Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawoki lafiya"
Big boy yace "nima zan gaishe da mamanki"
Saudart tace "mamanmu dai kai ka ware kanka kenan?"
Yasa dariya yana yi mata gwalo.
Kiran sallahr magariba da akayi ne yasata mik'ewa ta rik'e masa hannu suka isa bedroom d'inta ta zaunar dashi akan gado ta shiga toilet d'auro alwalah, tana idarwa ta kamo hannunsa tace "zo kayi alwalah muyi sallah tare"
Ta taimaka masa yayi alwalar suka fito a tare ta shimfid'a musu sallahya ta kabbara sallah, tana idarwa ta fara adu'a a fili domin big boy yaji shima ya dingayi, bayan ta idar tace "gaji adu'ar da nakeyi ko?" Yace mata "eh" tace "to kadingayi, adu'arku yara tafi saurin k'ar6uwa kaji"
Big boy yace "to momy"
Sai da sukayi sallahar isha'i sannan ta ninke sallahyar ta fito parlo gurin abincin data jere a dinning ta zaunar da big boy akan kujera tace "tuwon shinkafa ko farfesu"
Big boy yace "tuwo momy tuwo"
Tayi dariya tasa masa itama tuwon tasa sukaci, yau kam yunwa takeji gashi mai gidan har k'arfe 9:pm bai dawo ba, bazata iya jiransa ba Dan haka ta samusu suci.
Sai da suka gama ci sannan ya shigo ya samesu akan kafet suna shan A.C, big boy yaje da gudu yayi mass oyoyo, ita Kuma tana dariya, Hamma Aliyu yace kinga kema dai yanzu akwai lefinki guda d'aya Wanda da kinayi yanzu Kuma kin dena"
Saudart ta sunkuyar da kanta tana cewa "sannu da dawowa, naga ka jima ne Allah yasa lafiya"
Hamma Aliyu yace lafiya Lau wlhi munata shan hira ne dasu Hajiya shine ban fito da wuri ba,
Yana rungume da big boy ya fara Hamma alamar barci yazo, ya d'agasa cak ya kaishi gasonsa dake can gefe da gadon Saudart yayi masa adu'a ya tofa masa...!

Kaina a k'asa Ina baku hak'uri akan latti da nayi please and please kuyi hak'uri naji sauk'i masu kirana a waya da masu yimin fatan samun sauk'i ta WhatsApp nagode.

08141799224
*FALAKšŸ’*

Mom Islam


E.O.W

Page 49-50

Yana shirin fitowa Saudart ta shigo.

"Yauwa baby muje d'akina zamuyi magana"
Saudart ta kama hannun Hamma Aliyu suka wuce d'akinsa,
Akan bed suka zube kowannensu fuskarsa d'auke da murmishi.
Saudart ta zuba masa ido tana kallonsa,
Hamma Aliyu ya hura mata iska kafin yace "uhm bafa guduwa zanyi ba"
Ba shiba har itama dariya tayi tana toshe baki, ya janyota jikinsa kafin yace kin yimin tambayoyi a k'alla sunkai kala biyar ko sunfi ma?"
Saudart tace "uhm"
Maganar sxx da shan nipples abinda yasa na dena Sha, kinyi shayarwa shine dalili ina tunanin har yanzu da ragowar ruwan nono,
Rashin dad'ewa ta matsalar itace "gaskiya da nafi jinki a matse yanzu kam dana fara sai inji kin bud'e.

"Kince nafi son big boy akanki, wannan ba haka bane, kece ta farko kuma big boy a jikinki aka samoshi dole inso abinda yakeda nasaba "dake.

