Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1:41PM, 2/22/2017] Halima: ```YAZANYI DA AUREN ADNAN.?```



```© UMMU SABREENA
ND
ANTY AYSHA
ND
JAM33LA```



<<1~5>>





Gudu take acikin daji, cikin tsakiyar duhun dare, nan taci karo da wani babban dutse ta fadi a 'kasa tana nishin wahala,ta waiga hagu ,ta waiga dama, bata ganshi ya biyo ta ba, ta tsugunnan da kanta idanunta na zubar da hawaye mai cike da firgici , 'dagowan da zatayi kawai ta ga macijin a gabanta ya fasa kai zai sareta ,ta fasa wani wawan ihu wanda yayi sanadiyyar tashin ta daga baccin datakeyi ,ta ri'ke kai tana maimata sunan Allah a fili, "mafarkan data keyi kenan yawanci ,sai taga maciji ya biyota , yana zuwa zai sareta sai ta farka ,
"innalillahi wa inna ilaihi raji'un",ta sauko a hankali daga kan gadonta ta nufi bayi tayo alwala duk da tsoron dake cikin ranta bai hanata gurfana agaban ubangijinta ba tana mai kai kuka gurin mai ji kuma mai ganin ta a kodayaushe ,bayan ta idar ta dauki alqur'ani ta karanta sannan ta mi'ke ta cire hijjabi ta ninke daddumar ta kwanta ,sai wajajen asuba sannan nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
wanshekare da safe misali karfe goma na safiyar asabar ,mama ce zaune ita da dad zaune suna breakfast ,dad ya kalli mama yace "wai haryanxu aisha bata tashi bane ?", mama ta aje cup din dake hannunta tace "kasan ai sabida yau ba makaranta shiyasa take ta hutawa ", yayi murmushi yace "mamana kenan akwai san hutu ga shagwaba", suka gama karyawa sannan mama ta rakashi ya wuce office.
Karfe daya na rana ya buga dai dai ,mama ta mi'ke ta nufi 'dakin Aisha ,ta tura 'kofa ta shiga ta hangota can tsakiyar gado tanata baccinta ,
mama ta matsa kusa da ita tana tashinta "Aisha! Aisha!! Aisha!!! Ki tashi mana ,karfe daya na rana fa ,ko karyawa bakiyi ba,lafiyarki kuwa?
" ta bude manya manyan idanuwan a hankali tace " mama wallahi duk gajiyar schl ne ," "to ai baccin ya isa haka ko" tace "to mama ganinan fitowa",
ta mi'ke tayo wanka da brush sannan ta yi alwala ta nufo falo gurin mama dake zaune tana karanta jarida ,ta matsa kusa da ita ta kanga jikinta jikin mama tana sha'kar kamshin turaren dake tashi a jikin mahaifiyar tata ,ta dan lumshe ido tana fadin "mama mun wuni lafiya "? "Lafiya lau auta ya gajiya ?
" Alhamdulillahi kije ki zubo abinci mana ya kitchen nasa miki a cooler",
Alhaji muhammad shine mahaifinsu, yanada mata daya mai suna hajiya hassana (mama) ,dan kasuwa ne sosai wanda suke zaune a kaduna u/sanusi ,
Allah ya albarkacesu da yara guda uku dukkansu mata ,
Hannatu itace babbar 'yarsu tanada yara guda hudu, maryam,afrin,al'amin sai karaminsu muhammad ,tana zaune a unguwar dosa anan kaduna .
Sai maryam wacce take da yara biyu ,Abduljabbar da Amatullah wacce taci sunan mama ,tana zaune a zariya wanda anan gidanta Aisha wacce ake kira da adla kuma itace autar mama ,sabida anan zariyan take karatu, yanxu ta dawo weekend ne wurin mama wannan kenan!





```YAZANYI DA AUREN ADNAN.?```



```©UMMU SABREENA,
AUNTY AYSHA
ND
JAM33LERH```



5~10




Da yamma adla na kwance a falo ,wayarta ce a hannunta tana latse latse ,bakar riga ce a jikinta 'kirar blackberry ta daure kanta da bakin dankwalin rigar ,duk da bawani kwalliya tayi ba amma kyanta ya fito sosai ,idanuwan nan nata manya, ga gashin kanta daya kusan rufe mata goshi nan ya kwanta luf a kanta '
Lebanta dan dai dai kaman ita tayi kanta, komai nata cis cis dan irin jikin mama gareta.
