Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, jibi inda kika rame , murmishi Afnan tayi , lokacin da ta mik'e ,zatayi kitchen batace komai ba, ruwa ta d'ibo wa Salma a jug kana ta had'o mata da abinci da tagama yanzu , taliya ce ,mai da yaji , kuma ke6e baki tayi tace ”ta6 Allah ya kyauta sis yanzu abinda kikeci kenan?" juyowa Afnan tayi tace ”mai yasa kika biyoni ,kitchen ?”kinzo ki kuma 6atamin rai ko just ki forgetting komai ,but ya wuce ,komai Allah ne mai yi kuma komai kikaga bawansa dashi , bawai baya sonsa bane .✍️.

Kuyi hakuri nayi tafiya ne wlh ba lallai gobe kusami update ba , ku fahimceni biki mukeyi, masu sharhi naga sharhinku Allah nagode🙏.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

*zai koma na kud'i tunda kuna karantawa amma bakwa sharhi*

*karku manta wlh zan dena post a Watsapp zan koma wattpad yafimin* 👌👌

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

🅿️EPISODE 7 & 8

Fad'in haka yasa Salma shiru da bakinta , tana gama shan ruwan ta mik'e tace ”sis mukam zamu wuce ,ga wanan kya rage wani abu, no bana so , Afnan tace ”lokacin da ta kamo hanun Sudais tana shirin yin hnyar waje , tsaki Salma taja kana tace ”wlh tunda kikace auran talaka ,hmm ina tausaya miki ko dady , yanzu baya ambaton sunanki , Afnan ce tayi dariyar yak'e wace tafi kuka ciwo ,tace ”ina da Allah tunda kowa na gudu na please in wucewa zakiyi ki fice, karki k'aramin ciwon kai , okay don't worry , nice ma nazo inda kike ,tunda ke ba neman mu kikeyi ba ,wani wawan mari ,Afnan ta wanka wa Salma , Kana tace ”ficemin a gida ,bana neman temakon ku bance kowa ya temaka min ba , rik'e da kumatu , Salma ta fizge hanun Sudais a na Afnan suka wuce a zuciye , komawa kan kujera Afnan tayi ,rik'e da kanta , cikin damuwa da 6acin rai ta sa kuka mai tsuma zuciya , innalilahi wa inna'ilaihir raji'un ta ambata cikin muryar kuka , ya Allah kayimin magananin matsala ta , tun farkon aure na banida kwanciyar hankali , oh Allah ka duba lamurana, ta kwanta tana kuka ,Fatima ce ta shigo ,hanunta rik'e da wani abu a gora kamar zuma , da sallama ta shiga gidan Afnan tace ”matar Haisam na kawo miki wani sirri na musamman , da jajanyen idanunta Afnan ta dubi Salma, tace ”wa'alaikumus salam , tsoro ne ya kama Fatima tace ”yau kuma maiya faru ?"Afnan ce tace ”dan Allah ki tayani da adu'a Fatima ,insha Allah barinje gida cewar Fatima , Afnan ce tace ”mai kika kawo , a'a kibari zuwa gobe mayi magana ,to Afnan tace Fatima ta wuce gida."

