Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aura d'ankwalinta , ta yafa gyale ta fito parlor ,gidan shiru kamar ba mutane , dake Anty ce da y'ar aiki ,kawai a gidan mijinta yatafi k'asar waje , sai kuma drivers da masu bawa flawoyi ruwa , zama tayi a parlor rik'e da hand bag d'inta da wayarta a hannu , jiran fitowar Anty takeyi amma shiru , daurewa tayi ta nufi kitchen ,ta tsiyayo ruwan zafi a flaks tasa lipton ,da madara da da sugar ta dauki biscuit ,tadawo parlor ,tana sha , harta gama sha Anty shiru , kuma mik'ewa tayi ta nufi bedroom d'in anty tafara nocking , tare da sallama , Anty da tayi sallah yanzu take shirin komawa bacci tace ”daughter lafiya kuwa?".

Lafiya Anty ceawar Afnan , inason komawa gida ne ,murmishi Anty tayi mai cike da maganganu sai kuma naji tace ”to babu damuwa jekiyi breakfast ,yanzu zanyi wanka , nayi cewar Afnan ,to ki jirani ganinan fitowa , to kawai tace ”ba haka taso ji daga bakin Anty ba ta koma parlor tacigaba da zaman jira ,tana kwance a parlor har k'arfe takwas kuma tasan k'arfe goma Haisam yake fita, tana shawarar tashi sai ga Anty nan ta fito sanye da doguwar riga pink color mai adon fararen stone a jiki , kanta tayi rolling d'in d'ankwalin , tayi kyau babu lefi , kasancewarta fara , zama tayi kusada Afnan tace ”daughter ,na d'auka zaki yimin kuwana uku ne , gimtse fuska Afnan tayi batare da tak'ara magana ba , Anty ce tace ”to mik'e mutafi tunda sammako zamuyi , amma biyoni d'aki daganan saiki d'auki akwatinki, rufawa Anty baya tayi suka zauna a bakin gado , Anty ta rik'o hanunta tace "daughter jeki bud'e bed site ki d'aukomin wata leda , mik'ewa Afnan tayi ta bud'e ta ciro ledar ta mik'awa Anty , kar6a Anty tayi ta bud'e ledar , ciro wata gorar Zuma tayi tace ”wanan ke naketa ajiyewa su sauran sun kar6i nasu so wanan karki wasa dashi , cokali biyu zaki dingasha ,safe rana dare , ta ciro wata roba mai dabino da kwakwa da Zuma a manne, tace ”wanan gumba ce karkiyi wasa , nasan ta 6angaren mijinki bakida matsala to karkiyi wasa gurin kyautata masa kuma kirik'e shan magani akan jari gadiya Afnan tayiwa ,Anty suka mik'e suka fice , direct gurin motocin gidan suka nufa , da gudu driver yazo ya durk'usa ya gaida Anty Ummi , da Afnan , Anty ummi ce ta nuna masa motar dazasu hau ,cikin azama ya fito da motar tare da bud'e musu back side, suka shiga."

