Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍
💦 🌹🌹🌹🌹🌹🌹💦
*LAMARIN KADDARAR AURE NA!!!.*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing_
_by_
👇
_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

*WRITER OF*✍️👇

*ZAINABU ABU*
*ZAZZAFAR KISHI*
*LADIDIN KAUYE*
*NANCY YAR KARYA*
*JININ ABBANA!!*

*AND NOW*
*LAMARIN AURE NA!!*

_INA MIK'A GODIYATA GA RABIL IZATI DAYA BANI IKON RUBUTO WANAN LITTAFI_

_BANYI DAN WANI KO WATA BA DUK WANDA YAJI YAZO DAI _DAI DA LABARINSA TO HASASHE NE , BAN YARDA A JUYAMIN LABARI BA DUK WANDA YAYI MIN HAKA SHIDA ALLAH_

*_MARUBUCIYAR👇_*
*ZANABU ABU*
*ZAZZAFAR KISHI*
*LADIDIN KAUYE*
*NANCY YAR KARYA*
*JININ ABBANA*

*AND NOW👇*
*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA*

My fans ya zamo free domin farincikin ku🤙

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

🅿️ EPISODE 1& 2

Gidane d'an madai daici , baza'a kira masu gidan da talakawa ba ,amma sunada rufin asiri , d'akuna biyar ne , a cikin gidan , da kitchen da d'akin matar gidan dakuma bayin waje sai d'akin bak'i daga gefe kuma a cikin d'akin matar gidan d'akin mai gidan ne a ciki ,wato mu had'u a parlor sai toilet a gefe , malale gidan yake da fasasun tails ,gefe ga pampo ,wata matashiyar mata na hango tana fitowa daga d'akinta , fara amma ba sol ba sanye take da doguwar riga ta atamfa mai ruwan ganye da kwaliyar flawoyi a jiki , rigar ta zauna a jikinta sosai , ta fito da asalin kyaun ta dakuma kyan diri na cikinta , hannayenta sanye suke a awar waro wuyanta kuwa wata sark'a ce y'ar k'arama , bakinnan yasha pink d'in jan baki , a k'ala zatayi shekara ashirin da biyar 25yrs , kitchen ta nufa , tukunyar dake kan risho ta sauke ta dawo ta koma d'akinta , ta fito da jug da food flaks , kitchen ta nufa , bud'e tukunyar da ta sauke yanzu tayi , jollof d'in shinkafa ce yaji salad da carrot da albasa , sai k'amshi take zubawa , bud'e kular tayi ta zuba abincin ta rufe , ruwa ta d'ibo a randa ta zuba a cikin jug d'in , ta maida murfin ta rufe , tirai ta d'auko a kwando mai adon falawoyi a jiki ta jera abincin da cokali da plet da kula a ciki , ta nufi parlorn ta dashi , wani d'an madai daicin tebur ta ajiyeshi , kana ta koma bedroom d'inta , ta zauna a gaban stool tana kallon dressing mirror , k'ara shafawa fuskarta powder tayi tare da k'ara feshe jikinta da humra masu k'amshi ."

Daga kanta tayi ta kalli agogon dake manne a jikin bango , k'arfe tara na dare , mik'ewa tayi ta k'arawa d'akin turaren wuta ta ciro wayarta dake , chaji wata number ta danna cikin sa sanyar murya tace ”amincin Allah ya tabbata a gareka mijina , daga cikin wayar wanda takira yace ”Afnan sarauniyar mata afuwan yau nayi dare ,yanayin aiki ne amma insha Allah ganinan , zuwa mekikeso ?"k'ara rage muryarta tayi tace ”banason komai Allah ya dawo dakai lafiya ,amen yace ”daganan suka kashe wayar , bacci ne yake k'ok'arin surarta tana k'in kwanciya , jiyo bugun k'ofa tasata ficewa da gudu , bud'e k'ofar tayi , tana ganinsa ta rungumesa tana dariyar farinciki , d'agata sama yayi yace ”ammata ba kya girma ko da alamu bakici abinci sosai ba ?" naci Afnan tace tana dariya , rik'o mata hannu yayi sukayi bedroom d'inshi , temaka masa tayi da cire kayan jikinsa ,ta rakashi toilet nanma ta temaka masa yayi wanka , wanan ta zamo al'adarsu tun tana amarya yanzu gashi shekararta biyu ,amma babu wanda zai ce tayi wanan shekarun komai nata kamar na budurwa , tare suke wanka sai dai inbabu mutum d'aya hakama cin abinci tare sukeyi abincin rana ko sbda babu organ nata sai lokacin da tayi ra'ayin cinsa ."