Dare nayi ta yi abubuwan da tasaba , shigowar Haisam misalin k'arfe 8pm yau ya dawo da wuri , jiki a sanyaye ta mik'e tayi masa oyoyo , ganin yau babu fara'a dakuma barkwancin da tasaba yi masa yasa shi ,k'are mata kallo ,rungumo ta yayi yana murza hanunta da ya rik'e gam , rurin da wayar sa keyi ne yasa shi sakinta , d'aga wayar yayi tare da sallama , jin muryar mama yasa shi k'ara matsawa nesa da Afnan dan yasan labarin gizo baya wuce na k'ok'i , jiyo muryar mama yayi tana cewa ,wlh inhar baka zo yanzu ba to wlh sai nayi mumunan 6ata maka rai , juyawa yayi yaga Afnan bata gurin ,ya rage muryarsa yace ”mama ganinan zuwa, karma kazo wlh zaka gane ta kashe wayar , k'ara sawa bedroom d'in Afnan yayi ,gajinta a zaune tana gyara powder fuskarta yasa shi , sakin fara'a yace ”my lovely barinje in dawo mekikeso ,in taho miki dashi¿" dariya tasa wace kamar ta dole ce tace ”dabino da kwakwa , to karki damu , cikin rawar jiki ya fice, ƙofar gida ya fita ya tada mashin ɗinsa ,kai tsaye gidansu ya nufa ,sallama yayi kana ya shige ɗakin mamanshi ,samunta yayi a zaune tana jijiga ƙafa, yana shiga ta miƙe ,cike da ɓacin rai tace "wato Haisam ban isa in gaya maka magana ba?" yanzu ƙarfe nawa? duba agogo ka gani ,Haisam ne ya kalli agogon hanunsa yace "ƙarfe goma ,to mekake nufi da maganar da muka yi dakai?" Haisam ne yace "kiyi haƙuri mama zanbi umarninki amma kibari zanyi shawara, shawarar banza cewar mama ,to wlh tun wuri kabi umarni na kokuwa na tsi.... innalilahi ya ALLAH mama ki gafarceni karkiyimin baki ,na yarda zanyi auran ,ywwa Allah yai maka albarka , nariga na gama magana hira zaka fara zuwa , kuma daga yau , a kid'ime ta kalli mama da keta washe hak'ora , dubu d'aya ya mik'a mata kana yasa Kai zai fice , dakatar dashi mama tayi , tace ”to yanzu bari a kirata a waya inyaso sai kaje ko?" shiru yayi bai ce komai ba , mama ce ta ciro wayarta a lalita ta mik'awa ,Haisam kana tace ”lalubo min lambar , Maimuna ,yana dubawa yaga number danna kira yayi ya mik'awa mama, hararar shi mama tayi tace ”nice mai zuwa zancen?" zaka fara nunamin halin naka ko?"cikin ladabi ya k'ar6i wayar , sallama tayi ,jiyayi ance "baby takake yakuma gajiyar aiki ?" muryar Haisam babu alamun fara'a yace ”zankira ki gobe , okay I love you , yana kashe wayar ya mik'awa mama."

Cikin fara'a mama tace ”to d'an albarka baka d'auki number ,Maimunatun ba , sbda gudun fad'an mama yasashi , kar6ar wayar ,ya d'auki number ya fice , 6angaren maimunatu kuwa murna cike da zuciyarta ta buga tsalle kana tace ”wanan gayen da alamu kyakyawa ne , zanso ganinsa , tayiwa wayar kiss ,sai k'arfe 11pm Haisam ya koma gida ,Afnan mai saurin kuka , taci kukanta ta gaji hartayi bacci , yana shigowa tare da mashin d'ainsa ya kulle gidan , ya jingine mashin d'in ,k'arasawa yayi ,bedroom d'in Afnan , samunta yayi tayi bacci ,haska fuskarta yai da fitilar wayarsa kasan cewar babu wutar nepa , ganin hawaye bushe a fuskarta , yasashi cewa Allah sarki baiwar Allah , ya koma d'akinsa yai alwalah ya kwanta, tunnin yarinyar ne keyi masa yawo a brain d'insa , tabbas yasan inhar Afnan tasan labarin nan to kashinsa ya bushe , dan wlh zata iya barinsa , yasan Afnan ba ajinsa bace , mahaifinta nada dukiya taban mamaki amma ta za6e shi, to wai shin ita haihuwar nan ba ta Allah bace ?" ganin yana shirin yin sa6o ne ya sashi yin shiru , yayi adu'a bacci mai nauyi ya kwashesa , washe gari antashi da sanyi sosai ,bayan sunyi sallahr asbha Afnan ta koma d'akin Haisam baccin safe , bacci mai nauyi yai awon gaba dasu ba su suka farka ba sai misalin k'arfe goma Na safe , Afnan ce ta fara bud'e ido ta zare jikinta a na Haisam , gyara gidan tayi ta koma d'ora abin karyawa , tana gamawa ta shige wanka , jera kayan shayin tayi a kan tebur , kana ta nufi d'akin Haisam , tana shirin tashin sa raji ya fara salati , kwantowa tayi kan cinyarsa tace ”barka da safiya , ruwan wanka ya kammala , okay to tayani cire kayan."

