Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata stone work, shima Hamma Aliyu kalarta yasa, sunyi kyau sosai, Saudart tasa mayafi mai pink haka ma takalmi da jaka duk kala d'aya, yayinda ta wadata wuyanta da sark'a mai tsada ta zinare, duk acikin kayan da dad ya kawo musu tsaraba ne wannan karon,
Hamma Aliyu yace "gaskiya wannan kwaliya muje in 6ata ta dan wlhi za'a cuceni a kallemin ke"
Saudart ta ruga waje da gudu tana dariya, shima fitowar yayi suka nufi parking space, suka shiga d'aya daga cikin motoci ukun daje jere a gurin,
Suna tafe big boy na cewa "Dady momy tana kallonka harda harara"
Hamma Aliyu yace "waya gaya maka harar takeyi?"
Big boy yace "naga idonta na rawa"
Suka shek'e da dariya,
Saudart tace "wai nikam ka sanarwa da Shuraim zuwanmu ko sai dai ya ganmu a hall?"
Hamma Aliyu yace "tuni ya sani gurin zamanki dabanne"
Suna cikin tafiya tace "oh ansa bikin autar Ummu fa saura kwana goma"
Hamma Aliyu yace "oh ikon Allah kamar ba kwanaki naji ance saura wata biyu ba"
Saudart tace "ai an dawo dashi wata d'aya shiyasa yayi kusa, amman zata dawo Nigeria anan za'ayi komai"
Hamma Aliyu yace "nifa lamarin autar Ummu yana bani mamaki, tace bata soyayya dan Allah ya akayi suka had'u da wannan har ake maganar aure?"
Saudart tayi dariya kafin tace "laah wai dama kai yarda kayi? ni nasan dole wannan ranar zatazo indai munada rai da lafiya"
Hamma Aliyu yace "to abin tunani ma ya Dad zeyi da maganar taimaka masa da takeyi?"
"Toh Allah ne masani, ni banmayi tunanin hakan ba wlhi"
Saudart ta fad'a tana cewa "munzo fa"

Dole yayi parking a bakin get tare da mik'a pass sannan suka shige,
Suna shiga yayi parking bai Bari ta tafi ita kad'ai ba ya hanata Wai duk inda zataje tare zasu tafi, Babu inda ta iya dole hakan tayi suka shiga rik'e da hannun juna,
Abin mamaki kallo ya dawo kansu kowa sai kallonsu yakeyi, badan yaron dake hannun Hamma Aliyu sunyi matuk'ar kama ba, da cewa za'ayi Saudart budurwa ce, saboda tanada kyan diri gata ba Mai jiki ba kamar dai Falak, sa6anin su Munira da sukeda k'iba.

Shuraim na daga zaune akan wata had'a d'd'iyar kujera shida amaryar ya d'agawa Hamma Aliyu hannu,

