Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwana da y'arsa shi zan kaiwa hari"
Maleek yayi tsaki mtsw, maganar hakan bata taso ba bakada hankali, wannan yarinyar tasan komai itace sirrinsa akwai abinda ita ta sani shi bai sani ba, yanzu kana zaune zata hango abinda ke cikin lungu da sak'o na gurinnan da muke, shiyas nakeso ta zamo babyna in biyata mu dinga aiki tare tunda naga yarinyar wayayyace".
Suna cikin magana, wayar Maleek tayi ring, ya d'aga da sauri yana cewa "wow Kaya sun iso lafiya?, a wuce dasu kawai inanan shigowa zuwa anjima"
Ya katse kiran, Manaf yace "wato Kaya na tafiya indaya kamata, zomuje kawai saboda akwai abubuwan da zamu gudanar.
Kai tsaye suka shiga mota, Manaf na driving Maleek na bashi labarin inda zasu cigaba da gudanar da aiyukan safarar kayan nasu, suna isowa Maleek ya fara fitowa a hankali cikin takunsa na k'asaita, ya shiga d'akin da aka sauke kayan, Manaf na yabi bayansa, suna cikin tafiya sukaji kamar motsin mutum, har sun tsaya suna dubawa ganin basuga kowaba yasa sukaci gaba da tafiya.
Mutanensa su biyar suka samu a ciki, kowanne da aikin da yakeyi, masu d'urawa a wasu k'ananun leda nayi masu zubawa a buhu sunayi masu zubawa a y'ar roba suma sunayi, guri ya cika da aiki Maleek yace "gaskiya Alhmdulilh ansami riba a wannan karon ninkakkiya naji dadi, zamu sake gina wani gurin a wata k'asar ba wannan ba, amma maganar nan ta zamo sirri tsakanina daku"
Mutanen gurin sukace angama me gida, a hannunsa yasa kafin ya sheka yace "uhnnn ahhh, sabon d'auka sabon farashi sabon sari sabon aiki, hhhh" dukansu suka kwashe da dariya.
Falak na kwance tana kwatanto Switzerland da abubuwan dake faruwa, abin tana ganinsa kamar a mafarki ne Wanda takejin hakan har cikin ranta, me dangantakarta da lek'en sirrin wasu bayan ga babban aiki a company d'in dad d'inta?.

Duk meson karantashi ta group d'ina ba WhatsApp yayimin magana mata zallah please Banda Kira 08141799224
#Team Falak
#Team Maleek
#Team ohooo waye naku wai yan Facebook bana kun sani Happy banyi tunanin zakuzo littafin sosai ba, yan WhatsApp kuwa babu me godiya daga wannan page din inhar ba shar'i ko comments bye bye zanje Facebook incigaba.