"Shikuma cewa da nakeyi maman big boy ai banga aibu ba, amman idan kinaso a sauya wani sunan sai a sauya princess Saudart"


Da sauri ta rungumeshi tana dariya,
Germany
Yau kwana biyu da zuwan sheik Abdul-Latif,
Ranar ta kasance Monday Dad yanata shirin tafiya Aiki amma banda Falak, daya kirata a waya ma cewa tayi ciwon ciki take, dad ya k'araso har d'akin abin mamaki ya sameta tana daddana waya, ya k'araso cikin tausasa murya yace "haba daughter meyasa zaki dena taimakon dad d'inki?"
Ko kallon dad d'in batayi ba tace "Dad ni yanzu ka Dena Sona komai sai dai inji kace Sheik Abdul-Latif sai kace ka sanshi"
Dad ya girgiza kai kafin yace "to kiyi hakuri zomuje ki za6i kalar furnitures d'in da kikeso"
"Dad wai auranne harda wani gado?"
Dad yace "eh mana ai dole ne ko kinaso mutane su fahimci abinda ke faruwa?"
Falak ta mik'e dama already ta shirya ta d'auki mayafi ta ninke a kafad'a, dad ya rik'e hannunta suka fito parlo, kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta tayi k'arfe 9:30am,
Dad yace "kiyi breakfast sai mu wuce ni nayi tun 8:am"
"No dad banajin yunwa muje kawai"
Bai tsaya sake yi mata magana ba, domin lalla6ata yakeyi suka wuce parking space, suka shiga mota.
Bayan sun iso company d'in motar tayi parking a inda ake ajiye motoci suka fiti, Falak ta kar6i y'ar ledar dake hannun dad tana dariya,
Dad yace "daughter kenan me kika gani"
Falak tace "dad invitation card nefa na bikin waye?"
Dad yace "na bikinki zan rabawa abokan arzik'i ne"
Abin ya sake bata dariya, sbda tana yiwa dad d'aukar yana aikin banza ko tace yana k'ona kud'insa, auran da ba wani jimawa zeyi ba, ai ko a hotel zasu zauna.
Suna shiga office Dad ya wuce sashen sa itama ta wuce bayan sun gaggaisa da mutane, sai tsokanarta suke suna cewa "Hajiya ashe biki yazo"
Falak tayi murmishin yak'e ta shige ciki, batasan sheik Abdul-Latif yaje yayo hotunan free weeding ba,
Abin mamaki baya k'arewa hotuna sun karad'e garuruwa harda Nigeria Facebook Instagram WhatsApp telegram Twitter da tiktok, gash hotunan sunyi farinjini, duk Wanda ya gani sai yayi saving ya d'ora a status da sauransu, abindai sai Wanda ya gani, sun dace sosai, Sheik Abdul-Latif yafi Falak gaske duk da itama d'in ba baya ba gurin kyau.
Tana zaune kamar ance duba Instagram, tana dubawa taga photonta an rubuta Mrs Sheik Abdul-Latif,
"Bura'uba"
Falak ta fad'a tana buga table ta zare farin gilashin dake manne a idonta ta fito waje tana mamakin raina mata hankali da wannan nonsense d'in yayi, "a inama ya Sami hotonta?"
Batada mai bata amsa dan haka ta koma ciki rai a 6ace,
Wunin ranar duk Wanda ya shigo cewa takeyi aje gurin dad ko gurin manyan ma'aikatan.
Zuwa yamma babu wanda ya gane kanta har dad d'in,
Tana zaune tana harhad'a kaya mutumin nata yayi sallama,
Runtse ido tayi ta bud'e tana searching d'in irin rashin mutuncin daya kamata tayi masa,
Sbda jira take taji yayi mata magana.
"Mrs Abdul-Latif"
Ya fad'a kansa tsaye,
"Meyasa zaka baza hotunanmu a duniya bayan ga alk'awarin da mukayi dakai akan wannan auran?"
Sheik Abdul-Latif ya gyara tsayuwa kafin yace "haba kyakkyawar mijinta haba tauraruwar mijinta"