Germany
Dad na zaune a parlo hannunsa rik'e da key's d'in mota, Falak ta shigo a gajiye ta zube kan kujera 1 sitter, dad yace "Daughter kin kammala shirye-shiryen?"
Falak tace "eh dad amma hotunan nan za'a tafi musu dashi ne?"
Dad yace "no kawai dai nayi ne"
Dad yagama komai na shirye-shiryen bikin Falak kan kace me maganar auran nasu taje inda basuyi tunani ba,
Ana saura kwana biyu tafiyarta biki biki ya rage saura kwana takwas,
Bata fita Company d'inba tanata shirye-shirye tayi gyaran gashi, da duk wasu abubuwa daya kamata, dad ya kira wata mata balarabiya, kasancewar had'in magungunan da take bawa Falak d'in basu da wasu hamami sai zak'i, dan yawancinsu Madara ne sai kaninfari da sauransu, abin mamaki had'i akeyi na musamman, aikam Falak Tasha a rashin sani dan sam batasan me abinda tasha yake nufi ba.
A ranar ita kadaice aiyuka sunyiwa dad yawa yasa bai shigo da wuri ba, shikuma sheik Abdul-Latif ya d'auka Dad d'in ya rigada ya shigo ne, ya shigo cikin nutsuwa yaji shiru, ko daga bacci ta tashi tasan me muryar dan haka ta amsa sallamar a cikin ranta dan karma yasan tana ciki bare ya dameta da shinshina jiki kamar rat,
Garin bud'e bud'en kofa ne ya bud'o d'akin Falak, tana tsaye tana jera Kaya a trolley sai ta shirya kayan ta wargajesu haka ta dingayi har yazo ya sameta, tana sanye da gajeren wando iya cinya sai rigarta t-shirt black color wandon blue rigar ta rufe mata cibiyarta, daga bakin k'ofar ya hango mazaunanta inda suke juyawa idan taje d'auko wani kayan, ya waro ido tare da toshe baki, kamar ance juya, saboda tsarguwa da tayi taji kamar ana kallonta suna had'a ido tace "me kazo yimin, daga auran taimako ka dawowa da Dad d'ina k'imar company d'insa sai shishigi nifa ka fita a harkata anyi 1 month saura 2 months auranmu ya mutu, Nima na rage oya ka fita"
A inda take maganar tsananin sha'awar kasancewa da ita yakeji, ta nunashi da hannu tace "malam ka fice nace ka fita..!!!!
Waro idanunsa yayi ya taho a hankali ta shige toilet ta 6uya tare da sanya key daga cikin toilet d'in tace "inkaga dama ka tafi, wlhi ina toilet dinnan har k'arfe tara na dare"
Dariya yayi mai sauti kafin yaci gaba da shirya mata kayan har yazo kan bra da pants, abin dariya sai ya rungumesu yana shinshinawa, nikuma nace "oh ashe haka yake shikuma"
A tunaninta ya riga ya fita ne, lokacin k'arfe 5:30pm ta fito tana y'ar wak'a ta gansa zaune akan bed ya d'ora k'afa d'aya bayan d'aya,
"Naci kamar kuturu"
Sheik Abdul-Latif yace "d'an mai-maita mana me kikace?"
Tayi shiru, shi abinma ya bashi dariya ko meye kuturun ma oho.
Yai saurin mik'ewa ya kamota tare da d'orata akan cinyarsa, tana kici kicin k'wacewa yana d'ad'a cakumota,
"Na barka da Allah, bakasan koni wacece ba shiyasa kake abinda kayi ra'ayi, wlhi idan raina ya 6aci zanyi maka abinda baki tsammani ba"
Bai kulata ba ya shafo gashin kanta dayasha gyara yace "Masha Allah kiny kyau my princess saura lalle"
Kamar jiya ta gantsara masa cizo ya saketa ta koma toilet ta rufe tana masifa,
Sai k'arfe 10pm yau dad ya dawo, shikuma sheik Abdul-Latif k'arfe "6:40pm yabar gidan, yana tafe yana tuno irin kewarta da yayi sosai yakejin zeyi missing d'inta idan ta tafi Nigeria,
Kasancewar tayi wanka jiya yasa tanayin sallahr isha'i ta kwanta ko abinci bataci ba, sai zumar magani datasha.
Acan Egypt kuwa Granny Tasha kuka a d'aki tare da tsinewa Abdul-Naseer dan cewa tayi yaci mutuncin ta, ko kad'an batajin dad'in dawo da ita gida sa yayi ba, kwananta uku da dawowa, ta tattaro kan babansu momy da Ummi tace su had'a mata kud'i zata koma gidan Abdul-Naseer,
Abba yace "Hajiya ki hak'ura in aka d'an sake kwanaki sai kije"
