Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya had'e hannayensa biyu , gwada lambar wayarta tafara dan yana son suyi maganar hidimomin da za'ayi a biki to gashi a kashe ranshi ne yakuma 6aci sai ya fara duba lambar momy , cikin sa'a ta shiga."

Ring d'aya aka d'aga muryar momy ce dan haka ya sa ssaura muryasa tare da d'an risinawa barka da yamma momy , ywwa "barka dan Allah Afnan na kusa?" a 'a batanan , shiru yayi can kuma yace "to ya kashe wayar , momy ce ta fito parlor dubata amma batanan komawa bedroom d'inta tayi ,ta hangota a nannad'e a gado fuskarta sharkaf da hawaye , da sauri momy ta k'arasa kusa da ita tace " daughter meyafaru?babu komai momy ,to maiya faru naji kiran Abdallah yana nemanki fad'a kukayi ? a'a momy , momy ce ta had'e rai babu alamun wasa tace "ni mahaifiyarki zaki 6oyewa damuwarki ko ?mik'ewa Afnan tayi inda abinda ta tsana bai wuce fushin momy ba dan haka batason fushinta , momy kwanannan Abdallah ya tsiromin da abubuwa marasa kyautawa ,shine da rungumata ,sai kuma tayi shiru murmishi momy tayi a ganinta tana ganin y'arta zatayiwa matarsa zarra ,karki damu daughter , momy tace " cike da nishad'i , yau saura kwana nawa ne bikin ?saura kwana goma fa kwantar da hankalinki , daganan momy ta mik'e ta fice , Afnan ta kasa fassara maganar da momy tayi mata ...✍️.

Kardai Ku manta karku jini shiru ne yasa nayi muku wanan , kunsan dai haryanzu ban dawo ba , dukda yanzu andena comments ina tunanin zanbarshi sai zuwa bayan sallah kawai 👌tunda Baku nuna damuwa ba⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️⛷️


💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 25 & 26

Ganin cikin Maimunatu yafara girma yasa Haisam fara kula da Maimunatu , hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba , tana ganin yanzu ya dawo sonta ne sosai , yau juma'a Haisam na zaune a kasuwa yaji wayarshi na ring cikin azama ya ɗauka ,jiyayi ance "kai ne Haisam ? eh nine Haisam yace "cikin rawar jiki duk da bai san mai kiransa ba ,amma yana tunanin alkairi ne ,malm Haisam muna nemanka a shagon mu na sai da turaruka muna odar su daga Dubai abokina ne ya bani lambarka , gaskiyarka da riƙon amana yasa nayi maka magana , cikin rawar jiki Haisam yace "to nagode ya waiga ya kalli ƴan tsirarun kayan dake jere a shagonsa kayan kwaliya ne basuda wani yawa amma Allah ya sanya masa albarka a cikin sana'ar ."

Ya naji kayi shiru ?babu komai Haisam yace sukayi sallama , Haisam na ajiye waya yafara saƙa da warwara anya zai yarda da ƙudirin mutumin nan ? baisan ko waye ba hmm , ya zurfafa cikin tunani yaji sallamar Abubakar babban abokinsa yanada shago a nan kasuwar jos ɗin wato ƴan tifa yana sana'ar sai da atamfofi ,shima yanada katafaren shago babba kuma suna bada sarin atamfofi , gefe kuma takalma ne masu kyau da tsada , Haisam abokina ya kiraka ?" Haisam ne yace "eh ya kira "to ka amince zaku fara kasuwanci tare ? uhm Haisam yace " bawai naƙi bane amma inason kasani wanan ɗan akurkin shagon da nake rainawa yana rufamin asiri ina tunanin ranar da Allah zai yi ikonsa ya zamo bana wancan shagon kaga akwai damuwa ,

Abubakar ne ya taɓi kafaɗar Haisam kana yace "karka fara wanan tunanin abokina insha Allah bazakayi kuka da Alhaji Jamilu ba ,mutum ne na mutane kuma bashida ƙeta , to Haisam yace "Allah ya zaɓa mana abinda zai zamo alkairi , amma bazan bar shago naba dole zan nemi mai zama a ciki , daganan sukayi sallama kowa ya kama gabansa ."

