
daga shigowa kasar ?"
Kwamishinan yansanda
Mahmudu Sidiri ya mikawa Alhaji
Hamisu hannu suka gaisa sannan
ya ce. "Alhajin Allah kwana biyu
rabonka da kasarmu" "Wallahi
kuwa ka ga sai yanzu
Allah ya dawo dani gashi ma
kuma ko tarbata ba a zo ba, na
buga waya har sau biyar gidan
amma babu amsa"
"Af, to shigo mana ai sai mu kai
ka gida"
Tun suna firamare har zuwa
sakandare suke tare, kaddara ce
irin ta rayuwa ta rabasu, daya ya
zama kwamishinan yan sanda
daya kuma fitaccen dan kasuwa.
Kwamishinan yansanda mahmud
ya dubi Alhaji Hamisu ya ce. "A
gaskiya lokaci yayi da
yakamata ka rinka tafiye-tafiyen
ka da kyakkyawar matar nan
taka, kada fa ka bari mu yi ma
fashi idan baka nan"
Mutanen biyu suka bushe da
dariya. Alhaji Hamisu yakai masa
zunguri ya ce.
"Har yanzu dai kana nan da
tsokanar nan taka kamar
zamanin makaranta, in ban da
abinka wane ne zai yi min fashin
Zainab dita, bayan na san duk
duniya ba ta da abin so da ya
wuce ni..." suka sake fashewa da
dariya. A can gaban motar da
suke ciki, baburan yan sanda ne
wajan guda shida suna ta faman
gudu gamida jiniya domin a
samarwa da kwamishina hanya.
Kwamishinan yansandan ya dubi
Alhaji Hamisu ya ce "kana da
labarin wata mata da yan fashi
suka kashe jiya, na ga an buga a
mujallu da jaridu". Alhaji Hamisu
ya girgiza kai cikin jimami ya ce.
"Kisa! Tab, wato Najeriya ma ta
fara baci da munanan dabi'un
kashe-kashen al'ummar nan
kamar a Amurka."****
Duk cutar da Allah ya halitta sai
da ya halicci maganinta, in kuwa
haka ne to ni na samo maganin
tamu cutar." Hajiya Zainab ta ce
tana duban Hilal.
Hilal ya dubi tangamemen dakin
shakatawar wanda wannan ita
ce shigarsa ta biyu sannan ya
dawo da idanunsa kan fuskar
zainab yana yi mata kallon rashin
fahimta.
"Wanne magani kike dashi ke da
kike matar aure kuma kike
kokarin yin soyayya da wani ?"
Hajiya Zainab ta girgiza kanta
cikin damuwa "Wani lokacin idan
kana magana wallahi kamar baka
sona Hilal." Kamanninsa suka
sauya.
"Ba haka bane Zainab ai ke kanki
ki dubi idanuna, can cikin kwayar
idanuna za ki hango sunanki a
rubuce a ciki." Hajiya Zainab ta
saki wani tattausan murmushi na
farin ciki sannan ta tashi daga
inda take ta zo kusa da shi ta
zauna, ta dubi inda Zuhuriyya ke
kwance ta ga tuni ta yi nisa a
cikin barcin da take.
"Hilal kasan da ana sayen mutum
da kudi, to da ko nawa ne in dai
har ina dashi kuma in za ka sayu
din zan bayar na sayeka, koda
kuwa hakan na nufin na bada
raina ne. Duk da yake dai
Hausawa sun ce wai ina amfanin
badi babu rai, to amman gara dai
na mutu saboda kai." Ta dan yi
shiru tana mayar da numfashi
sannan ta ci gaba da cewa.
"Ka ga dai gidan nan ban rasa ci
ba, ban rasa sha ba, a cikin arziki
muke ni da yata Zuhuriyya domin
babanta miloniya ne, haka nan
kuma duk abinda nake so na
rayuwar duniya Allah ya hore
mana, amma za ka yi mamaki
idan na ce da kai duk wannan
banzane a gurina."
"Dan me za ki fadi haka Zainab,
kada fa so ya saki fita daga
hankalinki, shin yanzu a rayuwar
mu ta yau har akwai wani
mutum da zai iya bude baki ya ce
da kudi banza."
"Kwarai kuwa gani nan." Hajiya
Zainab ta amsa masa. Kudi da
daular gidan nan basu bane a
gabana, ni so da kauna
ne a gabana." Ta dan yi shiru
sannan sai ta dubi Hilal ido da
ido ta ce.
