Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne to wata dabara ta
fado masa.
"Sannu abokina." Hilal ya ce da
yaron sa'ar da ya kawo dab
dashi. Yaron ya tsaya a daidai
tagar motar yayin da karensa
ma ya tsaya yana sunsuna jikin
motar. "Sannu da zuwa...ina
wuni."
Yaron ya ce cikin zazzakar murya.
Hilal ya lura da cewa
yaron kamshin alewar cakulan
ya ke yi. "Lafiya lau abokina." Hilal
ya
amsa sannan sai ya dubi yaron
ya ce "Dan Allah abokina, ko ka
san wata...ah anan layin ana ce
mata Zuhuriyya?"
Yaron ya dubi Hilal ido-da-ido ya
ce "Ni ma yayata sunanta
Zuhuriyya."
Hilal ya ji zuciyarsa ta harba
tsakanin hakarkarinsa.
"Uhm...ita yayar taka babba ce ?"
Yaron ya gyada kai cikin sauri ya
ce "Kwanan nan za a yi aurenta
ma."
Hilal ya dan yi jim,
kwakwalwarsa na ta tunanin
gaggawa, wannan al'amarin
caca ne, bari kawai na yanki
cacar me yiyuwa a dace. "Idan
ka kirawo min yayar taka za ta
zo?"
yaron ya karkata da kai gefe
guda sannan ya shafi bayan
karensa ya ce "Uhm to, bari in je
na kirawo ma ita, in ta ga dama
tana iya zuwa." yana gama fadin
haka sai ya juya da baya ya nufi
cikin gidan da ya fito karensa na
bin sa a baya. Hilal ya ji yawun
bakinsa ya
kafe...tabbasa in dai har ba
kuskure ya yi ba gidan da yaron
ya shiga bangarensu daya da
inda gidan marigayiya zainab
yake a wancan lokacin. To ko ma
dai mene ne, shi dai ya aika a
kirawo ta.
Hilal ya lumshe idanunsa gabansa
na faduwa, zuciyarsa
na ta sassaka abin da zai ce da
ita idan tafito. Tsawon mintuna
goma yana nan zaune cikin
motar, a zuciyarsa yana cewa.
Me yiyuwa ma ba zata fito ba.
Sannan ne to ya ji motsin an
bude kofa. Yaron ya ruga a guje
shi kadai babu karensa, ya zo
inda Hilal yake, ya leka ta tagar
motar ya ce.
"Wai ta ce ka karasa kofar gida."
jikinsa na rawa, kafafunsa sun
koma kamar na roba sun yi
rauni, a haka Hilal ya bude kofar
motar sannan ya ce da yaron
"Muje ko"
Yaron na gaba Hilal na bin sa a
baya har suka kai daidai katuwar
kofar launin toka-toka. Tun daga
kofar Hilal ya ji wani tattausan
kamshi ya bugi hancinsa sannan
ba tare da tsammata ba sai kofar
ta bude sannan kyakkyawar
surar ta fito.
Hilal ya dafe kirji a firgice da abin
da ya gani numfashinsa ya
dauke, yawun bakinsa ya kafe. A
tsaye a kofar gidan, sanye da riga
da siket matsattsu, na wani
irin yadi mai santsi mai launi jaja-
jaja, kafafunta sanye cikin farin
takalmi, wani dan siririn gyale
mai kamar rawani a saman
gashin kanta me shiki a cikin
hasken fitulun kofar gidan
Kyakkyawan bakinta shan zuciya
na taunar cingam tana
dubansa a gatsine.....
.
Marigayiya Hajiya Zainab Hilal yake gani. Na
shiga Uku. tun da nake ban taba
ganin fatalwa ba a zahiri sai yau.
Hilal ya ce cikin wata murya
shakakkiya shin ko daman bata
mutu ba? Sannan sai ya dubeta
a rude ya ce bakinsa na kyarma.
"Zainab..."
Budurwar ta dubeshi cikin
mamaki sannan ta ce dashi cikin
wata murya mai taushin gaske.
"Rufa min asiri bawan
Allah...Zainab sunan mahaifiyata
ne, ni sunana ZUHURIYYA!."
kusan mintuna uku suka yi tsaye
suna kallon juna. Budurwar na
cewa cikin zuciyarta. Wannan
kyakkyawan mutumin kuwa
kansa daya? Ko shakka ba ta yi
mutumin dake tsaye a gabanta
kyakkyawa ne na hakika haka
nan akwai wani abu a tattare da
mutumin da ta ji tana so, ita
kanta ba ta san komene ne ba.