Haisam ne ya tada mashin ɗinsa bayan ya rufe shago duba agogon hanunsa yayi ƙarfe biyar na yamma , hakan yasa shi ɗaukar titin da zai sadashi da gidan sa , yana isa ya kashe mashin ɗin tare da tura ƙofar kasancewar Maimunatu ba rufewa takeyi ba ,ya shiga da mashin ɗinsa ya kullo ƙofar , da bayan ya jingine mashin ɗin ya nufi ɗakinsa ya kwanta batare da ya doshi ɗakin Maimunatu ba , da shigowarsa da komai Maimunatu na gani ta windo."

Yunƙurowa tayi da ƙaton cikinta a ƙalla zaiyi wata biyar ta gyara ɗaurin zaninta , saukowa tayi daga gadonta kana ta fito palo , ganin yamma tayi bata ɗora komai ba yasata jan dogon tsaki tace "wanan wace irin rayuwa ce ga ciki ga aiki ni wlhi bazan iya ba sai kace wata baiwa , haka dai ta ƙarasa ɗakin Haisam ta tura ƙofar babu sallama, hangoshi tayi kwance dagashi sai gajeran wando ,sosa kai tayi tare da yatsina fuska tace "sannu da dawowa , juyowa yayi ya ɗan kalleta yace "yawwa ya jikin ? da sauƙi tace kana ta zauna gefensa ,yanzu dai yaɗan rage tsanar da yayi mata albarkacin wanan ciki na jikinta , shima a halin yanzu yana son ganin jininsa , shiyasa yake ɗan sakin jiki da ita , janyota yayi tare da rungumeta yafara haɗe bakinsu guri guda tare da shafa bayanta , tuno azabar da tasha a daren su na farko tayi kuma tunda Haisam ya yi sex da ita bai ƙara yiba sai yau , zaro ido tayi kuma gashi tanason ta cima burinta na wani shu'umin magani da mamanta ta kawo mata hakan yasata daurewa ta fara maida masa da martani , ganin cikin zafin nama yake komai yasata fahimtar yana buƙatar ta , cikin zuciyarta tace "Allah ka bani ikon daurewa a wanan karon , fitowa nayi domin leƙa gidansu momy."

Yau alhamis ,asabar ɗaurin aure gida yafara cika da baƙi su Anty Aisha itace a sahun gaba su momy da Anty ba ƙaramin haushi sukeji ba akan rashin yawan shawarar da Alhaji bayayi dasu , amma a hakan hausawa sukace komai wayon amarya ..... yau takama juma'a akayi sa lalle kasancewar Abdallah ya cikawa Afnan account batada matsala da kuɗi, komai tsadar tsadar abu inhar momy tagani to bata ƙyashin siya saboda kyansa , babu wani wasanni da sukayi , washe gari asabar dubban al'umma suka sheda ɗaurin auran ABDALLAH DA AFNAN akan sadaki mafi albarka dubu ɗari lakan ba ajalan ba , kowa ka gani fuskarsa cike take da annuri anci ansha amarya na hango sanye da wani haɗaɗen less mai ruwan pink da flawoyi baƙake a jiki ba ƙaramin kyau tayi ba fuskarnan tasha makeup sai sheƙi takeyi , ƴan uwan momy ne suka riƙe hanunta suka shiga da ita sashen Alhaji kasancewar babu kowa duk suna ɗakin baƙi , Alhaji munkawo Afnan ne ka sanya mata albarka , cikin farinciki dakuma nishaɗi dan Afnan ta auri wanda dady yakeso yasashi cewa , Allah ya albarkaci auranki Afnan Allah yayi miki albarka , kanta a sunkuye wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga fuskarta."

Tunowa tayi da lokacin auranta da Haisam dady ko kulata bayayi da aka kawota gabansa lokacin da za'a kaita gidan mijinta cewa yayi bashida abin cewa , amma yau itace yake cewa haka , tashi kuje Allah yayi miki albarka yar albarka , wani sanyi taji ko ba komai zata aurin zaɓin iyayenta a gurinta babu abinda yakai farincikin su a gurinta."

Ɗakin Anty suka wuce da ita itama fuskarta cike da fara'a tace "madallah naji daɗin ganin wanan rana , anty Ummi dake gefe ta ja Afnan wani ɗaki banji mai sukace ba suka fito suka koma ɗakin momy.