Falak tace "tauraruwar dad dai Allah ya kyauta, kuda kuka d'auki soyayya da amfani kuje ku k'arata a haka zaku k'are wlhi, ta janyo system d'inta ta rik'e a hannu kafin tace "kaga wannan wlhi Allah ya fiyemin komai musamman ma wannan k'addararren auran"
Sheik Abdul-Latif yace "Auranmu mai inganci ne wlhi sai na koyar dake soyayyata sai na ilmantar dake menene so sai na nuna miki tsantsar shak'uwa da banbancinta da soyayya sai na nuna miki rayuwa babu ni zai iya zame miki tamkar duhu a rayuwar ki"
"Kull wlhi ka gyara kalamanka ba'a haifo Falak domin tayi soyayya ba, ko ce maka akayi soyayya nazoyi duniya?"
"Sheik Abdul-Latif ya sheik Abdul-Latif yace " kowacce zuciya Allah ya halicceta da soyayyar Allah da manzonsa sannan kuma da soyayyar halitta, kinga kema kina ciki, da babu soyayya da baza ayi aure ba"
Falak tace "naji shikenan lokacin tafiya yayi"
Ta ra6a ta gefensa ta wuce.
A hankali ya furta "I love you Falak with all my heart"
A mota sai mai-maita maganar sheik Abdul-Latif takeyi, dad yanata yi mata magana Sam bata jinsa, har sai daya ta6ata sannan ta juyo.
A haka suka isa gida,
Dad bai sake cewa ta za6i irin kayan gadon da takeso ba yadai sa ayi mata mai tsadar gaske Wanda sai d'an wane da wance.
Talata.
Biki ya rage saura kwana ashirin da biyar, abu sai tafiya yake, a y'an kwanakin nan bikinma ko a jikin Falak dan sai sha'aninta takeyi babu ruwan ta,
Egyptā€¢ā€¢
Granny ce zaune a parlo tana ta sababi Amma Babu Wanda ya kulata a cikinsu, tasani Sarai Abdul-Naseer d'in yana ciki bawai ya fita bane,
Cikin d'aga murya tace "Nasiru wlhi zanci mutuncinka dama ka d'aukoni ne ka mayar dani kamar mara gata?"
Har yanzu dai shiru ba'ace mata komai ba,
Acan bedroom d'in Fadwa sunata sanya kayan da zasu bata tsoro tunda daren jiya ta hanasu watayawa, dan harya fara tunanin ya mayar da ita gida.
Tana turo k'ofa ba tare da tunanin komai ba ta hango wani dodanni anyi musu adon farin Kaya kamar gawa, da gudu ta ruga tana cewa "Nasiru nayi gamo kuzo ku fiddani daga gidannan ko me nakeci wlhi na hak'ura wannan masifa har Ina?"
Tana fita Abdul-Naseer ya mik'awa Fadwa hannu suka tafa ya cire kayan ya fito yana mik'a,
"Nasiru saboda rashin tausayi kana jina inata darara ihu shine ko kazo jin abinda yake faruwa ko?"
Abdul-Naseer ya rausayar da kansa kana yace "nifa daga bacci na tashi Ina matar gidan?"
"Oho idan iskancin nata ya motsa ko yankani za'ayi bazata fito taji ko meye ba,nidai shawarar dazan baka shine ka k'ara aure dan wlhi juya ka auro sai dai taci tayi Kashi kusan wata biyar kenan Ina la'akare da ita ko 6atan wata bata ta6a yiba"
Abdul-Naseer ya kamo hannun granny kafin yace "abinda nakeso kisani anan shine aihuwa da rashinta duk na Allah ne,ai Fadwa batayi dad'ewar da A'ace dole ta samu ciki a wannan tsukukun kwanakin ba"
"Au haka kace? Ina kallon komai da kukeyi kuma ina jinku, koda yaushe a band'aki kuke wuni kamar jikokin agwagi zaka kawomin maganar banz, gobe zanje gida in dawo idan na dawo zakaci sammaci Dan harda me ruk'iyya zan taho gidannan akwai aljanu gaskiya ban yarda dashi ba"
Abdul-Naseer yace "to"