Mom Islam
*FALAK🍒*

Zainab Habib/ Mom Islam


E.O.W

Page 7-8

Wayarta ta d'aga ta danna number Hamma Aliyu, kamar dama jiran Kiran nata yakeyi ya d'aga da sauri kafin yace "k'anwata"
Falak ta turo baki kafin tace "Hamma Aliyu har zan tafi bazakazo ba?"
Ya mayar mata da maganar kamar inda tayi masa yace "uhm Ina hanya ganinan"
Ta daka tsalle tana murna ta ajiye wayar, da gudu ta tafi d'akin Ummu, ta sameta a kwance tana bacci, cikin d'aga murya tace "Ummu Hamma na yana hanya"
"Kai Falak na gaji ne yasa na kwanta yanzu kuma ba lallai baccinnan ya d'aukeni ba"
Ta rungume Ummu tace "da izinin ubangiji zai d'aukeni harda mafarkin dad nayi miki wak'a kekuma kina rawa"
Ummu ta lumshe ido batace mata komai ba, d'akinsu Saudart da Munira da Hibba ta shiga wanada d'akinsu ya kasance a had'e nata kuma ita kad'ai, tana shiga ta samesu ko wacce hannunta rik'e da waya da alamu chart sukeyi, tace "hello" suka d'ago suka kalleta fuskokinsu d'auke da murmishi cikin had'in baki su biyu sukace auta lafiya kodai dad ya siya miki motar da kikeso ne?"
Falak ta zauna kafin tace "Hamma ne yake hanyar zuwa shine nazo gaya muku aunty Saudart naga kamar bakya farinciki"
Hibba tace "kyaleta itafa tace tana sonsa dan an matso da biki shine zaki wani dinga cin magani"
Saudart ta bige bakin Hibba suka fashe da dariya,
Ajiye wayar Saudart tayi ta sauko a hankali ta wuce kitchen,  abinda ta tabbatar yanaso tayi masa wato dankalin turawa da mai da yaji, idan zezo ta shiga kitchen dafa masa su Hibba suyita mata dariya, yauma kamar kullum kasancewar itace babbarsu suka shigo suka fara sana'ar tasu, bata kulasu ba taci gaba da aikinta, tana shirin saukewa wayarta tayi ring, a hankali ta d'aga kafin tace "my sweetheart kacemin kana hanya na jika shiru"
Hibba da Munira suka toshe baki suna dariya wai Saudart kamar ta shiga makarantar Love, tana ajiye waya ta juyo ta kallesu ta galla musu harar lokacin da ta juyo abincin a foodflaks, takai d'akin da suke saukar bak'i.
Falak ta k'walawa kira ta amsa kafin tace "inzo ne?"
Saudart tace "Baby ya iso yana kiranki"
Ta rufe abokiyar aikinta wato laptop ta fice waje, tsaye ta sameshi ya zura hannayensa cikin aljihu yana ganinta yace "Wai naji muryar antynki wani iri shin meke faruwa?"
Falak tace "Babu komai" yanzu bana nan za'ayi bikinku?"
Ta share siraran hawayen daya zubo mata,
Hamma Aliyu yace "ai kamar kina nan ne tunda zakiga komai kamar kina gurin.
Ta kawar da maganar da cewa "dad yace saura kwana biyar yau saura kwana hud'u in koma.
Ya rik'e hannunta suka shiga ciki.
Kai tsaye ta wuce d'akinta ta koma bakin aiki, shikuma ya fara rangad'a sallama kamar inda ya saba dayazo yake cika musu kunne,
Saudart ta taho da sauri tana sanye da riga da wando, sun kamata sosai kanta tasa hula wacce bata k'arasa rufe mata gashin kanta ba,
Ta kamo hannun Hamma Aliyu suka shiga d'akin da abincin yake tace "uhm mutane basa son surutu kaikam ka fara ko?"
'Dabi'unsa da bata cika soba shine, dayazo sai dai ta zauna akan cinyarsa, hakan akayi dayaci dankalin ya dinga santi yana cewa "shifa a k'ara dafa masa, Saudart ta turo baki kafin tace "am dama inason sanar dakai jiya da mukaje kasuwa Kaya sun tashi" ya k'yalk'yale da dariya kafin yace "to Banda abinki ATM d'ina fa yana gurinki nace harda auta a siyawa duk abinda takeso"
Falak
Cikin tashin hankali ta tura hannayenta a cikin gashin kanta, a tsorace tace "ina dad ya shiga wayo Allah na!!"
Ummu ta shigo da sauri tana cewa "auta kukan me kikeyi?"