"Hilal, na rasa kaunar mijina
domin bai damu da ni ba, yanzu
ka duba dai yau rabonsa da gida
ya fi wata biyar kuma koda yana
gida ma bashi da wani cikakken
lokacina harkokinsa kawai ya sa
a gaba yana zama ne dai kawai a
matsayinsa na fitaccen mai kudi
wanda ke mallakar kyakkyawar
mace..." Ta share hawaye.
"Ban san darajar so ba Hilal sai
da na hadu da kai na gane cewa
ashe so da kulawa sun fi komai
rayuwar ya mace. Hilal ni dabara
ta ko kuma in ce maganin
matsalar mu da nake tunani bai
wuce kawai idan maigidana yazo
ba in yi masa bayanin na gaji
dashi ya fadi duk abin da ya
kashe na biya shi tun da dai nima
iyayena ba talakawa bane ?"
"Me ki ke nufi ?" Hilal ya tambaya
cikin kaduwa. "Abin da nake nufi
shi ne zan
nemi ya sakeni da sharadin zan
biya shi duk abin da ya kashe
lokacin aurena ko kuma in auro
masa wata matar domin ni Hilal
kai nake so kai nake bege da
kauna bana jin kuma zan iya
zama da wani da namiji a doron
kasa idan ba kai ba."
"Kan ki daya kuwa Zainab ?" Hilal
ya tambaya a rude.
"Tabbas kaina daya Hilal in kuwa
baka yarda ba to bari in
tambayeka. Shin ka taba ganin
mutum da kai biyu ?"****
Masoyan biyu masu makauniyar
soyayya suka yi shiru na tsawon
lokaci suna duban juna, sannan
sai Hilal ya nisa gami da ajiyar
zuciya ya ce.
"Kina ganin yanzu za ki iya
rabuwa da duk daular dake
gidan nan domin kawai ki zauna
dani?"
Hajiya Zainab ta tabe baki ta
dubeshi da fararen idanuwanta.
"Hilal ka fi komai a gareni, ka
tuna fa ni na ce ma zan iya bada
raina ma saboda kai, to ina kuma
ga dukiya kazantar duniya kai
bari ma ka gani mu kulla
alkawari."
Kafin Hilal ya farga tuni Hajiya
Zainab tayi caraf ta rike
hannunsa ta zare wani
kyakkyawan zobe na lu'u-lu'u
dake dauke idanu ta sanya masa
a hannu.
Ta dubeshi ta yi murmushi.
"A wajen mahaifiyata na yi
gadonsu, ka ga dayan can a
hannun Zuhuriyya." Ta nuna
Zuhuriyya da dan yatsa.
"Ka rike shi da kyau, domin
zabon alkawari ne, dan
mahaifiyata da za ta bani shi sai
da ta ce dani mahaifina ne ya
bata shi a zamanin soyayyarsu, ta
ce dani kuma kada na bada shi
ga kowa sai wanda na ji ina
kauna fiye da komai a duniya."
Hajiya Zainab ta yi murmushi
sannan ta dada da cewa. "Hilal
kaine ka cancanci abin da
mahaifiyata ta ce shi yasa na
baka shi." A daidai lokacin ne to
ta kyalla ido ta hango zoben da
shima yake sanye dashi, to sai
dai kuma nasa na azurfa ne.****
"Kaima bani naka zoben." Zainab
ta tambaya. Hilal ya gama rudewa
da irin wannan so da wannan
matar aure ke yi masa, ya yi
kokarin ya cire zoben nasa amma
abin yaci tura, zoben ya rike dan
yatsansa gam-gam.
"A'a bari kada ka ji rauni, tashi na
nuna maka (toilet) ka shiga ciki
akwai SABULU idan ka shafa nan
da nan zoben zai fita."
"Kwarai...kuwa" Hilal ya ce
muryarsa na rawa, ya bita a baya
ta kai shi har can kuryar ginin
gidan inda bandakin yake ta ce
dashi cikin murmushi.
"Idan ka cire sai ka sameni a falo,
nima so nake ka sa min kamar
yadda na sa maka nawa zoben."
A daidai lokacin da ta dawo
dakin shakatwar ne to ta ga abin
da ya sa hantar cikinta kadawa.
A zaune a cikin daya daga cikin
kujerun alfarmar da ke falon,
yana kifkifta idanu kamar dillalin
rakuma DAKTA SADI NE.
