Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

My Facebook group
https://www.facebook.com/groups/126215122683287/

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 11 & 12

Anty na shirin mik'ewa tace ” yanzu ma anguwa zan zarce daga nan , ganin Alhaji na laluba aljihunsa yasata murmusawa , dubu uku ya mik'a mata tare da fatan Allah ya tsare , godiya tashiga kwararo masa ta mik'e ta fice , batason su had'u da kowa hakan yasata ficewa a ankare batare da sunyi ido biyu da matan gidan ba , fitarta keda wuya sai ga Anty ta shigo da sallama ,amsa sallamar yayi yana k'are mata kallo , to yau kuma yarintar ce ta motsa ?"matsowa kusa da Alhaji tayi tana mai kai cinyarta kan k'afarsa , tofa 🤨 Alhaji da zancen yafara sakin layi yace ”tashi muje ciki kinsan gidan baya rabo da bak'i , mik'ewa sukayi tare da turani waje suka rufo k'ofar , dare nayi yau Alhaji zai koma d'akin momyn Afnan , tun k'arfe hud'u na yamma tasa ake yimata gyare gyare , duba agogo tayi k'arfe biyar , toilet ta shige ta had'a ruwan wanka wanda yaji turaruka na musamman , tana fitowa tasa turaren wuta dana tsuguno ,kasancewar ta y'ar mai duguri bata wasa da gyaran jikinta bare ma matan gidan kowace tana k'ok'arin gyara kanta ,tana gamawa ta mulke jikinta da mayuka masu d'aukar hankali , wani mai ta tsiyayo ta shafe gashinta dashi ta zauna kan stool d'in dake gaban dress mirror tafara tsara kwaliya kasancewar lokacin ana kiran magrib tariga tayi alwalah , Afnan ce ta shigo da sanyin jiki ta dubi momy ,ta kawar da kai momy ko kallonta batayi ba ,ta mik'e ta d'auko cup da spoon ta dawo ta zauna magani ta d'auko a leda ta bud'e fridge ta d'auko nono mai sanyi ta dama , ganin zata sha yasa Afnan cewa "momy ina nawa , momy kallonta takeyi cikin tuhuma can kuma tace ”a lokacin da kika auri wanda zuciyata da hankali na sukeso to lokacinne zaki dinga ganin gata iri iri so yanzu kibi umarni na kiji dad'i a rayuwarki, sunkuyar da kai Afnan tayi tace ” momy yanzu duk akan auran Haisam ne dukanku kuka tsaneni ?" no Afnan ba tsanarki mukayi ba somukeyi ki gane ban bancin dake tsakanin talaka dakuma mai kud'i , Allah ya horewa mahaifinki company da dama ga dukiya mai yawa amma ace kin k'are ke y'ata ta cikina kin k'are a talaka futuk wanda in yayi kwana d'aya tak bai fita ba zakushiga damuwa."

Afnan dai tasaba da irin wanan fad'an yasata jan bakinta tayi shiru ,ta zubawa momy ido wani fitinanen leshi ta ciro a drowa mai kalar pink da adon black stone anyi mata d'inkin riga da zani rigar iya guwaiwa mai breastcot tai kyau sosai kasancewar ta mace mai dirin jiki sbda irin jikinta Afnan tayi , war waro ta sa kana taciro tsadajiyar sark'arta ta sanya ni dai gani nayi momy ta koma kamar yarinya , kamar ba ita ta haifi Salma da Afnan ba ,momy na gama kintsawa takuma feshe jikinta da humra ,itadai Afnan a halin yanzu kewar mijinta takeyi sosai ,sallamar dady ce tasasu kai duban su gareshi da alamun fad'a yashigo amma ganin momy tasha kwaliya yasashi sa sauta murya ya kalli Afnan ganin bashi take kalli ba yas shi kashewa momy ido kana yace ”in kin kammala ina jiranki a d'akina zamuyi magana Afnan ta lura da kallon da dady ya ke aikawa momy hakan yasata mik'ewa tayi bedroom d'in ta ta fad'a gado, tana tuno soyayyarsu da Haisam tabbas ta tafka uban kuskure dahar ta biyewa son zuciyarta yanzu gashinan daga dadyn har momy babu mai damuwa da damuwarta yau satinta biyu , tinda tacewa Haisam washe gari zatazo har yanzu shiru ko shine ya sashi yin fushi oho , miƙewa tayi dan gabatar da sallahar isha'i tana idarwa ta jerowa kanta adu'oi dakuma Haisam ɗinta."