Falak tace "Ummu zokiga zokiga inda wannan mugun ya shigo shagon dad yake kwasar kaya wai duk cc tv babu wanda ya gansa abin ma dai abin mamaki"
Ummu ta zaro ido cike da damuwa kafin tace "to ki kirashi a waya mana"
"Bata shiga"
Falak ta fad'a tana kuka.
Germany••
Dad zaune a masallaci, yasan akwai masu kula masa da kayayyakinsa dan haka koda yaushe idan ya shigo masallaci baya fitowa da wuri, sai yayi adu'oi sosai wani sa'in ma yayi bacci, yana zaune yaji jikinsa bai bashi ba, kamar akwai abinda ke shirin faruwa, ya fito tare da sanya takalmi ya dawo shago, ga mamakinta yaga ma'aikatan gurin sunata kaiwa da komowa ana gudanar da kasuwanci dai-dai, ya zauna tare da hawa whtsapp, abinda yaga anyi screen shot an turo masa ne yasa hankalinsa tashi yace "Falak idan baki dawo ba zan iya samun matsala"
"Nasan nayi asarori masu yawa amma zanso ki zauna ayi bikin Saudart ana kammalawa sai ki dawo"
Dad ya ajiye mata a WhatsApp ya sauka.
Hankalinta yayi nisa sosai saboda wasu abubuwa da bincikenta ya bata tabbas akwai masu harin shigowa dad d'inta wannan d'akin na sirri d'akin da ya kasance shine gatan mahaifinta duk Wanda suke a waje ko an had'asu bazasu kai kwatan wannan d'in ba,
Kamar ance ta duba WhatsApp, tana dubawa taga sak'on dad, ta buga tsalle ta taje ta tashi Ummu tana gaya mata, itama Ummu tayi farinciki sosai dan koba komai zata shiga cikin y'an uwanta ayi biki da ita,
Gadan gadan aka fara shirye-shiryen biki komai akace anaso sai dai dad ya turo da kudi,
Sosai gidan Saudart yayi kyau gunin sha'awa gashi madai-daci sai uban kud'i da aka kashe masa,
Biki ya rage saura kwana uku, kaf gidan suka tafi wankin kai da lalle, Banda Ummu dake gida tana had'a wa Saudart turaruka, sbda sana'ar Ummu kenan siyarda turaruka da kayan gyaran jiki.
Duk cikinsu babu wacce ta kama kafar Falak a kyau, zanen bak'in lallen nan kamar dan ita aka yishi, ga gyaran gashi da akayi mata suka dawo gida a gajiye,
Kowacce tayi d'akinta, sallah kawai Falak tayi ta kwanta sakamakon gajiya da tayi sam ta rasa nutsuwarta haka kawai take jinta babu dad'i, Ummu ta shigo hannunta d'auke da yam balls ta ajiye akan table tace "auta naga kinaso"
Falak ta sauko a hankali ta rik'e hannun Ummu tace "Ummu kiyimin adu'a inajina cikin wani yanayi na rashin jin dad'i"
"Inasha Allah Babu komai auta ki kwantar da hankalinki"
Falak tace "to Allah ya kare mana dad"
Ummu ta amsa da "amin"
Switzerland
Kwashewa sukayi da dariya Maleek yace "mutumin nan da kuke ganinsa d'an Nigeria ne amma brain d'insa tafi tamu kawo light duk inda kuke tunaninsa ya wuce nan, a wannan karon mun samo zinarai na lak500 zuwa gaba wannan d'akin da yake tak'ama dashi zamu d'auko duka".
Manaf dake gefensa yace "samun yaswirar gurin shine abu na farko daya kamata muyi inhar muka samu shine komai zezo da sauk'i.
Wayar Maleek tayi ring, ya d'aga cikin kausasashiyar muryarsa yace "sau nawa zan gaya miki idan ina cikin wannan yanayin karki sake ki kirani"
Ya ajiye wayar, Manaf ya mik'e cikin kulawa yace "kabarmin komai a hannuna ai acikin mutanen da suke jikinsa suke masa aiki a company akwai abokaina zanyi amfani da hakan ko nawa sukace sunaso zamu biya inhar d'akinnan zai zamo mallakinmu"
Maleek yasa dariya yace "k'anina shiyasa nake sonka bye"
Manaf na tafiya Maleek yayi wata muguwar dariya kafin yace "kaima kana gama min aiki kasheka zanyi bakada amfani Sam a cikin wannan rayuwar tawa"
Ya mik'e tare da gyara zaman rawanin daya d'aura a kansa, kai tsaye ya wuce gida.
