Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zeyi"
D'aya daga cikin y'an Jaridar yace "bakya ganin idan akayi haka ba'ayi rashin adalci ba?"
Falak ta gyara gashin kanta kafin tace "eh su zasuga hakan amma mu munyi ne domin kawo gyara please ku barni haka inada abunyi, sosai dad ya tsaya yana kallonta gata da k'arancin shekaru amma ko tsoron wani abun batayi "oh Falak" dad ya fad'a a hankali tare da shigewa ciki.
Ba iya masu aiki a company dinba hatta mutanen gari sun zagi Falak sun Kuma alak'antata da rashin Imani.
Yau bawani aikin kirki tayi ba, sakamakon wani yanayi da takejin kanta a ciki, lokaci-lokaci takanji gabanta ya fad'i ta mik'e zubur, dad ya kira wayarta yakai sau uku tana gani tak'i d'agawa, tunda yaga haka yasan yau daru ne ya motsa bari ya je inda take tunda you tana kan Sarauta, yana shiga ya sameta ta had'a kai da guwaiwa idanunta sunyi jawur, ta d'ago ta kalleshi, da ganin hakan yasan akwai gagarumar matsala wacce yake tsoron afkuwarta, jikinsa na rawa, yaja kujera kusa da ita ya zauna, kafin yace "haba y'ar albarka mai taimakawa dad d'inta mekuma zai faru please ki sanar dani'
"Dad zanje d'akin sirri, an rasa Taswira ko?"
"Eh an rasa harda kwalbar jini"
Kwalbar jini kai ne ka yarda ita ina tunanin tana cikin d'akunan, taswira kuwa akwai wasu wanda sukeyi mana aiki sune suka sace"
Dad ya zube a gurin zai fashe da kuka Falak tace "naga akwai gurin da akasa numbars ko kuma barmin komai a hannuna dad jeka kwanta"
Muryar dad kamar ta mai kuka yace "Falak wace irin kwanciya Ni bazan iya kwanciya ba"
Falak tace "Ina zuwa"
Bata jira abinda zaice ba ta shige da uban gudu tasa key ta bud'e d'akin duk iya k'warewarta hanyar bincike da baiwa da Allah yayi mata bata isa ta bud'e k'ofofinnan kai tsaye ba, batare da ta duba taswira ba, bata k'arasa cikin d'akin ba ta fara dube-dube, tana danna wasu numbobi a jikin k'ofar k'arshe tana yakice zufar dake sintiri a fuskarta, da sauri tabar gurin tana hamdala, kuma duk numbers d'in data sauya akwai a taswirar.
A inda tabar dad anan ta sameshi, ta duba agogo, tace "nashiga k'arfe 9:am na fito k'arfe 12pm, alhmdulilh, dad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin yace "Falak baki sanar dani komai ba"
Falak ta zubawa dad idanu kafin tace "dad akwai masu kawowa d'akin hari, yau ko gobe jibi ko gata, Allah shine masani nidai nabawa gurin kariya ne, am bazamuzo aiki Sunday ba dama, haka Monday ma zamu zauna a gida dad karka damu ni nasan me nakeyi"
"Falak, kinaso komai namu ya lalace ne? akwai mutanen da mukayi alk'awari dasu zasuzo su kar6i kaya Kuma na had'a musu me kike ganin zai faru"
"Komai mukasa gaba mu rok'i za6in Allah wlhi dad inhar kace sai kazo zan koma Nigeria bazan sake dawowa ba"
"Innalilahi wa inna ilaihir raji'un"
Dad ya ambata yasanta da taurin kai ga lafiya oho.
Wunin ranar daga ita harshi sun wuni cikin 6acin rai, ita a nata 6angaren tanason kawo gyara, shikuma dad yana ganin tanason ta kawo masa wani tsari ne, wala Allah ya kawo cigaba ko akasin hakan.
6:pm suka wuce gida, kai tsaye dad ya wuce bedroom d'insa, ga mamakinta sai yaga Falak zaune a parlonsa tanata sarrafa System, shifa abin har mamaki yake bashi, tabbas Falak tafishi sanin komai amma ita d'in sirrinsa ce, ba lallai ya iya koda kwatankwacin abinda tayi ba.
Cikin fara'a tace "dad yau kwana zamuyi babu bacci zoka zauna"
Ashe a cikin daren su Maleek suka shirya zuwa.
Babu Maleek d'in Kuma babu Arif, daga Manaf ne sai sauran mutanen daya gaiyyata masana k'ofofin sirri harda wanda Falak ta Kira mutum Uku.
Dad yaga alamun tafiyar mutane ko wanne bayansa goye da jaka,