Misalin ƙarfe takwasa kowa yayi sallah ya idar motoci suka fara hallara a harabar gidan , daga ganin motocin ma kasan kaf cikinsu babu na haya duk na ma'aikatane , Allah sarki rabuwa da iyaye sai dole Afnan ta ƙanƙame momy sai kuka takeyi momyn ma sai da ta zubar da hawaye sosai ganin Afnan tanata gursheƙen kuka, kasancewar ba wasu ƙawaye ta ɗiba masu yawa ba suka shige mota Afnan ma da ƙyar suka sanyata tanata kuka , ganin babu kowa a motar daga ita sai Abdallah a gefe , sai ma yanzu ta lura dashi , a gefenta sai direba , da ya maida hankalinshi ga wayar dake hanunshi , waro ido Afnan tayi shima Abdallah maida mata da martanin waro idon yayi ya sanya hanunshi cikin nata suka fice , kasancewar kowa ya fice daga gidan iya motarsu ce kawai, Afnan dai bata yi magana ba kasancewar jinta takeyi kamar zazzaɓi ne zai kamata , tafara haɗe hannayenta biyu tare da rintse idonta dataji yana yimata zafi .....✍️.

Ga masu buƙatar littafin daga farko zaku iya duba wattpad momislam 2020


💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 27 & 28

Ganin idanunta sunyi ja tana ta rawar sanyi yasa Abdallah cewa dreba muje asibiti a dubata kar ka wuce damu gida , to yace "ya juya motarsa basuyi wata tafiya mai tsayi ba sai gasu sun iso asibitin kulawa likita yafara bata , cewa "Abdallah yayi muje office muyi magana , ok Abdallah yace kana ya rufawa likita baya da isarsu kowa ya zauna likita yace "wanan matarka ce ?eh Abdallah yace "to tana buƙatar kulawa , Abdallah ne yace " menene ainihin abinda ke damunta ?"rashin bacci ne amma bayan shi babu wata matsala shine ya haifar mata da zazzaɓi amma zan haɗa mata magani insha Allah zata war ware , godiya Abdallah yayi masa bayan sun karɓi magani suka ɗauki hanyar da zata sadasu da katafaren gidan amarya , kasancewar hospital ɗin a kan titi yake suna isowa dreba yayi horn mai gadi ya buɗe get ɗin sa kai sukayi cikin gidan , samun mutane sukayi cirko cirko a tsaye kowa da mamaki a fuskarshi , ina ango yakai amarya."

Buɗe murfin motar kowannen su yayi ,Abdallah ya rungumo Afnan suka fito Anty Aisha ce ta taho zuwa gurinsu tace "me yafaru munata jajanta rashin ganinku , murmishi Abdallah yayi yace "batajin daɗi ne shine muka wuce , asibiti to Allah yabada lafiya , amen Abdallah yace "anty ummi na tsaye tana kallon ikon Allah , haka kowa keta ɗan taɓe baki ko mai yasa oho ."

wata mata dake gefe da alamu itama ƴar uwar momy ce ta karɓi Afnan ta shige da ita ciki , gaskiya faɗin tsaruwar gidan ma ɓata lokaci ne maƙudan kuɗin da Abdallah ya kashe bazasu faɗu ba , part ɗin Afnan ɗin na can nesa sana uwar gida amma da tafiya a tsakaninsu dan kowanne da nisa gidan babba ne , zaunar da ita tayi a tsararen ɗakinta dayaji flawoyi ga wani ƙamshi dake tashi , gaskiya komai na ɗakin abin birgewa ne kasancewar dady ma ya kashe nera,

Iya mutum uku ne ragowa dare yayi sauran sun tafi suma suna gama gyara ta kasancewar batada kafiya ta kwanta sukayi mata sallama suka wuce , misalin ƙarfe sha ɗaya na dare shugaba ya shigo bayan yasa dreba yakai su anty gida , sanye yake da wata baƙar doguwar riga mai hula , sai tashin ƙamshi yakeyi saboda shi ma abocin tsafta ne dakuma son ƙamshi ,