Tayashi tayi suka shige toilet yai wanka , yana fitowa ta taimaka masa ya shafa mai ,ta ciro masa kaya ya sanya shadda ce green taji aiki ,inka ganshi kamar sabon ango sai wani shek'i yake zubawa , bayan sungama breakfast ,ya dubeta cikin tausayawa zai yimata magana ya fasa , Afnan ta lura da yanayin sa , tace ”akwai magana a bakinka ko ?"gayamin mai ya faru? Haisam ne ya marai raice ,fuskar kamar mai shirin kuka yace ” lovely mama ce ...mama tace me ?"inajinka , shiru Haisam yayi kana yace ”aure takeson in k'ara , a razane Afnan ta mik'e lokaci d'aya hawaye suka cika mata ido ,ta dubi Haisam da kansa yake k'asa , yak'i had'a ido da ita , hmm kawai Afnan tace ”ta shige bedroom , ta janyo akwatinta , wanda ta d'ibi kayanta na kwanaki da tayi yaji, shirin sa hijab takeyi Haisam ya sha gabanta , yace ”dan Allah ki saurare ni kiyi hak'uri , a fad'ace ta dubeshi tace ”a halin yanzu bana k'aunar jin sautin muryar ka kabani guri intafi gidan iyayena , ada bana tunanin tafiya gidan mu yau kam wlh bazan kwana anan gidan ba , kuka takeyi mai ban tausayi , ta juyo da jajayen idanunta tace ”ada in ana yimin gori nakanji haushi , wai yau bakinka ne ke gayamin maganar aure,? kai da kanka kamar a mafarki."

Haisam yayi magiyar duniya Afnan tak'i yarda ta zauna , komawa bakin k'ofa yayi da gudu ya tare yana kallonta , amma nace dai karki fita ko?"idanunta da suka rufe tace ”koma me zakace kace dan wlh nikam nagaji da gorin da ake yimin , ta k'arashe maganar da share hawayen da suka kwaranyo mata , kasancewar ta doguwa kuma mai k'arfin jiki , ta shammaci Haisam ta turashi gefe , taja akwatinta ta fice , tsabar 6acin rai hartazo bakin titi bata lura ba , sbda tsakaninsu da d'an tafiya ,mai mashin ta tare tace ”ya kaita unguwar su , d'ora akwatin tayi itama ta hau suka d'auki hanya , suna isa gidan ta bud'e jakar hanunta ta mik'a masa kud'insa , kasa shiga gidan tayi dan rabonta da gidanan zatakai wata shida , tunda ta ta6a kawo k'ara mutanen gidan suka koreta kamar ba gidan su ba , cikin sanyin jiki taja akwatinta , ta bud'e get d'in ta shige , jikinta ne yakuma sanyi sbda tana tunanin abinda zata je ta tarar, bud'e k'ofar da zata sadata da d'akin mahaifiyar tata tayi , ganin babu ,yasata samun guri ta zauna ,jin alamun shigowar mutum yasata dai daita nutsuwar ta , mezan gani? nace mezan gani? uban me kikazo yimin da akwati?" cikin kuka Afnan ta gangaro daga kan kujerar da take zaune tace "mama ki yafemin dan Allah ,Haisam ne zai ƙara aure...aure?!!cewar momy ,da kyau kinga irin abinda muke jiye miki ko? dady ne ya shigo yana cewa"menakeji kamar hayaniya , hango Afnan yayi durƙushe a ƙasa yace "mekikazo yi ?bakin canza iyaye bane ? dady wlh ba haka bane kuyi hak'uri , momy ce tace ”wai aure mijin zai k'ara shine tazo , dady ne yace ” to ta tattara ta koma ai mijin ta za6a akan mu to taje ta rik'e mijin , suna tsaye a kanta suna zazzaga mata masifa ."