Tabbas beji dad'in aibanta masa mata da takeyi ba,Amma babu inda ya iya da ita dole ya lalla6ata su rabu lafiya, sai yanzu yake nadamar kawota gidansa.
Jiki a sanyaye ya shiga bedroom d'in Fadwa, ya sameta ta jik'e da hawaye, ya janyota jikinsa yace "haba mai ya faru Kuma?"
"Abdul-Naseer Allah yasan ina sonka kaima nasan kana Sona, amma ga kakar ka tana neman rabamu, nima inason inga na aihu k'ila haka Allah ya halicceni"
Ta fashe da matsanancin kuka mai ratsa zuciya,
Bazai iya jurewa ganin kukanta ba yace "d'auko mayafi mu fita"
Babu musu ta d'auko suka fito, y'ar sa ido tana zaune a parlo tana ganinsu tace "ina zuwa?"
Abdul-Naseer yace "zamuje gaisuwar marar lafiya ne"
"Au ni kad'ai zaku Bari a gidan?"
Abdul-Naseer yayi mata gatse yace "in zaki taho"
Aiko granny ta d'auko mayafi ta fito suka jera a tare suka je parking space suka shiga mota,
Yana driving yana kallon mood d'in Fadwa daya sauya tashi d'aya,
Haka suke tafiya babu mai cewa kowa komai har suka isa gidan su Abdul-Naseer d'in, granny na ganin yayi horn a bakin get tace "oh kana nufin ni bazakaje dani dubiyarba kenan?"
Abdul-Naseer ya dafe kansa yace "dan Allah ki shiga zan dawo mu tafi anjima"
"To"
Tace, abinka da tsufa sai jera musu Allah ya isa takeyi tana cewa "munafuki ya fifita matarsa akan kakarsa"
Tana shigewa Abdul-Naseer yayiwa motar key a guje.
Sunyi tafiya mai nisa kafin ya tsaya a gefen titi, yace "My Fadwa ki ajiye a ranki Abdul-Naseer naki ne bana wata ba, nasan daga d'azu zuwa yanzu granny ta sanya miki tantama a cikin zuciyarki please ki cire ki watsar da komai muci gaba da rayuwarmu"
Fadwa ta share hawaye kafin tace "kayimin alk'awarin bazaka yimin kishiya ba" wlhi bazan iya jure ganinka tare da wata ba"
Abdul-Naseer yace " I promise insha Allah sai dai wani ikon Allah"
Daga haka yaci gaba da tafiya har suka isa restaurant, take away yayi musu na foods da drinks daga nan suka dawo gida, ya k'udurta a ransa bazai sake dawoda granny gidansa ba sbda tana neman tarwatsa masa farinciki.
Acan 6angaren granny abin harya isheta, har anyi magriba Abdul-Naseer bezo d'aukarta ba, dole tayi alwalah tayi Sallah tana jiran zuwansa, bata gama tsurewa ba sai da taji anyi isha'i har wajen k'arfe tara.har goma shiru bai zoba, dole ta kwanta badan yaso ba, sbda ta saba dacin kayan k'walama a gidan, anan kuwa kafin ta rarrafa tahau steps ta gayawa masu gidan sai taci kwakwa"
Switzerland
"Hindu meyasa kike son nace min ne bayan kinsan nace yanzu ba wannan rayuwar bace a gabana"
Maleek ya fad'a yana kissing d'in Hindu,
Ratayo hannuwanta tayi a kafad'ar sa kafin tace "nayi kewarka wajen one month kenan bama tare"
Maleek ya watsa mata kud'i mai yawa kana yace "zan nemeki sorry my sweet lady"
Bataji zafin wulakancin da yayi mata ba, kasancewar ya watsa mata abinda tafiso Wanda yake wanke mata zuciya,
Tana tafiya, Maleek ya d'aga waya ya kira wani saurayi wanda befi 20yrs ba, yace "ya maganar da mukayi dakai zan baka duk abinda kakeso gida Mai kyau sabuwar mota y'ar yayi kai koma meye"
Yaron yace "okay ai gobe ne alk'awarin sbda yau munada jarabawa"
Idan kukaga ban turo k'arfe 8:pm ba ayimi afuwa zuwa 9:pm please