Sai gashi sunata haska gurin da fitila kasancewar koda gurin k'wan wutan anyi masa gida ne, sunyi nisa a tafiyar tasu, d'aya daga cikinsu yace "ku tsaya mu duba taswirar nan naga tsakaninmu da gurin zai iya kaiwa tazara 100, suka zato ido ai babu musu suka buɗe Taswira, da mamakinsu suda aka ce musu tafiya ta kwana biyu ko su kwana nawa zasuyi oho,
Cikin firgici da tsoro sukaga tsakaninsu da inda zasuje tafiyar wata biyu gashi sunyi gaba Babu halin fitowa sai an k'arasa, dama a k'a ida k'oshi dad d'inne zai shiga yake ganin ya fasa to bazai iya dawowa ba ko bazai d'auki komai ba sai ya shiga ya fito,
"Tafiyar wata biyu!!!"
Manaf yace cikin firgici dukkansu sun firgita sosai.
Dad yayi murmishi kafin ya dafa kan Falak yace "ubangiji yayi miki albarka ubangiji yasa ki gama lafiya ubangiji ya dauwaamar da farinciki a cikin rayuwarki, hausawa sunce abinda babba ya hango yaro ko tahau rimi bazai hangoshi ba, to nidai nace abinda my lovely daughter Falak ta hango dad bazai hangoshi ba"
Falak tayi murmishi tashi d'aya ta gimtse fuska saboda ganin taswirar dad d'inta da tayi a shimfid'e a k'asa suna neman hanya, duk wata hanya da zata sadasu da d'akin,
Falak tace "dad akwai matsala abin yana neman fin k'arfina"
Dad yace "Falak yanzu k'arfe 2:am na dare jeki kwanta a k'arasa aikin da safe"
"Haba dad suda sukazo neman Haram sun hana idonsu bacci, mu da muke neman halak muke gyara kayanmu shine zamuyi bacci?"
Dad ya zabga tagumi har yana gumi.
Taci gaba da sarrafa System d'in cikin k'warewa.
Switzerland
Night
6:11pm Beauty tana zaune akan sallahya ta idar da sallah Momy ta shigo hannunta d'auke da tea Mai milk, badan kartace bazata shaba ta tayarwa da momyn hankali ba, da tace ko ganinsa batasonyi.
Ta k'irk'iro murmishin da zaisa momy karta gane damuwar da take ciki.
Cikin farinciki momy tace "naji dadi dana ganki cikin farinciki Sha magani kisha tea ki kula da kanki bye sai da safe karki manta da adu'ar kwanciya bacci"
11:pm tana kwance tana game a waya taji ana nocking tayi kamar batajiba, ya Kuma nocking har wajen sau babu adadi, taki tashi ta buɗe tasan bazai wuce yayanta Arif ba, tana kuma rok'on ubangiji daya ku6utar da ita daga sharrinsa,
Cikin sanyin murya yace "ashe kin shirya a kashe momy"
Tayi masa banza kamar bada ita yakeyi ba.
Koda ya gaji da nocking ya koma d'akinsa tare da Shan alwashin saiya lalata masa rayuwa tunda ta lalata masa komai nasa tare da burin dayaci akan zumar da zai Sha a daren yau.
Maleek, shima yana zaune beyi bacci ba, da gyangyadi ya fara d'aukarsa sai yaji an rafko masa Kira ana tabyarsa inda sukaga dare haka sukaga rana, sosai mutanen cikin d'akin sata lol dan banace d'akin sirri ba, sun shiga rud'u.
Nigeria••
Hankalin Ummu yafi kwanciya a halin yanzu sakamakon lokacin da Falak take gida, saboda tana dawowa Nigeria kafin ta koma Germany ake kidnapping d'inta, yanzu kuwa sai dai suyi waya.
Munira da Hibba sun fara zuwa aiki sakamakon sun kammala karatunsu.
Hibba tana aiki a hospital d'in Malam aminu Kano, ita Kuma tafara aiki a inda dad ya bud'ewa Ummu, wato gurin gyaran jiki had'a su turaruka humra da sauransu.
Yau Sunday, Munira bataje ko Ina ba, ta bud'e system d'inta tahau WhatsApp, ganin Falak tana online yasata yin video call tace "wato kin mance damu tunda kika tafi ko Kira Babu"
Falak da take kan aiki tai saurin amsa maganar Hibba tare da cewa Sorry aunty Hibba, ta fita a gurin Hibba tanata magana Falak hankalinta baya gurin.
Hibba taje d'akin Ummu da gudu rai a 6ace tace "Ummu ni nake yiwa Falak magana ko reply taki yimin muskilancin ya dawo kaina kenan..?