Dama tasan za'ayi haka , amma zata jure koma menene da zai faru , ficewa dady yayi ba tare da yace ”komai ba , momy ce ta zauna a gefen kujera tace ”in har kinason farinciki na to wlh sai dai kibar auran wanan munafikin dan bamu gaji tsiya ba , har meyaci dazai wulak'antaki , cikin sha shek'ar kuka tace ”momy bazan iya rayuwa babu Haisam ba , mari momy ta wanka mata tace ”uwar wa kike gayawa haka , to keda Haisam kunyi hanun riga ,inhar inada rai da lafiya to babu ke babu d'an talakawa ,momy ta k'arashe maganar ,tana nunata da yatsa , kuka Afnan ta saki tare da kwantar da kanta a kujerar dake gefenta , mom na fita direct d'akin Anty tayi anty na ninke kaya ta zauna gefen gadonta , cikin 6acin rai tace ”yarinyar ki ta dawo wai mijin zai k'ara aure , ehee aure kuma? cewar anty me ya tara dahar yake tunanin k'aro aure? " mu dama ba son auranan mukeyi ba ,kawai ta zauna Allah ya fito mata da wani dan wlh wanan yaron ba kalar Afnan bane, momy ce tace ”ganemin dai ,ana haka suka jiyo sallamar Anty ummi ta shigo , nanfa hira ta kaure , suka fara bata labarin Afnan ta dawo gida , cikin rashin jin dad'in maganar tasu tace ”wai maiyasa kuke haka ne ? bakwa tunanin mai kud'i da talaka duka Allah ne ya yisu ? kuma akwai lokacin da Allah zai azurta talakan , momy ce ta dubi Anty ummi tace ”duk da haka dai , girgiza kai Anty ummi tayi dan tasan basajin kira sunyi nisa , anty dake gefe tana yiwa Anty ummi kallon wulak'anci ta juya kai gefe..✍️.

Nayi tafiya ne bazaku dinga samun update kullum ba so yanzu dai sharhi da comments nake so .👌

Vote and follow me on wattpad👍.

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦
💍 💍 💍

*LAMARIN K'ADDARAR AURE NA!!!*

💍 💍 💍
💦🌹🌹🌹🌹🌹💦

_Story and writing by_

_ZAINAB HABIB_
_{Mom islam}_

My wattpad momislam2020

Zainabhabibu713 gmail.com

My telegram link
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2

*💦{AREWA WRITER'S ASSOCIATION}💦*

*BISMILLAHIR RAHMANI RAHIM*

EPISODE 9 & 10

Washe gari , mama tayi sammako da sassafe lokacin k'arfe bakwai 7am bubuga k'ofar gidan su Haisam tafara cikin gaggawa , Haisam daya farka daga baccin asbha ya mik'e yana mik'a ya isa bakin k'ofar ya bud'e , ganin mama yasashi d'an durk'usawa yace ”barka mama sannu da zuwa ,yawwa kawai tace ”ta ra6a ta gefensa ta wuce ,ganin gidan ba inda tasaba gani ba ,yasata cewa "ina matar gidan?" sosa kansa yayi kana yace ”ta tafi anguwa , bud'ar bakin mama tace ”Allah yasa intaje karta dawo , shidai Haisam burinsa yaga fitar mama lafiya , ganin ba shirin fita takeyi ba yasashi ,jingina da bango , mama ce ta dubeshi tace ”insha Allah nanda sati biyar ka zamo ango da yardar Allah zaku shekare da jariri , Allah yasa kawai Haisam yace ”dan bashida amsar da zai bata , juyawa tayi zata fice ta juyo tace ”to yakamata kaje gurin yarinyar ku fahimci juna ko ?"to Haisam yace ”da alamun k'aguwa a fuskarsa , mancewa tayi da sallamar ma ta fice , Alhmdulh Haisam yace ”ya koma d'aki yana cewa "dame zanji ga Afnan bata gida ga mama tazo min da wani batu , gaskiya bansan ina zan sa rayuwata ba."