Hilal, na tsaye yana dubanta sama
da kasa, tabbas babu maraba ita
da
marigayiya Zainab, to sai da sa'ar
da kaduwar ta dan sake shi ya
lura
shekarunta a yanzu basu kai
shekarun marigayiya Zainab ba a
wancan
lokacin. Ko shakka ba ya yi
wannan budurwar dake tsaye
agabansa yar yarinya Zuhuriyya
ce da
ya bari kwance tana barci sa'ar
da
aka kashe mahaifiyarta Zainab.
"Malam kai nake sauraro ka sa an
yi kirana
kuma ka yi shiru." Hilal ya yi
firgigit. Tattausar muryarta ita ta
dawo da shi cikin hayyacinsa.
"Ki gafarce ni ranki ya dade." Hilal
yace gami da haske ta da
faffadan
murmushi lokaci guda kuma
zuciyarsa na
dawurwuri tana nemo masa abin
da ya kamata ya fada mata.
"Shiga gida Shafi'u...yanzu nima
zan taho." Zuhuriyya ta ce da
yaron
da ya cewa Hilal shi kanenta ne.
Cikin sauri Hilal ya dubi yaron
"Abokina tafiya za kayi...na gode
to."
Ina ma ace ina da daddadar
cakulan
da na bashi. Hilal ya ce cikin
zuciyarsa.
Yaron ya wuce cikin gida karensa
na
bin sa a baya kamar inuwa.
"Uhm hum ina sauraronka."
Zuhuriyya ta ce dashi. Irin
muryarsu
daya da mahaifiyarta sai dai tata
ta
dan fi taushi kadan. Hilal ya gyara
tsayuwa.
"Ah, kin san dai yadda al'amarin
Allah ya ke...ran nan ne zan wuce
na
hange
ki...shi ne to na ga ya kamata na
tsaya
mu dan gaisa."
Zuhuriyya ta jingina da jikin kofar
kanta a
sunkuye ta tsuke baki ta ce.
"To ai mun gaisa din ko, na iya
tafiya..."
Hilal ya ji kirjinsa ya buga "Eh, to
abin
ya wuce da haka Zuhuriyya...dom
in na
ji a raina ina kaunarki." Ya dan yi
shiru yana duban yanayin
fuskarta
sannan sai ya dada da cewa.
"Allah sa dai abin da na fada ba
zai
sosa miki zuciya ba." Ga
mamakinsa
sai ya ga ta girgiza kai da
murmushi. "Ya
ya mutumin da ya ce yana
kaunarka zai yi laifi, ni ko kadan
baka
yi min laifi ba, sai dai kawai ina
fargabar ka zo a makare."
Hilal ya dubeta ido da ido "Me
kike
nufi da na zo a makare?" "Ina
nufin an yi
min miji domin nan da
kwana bakwai za a yi mana
baiko
dashi."
Abin da ta ce bai zo masa a
bazata ba,
tun da daman kanenta ya ce
dashi an
kusa aurenta. "Lallai na fi kowa
rashin
sa'a aduniya." Hilal ya ce yana
duban
fuskarta me sheki. Da kyar yake
iya
hadiyar yawu domin gani yake yi
kamar da marigayiya zainab suke
tsaye, to sai dai ko kusa ko alama
wannan
budurwar dake tsaye agabansa
bata nuna alamun tama
gane shi ba.
"Me ya sa ka ce haka?
"Saboda na rasa kyakkyawa
kamar
ki." Hakan da ya ce shi ya sa ta
dubansa
da wani faffadan murmushi.
"Kada ka damu kaima Allah zai
baka
wacce ta fi ni."
"To Allah ya sa." Hilal ya ce yana
duban zoben dake dan yatsanta
ko
shakka ba ya yi zobensa ne da ya
sa mata
a daren da aka kashe
mahaifiyarta.
"Ni zan tafi ka ga dare ya fara."
"To amma kafin ki tafi zan so ki yi
min
wata alfarma daya."
Zuhuriyya ta dubeshi ta ce "Wace
alfarma
kuma, na fada maka na riga
na zabi mijin aurena."
"Na ji, na kuma fahimce ki, amma
idan babu damuwa zan ringa
zuwa
lokaci-lokaci muna dan
gaisawa...a
matsayina na dan uwanki."
Zuhuriyya ta
danyi shiru. Ta san cewa
idan ta sake mijin da zai aureta
ya
gansu tare ransa ba karamin baci
zai
yi ba, to sai dai kuma akwai wani
abu
mai karfin gaske, wani abu mai
kama
da mayen karfe tattare da
kyakkyawan
mutumin, wanda ke
fizgarta, ta ji kuma tana son ta
sake
ganinsa takuma sake jin wannan
daddadar murya. Zuhuriyya ta yi
mamakin jin yadda hankalinta ya
kwanta da mutumin don ji take
yi kamar
ta dade da saninsa.