Yana shiga ya samu yarinyarsa ta dawo gida kasancewar ta kammala karatu dawowarta suke jira, tana ganinsa ta taho da gudu ta rungumeshi, kafin tace "Papa Ina Arif?" Maleek ya basar da zancen ta hanyar cewa "kin huta kuwa? Ina mamanki tazo ta kawo mana shayi"
Cikin shagwa6a ta rungume Maleek ta Kuma mai-maita "papa Ina Arif"
"Beauty kinason ranki ya 6aci ko? to Arif yana Nigeria gurin abokinsa shikenan".
Gabanta ya fad'i tasan har yanzu papa d'inta bazai k'yale dad d'in aminiyarta Falak ba, shin Anya tunda ta dawo makaranta ta gama bazata taya Falak farautar mahaifinta ba kuwa?"
Maleek yace "kinyi shiru muje mana"
Jiki a sanyaye beauty ta wuce ta barshi a guri , ta fad'a d'akinta tare da danna number yayanta Arif, sai da wayar tayi ringing sau uku sannan ya d'aga murya irinta mai maye yace "waye ban gane dake ba?"
"Yah Arif badai ka koma halin dana hanaka ba, da mukayi alk'awari akan cewa zaka fasa?"
"Arif ya Katse Kiran tare dajan tsaki mtsw"
Beauty ta fice da gudu ta hau steps zuwa gurin mom d'inta, tana zuwa ta ganta kwance akan kafar Maleek tana kuka tace "mom har yanzu Yah Arif bai dena shaye-shaye ba"
Maleek ya daka mata tsawa kafin yace "6acemin da gani ke wace irin yarinya ce kamar aljana anya ke jinina ce kuwa?"
Mom d'in beauty ta girgiza kai kafin tace "haba Papa me yasa kake irin wannan furucin bayan kasan beauty gaskiya take fad'a"
Maleek ya turo mom a hassale yana cewa "wannan yarinyar da kike gani batada hankali shiyasa bana sake mata fuska inhar nace zan sake mata zata iya fad'ar koma menene.
Beauty na komawa d'akinta taje gurin window ta bud'e labule tana ganin inda sararin samaniya ya had'a ga wani gagarumin hadari da yake had'uwa, da sauri ta zame k'asa ta furta "subanallah"
Daga nan ta jingina da bango tana hararo irin binciken da zatayiwa Arif shin kodai papa ya sashi wani aiki ne?, dan karsu gano yasa take 6oye musu"
Allah shine ya barwa kansa sani.
Nigeria
Kano
Yau Fulani day na Saudart, a inda Falak tayi shigar Fulani tayi kyau kai kace itace amaryar,
Gidan Ummu an cika sosai y'an uwa da abokan arziki kamar ranar ne biki,
Wata mata tazo tana washe baki tace" maman Saudart ashe kunada y'a baturiya ban sani ba? ina yiwa yarona kamu"
Murmishi kawai Ummu tayi kafin tace "Allah ya nuna mana"
Yawancin mutane basu san Falak ba, kasancewar ba a Nigeria aka haifeta ba, amman y'an uwan momy sun santa.
Washe gari ta kasance d'aurin aure, sunyi kyau yauma dukkansu hud'un kayan jikinsu iri d'aya, sunyi shigar weeding gwn ko Ina suka gifta photo ake yi musu, k'arfe hud'u 4:pm motocin d'aukar amarya suka iso, Saudart tayi kukan rabuwa da Ummu kamar me, itama Ummun tayi kuka sosai saboda d'a da uwa sai Allah, yayar Ummu ta kamo hannun Saudart zata shigar da ita mota, Saudart tace "Ina Falak?"
"Innalilahi wa inna ilaihir raji'un" Ummu ta ambata lokacin da taji ance ba'aga Falak ba, hankalin kowa ya tashi Munira ta fasa ihu cikin tashin hankali tace "shikenan ankuma d'auke y'ar uwarmu Falak me kikayi musu, keda ba fita kikeyi ba?"
"Ummu ta fad'i k'asa sumammiya"
Mutane sukayo kanta, hankalin su Saudart Munira da Hibba duk ya tashi, Saudart ta koma cikin gida da gudu tace "indai ba'aga Falak ba bazata jeba"
Babu wanda yayi yunk'urin takura mata, sai komawa da motoci sukayi jiki a sanyaye..
Ƙarfe 8:pm na dare zan dinga posting insha Allah, ƴan Facebook kuma 9:am na safe nagode masu son shiga group d'ina na WhatsApp suyimin magana ta wannan number 08141799224 mata zallah
Share fisabililah