Temaka masa tayi da shafa mai , ta dubo masa kayansa a drowa , wando gajere da farar singlet , gado ya hau zai bud'e laptop d'insa , cikin Maria raicewar murya tafara bubuga k'afa tana cewa uhm uhm my Hubby kazo muje kaci abinci , Hankalinshi ya tafi ga laptop d'in da ya bud'e , yace ”jeki ganinan , no bazan wuce ba harsai ka taso ,mik'ewa yayi tana gaba yana biye da ita , teburin data jera masa abincin sa ta nufa , bayan ya zauna ne , ta zubo masa tare da sa nata cokalin tana bashi a baki , shima hakan yake himata , har sai da suka k'oshi sanan kowa yai brush , Afnan na ganin Haisam zai wuce ,bedroom d'inshi ta rik'o masa hannu cikin shagwa6a tace ”yanzu lokacin bacci ne kadinga hutawa rayuwarka , badan Haisam yaso ba ta dawo suka wuce nata bedroom d'in ."

Washe gari ta tashi da shirin zuwa anguwa , bayan Haisam ya fita tagama komai na gidan da yazame mata farillah , misalin sha biyu na rana ,tajiyo ana bubuga k'ofa , mik'ewa tayi ta je gurin mai buga k'ofar , tana bud'ewa gabanta ya fad'i , mama ce sanye da hijabi , tasan lokacin kukanta yazo , cike da masifa mama , ta shige ciki batare da tayi sallama ba ,Afnan ce ta bi yanta ,a parlor maman ta tsaye tana k'arewa gidan kallo , mtsw taja tsaki ,tafara sababi , ga gida har gida ,amma babu y'a y'a nikam Haisamu ya kwaso mana juya , ta fashe da kuka ,

Afnan data mik'e daga durk'uson da tayi tace ”mama itafa aihuwa rabo ce , kee rufemin baki banason kinibibi , wayasani ma ko kafin auran naku kinje kinsha abinan na hana d'aukar ciki , shiru Afnan tayi ta sunkuyar da kai k'asa , inda sabo ta saba da gorin mama , amma ba'a sabo da wulak'anci , yasata fashewa da kuka mai ban tausayi, kitchen mama ta shiga hango gwan gwanin madara yasata Ciro ledar da ta sak'ale a Mara tasa cikali ta d'ibi madarar ta fito , itadai Afnan ta koma d'akinta ."

Mama na fitowa tayi waje ko rufo k'ofar batayi ba , Afnan ce ta mik'e ta fito waje , wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata , tanata zancen zuci ,ace tunda nayi aure banida kwanciyar hankali uwar miji tasani gaba , akan maganar aihuwa , ta kuma fashewa da kuka , tana cikin haka mak'ociyarta ta shigo suna mutunci sosai sunanta Fatima , mamaki ne ya kamata ganin k'ofar gidan a bud'e , shigowa tayi da sallama tace ”Afnan har yanzu baki shirya bane ,ni gashi harna gama komai , kan Afnan a sunkuye bata d'ago ba , Fatima ce ta rik'o hanunta tare da shigewa da ita d'aki suka zauna , Fatima ce tace ”ko baki gayamin ba nasan mama ta shigo amma dan Allah kiyi hak'uri ki cire wanan surutun nata a zuciyarki , Allah ne me bawa kowa aihuwa kemafa bawai baya sanki bane ya hanaki , kuma ko asibiti da kikaje kince likitar tace ”lokacine beyi ba amma zaki biye mata hankalinki yadinga tashi ?".