Nan taji dawowan dad ,
Da sauri ta tashi taje anso jakar dake hannunshi tana mishi sannu da zuwa ,ya amsa cikin jin dadi yace
"Adla , dazun nake tambayar mama baki tashi bane tace min kinata bacci ne , nace gaskiya adla tayi min wayau sai hutawanta take ,ya fadi haka yana mai zama a kusa da ita ,
Tayi murmushi wanda beauty point dinta suka lotsa " abbana bawani wayau ,wallahi na gaji dayawa ne, kuma gashi bana samun baccinne sosai sai nazo gidan mama",
Mama ta fito daga 'dakinta jin dawowar mai gidan nata, ta zauna tana mai mishi sannu da dawowa ,
tace "adla har kin gama girkinne ?", "eh mama ta gama har na jera a dinning ma ",
Dad yace " maman adla wai kinji autarki bata samun bacci a gidan maryam sai tazo nan, ya fadi haka da zolaya ,
"Eh mana abbana wallahi idan mai sunan mama ta fara kuka cikin dare a gidannan kowa sai ya farka dan har karnukan gidan tashin su take ",
Dad yayi dariya sosai , yayinda itakuwa mama ta harareta tace " banason sharri adla ,mai sunan nawa ai tafi abduljabbar hakuri ,ita da ba ruwanta ",
"Bawaninan mama wallahi ummi fitinanniya ce " ,
Dad yayi murmushi yace " kyalesu adla , da mamarku da mai sunanta duk zanyi maganinsu ",
Mama ta tashi ta nufi dakinta dan taji anata kiraye kirayen sallar magriba, itama adla ta mi'ke ta wuce nata dakin tana mai jin dadin yanayin garin domin hadari ne ya hadu ,iska ta ko'ina shigowa yake .
Bayan sunyi sallah ne suka sauko falo ,
Mama ta mi'ke ta kawo musu abincin nan tsakiyar falo ta zuzzuba musu sunaci suna hira cikin nishadi.
Dad ya dauki tissue ya goge bakinsa yana fadin " naga alama auta ta kusa tafi mamarta iya girki ",
Mama ta aje cokalin hannunta tace " da sauki ai tunda dai nina koya mata " ,
Adla tayi dariya " abbana dama nagaya maka nafi mama iya girki ,nata hannun ya tsufa ,nawa hannun kuwa sabo ne ",
"Kice min kawai mamarku ta tsufa ",
Mama ta 'danyi murmushi mai sauti " kowa yasan dai da tsohuwar zuma ake magani ",
Adla ta mi'ke tana dariya ta wuce dakinta ,
Wayar dad tayi 'kara ya dauka tare da sallama dan ganin nombar amininshi ne wato Alhaji Aliyu ajiya , bayan sungaisa ne yake shaidawa dad cewa yananan dawowa ranar monday daga italy , dad ya mishi fatan alkhairi sannan ya kashe wayar ,
Ya kalli mama yace " abotarmu nida aliyyu ta har abada ne dan kuwa jinsa nake har cikin raina ,tun muna 'kanana muke tare gashi har girma , ban 'dauke aliyyu a matsayin amini kawai ba ,na dauke shi ne a matsayin 'dan uwa",
Mama tayi murmushi " gaskiya alhaji aliyyu mutun ne ,matar shi ce kawai sai a hankali dan kuwa a tunanina gaskiya baiyi sa'ar mata ba ",
Dad ya 'dan kalleta da gefen ido yayi dan dariya "wannan matsalar kuce ta mata maman adla ,amma bata shafemu ba mu mazajenku ",
Tayi shiru bata ce masa komai ba sabida tasan cewan aliyyu mutmin kirki ne kuma shine babban aminin dadyn adla ,
Yanada mata daya mai suna Hajja balaraba , mazajensu aminai nai amma matansu halinsu yasha bambam ,
Ita hajja balaraba mace ce mai son duniya da 'kawarta gata da kyaman wanda baida shi ,abinda yasa ma batawa maman adla sabida tsakaninsu kar tasan kar ne , kuma dai mazajensu tare suke kasuwanci balle ta nuna mata kudi , sai dai tayiwa wasu amma batayi agaban mama ko tayi mata ,
Dan mama bata daukan rainin hankali irinna hajja , suna shiri da juna amma ba chan sosai ba kuma suna gaisawa amma kowacce tasan halin kowacce ,
Danta daya namiji mai suna "ADNAN" ,ba anan yake karatu ba yana 'kasar Germany ,
Domin tunda yagama primary abban shi ya kaishi can , ta 'dauki son duniya ta daura mishi domin shi kadai gareta
[8:28PM, 2/23/2017] Halima: ```YAZANYI DA AUREN ADNAN?.```




```© UMMU SABREENA,
ANTY AYSHA
AND
JAM33LERH```

```20-25```




Bayan alhj.aliyu ya tafi ne da yamma banyan Dad yqdawo Daga masallaci suna zaune da mama a bedroom dinsa ya kalleta " inaso ki saurareni da kyau ,wannan maganar da zanfada miki yanxu ba shawararki nake nemaba ,a ah! Kawai dai a matsayinki na mahaifiyar adla ne yasa zanfada miki ,sabida mun riga mun gama maganar ,abinda kawai nakeso naji Daga gareki shine fatan alkhairi, nasanki maman adla kinada fahimta da hakuri Dan haka na yanke shawarar koban gayamikiba zaki fahimta ,to inaso ki saurareni da kunnan basira .