Masu son group suyimin magana WhatsApp only mata zalla 08141799224
*FALAK🍒*


Mom Islam




E.O.W



Page 17-18


Ummu tayi murmishi kafin tace "haba Hibba kudinga fahimta mana kodai aiki ne yayi mata yawa"
Hibba tayi murmishi.
Germany
Sunday
Shigarsu da komai Falak ta sani, cikin mamaki Dad yace "wato sunzo kwashe komai kenan?"
Kafin ta bashi amsa sukaji ana kiran sallahar asbha, dad yace "tabbas yau kwanan zaune mukayi"
Cikin sauri ya mik'e ya koma d'akinsa itama ta mik'e hankalinta na gurin d'akin dad, Tasha alwashin bazata je duba kowa ba, yunwa ma ta ishesu.
Sallah kawai tayi ta fito sanye da hijab hannunta rik'e da alkur'ani, parlo ta dawo tayi karatun kafin ta mayar inda ta d'auko, cikin k'an-k'anin lokaci tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga mai mad'auri, bak'a, sosai rigar tayi mata kyau, tayi simple makeup tare da rolling mayafin a kanta, kamar kullum ta d'auki abokiyar aikinta wato system d'inta ta fito gurin dad da shima ya kintsa,
"Good morning Dad"
"Morning how are you my daughter"
"Am fine Dad"
Falak ta fad'a tana mik'ewa, "Ina zuwa ki Bari a kawo breakfast mana"
Dad ya fad'a yana kallonta,
"A'a dad zan karya acan akwai abinda nakeson yi acan"
Dad yace "gara kidinga hutawa saboda hutun k'walawa shike kawo tunani mai zurfin gaske"
"To kawai tace tayi waje, ta barshi a guri "
Yau ta rigashi zuwa, tun daga bakin get motarsu na tafiya takejin gabanta ya tsananta fad'uwa fiye da koysushe, ta ambaci "innalilahi wa inna ilaihir raji'un"
Ana parking ta sauka ta shige da sauri tare da hawa steps d'in, zuciyarta ta bata shawarar ta shiga ta duba wad'annan mutane, da sauri tace "never!! wlhi kozasu mutu"
Tana zaune wani tsoho ya shigo wai ta temaka masa, ta mik'e da sauri kafin tace "haba baba jikinka bai nuna kana cikin wahala ba amma ga wannan" ta mik'a masa kud'ad'e masu yawa, yana kar6a shocking ya kamata jikinta babu inda baya 6ari dan azaba, cikin tsananin mamaki sai ga tsohon nan ya cire fatar dake jikin fuskarshi ashe matashi ne.