"Ba komai...dan dai gaisuwa kana
iya
zuwa idan ka sami lokaci."
Zuhuriyya
ta ce dashi.
"Godiya nake ranki ya dade."
"Ni ke da godiya, da ka taso ka zo
har
gurina." Zuhuriyya ta ce, sannan
ga
mamakinsa sai yaga ta bar jikin
kofar gidan da ta ke jingine ta
fito
waje sosai.
Ganin haka sai ya dauki haske, ya
juya ya nufi inda motarsa take.
Zuhuriyya ba biye da shi a baya.
Ko da
suka je daidai da inda motar take
sai
ya bude motar sannan ya dubi
zoben dake hannunta ya ce.
"INA SON ZOBEBINDIGAR KWALI--> 17
.
Ya bude motar sannan ya dubi
zoben dake hannunta ya ce
"INA SON ZOBEN NAN DAKE
HANNUN KI WALLAHI"
Zuhuriyya ta dubi zoben cikin
murmushi ta ce "Allah ko?
Tsohon
zobene nima nake ta fama
dashi."
Hilal ya yi kamar ya tambayeta
inda ta
sami zoben sai dai ya sauya
shawara.
"To Allah ya kiyaye. ni na tafi." Ta
juya
tana rausaya ta nufi kofar gidan
sannan ta tsaya tana hangensa.
Hilal ya tashi motar ya fara
tukawa
sannan ne to ya hangeta ta cikin
madubi tana daga masa hannu.
Koda Hilal ya fara tafiya sai ya yi
ajiyar
zuciya. Bai yi mamakin rashin
gane shi da Zuhuriyya ta yi ba
domin yasan
shekaru ashirin da daya sun yi
yawan
da za ta iya manta Hilal dinta. To
amma
duk da haka ya lura akwai wani
boyayyen abu da ke janyo su
yana kokarin
hadasu. Hilal ya yi tsaki sa'ar da
ya tuna da cewa kusan zuwan
banza ya yi domin bai ko kama
hanyar da zai bi ya nemi
azzalumin da
ya kashe mahaifiyarta
ba.************ ****
.
Washegari da safe misalin karfe
goma
sha daya, Rukayya da Hilal suka
isa
gidan cikin marsandin Rukayya.
Rabon Hilal da gidan tun wata
rana da
suka zo da yan ajinsu gaba daya
domin su yiwa mahaifiyar
Rukayya ta'aziyar wani karamin
kanin
Rukayya da ya rasu.
Aka shiga da Hilal wani katon
dakin shakatawa.
"Zauna anan na kirawo maka ita
ku gaisa." Rukayya ta ce cikin
murmushi. Hilal ya gyada mata
kai. "Ya ya na ga duk kana gumi
kamar ka hadiyi kunama?"
Hilal ya dubeta da murmushi ya
ce "Ke fa ba kya rabuwa da
tsokana dan Allah je ki kirawota
din an gaya miki tsoro nake
ji...sai ka ce wani karamin yaro."
Tana rausaya ta shige zuwa cikin
gidan. Ba dade ba sai ga ta ita da
mahaifiyarta.
Bayan sun gaisa, sai Hilal ya lura
ashe itama kamar Zuhuriyya,
Rukayya kamar hoton
mahaifiyarta take. Suka yi yan
surutai a kunyace sannan Hilal ya
yi sallama da mahaifiyar Rukayya
suka fita.
Lokacin da Rukayya ta dawo
daga rakiyar Hilal ne to ta sami
mahaifiyarta zaune a falon tana
jiran dawowarta.
"Rukayya....wan nan kuma daga
ina kika samo shi?"
Rukayya ta sunkuyar da kai.
"Mama ba ki gane shi ba, shi ne
fa dan ajin nan namu da kike
ganin hotonsa kullum a gurina."
Mahaifiyarta ta dubeta cikin
mamaki ta ce A'a ha, iko sai Allah
saurayin da ake cewa ya mutu
shi ne kuma ya dawo?"
Rukayya ta gyada kai cikin farin
ciki sannan ta sunkuyar da kai ta
ce "Mama...kwanan nan zan yi
aure."
Wani zazzafan hawaye na farin
ciki ya subuce daga idanun
mahaifiyarta tata. Wannan ita ce
kalmar da a kullum kwanan
duniya take fatan ta fito daga
bakin diyarta Rukayya. "Shi din za
ki aura? Rukayya ta
gyada kai a kunyace.*******
****
Daga ita sai doguwar riga mai
shara-shara shudiya kanta babu
dankwali hakan shi ya bai wa
siraran gashin kanta masu tsayi
da sheki bajewa akan doron
matashin kan da take kwance.