Afnan ce a share hawayenta tace ”Fatima kinfi kowa San in halin da nake ciki kuma kinfi kowa na anguwar nan sanin halin mama , takuma share hawayen da suka sake zubo mata race ”aurena da Haisam yin Allah bana mutum ba ,cikin tausayawa Fatima tace ”nasani amma kirage sawa kanki damuwa , tashi ki shirya muyi mu tafi , cikin fushi Afnan tace ”Fatima bazan iya zuwa ba wlh kwai kije zanje wata rana , babu rarrashin da Fatima batayiwa Afnan ba 'amma furr tak'i , haka Fatima ta wuce gida zuciyarta babu dad'i ko kad'an, bedroom d'inta ta koma ta kifa kanta akan fillo tana kuka , tana cewa ya Allah ka kawomin aihuwa cikin satinan Allah ka duba irin gorin da nakesha a gurin dangin mijina ."

Tana cikin kuka taji wayarta tana ring dubs mai kiran tayi , ganin my husband ,yasata dai daita muryata ,tace ”amincin Allah ya tabbata a gareka mijina ya aikin , dafatan babu wata matsala ko ?"dariya Haisam yayi yace ”wato ni zaki yiwa wayo ko ?"waya saminke kuka ? dariyar yak'e tayi kamar yana ganinta tace ”ba kuka nakeyi ba, kwai kai na ke ciwo , hmm Haisam yace ”badan ya yarda ba yace ”to ki kularmin da kanki , daganan sukayi sallama jiki a sanyaye , sallama taji na muryoyi da dama tasan ko suwaye , hakan yasata mik'ewa ta fito parlor su biyu ne y'ammata ,da Khadija da Aisha , taunar cingom sukeyi cikin isa da wulak'anci , Afnan ce ta k'araso da fara'arta tace ”ah sanunku da zuwa , ko kallo bata ishesu ba bare tasa ran zasu amsa mata , neman guri tayi ta zauna a gefen kujera , Khadija mai shekara goma sha biyar ta mik'e tana yarfe hannu tayi kitchen , Afnan ce ta taso cikin zafin rai tace ”gaskiya yau bazan yarda ba ,kunason wulak'anta min gida , Aisha ce ta mik'e tare da gallawa Afnan harara tace ”gidan yayan mu ne dole muyi abinda ranmu yakeso ."

Zuciya ce ta d'ibi Afnan ta wankawa Aisha mari ,da gudu Khadija ta shigo jin k'arar kukan Aishe ta cakumi wuyan Afnan , Afnan ce ta kaimata mari , dayake k'arfi ba d'aya ba , Afnan ta nad'a musu duka , girkin da basuyi ba kenan suka , wuce gida rai a 6ace , zama Afnan tayi tana girgiza k'afa , tana jiran abinda zai biyo baya, indomie ta dafa dan yunwa ce ta addabeta , tana gama dafawa ta kwashe a plet ta fito kenan ta jiyo tafiyar da bata tunanin ta kowace face ta mama , mama na shigowa ta ka6ar da abincin kana ta murjeshi a k'asa , bala'i tafara yo gidan ubanki ne kokuwa , dan sunzo ziyara gidan yayansu shine zakiyi musu duka , matsiyaciya juya kawai , Afnan ce ta dubi mama ido cike da hawaye tace ”mama menayi dahar kike jifana da wanan mugun kalamin ?"marine ya biyo bayan k'arshen maganar ta , juyawa mama tayi tana dura mata zagi."