Sunyi tafiya sanan suka iso gidan , Anty a duk lokacin da tazo unguwarsu , Afnan sai ta jinjina kai , to yauma kamar kulum girgiza kai tayi ,saboda anguwar talakawa ce sosai , banda so gamon jini mezai kawo Afnan anguwar nan da gatanta ,ga mahaifinta shahararen mai kud'i, kasancewar drivern yasan gidan Afnan d'in yasashi parking ,a k'ofar gidan, farinciki fal zuciyar Afnan zataga rabin ranta , harta mance wulak'ancin da ya sanyata fushi , jin Anty ta bud'e murfin motar yasata yunk'urowa ,Anty na fita itama ta fito suka kulle , motar da isarsu k'ofar gidan suka fara nocking , sbda ko da Afnan take nan bata barin k'ofarta a bud'e , jin ana zare sak'ata ,yasasu gyara tsayuwar su , Haisam ne yafito da fara'arsa , yana musu sannu da zuwa ,Anty ce ta amsa Afnan ta kasa koda had'a ido dashi , kai tsaye cikin gidan suka wuce , ko ina fess babu datti , Haisam ne ya d'auko key ya bud'e k'ofar d'akin Afnan su Anty suka shiga , d'akin natama babu datti ko kad'an sai tashin k'amshi yakeyi , da sallama ya shigo ya durk'usa ya gaida Anty Afnan cikin jin kunya ta gaisheshi , ,ya mik'e ya fita, anty ce ta k'ara yimata tuni akan ladabi da biyayya dakuma iya kalami mai sanyaya zuciya , dakuma iya sarafa miji a lokacin da yake cikin 6acin rai , kowace nasiha ta Anty ta zauna daram a kwakwal war Afnan , anty ce tace ”to inaso yau kisha wanan abin dana baki karkiyi wasa dan Allah , to Afnan tace ”Anty ta ciro kud'i zasuyi 20k tabawa Afnan , sosai Afnan taji dad'i , daganan Anty ta fito , tana shirin sa takalmi saiga Haisam ya shigo da alamu fita yayi da k'atuwar leda bak'a a hanunsa , yana ganin Anty yace ”dan Allah Anty ki koma Ante na dariya ta koma ciki ,ta zauna a parlor , Afnan ce ta fito da hijab tana shirin raka Anty mota , ganin Haisam ya ajiye leda ya fita ,yasata bud'e ledar ta lek'a ,dariya Anty tayi tace ”to sarkin kwad'ayi abin nema ya samu ,Afnan tasa dariya , dawowa yayi da plet a hanunsa ya bud'e ledar ya fitoda kaji manya gasasu da ,lemun gora maltina da viju milk da fanta , kasancewar a ya yanke suke yasashi zubawa a babban plet yace ”anty dan Allah kici , Anty na murmishi ta d'auki yanka d'aya ta jefa a bakinta ta mik'e tace ”Allah yayi muku albarka , Haisam dan Allah aci gaba da hak'uri , Afnan tabi bayanta ."

Sai da motar ,Anty ta 6ace Afnan ta dawo gida da kuka , fad'awa jikin Haisam tayi tana kuka ,Haisam da yana fushi da Afnan ,ganin tana kuka yasashi rungumota , tafara share mata hawaye , ganin tak'i dena kukan ya sa6ata a baya yana yimata wak'a yana cewa "wanene ya ta6amin y'ar baby na ,inkamashi , Afnan ta tuntsire da dariya , tafara yimasa cakul kuli yana zulewa , sauketa yayi , yana dariya , filon kujera ta wurga masa aikuwa suka fara karad'e gidan da dariyaku suna gudu , wanan ya jefi wanan haka dai suka dingayi, suna haka har k'arfe , 11 pm tayi basu sani ba ,jin shugowar mutum sukaji babu sallama , cikin masifa tafara zazzaga ruwan bala'i ,tana cewa " yanzu Haisam asirin da sukayi maka harya fara tasiri a kanka? " to bazan yarda ba , tsabar rashin aikinyi shine ka biye mata kuke wasan banza kamar awakai ?to wlh ko kazo ka tafi aiki ko kaci gidanku , parlor mama ta shiga , ganin gasasun kaji baje a faranti yasata zare ido tace ”kai Haisam abinda kukeci kenan?"nashiga uku ni Lauratu , tadama abinda kuka koma ci kena?tabb hmm lallai ashe mallakar tafi haka ?" yana shirin magana ta wanka masa mari , tace ”maza kazo gida ina nemanka , munafuka tun kafin yasami mai gadonsa shine kikeson tatseshi ko dan kinga ke juya ce bakya aihuwa, ko wata tazo kartasami ragowa , kuce ma kundena cin hatsi saimu talakawa , Afnan ce ta rufe baki ta shige bedroom d'inta da gudu tasa key ."