Duk kusan minti guda sai ta yi
juyi, ta kasa barci kusan sa'o'i
uku kenan tana ta mutsu-mutsu
akan gadon kamar kifi a cikin
koma, da ta rufe idanunta sai ta
ganshi tsaye a kofar gidan yana
yi mata murmushi.
"Na shiga uku!" Ta ce da kanta
"Me ke damuna ne?" A daidai
lokacin ne agogon dake kan dan
teburin dake dab da gadon
Zuhuriyya ya dauki jiniya. Karfe
goma sha biyu na dare. Tun sa'ar
da mutumin ya bar
kofar gidan ba ta sake samun
sukuni a zuciyarta ba abin kamar
asiri haka kawai sai ta ji babu
abin da take so sai ta sake
ganinsa. Za ta so ace ya sake
dawowa, domin su yi ta hira tana
sauraron muryarsa tana
kuma kallon fuskarsa kyakkyawa.
Zuhuriyya ta zargi kanta da
wauta dan me za ta bar shi ya
tafi ko sunansa ba ta sani ba.
Abin da ke damun zuciyarta
shine, tun sa'ar da ta kalli
mutumin ta fara tunanin kamar
ta san shi, kamar sun taba
haduwa a wani
guri daban, to sai dai kuma har
ya tafi bata iya tunano inda ta
taba ganin nasa ba.
Zuhuriyya ta mike zaune akan
gadon, sannan ta janyo littafin
hoton dake daf da ita, ta bude
shafin da hoton mijin da zata
aura yake ta kura masa idanu, a
tunaninta wai ganin surar mijin
da zata aura na iya kawar mata
da tunanin mutumin. Ga
mamkinta sai ta ga kamar fuskar
mijin da take tunanin auren ta yi
mata tsufa sosai sannan ne to ta
tambayi kanta tambaya mai
tsada.
.
"WAI SHIN ME NA GANO AJIKIN
MUTUMIN NAN DA YAYI KUSAN
SA'A DA UBANA ?
KUDI ? AI MUNADA SHI
KYAU ? AI BASHIDA MA KYAUN..."
.
Tunaninta ya katse domin ta san
ganin mutumin dazu ne ya
munana mata mijin da zata aura.
Zuhuriyya ta rufe littafin hotunan,
ta dada kwanciya rub da ciki
akan gadon sannan ta fara bijiro
da surar mutumin cikin zuciyarta
tare da kokarin ta tuno inda ta
taba ganinsa. A haka barci ya
dauketa a cikin barcin ne to ta yi
mafarkin mahaifiyarta a ranar da
ake bikin zagayowar ranar
haihuwarta.**** ********
"Kada ka yaudari kanka Hilal,
bakin rijiya ba gurin wasan
makaho ba ne, wannan budurwa
ba ta dace da kai ba in ma ta
dace din ba wani damuwa ta yi
da kai ba gara ma ka cireta daga
cikin zuciyarka ka auri me
kaunarka tsawon shekaru
ashirin da daya gami da
kyautatawa mahaifiyarka."
Duk wannan dogon bayani
zuciyar Hilal ce ke yi masa cikin
wata boyayyiyar murya da shi
kadai ne ke iya jin ta. Fitowarsa
kenan daga wanka ba a dade ba
ya sanya doguwar riga launin
kasa tazarce ya dora hula irin
kayan sannan ya fesa turare
kana cikin sauri ya jefa kafarsa
cikin wani bakin takalmi na yan
birni mai daukar ido kamar
madubi ya nufi kofar gida inda
dankareriyar motarsa take. Cikin
sauri ya shigo, sannan ya tuka
motar ya fara tafiya yana duban
agogon cikin damuwa.
Kamata ya yi fa ace yanzu
gidansu Rukayya zani. Hilal ya
fadawa kansa. A daidai lokacin
da ya hau kan babban titi ya
karawa motar gudu.
Hilal ya gama yanke shawara a
zuciyarsa, tabbas Rukayya zai
aura to sai dai kuma abu biyu ne
ke damun zuciyarsa a yanzu. Na
farko dai shi ne ya riga ya dauki
alkawarin in dai mutumin nan da
ya kashe zainab yana raye sai ya
gano duk in da yake, to ga shi
kuma har yanzu nan bai sami ko
da hanya daya ba da take nuni
da inda zai bi ya gane mutumin.
...dan samari tashi ka fice daga
gidan nan tun kafin mijinta ya
rutsa da kai ni zan iya rufa maka
asiri a matsayina na abokin
mijinta...