Afnan ce ta koma d'aki rik'e da kumatu tana kuka , janyo akwatin ta dake saman durowa tayi tafara loda kaya , sai da ta cikashi tabb sanan ta d'auki hijab d'inta ta fito waje , kulle gidan , ta mik'awa Fatima mukulli Fatima da ganinta tace ”ina zuwa kuma yau , Afnan na kuka tace ”zani gidan iyayena , bazan zauna ba , Fatima cikin tausayawa tace ”karkitafi bada izinin mijinki ba ,girgiza kai Afnan tayi tace ”karkiyimin haka ,iya hak'uri nayi to yau nagaji da zagarmin iyaye da akeyi wlh , babu inda Fatima ta iya ,sabda tasan iya hak'uri Afnan tanayi , an k'ureta ne , haka ta k'ar6i mukullin ta janyo hijab a igiyar shanya tabi bayan Afnan , mashin ta tara ,sai da ta d'ora akwatin sanan ta hau tana d'agawa Fatima hannu ."

Mislin k'arfe goma na dare Haisam ne ya keta bubuga k'ofa amma shiru , cikin mamaki ya nemi guri a kan mashin d'insa yana jira Afnan tazo ta bud'e masa , yasan dai bata bacci sai ya dawo , sallamar da yaji ne ta katse masa tunaninsa , mijin Fatima ne ya mik'a masa hannu ."

Bayan sun gaisa ya mik'a masa mukulli , cikin rashin fahimta Haisam yace ”wanan mukullin kamar na gidana ?"mijin Fatima ne yace ”eh shine mai d'akin naka ce tabawa Fatima tabaka , ran Haisam babu dad'i ya kar6i mukullin ya bud'e gidan , shi ko lura ma baiyi ba gidan da kwad'o sai yanzu ."

Shiga da mashin d'in yayi ya ciro wayarsa a aljihu , ya danno lambar Afnan , jiyayi ance a kashe take , cikin tashin hankali ya bud'e parlorn ya shige bedroom d'insa , zama yayi a bakin katifar tasa cike da tunani , tun zamansu da Afnan bata ta6a tafiya anguwa bata sanar masa ba , to anya yau lafiya kuwa?" sai sak'e sak'e yakeyi a zuciyar sa , tun a hanya yakejin yunwa ,amma da yashigo yaga gidan babu gimbiyarshi yasashi ,jin komai ya ishe shi , ya had'e kai da gwuwai wa ."


*FARKON LABARI*
Afnan yarinya ce ga Alhaji Nasir , Alhaji Nasir yanada arzik'i dai dai gwar gwado , zuwa makkan shi sau biyu , yanada mata biyu , da Hajiya Zainab da Hajiya Wasila , Hajiya Zainab tanada yara biyu ,da Afnan da Salma ,Hajiya wasila nada yaro d'aya babba mai suna Usman ,duka yaran nasu sun girma kuma suna gidan aure , Alhaji Nasir yanada zafin rai sosai kuma ba kasafai yakeson ana kawo complain d'in yaransa ba , inhar kunason zaman lafiya dole kaso yaransa koda sunyi abin rashin kyautawa, kowace a cikinsu na k'ok'arin ganin sun kyautatawa y'ay'ansu ,amma baya gani , yanada wata yaya mai suna Anty Aisha , bata k'aunar matanshi ko kad'an ita kuma Allah bai ta6a bata aihuwa ba , ta tsani taga y'ay'an mutane , kuma a hakan tasami shiga , a gurin Alhaji Nasir ."