Mom Islam
*FALAK🍒*



Mom Islam

E.O.W

Page 9-10
Cikin tashin hankali sukayo kan Ummu wacce babu numfashi a tare da ita, aka yayyafa mata ruwa ta bud'e ido a hankali, bayan tace "Alhmdulilh tace Falak"
Wannan ya kalli wannan wancan ya kalli wancan, ana cikin haka wayar Ummu dake hannun yayarta tayi ring, aka mik'awa Ummu,
Cikin sanyin murya Ummu tace "Aslamu alaikum"
Daga can cikin wayar akace "yarinyarki tana hannunmu indan kuna sonta zaku iya biyan kud'in da zamu gaya muku"
"Ummu ta zaro ido cikin tashin hankali, ta kashe ta gwada number dad, cikin sa'a ya d'aga, tare da cewa Hajiya ya akayi? tun dazu nakeson kiranki aiyuka ne sukayimin yawa"
Cikin sanyin murya tace "anyi kidnapping Falak wai meyasa haka ne? nidai ka shirya lokacin dawowa dan nagaji da wannan tarzomar"
Gaban Dad ya fad'i, amma ya wayance da cewa "zata dawo insha Allah karki damu"
Cikin masifa Ummu tace "ban gane Karin damu ba haba"
Dad ya kashe wayar hankali a tashe yace "to suwaye?"
Anan 6angaren Ummu yan uwanta dake kusa da ita wasu na cewa, wlhi karta yarda k'ila ma akwai sa hannunsa a ciki shiyasa baya damuwa, wasu Kuma suce gara zaman Falak a Germany akan zamanta a Nigeria"
Ummu dai banda kuka babu abinda takeyi.