Nagode da shar'i wlhi shike k'aramin k'warin guwaiwa.

08141799224
*FALAKšŸ’*


Mom Islam

E.O.W


*_Inayi muku albishir da sabon littafina mai suna WAKE ʊAYA, ba sai nace muku komai ba duk Wanda ya karanta FALAKšŸ’zai bada labari_*

Page 51-52
Germany
Yau Falak ta riga Dad fita, tana zuwa company ta samu sheik Abdul-Latif da wasu mutane a tsaye, bata bi takansu ba ta shige dan ba sune a gabanta ba.
Shawarar d'auko system d'inta tayi domin ta duba abubuwan da suka faru jiya da tak'i zuwa office.
"Whtsapp"
Ta fad'a da cold voice d'inta,
Sak'onni rututu ne suka fara shigowa, na mutum biyu ta aiyyana a ranta zata duba, Ummu da Dad,
Farko ta bud'e na Dad, video ya turo mata na gidan da sheik Abdul-Latif ya siya kayan furnitures d'in kuwa wanda yasa akayi order d'insu,
Tana dariya tace "wlhi gidannan yayi kayau ammafa idan ni aka siyawa anyi asarar kud'i wlhi"
Ta fita a Dad ta duba na Ummu.
Anko suka fitar, shadda wagambari wacce a farashin sari takai 100k five yard golden color,
Falak ta rik'e baki tayiwa Ummu voice tace "Ummu kina tunanin wannan shaddar mai tsada nawa za'a kashe?"
Cikin sa'a Ummu tahau online tace "kinci gidanku ko wanne mutum d'aya 100k Falak 100, Saudart 100k Munira 100k Hibba 100, sannan ni da dad 200k nawa ya kama?"
Falak tace "700k"
Ummu tace "kina ganin kud'in yayi yawa ne?"
Falak tace "eh Ummu a tausayawa dad"
Ummu tasa dariya kafin tace "na mance ban gaya miki ba, jiya dad d'inku yaba saurayinki waya muka gaisa har saurayin yace dole sai dai mu turo da account number, da fari nak'i Dan har kashe waya nayi, dad yace "dole in turo ba'a mayar da hannun kyauta baya bayan mun tura sai gashi ya turo mana da dubu d'ari biyar"
Falak ta dafe k'irji ta kasa cewa komai kawai ta tsinci kanta da kashe data ta kifa kanta akan table.
Sallama dad yayi a k'ofar office d'in nata yaji shiru, daga k'arshe dai ya murd'a handle d'in k'ofar ya shiga da sallama, samunta yayi ta kifa kai, yayi magana har sau uku Amma bata d'ago ba, cikin tsoro ya tallafo kanta yana cewa "daughter.."
Shiru nanma, sai daga baya ya gano ai suma tayi, ya d'auko ruwa ya yayyafa mata,
A hankali ta bud'e idanunta ta saukesu akan dad kafin ta fashe da kuka,
"Meya faru?"
Dad ya tambayeta fuskarsa akwai alamar damuwa,
"Dad ka kaini hospital please a duba brain d'ina"
"Wace irin magana kike fad'a FALAK?"
Ta sunkuyar dakai hawaye na zuba a idonta tace "jiri nakeji ka kaini asamin drip"
Dad ya kalli agogon hannunsa kafin yace yanzu k'arfe 10:am zamuyi meeting barin samo Mai kaiki oya yi K'arfi da jikinki muje parking space"
Falak ta gyara zaman mayafinta tare da mik'ewa ta d'auki wayarta Dad na rik'e da hannunta suka fice, lokacin da suka fito sheik Abdul-Latif na shigowa da motarsa, yau sabuwa fil aka hawo mai masifar kyau,gata dark blue.
Sheik Abdul-Latif na ganinsu yayi parking a gefe, sakamakon ganin mutuniyar tasa da yayi sai wani had'e hanya take kamar zata fad'i,
Bata ma san shine yayi parking d'in ba, saboda k'ank'ancewa da idanunta sukayi, musamman yanzu da zazzafan zazza6i ya dirar mata, batajin maganar ma da sukeyi itadai tasan a tsaye take.
Dad yace "wlhi na shiga office d'inta na samu ta kifa kai akan table kuje dai hospital kawai, sheik Abdul-Latif ya kamo hannunta yasata a gidan gaba shima ya shiga suka wuce hospital.
Sosai ta kwantar da kanta a jikin kujerar motar Sam ko iya bud'e ido batayi sbda tsananin zafin zazza6in,
Cikin ikon Allah suka iso katafaren asibitin UniversitƤtsmedizin Berlin Berlin hospital dake nan Germany,