Kuma shawarar ta tana aiki sosai , acikin y'a y'anshi Afnan ce bata auri mai kud'i ba , kasancewar batada hangen nesa , kuma Allah ne ya had'ata da Haisam , a gurin wani biki da sukaje , shekaru uku da suka wuce , na k'awarta , yanayin kamun kanta yasa Haisam jin yana sonta , sun dad'e suna soyayya , kuma a soyayyarsu sunci karo da mahassada da makusa , kaf cikin dangin ,dadynta da Hajiya Zainab da Hajiya Wasila babu mai son auran , hakan yasa duk wuyar da takesha bata magana ,saboda tasan babu mai temaka mata , wata k'awar mahaifiyarta mai suna anty Ummi 'itace mai zuwa gidanta ta kawo mata abubuwan da zasu amfaneta ,kuma take tambayarta matsalar ta ,itama Rana kai mata ziyara sosai bata d'aukar lokaci mai tsayi bataje ba, Suna shiri da y'ay'an ta sosai kuma ziyartar junansu , wanan kenan ."

Suna zuwa anguwar su Anty Umma ta sauka , Ciro kud'i a jakarta tayi ta mik'awa mai mashin ,tafara bubuga k'ofar , mai gadi ne ya fito yana washe baki , gaisawa sukayi Afnan ta shige ciki , direct parlorn da zai sadata da , Anty Ummi tayi ,parlor ne tsarare yasha kayan alatu komai na gidan a in burgewa ne , inka shiga parlorn kamar karka fito saboda wani k'amshi da keyiwa mutane sallama , Afnan ganin bataga Anty a parlor ba yasata wucewa bedroom d'inta ,samunta tayi tana waya, janyo akwatin nata tayi ta zauna a bakin gado, saboda bata ban banta Anty Ummi da mahaifiyarta ba , kasancewar bata nuna mata wani abu dazai 6ata mata rai , Anty na gama waya ta zauna a bakin gadon kusada Afnan , idanun Afnan sun ciciko da hawaye ta kifa kanta a cinyar Anty , mamaki ne ya kama anty ganin akwati a gefe kuma ga Afnan na kuka ."

Anty ce ta d'agowa Afnan kai tare da jero mata tambayoyi , meyafaru mai Haisam d'in yayi miki ?kodai mahaifiyar tasa ce? "babu tambayar da Afnan ta amsa sabida kuka yaci k'arfinta ,cikin tausayawa anty ke kallonta tana girgiza kai , Anty ce ta shiga toilet ta had'a mata ruwan zafi ,ta bud'e mata sabon brush da man goge baki , ta tara mata ruwa a bahon wanka ....✍️.

Idan naga comments zan cigaba ,saboda kune na maidashi free , rashin sharhi zaisa ya zamo na kud'i🤙.
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

*MARUBUCIYAR👇*
*ZAINABU ABU*
*ZAZZAFAR KISHI*
*LADIDIN KAUYE*
*NANCY YAR KARYA*
*AND NOW*👇
*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA*

*DOMIN KU YASA NA MAIDA WANNAN LITTAFIN KYAUTA👌RASHIN SHARHI ZAI SA NA MAI DASHI NA KU'DI*

WATTPAD momislam2020
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

🅿️EPISODE 3 & 4

Taji dad'in wankan , ta fito d'aure da tawul dakuma wani a kanta, Anty data ciro mata kaya a 'akwati masu kyau tace ”kshafa mai kiyi kwaliya inkin gama ga abinci can a dining sai muyi magana , to tace ” ta je gaban dress mirror ta shafa mai da powder , ta sanya janbaki da kwali , ta d'auko kayan da Anty ta za6a mata , riga da skirt na atamfa ,dinkin ba k'aramin kyau yayi mata ba , dama itan mai kyauce ,kowane kaya tasa sai ya amshi jikinta , mik'ewa tayi ta fito daga bedroom d'in tabar Anty da sak'a da warwara , dining ta nufa ta bud'e food flaks d'in wani tashin k'amshi tayi a duka kulolin macaroni ,ce da taji kayan lambu sai farfesu a gefe rufe na farfesun tayi ,tafara cin abincin sai da ta k'oshi sanan ta bud'e farfesun tafara ci , tana gamawa tasha lemun kwakwa ta mik'e ta koma parlor , y'ar aiki ce tazo ta kwashe kayan tayi dasu kitchen , anty na bedroom tana zaman jiran Afnan ,batasan Afnan ta koma gaban TV ba , MBC 2 take kallo film d'in yasata nishad'i sosai , hakan yasata mancewa da wata damuwa da take ciki."