Granny tace "banda rainin wayo Dan na tambayeka kud'i shine zaka dinga gayamin magana nifa bana son munafurci, ba k'aramin k'ok'ar nakeyi ba gurin taya Fadwa aiki, kullum Ina kicin kamar tsohuwar kuku yanzu haka nasan tana can tana Shan bak'ar wahala tunda bana nan"
Dayake Ummi tasan hali batace komai ba, ta mik'a mata d'ari biyar tace "to ko kefa, dukda dai nasan a jikin d'ana aka samu"
Abban ya Mik'a mata dubu biyu yace "zomuje in ajiyeki a k'ofar gida fita zanyi"
Cikin sauri ta d'auko akwatin data loda kayanta ta fito tana gyara zaman mayafinta tacewa Ummi, nabaku guri ku sake"
Ummi dai batace komai ba har granny ta wuce gurinda ake ajiye mota ta shiga suka wuce gidan Abdul-Naseer,
Fadwa••
Tashi d'aya taji gabanta nata fad'uwa ta dinga ambaton innalilahi wa inna ilaihir, Abdul-Naseer dake shirin fita aiki yazo kusa da ita yace "haba baby yanaga mood d'inki ya sauya bayan kafin in shiga d'aki ba haka na barki ba?"
Fadwa ta juyo tace "Babu komai kasan yanayin rayuwa"
Badan ya yarda Babu komai d'inba sai Dan bayason ya cika matsa mata, dan haka ya koma ciki yana sake shiryawa.
Sallamar granny dataji ne ya sata waro ido gabanta na tsananta fad'uwa, Dan a tunaninta anyi zamanne tazo gaya mata ko Abdul-Naseer ya saketa ko ya k'aro aure, sai taji granny ta balbaleta da masifa tana cewa "kn wani kafeni da ido kamar na mujiya ko kar6ar kayan kyayi ai kinayi kamar baki San daga inda na fito ba"
Jikin Fadwa a sanyaye ta kar6i jakar kayan ta wuce mata dashi d'akinta kafin ta durk'usa ta gaisheta ta fito, har zatayi bedroom d'in Abdul-Naseer granny ta k'wala mata kira,tazo da sauri tace "ubgo wannan"
Fadwa tayi kamar bataji ba, Granny tace "yau naga gantalewa Banda iskanci in baki maganin dad'in zaman lafiya kice ke ba haka ba?"
Fadwa tace "ai muna zaune lafiya"
Granny tace "ke wawuya yanzu Babu macen da take zama, dukda shid'in jikana ne ke naga kinada biyayya shine nace barin kawo miki domin kid'an dinga yago mana wani abun mu fara safara zuwa Dubai"
Sosai Fadwa taji mamakin surutun granny ta kar6i maganin ta wuce.
Bata nunawa Abdul-Naseer d'inba ta wurga can waje ta window ta wuce gurinda, yana shirin fita tace "granny fa ta dawo"
"Haba?"
"To duba ka gani"
Abdul-Naseer yace "metazoyi mana?"
Cikin shagwa6a Fadwa tace "baby Ina zan sani, kodai ta kawo maka photon budurwar da zaka aura ne?"
Ya had'e rai, ya ja kunnenta da k'arfi sai da tayi k'ara kafin yace "karki sake banason haka"
Hugging d'inta yayi, wannan al'adarsu ce idan ya dawo sai tayi masa oyoyo da gudu take zuwa ta rungumeshi, hakanidan zai fita sai yayi mata hot kisses sannan zai fice,
Ko d'akin granny bai nufa ba ya wuce cikin sand'a har yana k'arawa da gudu, yana zuwa parking space granny ta hango fitarshi, sbda window d'inta yana kallon hanyar gurin, ta dawo ta zauna kana tace
"Kan uba wato saboda tsabar iskanci da munafurci da bawa mace Amana da izgilanci da tsantsagwaron tantiranci shine zai wuce ba tare da yayimin magana ba ko?, wlhi yaci bashi munafuki"
Ta k'arashe maganar tana turo d'aurin d'ankwali gaba,
Acan bedroom d'in Fadwa Sam ta mance granny na gidan, ta fito daga ita sai mini skirt da y'ar riga iya breast d'inta ya rufe kanta babu d'ankwali ta taho tana wak'ar larabawa, Granny na ganinta tahau tafa hannu tana cewa "yau naga tsiya naga arzik'i naga iskanci a had'e, wannan shigar kuma yaushe kika koyota"
Fadwa ta koma ciki jiki a sanyaye ta zumbula abaya tare da fitowa ko kallon inda granny din take batayi ba ta wuce kitchen,
Granny tace "wato badan nasan gidan iyayen yarinyar nanba wlhi zance karuwa Nasuru ya auro, saboda tacewa ta fito haka, wlh matan yanzu suna iskanci mu zamaninmu ai bamuti wannan ta6arar ba...
Ayimin hak'uri..
Kardai ku mance da hadaden littafin WAKE ƊAYA 🥰 ina gaiyatar masoya Falak dasu karantashi kuji abinda labarin ya k'unsa
08141799224 Mom Islam
*FALAK🍒*