Haisam zai bita mama ta dakatar dashi tare da cewa kana binta walhi sai kayi nadama , lashe maka zuciya tayi ?"kokuwa tsoronta kakeji ?niban isa inyimata fad'aba kenan ? ta jero masa wa'inan tambayoyin , tabbas dayasan ,mama zata shigo a dai _dai wanan lokacin da bai tsaya a gidaba dayayi sammakon fita , mama ce tace ”tattaro min naman da lemon duka ka k'ullemin su a leda , cikin rawar jiki Haisam ya tatara ya k'ulle ya mik'awa mama ,tana k'ar6a ta fice tana kaiwa tsakar gida tace ”saura karka taho mutafi wlh zakaga abinda zai biyo baya, tana tafiya ,Haisam yayi hanyar d'akin Afnan yana bubugawa , yana cewa "dan Allah ki bud'e ki saurareni Afnan , kuka yaci k'arfinta tace ”kaje kiran mama kaje kawai , Haisam tun yana tsaye harya gaji da tsayuwa ya fice, daga gidan zuciyarshi babu dad'i, mashin d'inshi ya tayar ya nufi gidan su , gidane k'ato daga ganin gidan zakasan gidan yawa ne mutane ne a ciki zasuyi biyar kowa da d'akinsa , d'akin mama shine farko sai d'akin kishiyarta da tarasu tabar yara sune y'ammatan da sukayiwa Afnan rashin kunya , mama iya Haisam ne yaronta ,ta d'auki son duniya ta d'ora masa sai dai ba kasafai takeson wani yaci arzikinsa ba , aciki kuwa harda mahaifinsa da matarsa , hakan yasa take taka tsan tsan da komai nashi kuma koda ya kawo yace ”tabawa mahaifinshi zatace to ,yana fita ta 6oye , yanzu kam harya zame mata jiki ,kuma dole mahaifinshi yake hak'uri da Halinshi , kowa na gidan yasan masifarta bata barin kowa , sallama Haisam yayi a k'ofar d'akin maman nashi , ko amsawa batayi ba tace ”inka gama munafurcin naka kashigo , shigowa yayi jiki babu k'wari ya zauna a tsakiyar d'akin da aka shimfid'a tabarma kasancewar babu leda a d'akin , yai shiru , kagama bata hak'urin ?"nace kagama bata hak'urin ?"eyee ? kan Haisam na k'asa bai d'ago ba yace ”kiyi hak'uri mama , dakata cewar mama , banason ban hak'urinka banason duk wata kalma dazata karyamin zuciya tunda kai bakasan zuru ba ,wlh Haisam ka kiyayeni , kokuma nayima!!!, Haisam ne ya matso ya katse mata maganar ta hanyar shafa hanunta a fuskarshi , kawar da kai mama tayi , sbda inta fara sababin fad'anta to batajin gari."

To kiyi hak'uri mama dan Allah ,shiru tayi tana girgiza k'afa tace ”ai na hak'ura tunda har gashi zanyima albishir da sabuwar matar danayi ma , ehee?" waro ido mama tayi tace ”kajimun wulak'anci ni sa'ar wasanka ce ?to aure zakayi budurwa mai aihuwa Allah yasama aihuwar fari ta haifo mana y'an biyu , mama na maganar tana dariya , Haisam da zuciyarshi ke bugawa hankalinshi ya tashi ,ya dubi mama tare da had'e hanuwanshi biyu yace ”dan Allah dan girman Allah mama kiyi hak'uri ki janye maganar nan, shek'ewa da dariya mama tayi tace ”walahi sai kayi aure kaji na rantse ,bazaka zauna da juya ba kana cefane tanaci tana zuwa kashi , yanzu ma iskancin da kuka d'aukarwa kanku ,kundena cin abinci sai naman kaza ,ni gani a nan a bushe kukwa kunyi dumur mur , Haisam zaiyi magana mama ta dakatar dashi da cewa , nasan mezakace ,dan haka inason ayi bikin nanda wata biyu ai nasan jarin shagon yanzu ya bunk'asa da wacan juyar na aihuwa ai da yanzu ka kaini makka....✍️.
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