Cikin kulawa irin tasu da marar lafiya, dan kamar zasu mayar da ita ciki, tunda aka bata gado masu tattalinta suka shigo, hankalinsa nakanta, ita kuma sai bacci takeyi.
Har k'arfe 1:30pm bata farka ba, ya mik'e da niyar zuwa ya gabatar da alwalah kafin ta farka,
Ana idarda sallah ya dawo, ya sameta a zaune an bud'e mata drinks d'in daya ajiye an had'a mata tea, a hankali ta d'ago ido ta kalleshi ta kawar gefe sabda tuno farincikin da Ummu tayi da kud'in daya tura musu, shiko besan abinda ke wakana ba,
Cikin kulawa yace "sannu princess"
"Uhm"
Tace bakinta a kunshe, kai kace wacce ta cusa bread.
Bai samu yasa Abu Mai nauyi a cikinsa ba, duk da shid'in gwanin kwasar girki ne, sai drinks dayasa Allah yasa ma mai kauri ne.
Haka sukayi zaman kurame, dayaga ko kulashi batayi ba ya shiga danne-danne a wayarsa, sai a lokacin ta tuna ai ta fito da waya bata Kuma San inda wayar tata tayi ba, gashi tana son tambayarsa bata son raini,
Har yamma tayi tana kan gadon a zaune bata motsa ba, har yayi la'asar ya dawo, yace "ki tashi muje kiyi alwalah ko a zaune sai kiyi sallahar"
"Banayi"
Falak ta fad'a kai tsaye, sheik Abdul-Latif yace "ashe dai zamu samu baby nan kusa?"
Sam takasa fahimtar abinda yake nufi, Dan harga Allah itakam bata d'auka shima ya mayarda abin serious ba kamar inda ta d'auki auren nasu a shirme, sai ta watsar da zancen nasa.
Wayarsa ta fara ringing, taga ya d'aga tare da durk'usa har k'asa yace "Imam muna hospital princess ce babu lafiya"
Already sunsan ita d'in ce tunda sunan da yake kiranta dashi kenan a gidansu.
Imam yace "kodai muzo ne?"
Sheik Abdul-Latif yace "a'a yanzu ma za'a sallamemu an kirani a office da sauk'i"
Imam yace "a mik'awa Falak wayar"
Duk rashin mutuncin data shiryawa kanta sai ta fasa ta sunkuyar da kai cikin ladabi da ban girma ta gaishesa, ya amsa cikin kulawa kafin yayi mata ya jiki tace masa yai sauk'i"
Zuwa k'arfe 6:pm aka rubuto musu sallama, a office d'inne sheik Abdul-Latif yake tambayar doctor abinda ke damun Falak d'in, doctor yace "ba wata babbar matsala bace firgita tayi amma yanzu komai normal sai dai k'arfin jiki, shima insha Allah zamuyi k'ok'ari ga wannan paper kaje pharmacy ka siyo Allah ya bata lafiya".
Kallon kud'in yayi a takardar sallamar, ya mik'a šŸ§ d'insa aka ciri kud'i yaje zai kama mata hannu domin su fito, ta fizge hannun ta matsa daga inda yake, dole ce tasata hawa motar badan taso ba sai dai saboda kar dad ya fahimci wani abun,
Ta jima a motar kafin ya shigo hannunsa rik'e da leda, ya tayar da motar suka wuce".
Yana driving yana satar kallonta, ita kuma tanata yamutsa fuska a back side, sbda wannan karon tak'i shiga gaba.
Har suka iso bece mata ba bata ce masa ba,
Yayi Horn a bakin get d'in gidansu, ana budewa ya shiga da motar yana parking dole dai ya rik'e mata hannu suka k'arasa badan taso ba.
Har bedroom d'inta ya kaita, suna shiga ta fizge hannu kafin tace "dan Allah ka wuce"
Sheik Abdul-Latif ya kalleta da mamaki a zuciyarsa yace "wato taga munzo gida?"
Kamar daga sama cikin mamaki da tsoro Sheik Abdul-Latif ya cire alkyabbar dake jikinsa ya wurga gefe yayi mata rumfa da faffad'an k'irjinsa,
K'amshin turarensa ya addabi d'akin,
K'wayar idonta yake kallo ita Kuma ta wani d'aga idon sama daga k'arshe ta runtse idanunta saboda ta gama saddak'arwa wannan kasheta zeyi bawai zai barta da numfashi bane,
Sam batasan, haka a soyayya ba shiyasa ma bata kawo, soyayyar yake gwada mata ba,
Jira kawai take taji ya shak'eta babu buk'atar tayi ihu saboda idan wani yazo cetonta zai iya had'awa dashi, cikin sanyin murya irinta marar lafiya tace "kabari inyiwa Dad magana kafin in ambaci innalilahi wa inna ilaihir nasan ko yanzu na mutu bazan mutu da bak'incikinsa ba"