Mom Islam



E.O.W


Marubuciyar
Guntun goro
Tsautsayin tauna
Wake ɗaya
Falak
Jinin Abbana
Nancy ƴar ƙarya
Zaɓin shi ce
Yarinya mai taɓargaza
Lamarin ƙaddarar aurena
Diyana
Ladidi ƙauye
Mk mijin delu
Nida yarinya
Macen sirri
Da sauransu.

Page 55-56

Washe gari sheik Abdul-Latif yazo da wuri, ya zauna a parlo tare da kiran number Dad d'in,
Cikin farinciki Dad ya fito daga bedroom d'insa kafin yace "muje part d'in daughter"
Suka wuce gurin Falak, a parlo suka tsaya saboda ganin trolley d'inta da sukayi a ajiye, Dad yace "Bari inyi mata magana"
Dad ya shiga bedroom d'inta yaga wayam, babu Falak babu alamarta, a tsorace ya fara nocking a toilet yaga k'ofar ta bud'e, gabansa ya bada rass, da sauri ya juya ya dawo parlo ya kalli sheik Abdul-Latif yace "ban ganta ba, kozaka Kira mana wayarta, nabar tawa wayar a d'aki"
Sheik Abdul-Latif ya gwada number shiru switch of, yace "dad mu tambayi Mai gadi ko yaga fitarta, dad ya zube akan kujera kafin yace "jeka tambayo shi ina jiranka, sosai dad ya shiga damuwa saboda koda Wasa bata fita a gidan idan ba gurin aiki zataje ba to Ina Falak d'in taje?" Bashi da me bashi amsa dan haka ya yayi tagumi.
Da sauri Sheik Abdul-Latif ya shigo, dad na ganinsa ya mik'e tare da cewa "ya akayi ta fitan?"
Yace be ganta ba wlhi nidai ina ganin muje company ko taje sallama da y'an can,
Dad yabi shawarar sheik Abdul-Latif suka wuce company, canma wayam bata nan itada ko fita kasuwa ba damunta yayi ba, gashi dad ya asalin shiga damuwa ya kasa ta6uka komai.
Ranar dai sun shiga munmunan tashin hankali saboda rashin ganin Falak d'in, Sheik Abdul-Latif dake tsaye rabi hankalinsa na kan TV ya ta6o Dad kafin yace "waccan kamar Falak?"
"Cikin in ina dad yace eh..eh..i..ita..ce"
Dad ya fashe da kuka, yana cewa "meyasa Falak zatayi min haka, meya had'ata da gurin party?"
Suna zaune a gurin har k'arfe tara tayi, Kuma k'arfe 10:am jirginsu zai tashi,, dad ya kalli sheik Abdul-Latif yace "sake kiramin numberta"
Sheik Abdul-Latif ya kuma gwada number cikin sa'a ta shiga, dad yace "bani wayar"
Cikin kuka Falak tace "am sorry dad dan girman Allah ka yafemin ina zuwa yanzu"
Dad ya ajiye wayar ba tare da yace komai ba, saboda bata da number sheik Abdul-Latif d'in, kasancewar da farko muryar Dad d'in taji.
Mintuna ashirin da biyar suka wuce sai gata nan ta shigo direct parlonta ta fara kallonsu, sai kuma ta share zufar data karyo mata tana sanye da sari wanda yayi matuk'ar yi mata kyau,
"Ina kikaje?"
Sheik Abdul-Latif ya tambaya,
"Ina ruwanka?"
Falak ta fad'a tana hararasa,
Cikin fushi dad yace "wato a yanzu kin Dena gujewa 6acin Raina ko, kinfi son ki ganni a kwance gadon asibiti?"
Falak ta fashe da kuka ta mik'awa Dad wayarta tace "ka kalli wannan videon"
Abinda ya faru a jiki shine, ana cewa..
"Hhh, amarya, muddin baki bi abinda mukeso ba wlhi burin mahaifinki bazai ta6a cika ba, mun duba y'an matan Germany kaf babu wacce ta dace da mu sanyata a tallar company d'inmu na had'a sabulun wanka daya wuce ke, idan kika k'i yarda wlhi sai mun kashe mahaifinki, domin kin durk'usar mana da komai d'in da muka shirya"