Yau kwananta biyu a gidan su hakan ya yiwa dady dad'i kasancewar yafi son yaga duk zuri'arsa sun auri mai kud'i , zaune suke da rana kowa da farfesu a gabanshi , Afnan wayace a hanunta , ta gwada number Haisam shiru tak'i shiga , hakan yasata shiga damuwa tace ”wayo Allah , hankalin kowa na parlorn ya dawo kanta , momy ce tace ”to mai yafaru kuma?"sunkuyar da kai Afnan tayi tace ”babu komai , dady ne yace ”yanzu so nakeyi wanan yaron yazo ya baki takardar ki kinga zaki fara sabuwar rayuwa ko , uhm kawai Afnan tace ”kana ta maida hankali ga abinda take ci ta ajiye wayar a gefe , suna kammala ciye ciyensu mai aiki ta kwashe kayan ta kai kitchen , Afnan ce ta mik'e ta nufi d'akinta na da lokacin tana budurwa , fad'awa makeken gadonta tayi wanda fentin jikinsa pink ne ,kifa kanta tayi a fillo tafara rera kuka , tana dana sanin fitowa daga gidan mijinta mai yasa tayi haka ?"anya tayiwa rayuwarta adlaci kuwa? kodai zata gudu ne ?"wata zuciyar ce tace ”inhar kika gudu to zaki janyowa kanki mumunan hukunci gurin dady da Anty Bilki."

Mama na komawa gida ta fasa asusunta ,kud'i ta k'irga sunkai dubu ashirin ,kuma duk a kud'in da Haisam yake bata ne take tarawa , gud'a ta rangad'a wanda hakan yai sanadiyar juyo da hankalin mata gidan , tanajin alamun tafiya ta danne kud'in a k'asan cinyarta tace ”kowa ya watse ba komai nake ciba , duniyar ce ta yimin dad'i , komawa sukayi dan suna ,tunanin fad'a irinna mama , suna komawa ta janyo kud'in ,ta gyarasu tasa a lalita , ficewa tayi gidan wata dilaliya dake kusa dasu , tana sai da kayan d'aki da bokitaye da sauransu na amfani , sababbi da tsofafi , da sallama mama ta shiga , gidan samun dillaliya tayi a zaune tana k'arga kud'i , cikin fara'a d'ajin sallamar mama yasata , gyara zama tace ”barka da zuwa , ywwa mama tace ”inason kayan sa lalle bokiti ta kofin silba da kwano shima na silba , magajiya ce tace ”angama kud'inki dubu biyar , cikin rawar jiki mama ta mik'awa dilaliya kud'in aka had'a mata , cewa tayi sai zuwa dare zatazo ta d'aika dan munafukai sunyi yawa ."
Tafawa sukayi kana mama ta fice , bayan isha'i mama ta yafo gyale tayi ,hanyar gidan su magajiya , samun kayan tayi a gefe a baranda ta ajiye mata , dajin sallamar mama yasa magajiya fitowa ta nunawa mama kayan , d'auka tayi ta fice kai tsaye gidan su ta nufa , sai da ta lek'a babu kowa a tsakar gidan sanan ta wuce , washe gari ta shiga kasuwa ta siyo kayan buk'ata , tana dawowa baba yake tambayarta ina taje. "