Mama tasa ankai kuɗin aure , iyayen Maimunatu sun yanke lokaci kasancewar su mama sun roƙa kar asa bikin da nisa ,cikin sa'a kasancewar a shirye suke suka amince yau saura sati biyu biki , Haisam na burin zuwa gidansu Afnan yana tsoro yasan dole zai fuskanci cin mutunci da cin zarafi daga duka ɓan garorin guda biyu , wanan shike sage masa gwaiwa ya kasa zuwa ,ga matsa masa da mama tashiga yi yanzu bashida saƙat kasancewar biki ya kusa tasashi siyo akwati ya kawo ɗakinta ,aikuwa haka akayi dan gudun tashin hankali , akwatuna ukune biyu manya ɗaya ƙarami cikin fara'a mama tadinga sanya masa albarka , yanzu kam Haisam yafara cire rai da samun Afnan saboda dalilai da dama hakan yasa ya haƙura da auran da ake shirin liƙa masa amma badan yana soba ,kwanci tashi asarar mai rai yau biki saura kwana uku sbda Haisam yagama haɗa kayan akwati yasa Mama kwantar da hanlinta ,hidima akeyi sosai baba kam baya kula lamuranta dan zata iya tsigesa ba tsoro bare fargaba , ƴan uwa kowa sai yayi tsegumin wanan aure ,kowa tambayarsa itace to ina matarsa , kaf cikinsu ba suda mai basu amsa yasasu jan baki sukayi shiru."

Biki yayi biki Haisam bai gaiyyaci kowa ba sai dai ya gayyaci abokansa na anguwa , suma gudun kar suyita yi dashi ne amma da babu wanda zai bawa labarin auran da yazamo tamkar auran dole , bayan an ɗaura aure Maimunatu ta kira Haisam ko akwai wani events da za'ayi ?"cikin baƙar magana Haisam yace "to ni babu wani shirme da za'a kawomin ,
"kuma kidena rawar kai ba sonki nakeyi ba liƙamin ke akayi dan haka karki ƙara koda marmarin kirana kinaji ko?" Maimunatu da jikinta yai sanyi duk azabar masifarta amma takasa mayarwa Haisam martani lallai ko zata rama koba yanzu ba katse wayar yayi tare da jan dogon tsaki, ɗakin Afnan ya shiga ganin komai kamar tana nan Allah sarki masoyoyiyar gaskiya Haisam ya faɗa lokacin da ya kwanta a gadon Afnan ya luluɓe jikinsa da blanket ƙamshin turarenta ne yake masa yawo ,gani yake kamar zai ganta kwance kusa dashi , tabbas Afnan da Allah ya bata aihuwa da babu abinda zai hana ƴa ƴanta su taso cikin irin halinta , duk da Allah yayiwa mahaifinta arziƙi hakan baisa ta ɗauki talaka da ƙyama ba , kwance yake duk wannan tunanin da yakeyi , wasu hawaye ne masu zafi zuka kwaranyo masa agefe idansa ,tunowa yayi ashefa wai shine ango ko ?"kuma yau za'a kawo amarya ,tabb to ni mema zanyi? miƙewa yayi ya fice a ɗakin , yasa takalmi yana shirin fita yaji sallamar Fatima ɗago kai yayi tare da amsa sallamar Fatima ce tace "ina yini Haisam lpy lou y gida bata amsa ba tace "har yanzu Afnan bata dawo ba ?eh Haisam ya bata amsa bata dawo ba nima jiranta nakeyi , ficewa tayi batare da ta ƙara bi ta kansa ba , tana faɗawa gida ta saki kuka mai cin rai , shikenan Afnan ko shawara babu yanzu gashinan ya tafi ta barta takuma sakin kuka."