Karku manta nace gajeren labari ne, dubada inda littafin nake jinsa a raina dakuma sak'on da nakeson isarwa, zai kai Book1,2,3,4 kun gane, akwai mutane da dama da zasuce banyi musu adalci ba, kuyi hakuri banyiwa kowa dole ba, a page 30 zan tsayar da wannan shafin zakuyi hakuri da hakanne idan har kun fahimci abinda nake nufi, mean yanzu littafin FALAK is Book1,2,3,4 duk meso sai yayi magana, zanyi normal group 300 zanyi Vip 500 zanyi special 1k nagode.
Gadai Falak a zaune Amma ko numfashi batayi, matashin saurayin ya cire bak'ar hular kansa kafin ya fara dube-dube, fari ne tass ba d'an Nigeria ba, cikin sa'a yaci karo da system d'in Falak, da sauri yaja kujera ya bud'eta yana dariya, abinda bai sani ba anan shine besan ko wacece Falak ba, mahaifinta ma baisan ko wacece ba balle shi da ba kowa ba.
Yayi, yayi ya Kuna amma abin ya gagara, duk da AC dake kad'awa Amma a banza sai sharce zufa yake, cikin yacin rai ya mik'e daga gurin da yake zaune ya fara y'an dube-dube kozai samu wani abu mai muhimmanci.
Ya watsar da komai na gurin cikin harda system d'in Falak, a tunaninsa komai ya lalace, damuwarsa anan shine idan ya komawa wanda ya aikosa da maganar bai samu abinda yake soba to wallahi sunansa gawa,
Cikin k'warin guwaiwa Falak ta mik'e idanunta sukayi kalar blue ta shak'o wuyansa ta bugashi a k'asa ta kuma d'agashi ta buga a k'asa kafin ta fara magana cikin wata iriyar murya, waye kai waye ya turoka me kazo nema?"
Da sauri matashin yace "ke nazo nema kuma nad'au alwashin bazan bar nanba har sai naga bayanki"
Falak tayi masa shak'a wacce takusa kaishi lahira kafin tace "kalma ta karshe rayuwarka ta k'arshe zamanka na k'arshe farincikinka na k'arshe a wannan duniyar waye ya aikoka?"
Da k'yar bakinsa na mugun zubar da jini yace "Maleek, Abdull-Maleek shine ya aikoni"
"Switzerland ko?"
Falar ta fad'a tana d'aga masa gira, bakinta duk jini,
"E...eh...eh shine"
Falak ta sakeshi tare da turashi cikin haushi da masifa tace "meyasa yake turoku? meyasa bazai zo ya sadaukar da rayuwarsa ba akan abinda yake nema, meyasa ku dabbobi da yake aikoku kuke biye masa kuci kud'i ku salwantar da rayuwarki akan dukiyar da bakuda tabbacin zaki sameta a wahalce kokuma ku mutu gurin nemanta?"
Jikinsa na karkarwa yace "na tuba kiyi min rai"
Falak ta nunashi da Zara zaran y'an yatsu ta kafin tace "last worning wlhi ko inuwarka na Kuma gani saina hallaka ka garama ka koma gaban iyayenka"
Ya mik'e ya fice da uban gudu, lokacin da dad yake isowa a mota shikuma saurayin ya fice da uban gudu,
Da sauri Dad ya fito a mota tun kafin akai ga gama parking, ya wuce office d'in Falak da gudunsa, yana shiga ya rik'e baki tare da k'arasawa gurinta, yasan yau an ta6o masa Falak, duk abinda ya ta6a lafiyar jikinta tabbas babban abu ne"
Dad ya kallleta kafin yace "Falak meke faruwa kin taho batare da kin sanar dani abinda ke faruwa ba"
Falak ta runtse ido kafin tace "dad dole zan koma Nigeria dad wannan rayuwa tacin Amana da salwantar da rai akan dukiyar wani ta isheni, Dad yanzu nakuss yi kisan kai"
Dad ya zaro ido kafin ya kakkali kayayyakin da aka zubo dasu yace "kai Allah kana gani"
A zuciye Falak tace "zata shiga wannan d'akin , Dad ya janyota takusa fad'uwa cikin fad'a yace "kefa kike yimin fad'a jiya kince abi komai a hankali yanzu Kuma kina neman wargatsa komai,
"Gayamin waye ya fita anan yanzu?"
Falak na kuka tace "Maleek ne ya aikoshi Dad bansan me yazo d'auka ba"