Maganar auran Haisam tayi masa , dayake shima kamar ta gama dashi yasashi yin shiru, wata k'anwarta ta kirawo suka shirya kayansu , number Haisam ta kira , cikin sa'a ya d'aga maza maza kazo mama tace ”masa cikin sauri yace ”ganinan zuwa , ba a d'au lokaci mai tsayi ba Haisam ya k'araso gidan , da sallama ya shiga ganin mahaifiyarsa da k'anwarta yasashi durk'usawa ya gaishe su , amsawa sukayi cikin fara'a , k'anwar mama ce ta dubi Haisam tace ”ya maganar kai sadaki , zaiyi magana mama tace ”wlh mudin kaimin wata maganar da bata shafi na Maimunatu ba sai na sa6a maka , cikin sanyin jiki Haisam yace ”sati mai zuwa zan bada akai nawa sukace ?"mama ce tace ”basu yanke ba amma zan kuma tura manya , okay kawai Haisam yace ”kana ya mik'e ya fita."

Bayan ya mik'a musu d'ari biyar biyar yayi gaba, albarka suka shiga sanya masa , shiko yayi gaba , tundaga wanan rana Haisam ya zamo bashida walwala , yana tunanin zuwa gidansu Afnan yana tsoro saboda ra'ayinsu ta rik'a k'a , da komawarsa gida yai wanka ya janyo filon Afnan ya rungume yanajin kewar matarshi , cikin sanyin jiki ya janyo wayarsa , yafara lalubar number Afnan , cikin rashin sa'a yaji a kashe , tsaki yayi ya maida kansa ya kwanta yana tunani da ban daban , oh god wai maiyasa Afnan zatayimin haka ?"in anyi magana tace tana sona to wai shin haka so yake?" mik'ewa yayi ya nufi toilet d'in d'akin Afnan d'in , cikin sanyin jiki , alwalah yayi ya tada sallah lokacin anayin isha'i , nafila yayi ya kai kukansa ga rabil izati, ya dawo yakuma gwada number Afnan , cikin sa'a ta shiga , wani sanyi ne ya ziyarci zuciyarsa lokacin da yaji sautin muryar ta ta doki dodon kunensa , lumshe ido yayi , yana saurarar sallamar ta , hak'ik'a yayi kewar matarsa sai dai a halin yanzu yana ganin kamar bazata dawo gareshi ba, jin shiru yasa Afnan cewa my honey kayi shiru kuma lpy ? Haisam ne yace ”inafa lafiya kina gani tunaninki yana neman sani cikin uquba wlh karki d'auki hak'k'ina , kinsan dai ban baki izinin tafiya ba ko?"

A halin yanzu bazan iya jure rashinki ba a kusa dani, walh kin horani , wane laifi nayi miki dahar kike k'ok'arin azbtar dani , kalaman mijinta suna shigarta a hankali , k'ara rungumo filon da take zaune a kujera tayi kana tai rau rau da idanu tace ”zan dawo mijina dan Allah karka yi fushi dani zan dawo, k'ara sa sauta murya Haisam yayi yace ”to yaushe zaki dawo inyi miki tanadi na musamman , murmishin yak'e tayi tace ”zan dawo surprise zan yimaka , okay to Allah ya dawomin dake lafiya , suka ajiye wayar , momy dake tsaye a kanta tace ”keda mara zuciyar nan kuke waya ko ?"to babu maganar komawarki gidansa ,karma in k'araji , wlh zan sa6a miki , sunkuyar da kai Afnan tayi tace ”momy kiyi hak'uri dan Allah bazan sake ba , wucewa momy tayi batare da tabi ta kanta ba , washe gari Haisam ya gyara gida ya wanke ya sa turaren wuta ya gyara gado ya wanke toilet yanata farinciki, komai cikin zumid'i yakeyi , yana gama gyare gyaren , ya shige wanka yana fitowa ya shafe jikinshi da turaruka masu k'amshi ya ciro dakakkiyar shaddar sa mai kalar ruwan toka yasa yakuma feshe jikisa da turaruka, d'aga kansa yayi k'arfe sha d'aya na rana 11am k'ara gwada number Afnan yayi , jin shiru tak'i shiga yasa shi doka tagumi ."