Tuno ɗaurin auran Afnan yayi da ya kashe kuɗi sosai wanan kam tamkar za'a sashi a kurkuku yakeji tunda babu mai sa ssauta maganar auran ,ganin Fatima ta fice ya sashi koma wa bedroom ɗinshi ya kwanta , jin kwanciyar babu daɗi yasashi juyi a gadon , jin an rangaɗa sallama yasashi miƙewa jiki babu ƙwari , ganin mata da yawa ga motar kaya a waje ya matsa gefe ba tare da ya kallesu ba kanshi a ƙasa yace "ina yininku sama sama suka amsa ,ganin gidan babu lefi yasa su washe baki suna sanya alkairi , a wane ɗakin za'ayi jeren?" Haisam ne yace"ga ɗaki can ,ɗakin baƙi ne zaku iya yin jeren a ciki , wata daga ciki da alama ƴar uwar Maimunatu ce ta turo ɗaurin ɗankwali gaba tace " aikuwa sai dai in a fito da kayan ɗakin kishiyarta a jera na Maimunatu , danƙari Haisam yac" lokacin da yake shirin ciro kwaɗon ƙofa a aljihunsa ya kulle ɗakin Afnan sa kai yayi ya fice ,kan uba to wlh Maimunatu zatasha wuya a gidan wanan shu'umin sai ta tashi tsaye ,wata daga gefe da tun shigowarsu batayi magana ba tace "wayasani ko kishiyar tata azabarshi ce ta korata gidansu , haka dai suka dinga tsegumi , ganin hakan bazai fishesu ba yasasu komawa bakin aikin nasu , dole a ɗakin baƙin suka yimata jere ɗakin bawani mai girma bane amma dai kayan sun zauna sunyi kyau amma ko ƙafar na Afnan basu kamo ba, kasancewar iyayen Maimunatu talakawa, suna gamawa suka kullo ƙofar suka fito kowa na tofa albarkacin bakinsa akan Haisam shiko ya fice ya barsu."

Ƴan kai amarya ne keta shiri dan mama ta kira Haisam a waya akan ya kawo motoci , dole yakebon umarnin ta haka yaje ya taho da motoci aka rakasu gidan su Maimunatu ,kowa sai kururuwar shiga mota yakeyi ƙanwar maman Maimunatu da basu fito da Amarya ba sunanan suna yimata uɗubar tsiya akan ta koyi tattali mijinta mai yawan cefane , tadinga ɓoye wani abin tana kawowa gidan su komai da aka gaya mata ya shigeta sosai musamman ma maganar tara kuɗi, haka acikin abokan Haisam wai ya shiga gidan su amarya yace "ita suke jira tayi ta fito , luluɓo mata fuska sukayi aka nufi ɓota da ita sunyinyi tafiya mai nisa sanan suka iso gidan ,jin guɗa yayi yawa ya sanya Fatima leƙowa taga ko suwaye , ganin mata nata shiga gidan Afnan yasata riƙe baki tace "angama Haisam ma yayi aure ta sa kuka shikenan Haisam ya saki Afnan wane laifi tayi masa dahar yayi mata haka ?"kasa zaman gidan tayi ta kulle ƙofa ta nufi maƙotansu."

Maimaicin abinda Haisam yayi musu suka fara Maimunatu buɗe ido tayi tana ƙarewa ɗakin kallo babu laifi yayi kyau sosai ta maida mayafinta ta rufe , faɗa aka shiga yi mata har ƙarfe tara na dare , kowa ya cire ran Haisam bazai kawo mota ba , sunata dai zaune wata a cikinsu ma batada kuɗin komawa horn sukaji lokacin ƙarfe tara da rabi hamdala sukayi ✍️.