Kasancewar zazzaɓin nata ya sauka yasata yin ƙarfi da jikinta tace "barka da zuwa , ajiye ledar hanunsa yayi ya cire agogon dake manne a tsin tsiyar hannunsa yakai dubansa gareta suka sakarwa junansu murmushi ywwa Afy ya jikin "da sauƙi tace "tare da rage idanunta ta maidasu ƙanana ,to masha Allah , yanzu dai dare yayi ki tashi mu nuna godiyarmu ga Allah ta hanyar yin sallah , sunkuyar da kai Afnan tayi tace "banayi whattt....!!! mekikace ? mai maita masa tayi da cewar banayi , alamun ɓacin rai sun baiyyana a fuskarsa ƙarara sai taji yace "to zokici abinci karki zauna da yunwa , tunowa tayi rabonta da abinci tun na safe gakuma wata masifafiyar yunwa na addabar ta ."

saukowa tayi ta cire mayafinta ta ajiyeshi a kan gado ,Abdallah ne ya haɗiyi wani yawu kai kace "wanda yaga mai siyarda awara , lol fitowa tsararen falon sukayi a jere tana gaba yana baya yana kallon abinda yake ɗauke masa hankali , zama tayi a ɗaya daga cikin jerun kujerun tare da janyo ledar da ya ajiye a gefe , miƙewa Abdallah yayi ya nufi kitchen, ya wanko plet ya kawo mata da cup, kasancewar a ya yanke take yasata ɗiba ta zuba a plet ɗin tafara ci shiko a haka dai wayarsa yake dannawa amma inka lura da satar kallon da yake yimata ba wayarce ta ɗauke masa hankali ba , tana gama ci ta tatara sauran takai kitchen bayan ta kora lemu mai sanyi dawowa tayi ta zauna tare da duba wayarta ganin ƙarfe ɗaya saura yasata , zaro ido ta kalli Abdallah da ya kawar da kai,

Dare yayi zan kwanta , Afnan tace "ba tare da ta dubeshi ba ok muje niba baccin nakeji , har tafara gaba Abdallah yace "to jirani takowa yayi zuwa gabanta ya riƙe hanunta suka wuce bedroom , kasa cire kayan jikinta tayi ta maida na bacci abin ya gagara irin kallon da Abdallah yake yimata yasata kwanciya tare da juya baya , shima bin gadon yayi ya kwanta tare da rungumeta ya juyo da fuskarta tana kallon tasa , nunfashin su na cuɗanya dana juna , uhm bacci nakeji Afnan tace "lokacin da taji hanun Abdallah a rigarta , cirin sanyin murya yace "to ai yanzu lokacin hutawa ne , bana sallah , cewar Afnan no karki damu ki yarda dani na matsu pls , cikin tashin hankali Afnan ta dubeshi tace "kadai sani ba ƙarya zanyima ba amma mai yasa zaka saɓawa faɗar Allah , nifa ba komai zan yimiki ba to ai ke mallakina ce , eh nasani amma ka barni nayi bacci , Abdallah ne yayi wani irin murmishi tareda ƙara matseta yace "gurinda Allah ya haramta min ƙasanki ne amma daga saman cibiyarki har komai ma zan iya amfani dashi , wanka ya shiga yayi kana ya dawo ya kwanta , Afnan batasan lokacin da baccci mai nauyi ya yi nasarar ɗaukarta ba , shiko ya daɗe baiyi bacci ba yanata juyi shi kaɗai yasan halin da yake ciki ."

Haisam ya kama sana'arshi baji ba gani kasancewar ya roƙi zaɓin Allah akan wanan Alhajin da yakeson ya zauna masa a shago yaƙi yarda , Abubakar yayi yayi amma yaƙi yarda ,

Mama ce keta rangaɗa sallama lokacin ƙarfe goma na safe Haisam na bacci kasancewar bai fiya fita ranar asabar ba yana hutawa.

Mama ce tace "inata kwaɗa sallama ko babu kowa ne a gidan ? cikin ɗaga murya take maganar , walaikis salam gani waye mai dako min tsawa , Maimunatu ta faɗa.

Mama dake ƙarasowa tace "baiwar Allah kice rabo aka samu ? yatsine fuska Maimunatu tayi kana tace "rabo dai muka samu, mama dake murna tana tafa hannu tace "to masha Allah to mushiga daga ciki man , wa ? wlh babu mai shigarmin ɗaki na gyarashi sai dai in ɗauko miki tabarma mijina yana ciki yana bacci , mama ce ta riƙe baki tana kallon Maimunatu da cikinta ya fito sosai dan ga dukkan alamu zai kai wata takwas dan daƙyar take duƙawa , abinka da mai ciki mama ta tausaya mata ƙwarai da gaske ta yunƙura tare da cewa ƴar albarka mai za'a tayaki dashi ? kai kaice baki maimunatu tayi tace " nifa ba gaiyyar kowa nakeyi ba dan haka a ƙyaleni✍️.