Ta juyo tana kallonsa " ya zayyanemata duk yadda sukayi da abban adnan,ido kawai tazuba mishi ko kyaftawa babu, itadai bazatace ADNAN yaron banza bane tunda ance zato zinibi ne, amma wani hanzari ba gudu ba, tarbiyyarshi take kokwanto, ba'a Nigeria ya girma ba, tun tasowarshi a germany yake rayuwarshi, gakuma uwa uba hajja balaraba da gaskiya bata fatan hada zuriya da ita, kuma yadda takeson ADNAN bata tsammanin akwai abinda yaron zaiyi aga laifin shi, inta Abban adnan ne to bazata guji zuriyarshi ba "

Ta sauke nannauyan ajiyar zuciya tace "Hmmm Allah ya sanya alkhairi, amma ai jibi ne jumma'ah ko? ",

Dad yace " eh ranar jumma'ah za'a daura insha'allah, amma banaso ki fadama ita adlan, nafiso insunyi hutu tadawo sai a gaya mata ",

Ta gyada mishi kai taja bargo ta kwanta zuciyarta cike da sak'e sak'e akan wannan aure

Saukowa take a hankali daga matakalan jirgi ,tana amsa waya, ta isa ga driver dayazo daukanta, ya fito ya dan du'ka yana gaisheta,

Ta amsa tana kokarin shiga cikin motar, suna isa gida 'yan aikin gidan suka fito sunata kwasar gaisuwa .

Ta dauko wayarta ta latsa nombar maigidan nata take sanar masa dacewa gata a Nigeria tadawo.

Kafin kace wani abu masu kula da girkin gidan sun cikata da abinci kala kala. Ta dan kalli inda abincin yake ta yatsina fuska tace "bari nayo wanka nayi.sallah sai nazo naci abincin ",

Da yamma Alhaji aliyu ya iso gidan, ta tarbeshi da sannu dazuwa, bayan sun zauna yake tambayanta ina Adnan?,

Tayi murmushi najin dadin an ambaci dan nata " adnan yana can karatu yakusa ya kare, baka ganshi ba yakoma bature sak ",

Alhj aliyu yayi dariya " lallai germany ta anshe shi 'dan nema",

Sukayi dariya dukka




```YAZANYI DA AUREN ADNAN?```



```UMMU SABREENA,
ANTY AYSHA,
ND
JAMEELERH

25-30```

Wanshekare dasafe, mama ta dauki waya takira hannatu da Maryam tace suzo tanason ganinsu, amma tacewa maryam karta fadawa Adla cewan nan zatazo sabida kar tace zata biyo ta.