Follow me and vote on wattpad
Nayi tafiya ne shiyasa kuka jini shiru

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

Zainabhabibu713 gmail.com

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

My facbook group
https://www.facebook.com/groups/126215122683287/

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 13 & 14

Kufito mu tafi suka ji ana cewa , da sauri suka miƙe suna yiwa amarya sallama , tun tana saka ran shigowar ango harta fara cire rai agogonta dake manne a jikin bango ta ɗaga kai ta kalla ƙarfe shabiyu na dare to ko bazai zo bane ?"ta faɗa cikin ranta gyara kwanciyarta tayi ba tare da ta cire kayan jikinta ba , ɓangaren Haisam harya shigo ya kwanta a ɗakinsa duk bata sani ba , da asbha ya miƙe cikin salati yayi alwala ya fito da shirin tafiya masallaci tunowa yayi da ace Afnan ce a gidannan da tuni komai ya gyaru amma amarya guda ta saki baki tana bacci , ficewa yayi yabar gidan ya nufi masallacin kusa dasu ko nafilar ma yau baiyi ba ,ƙarfe takwas Maimunatu tayi miƙa tare da salati ta kalli agogo ganin ƙarfe takwas yasata cewa "kan uba wai na makara ne shiyasa na tashi inajin wata azababiyar yunwa , toilet ta nufa ta yi alwala tazo ta tada sallah ko cikakiyar adu'a batayi ba ta shige kitchen, ganin indomie guda uku manya a jere ya sanyata murna to ina zanga ƙwai?" to me hawa sama ya taka leda ai sai tafiya barin dafa indomin ina gamawa na haɗa shayi mai kauri nasha ko zanji sanyi a raina tunda rabona da abinci tun jiya da yamma , ɗaya da rabi ta dafa ta cika kofi da ruwan lifton kasancewar ta nemi madara ta rasa ,Haisam ne ya fito palo kasancewar dole zasu haɗu tunda a palorn take zaune , ganinta yayi ta mimiƙe ƙafafuwanta tanata loda abinci , Maimunatu ce ta ɗago kai ta ƙarewa Haisam kallo cikin zuciyarta tace "nayi sa'ar gwarzon miji mai jini a jika , ta miƙe tana suɗe hannu tace "barka mijina wai a ina ka kwana ?"a gidan ku , nace "a gidanku meyasa bakice nemana ba ?aida kinsan inda na kwana."

Bata damu da maganganun da ya faɗa mata ba ta ruƙo hanunsa tana shinshina ,to sabon salo sai kace maiyya ? Maimunatu ce ta zaro ido tace "kowane miji yana alfahari da daren farkonsa shida matarsa amma kai kamar bakayi , gyara tsayuwa Haisam yayi yace "daren baƙinciki ko ?"to kishirya zaman ƙunci a gidannan dan walah keda jin daɗi muddin kina gidanan kunyi sallama ,oho dai nariga na sameka mekuma yarage kawai kazo mu buɗe soyayyar mu , wani kallon banza Haisam yai mata kana ya fice , Maimunatu ce tayiwa mamanta waya akan taje gurin malamin da suke zuwa dan sunji daɗinsa tun akan maganar auran gashi yanzu ta sami Haisam sunso ya mance da Afnan amma abin ya gagara ,maman ce tace "to ina magun gunan da na ƙulle miki a baƙar leda , Maimuna ce tace "nayi amfani dasu amma shiru , to ki kwantar da hankalinki insha Allah anjima zani ,duk iskancin sa zai sakko yanzu dai babbar damuwar shine inda za'ayi ya kwanta dake har kisami ciki , daganan kinga sabon gata zai rashi da gurinshi da gurin uwarshi , Maimunatu ce ta nisa kana tace "hmm yaushe ma ya shigo ɗakin nawa to jiyama ban san a gidan ta kwana ba , ɓama ce tace"ke wawiya ce bakida tunani meyasa bazaki san inda zakiyi ba sai kace ba mace ba ?"nifa duk iskancin namiji sai na juyashi naga kamar ke bazakiyi gado naba ko ?mama zan gwada karki damu cewar Maimunatu sukayi sallama , tana gama cin abincin ta miƙe ta nufi bedroom ɗunta ta kawanta , tanata tunanin maganar mahaifiyar tata."

Tabbas inhar Haisam bai kwanta dani ba bazan sami gata ba dan nasan kaf danginmu babu wacce bata aihuwa , to yazanyi ?" kemis zani in siyo ƙwaya , janyo dogon hijabinta tayi ta sanya ta ciro ɗari biyar acikin jakarta ta fice tare da janyo ƙofar gidan , ganin kemis a kusa da su ba sai tasha wutaba yasa ta shiga ,Allah yasa babu layi , ta ce abata maganin tada sha'awa , ƙare mata kallo likitan yayi yace "baiwar Allah wa zaki bawa wanan maganin?"mijina tabashi amsa a taƙaice , mijinki kuma ba auran soyayya kukayi ba ?" Maimunatu ce ta dakatar dashi tare da cewa "kaga malam idan baka dashi kokuma bazaka bani ba in wuce ,wanan tambayar banga amfaninta ba , mai kemis ne yayi murmishi yace "karki damu indai magani ne zan baki , cikin zuciyarsa yace "wlh sai na shirya miki gadar mugunta da zaki sha wuya , sachet ɗaya ya miƙa mata yace " kibashi biyu kekuma gobe kisha biyu ,to nawa ne ɗari biyar ,ya bata amsa cikin zumuɗi tace "inkasan wata bakasan wata ba wlh sai kazo da ƙafafuwanka kana haɗani da Allah , zanga ƙarshen taurin kai ,tana tafiya tana maganar shiko mai kemis tana fita ya tuntsure da dariya tana tafa hannu."