Switzerland
Washe gari, Beauty taji tsoron fitowa saboda Had'uwarta da Arif, koda momy ta lek'o d'akin ta sameta a kwance kamar marar lafiya, momy tace "beauty kinada damuwa amma kike k'in sanar dani ko?"
Ganin inuwar k'afar Arif yasa beauty cewa "ciwon mara da nayi jiya shine ya haifarmin da zazza6i momy amma yanzu alhmdulilh"
Momy na mik'ewa zata fice, Arif yabar gurin cikin sand'a
Washe gari ta kama Monday, yau momy zataje Egypt ita da Ummu Amal y'ar uwarta ana bikin k'aninsu (autansu) kasancewar aure ne ya kawosu Switzerland,
K'arfe 7:am momy ta shirya ta fito ta sami beauty dake kitchen tana had'a breakfast, momy tace "beauty ko iya tea ne yayi had'a min please kinga yanzu Ummu Shukura ta kira Wai ta fito"
Beauty ta had'a tea d'in ta kawo mata d'aki, momy na gama Sha ta mik'e, Maleek ya shigo cikin shirinsa na turawa wuyansa da wani abu kamar mayafi,
Ya kamo hannun Momy kafin yayi masa kiss yace "zanyi kewarki matata fatan dai bazaki kai 2weeks acan ba?"
Beauty ta fice cikin jin kunya, a zuciyarta tace "shidai baba ko kunyar Ina guri yabar yin abu bazai Dena ba".
Maleek ya wani rungumeta kamar zai mayar da ita ciki, a zuciyarsa da abinda yake kudurtawa bayan tafiyarta,
Momy tace "zanyi missing d'inka mijina"
Maleek ya had'e bakinsu guri d'aya tare da sanya hannunsa k'asanta yana wasa dashi, cikin sanyin murya tace "megida kanason kasa nayi late ko?"
"Yakamata ki bani farinciki kafin ki tafi"
Momy tayi mamakin wannan zallar soyayya da Maleek yake gwada mata, amman sai ta biye masa, Ummu Shukura kam tayi Miss call har uku amma momy bataji ba, Maleek yaji yak'i magana, ana hud'u ne momyn ta d'aga tace "kin zo inda zamu had'unne?"
Ummu Shukura tace "a'a wlhi na koma bak'i nayi"
Maleek ya kar6e wayar yana rage kayan jikinsa, itama din ya rabata da nata kayan yana wani sinsinar gefen kunnenta da ya jiyo k'amshin turare, a kullum mamakinsa shine, idan yazo xx da ita koda yaushe a matse take, bakamar sauran matan da dayazo sai yaji abu ya shige zuruf ba, ya dad'e a kanta yana sumbatu daga k'arshe ya farayi a hankali, itama kanta ta gaji, Saboda Maleek wani iri namiji ne, tun yana abu ta dad'i har abun yazo ya fice maka Sam a cikin ranka, dak'yar ya d'agata, cikin sauri ta sake wanka ta fito ta sameshi kwance a gurin ya baje kamar gona, Momy tace "please me gida ka gyara jikinka idan Beauty ta shigo fa?"
Maleek yace "ai tare da matata nake"
Momy tai saurin kamo hannunsa tana d'an yi masa wasan yaudara ya shige toilet.
Allah yasa sunyi sa6ani sai ga Beauty ta shigo tana cewa "momy Ummu Shukura ta kira wayarki wai bata shiga ba tace ki fito itama ta fito".
Momy tace "to insha Allah"
Abinda yaba beauty mamaki shine momy na busar da kai bayan haka tana shafa mai tana sauya kaya ta fice kai tsaye.
Beauty babu abinda bata sani ba sai dai wanda ba'ayshi ko anyi maganarsa ba, wato na dangane da mahaifinta, sosai take binciken duk wani abu. Da zaisa ta gano ko menene alak'arsa da abun.
Momy na gama kintsawa Maleek yayi mata transfer na kud'i masu yawa, kafin yace dole ta gaya masa kwana nawa zatayi?"
Momy tace "tow weeks"
Maleek ya rungumota saboda ba k'aramin dadi yaji ba kafin yace "nagode da farincikin da kika sanyani inayi miki fatan tafiya lafiya ki dawo lafiya"
Haka suka rabu cikin farinciki, ta shiga d'akin beauty tayi mata nasiha kafin tace "idan ta sauka zata kirata"
Momy tace "ban Sami wayar Arif ba, koda yake shi bai damu da kowa ba natafi"
Beauty tace "momy Allah ya tsare hanya"
Itama tad'au alwashin momy na tafiya zatabar gidan kodan halinda zata tsinci kanta a ciki ta gwammace tayi rayuwa a wani gurin ba agaban wad'annan azzalumain ba,
Zuwa yamma Maleek ya Kira beauty a waya yace mata, idan taga bai dawo ba zai kwana a wani guri akwai aikin da sukeyi karta damu, idan tanada matsalar kud'i ta duba loka"
Dama abinda takeson ji kenan, zuwa dare ta kammala abinci ta sawa Arif ta ajiye masa a d'akinsa, tana shirin fitowa ya tareta, kafin yace "yakamata ki bani abinda na nema idan kink'i kinsan meye zai biyo baya? Wlhi sai momy tayi hatsari ko a gurin dawowa, kinsan za'a fara tunanin mutuwa ko rayuwa ko?"
Beauty na mutuwar son momy, inda abinda zai ta6a momy bata k'aunarsa, da ana neman za6in mutum gurin mutuwa da tace a kasheta abar mata momynta.
Beauty ta marai raice fuska kamar ta mai shirin yin kuka tace "haba brother kasan illar yin hakan fa, ko wani ne ya tareni zai lalatamin mutuncina ai ka hanashi sai inda k'arfinka ya k'are, ya galla mata harara lokacin daya kwantar da ita akan kujera ya jefa wasu tablet guda uku a cikin lemu daya tsiyaya a cup ya mik'a mata cikin tsawa yace "Sha..!!"
A firgice ta kar6a tayi kamar tanasha ta ajiye, cikin masifa yace "kinsan dai ni ba k'aramin yaro bane ko? nasan bakisha ba wallahi sai kin shanye duka"
Ya d'auko k'atuwar wuk'a yana yi mata nuni da ita, da sauri ta kar6i cup din...