********************
Bayan sati d'aya , Afnan ta rame sosai momy da dady sun kuma matsa mata akan bazata koma gidan Haisam ba , Haisam tayi kira a waya shiru , tun tana shiga ba'a d'agawa har yazo a kashe ,damuwa sosai ya shiga gashi safiyar yau mama ta matsa masa akan kud'in auran da yayi alk'awari, ba shiri ya tattara ragowar kud'insa na bank ya nufi gidan su mama , tana ganinshi tahau washe baki Haisam kansa na sunkuye ya wuce d'akin maman itama shigowa tayi tare da janyo bokiti ta mik'a gabansa ta zauna , Haisam ne yace ”mama wanan kayan fa?"washe hak'ora mama tayi tace ”wato da tsumun mu muke tare , jingina kai Haisam yayi batare da yakuma magana ba , ciro kud'i yayi yana juyasu ya ajiyesu a gaban mama , wani irin farinciki ne ya lulu6e mama , tace ”d'an albarka Allah yasa wanan auran kayi a sa'a , abin mamaki da ya dami Haisam shine mama bata ta6a kiran sunan Afnan kokuma cigiyarta , sai ta batun sabon aure take, maganar da mama tayi ne ya sashi dawowa daga duniyar tunani Haisamu kud'in nawa ne , kansa a sunkuye yace ”dubu d'ari ne farinciki fal zuciyarta tace ”Allah yai maka albarka ,amen Haisam yace ”kana ya mik'e yace ”to mama zan tafi , zaro ido tayi tace ”wato ni yanzu nazamo abokiyar jin kunyarka ko ?"
Ran Haisam babu dad'i yasa kai ya fice .

Anty Aishe ce keta doka sallama a parlorn Alhaji, amsawa yayi tare da cewa "Anty kishigo mana , shigowa tayi tana dad'a k'arewa Alhajin kallo , murmushin mugunta tayi dan tanada labarin Afnan ta dawo gida , shine tazo tayi ziga , Alhaji barka da hutawa ,yawwa Anty kinzo lafiya , lafiya lau Anty tace ” sai kuma naji wai wanan yarinya ta dawo gida?" uhm kedai bari Anty wlh abin yayimin ciwo dan rainin wayo ma aure zai k'ara , to bama batun auran ba ,mai yaci bare ya basu da har zai tattago wa kansa aure ?"nisawa Anty tayi kana tace ”to albishirinka yanzu daga kusada gidansu nake dan in tambayi halin da Afnan d'in take ciki , ashe kusan kullum sai uwar mijin tazo tayi mata duka , kuma tace ”sai ta wanke mata kaya🤭anty ta shararo k'arya .... cikin tunzura Alhaji yace ”dama wanan wahalar takesha shine ta zauna ?so takeyi ya kasheta ya huta ko."
Gyara zama Anty tayi tace ”koni ba son auranan nakeyi ba kai ka biyewa dangin uwarta dahar sukaci galaba akanka , ran Alhaji ya 6aci sosai ,yanzu kam ya yards da maganar Anty Aisha tabbas laifin momy ne aikuwa babu ita babu auran Haisam, dama ni ba son yarana sudinga shan wahala nakeyi ba , jeki kiramin Wasila 🤔dan k'ari tau babu batun cewa momy , Anty Aisha ce ta dubi Alhaji tace ”gaskiya bazanje ba karma ka kirata yanzu dan wlh zataga kamar nice na zugaka ka cimata mutunci , eh hakane .✍️

Follow me and vote on wattpad.

Dalilin k'inyin post d'ina shine kuna karantawa bakwa sharhi👌

💦🌹🌹🌹🌹🌹💦


Please Login or Register in order to submit comment