Hilal ya tuna da kalaman
mutumin a ranar da ya kama shi
a gidan marigayiya Zainab
Wannan ita ce hujjar fitowar Hilal
a wannan lokaci domin in dai
har abokin mijin Zainab ne akwai
yiyuwar Zuhuriyya ta iya saninsa.
To sai dai kuma akwai abu na
biyu dake damun zuciyar Hilal, shi
ne Zuhuriyya. A daren jiya da kyar
ya runtsa, domin da ya rufe
idanunsa sai ya ga fuskarta,
tunaninta ya fara yawaita a
zuciyarsa.
Hilal baya farin ciki da haka
domin ya riga ya yankewa
zuciyarsa cewa ba shi da wata
matar aure sai Rukayya.
"Hajiya Zainab ita nake so ta riga
ta mutu..." Hilal ya fadawa kansa
"Zuhuriyya daban rayuwata
daban, tana da wanda take
so...babu ruwana da ita." Hilal ya
sake fadawa kansa.
To amma sa'ar da ya karkata kan
motar ya shiga layin shi kansa ya
san abin da ya fadawa kan nasa
babbar karya ce domin ya san
muddin zai ci gaba da ganin
Zuhuriyya tsahon son
mahaifiyarta dake cikin ransa na
iya yin tasiri a kansa. Ko a lokacin
ya fi dokin ganin Zuhuriyya akan
Rukayya.
Karfe biyar da yan mintuna
agogon dake cikin motar ya
nunawa Hilal. Kamar jiya a
wannan karon ma a hankali yake
tafiya a cikin layin to sai dai kuma
akwai saukin faduwar gaba
sabanin jiya a kalla dai yanzu ya
san ta san shi.
Hilal na wuce wasu tagwayen
gidaje masu kama daya, sai ya
hango Zuhuriyya tsaye a jikin
wata katuwar mota shudiya kirar
Toyota, mai duhun gilasai, domin
daga inda yake ba ya iya hango
wanda ke cikin motar. Wannan
shi ya sa Hilal yin fakin a gefe
guda bai karasa kofar gidan ba.
Ga mamakinsa sai ya ji zuciyarsa
ta harzuka, ransa ya baci.
"Me ke damuna ne? Hilal ya
tambayi kansa, sannan ya dan
dada kwantarwa da kansa
hankali sai ya saki wani
busasshen murmushin yake
wanda ya fi kuka ciwo.
"Mijinta ne...tabbas mijin da zata
aura ne...to in ma wanene ina
ruwana...Zuhuri yya kamar ya' ce
a gurina." Hilal ya sake fadawa
kansa yana kuma kokarin
lallashin zuciyarsa domin ji yake
yi kamar za ta tsaga kirjinsa ta
fito saboda tsananin kishi, Ba'a
dade ba sai ya ji gumi ya fara
wanke masa fuska, cikin sauri ya
lalubi aljihun tazarcensa ya zaro
wani farin kyalle ya goge
fuskarsa, sannan ya lumshe
idanu gami da ajiyar zuciya ya
fara addu'a.
"Allah...ka rabani da ciwon son
abin da zan sha wuya ban same
shi ba.
A daidai lokacin da ya fara
addu'ar ne ya ji sautin injin mota
ta nufo inda yake. Hilal ya bude
idanunsa sai ya ga ashe shudiyar
motar ce da ya ga Zuhuriyya
tsaye kusa da ita. Hilal ya yi
kokarin hangen mutumin da ke
cikin motar, amma da yake motar
ta riga ta dan gifta kafin ya bude
idanunsa kuma duk gilasan gefe
na motar masu duhu ne, bai iya
ganin direban motar ba, amma
ya ji tattausan kidan wata wakar
fim na Hausa na tashi daga cikin
motar. Zuciyarsa Na.BINDIGAR KWALI--> 18
.
Zuciyarsa na kuna kamar ta kama
da wuta Hilal ya kunna motar da
niyyar ya karasa kofar gidan
dubawar da zai yi haka, sai ya
hangi Zuhuriyya ta cikin madubin
motar ta nufi inda yake dauke da
wata farar ambulan a hannu. Dan
haka sai ya kashe motar, sannan
ya fara niyyar kiranta idan ta zo
wucewa domin ga tsammaninsa
gidan makwabta za ta shiga.
Amma ga mamakinsa sai ya ga
kai tsaye gurinsa ta taho.
"Sannu da zuwa...kai na gani na
taho."
Zuhuriyya ta ce lokacin da ta
karaso ta bangaren da yake
rungume da farar ambulan din
gami da faffadan murmushinta.