Dad ya ajiye wayar gefe, shima ya fashe da kuka,
"Yanzu akan haka kika za6i kije duniya kiyi rawa?"
"Fuskar Falak a jik'e da hawaye tace "dad meye amfanin rayuwata bayan ban faranta maka ba, banyi abinda ya zamo haramun ba, iya rawa nayi musu Kuma ban buk'aci da su biyani ba yanzu ba gashi na dawo lafiya ba, kaga zasu barka shikenan"
Sheikh Abdul-Latif ya rungumeta yana share hawayen daya zubo masa, Falak ta zame jikinta a nasa tare da hararasa, dad yace "k'arfe tara da rabi muyi sauri fa"
Bata tsaya sauya kaya ba ta wuce kai tsaye bedroom d'inta ta d'auki abubuwan da zata buk'ata ta lodasu kafin suka wuce airport, fuskar sheik Abdul-Latif wani iri kamar Wanda aka ce masa gobe zaka mutu.
Nigeria
Acan Hall kuwa, an mik'awa Saudar abin magana ta fad'i jawabai game da abokin mijinta,
Ta fara jawabai kamar haka da harshen fulatanci..
Assalamualaikum, meen deebo sobajo ango unn, middo wanna amarya lelle, min mi anndi gurko ma sosai an, a waddi sa'a , gurkumma goddu kirki ummm, oddo balle gurku an sosai , sai dai àddua min be makko, Allah hukke umm judde jam,
Sosai abin ya k'ayatar masu d'aukar photo sukazo zasu d'auka Hamma Aliyu ya dakatar dasu yaje ya kamo hannunta suka zauna,
Shuraim ya nunawa amaryar Hamma Aliyu sukasa dariya, take ce mata soyayyarsu tana burgeshi, gashi har sunada yaro Amma kullum suna k'ara san junansu,
Bayan an sa kid'a anyi rawa, amman banda saudar sbda ya hanata yana rik'e da hannunta a inda suke zaune, aka rarraba gift d'in shaddoji masu masifar kyau da abinci a take away da drinks na gora,
Anyi taro lafiya an watse lafiya.
Switzerland
Safiyar yau beauty ta tashi da matsanancin ciwon mara, tana zaune ko gabanta bata gani, sam takasa koda ihu ne sai hawaye dake sintiri a fuskarta, Arif ya shigo da gadara yana 6alle botir d'in rigarsa, ya ganta a wannan halin, duk iya zalincinsa baya iya jure yaga mutum yana halin rashin lafiya, yai saurin isa inda take, ya tallafo kanta da yayi zafi sosai cikin tausayawa yace "Beauty tashi muje hospital"
Babu musu ta mik'e tana sanye da riga da wando ya kamata sosai Arif ya cire mata su yasa mata doguwar riga, Niko nace ashe yana kishinta duk iskancinsa,
Suna zuwa hospital aka bata taimakon gaggawa tare da yi mata gwaji, anan ne aka tabbatar masa da tana d'auke da juna biyu na wata biyu, mamaki ya kama Arif, a zuciyarsa yace "kodai tun lokacin da nayi mata fyd'e shine ta samu ciki?"
Daga k'arshe ya duba takardar da aka bashi, yaje ya biya kud'i kafin yaje ya kar6i magani akayi masa bayanin kar a dinga 6ata mata rai, kana kar ta dinga d'aukar abu mai nauyi daga k'arshe sukace tana buk'atar walwalah a tare da ita,
Koda suka koma gida, yaji soyayyar cikin jikinta na dad'a shiga ransa, har wani shauk'i yakeji, ga kulawa ta musamman da yake bata, ammafa idan buk'atarsa ta motsa sai dai yaje ya sami matan waje haka yakeyi har lokacin da cikin nata ya fara fitowa,
Momy bata sake zuwa gidan ba koda aike ita a dole tayi fushi, haka ma beauty bata ta6a marmarin zuwa gidan momyn ba, burinta bai wuce ace cikin dake jikinta ya 6are ba, da tafi kowa farinci, saboda tsanarsa da Allah ya d'ora mata"