DOMIN SAMUN LITTAFIN NAN TUNDAGA FARKO ZAKU IYA ZIYARTAR wattpad momislam2020

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 29 & 30

Zama mama tayi a tabarmar niko nace Allah sarki Afnan wargi ma guri yake samu , Maimunatu datasha ɗaurin ƙirji ta dubi mama daketa ƙare mata kallo ta galla mata harara , abinku da ƴar lelen mata mama ta sakar mata murmishi, Haisam ne ya fito da alamun hayaniyar su ce ta tayar dashi , faɗaɗa fara'arsa yayi kana yace " ah mama kece a gidan namu ?fuskar mama ɗauke da murmishi tace "wlh nazo duba Maimunatu ne , Hausam ne ya durƙusa tare da gaishe da mama, amsawa tayi amma isanta na kan maimunatu dan cikin jikinta yayi girma da yawa sosai kamar mai aihuwar ƴan uku , itako sai aikawa mama da harara takeyi dan ta tsani mama tunda taga take takenta na bibiyar gidan .

"uhm Haisam dama cewa nayi naga kamar Maimunatu bata iya aiki sosai to inba damuwa mezai hana in dawo gidannan indinga temakon ta tunda yanzu naga Allah ya buɗa maka sosai kuma ba ƴar aiki ka ɗauko mata ba ?, Haisam ne yace "to ai mama gara a ɗauko ƴar aikin kamarki ki zo gidannan kina aiki , mama ce tayiwa Haisam daƙuwa tace "kaci gidanku Maimunatu ai ƴata ce inda zan riƙeka haka zan riƙeta dan haka ka ƙyaleni in zauna kawai zan kwaso kayana zuwa su wanki da shara ai kaga su sunfiya sa tsuguno taji da wanke wanke da gyaran ɗaki , Maimunatu dake gefe ta taɓe baki tace "taɓɓ wlh nikam anaso a takuramin ne yo banda takura meye nawani zuwa ace za'adinga yimin aiki dacan wa yake yimin?cikin zafin nama Haisam ya miƙe zai wanka mata mari dakatar dashi mama tayi da cewa kull ba'a taɓa mai ciki koda gaba karkayi kuskuren sake kwatanta hakan , sunkuyar da kansa yayi yace "to mama , kidawo da kayanki kawai tunda ankwashe kayan ɗakin can , cikin murna mama tadinga sa musu albarka , miƙewa tayi tana duban Maimunatu tace "to barin tafi sai nadawo ko kallonta Maimunatu batayi ba ta ɗauke kai gefe ."

Washe gari tun da safe Afnan ta samu tayi wankan tsarki tayi sallahr asbah , dawowar Abdallah daga masallaci kenan ya tarar da ita tana sallah , farinciki fal zuciyarshi zama yayi gefe gado yana ƙarewa kyakyawar fuskarta kallo tare da lumshe ido , ƙarar wayarsa ce ta fargar dashi aga kalon Afnan , aslm yace "cikin firgici naji yace "ganinan zuwa kuyi dashi asibiti , Afnan dake gefe gabanta na faɗuwa tunda taji ance asibiti tasan ba lafiya ba, juyawa tayi bayan ta shafa adu'ar tace "barka da safiya mijina , ywwa barka Abdallah yace dan hankalinshi na gurin masu zuwa asibiti ƙara kai dubanta tayi gareshi tace "waye babu lafiya ?"Sadiq ne Abdallah yabata amsa a taƙaice , waye Sadiq ? yarona ne Abdallah yace ,nizan fita zan dubasu , in da wata matsalar ki kirani a waya ,to Afnan tace jikinta a sanyaye taƙara da cewa"Allah ya bashi lafiya mai ɗorewa.