Falak, zaune take akan kujera abindai sai ya bawa mai karatu mamaki, saboda k'afa ta d'ora d'aya kan d'aya kafin ta zuk'i 5aliv ta kalli saurayin dake zaune kujerar dake kallon tata tace "to hankalinka ya kwanta ka tayarwa da family d'inmu hankali, shin kana ganin zakaga haske a rayuwarka? kidnapping d'ina da kayi bazai janyo maka arziki ba sai dai tsiya"
Saurayin ya gyara zaman bak'in glass din idonsa kafin yace "kaf garin Kano babu wanda besan mahaifinki ba, dan haka inba ta wannan hanyar aka biyo masa ba tabbas baza'a zauna lafiya ba" Falak tayi tafi kafin tace "zefi maka ka nemi halak d'inga arziki baya zuwa ma bawa yana kwance yana bacci, karkayi tunanin zaka samu kud'i, ka shiga tarkon Falak, don't worry akwai muhimman abubuwa just mance kawai, bayanni mutane nawa kayi kidnapping?" cikin gadara saurayin yace "mutane biyar hardake shida, duk Wanda muka d'auka muna samun kud'i dan haka ke sai mun ninka abinda muke samu a kanki"
Falak tayi murmishi Wanda ya Kuma baiyyanar da sihirtaccen kyawunta kafin tace "okay muje zuwa"
A hankali saurayin ya taso, ya sanya hannunsa ya ta6o boobs d'inta, aahh ashh laushi"
Abinda ya ambata kenan, Falak ta furzar da iska lokacin da take mik'a kamar tana yi masa nuni da ilahirin jikinta, cikin sauri yakai mata runguma, jin tudun boob d'in nata ya sashi rikicewa kafin yace "ashe ke y'ar hannu ce, okay yanzu wasan zai fara please ki bani had'in kai in jiyar dake dad'in da dukkan guys din da kike mu'a mala basu ta6a baki ba"
Had'a idon da zasuyi idanunta suka sauya lau I zuwa kalar Blu, a tsorace yace "harda yimin kwalliya ne?"
Ta mik'e k'irjinta a bank'are ta fice cikin salo na d'aukar hankali ta matso gabansa, kafin ta zuba masa manyan idanuwanta, tace "ni ba irin macen da kake zato bace, ka kiyaye shiga gonar daba taka ba" tana gama fad'ar haka tayi hanyar waje zata fita, ya fincikota ta fad'a jikinsa, ya fara 6alle mata botir din rigarta, da sauri yakai bakinsa k'irjinta tare da fad'in wow, so beautiful" Falak ta tofa masa miyau kafin ta ham6aresa da kafarta, yana shirin kamota ta mak'alar masa da k'afa d'aya, ta fice, tare da yiwa k'ofar key kasancewar taga key a jikin k'ofar, wayar tafi da gidanka data gani ne yasa taje tasa number dad cikin sa'a ta shiga, Falak tace "dad nice" da sauri yace "my Falak ashe abinda ya faru dake kenan"
"Dad akwai buk'atar jam'an tsaro dad please ad'au mataki"
Gida mai lamta takwas anguwar... sosai hankalin saurayin ya tashi, ya fara dukan k'ofa yana cewa dama ashe ke ma'aikaciyar tsaro ce? Amma kin cuceni"
Daga main parlo Falak tace "ka cuci kanka dai, karkayi tunanin wannan kidnapping d'in shine na farko a gurina, Wanda suka fika ma sunyi, naga kai a gida kakeyi.., cikin hikima da siyasa jami'an tsaro masu farin kaya suka fara ragargaza k'ofofin da suka gani a rufe, kowacce k'ofa suka bige sai y'an mata da manyan mata sun fito, ashe idan sukayi kidnapping mutane suna amfani dasu ne, Falak ce tafi k'arfinsu. Falak ta gyara zaman I.D d'inta da koda yaushe yake mak'ale a wuyanta cikin riga.
Ga mamakinta naga sunata gaisawa da jami'an sirrin sukayi mata congrats kafin suka wuce da mutane 13 hardashi 14 aka shigar dasu mota ita Kuma aka wuce da ita gida.
DSS
Ma'aikatan tsaron jiha da akafi sani da SSS, itace k'ungiyar da aka bawa aikin lek'en asirin Nigeria, ma'aikatar tsaron jiha tana aiki a k'ark'ashin shuwagabanci kai tsaye kuma tana k'ark'ashin ikon mai bada shawara, kan harkokin tsaro.
Dad yana d'aya daga cikinsu, Falak ta kasance itace mabiyarsa domin shi ta karanta, sosai hartafi mahaifinta k'warewa akan harkar, Ummu bata san Falak na aikin ba, kasancewar tanada k'arancin shekaru.
Saudart Hibba da Munira da Ummu dukkansu suna zaune sai ragowar yan uwan Ummu da dad da sukazo biki suna zazzaune, sukaga Falak kamar an jefota, Ummu na ganinta ta fashe da kuka, kafin tace "Falak harkin saba da rayuwar wahala, sauran y'an uwanta suka rungumeta Saudart ta share hawayen daya kwaranyo mata kafin tace "sis karki sake fita dan Allah, tunda kyawun da Allah yayi miki shike cutar dake please ki daure kome kikeso kiyi waya a kawo miki".
Saudart ta fad'a tana rungume da Falak, Falak tayi murmishi kafin tace "aunty Saudart insha Allah kamar inda nake zuwa nake dawowa babu wanda zeyi nasara akaina insha Allah"
Dukkansu suka amsa da Allah yasa.
Washe gari Hamma Aliyu ya rangad'o kirs a wayar Falak, ta d'aga tana dariya, yace "y'ar rainin wayo kin dawo kenan? nikam bazaki dena fita ba bare a Dena d'auke mana ke?"