*Rashin sharhi zaisa ya komai na kud'i👌.
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

🅿️EPISODE 5 & 6

Sunkuyar da kai k'asa Haisam yayi yace ”ki k'ara hak'uri mama ,insha Allah Afnan zata haihu , banzan kallo ta watsa masa ,kana tace ”ubanwa kafi sanin tin tini ?"aure babu fashi na rantse da Allah kamar kayishi , cikin sanyin jiki Haisam ya mik'e tare da gyra hular kansa yace ”mama nabarki lafiya , ko kalonsa batayi ba , ya fice ,mashin d'insa ya hau kana ya nufi gidansa , samun k'ofar gidan a bud'e yasashi sanin , Afnan bata fito ba , to har yanzu 6acin ran ne , ya tambayi kansa , kulle k'ofar yayi yasa sak'ata kana ya nufi cikin gidan , yana shiga direct ya wuce parlorn da zai sadashi da ita , yana shiga parlorn ya ganta ,a kwance a kan 3 sitter idanunta , na kallon sama , d'ago mata kai yayi yace ”my sweetheart , inata sallama amma baki kulani ba ?"maida kalonta tai zuwa gareshi , da fararen idanunta masu rikitashi , batace komai ba , Haisam , daya shiga damuwa ganin 6acin rai k'arara a fuskar ,Afnan ya kuma janyota jikinta ya zauna a gefen ta ya d'orata a kan cinyarsa yace ”dan Allah kiyi hak'uri , tabbas abinda mama tafad'a bai dace , ba kinsan kuma mahaifiya dole nayi mata biyayya , Afnan ce ta shafo gefen kumatun Haisam ,tace ” abin alfahari na karka damu , nice nace ina sonka kuma har gobe bazan dena sonka ba , cikin farinciki ya had'e hannayensa biyu alamar godiya , ya rik'o hanunta ya mik'ar da ita , kana yace ”zo mushiga kitchen inkuma bazaki iya ba , ni barinje ko ruwan zafi in dafa miki."

Hanunta ta rataya a kafa d'arshi suka nufi kitchen , indomie suka dafa da suka soya k'wai , kana suka juye a plet suka nufi parlor , zama tayi a kan kafet d'in da ya mamaye tsakiyar d'akin ,shima ya zauna kusa da ita , sai da suka gama ciyar da junansu , hira sukeyi ,cikin nishad'i kamar ba ita ta gama kuka ba , saboda faranta mata yasashi k'in fita aiki sunata gwada wa junansu soyayya , sauya salonsa yayi zuwa had'e bakinsu guri d'aya ganin hakan yasa nabasu guri , a duk lokacin da Haisam ya sami nutsuwa da Afnan , yana sanya mata albarka fiyeda tunani dan jinta yakeyi kamar sabuwar amarya , wanka sukayi a tare suna fitowa suka shafa mai mai k'amshi , Afnan ta sauya kaya zuwa doguwar riga milk color mai adon flawoyi , Haisam da yayi shigar k'ananun kaya shima yai kyau sosai , turare Afnan ta d'auko a gaban dress mirror ta fesa masa turare ,tace ”gaskiya my man kayi kyau sosai ,karfa y'an mata su kallemin kai , dariya Haisam yayi tare da rungumo Afnan yace ” tabb babu mai kallo na kedai ki kularmin da kanki , kiss ya manna mata a goshi tayi masa Allah ya tsare , yana fita ta sakawa k'ofar sak'ata ,ta koma bedroom d'inta tafara gyara gado , ta goge ledar d'akin tare da goge gadonta , kasancewar ta mace mara son k'azanta , komawa parlor tayi tafara sharewa ta goge ta goge TV , ta koma tsakar gida ta share takuma wankeshi fess , ta sa turaren wuta mai k'amshi , cikin k'an k'anin lokaci gidan yad'au k'amshi , tana shirin wanke _wanke , taji k'arar buga k'ofa , k'in tashi tayi dan tasan bazai wuce mama ba , kuma yau batada niyar k'unsar bak'in ciki , dan haka tacigaba da aikinta , cikin d'agun murya akace , Fatima ce fa ,da gudu Afnan taje ta bud'ewa Fatima k'ofa tareda k'yal k'yalewa da dariya suka shige parlor , zama sukayi ,Fatima tace ”matsoraciya ,kindawo ko magana babu ?"Afnan ce tace ”ke my man ne yabani tausayi , kuma nayi kewarshi so kinga dole in damu , cikin mamaki na soyayyar su Afnan Fatima tasa dariya kana tace ”masoyan asali , nima da Umar zai yarda da mundinga soyewa , suka kwashe da dariya , Afnan ce tace ”ban gane ba kina nufin ko irin shagwa6ar nan bakya yimasa ?".