"Zai...nab" ya ce bakinsa na rawa
kamar wanda ke shirin hawa
bori.****
Bakin cikin sake ganinsa ya
shake Hajiya Zainab kamar ta
fashe.
"Shin ban ce da kai ka rabu dani
bane!" Hajiya Zainab ta ce cikin
karaji.
"Ba zan iya rabuwa da ke bane
Zainab, ban san abin da kika yi
min ba Zainab, domin ji nake yi
idan na rasa ki rayuwata ta zo
karshe kenan."
Idan kuwa hakane, to ina
tabbatar maka da cewa kai kam
an busa kahon tashin
alkiyamarka, domin bani
kaunarka, ban son ganinka, kai
bana fatan ma na sake ganin
wanda ma ya ganka tashi kuma
ka fice min daga gida tun da ba
gidan ubanka bane."
Wani abu ya zo ya tokare masa
makogoro.....
BINDIGAR KWALI--> 9
.
Ka fice min daga gida tun da ba
gidan ubanka bane."
Wani abu ya zo ya tokare masa
makogoro.
"Dan Allah Zainab ki yafe ni,
Wallahi ba zan taba iya daina
kaunarki ba...kin ji Zainab don
Allah ki yi hakuri, duk zancen
kudin nan ma da na ce ki bani ni
na fasa bana son ko kwabo ke
kawai nake bukata". Hajiya
Zainab ta dubi hanyar bandakin a
tsorace, bata son Hilal ya tarar da
Dakta Sadi a cikin dakin nan.
"Na ce da kai ka tashi ka fita wai
shin kai wanne irin tsohon maye
ne? Ka ga fa wallahi in ba ka fita
ba zan sake ruguza maka kwalba
aka irin ta ran nan, nan da nan
sai Zainab ta dauki kwalbar
lemon (Tree Top) ta nufi inda
yake zaune yana zubar da
hawaye. Ga mamakinta sai ta ga
ko gezau bai yi ba.
"Zainab, wallahi sai dai ki
kasheni, amma ni ban daina
sonki, in baki sani ba bari in fada
miki tuni na yi babban kuskuren
da ban taba yin sa ba saboda ke,
tiyatar da na yi jiya a asibitin
mijinki na manta da almkusa
guda biyu a cikin mutamin ya
mutu duk dan saboda wannan
ko..." Zainab ta katse shi ta ce.
"Wannan matsalarka ce ni babu
abin da ya shafeni tashi ka fice
na ce da kai." Ta yi shiru tana
waigen hanyar da Hilal zai bullo
can sai ta ga kamar motsi, nan da
nan sai ta daga kwalbar lemon
(Tree Top) din dake hannunta ta
ce da Dakta Sadi cikin karaji.
"Fice maye!" Dakta Sadi ya gane
abin da take gudu, ya kuma gane
cewa ba ita kadai ba ce a cikin
gidan. Kishi da bakin ciki mai
tsananin gaske suka tokare kirjin
Dakta Sadi, hankalinsa ya
fugunzuma ransa ya baci,
idanunsa suka yi jajur da su
kamar danjar mota. Da kyar yake
numfashi kamar kumurcin maciji.
Bai yi aune ba sai ya ji Zainab ta
ruguza masa kwalbar a tsakiyar
ka, kwalbar ta tarwatse, jini ya yi
tsartuwa daga kan Dakta
Sadi.**********
**************
"Fice na ce, ko na kara maka."
Zainab ta ce cikin karaji sauran
tsinin kwalbar rike ahannunta.
Dakta Sadi ya mike cikin fushi
tuni jini ya gama wanke fuskarsa.
"Daga yau...ba zaki sake dukan
wani ba, shegiya karuwar gida."
Dakta Sadi ya ce cikin fushi, nan
da nan ya nufi Hajiya Zainab da
gudu. Tun kafin ya karaso Zainab
ta kwalla ihu cikin firgita, domin
ganin kwayar idanunsa ma
kawai sun isa su nuna mata
cewa kwanakinta sun zo karshe
a duniya. Dakta Sadi ya kama
hannunta mai dauke da tsinin
kwalbar ba tausayi ba imani sai
kawai ya burma tsinin kwalbar a
ruwan cikinta, Zainab ta fadi,
gami da kara mai tsanani, daga
nan kuma bata sake ko da
shurawa ba, abu na karshe da ya
darsu a zuciyarta shi ne tunanin
masoyinta Hilal. Hilal ya rugo da
gudu daga
bandakin cikin firgici, yana zuwa
sai suka yi ido biyu da Dakta Sadi
cikin jini, sannan ya dubi Zainab
kwance itama cikin jini.