Maleek••
Kamar inda bokansa ya fad'a yau litinin yau zaiyi kud'i naban mamaki tunda sun cika sharud'a, su uku Manaf da Arif dashi kansa, kowa ya kwanta da namiji d'an uwansa kasancewar anyi aikin bokanci dukkansu biyun badan sunso hakan ba, k'arfe 2:pm su Maleek suka fito daga masallaci ya gaiyyacesu zuwa ke6a6en gidansa, suna shiga suka zauna a parlo ya shiga ciki sai gashi ya fito musu da kud'ad'e masu yawa wanda idan suka tsaya k'irgawa sai sun 6ata lokaci, sai dai bank, Manaf ya zaro ido jikinsa na karkarwa yace "a Ina ka samu wannan kud'ad'en Yaya?"
Maleek ya shek'e da dariya kafin yace "bana buk'atar bincike ko doguwar magana, wannan naka ne wannan na Arif kuji dad'inku"
Arif dama ba yanzu bane sabon rik'e ire-iren kud'ad'en a gurinsa, sai dai zai iya cewa "wannan sunfi na ko yaushe yawa"
Bayan sunci sun k'oshi a gidan Maleek d'in suka kama hanyar zuwa gida, ko wanne rik'e da jakar kud'i a hannunsa.
Nigeria, airport..
Ummu Saudart da Munira da Hibba dukkansu sunyo ayari zuwa airport suna zaune a inda aka tanadar,
'Daga idon da Ummu zatayi taga jirginsu Falak na sauka, zubawa mutanen da suketa fitowa idanu tayi tanason taga fitowar Falak,can hangota tana sanye da sari, ba k'aramin kyau tayi ba, ta lullu6e kanta da mayafin tana ta murmishi, kasancewar ta hango mahaifiyar tata nata raba idanu, Su Saudart ma sun hangota, tana isowa da ta kusa zuwa gurinsu ta rugo da gudu ta rungume Ummu tana dariya, wani hawayen farinciki ya kwaranyo wa Ummu suka shiga mota suka wuce gida.
Abin mamaki, an Zagaye gidan da furanni sosai gidan yayi kyau ga walimar cin abinci da aka shirya, ga mamakin Falak taga gidan ya cika da y'an uwan dad da na Ummu duk sun hallara suna jiran shigowarta,
Driver na parking suka fito, mutanen da suka taru sunajin k'ugin mota sukayo waje da sauri ana cewa *"Happy birthday to you Falak* sai a lokacin ta tuna ai yau ne birthday d'inta ashe shiyasa Dad ya matsa ta taho,
Suna k'arasawa ciki kowa ya fara kallonta, sai cewa sukeyi tayi k'iba takara haske Takoma kamar ka ta6ata jini ya fito, a tak'aice dai ta koma kamar balarabiya,
Ko hutawa batayi ba aka fara gudanar da bikin birthday party d'inta aka yanka cake me d'auke da sunanta anci ansha an goge wuya,
Egypt
Har k'arfe 9:pm Abdul-Naseer bai dawo ba, Fadwa ta gaji da jiransa ta koma d'akinta ta kirashi yace "yakusa shigowa tayi hakuri"
Kamar granny tasan lokacin da zai dawo ta d'ibo bargo da pilo ta dawo parlo ta kwanta akan kafet, sallamarsa da taji ne ya sata mik'ewa zumbur tare da cewa "sannu da dawowa, kaga ni dana damu dakai gashi nazo na zauna ita kuwa ko oho tanacan tana sharar bacci"
Abdul-Naseer yayi murmishi kafin yace granny ga kaza please kiyi hak'uri ban taho miki da tuffa ba"
Jikin granny na rawa tace "d'an albarka shiyasa nake sonka, ai akwaika da hankali ga kyakkyawan hali kamar na mahaifinka Allah ya saka da alkairi, ammandai ka siyowa matarka ko?, karta zo ta ganni taji haushi kasan yaran yanzu mugun hali garesu kishi harda iyayen miji nikuma banason wata matsala ta giufta muna zaune lafiya daku"...
*FALAK🍒*