Fuskarta yalwace da murmishi ta gyara zamanta tare da maida hankalinta ga TV , Anty ce ta fito da wayarta daga hand bag d'inta ,ganin a kashe yasata kunnawa , tace ”oh ko menene yasa Afnan fushi harta kashe waya oho , Anty na cikin tunani taji Ring d'in wayar , ganin sunan my Husband ,na yawo a screen d'in wayar yasata mik'ewa da sauri , ta nufi parlor , ganin Afnan na kallo yasata kuma harda dariya ,yasata tsayawa ,tana kalonta , wayarce ta kuma ruri a karo na biyu , hankalin Afnan ne ya juya ga gurin da tajiyo k'arar wayar ta , kalon kalo sukayi da Anty ta sunkuyar da kanta k'asa , k'arasowa Anty tayi kana ta mik'a mata wayar ,tace ”ki amsa man , d'agawa tayi cikin sanyin murya tace ”Aslamu Alaikum , wa'alaikissalm ,yakike ina kika shiga nazo gida bakya nan ?"shiru Afnan tayi can kuma tace ”gobe zan dawo , ran Haisam in yayi dubu ya 6aci ,Afnan ba k'aramin 6ata masa rai tayi ba , ajiye wayar yayi batare da yakuma magana ba ya fad'a gado zuciyarshi na k'una , da tunani iri iri ."

K'arasowa Anty tayi ta zauna a kujera mai kallon ta Afnan ta d'auki remote ta kashe TV , Afnan maiyasa zaki bar gidan mijinki ba tare da izinin shi ba , kuma ba tare da kinyimin waya ba¿"eh tambayarki nakeyi , Afnan idanunta zun ciko da k'wallah tabawa Anty labarin dalilin tahowarta , Anty ta tausaya mata sosai ,musamman ma akan gorin rashin aihuwa , amma Allah maji rok'on bawansa sekaga Allah ya kawo , Anty ce tace ”to yanzu dai tunda dare yayi mubari zuwa gobe ,in Allah ya kaimu sai in maidaki ,to Afnan tace ”tare da mik'ewa ta nufi wani d'aki da ban na y'ammatan gidan kasancewar sunyi aure, juyi takeyi a gadon rungume da pillow ,da rasa abinda ke yimata dad'i , hawaye ne masu zafi suka kwaranyo mata , tace ”ko ya Haisam zaiji inyazo yasamu bananan sai Allah , tuno Fatima mak'ociyarta tayi , da tace ”Afnan karki tafi batare da sanin mijinki ba , ina idanunta sun rufe, lokacin tana cikin tsananin 6acin rai ,kuma juyawa tayi taji sam kwanciyar babu dad'i ,tasaba dajin d'umin mijinta yanzu kam komai komai ya kwance mata , tarasa washe shawara zataba zuciyarta , tsananta kukan tayi amma ba'a jiyo sautin sa sosai ."

Washe gari tun misalin k'arfe hud'u na asbha ta tashi ,tayi wanka tayi alwalah ,tafara jero nafil fili ,tanata kai kukanta gurin Allah , tana idarwa ,ta koma gaban dress mirror ta janyo stool d'in ta zauna tare da cire d'an kwalin kanta tafara tsara kwaliya , dama gwanace , tana gamawa ta feshe jikinta da turare kasancewar ba bu inda zataje daga nan sai gidanta , batajin ma zata iya yin breakfast ,a gidan Anty saboda kewar mijinta takeyi ,jiyo kiraye kirayen sallah tayi daga masallatai da dama , hakan yasata sanya hijab tabi wani masallaci sallah , suna idarwa ta yi adu'a ta shafa ta cire hijab d'in ta

Please Login or Register in order to submit comment