Fatima ce tace ”mutum sai kiga ya shigo gida babu fara'a ,to yazan yi masa?, gyara zama Afnan tayi kana tace” to yanzu dai ya kamata kisani ,kwaliya da tsafta itace ginshik'in komai , musamman in kika had'a da k'amshi , kuma sai abin yafi bada kala, agogo Afnan ta duba k'arfe hud'u na yamma , hakan yayi dai dai da shigowar ,wata budurwa mai jiki bak'a , kai tsaye ,d'akin dasu Afnan suke ta zarce, samunsu tayi itada Fatima suna hira,wani irin kallo tayi musu , budurwar tace ”wacece Afnan?" Afnan da gabanta yake fad'uwa ta kalli Fatima , Fatima ma ta kalle ta , tace ”to malama babu sallama babu gaisuwa ,sai nema?"girgiza budurwar tayi tace ”to ai ba ita ta kawoni ba dan haka matar gidan nakeson gani, Fatima da Afnan suka mik'e ,Afnan tace ”nice mai gidan ,mai kikeso ?"budurwar ce tace ”tunda naga mai gidan ai magana ,ta k'are , ta juya ta fice, mamaki ne ya kama su Fatima suna bak'in cikin dalilin da yasa basu nakad'a mata duka ba , amma babu komai ,Afnan tace ”idanunta cike da hawaye , Fatima da tsoron kar a yimusu duka yasata ,raku6ewa gefe , tana shan majina kamar wacce taci abinci mai yaji ,tace ”Afnan sai hak'uri."

Haushi Fatima taba Afnan, wani mugun kallo tayi mata kana tace ”dama kamaki tayi ta sambad'eki , kekam anyi ma tsoraciya , tsoro yayi miki yawa , neman Fatima tayi ta rasa , komawa parlor tayi ta zauna a gefen hanun kujera , ta fara tunanin wanan budur war , to daga ina take ?" mik'ewa tayi dan tasan inta tsaya tunani ,har Haisam ya dawo batayi komai ba ,tsin tsiya ta d'auka ta kuma sharo ko ina na d'akin , dukda dai ba datti yayi ba , tasa turaren wuta , takuma fesa room freshner ad'akin , komawa toilet tayi ta wanke nata ,kana ta wanke na d'akin ,Haisam tana gamawa ta shige wanka, lokacin k'arfe 7pm tayi alwalah ,ta fito ,tanayin sallah ta zauna tsara kwaliya , dama tayi girkinta , mayukanta masu k'amshi ta shafa ,kana ta shafa powder ,tasa janbaki da gazal ta sanya kwali , tayi kyau sosai, mini skirt d'inta da ya tsaya mata iya gwuiwa tasa ,mai kalar pink sai farar riga , fara mai yan kaken hannu iya cibiya , ta kama kanta da yake a tsefe da abin kama gashi ,ta sanya pink d'in hula ,a gaban hular an rubuta my baby ."