Idan baku manta ba, da nace muku gajeren labari ne, yanzu kam wasan ma ba'a fara ba, littafin FALAK iya kaiwa Book1,2,3,4 insha Allah, banyiwa kowa dole ba, nasan masoyan Falak zasu so jin labarin ba'ayi komai ba, dalilin da yasa nace muku labarin zeyi tsayi kenan, a page 30 zan tsaya Ina Mai baku hak'uri, bawai ina nufin wani abun bane,
normal group 300 posting d'aya a Rana
Zanyi Vip group 500 posting biyu zuwa uku a rana.
Zanyi special wato manyan mata masu so ta private 1k posting sau hud'u a Rana.
Ba lallai kullum y'an normal su samu ba, falyakun khairan... Kafad'i alkairi ko kayi shiru...

Dama gareku masu son adama dasu a doguwar tafiya mai d'auke da sabon salon cakwakiya zasu iya biyan kudinku tanan. 3175689751,Zainab Habib first bank.
Idan katin mtn ne zaku d'auki hoton katin ku turo ta wannan number 08141799224
Masu son shiga group d'ina suyimin magana WhatsApp only mata zalla 08141799224

Mom Islam

Masu son shiga group d'ina suyimin magana WhatsApp only mata zalla 08141799224

Mom Islam
*FALAK🍒*



Mom Islam


E.O.W


Page 19-20

Beauty ta kafa kai kenan wayar Arif ta fara ring, yai saurin d'agawa tare da cewa "my lovely dad am coming"
Taga ya fice da sauri.
Jikinta na karkarwa tabar d'akin har tana bigewa da bango, tana zuwa d'akinta ta fad'a gado tare da dafe k'irji ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, kuka takeyi sosai kamar wacce aka yiwa duka, a daren dai ko abinci bataci ba haka ta kwanta zuciyarta a cunkushe da tarin bak'inciki.
Maleek•
Cikin hanzari ya iso bedroom d'in Maleek, Arif yace "my dad gani"
Abin mamaki nace ashe yana nan yace kar tayi abinci dashi?.
Maleek yace "ya maganar kayannan suna shiga kuwa?"
Arif yace "eh dad ai kullum cinikinsu akeyi ina tunanin saima anyi sabon d'iba"
Maleek yayi murmishi kafin yace "ubangiji ya barni dakai my lovely son"
Arif yace "Amin ya rabbi"
Daga nan Arif ya fice, a cikin daren ya wuce inda dad d'in yake siyarda cocaine (hodar ibilis) kasancewar babu nisa a tsakaninsu, yana gudun kar dad d'in yazo ya ritsashi bai gama lissafi ba, a tak'aice dai anan ya kwana.
Germany
Yau kwanan bak'insu Falak wato 6arayi kwanansu uku a cikin d'akin, amma suna nan jiya I yau, dan babu abinda ya sauya zani, kullum cikin duba Taswira suke had'e da bincike tare da wani boka da already dama anzo dashi.
Yau sun shiga k'ofa ta biyu, matsatsinta ya isu, basuda halin komawa baya, cikin tsananin tashin hankali da tsoro ga zafi da ko shan iska gurin bayayi, suka fara jimanta halin da zasu shiga sunzo da gorar ruwa harda kayan itatuwa duk sun taho dashi tun kafin akai sati sun cinye fin rabi, ruwa kuwa yakusa k'arewa, cikin nawuyacin hali Manaf yace "gaskiya bazan iya wannan aikin ba komawa zanyi har ga Allah akwai cutuwa a ciki, banga alamun zamuyi nasara ba"
Boka ya sheke da dariya kafin yace "ai a k'a idar wannan d'aki idan aka shigo dole sai an shiga ciki kafin a fito"
Manaf yace "munyi tafiya kamar wasu marasa galihu ko kwata bamuyi ba nidai na gaji"