Falak tace "Hamma Aliyu zoka d'auki matarka na dawo"
Lamarin Falak na basu mamaki sbda ko nuna damuwa batayi kamar ma cikin farinciki take dawowa.
Ranar Ummu sai bacci 6arawo dan sai juyi takeyi, tana tunanin yarinyarta kenan bazata ta6a yin rayuwa irin ta mutane ba, shin hakan rayuwar Falak zata dinga tafiya a halin matsatsi?"
Ta share hawayen dake bin fuskarta kafin ta janyo wayarta kasancewar message data gani daga dad, "kihau whatsapp"
Da sauri ta kunna data sakonni suka fara shigowa, taci karo da sakon dad tana budewa taga yace "naso ki biyo Falak keda su Hibba ku taho gurina inada buk'atarki a kusa dani, tunaninki na neman hargitsamin lissafi"
Ummu ta gyara kwanciyarta kafin ta sauya kayan zuwa doguwar riga abaya, ta ajiye wayar tafara video tana cewa "na fika missing wlhi koda yaushe inajin kamar mu kasance amma babu hali kayi nisa, yakamata dai Falak d'in tazo, idan taje gurinka sai ka dawo kai" ta tura masa.
Washe gari.
Tun safe motar d'aukar amarya ta k'araso dama kwanan shekaranjiya da k'yar Hamma Aliyu yayishi cikin tunanin Saudart, dama ya-ya bare an d'aura.
Falak naji tana gani Ummu ta hanata zuwa ko'ina sai su Hibba da Munira ne sukaje, Falak tayi kuka sosai dole ta hak'ura bacci ya d'auketa tana kwance.
A jere motocin suke tafiya, sannu a hankali suka iso anguwar da gidan amaryar yake, Zoo road,  cikin nutsuwa ds jerawa motocin suka dinga shiga cikin had'ad'd'en gidan, motar farko tasu Saudar tayi parking kafin ta iyaye sai ta k'awaye sai ta y'an anguwa sai abokai, kaf d'insu sai da suka yaba da kyan gidan da tsare tsaren dake ciki,
Komai yaji a parlon kowa na sanya albarka cikin farinciki, k'arfe 4:pm kowa yabar gidan Saudar, banda k'awaye, Hibba da Munira Ummu tayi waya akan su koma gida dole suka koma,
Saudart Tasha kuka harda majina, Allah sarki rabuwa da y'an uwa, kafin y'an uwan Ummu su tafi sai da suka sakata ta sake yin wanka ta gyara jikinta sannan suka tafi, ta kasa saka komai a bakinta sam ko dama can ba ma'abociyar cin abincin bane, k'arfe 8:pm abokan Hamma Aliyu dashi kansa Hamma Aliyun suka shigo, sai da suka siyi bakin amarya akayi adu'oi sannan suka tafi, Hamma Aliyu ya dawo tare da gyara mazaunin ledar kajin da yasan ba lallai wacce ya siyo dominta taci ba, kasancewar yasanta batun yauba nama bai dameta ba, ya cire agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa, kafin ya cire hularsa ya ajiye asaman dressing mirror ya juyo ya kalleta tana tsakiyar gado kanta rufe da kyakkyawan mayafi, farinciki da nishad'in dake malale a cikin zuciyarsa abin ba'a magana, ya janye mayafin s hankali tare da sanya lallausan hannunsa ya tallafo ha6arta yace "Babyna"
"Uhm" kawai tace tare da juyar da kanta, cak ya d'agata ya d'ora akan cinyarsa kafin yace "haba babyn Hamma meyasa yau kuma bazakiyi min magana ba?"
Saudart ta d'ago fuskarta dake tsare da makeup tace "nagaji sosai"
A hankali ya d'an kwantar da ita kai kace baby, ya fara mammatsa mata ko Ina a hankali, tun tanajin dad'i har bacci ya d'auketa, ba hakan yasoba, ya dinga shafo fuskarta kamar wanda ya sami TV kafin ya d'aga doguwar rigarta sama ya tura hannunsa cikin rigar ya cafko nipples d'inta da hannuwansa biyu ya fara murzasu a hankali cikin hikima idanunsa a lumshe kamar Wanda ya sami katifa lolz, a hankali ya gangaro shafaffiyar mararta kamar batacin abinci ya dinga shafawa, yana aiyans anan baby's d'ins zasu zauna" juyin da tayi ne ya bashi damar zura hannayensa cikin pants d'inta yana shafa k'asanta cikin hikima, baiwar Allah bacci yayi nauyi batasan me akeyi ba, rawar da jikinsa ya shigayi ne tashi d'aya ya mik'e jin harya jik'e, cikin yanayin buk'atuwa yayi bedroom, sai daya shiga ma ya cire kayan ya wurgosu kan kujera kafin yayi wanka yana wankan yana tuno inda zasu raya daren amarcinsu cikin farinciki da nishad'i.
Yana fitowa d'aure da towel a k'ugunsa ya matso yana k'arewa siririyar Fuskarta kallo, kafin ya d'aga hannu sama yace "Allah na gode maka daka bani farincikina macen da nafi so a duniya fiye da kowacce y'a mace, Allah na gode maka daka za6amin kyakkyawar mace Mai kyakkyawan hali, y'ar uwata kuma k'anwata, Allah in zaka bamu zuri'a ka bamu masu tausayinmu wanda zasu taso a masu d'aukaka musulunci" ya shafa adu'ar tare da diban kayan ya fice, sai gashi ya dawo dagashi sai boxes, ya haye gado tare rungumeta sosai kamar zai shige jikinta, yaja musu blanket, numfashinsa na shigar nata hakama nata yana shiga numfashinta, sosai yake lumshe ido har bacci 6arawo shima ya d'aukeshi, bayan yayi musu adu'a