"Har ka dawo mu sake gaisawar
haka da wurwuri, ai na dauka sai
nan da wata zan sake ganinka?"
Hilal, zuciya na bugu, ya dubeta
da murmushin yake. "Ji na yi ba
zan iya daurewa ba sai na sake
zuwa na yi kwalli da...kyakkyawar
fuskarki."
Zuhuriyya ta fashe da wata
zazzakar dariya gami da rufe
idanu "Kai dai wallahi ba ka
rabuwa da tsokana, ina wata
kyakkyawar fuskar take anan,
kuma ina kai ina kallon fuskar
matar wani."
Hilal ya ji kamar ta soka masa
wuka a kahon zuci. "Wan...nan da
na hange ku tare shi ne mijin
naki?"
Zuhuriyya ta gyada kai "Shi ne
mana, ai da ka karaso ma kun
gaisa"
Hilal ya yi murmushin yake "Zan
so ace kuwa mun gaisa" Ya yi
karya "Amma ba komai wata
rana ma gaisa"
"Haka ne" Zuhuriyya ta ce tana
wasa da farar ambulan din dake
hannunta Hilal ya lura kamar
hotunane a ciki.
Suka yi shiru na dan lokaci. Hilal
ya yi zaton za ta ce dashi "Ni zan
tafi" Amma maimakon haka sai
ya ga ta ci gaba da tsayuwa.
"In ba damuwa...ina ganin ai
gara ki zagayo nan ki zauna
ko...maimakon ki yi ta tsayuwa"
Hilal ya ce da ita a tausashe.
Zuhuriyya ta dan yi jim, sannan
ba tare da ta dube shi ba sai ta
ce "To" Tana rangwada kamar
dawisu ta zagaya daya bangaren
motar. Tun kafin ta karasa Hilal ya
bude mata kofar motar gidan
gaba, Zuhuriyya ta zauna a
hankali, kusan duk a tsorace,
kafafunta a waje, amma ta yi
kokarin juyowa kadan yadda za
ta ke ganinsa, ta ajiye farar
ambulan din a kan cinyarta.
Hilal ya dubeta da murmushi
sannan ya dubi farar ambulan
din dake kan cinyarta ya ce
"Wannan ko hoton mutumin ne a
ciki?"
Zuhuriyya ta gyada kai "Mijina za
ka ce"
Hilal ya ji kamar ta kara soka
masa kibiya a kahon zuci, sannan
ya dubi fuskarsa yana cewa "Na
san dai ko wane ne mijin nan
nata sai dai ya fi ni kuruciya,
amma ba dai kyawun fuska ba."
"Mijin naki a ina yake?" Hilal ya
tambayeta zuciyarsa na kuna.
Zuhuriyya ta sunkuyar da kai
gami da tsuke baki. "Likita ne...a
asibitin kudi na baba na...me
yiyuwa ma ka sanshi kwararran
likita ne anan gidajen ma'aikata
na asibitin ma yake gida mai
lamba (24)" Zuhiriyya ta dan yi
shiru tana duban Hilal.
"Ah, ki ce layin mu daya, nima
likita na karanta."
Hilal ya ce, zuciyarsa na tuna
bakin cikin ranar da aka koreshi
a shekararsa ta karshe a Ikko.
"Ashe kai ma likita ne?" Hilal ya
gyada kai yana kallon farar
ambulan din dake hannunta.
Haka kawai sai ya ji yana son ya
ga hoton wannan miji da take
son aura.
"Zan iya ganin hoton mijin na
ki?" Hilal ya bukata yana kallonta
ido da ido. Zuhuriyya ta dubeshi
cikin mamaki.
"Me za ka gani a hotonsa...ba fa
wani saurayi bane...kai ma ka fi
shi yarinta." Akwai alamun daci a
muryarta sa'ar da ta furta
bayanin.
"Babu ruwana da tsufansa, ni dai
so nake kawai na ganshi, kika
sani ko wata rana ma hadu da
shi bayan ya aureki...ina laifi idan
mun yi mutunci da shi."
Zuhuriyya ta zunkuda kafada.
"Tun da dai ka dage gashi nan ka
gani, amma fa na fada ma ba
yaro bane..." Ta mika masa farar
ambulan din ta dauke kai gefe
guda.
Hilal ya karbi farar ambulan din
ya zaro hotunan sannan ya sami
kansa yana kallon wasu fararen
idanu kamar idanun maciji.
HILAL YAJI KAMAR AN TAFKA MASA
GUDUMA A KIRJI.
.