Hannatu ce ta fara isowa sannan maryam, duk sun hadu a falo sun gaisa, nan ne mama take kora musu jawabin abinda mahaifinsu ya cemata gameda auren adla, ta kara da cewa " kune 'ya 'ya na kuma kune yayyinta, dan haka ya kuka gani?,

Hannatu ta nunfasa "lallai dole hankalinki yayashi mama, ba komai bane abinji sai hajja, ga shi kuma sudai yara ba son juna suke ba, ina tsammanin ma bai santa ba a fuska itama bata san shi ba, sukuma su dad sun yanke hukunci, amma wannan saidai muyita musu addu'a yadda dai dad yace tunda anyi angama ",

"Amma kina tsammanin adla bazata 'ki ba?,

Maryam tace "ai mama kinsan autar taki akwai hakuri nasan.zata yadda, dan haka karkisa damuwan hajja acikin zuciyarki tunda ba tare zasu zauna ba, inaa ganin bawani problem ",

Mama ta sauke ajiyar zuciya "shikenan Allah yamana zabi na alkhairi ".

Suka amsa da amin

Maryam tace " ranar juma'ah kikace ko mama? ",

"Eh ranar Friday ne ",

"Kenan gobe ne, to ko na kwana ne?,

"A ah mairo ki koma gida kar ita auta tayi zaton ba lafiya ne, ai daurawa kawai zasuyi, taron biki kuwa sai yadawo saura wata biyu",

"Ohk Allah ya kaimu.",

Shiko Alhj aliyu bai gayawa hajja ba sabida yasan halinta yadda taci buri kan adnan dayawa, ya barine sai an daura sai ya sanar mata, ba yadda zata iya .

Ranar juma'ah misalin karfe sha daya na safe aka shaida daurin auren ADNAN DA AISHA (ADLA) wanda dad ya zama waliyyin ango shikuma Alhaji aliyu Waliyyin amarya.

Daurin auren duk da a qurarran lokaci suka sanar amma bai hana mutane taruwa sosai ba. Kowa kagani cikin farin ciki

Da yamma Alhaji aliyu ya shigo gidansa, hajja yasamu kwance ta mik'e k'afa ana mata tausa ita kuma tana ansa waya, ladi mai aiki ta mi'ke ta na mai gaisheshi sannan ta fita da sauri ,ya gitgixa kai yasamu wuri ya zauna.

Ta kare wayar sannan ta juyo tana murmushi tace " Alhaji sannu dazuwa yau naga ka shigo da wuri ne ",

Ya cire malunmalun dayasa ya kalleta "eh sabida naje wani wuri ne ",

Taga alamun yau ba wasa a fuskar shi dan haka tasha jinin jikinta, dan kuwa tana shakkarsa komai abinta.

Ya katse mata tunani tahanyar fadin " inaso kibani hankalinki anan balaraba, magana ce zamuyi mai mahinmmanci, banason tashin hankali, abu dai anriga anyishi dan haka ki saurareni dakyau kiji hukuncin dana yanke, nida aminina mun yanke shawarar hada zuriyar mu aure, kamar yadda kika sani wannan bawani bane illa alhj Muh'd, yau an daura auren ADNAN da ADLA, dan haka banason jin komai daga gareki sai addu'a,

Ta hadiya wani kakkauran miyau, tadan goge zufar data keto mata tace "amma maiyasa baka fada min ba a matsayina na mahaifiyar shi? ",

"Sabida nasan halinku na mata abun zai iya baci, dan haka shima Adnan din dan inada iko dashi ne, kuma kar ki sanar mishi har sai yadawo zangaya mishi sannan sai kiyi taronki ",

Ta sauke ajiyar zuciya badan taso ba, sai dan ba yadda ta iya, kuma ita before akwai wata yarinyar kawarta da takema adnan sha'awar ya aura, ba'anan suke zaune ba suna italy, kuma masu azziki ne sosai, amma bakomai zata yi shiru akan wannan maganar sabida kar ace matsala daga wurin ta ta bullo, zata yi musu bakam amma zasu sha mamaki, "hmm tayi dariyar mugunta ", hajja kenan
[7:37PM, 2/24/2017] Halima: ```YAZANYI DA AUREN ADNAN?```




```© UMMU SABREENA,
AUNTY AYSHA,
ND
JAMEELERH```



```40-45```



Wanshekare a safiyar laraba, dady aliyu ne tare da iyalansa suna karin kumallo, hajja ce tayi tayi serving kowa, sunaci suna hira cikin jin dadi da annashuwa, dady aliyu ya aje fork din dake hannunsa ya kalli adnan yace " dama adnan akwai wata magana mai mahimmanci da zamuyi dakai ",
Hajja najin haka ta tsuke fuska ta hade rai,ita za'a takura mata 'da, kunji fa masu karatu kamar wani 'danta ita kadai!,