"Zainab...ah wayo Zainab!" Hilal ya
fashe da kuka cikin razana
sannan ya durkusa yana
jujjuyata.
A haka Dakta Sadi ya zurare abin
sa ya bar gidan. Hilal ya mike
tsaye yana kuka hannuwansa
akan kirjin Zainab. Tabbas ta
mutu ko shakka babu, yanzu kam
ta tabbata zamansa a kano ya zo
karshe, shi da kano kam sai
abinda hali ya yi, ya mike tsaye
yana kuka ya nufo kan kujera
inda Zuhuriyya ke kwance tana
barci abinta. Hilal ya shafi
fuskarta, sannan yacire zoben da
a da ya yi niyyar ya sawa uwarta
sai ya kama hannun ZUHURIYYA
ya sa mata zoben. Tun hawaye
na zuba a idanunsa
har hawayen ya kafe. A daidai
lokacin ne to ya ji kamar sautin
jiniyar yansanda ta nufo gidan.
Nan da nan ya dawo cikin
hayyacinsa, domin ya san idan
aka sameshi agidan ko shakka
ba ya yi ya gama yawo, domin
babu wanda zai yarda ba shi ya
kashe Zainab ba. Hilal ya durkusa
a gaban Zainab ya yi mata duban
karshe sannan ya ce.
"Allah ya gafarta miki Zainab ba
zan manta dake ba har iya
rayuwata" ya mike tsaye ya sake
komawa in da Zuhuriyya take
barci ya dauki bindigar robarta
ya jefa a aljihu, sannan sai ya
shafi fuskarta.
"Sai wata rana Zuhuriyya
Zainab...Zainb sai wata rana" ya
fice daga dakin cikin sauri, ko da
ya kai kofar gidan sai ya ji sautin
jiniyar ya fara matsowa kusa da
kofar gidan
.
Nan da nan ya kara sauri ya fice
daga gidan yana mai godiya ga
Allah da ya sa Hajiya Zainab ta
kori duk masu gadi da hadiman
gidan ko da ya hau kan titi ya
fara tafiya sai ya ga bakaken
motoci fijo-fijo guda uku da
marsandi daya sun tsaya a kofar
gidan. Hilal ya kara sauri har
yanzu
hawaye bai daina zuba akan
fuskarsa ba. Ko da ya fara nisa da
gidan sai ya taba bindigar robar
dake aljihunsa da danyatsa.
KARSHEN LITTAFI NA DAYA 1
LITTAFI NA BIYU 2
A zaune yake yana ta mafarki da
wata kyakkyawar budurwa wai
tana tsaye a gabansa tana yi
masa murmushi wani
kyakkyawan kofin azurfa a
hannunta tana kokarin sa masa
kofin a baki.
"Ba zan sha ba" ya ce da ita a
cikin mafarkin
"Saboda me?" Budurwar ta
tambayeshi cikin tsananin
mamaki
"Saboda ban sanki ba ban kuma
taba ganin ki ba." Budurwar ta
zabura a firgice har kofin dake
hannunta ya girgiza wani abu
kamar nono ya fantsala daga
cikin kofin.
"Lallai ka bani mamaki wallahi
ban taba tsammanin za ka manta
da ni ba ashe yanzu har akwai
wani zamani da zai zo masoyi ya
manta da masoyiya?" Tana gama
fadin haka sai budurwar ta taba
shi a kafada ta ce
"Shi kenan tunda ka ce baka
sanni ba." Budurwar ta juya a
hankali ranta a bace ta bar shi
anan tsaye A daidai lokacin da ya
bude baki zai yi kiranta ne ya ji
an girgiza kafadarsa a tausashe
Hilal ya farka daga nannauyan
barcin a rude sannan ya dubi
fasinjojin dake cikin jirgin yana
kokarin hangen kyakkyawar
budurwar a cikin fasinjojin
"Ya kamata ka sassauta bel din
ka dan mun riga mun zo."
Kakkauran mutumin mai sanye
da shudiyar kwat ya ce dashi tuni
har ya cire nasa bel din. Hilal
ya yi doguwar mika akan kujerar
jirgin gami da hamma sannan ya
dubu mutumin da tattausan
murmushi ya ce.