Mom Islam

Arewabook@momIslam11

E.O.W

Page 57-58

Abdul-Naseer yayi murmishi kafin yace "ai Fadwa batacin nama"

"A'a kace tabar dad'i shiyasa duk zuwan da nakeyi sai inga tayi miya ba nama, kumafa ina ga kana siyowa ko tana tattarawa iyayenta ne?"

Abdul-Naseer ya mik'e kana yace "zan shiga ciki sai da safe"

Granny ta wurga masa harar tare da turo baki gaba.

Kai tsaye d'akin Fadwa ya shiga tare dayin sallama ta rungumeshi da sauri ya d'agata sama yana cewa "naji ki fayau Ina tunanin yau bakici komai ba"
"Naci"
Fadwa ta fad'a tanayi masa murmushi,

Tunda taga granny tazo ta dena ajiye masa abinci a dinning sai dai ta shigo dashi bedroom d'inta ta ajiye masa akan table saboda sa ido irinna granny dakuma gani Babu k'yalewa.
Nigeria••
Sai wajen k'arfe 9:30 Hamma Aliyu yazo ya d'auki Saudart suka wuce gida, yana tsokanar Falak.
Washe gari da ragowar y'an uwan Ummu biki ya rage saura kwana biyar, anata hada hadar biki anyi anko yakai kala biyar iyaye da nasu y'an mata da nasu yayu da nasu ka kanni da nasu sai Kuma na k'ananan yara suma da nasu,
A y'an kwanakinnan Sam Saudart dasu Munira basu da zama, Hibba kam rufe shago tayi saboda bama zuwansa takeyi koda yaushe ba,
Sunje kasuwa sun siyo hanbag mai hannu wacce idan mutum ya rataya tsayin hannun zai kai kwankwaso a cikin ko wacce ansa Zobunan azurfa masu tsadar gaske wanda Dad ya Aiko dashi da turare shima ba d'an Nigeria ba, kafin zuwan Falak.
ledar walima Kuma ansa turaren tsinke irin mai guda d'ari sai kasko shima Mai kyau.
Harda ledar fulani day suka bugo Wanda Falak ta aiyyana a ranta bazataje ko guda d'aya ba, bama zata fara gaya musu ba bare hankali ya tashi.
Ana biki saura kwana biyu, Falak ta sake Shan gyaran jiki bayan Wanda akayi mata a Germany sosai ta fito kamar wata balarabiya tsabar kyau, ga haske da fatarta ta sakeyi gunin sha'a wa, a yau Friday sukaje lalle da wani gyaran kai bayan Wanda taje akayi mata, lallen yayi masifar yi mata kyau, mai zanen ja da bak'i har kafarta, ranar asabar dad da Imam da sheik Abdul-Latif da sauran abokan arziki suka sauka a Nigeria, iya dad ne kawai bak'ar fata, dukda shima d'in bawai bak'i bane amma a gabansu dole zai kasance bak'i,