Shimafa bai fahimci abinda take nufi ba, had'a jikinsa Kuma da yayi da nata ba k'aramin kasala ya haifar masa ba, ya kasa daurewa da Kuma mik'ewa yayi tafiyarsa ya k'udurta a ransa yau sai ya tsotse wannan bakin da yake bashi sha'awa,
Ko uffan bece mata ba ya had'e bakin nasu guri d'aya jikinsa har yana rawa, Falak tace "wlhi sai nayi maka ihu, a wani film dana ta6a kallo wannan abun da kayi yana nufin fyd'e kenan"
Sheikh Abdul-Latif ya runtse ido tare da yin kyakkyawan murmishi yace "wannan abun da nakeson yi miki shine...
Sai ya sanya bakinsa ya janyo harsheta ya fara tsotsa, dannewar da yayi mata bana Wasa bane, dan haka yasa ta kasa tureshi sai dai ta jira d'agawar da zeyi,
Kamar me neman wani abu a bakinta haka ya dinga dashewa, har yakai hannu zai ta6o mata breast ta bige hannun tare da cizonshi a harshe, da sauri ya mik'e sai Kuma taga yana dariya, a fili yace "haduwar jikinmu ya haifarmin da matsananciyar sha'awa ina fatan zaki amince in ajiyeta kafin nan kafin darenmu na farko?"
"What!!!"
"Mtsw wannan iskanci ne Please fita, sa'arka d'aya bani da lafiya wlhi da saina illataka"
Sheik Abdul-Latif yasa alkyabbarsa kafin yace "bazaki iya ba" ya fice.
Kallon ledar maganin tayi ta janyo tare da karanta lokutan daya kamata Tasha ta mayar ta ajiye.
Sai da akayi isha'i sannan Dad ya dawo, ya shigo hannunsa rik'e da frame mai d'auke da photon Falak da dad harda Ummu d'ayan Kuma dukkansu harda su Saudart.
Kasancewar tasami sauk'i ba kamar d'azu ba, yasa ta fito parlo parlo ta zauna, tana ganinsa ta washe hakora, photon da Dad ya nuna mata sunyi mata kyau sosai, amman dad bai sanar mata ga Wanda zai bawa ba, ko ga inda zaisa ba.
SWITZERLAND
Yau satin beauty uku
Safiyar talata momy tazo lokacin k'arfe bakwai, 7am momy ta lura da abubuwan da suke faruwa, momy ta janyo beauty jikinta kafin tace "Islam meke faruwa?"
Beauty ta fashe da kuka kwai ta tsinci kanta da bawa momy labari har akan gawar
Cikin firgici momy ta kira number Arif cikin sa'a ta shiga, yana d'agawa tace "kana ina ne?"
Arif yace "ina haryar zuwa gida gurin beauty"
Momy tace "to shikenan, kafin ta rufe baki sai gashi ya shigo ashe yana k'ofar d'aki suke maganar.
Arif ya shigo ko sallama Babu, already ma yariga da ya cire komai sai boxes ya shigo da niyar firgitata ya far mata.
yaga momy, a zaune cikin firgici ya durk'usa a gabanta ladabin dole yace "sannu da zuwa momy"
Yauwa tace "kafin tace "Arif banji dad'in ganin beauty haka ba, yarinya ta wulakance ko kyan gani Babu?"
Arif yace "momy komai akwai a gidannan kud'i abinci"
Momy tace "duk arzik'in gidan aure inhar Babu kwanciyar hankali wlhi aikin banza be"
Arif yayi shiru, momy tace "meya kawo gawa cikin gidannan?"
Gaban Arif ya bada duuum.
Momy ta ajiye mayafinta a gefe ta fara searching ko Ina, Babu d'akin da bata bud'e ba, Amma bata ga gawa ba ko abinda yayi kama da cutarwa,
Momy ta dawo Babu k'warin guwaiwa tace "beauty kekuma sakaiyyar da zakiyimin kenan?"
Nayi miki inuwa kina neman jefani Rana? So kikeyi kice Arif yana kisa domin a raba auranku ko? Wlhi duk abinda kika sake fad'a koda Wasa bazan sake yarda dashi ba tunda baki da kirki"
Momy ta fice hannunta rik'e da mayafi rai a 6ace, Arif yayi murmishi ita Kuma beauty ta fashe da kuka, ya janyota da K'arfi ta fad'a jikinsa ya zuge zip d'in rigarta tare da fitoda breast d'inta waje ya kama kamar wani marar hankali tasa ihu saboda zafi takeji kamar zai cire mata kan nipples....!