Da Allah ya sa Zuhuriyya na lura da ta ga
zaburar da Hilal ya yi sa'ar da ya
ga hoton. Doguwar fuskar dake
kallonsa da fararen idanu a
tsaitsaye gami da dogon hanci
mai dan doro kamar hancin aku
su suka hautsuna hanjin cikin
Hilal, suka dagula duk wani lissafi
dake kwakwalwarsa, sannan
sake yi jifa da tunaninsa zuwa
can baya...shekaru ashirin da
daya da suka wuce, har abada
koda zai yi tsahon ran shekara
dubu a duniya Hilal ba zai taba
manta fuskar mutumin ba.
Jikinsa na rawa Hilal ya ajiye
hoton a hankali sannan ya dubi
Zuhuriyya muryarsa na rawa ya
ce a sassarke.
"Wannan shi ne mijin da za ki
aura?"
Zuhuriyya ta gyada kai. "Ya ya
sunan shi?" Zuhuriyya ta dubeshi
cikin zargi.
"Me ya sa kake son ka san
sunansa?"
"Saboda ya yi min kama da wani
mutum da na sani tun ina
karami."
Zuhuriyya ta lumshe idanu ta ce
"Ai daman na fada ma da wahala
ma idan ba ka san shi ba
sananne ne in dai kana zuwa
Jumare Special Hospital dole ka
san shi...sunansa DAKTA SADI."
Hilal ya lumshe idanu, ji yake yi
kamar zai sume, domin a karo na
farko cikin shekaru ashirin da
daya ya gano adireshi da sunan
azzalumin da ya kashe uwa
yanzu kuma yake kokarin auren
diyarta MARAINIYA Zuhuriyya.********
.
Lokacin da Hilal ya kawo kofar
asibitin tuni har goma na dare ta
wuce. "Lokacin ziyara ya wuce."
Maigadin asibitin ya ce dashi,
wani motsattsen tsohone mai
fuska da tsayi kamar silifan
tsofaffi kansa babu gashi sai
wasu adadi dake makale akan
doron kan shan kwai adadin
yawan gashin bai fi ashirin da
uku ba. "Ka gafarce ni baba, ba
ziyarar
marar lafiya na zo ba gidan dakta
Sadi na ke son zuwa."
Dattijon me gadin ya karkatar da
kai gefe guda.
"Ba ta nan ake shiga gidajen
ma'aikata ba, zagaya ta can baya
bangaren katangar kudu za ka
ga shudiyar kofa ta nan ake
shiga."
"Na gode." Hilal ya ce da faffadan
murmushi kai ka ce gafara
dattijon ya yi masa. Mintuna uku
da faruwar hakan
Hilal ya ja birki a kofar gida mai
lamba ashirin da hudu (24)
Tun karfe biyar din da suke tare
da Zuhuriyya basu sami damar
rabuwa da juna ba sai karfe tara.
Lokacin da magariba ta yi sai Hilal
ya kada baki ya ce.
"Ya kamata na tafi kin ga lokacin
sallah ya yi."
"Ba ga masallaci can ba, akan
kwana je ka yi sallar ka dawo
mana ko wani gurin za ka?"
Zuhuriyya ta ce. Abin ya bashi
mamaki shi kansa yana son ya
tsaya ya yi ta sauraron daddadar
muryarta, to amma ba zai iya jin
wani dadi ba a duniya bayan
babban makiyinsa na nan raye a
duniya ya kashe wacce ya fi
kauna fiye da komai a duniya.
"Akwai wani tsohon abokina da
na dade ban kai masa ziyara ba
gidansu nake son zuwa." Hilal ya
yi mata karya.
"Ka bari to ka tafi karfe tara ku
maza dare baya hana ku yawo..."
Zuhuriyya ta ce "In ban da abinka
yanzu idan na yi aure kuma ba
shi kenan ba." Akwai alamun
sosuwar zuciya a muryarta sa'ar
da ta ce hakan.
Lokacin da karfe tara ta yi, sai
Hilal ya dubi agogo. Zuhuriyya ta
dubeshi cikin damuwa. "Har
karfe taran ta yi?" Hilal ya
gyada kai "Ai kin san yanzu dare
baya wuyar yi."
Zuhuriyya ta sunkuyar da kai
kasa "Za ka dawo gobe ne?" Hilal
ya ji zuciyarsa ta harba. "Me...me
zai hana indai kin ce na
dawo din."
Zuhuriyya ta fita daga motar ta
rufe masa kofar sannan ta leka ta
tagar motar, ta ce dashi a
tausashe.