Ayimin hak'uri lokaci ya kure, comments dinku ne zausa wani lokacin inyi muku posting sau biyu a Rana, ga masu son shiga group d'ina suyimin magana 08141799224 WhatsApp only mata zalla please.
WhatsApp posting 8:pm
Facebook posting 10:am
Mom Islam
*FALAK🍒*


Mom Islam


E.O.W


Page 11-12
Sanyin asbha ne ya fara kad'awa a hankali, Hamma Aliyu yayi juyi tare da sake rungumo Saudart da take shirin tashi,
Ta bud'e idanta a hankali kafin tace "Hamma naji kamar ana kiran sallahr ne, ya d'ago kansa tare da mik'ewa zaune yace "eh amma bana shiga ba"
Ya janyota jikinsa yana shafa k'ananun kitson da akayi mata tare da cewa "jiya shine kikayi barci da wuri ko?"
Tasa hannunta ta rufe masa baki tana dariya, harya sauko daga kan bed d'in ya dawo a hankali ya shafi gefen fuskarta tare da kwantar da kansa akan boobs d'inta ya wuce bedroom, kasancewar akwai ishashen lokaci sai da yayi wanka kafin ya d'auro alwalah, itama tayi alwalar sukayi nafila sannan ya wuce masallaci, ana kiran sallahar asbha ta mik'e tabi masallacin, ana idarwa

Please Login or Register in order to submit comment