Ayi hakuri bamu da wuta Amma yanzu komai normal zaku dinga jina,
Masoyana masoya littafin FALAK, inayi muku albishir da sabon littafina Wanda yazo da sabon salo kardai ince yafi Falak kuce ba hakaba, wlhi Ina baku labarin cakwakiyar dake cikin littafin sai ya baku mamaki ga sarkakiya, sai a cikin littafina mai suna WAKE ʊAYA... Nafara posting d'insa yau d'innan 08141799224 Mom Islam
*FALAKšŸ’*

Mom Islam


E.O.W


Page 53-54

Yana mik'ewa tace "Allah ya isa"

Duk iya dauriyarta gurin jure hakan ta kasa dole ta had'ashi da Allah, bai kulata ba ya fice,
Beauty ta dinga rera kuka.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya mata cikin k'unci da rashin walwalah a 6angaren momy kuwa sam bata yarda da maganar beauty shiyasa ko marmarin zuwa gidan beautyn batayi dan bak'inciki.

Nigeria
"Sweetheart kiyi sauri ki fito wlhi idan mukayi late kece kika jawo mana"

Hamma Aliyu ya fad'a yana kallon big boy dayasha wankan shadda mai ruwan k'asa harda malun-malun, Saudart ta fito, gaskiya ban ganeta ba, ammandai ganinta a gidan yasa dole nace "eh itace fa"
Tana sanye da shadda irinta big boy anyi

Please Login or Register in order to submit comment