Da fara'a ta shiga gidan kai tsaye ɗakin Haisam ta shige , ganin ruwan gora a gefe ga kuma fanta ta gora ansha ragowar zaiyi rabi yasata dan daƙa maganin ta juye a ciki ta girgiza ta ajiye ta fice , wanka tayi ta wanke kwanukan da taci abinci , shara ce dai Allah bai bata ikon yi ba,

Labari ya isarwa Afnan maganar bikin Haisam , tasawa kanta damuwa sosai momy ta sata a gaba da faɗa akan ta damu da Haisam shiko bai damu da ita ba , tun tana damuwa har tazo ta fara ragewa sbda dena tunanin Haisam zaiyi wuya ,taci kuka har ta haƙura , dady yanzu yafara kula Afnan ya canza mata waya ya bata kuɗi mai yawa tayi siyayya hakan tafara rage mata damuwa , Anty ummi rabonta da gidansu an daɗe , kasancewar tunda anty ta cimata mutunci ta tafi ranta a ɓace , yau tana son zuwa gidan su anty ummi tana tsoron tambaya dan dady ya hanata fita , harta fito da gyle ta maida tama haƙura da fita kwata kwata gashi yanzu batada number kowa ,

Salma ce ta shigo da sallama riƙe da Sudais a hanunta , da sauri Afnan ta fito tana cewa"oyoyo my sister cikin fara'a suka rungumi juna ,Salma ce ta ɗauki Sudais tana yimasa wasa , ƙarasawa Palorn momy sukayi , momy na zaune a kan kujera ta fara yimusu oyoyo , ganin yaran nata reras yasata sakin fara'a , Salma ce tace "momy yaushe Anty Afnan tazo ?"momy ce tace "ai ta kwan biyu takardar ta muke jira yazo ya bata , ashe ma har yayi sabon aure , riƙe haɓa Salma tayi tace "tun farko abinda nake faɗa muku kenan yanzu gashi ya maida anty bazawara , momy ce taja ƙwafa tace "ai yanzu komai ya wuce , baban farinciki na ma shine , batada ciki kina bazatayi wuyar samun miji ba ,✍️.

My fans banfa dawo ba kuyi haƙuri

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

Zainabhabibu713 gmail.com

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 15 & 16

Haka dai suka dinga hirarsu Anty ce ta shigo ta samesu a palo cewa tayi" aa saukar yaushe ?"Salma ce tace"Anty ban jima ba , gaisawa sukayi hira ta ɓarke tsakaninsu , wanda duk rabin hurar ta Anty Afnan ce , hakan ya sata ƙin kulasu dan inda abinda ta tsana bai wuce hirar Haisam ba ,sai yamma Salma ta fara shirin tafiya , momy ta bata turaruka da su zuma , kirane ya shigo wayarta , ganin number mijin yasata cewa "to drivern mu ya ƙaraso ,bata samu haɗuwa da dady ba hakan yasata tafiya tace "a gaishe shi, momy ce ta ƙwalawa Afnan kira kasancewar ta koma ɗakinta , amsawa tayi ta fito , momy ce tace "zo kiyi wanka kiyi kwaliya dan Allah ji tsara kwaliyar maiya faru momy ?" sai kin tambayeni ko kina ganin zan cutar dake ne ? a'a Afnan tace " ta shige toilet tafara wanka da sabulun da momy ta bata mai ƙamshi , tana fitowa ta tarar da momy a ɗakinta da kaya a hannu tana gama kwaliya tace "momy wanan kayan zan sa?"cikin fara'a momy tace "eh man ƴar albarka karɓa Afnan tayi tasa momy ta miƙo mata sarƙa da ɗankunne da war waro , kana ta miƙa mata turare mai ƙamshi , feshe ko ina na jikinta tayi ta juyo tace "momy nayi kyau?".