"Bawan Allah, gashi ko sunanka
ban sani ba, amma wallahi ji
nake yi kamar na fi shekara
goma da saninka shi ya sa bana
son rabuwa da kai." Hilal ya ce a
ransa., Kin fi shekara ashirin da
daya da sanina yar budurwa,
tunawa ne kawai kika kasa.
Sannan sai ya dubeta ya ce a fili.
"Gobe war haka muna tare...nima
ji nake yi kamar na fi shekara
ashirin da saninki........BINDIGAR KWALI--> 19
.
Zuhuriyya ta saki wata faffadar
dariya hannunta kankame da
tagar motar.
"Allah ya kiyaye to ka gaida gida...ina jiranka goben." Ta
juya a hankali ta nufi kofar gidansu.
Har ta shige gida bata juyo ta
kalleshi ba.
A yanzu da Hilal ke zaune cikin
motar yana kallon dan madaidaicin gidan Likitan wanda
ke zagaye da dogayen bishiyoyi
da shuke-shuken furanni sai ya
yi mamakin in har Zuhuriyya ta
taba cewa da daktan "Ina jiranka gobe. Me yiyu ta taba
fada masa hakan. Hilal ya ce da kansa. Tun
da dai ita bata san shi ya kashe mata mahaifiya ba."
Tsawon mintuna goma Hilal na
zaune yana kallon gidan. Babu
wani mahaluki da ya shiga ko ya
fita daga gidan. Don haka jikinsa
na rawa sai Hilal ya rufe motarsa
sannan ya taka a kasa ya ratsa ta
tsakanin shuke-shuken da bisoshin da ke gidan ya nufi
kofar gidan yana sauraro babu
komai sai tattausan kidan zamanin dake tasowa daga
cikin
gidan. Hilal ya dauke
numfashinsa sannan ya danna kararrawar dake manne a
jikin
bango. Dannawarsa ke da wuya
sai kofar ta bude kai ka ce daman jira ake yi ya danna a
bude kofar.
"Malam da Allah ka bar ni na huta
bana iya ganin majinyata a gida
gobe ka sameni a asibiti." Dakta
sadi ya ce da Hilal a fadace daga
shi sai gajeren wando babu
komai a jikinsa. Hilal ya ji kamar
ya daga hannu ya naushe shi sai
ya hana zuciyarsa.
"Ba rashin lafiya ta kawo ni ba
magana nake son yi da kai." Hilal
ya ce yana dubansa ido da ido.
Dakta sadi ya dubi kyakkyawan
mutumin sama da kasa bai gane
shi ba amma jikinsa na bashi cewa kamar ya taba ganinsa
a
wani wuri.
"Ba na iya ganawa da kowane mutum a wannan
lokacin..ka zo gobe ka sameni a ofis yanzu lokacin hutuna
ne."
"Ni yanzu nake son magana dakai idan aka kai gobe ai ta
yi
tsami maganar."
"To ka bar ta ta yi tsamin ta har
ta rube dan bani da ra'ayin jinta a yanzu." Dakta sadi ya
ce a
harzuke.
"ka da ka yi fushi Dakta." Hilal ya
ce dashi a tausashe "Na san dan ba ka san wacce magana
ce ke
tafe da ni ba shi yasa kake kokarin korata."
Dakta sadi ya dubi Kyakkyawan
mutumin a rude. A zuciyarsa yana cewa yau Allah ya
hadani da mahaukacin mutum lallai ciwon
hauka ne ke damunsa. amma
dan me za a turo min mahaukaci da wannan daren bayan
kowa ya san ni ba likitan mahaukata
bane?
"Dan Allah malam ka da ka takurawa rayuwata.. wacce
magana kake son fada min ne?" Hilal ya dafa kofar gidan
da
hannunsa sannan ya dubi Dakta
Sadi da faffadan murmushi.
"Daman magana na zo ma da ita
akan tsohuwar masoyiyarka
Hajiya Zainab wacce ka kashe...amma tun da ka ce baka
son ji yanzu to mu bari sai gobe
din idan na sami lokaci na dawo
in kuma ban samu ba na fadawa amaryarka Zuhuriyya sai
ta yi
maka bayani." Hilal na gama fadin
haka sai ya juya zai tafi. Dakta Sadi ya zabura a tsorace
"A'a....malam.. .shigo-shigo daga ciki dan Allah." Hilal ya
juyo kadan kana ya
girgiza kai ya ce.
"Ka je ka huta kada na bata ma lokacin barcinka ka huta
lafiya Sai goben ma hadu kamar
wannan lokacin." Cikin sauri Hilal
ya juya zuwa gurin da ya ajiye motarsa. Koda ya kai ga
motar
sai ya juyo ya dubi kofar gidan. Dakta Sadi na

Please Login or Register in order to submit comment