Ummu Tasha ado abin ba'a magana kamar ba ita ta haifo su Saudart ba tayi kyau sosai, su Dad na isowa suka kirata ta tura driver ya kwaso su,kai tsaye dad yace a wuce dasu guest house d'insa kana yasa ayi musu take away na abinci a babban restaurant na garin Gombe, cikin hukuncin ubangiji kafin su isa abincin ya isa, katafaren gidan dad kenen wanda tsakaninsa da gidan Ummu yakai nera d'ari, gidane had'ad'd'e wanda kullum sai anyi mopping an tsaftaceshi, bayan sun isa sun huta dayake su biyar ne, ko wannensu yayi wanka ya sauya Kaya suka nufi dinning room Dan cin abinci, sheik Abdul-Latif yace "Sheik Abdul-Latif ya bud'e Abincin Wanda a k'alla zeyi na 30k sheik Abdul-Latif yace "Imam wanne kakeso?"
Imam yayi murmishi yace "abinci ba kalar namu ba, da yarensu suke maganar shikuma dad yana bedroom yana waya da Ummu.
Imaam yakai lomar abincin bakinsa ya lumshe ido yana Santi.
Acan gidan Ummu kuwa bak'inciki fal Cikin Falak cewa take "meya kawo sheik Abdul-Latif Nigeria wace alak'ar suka k'ulla dazai kashe kud'in zuwa?"
Bata sake Ummmu taji na bare ta fuskanci fad'a da gareta Dan haka tayi shiru da bakinta amma ta ke6e kanta a d'aki.
Washe gari da misalin k'arfe 1:30pm Falak tasha makeup tayi kyau sosai ranar tasa wata riga Tasha ado daga ganin rigar ma zakasan taci kud'i,
A hotel akayi order abinci sai dai adinga kar6owa su Ummu ko tukunya basu Dora ba sai masu wanka da sauransu.
K'arfe 2:pm dubban al'umma suka sheda d'aurin auran Falak da Sheik Abdul-Latif lakadan ba ajalan ba, idan kaga mutanen da suka halaci d'aurin auren sai kayi mamaki saboda yawansu, duk da dady ba mazaunin Nigeria bane, tunda aka dawo d'aurin auren Falak na gidan Saudart gabanta sai dukan uku-uku yakeyi tarasa dalilin hakan, Amma ta rubuta a ranta auren wata biyar zasuyi ko wata uku kafin sheik d'in ya gama dai-daita company d'in dad,
Anyi rabon gifts sosai abin Kuma ya burge mahaifin Sheik Abdul-Latif yasa dad ya rakashi banki ya ciro kud'i ya diga sadakar dari biyar har na dubu ashirin,
Bikin Falak da Sheik Abdul-Latif ya kafa tarihi, kowa yaga bature ko balarabe sai abin ya girgizasu, tambayar tasu anan shine dama balarabe yana auran bak'ar fata?
Acan guest house d'in Dad, iya sheik Abdul-Latif ne ya dawo ya kwanta a bed zuciyarsa nata bugawa da K'arfi kamar zata fito, ya rasa ta inda zai fara misalta ranar yau to shikuma fad'uwar gaban da yakeji na meye?"
Cire kayan da be saba sawa yayi ba, wato

Please Login or Register in order to submit comment