"Sosai ma my daughter kinyi kyau , yanzu kinsan abinda nakeso dake? a'a Afnan tace "to baƙo zakiyi daga Kano zai zo nan Abuja so ina san ki tarbeshi da mutunci yaron abokin dadynku ne insha Allah Afnan tace "in ya iso zai kiraki a waya oky momy , jekisa a gyara ɗakin saukar baƙi , ficewa Afnan tayi dan isarda saƙon momy ,turare mai ƙamshi aka sanya a ɗakin , ƙarar wayar Afnan ce ta dawo da ita daga duniyar tunani sbda tana tunanin to shi waye kuma mezai kawoshi , inko soyayya ce hmm , amsa kiran tayi tare da sallama a bakinta , wa/alaikis salam barka taji ance daga ɗayan ɓangaren gimbiyar mata kuma sarauniya , gani gurin parking ɗin mota oky Afnan tace "tana shirin miƙewa , da fitarta ta hango wani kya kyawan saurayi lol to koma dai bazawari ne ,nidai ya yimin kama da saurayi , yana hangota ya haɗiyi wani miyau tare da magana a zuciyarsa , shin wanan bazawara ce ?"anya nifa naga kamar budurwa , ga tsayi ga kyau komai na jikinta mai ɗaukar hankali kai masha Allah ,kona aureta bazan haɗata da matata ba 🤭wai dama yanada mata ?"fans kuzo muji , sallamar da Afnan tayi ne yasashi daɗa ƙare mata kallo ,yana amsa sallamar yace "gimbiya sarautar mata kuma mata a gurin Abdallah , waro ido Afnan tayi tace "wanan kirari haka ?.

To zomu shiga gida ƙin jerawa yayi da ita tana gaba yana baya ,yana kallon yanayin takunta , jinjinawa yakeyi a zuciyarsa inhar yasami Afnan to yasami farinciki gashi ya riƙe sunanta gam , suna shiga ya zauna a ƙayataciyar kujerar da ta ƙarawa ɗakin kyau , nesa dashi Afnan ta zauna tunani ne ya faɗo mata ashefa tanada aure zata tsaya hira innalilahi to yanzu yazanyi ?"momy fa na sane wlh , Abdallah ne yace "gimbiya bamu gaisa ba lokacinne ta ƙare masa kallo ba wani yaro bane dan zai kai shekara talatin da biyar ko fima amma kasancewar nera ta zauna sai ta ɓoye shekarun nasa , murmishi tayi tace "ina yini lpy dafatan nasami mazauni a zuciyarki , tsintar kanta tayi da cewa insha Allah, ganin abin takeyi kamar almara wai itace a gaban wani harda tsara kwaliya ba mijinta ba kai ina!!, Abdallah ya lura hankalinta baya gurinshi dan tun ɗazu yake magana batasan yana yiba amma hakan bai ɓata masa rai ba ,sbda tunda ya ganta yaji zuciyarsa ta amince da auren ta kuma dukiya ko nawa take buƙata zai kashe dan yaga ya sameta."

To Afnan barin shiga mu gaisa da dady yacemin yana hanya ɗazu da alama yama ƙaraso , to kawai Afnan tace "ta miƙe jiki babu ƙwari tayi bedroom ɗin momy , momy na ganinta ta faɗaɗa fara'arta tana cewa my daughter ya kukayi , zama gefen gadon momy Afnan tayi tace "mun gaisa yace "bari yaje gurin dady su gaisa , oh amma babu wata matsala ko ?"eh Afnan tace " momy kinsan fa da aure na nake kula wani , haɗe rai momy tayi tace "to ai Haisam ya sakeki yau kwana biyar kenan gama takardar , cikin ƙaguwa da ganin takardar , sbda gani takeyi momy kamar wasa take yimata , miƙa mata takardar momy tayi , Afnan ce ta nutsu ta fara karantawa .

ASLAMU ALAIKUM
NI HAISAM NA SAKI AFNAN SAKI BIYU,

Maimai tawa tadin gayi a zuciyar ta ya sakeni ?" Haisam ya iya sakina ? kalonta momy tayi tace "Afnan inason ki kwantar da hankalinki yanzu kina fita idda zaki yi auranki , namiji ba ɗan goyo bane ,yakamata kisani daga lokacin da yayi sabon aure shikenan kin zamo abin wula ƙantawa ,yanzu kinga aya a auranki da Haisam ko , fashewa da kuka Afnan tayi tana juya takardar tana kuka , yayi kyau zan cireka a zuciyata in huta tunda ba sona kakeyi ba , taɓe baki momy tayi tace" "dama menene abin so a gurin

Please Login or Register in order to submit comment