dady aliyu yacigaba " munyi shawara dakai da dadynka (dadyn adla ,dan haka yake cemasa) lokacin baka 'kasar, muka yanke hukuncin hada auren ka da Aisha 'yar wurinsa, dan haka nasan kai yaro ne mai hankali da bin iyaye, inafatan bazaka bani kunya ba ",
Adnan yayi shiru yana kallon dadynsa ,yayi murmushi a ransa yace " shi ko da yayi rayuwarsa a germany bai damu da mata ba, ko a chan yanda mata ke binsa har gida baya kulasu, balle kuma anan Niger, to zaidai yadda da auren ne sabida kawai yafarantawa mahaifinsa rai",
Ya dago kai yace " bakomai dad allah ya sanya alkhairi ",
Zo kuga fuskar hajja kamar ta daura hannu akai ta fasa ihu,
dad yace "ubangiji Allah ya maka albarka",
"Amin dad ",
"Yawwa zamuyi magana da mahaifiyar ka akan kudin daza'a kashe na komai da komai",
Su hajja anji maganar kudi " eh ai dama satin nan zanje Saudi, sai a hado mata kayan lefe achan ",
Dad yace "bakomai innadawo sai ki fadi nawa zan baki, kai kuma adnan ka shirya anjima da daddare zamuje gidan dadyn adla ka gaishe su ",
"To dad Allah ya kaimu ", ya tashi ya fita ,sanye yake da wasu riga da wando fari da baki, yayi sosai, ga sajen shi nan yayi mishi kyau a fuska,
justice ya kirashi a waya yace mashi gani nan zuwa,
"Mama bari naje gidan anty hannatu zuwa dare zan dawo "
"To ammafa kar ki ce zaki zauna kinsan dadynki yace baison yawan fita ",
Ta samu hijjabinta dogo har 'kasa ,atamfa ce a jikinta riga da sket, hoda ce kawai a fuskarta sai ta shafa lip gloss a bakinta, tayi kyau duk da batayi make up sosai ba,
Ana kiraye kirayen sallar magriba motar dad ta kunno kai tare da motar dady aliyu,
babban falon kasa suka zauna,
Mama ta sauko da fara'arta tana musu sannu da zuwa,
Adnan ya tsugunna yana gaida ita, tayi murmushi tace "lallai wannan yaro ya girma, aini ban ganeshi ba ",
Sukayi dariya banda adnan da yayi murmushi,
dadyn adla yace " bari muyi sallah tukun ",
Kafin su dawo mama ta jera musu abinci sai kamshi ke tashi.
bayan sun shigo ne suka nifi wurin cin abincin,
Dady aliyu yace "wai banga 'yata bane ko tana makarantane? ",
Mama ta karbe zancen"tadawo shekaran jiya, dazunnan na aiketa gidan maman afrin ",
Bayan sungama cin abincinne dady aliyu ya ansa wayar dadyn adla ya dauki nomnar ta,
Dad ya kalli mama yace " maman adla ba yanxu adlan zata dawo bane dan sugaisa da adnan? ",
Mama tace "kasan adla da son hira yanxu haka tana chan sunata surutu da yara ,gashi bata tafi da wayarta ba, bari na kira wayar maman afrin 'din " ,
Dady aliyu ya katse ta " ki barta kawai maman.adla, ai zai dawo sai su gaisa ",
" to shikenan sai yazo, tafadi hakan da murmushi a fuskarta ,
Da zasu tafi sukaje suka musu rakiya har mota, dady aliyu yace mata dad sai sunyi waya.
[18:51, 8/4/2016] ummu sabreena.mywapblog.c: ~YAZANYI DA AUREN ADNAN? ~
NA UMMU SABREENA,
AUNTY AYSHA,
ND
JAMEELERH
45-50
Ita kuwa mama lokacin data dawo daki sai taji kamar zuciyarta tana tan tama akan adnan, ai to dole tayi tantama akan tarbiyyar hajja, duk da daga gani ba halin ta dai ya biyo ba, amma dai bazatayi saurin yanke hukun ci ba,
Koda adla tadawo mama ke fada mata zuwan su adnan saida gabanta yafadi, dan ita tama manta dawani maganar aure, saida taje gidan anty hannatu take tsokanarta amarya, yanxu kuma ga mama tace sun zo, a sabile ta haye 'dakinta a ranta take fadin "oh ni adla YAZANYI DA AUREN ADNAN? Allah kamin zabi na alkhairi ,duk da bata taba ganin shi ba amma idan ta tuno shi.ko taji an ambaci sunansa sai gabanta ya yanke ya fadi ,
Dady aliyu dakansa ya bawa adnan nombar adla yace gashi yakirata kuma yanaso yadinga lekawa wurinta yana dubata, ya amsa da to kawai amma shi ina yaga lokacinta.