Da isarshi asibitin ya samu anba Sadiq gado , Sadiq yaro ne da a ƙalla zai kai shekara goma sha takwas mahaifiyarshi wato mata agun Abdallah sunanta Shamsiya ,gaishe da Abdallahn tayi yace "mata ya mai jikin da sauƙi tace "to ya amarya washe baki Abdallah yayi tare da cewa amarya tana lafiya tana gaisheki idanun sa na kan Sadiq dake bacci ta galla masa harara tace "ina amsawa , duba agogon dake ɗaure a hanunsa yayi yace "yanzu ƙarfe ɗaya saura zanje zuwa anjima zan dawo , miƙewa tsaye tayi tasha gabansa tace "ciwo ya kori komai maiyasa bazaka bawa ɗanka kulawa ba ? Abdallah ne yace " kiyi haƙuri zan dawo anjima, ƙwafa tayi batare da ta ko lallesa ba ta koma ta zauna zuciyarta babu daɗi, kai tsaye motarsa ya nufa tuƙi yakeyi hankalinsa na gurin Afnan cikin zuciyarsa yana cewa "inda nayiwa wanan rana buri bazan bari yauma nakuma rasa farinciki ba , gudu yake yi a titi ikon Allah ne ya kaishi gida , ƙarar horn ɗin da mai gadi yaji ne yasashi tashi buɗe ƙofar da azama , Abdallah ya shige dan baima lura da gaisuwar da baba mai gadi yake yimasa ba.

Zaune take a katafaren falonta mai sanye da kayan more rayuwa faɗin tsaruwar falon ma ɓata lokaci ne dan koni tsayawa nayi ina ƙare masa kallo , hangota nayi kwance a ɗaya daga cikin kujerun da alama waya takeyi ,

Jinayi tace " momy nasami tsarki kuma nayi amfani da magun gunan tun ɗazu , daga can ɓangaren momy tace "yawwa ƴar albarka dan haka nake sonki kinsan su masu matan nan wlh sai da gyara jiki kuma insha Allah nasa a tahomin da wani haɗaɗen magani da turare insha Allah zakisha mamaki ."

Dariya Afnan tayi tace "momy na kenan Allah ya barmu tare gaskiya sai yanzu na tabbatar aurena da Haisam ba alkairi bane , kinga breakfast ɗina na yau dakuma ranar danazo hmm momy ba'a magana , kwashewa da dariya momy tayi kana tace "ai ba tun yanzu nake nusar dake dai dai ba kinƙi fahimta kice yanzu kin dawo hanya ?gaskiya kam momy ,daganan sukayi sallama ,

Jin sallamar Abdallah yasata miƙewa tare da kashe masa ido , kallon shugar jikinta yayi , can kuma ya faɗaɗa fara'arsa ya buɗe hannayensa duka da sauri ta faɗa jikinsa tare da rungumeshi ta zaunar dashi a palo , oh Allah na gaji , Abdallah yace "lokacin da yake shafo dogon gashin kan Afnan da yasha gyara."

Ƙara narkewa Afnan tayi tace "baby ka gaji ko ? uhm Abdallah yace" dan wanan shagwaɓar tata tana rikitashi wani lokacin , Afnan ce tace "tashi muje inyima tausa , abin nema ya samu aikuwa cikin azama gogan ya miƙe tare da ɗaukar Afnan kamar jaririya ya kaita bedroom ɗin ɗakinsa ...

Cire mata ɗankune yayi da warwaro ya kwanta gefe tare da rungumota sunajin nunfashin juna , am sorry baby kiyi haƙuri dani pls ni mabuƙaci ne !!!...wata azababiyar faɗuwar gaba ne ya ɗarsu a zuciyar Afnan , kasancewarta wayayiyar mace ƴar boko yasa bata nuna masa alamun damuwa ba amma gaskiya a ƙarƙashin zuciyarta tsorone ya dirar mata , idanunsa a lumshe yafara hura mata iska ta kunne yana shafa gashin kanta hakan yasa ta mance da komai tafara maida masa , daganan salo ya sauya zuwa cire .....am sorry nafito kasancewar naga gidan Haisam ana drama .

Da sallama mama ta shigo kasancewar Haisam bai fita ba shine ya amsa sallamar , kayane ta ɗibosu zasuyi kala ashirin ta ajiyesu a tsakar gida , Haisam ne yace "mama zo in nuna miki ɗakin da zaki zauna cikin rawar jiki mama ta miƙe ta bi bayan Haisam , Maimunatu na ɗaki baƙin ciki ya isheta....✍️.

Uzururuka sunyimin yawa bawai ina yimuku wula ƙanci bane kuyi haƙuri kunkusa samun post kullum afuwan

Please Login or Register in order to submit comment