K'ara feshe jikinta tayi da had'a d'un humra masu tada hankali ,ta zauna jiran , kiran sallahr isha'i , bayan wasu mintuna ,tajiyo kiran sallah ,hakan yasa ta mik'ewa , ta fara gabatar da sallaha , tana idarwa ta fara salatin annabi tare da kwararo adu'oi na bud'i dakuma k'arin soyayya a gurin mijinta , bayan ta kammalah ,ta nad'e abin sallar, ta d'auko wayarta dake jone a charge ,ta fara duba number Haisam ,cikin sa'a ta shiga , yana d'auka kafin tayi magana carab ,yace ”gimbiya yakk ya gida ?dafatan dai babu wata matsala ko ?"rage sautin muryarta ,tayi kana tace ”uhm ni ka barni sai kewar kallon fuskarka nakeyi ,yasan dole sai an lalla6a ta ,dan haka yace ”to ayimin hak'uri gani nan insha Allah yanzu ."
Dariya tayi ,tace ”fatan alkairi mijina Allah ya dawo min dakai lafiya , amen yace ”ki kulamin da kanki, I love you , kashe ido d'aya tayi kamar yana ganin ta tace ”love yau 2, kallo ta kuna ,a tashar MBC 2 wani film da suka sa ne a ja hankalinta , har k'arfe ,tara a rabi, jin k'arar mashin d'in Haisam ya sata mik'ewa, ta 6oye a jikin labule , sallama yakeyi shiru , baiji anyi magana ba ,my baby ina kika shigane ?"da gudu ta rungume shi tana ,oyoyo mijina , d'a gata sama yayi ya mai data bayan sa ,yana juyi da ita kamar yarinya, rad'a masa tayi a kunne "zomuje muyi wanka, shima cikin rad'a yace ”ba yanzu ba , sauka tayi a bayan nasa, taje bayi ta d'auko bucket ,ta zuba masa ruwan tare da sirkawa, tana shiga ta ganshi zaune da alamun damuwa , zama tayi kusa dashi tace ”mijina lafiya kuwa naganka haka?" babu komai yace ”ya kalle ta ,komai nata birgeshi yakeyi ,amma mama zatace ya k'aro aure ,gaskiya shikam ba 'ayi masa adalci ba ,Afnan ta lura akwai abinda ke damun mijinta dan haka ,ta mik'ar dashi ,tare da cire masa ma6allin rigarsa , jikinshi yayi sanyi matuk'a ,tunda ya tuno da hukuncin da mama ta keson yankewa."

Haka dai jikin nasa babu k'wari ta temaka masa yayi wanka, yana fitowa ta fito masa da kayansa , ya Sanya , marasa nauyi , zubo masa macaroni tayi a plet , wace taji kayan k'amshi da albasa, sanin baya cikin han kalinshi ya sata d'aukan cokali tafara bashi a baki , ci yakeyi kamar mara lafiya , hakan sam bai yiwa , Afnan dad'i ba, cikin zuciyar ta tace ”zan bishi a hankali insha Allah zai fad'amin koma menene ,ganin har yanzu yak'i sakin jikinsa yasata ,fashewa da kuka , kasancewar ta mai saurin kuka , kallonta yayi cikin tashin hankali ,yace ”mai kuma ya faru”mik'ewa tayi ta shige bedroom ,ko kulasa batayi ba , damuyoyi biyu kenan , Haisam ya ce lokacin da ya mik'e zuwa bawa Afnan hak'uri , ranta ya 6aci matuk'a saboda a rayuwarta bata son tayiwa mutum magana ya shareta , shikam Haisam oga ne ,bakin gado ya zauna tare da janyota jikinsa yana shafa gashin kanta , k'arfin hali kawai, ya keyi, amma ba dan zuciyarsa na yimasa dad'i ba, shuru tayi kamar ba ita keyin kukan ba , ta d'ago ido tana kallon sa ,murmishin dole ya k'ir k'iro , hakan yasa ta maida masa da murmishin , haka dai ya samu ya lalla6a ta har bacci mai nauyi yayi nasarar d'aukarta, gyara mata kwanciya yayi tare da lulu6eta kasancewar ,garin ana sanyi , ya mik'e a hankali ya ,koma bedroom d'insa , zagaye d'akin ya shiga yi yana mai k'ara tuno kudirin maman nashi , tausayawa Afnan yakeyi ,ya koma ya kwanta ,bacci 6arawo ya kwashe shi ,k'arfe kiran sallahr farko a kunnen sa , hakan yasa shi yin adu'ar tashi daga bacci ya shiga toilet ya d'auro alwalah , sai da yayi nafil fili sanan ya ,tafi d'akin Afnan , ya kwanta gefenta yana shafa fuskarta ,tare da hura mata iska ,bud'e ido tayi ta sakar masa murmishi ,shima hakan yayi mata ,yace ”lokaci yayi nisa kitashi kiyi sallah."