Dady aliyu ranar friday suna tare da dad, yake tambayarsa yaushe ne adla zata tare gidan mijinta
" haba aliyu, ai kai nake jira kasa rana, kaine fa dadynta ",
Dady aliyu yayi murmushi yace " shikenan bari asa nan da wata daya, kenan sati 4 ",
"Shikenan zan sanar musu can, allah ya kaimu, ",
Dady aliyu yace "kuma Muh'd banaso kace zakayiwa aisha komai, ni zan mata komai na kaya",
Dad yayi murmushin jindadi yace " bakomai baban adla ,Allah ya basu zuriya ta gari ",
Shima dady aliyu dariya yayi "amin amin "
Koda dad yagayawa mama murmushi tayi tace " aliyu kenan akwai zumunci da alkhairi ",
Tun daga lokacin mama taketa gyaran autarta ciki da waje .
Dady aliyu yabawa hajja makudan kudi yace tayowa adla siyayyan kayan lefe dana daki,
dady aliyu ya tambayi adnan ko yaje wurin adla kuwa?
Sai ya sillo karya yace ai suna waya, abunda yasa bai jeba aikine yamishi yawa a office, dady yace masa to ya daure yaje.
Ita kuwa mutuniyar dama batasa ran zaizo ba, dan yadda yake jin kansa baya son ta to itama ba son shi take ba,
bayan hajja tadawo ne tajido kaya sosai kuma ta ci ribar sauran kudin dan kuwa cemasa tayi bazai isa ba kuma ya 'kara tura mata wasu
Ana sauran kwana goma aka zo kawo kayan lefe, kawayen hajja su biyu sai yayarta da kanwar dady aliyu,
mama ta anshe su cikin mutunci dan kuwa dad ya sanar mata da zuwansu, maryam da hannatu da inna husaina su suka tayata aka musu girki kala kala,
anata raha da dariya, kuma kaya sunyi kyau sosai sai sam barka ,aka basu tukwicin kudi dubuu dari cip,
Dady aliyu yace bayason wasu events dayawa dan koda ya tambayi adnan cewa yayi shi walima kawai zai yi,
dan haka tace zata mothers day iya kawayenta,
ita dama mama walima kawai suka shirya ana gobe daurin aure.
Komawar anty maryam sai adla ta bita dan tagayawa wasu frnds dinta na chan mkrnt,
Koda mama ta tambayi adla ko adnan din yazo sai tace ai suna waya kuma yace mata zaizo,
Kuma koda yaushe cikin gyara take, na mama daban, na inna husaina daban, na anty Maryama da hannatu daban, tayi wani uban kyau tayi haske sai sheki takeyi, komai nata ya karu sbd tasha gyara,
Ranar walima akayi mata lalle mai kyau sannan taje ta gyaro kanta wannan kuwa duk aikin anty maryam ne ,dan kuwa inta itace ta tafi a haka ,da akayi walima da daddare ta zaune a daki itada anty maryam dan kuwa gidan acike yake bayan.sunyi.sallar isha'i tayi wayar ta yi ringing, ta dauka da sallama "jin muryarta yayi kamar bana mutane ba dan zaqi ,
Ya amsa da "wa alaikissalam, ya gida ya hidima ",
"Alhamdulillahi "
Kina magana da Adnan, kuma ina kofar gidanku ina jiranki ",
Tayi shiru tana tunanin dama wannan mutumin dama yasan da ita? ,dayaji shirun yayi yawa ne sai ya kashe wayar.
ta mike kirjinta sai bugawa yake ta dauki hijjabinta ta fito, fita tayi harban wajen gidan su mota dayace a wajen wata dark blue da tinted glass, ta karasa jikin motar ta 'dan kwan kwasa glass din motar, a hankali motar ta bude sukayi ido biyu da juna
[7:49AM, 2/25/2017] Halima: ```YAZANYI DA AUREN ADNAN*?
*NA UMMU SABREENA*,
*AUNTY AISHA*,


Please Login or Register in order to submit comment