Boka ya rungume Manaf dake wani irin tari, kafin yace "kayi hakuri inada yak'inin sai munje gurinnan nayi muku alk'awarin duk Wanda yaji jikinsa babu K'arfi yayimin magana zanyi masa magani"
Tashi d'aya Manaf yaji k'arfin jikinsa sukaci gaba da tafiya babu iyaka, anan k'ofa ta biyun da ko rabinta basuyi ba anan dare yayi musu, dole suka gwamutsu cikin matsatsi suka fara bacci, dan babu gurin kwanciya.
Falak•
Yauma kamar jiya sam bacci ya k'auracewa idonta ta kasa koda runtsawa, aikinsa takeyi ma bazai bari bacci yayi nasarar d'aukarta ba, a koda yaushe tana binciken inda zata k'arawa d'akin sirrin dad d'inta tsaro domin kareshi daga sharrin azzalumai, cikin hukuncin ubangiji take samun nasara da abubuwan da zasu dinga taimakarta.
Tunda suka dawo dad ya wuce part d'insa kasancewar yau ko gurinsa batazo ba, shiko har yayi bacci saboda rashin baccin da beyi ba jiya,
Iyakan Falak abin yaso ya zame mata jiki, saboda tana nunawa bacci halin ko ina kula, sai ta kusan raba dare a gaban system, a Nigeria nema take samu take hutawa, idan ta dawo gurin dad babu halin kwanciya bare hutu ko tayi charting da wani inba searching akan abubuwan da zai kawo musu ci gaba ba.
Cikin rashin tsammani tana shirin rufe system d'in taje ta kwanta taji kiran sallahr asbha, da sauri ta kalli agogo tana mamakin "oh kodayake ba'a mamaki da ikon Allah"
Taje tayo alwalah tayi nafila kafin ta kabbara sallah lokacin an shiga, tana idarwa ta d'auko alkur'ani mai girma kamar kullum da ta sabarwa kanta, bayan tayi karatun ta mayar dashi mazauninsa,
Ta koma gado tare da Jan blanket, hhh kunsan fa hausawa sunce ba'a cin bashin bacci, aikuwa yayi awon gaba da ita, har k'arfe 8:30 tayi ankawo mata breakfast sai akan dinning aka ajiye bata tashi ba, dad harya yi breakfast ya shirya ita yake jira, dan gudu gudu ya shirya sabda kartazo ta uzura masa, ya jita shiru har yanzu, kai tsaye ya taho part d'inta a hankali yake ambatar "my daughter" shiru bata amsa ba, ya taho a hankali ya murd'a handle d'in k'ofar, ya ganta ta rufa da bargo, ya janyo k'ofar a hankali ya dawo parlo, system d'inta daya gani jone a chaji ne yasashi cewa "k'ilama bata samu tayi bacci ba, Allah yayi miki albarka y'ata" a hankali yake maganar ya fice.
Parking space yaje, ya shiga mota aka wuce dashi gurin aiki,
Alhmdulilh yau kam beji fad'uwar gaba kamar koda yaushe da yake jiba idan yazo zai shiga company d'in, yayi aikinsa cikin yardar ubangiji sosai yayi komai cikin nutsuwa, har wasu kayayyakin da aka basa contract ya bayar an had'asu, yana zaune yana hutawa har k'arfe 1:pm na rana tayi, wata mota fara mai kyan gaske tayi parking, sai da akayi checking mutumin kafin ya shiga, bayan sun gaisa da dad yace ga list d'in kayan da yake so, k'ofofi ne na zinare sai table shima na zinare, mutumin Mai kirki ya ninkawa dad kud'i fiye da inda ya siya, tun daga lokacin sukayi musayar lambar waya, dad yayi masa godiya mutumin ya tafi, jikin dad na rawa ya rangad'o wa Falak Kira, yanzu ma ta fito daga wanka tana d'aure da towel, taje da sauri ta

Please Login or Register in order to submit comment