To tace ”masa ganin zai tafi ne tace ”Allah ya dawo min dakai lafiya mijina , amen ya Allah my honey, cewar Haisam lokacin da yake shirin sa takalmi,kasancewar yana dad'ewa a masallaci , yasata kunna risho ta d'ora ruwan zafi ta dawo tayi alwala ,tayi sallah tana idarwa ,bayan tayi adu'oin ta , da ta saba , ta mik'e ta fara da gyra gado ta tsaftace ko ina tasa turaren wuta mai k'amshi , juye ruwan wankan tayi , ta shige toilet tayi wanka, tana fitowa ta koma kitchen ,ta juye wanda ta mayar , jin shigowar Haisam , tayi yana shigowa parlor ta durk'usa tace ”barka da safiya my man , da fara'arsa yace ”gimbiya ta kintashi lpy , lafiya Lou tace ”ruwan wanka ya kammalu yana toilet , okay Haisam yace ”please zamuje ki tayani cire kaya, mik'ewa sukayi rik'e da hanun juna , suna gama cire kayan, ya shiga wanka ita kuma ta fara kwaliya bayan ta d'ora shayi a kitchen, riga da zani ta sa na atamfa mai ratsin green da fari sai d'ingon bak'i a gefe , tayi kyau sosai ,d'akinsa ya wuce sai da ya gama shiryawa , sanan ya fito sanye da k'ananun kaya , sun amshi jikinsa kasan cewa shi fari dogo kya kyawa ,wow mijina wanan kyau haka?" dariya yayi yace ”kai matar Haisam wanan kashe kala haka , kamar zamuje , rufe masa baki tayi tace ”na gama tea madara da sauran su zan sa ,so me za'a dafa indomie ko doya da k'wai , kawai kiyi indomie and egg zai fi sauri , ficewa Afnan tayi ta fara hidimar girki , misalin k'arfe 9am ta kammala komai ta jerasu a tebur da cokula da cup , suna karyawa suna hira , Haisam ne ya mik'e tare da cewa ni zan tafi , ki kularmin da kanki , Allah ya tsare Allah ya bada sa'a , amen Haisam yace bayan ya bata kud'in cefane ya fice , kwashe kwanukan da suka gama breakfast tayi ,kana ta wanke su ta dawo ,ta kunna kallo ,misalin k'arfe uku na rana , taji alamar bugun k'ofa , mik'e wa tayi ,dan bacci ma takeyi sbda tana fashin sallah , k'arasawa tayi , bakin k'ofar , ganin k'anwarta Salma yasata fad'ad'a fara'ar ta ."

"Tace my sis barka da zuwa , d'aukan yaron tayi mai suna Sudais suka k'arasa parlor, suna zama Salma ta ,yamutsa fuska, kana tace ”yanzu sis wanan rayuwar da kika za6awa kanki yayi kenan, kin zauna gidan talaka yana baki wuya

Please Login or Register in order to submit comment