"Wallahi wani nannauyan barci
ne ya daukeni har da mafarki."
"Ina fatan dai mafarkin naka na
alheri ne?" Mutumin ya
tambayeshi. Hilal ya yi shiru yana
gajeran tunani domin shi kansa
bai san ma'anar mafarkin da yayi
ba. "Eh, to na alkairi ne mana tun
da dai na yi ido biyu da wata
kyakkyawar fuska tana yi min
murmushi." Mutumin ya fashe da
dariya, sannan ya kama hannun
Hilal ya ce.
"Zo mu tafi an fara fita." Hilal ya ji
gabansa ya fadi sa'ar da ya fara
gangarowa daga matattakalar
jirgin, idanunsa na ta shawagi a
farfajiyar filin saukar jirgin
saman. Abu biyu ne suka cafki
zuciyarsa a lokacin bakin ciki da
kuma doki. Hilal yana doki ne
domin rabonsa da kano yau
shekaru ashirin da daya kenan.
Tun daga ganin tsarin filin
saukar jirgin saman jikinsa ya
bashi cewa ko kusa ko alama
wannan bata yi kama da kanon
da ya sani a da can ba. Ya yi
mamakin yadda zai ga garin
kano a halin yanzu. Sannu a
hankali har suka kawo izuwa
farfajiyar filin saukar jirgin
saman sannan suka bi ta cikin
dakin tarbar baki suka fice izuwa
farfajiyar bayan gine-ginen filin.
Har yanzu Hilal tafiya yake yana ta
kalle-kalle kamar sauna to sai dai
shi kallonsa ba na kauyanci bane
kallo ne na ya dade rabonsa da
KANON DABO.**********
*************
Hilal ya ci gaba da tafiya janye da
wasu tika-tikan akwatuna guda
biyu yayin da wani jibgegen
saurayi ke biye dashi janye da
wasu akwatuna shudaye guda
biyu. A daidai lokacin da suka
kawo dab da inda jerin gwanon
motocin hayar dake filin saukar
jirgin saman ne Hilal ya hangi
wasu matasan ma'aurata guda
biyu, suna tafe da yar karamar
yarinyarsu a rike a hannun mijin
cikin fara'a da farin ciki.
"Lah! Baba dubi jirgi kamar zai
fado." yarinyar ta ce cikin karaji.
Uwar ta fashe da dariya sannan
ta ce da yarinyar "Da Allah rufe
bakinki shashasha yar kauye".
"A'a rabu da ita ta kalli abinta,
kema ba yar kauyan bace, wa ya
san ma abin da za ki yi da ke ce
ita." uban ne ya ce da uwar cikin
murmushi sannan sai ya dada
janyo yarinyar kusa da shi ya ce.
"Zo mu bi ta can na saya miki
jirgin roba."
Hilal ya lura da duk abin da ke
faruwa, hakan shi ya sa zuciyarsa
kuna sannan wani irin kadaici da
bai taba jin irinsa a duniya ba ya
lullubeshi. A yanzu kam ya san
duk fadin kano in ka dauke
mahaifansa bashi da kowa sai
mutum daya, mutum daya din da
shi kansa a yanzu bai san halin
da take ciki ba. Ganin wannan
yarinya shi ya tuna masa da ita,
domin a lokacin da ya bar ta ba
tafi wannan yarinyar ba. Hilal ya
share gumi, a daidai lokacin da
aka fara sa akwatinansa a bayan
motar.
"Na gode fa." Hilal ya ce da
jibgegen saurayin da ya rako shi
da jakankunansa guda biyu, kana
ya lalubi aljihunsa ya tsamo wasu
adadi na takardun masu gidan
rana ya mika masa. Saurayin ya
karbi kudin cikin sauri har da
dan rankwafawa.
"Kudi masu sa kato ladabi." Hilal
ya ce cikin zuciyarsa, sannan sai
ya bude bayan motar ya shiga,
direban ya tuka motar suka nufi
cikin birnin kano.
Koda suka fara tafiya sai Hilal ya
sauke gilashin motar domin ya
sami damar ganin irin sauyin da
aka samu a birnin kano
BAYAN TAFIYARSA BABU SHIRI
BINDIGAR KWALI--> 10
.
Koda suka fara tafiya sai

Please Login or Register in order to submit comment